Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fakaice Batool ta xabgawa Ma'u harara ta dawo ta dauki maganin tasha tabar wajen da sauri kada xuciarta ya buga





A kwana a tashi asarar mai rai, yau sauran sati daya bikinsu Ma'u, duk wani tanadi an gama Mami da Ummi sunsa kaimi wajen gyara yaransu ga Ammi ma tana basa nata gudumawar

Kada kaso kaga yadda Ma'u ta koma ta kara cika fatarta ta goge tayi haske sai sheki take, abunka da farar mace sai haska waje take

Goga Bature kam ya gama fita hayyacinsa ya rame ya koma kamar wadda yayi jinya (koda yake yayi jinyar xucia), damar yaya lfyr kora bare ya fara xayo miskilancine yaci Uban nada

Koda Ummi ta kirasa maganar komawar Zahra cewa yayi ya hakura amma tayi xamanta sai bayan biki

Bai so xuwa bikinba amma baida excuse ne yasa yanke sai ranar alhamis xaixo ana gobe daurin aure


Allah sarki Batool tayi kokari ssai wajen danne xuciarta ta fawwalawa Allah komai tashiga cikin ribibin bikin aka dama da ita ssai ssai


Bikin axo a gani akayi tun ranar litinin aka fara event na biki, ummi da 'yan uwanta sun fito sun nuna su isassune sunyi ruwan kudi, yayinda a gefe guda sukewa Ma'u daria don sunsan kawai bayyanowa xatayi a wajen event amma daurin auren bada ita xa'ayiba


Ranar alhamis da yamma Bature ya iso, duk wadda ya gansa sai ya bincikesa ko ya tashi daga jinyane, wadda yake ganin damansu baya tanka musu wadda kuma yake ganin damarsu yace "eh"

Mami datasan dawan garin ko tambayarsa batayiba ido kawai ta xuba masa


Sai bayan ya dawo daga sallar isha'i ya shiga wajen Ammi don daxun mutane sunyi yawa a part dinta shi kuma baison hayaniya


Yanxun ma akwai mutane amma basu kai na daxun ba, ratsasu yayi ya kamar baisan wasu daga cikinsu ba ya wuce direct bedroom na Ammi

Bbu kowa a bedroom din karar ruwa a toilet ne yasa Bature nade kan bed dinta yayi kwanciyarsa yana jiran fitowar Ammi daga toilet don duk xatonsa itace ke wanka

Kurawa pic din Ma'u dake manne a bangon dakin ido yayi, yanajin sonta na kewayawa dukkan gabbansa


Fitowa Ma'u tayi daga toilet daga ita sai dan karamin towel dako cinyarta bai kaiba tana rausaya jikinta wai ita tana practical abunda mai Falmata ta koya mata

Tunda ta fito Bature ya kura mata ido ko kiftawa bayayi, ta gama tafia dashi, idan badon ya mata farin saniba daxaice ba ita bace, take kasala ya mamayeshi ya kasa tabukawa kansa komai


Ma'u ko bata san ma da akwai mutum dakinba, Salle tayi ta fada kan bed din tanacewa

"Ayyah bed dinmu da Ammina bari na miki kwanciyar bye by......."

Sauran maganarne ya makale mata sakamakon fadawa kan Bature datayi

Bude bakinta tayi da niyar sa ihu, don ta gama tsorata

Cikin xafin nama Bature ya hade bakinsu don shine kawai mafita kada ta tara musu jama'a, gashi kuma ta danne duk hannunsa

Bada niya yayi hakanba amma tunda yaji lallausar lips dinta cikin bakinsa sai kai ya fara sha kamar lollipop

Duk da a rude Ma'u take ga tsoro ya mamayeta amma bai hanata jin dadin yadda yake tsotse mata lips dinba

Take jikinta ya fara sakewa ta kwanta lip a jikinshi, ita duk xatonta Abdallah ne

Sanda Bature yasha lips dinta iya son ransa kan ya xare bakinsa cikin nata nanma don ya fara hawa network ne yana tsoron kada ya xarce

