Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzun ya za'a yi Fadil."?da sauri ya dago kanshi sannan yace."Ai shiyasa na gaya maki dan ki sa ma man mafita, dan wallahi ji nike na kusa mutuwa." ya fadi ya kuka bisa cinyar Umma, dan komawa yayi ya kwanta, ji yayi zaman baya daukarshi, dan kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro. Cewa Umma tayi."Subuhanalillah, Fadil kuka fa kake, saboda mace."?kallon Umma yayi sannan yace."Umma ina iya yin komai saboda Rumaisa, Umma ban san wani kallar so nike ma Rumaisa ba, Allah ya jarabeni da masifar sonta, Umma dan Allah ki taimaki rayuwa pls Umma na." cewa Umma tayi."To shikenan, tashi muyi magana."tashi yayi yana cewa."to ina jinki Umma."kallonshi tayi tta fidda wasa a fuskarta sannan tace."ka tabbata ka son Rumaisa da gaske? Dan na san ka kai wani kallar mutun ne, ba'a gane gabanka balle kanka."cewa yayi." Eh Umma ina son Rumaisa sosai, ki yarda dani Umma."numfasawa Umma tayi, sannan tace."to na san gobe zata Isilamiya ka bita hanyar Isilamiyar sai ka samu ka tare ta kaji Fadil."murmushi yayi yana share hawaye yace."eh Umma zanyi haka Insha Allah."ce mashi Umma tayi."komai kuka yi da ita ka gaya man."cewa yayi."To shikenan Umma."cewa Umma tayi."yauwa tashi ka tafi kayi sallah lokacin sallah yayi."tashi yayi yana cewa."to ni daga masallaci zan wuce gidan su Abdullah.".."to Fadil."

Bayan Fadil ya dawo daga masallaci, yayi wanka ya shirya, ya wuce gidan su Abdullah, yana shiga ya wuce part din Addan su Abdullah, dukawa yayi ta fara gaidata."Adda, ina wuni."?cewa tayi."Lafiya lau Fadil, ya gida da Ummarka."?....."Lafiya lau, Adda, na samaiku lafiya."?.... "Lafiya lau." nan Fadil ya wuce part din Abdullah, yana shiga Abdullah yace." Mr's Rumaisa, har ka iso kenan."? Zama yayi yana cewa."Ba dole ba Abdullah, tunda ina neman mafita ba."dariya Abdullah yayi sannan yace."to yanzun ya kuka yi da Umma."? Cewa Fadil yayi sannan yace."Hmmm, Umma tace man, gobe naje Isilamiyarsu na tarai ta a hanya."harararshi Abdullah yayi sannan yace."wai da kasan tana zuwa Isilamiya ka tsaya ba kanka wahala."?murmushi Fadil yayi sannan yace. "Hmmm ni na manta Ruma tana zuwa Isilamiya wallahi, sai da Umma ta fadi sannan."
Nan dai suka shirya yanda zai yi shine bai bar gidan su Abdullah ba sai bayan isha'i, bayan sunyi sallah ya hau motarshi ya wuce gida, yana shiga yayi ma su Umma sai da safe ya wuce part din shi....
Washe gari tunda safe Fadil ya tashi ya shirya yayi duk abunda yake, yaje ya gaida Umma ko breakfast bai tsaya yayi ba,  dan  ji yake kamar yayi fiffike ya ganshi gun Isilamiyar.

Tun karfe 11am yake zaune bakin Isilamiya, da yake ba da motarshi yaje ba, da motar Abdullah ya je gun, kan idonshi yaga Rumaisa ta wuce da nikaq a fuskarta, sai kash🤦‍♀️Rumaisa bata son tsiyuwarta kawai Fadil yana gane wa balle ta fiya ma😁...
Yayi dariya sosai, wai shi Ruma tasa ma nikaq dan kawai kar ya ganta, haka Fadil yai ta zama har aka  taso su Rumaisa daga Isilamiya, tana cikin tafiya taje ance mata...
"Hello pretty kin gama boye fuskar ko."?
Wai gowar da Rumaisa zata yi suka yi ido da ido da Fadil,wani wawan Kallo tayi mashi sannan tace. "lafiya malan? Zaka wani tsada mutun kan hanya."murmushi yayi sannan yace."Ruma ni ne fa, kike yi ma haka."numfasawa yayi na wani dan lokaci yanajin yanda kirjinshi yake mashi zafi akan abunda Ruma take mashi, cewa yayi."Ruma gaya man laifin da nayi maki kike yin man kalar wannan hukuncin."? Tsaki tayi marar sauti, sannan tace."Ni ba laifin da kayi man."matsowa yayi kusa da Ita sannan yace."Kuma shine kike yi man haka."?  matsawa tayi, tana kallon shi sannan tace."Eh Fadil nayi maka haka, to tsaya kaji, daga yau bani bakai."da sauri ya kamo hannunta yana cewa."Ruma amma.."dakata malan, karka sake kasake zo mana gida, nima zan bar zuwa gidan ku, dan haka bani *SONKA* , kaje ka samu dai dai dakai badai ni ba."Rumaisa tace haka tana fisge hannunta daga rikon da yayi mata, tana mashi kallon baka isa ba, hawaye yake yana cewa."Ruuuuuuma, plssssssss, karkiyi man haka, karkice baki sona plssssss,kiyi man ko wani hukunci amman karki ce baki sona,wallahi inasonki sosai ki daure ki anshi soyayya ta."cikin fushi Rumaisa tace."haba wai kai wani kallar mutun ne nace maka *BANI SONKA, BANI* *SONKA* , haba *ANA SO* *DOLE NE...*"?
Nan take Fadil ya fadi kasa yana kiran sunan Ruma yana cewa. dan Allah ki taimaka man.. Bai ida maganar ba  sai kuma ya fara aman jini yana kiran Rumaisa dan Allah ki tausaya man ki soni.
Rumaisa ta kama ihu tana neman agajin mutane wani Malamin su ta gane ta fara cewa."Malan dan Allah ka taimaka man.'Cewa yayi."yi shiru baiwar Allah yanzun zamu kai shi asibiti kinji."nan suka taimaka aka sa shi a mota, Rumaisa ta shiga tana kuka, tana cewa..
"Fadil dan Allah karka mutu kabarni, ka tausaya ma zuciya ta Fadil, ban shirya rasaka ba dan yanzun,na boni ni Rumaisa, yanzun banda sauran wani masoyi na gaskiya, ya zan ce ma Umma, wayyo Allah."
Nan suka iso asibiti, aka anshe shi emergency, nan likitoci suka runkuɓa a kanshi dan su ceto rayuwarshi."cikin wanda suka kawo Fadil asibiti yace ma Rumaisa."Baiwar Allah ba kuka zaki yi ba, addu'a zaki yi mashi, yanzun bani wayarshi a kira Mamanshi ko."? Miƙa mashi kawai tayi bayan ta fidda password.

Haka aka Kira Umma aka gaya mata halin da Fadil yake cike yanzun haka yana asibiti, aman jini yay, cewa Umma tayi cikin tashin hankali."Dan Allah kuna wani asibitin."?cewa yayi. "Muna DOCTOR MARYAM PRIVATE HOSPITAL....
Cikin tashin hankali Umma ta dauki hanyar hospital dinta, tana salati tana addu'a tana cewa Allah ya kare mata Fadil dinta.. 
Tana zuwa ta tadda Rumaisa zaune tana kuka,kallon Rumaisa tayi sannan tace."Rumaisa mai ya samu Fadil? Ki gaya man mai yasa mu Yayanku."?
Da gudu ta rumgume Umma cikin Kuka take cewa."Umma dan nace ya kyaleni bani son shi shine kawai ya fadi yana aman jini."shafa bayanta Umma tayi sannan tace."To yi shiru kinji Rumaisa, bari na shiga naga ya ake cikin yanzun."Girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace."Umma dan Allah  karda ya mutu, wallahi ina son shi, ki taimake ni dan girman Allah Umma."fahimtar da Umma tayi Rumaisa bata cikin haiyacinta, cema Fadila tayi."
Fadila zauna da ita bata cikin hankalinta yanzun."cewa tayi."To shikenan Umma, kawata  dan Allah kiyi shiru,insah Allah ba abunda zai samu yaya Fadil, kiyi shiru pls....
*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page_45&46


*Iye iye nanaye 🤗, inji mawaƙa, haka maganar take, idan Allah ya nufa zaka cigaba, zaka zama wani tam ba wanda ya isa ya hana, duk ko bakin cikin mutun da hassadarshi🤣, dan haka nidai Jameey yar'mutan kankia sai dai a ganni a kyale nan gani nan bari, idan ko aka shigoman gonata zan shafa ma👀kwali nayi ma mutun abunda baya tunani, dan haka sai a kiyaye🤓*

_Masoyana kuna raina, kamar yanda nima nike ranku, inayinku over and over, soyayyar da kuke nunaman tana sani farinciki sosai💋_


Kallon Fadila Rumaisa tayi yana girgiza kai sannan tace."Fadila taya zanyi shiru, bayan kinsan ina cikin matsala, masoyina baya lafiya,  amman fa Fadila Yaya Fadil Aman jini fa yake, ni ya zanyi da raina, nasan ban kyauta ma kaina ba."