Yana sakin bakinta idonta a limshe ta maida kanta kirjinshi ta kwantar tana sauke lumfashi a slow

Shima Bature haka takasance ga numfashinshi

A kasalance tace

"Hayati kanada gaggawa, gobe fah xa'a daura na xama taka, gobe ya warhaka muna tare, wai ka manta a dakin Ammi muke kada taxo ta samemu ta yadamu"

Kalamanta ba karamin bakantawa Bature sukayi ba, yadda yake sontan nan har tana wani maganar Abdallah

A harxuke ya tureta daga jikinshi ya mike rai bace

Firgici, tsoro, rudewa su suka ma Ma'u dirar mikiya da idonta suka mata toxali da Bature, jikinta har rawa yake

" Uban me ya kawoki jikina, kin koma 'yar iska ko, yau xan magantaki wlh kada kiga xakiyi aure"

Take hawaye ya fara ambaliya a fuskarta

"Don girman Allah Ya Bature kayi hakuri wlh ban san kai bane kuma wlh ba haka nakeba"

"Shut up"

Ya daka mata tsawan da ya kara firgitata

Tsaki yaja ya fice daga dakin rai bace, ajiyar xucia Ma'u ta sauke tana godewa Allah da bai daketa ba


Dole ta koma toilet ta sake wanka ta fito ta shirya ta koma kan bed din, pillow da Bature ya dora kansa ta janyo kamshin tularensa na manne a jikin pillow, kan hancinta ta dora pillow tana jin kamshin turaren ta limshe idonta, take abunda ya faru ya shiga dawo mata

Murmushi ta sake tace

"Allah yasa Ya Abdallah ya iya irin wannan kiss, ashe Anty Zahra na diban dadi, Ya Bature ya hadu amma muguntarsa ce ta batasa"

Daga pillow taji anyi daga hancinta, rai bace ta bude idonta ta waresu kan Batool

Xama Batool tayi a gefen gadon ta mikowa Ma'u jug dake hannunta tace

"Gashi inji Mami wai ki shanye yanxu"

Kwace pillownta Ma'u tayi tace

"Allah baxan iya shaba na koshi yanxu na gama shan na Ammi"

Baki Batool ta tabe tace

"Nidai Mami tace na dawo mata da jug nata bbu komai ciki"

Fuskar tausayi Ma'u tayi tace

"Pls Sis ki shanye sai ki kai mata"

Baki Batool ta washe tace

"Baxai gagara ba ai daga gani xanyi dadi"

Bbu bata lokaci Batool ta shanye had in tass tayi gaba


Part dinsa Bature ya kulle da key ya kashe duk wayoyinsa don bayason damuwar Zahra

Kaurace masa bacci yayi sai tunanin Ma'u da albarkatun dake jikinta yake

Ga xuciarsa na kunan rashinta daxaiyi

Kuka mai isansa yayi, ya rarrashi kansa yaci gaba da tunanin Ma'u



JUMMA'A

Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, yaune akasa ranar daurin auren su Ma'u

1:10pm Abba ya gama shirinsa tsaf cikin manyan kaya Mami data tayishi shiryawa ta feffesa masa tulare

"Mijinah kaga yadda ka fita kamar Kaine Angon"

Mami tayi maganar tana karewa Mijinta kallon

Murmushin jin dadi Abba yayi yace

"Nagode Matata"

Tare suka jera har falon

Suna fita Abbu na shigowa shida Ummi

Kallo daya xaka musu ka karanci tashin hankali a fuskarsu

"Lfy kuwa?"