Tashi Fadila tayi tana lailashin Rumaisa sannan tace."to yanda zaki yi da rainki, shine kiyi addu'a, kuma insha Allah ba wani abu ki ringa yimai hasashen alkhari, mana Rumaisar Yaya Fadil."zaunawa Rumaisa tayi tana cewa."To Fadila nagode sosai."murmushin karfin hali Fadila tayi sannan tace ma Rumaisa."yanzun tashi mu tafi mu daho mashi abincin kafin a fito dashi."girgiza kai Rumaisa tayi tana cewa."Aah Fadila kedai ki tafi ki daho mashi, nidai ina nan har sai naga an fito dashi."shiru Fadila tayi tana dan tunani na wani lokaci sannan tace."To Rumaisa, tunda baki zuwa, bari na kira Dear  yazo ya dauke ni, sai na hado mashi."cewa tayi."ki hado mashi harda tea please."harararta tayi sannan tace."shi da yace ban iya hada tea ba sai dai ke, amman zanyi dai dan baya lafiya,  bari na kira shi, mu tafi."

Dauko wayarta tayi, tana kiran Abdullah."Hello Dear, kana jina."daga can bangaren Abdullah yace."yes Sweety am hearing you, what wrong."? Murmushi tayi sannan tace."Da man yaya Fadil yana hospital."tashi Abdullah yayi daga zaune sannan yace."what? Kina nufin Fadil baya lafiya."? Cewa Fadila tayi."Eh Dear  yanzun haka ina hospital, kazo ka dauke ni naje gida na hado mashi abinci."tashi Abdullah yayi yana cewa."ok wait for me am coming now." Cewa tayi."ok safe trip."waigowa Fadila, taga Rumaisa tana kuka,matsowa tayi kusa da ita tana cewa."Yanzun tsakani da Allah Rumaisar Mama, har yanzun baki daina kukan ba? Shi yaya Fadil ba mutuwa yayi ba."

"Hmm  Fadila kenan baki san yanda nike ji ba shiyasa kike cewa haka."kallon Fadila tayi sannan tace. "Uhmmm nidai na tafi kinga dear har ya iso." Cewa tayi."to Fadila ki gaida da man da Abdullah.".."to zai ji."


Haɗe hannuwanta tayi waje ɗaya, ta langwaɓar da kanta gefe tace."Dear sorry na barka tsaye." murmushi yayi, dan yanda tayi sosai tayi mashi kyau, cewa yayi."bakomai Sweety,shigo mu tafi ko."? Shigiwa tayi tana cewa."ok, ya gida."?..."lafiya lau."..."ya Adda ta take."?..."tana lafiya lau,wai Sweety da yaushe aka kawo Fadil hospital? Daga gidan mu yake,ya anshi motana zai je wajen Rumaisa." numfasawa Fadila tayi sannan tace."to wallahi ,muma anyi mana waya ance muzo yana asibiti,abun da mamaki da muka tadda Rumaisa tana kuka."murmushin taƙaici Abdullah yayi sannan yace."To may be ,itace tayi causing din matsalar ko."? Shiru Fadila tayi na wani lokaci sannan tace."nima haka naki tunani,to ka bani some minute, yanzun zan fito." fitowa tayi zata shiga gida, dan har sun iso, cewa yayi yana murmushi."to a fito lafiya."

Fitowar Umma kenan, daga wajen Fadil, da sauri Rumaisa tazo wajen Umma tana cewa."Umma ya jikin yaya Fadil."? Dafa mata kafaɗa Umma tayi, kallonta tayi sosai taga duk ta rame rana daya kawai duk ta fita haiyacinta, girgiza kai tayi tana murmushi sannan tace."da sauki,yanzun za'a fito da shi a kanshi resting room." sauke naunauyar ajiyar zuciya Rumaisa tayi sannan tace."wash Alhmdulh,har naji sauki Umma." Umma Soyayyar dasu Rumaisa suke ma juna tayi, dan basujin kunya a gaban kowa suke nuna son junansu, cewa tayi.yanzun ina Fadila take."? Cewa Rumaisa tayi."ta tafi ta hado mashi abinci,yanzun Umma ina iya zuwa na ganshi."? Dakuwa Umma tayi mata sannan tace."Aah bacci yake, yana bukatar hutu,yanzun  biyo ni office zamu yi magana."