Abunda Mami ta tambaya

"Ina kikaga lfy Fateema xamu hada haramci idan badon Allah ya taimaka Hawwa ta fadamin yanxu ba"

Cesar Abbu na matsowa kusa da Abba

"Haramci kuma"

Abba yayi tambayar yana duban Abbu don neman karin bayani


Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻

INA ALFAHARI DAKU

Zauren Biebie Isa (ZBI)
Tapital Pulaku
Rufaida Omar Fans (ROF)
Kainuwa Writer's Association
Ummu Subay'a Fans
🅿herty Novels
KanuShuwa
Proudly Kanuri
Gembu Pullo

1⃣4⃣

"Yanxu Hawwa ta sameni take sanardani, wai ta shayarda Ma'u lokacin tana karama"

A tare Abba da Mami suka xauna kan cushion cikin jimami

A hankali Abba ya dinga maimaita
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"

Abbu da Ummi ma xama sukai kan cushion

Abbu yace

"To yanxu Yaya mekake gani xa'ayi, ko a daura auren Hisham da Shukrah kadai"

Cikin sauri Ummi tace"a'a hakan bai kamata ba tunda Allah ya axurtamu da yara mata mexai hana mu hada shi Abdallah da Zainab ta wajen Anty Turai"

"Idan munyi haka munyi gaban kanmu, kuje kawai xamuyi shawara da Ammi, bukatarki baxata gagaraba Hawwa, Fateema kice ma Ammi munada magana da ita"

Cewar Abba yana cire hulan kansa

Tare Mami suka bar falon da Ummi, dadi ssai Ummi taji don a ganinta komai ya tafi daidai


Farar gare da jomfa Bature ya saka hula, takalmi da agogo duk farare yasa, feshe jikinsa yayi da tularensa na Giant ya kuma dora da Amirul Arab

Cikin takun katsaita da ixxa ya fito daga part dinsa ya nufi cikin gida

A hanya yaci karo da Balarabe dauke da Amal

" woow My Man kaga yadda kayi kyau kuwa kamar kaine Angon, koda shike Angon ne don nasan jiya da daddare ka angonce da Zahra"

Harara Bature ya watsawa Balarabe

"Diyarkace fah a hannunka, kasan yaran yanxu da konennen wayo"

Daria Balarabe yayi yace

"Gaskia kam yanxu ma take cemin na kaita wajen Ammi ta bata fura da Nono"

Hango Batool Bature yayi tana faman shiga part din Ammin

"Mikawa Batool mana ta kaita mu wuce masallaci to 2fah"

Kiran Batool Balarabe yayi ya mika mata Amal suka wuce masallacin anguwarsu kuma anan xa'a daura auren

Bbu abunda ke tashi a bedroom na Ummi sai sautin Shewa da daria

Lubna tace

"Anty Hawwa ya kamata Ku bani kyauta fa"

Hajiya Turai da tayi kwanciyar katsaita kan bed tace

"Kyautarki ta musammance Autarmu"

Ummi dake feshe jikinta da tulare tace

"Anty da fatar kin gyara Zee don Abdallah na ya kwashi gara"

Daria sukasa hadda Shewa

Zahra dake kwance gefen Hajiya Turai tace

"Yanxu duk gyaran da sukama Ma'u ya tashi a banxa, Allah sarki har taban tausayi"

Wani dariar ta suka kuma sawa
Ummi tace

"Next week sai ki tattarata Ku koma da ita don ni baxan juri iskancinta ba"

Dafe kirji Lubna tayi tace

"Da Ma'u xasu koma, lalle kunason dibo ruwan dafa kanku, wannan shegiyar yarinya mai karuwar jikin xata xauna da Zahra ga kuma Bature a gefe"

Baki Zahra ta tabe

"Na nawa kuma ai a wajenmu take, tare muka dawo, wlh duk karuwancin jikinta ko kallo bata ishi Ya Bature ba, shifa bbu ruwansa da mata"

Harara Hajiya Turai ta xabga mata tace

"Hmmm namiji ko? Ai maxa basa raina mace komin kankantarta balle kuma Ma'un nan, don haka kada ki yarda ki koma da ita"

"Toh"

Kawai Zahra tace tana kara lafewa akan bed din

A extra bedroom dake part din Ammi Shukrah da Ma'u tare da kawayensu suka kebe kansu sunata hira, anan Batool ta samesu ta sumduma hirar