Fitowa Fadila tayi tana cewa."Dear har na gama,mu wuce ko."?ansar coolers din hannunta yayi yana cewa.Tom Sweety ,mu wuce." Sun fara tafiya Abdullah ya waigo ya kalli Fadila sannan yace."sweety." Cewa tayi."Naam Dear." Cigaba da driving dinshi yayi, sai da ya dauki lokaci sannan yace."ina son na tambaye ki."? Shiru tayi sannan kuma tace."to ina jinka."cewa yayi."OK kinsan Fadil ya na son Rumaisa."?...."Eh na sani." Kallon Mamaki Abdullah yayi ma Fadil sannan yace."tun yaushe kika san Yayanki yana son kawarki."? Murmushi Fadila tayi, dan taga yanda Abdullah yake mamaki dan tace tasan Fadil yana son Rumaisa, cewa tayi."ba tun yau ba na fahimci Yaya Fadil yana son Rumaisa." Murmushi shima Abdullah, yayi sannan yace."Tom bayan nan fa."? cewa tayi."Eh naso na fahimtar da ita Rumaisa, Amman sai tace ita mutuncine tsakaninta da Fadil,da naga bata yarda sai na kyaleta." Cewa Abdullah yayi."Uhmmm Sweety,to kin san Fadil ya gaya ma Rumaisa yana son ta."? Cewa tayi."Eh to daga baya naji a bakin Yaya Fadil,a jiya kenan, Amman da man kwanakin baya Rumaisa bata zuwa aiki da wuri kuma da wuri take koma wa gida."
Kallonta Abdullah kawai, dan bai gamsu da maganar Sweetyn tashi ba,dan yasan Rumaisa ta gaya mata Fadil yana son ta, kin gaya mashi gaskiya kawai tayi, kuma ta manta shi Barrister ne, yana gane maganar gaskiya da karya, cewa yayi."OK nagode Sweety, mun iso ,ki gaida man da Umma, anjima zan dawo dan nasan yanzun Fadil bai farka ba.".."to dear byeee."

"Rumaisa, ya jikin Yaya."? kallon Fadila tayi sannan tace."da sauki sosai, yanzun aka kai shi resting room, muje ki raka ni office din Umma."cewa Fadila tayi." To bari na ajiye abincin ko."..."ok ina jiranki."..."mu tafi to." cewa Rumaisa tayi."Fadila yau naga bala'in karki so kiji yau yanda naji, ashe  haka SO yake." dariya Fadila tayi sannan tace." sai yau kika gane kenan yar nema."? Shiru Rumaisa tayi, dan ta lura yanzun Fadila zata kama tsokanarta, shiga sukayi office din Umma, sallama sukayi.

"Sallama Alaikum." dago kanta Umma tayi sannan tace."Amin wa'alaikumus sallama, ku shigo, sai yanzun kike zuwa ko."? Kasa da kai Rumaisa tayi sannan tace. "Aa Umma na jira Fadila ne."harararta Umma tayi sannan tace."ai da yake keda Fadila nike nema."cewa Fadila tayi."Umma ba'ason muji mai zaku ce kenan."? Harararta Umma tayi sannan tace."Ban sani ba, yanzun ku zauna."



zaunawa sukayi, kallon Rumaisa Umma tayi sannan tace."Yauwa  Rumaisa, kina jina ko."? A sanyaye ta dago kanta tana kalllon Umma, dan rainta ya bata Fadil ba lafiya, cewa tayi. "Eh Umma." kallonta sosai Umma tayi sannan tace."Fadil ya kusa ka muwa da heart attack."hawaye ne masu zafi suka zuboma Rumaisa kas tsadasu tayi, cikin inda indar kuka tace."heart attack Umma."? Cewa Umma tayi."Eh ai ba wani abun tashin hankali bane, in dai mun bi hanyar da ya kama ta, dan yanzun aiki ya ganmu, mu duka baki dayanmu, dan yanzun ya zama dole mu guji abunda zai batama Fadil rai ko ya yake." cire glass din fuskarta Umma tayi, tana goge zufa sannan tace."Ya zama dole, ke Rumaisa daga yau ki fara nuna ma Fadil kalar son da kike yi mashi, dan shine zai sa ya samu saukin ciwon shi,dan haka daga yau sai ki fara naki aikin, muma zamu yi namu aikin, shi heart attack ba wani ciwon tashin hankali ba ne kin gane ko Rumaisa, kawai mubi abunda ya kama ta, abunda ya kamata shine mu kiyaye duk abunda zai ɓata ma Fadil rai, kamar yanda na gaya maki a farko."