"Mutumiyata kinga yadda kika kika haskaka kuwa, lalle Ya Abdallah xai kwashi garabasa"

Cewar wata kawar Ma'u

Fari da ido Ma'u tayi tace

"Kuma xanci ubana a hannunsa, wlh duk tsoro ya cikani yadda Salma taban lbr"

Daria suka sa hadda Shewa

Salma da itace kawai matar aure cikinsu tace

"Wlh xamama sai ya gagareki idan kika samu jarabebbe"

Ido Ma'u da Shukrah suka ware

Shukrah tace

"Nashiga 3 duk kuma yana jiranmu"

Dariar mugunta Salma tasa tace

"Rass yana jiranku"

Tsoro ssai Salma ta shiga basu tana musu dariar mugunta



Babban masallacin ya cika ssai da mutane har bbu hanyar wucewa manyan attajirai, 'yan siyasa da 'yan kasuwa duk sun samu hallarar daurin auren


Bature da Balarabe tare da abokanayensu suna xaune a wajen masallacin suna jiran daurin auren kamar daga sama sukaji maroki nasanarda

"An daura Auren Muhammad da Asma'u, Hisham da Shukrah, Abdallah da Batool"

Kamar mutum mutumi Bature ya daskare jira kawai yake ya tashi daga baccinda yake don duk xatonsa mafarki yake

Jijjigasa Balarabe yayi yace

"Wai meke faruwane Bature pls kamin bayani"

Sai lokacin Bature ya gane ba mafarki bane xahirine

Ture hannun Balarabe yayi daga jikinsa ya mike ya shiga cusa kansa yana neman wadda xai tabbatar masa gaskiar abunda yakeji

Karo yayi da Abdallah daya gama fita hayyacinsa idonsa ya kade yayi ja yana tangal tangal kamar xai fadi ga Hisham kuma a bayansa yana kokarin cin masa

Faduwa yayi jikin Bature ya fara kuka mai tsuma rai

Rumgumeshi Bature yayi cikin tausayawa ya jashi suka bar wajen

Emergency Family meeting aka kira

Bbu wadda bai hallara a falon Abba ba

Ummi sai murmushi take dataga Abdallah na kuka, axatonta an daura auren da Zeece

Su Ma'u kuma mamakine ya kamasu ganin Abdallah na kuka don basuda lbrn abunda ya faru

Da sallama Abba ya fara daga bisani ya dora

"Nasan wasu sunji duk abunda ya faru wasu kuma basuda masaniya, da wadda sukaji da wadda basuji ba xan kara maimatawa, abisa bayanin da Hawwa ta mana na ta taba shayarda Ma'u hakan ya kawo haramcin aure tsakanin Ma'u da Abddallah, Ammi ta yanke hukuncin bawa Abdallah Batool ta kuma hada Ma'u da Bature, maganar danake yanxu an rigada an daura auren"

Ihu Ma'u tasaka yayinda Zahra ta biye mata itama tasa ihun

Ummi kam ta gaxa cewa komai wani abune ya tokareta a makoshinta


Rintse ido Batool tayi tana godewa Allah

Dakyar Bature ya danne duk farin cikin daya taso masa

"Wlh baxan xauna da Ya Bature ba, so kuke ya kasheni, kawai ya sakeni dana xauna dashi gwara na mutu"

Cewar Ma'u tana kuka hadda sheshsheka

Zahra ma cikin kuka tace

" wlh ba'amin adalciba ya xa'ayi a bawa Ya Bature Ma'u baicin ga Ya Balarabe ni gaskia baxan xauna da Ma'u a matsayin kishiyata ba, yarinyar data xauna a gabana na riketa kamar diyata"

Bugu Ammi takaiwa Bakin Zahra tace

"Kinci ubanki Zahra, taya Ma'u ta xama kamar diyarki ta ina kika haifeta shegiya, to ko ki mutu ko ki rayu Ma'u dai matar Baturene ko shi Baturen baida damar cewa baxai karbi Ma'u a matsayin mataba"

Dakyar Ummi ta iya bude bakinta tace

"Gaskia an nuna son kai cikin lamarin nan, dolene sai Ma'un tayi aure kodon anga Zahra bata haihuba ne aka kulla manakisa aka hada Ma'u da Bature don ta haihu, kuma ai na nemi alfarmar a hada Abdallah da Zainab aure amma akayi burus da maganata"


Murmushi Ammi tayi tace

"Hauwa tun kan a haifi ubanki aka haifeni, kinga nafiki sanin dunia na fiki sanin makirci da munafurci iri iri, xan iya rantsewa da Allah baki taba shayarda Ma'u ba, kawai makircinkine da 'yan uwanki kuka kisa wannan xancen don Abdallah ya auri Zainab ita kuma Ma'u ko oho, to ta Allah batakiba, Allah ya nuna ikonsa kaikayi ya koma kan mashekiya"

Kukan borin kunya da hauka Ummi ta saka tace

"Bayan duk abunda akamin kuma xa'amin sharri, nidai an tsaneni a gidan wlh don ni bare"

Mikewa tsaye Abdallah yayi yace

"Ummi kin cuceni, akan son xuciarki kika rabani da Ma'u dolene auren Zee, nagode Allah da ya hanaki farin cikinki kamar yadda kika hanani"

Daga kafarsa yayi don takawa yabar falon, take jiri ya dibeshi ya fadi a wajen a tsume

Kuyi hakuri da wannan

Yau banajin typing

Ummu subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻


Ina taya BATOOL MAMMAN murnar kammala littafinta na KASHE FITILA( Kunna Fitila injimu 'yan ROF group😜)
Gaskia kin
Fadakar
Nishadantar
Wa'axantar
Damu

Ina miki SON SO BATOOL

Xamuyi missing na son so



1⃣5⃣
"Kan uban nan, wlh baxai taba sabuwa ba, karyanki tasha karya Hawwa, ni xa'a ciwa mutunci a toxartani a idon dunia, har kinada bakin cemin inyi hakuri to idan ni nasan hakuri Zee batasan hakuri, son danki baxai kashemin diya ina kalloba dole kisan yadda xa'a"

Hajiya Turai ce ke wannan dirin yayinda ta tura dankwalinta goshi irin bbu mutuncin nan

Ummi dake kukan bakin ciki tace

"Da wanne xanji Anty da cin mutuncin da akamin ne koda kishiyarda akawa Zahra ko kuma da ciwon Abdallah gaku naki bala'in, pls barni najj da abunda ke damuna, naki nafilane"

Lubna da Zahra ke kwance kan cinyarta tanata sana'ar kuka tace

"Don Allah Anty kuyi hakuri mu xauna mu sulhunta tsakani muyi facing abunda ke gabanmu"

Wani uwar harara Ummi ta sakar mata tace

"Rufewa mutane baki ba duk ke kika cucemu ba, kika bamu gurbataccen shawara, Gashi yanxu mu bbu wan bbu kanin, kin samu a halin kanikayi"

Cike da mamaki Lubna ke duban Ummi tace

"Au hakama xakice, ubanwa na janyo gidana nace yaxo na bashi shawara, ba Ku kuka wanke sahunku kuka xoba, sai Ku dau kaddara haka Allah ya tsara, ga duka ga tsinka jaka"

Tana gamawa ta ture kan Zahra a cinyarta ta mike ta tattari kayakinta tace

"Na barku lfy,kuma duk abunda ya kara samunku bbu ruwan Lubna"

Itama Hajiya Turai daukar jakanta da mayafinta tayi tace

"Wlh wlh kinji na rantse duk inda xanshiga sai na shiga don nemowa diyata farin cikinta, kuma gaba dake har makara, ko bakin cikin kishiyarda aka dirkawa diyarkima ya isheki, abun kunya abun ashsha first in family Zahra ce aka tabama kishiya"

Ummi dai bbu bakin magana bakin ciki ya hanata cewa komai, haka tanaji tana gani Hajiya Turai da Lubna suka gama ci mata mutunci sukai gaba, ita kuka Zahra kuka



Birgima Ma'u keyi a bedroom din Ammi tana kuka kamar xata hadiye ranta, jama'a ssai ta tara sai hakuri ake bata, amma batajin na kowa sai kara volume take

"Allah ni baxan xauna da Ya Batureba nida Ya Abdallah xan xauna shine Mijinah"

Ammi da abun ya isheta ta fice dakin ta dau waya ta kira Bature yaxo yayi maganinta


Bbu jimawa sai ga Bature, kowa na ganinsa yabar dakin

Itako Ma'u bata sanma ya shigoba sai ci gaba da kukanta take, duk xatonta sun gaji da jin kukan ne suka waste

"Ke"

Bature ya daka mata tsawa

A firgice Ma'u ta tashi ta xauna tana raba ido

Ganin Bature ba karamin raxanata yayiba, xare mata ido yayi yace

"Kukan nan ya tsaya anan ya kuma kare anan, idan na kumajin kinyi kuka"

Kada kansa yayi irinta mugunta

"Kinsan sauran, kuma gobe as early as possible ki shirya xamu wuce Abuja"

Ko kwakwaran motsi Ma'u ta kasayi, tsoro duk ta lullubeta Allah Allah take kada ya bubbugeta

Bature na gama maganarsa ya fice daga dakin, dakyar Ma'u ta mike ta shige toilet kanta na tsarawa ga wani jaririn xaxxabi na damunta
*Ma'uBature*



A hankali hawaye ki sauka kuncin Batool dake xaune a bakin gadon da Abdallah ke kwance yana baccin wahala

Ta rasa hawayen farin cikine ko tausayin halinda Abdalkahnta ke ciki

Ko wani second godia takewa Allah daya bata farin cikinta

Ta gaji ga bacci takeji ga Ammi tace bbu wadda xaiyi jinyarsa sai ita

"Ma'u, Ma'u, Ku barmin Ma'uta"

Abunda Abdallah ke fada kenan bayan yadan bude idonsa

Cikin sanyin jiki Batool ta matso daf dashi ta fara kiran sunanshi

"Ya Abdallah, Ya Abdallah"

A hankali ya ware idonsa kan Batool

"Batool ina Ma'u, da gaske an daura mana aure, Ma'u ta auri Ya Bature? Pls Batool kicemin karyana, kicemin Mafarki nake"

Kuka mai tsanani Abdallah ya fashe dashi kamar mace, itama Batool biye masa tayi tana tana tayashi

Sanda sukai mai isarsu kan ya umarceta ta tallafa mishi takaisa toilet, bbu musu ta tallafa masa tana kaisa ta fito ta ja mishi kofa

Wanka yayi hadeda alwala ya fito daure da towel a kumkuminsa, tsadda kanta kasa Batool tayi don kunya ya lullubeta

Daukar kayan daxaisa yayi ya koma toilet din ya kintsa, salolin da suka wuce mishi ya rama, yayi addu'a mai tsawo hadda kukansa


Haye kan bed din yayi bayan ya kashe wutar dakin, ya dubi Batool dake xaune kan cushion yace

"Zoki kwanta"

A sanyaye tace

"Ni nan xan kwanta"

Shima a sanyaye yace

"Pls Batool don't let me to shout at you"

Jiki bbu kwari taxo ta haye kan bed din, nesa dashi ta kwanta

"Allah nagode maka da wannan jarabawar"

Abdallah ya fada yana rintse idonsa

Kuka ssai yaxoma Batool, don ssai Abdallah ya mugun bata tausayi, kasa danne kukan tai ya fito fili


Shima Abdallah tausayi ssai Batool ta basa, shi a ganinsa a xakunceta

A hankali ya mirginota jikinsa, wani shock dukkansu sukaji, rumgumeta yayi a kirjinta yana shafa gashinta kanta

A kasalance yace
" kiyi hakuri Batool nasan an xalunceki, mu barwa Allah komai shi xai saka mana"

Lumshe ido Batool tayi tanajin ddin yanayin

A xuciar ta tace

" an.xalunceka dai Malam, Batool kam faranta mata akayi"

A haka bacci mai dadi ya daukesu kowa da abunda ke ransa
*BatooAbdallah*



Washegari 6:20 Bature ya shigo Part na Ammi, kan sujud ya sameta tana laximi, Ma'u ko na gefenta tana aikin kuka da magiya ita baxatabi Bature ba sai dai ya saketa, tana ganisa tayi tsit ta hau share hawayenta

Murmushi Ammi tayi tace

"Ja'ira kici gaba mana"


Xama Bature yayi suka gaisa da Ammi

A tsorace Ma'u ta gaidashi

Kamar baxai amsaba yace

"lfy da fatar baki hada kayankiba"

"Duk na hadasu wlh"

Ma'u ta fada murya na rawa

Gyara xama Ammi tayi ta fuskanci Bature tace

"Turawa kada kaga an dau yarinyar nan an baka ta zama baiwarka ba kuma, ka riketa tsakani da Allah kamar yadda ka rike Zahra bbu duka bbu xagi, na tabbata yadda take tsoronka xata bika sau da kafa"


Baki Bature ya tabe yace

"Kinfa san kun xalunceni kun hadani da wannan fitinenniyar, nayi hakuri ban muku gardamaba kuma kina neman ki fadamin magana, sai dai batamin abuba babbala yarinya xanyi tunda kinsman yadda nake kika auramin ita"

Tsaki Ammi taja tace

"Ka dafata ma kasha bbu ruwana marainiyace Amanar Allah"

Baibi ta kan maganarta ba ya ciro wayarsa ya kira Jidda, tana dagawa yace

"Kije ki kiramin Zahra taxo mu wuce"


"Toh" Jidda tace


Rashin samun Zahra a Palo ne yasa Jidda shiga bedroom din Ummi direct

Jugum ta samesu ko wanne idonsa ya kumbura yayi ja

Ssai ta tausayawa Zahra da Ummi

Durkusawa tayi ta baida Ummi

A kasan makoshi Ummi ta amasa

Jidda bata damuba ta dubi Zahra tace

"Sis Ya Bature ne ya aikoni wai kixo Ku wuce"

"Bbu inda xata, ya tafi da fitsarerriyar Matarsa, tunda haka kuka fiso, wai ni Hawwa Dangin miji dai dangin Mijine ko daga tsasonsu kake, dubi yadda kuka rintse ido kuka ciwa Zahra mutunci da aurawa Bature Ma'u don kunga bata haihu, xan baku mamaki nima xan sanya Balarabe ya auri Zee muga ta tsiyarku kuma kuji inda dadi"

Mikewa Jidda tayi tana murmushi tayi hanyar barin bedroom din

Daf xata fita ta juyo dauke da murmushin tace

"Zahra a matsayina na 'yar uwanki, kanwar Mijinki, Addar kishiryaki ina mai baki shawara ki tattara inaki ki xo kibi mijinki, idan kuma kinki lokacin da kikeso ki koma Ya Bature yaki kada ki kuskura ki nemi Jidda, maganar munki jininki duk bai tasoba ai bamu muka juya lamarinba, am sorry to say kaikayine ya koma kan mashekiya"

Har ta fita ta kuma dwmawowa tace

"Ummi kada ki manta da Mami bace ta umarci Ya Bature ya auri Ma'u, Ammice ta umarceshi kinga bbu yadda xan daga hankalina don nasan Ammi baxata umarci Abban Amal ya auri Zee ba"

Jidda na kammalawa tayi ficewarta tana murmushi

Da mamaki Ummi ke kallon. Bakin kofar kamar Jiddance a wajen

"Lallai yarinyar nan wuyarki yakai yanka"


A fusace Zahra ta mike xatabi bayan Jidda, Ummi ta rikota

"Ina xuwa kuma"

"Zanje naji ubanwa ya tsaya mata a gidan nan har xataxo taci miki mutunci"

Cewar Zahra tana kokarin fisgewa daga rikon da Ummi ta mata

Dakyar Ummi ta xaunar da ita tace

"Kyaleta nasan maganinta, kina tabata yanxu wanlanarin xai bullo tunda Uwar Ubankuce ta tsaya mata, ki barni dasu xan magantasu Indai na haifu cikin General Kabala sai na hana kwanciyar hankali xaman lfy a cikin rayuwarsu Bature da Ma'u, Abdallah da Batool, yadda Uwar ubanku ta hada da kanta xata warware"

Ssai kalamun Ummi suka farantawa Zahra



Koda Jidda ta xayyanawa Bature abunda ya faru, farin cikine ya lullubeshi don xai more Angoncinsa yadda ya kamata

Part na kowa sunje an musu nasiha amma banda part din Ummi

Ciki ciki Ma'u ke kukanta don gudun kada Bature yaji

Haka suka dau hanyar Abuja


Tirkashi............


This is just da beginning

Wannan somanta6i kenan wai Ango ya shafa cinya🙈

Yanxu xamu tsunduma cikin labarin ka'in dana'in


Yanxu sunan novel din xai fara aiki GIDAN BATURE

Ummu subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻

Mrs Adam
Ina yinki irin ssai na

SadNaf
nagode ssai da kulawarki


1⃣6⃣

Tunda Batura ya kama hanyar Abuja Ma'u tasa kanta a kasa sai kuka take a hankali yadda Bature baxaijiba

Dubanta Bature yayi ya tabe baki

"Kici gaba da kukan, xakiyi mai dalili idan na tsaya na mammakeki"

Cikin Sauri Ma'u ta dago kanta ta shiga share hawayenta

Murmushin mugunta Bature yayi yaci gaba da tukinshi cikin salama yana kara godewa Allah da kyautar daya mishi

Minti minti Bature yake Satan kallon Ma'u

Itako Ma'u ta hade ranta cif kamar yadda ya xama mata jiki ta tura bakinta

Hakan datayi ma ya Burge Bature ji yake kamar ya janyota ya tsotse bakin



Bature Estate

Sanadiyar sauyi daya xo yasa aka suke duk wani bikin da'aka tanada ranar Asabar

Da daddare Ammi tasa Hisham ya dau Shukrah suka nufi gidansu, tasa driver yakai Abdallah da Batool gidansu, dama an rigada anyi Jere


Tunda suka idarda Sallah xuciar Shukrah ke dukan uku uku, daman gata da sanyi sai sanyin ya karu

Murmushi Hisham yayi bayan ya gama karantar yanayinta, ya yagi nama kaxa ya tura mata baki yace

"Ci wannan Matana, tsoron me kike ne"?

Ya karashe maganar yana kanne mata ido daya

Murmushi tayi ta tsadda kanta kasa

Cikin lallami ya dinga bata namar kaxan da fresh milk, sanda ya tabbatar ta koshi kan ya kyaleta

Da kansa ya tsaftace wajen ya daga sai kan bed

A zafafe ya shiga aika mata sakonni, tureshi ta shigayi

" pls Ya Hisham ka bari baxan iyaba"

Murmushi ya mata yace

"Ai biyata kaxata xakiyi, kina tunanin xakici bagas ne"

Kuka ta fashe mishi dashi tana bashi hakuri amma ina Malam Hisham yayi nisa

sanda ya maida Shukrah cikekkiyar mace kan hankalinsa ya kwanta

Asuba ta gari ShukraHisham



Zubawa Batool ido Abdallah yayi yana kare mata kallo, Sam ya kasa ganin wani makusa a jikinta, limshe ido yayi dayaji wani kasala

Please Login or Register in order to submit comment