Cewa Rumaisa tayi."to shikenan Umma, insha Allah zani kiyaye." cewa Umma tayi."yanzun ku tashi muje na san ya tashi baccin yanzun, sai yaci abinci, anjima in nagama aiki mu tafi gida.".."to Umma." nan suka tashi suka tafi wajen Fadil, zaunawa sukayi sannan Fadila tace."Yaya Fadil, ya jikin."? Cewa yayi."Da sauki Fadila, ina Umma."? Cewa tayi."Ga ta nan shigowa ta biya ta fara ganin wani patient."cewa yayi.""ok shikenan." Kallonshi Rumaisa tayi sannan tace."Yaya Fadil, sannu ya jikin."kallonta yayi sannna yace. "Alhmdulh Ruma, mai kika zo yi nan? Mai zaki yi gun makiyin ki?bayan kince baki sona, wuce kibar wajenan kafin raina ya baci." Nan take Rumaisa ta fara kuka, ita kuma Fadila ta fita ta bar masu dakin, kuka take tana cewa."Haba Yaya Fadil, dan Allah kabar cewa haka."cewa yayi."taya zan bar cewa hak? bayan da bakinki kika ce baki Sona."cewa tayi cikin shagwaɓe."to ai sharin sheɗen ne, wallahi INASONKA."tashi yayi zaune yana cewa."Ruma da gaske kina SONA."? Cewa yayi."Eh Yaya Fadil."ɗaga hannuwanshi sama yayi sannan yace."Alhmdulh Allah na gode maka, ni nama samu sauki, suzo su sallamaini." cewa tayi tana murmushi."To ai baka ci abincin ba."kallonta yayi sannan yace."ai naji na koshi tunda kince kina sona,yanzun ba abunda ke damuna Ruma." cewa tayi. "Nidai kaci kona yi maka kuka."ta fada tana harfa hannu tana bunbuga kafafu, ita a dole kuka zata yi.. 
Dafe kirji Fadil yayi, yana lumshe ido, sannan yace."Asssh Ruma, karki kasheni da Salonki, bani zanci, ai shikenan ko."? Cewa tayi cikin salon kissa tace."Eh Ehmna." nan Rumaisa ta ba Fadil abinci da kanta har sai da ya koshi sannan ta barshi haka, Umma ce ta shigo tana kallon Fadil tana cewa."Aah patient din ne haka, kamar bashi bane yake rai hannu ga Allah ba." kallon Umma yayi sannan yace."ni Umma na samu sauki, da man lafiyata lau ai."dariya Fadila tayi tana cewa."laaa kaji Yaya Fadil, kai dai kace kai da Rumaisa kun dai-daita kanku." Kallonta yayi sannan yace."ke yaushe na fara wasa dake."? Tareshi Umma tayi tana cewa."Aa kyale man Autata ta shana,  ka bari anjima sai mu wuce gida tare ni na wuce wajen Dr. Musa."tafiya Umma tayi, ta barsu suna ta hirarsu cikin natsadi, Abdullah ne ya shigo sallama yayi.
"Assalama Alaikum."..."Amin wa'alaikumus sallama." suka ansa a tare, cewa Abdullah yayi."to wai patient din na mu ne haka."kallon Abdullah yayi yana cewa."hmm na samu sauki ai, kuma sai yanzun ka gadamar zuwa ko."? Cewa Abdullah yayi."Aa nazo dazun lokacin kana duniya duniya lahira lahira."dariya yayi sannan yace."Aa sai dai lahirar baki daya."cewa Abdullah yayi."to dan lahira, yanzun Sweet sai ku tafi gida keda Rumaisa, ni sai nayi jinya ko."? Cewa Fadila tayi tana dariya sannan tace."Aiko dai Dear taso mu tafi Rumaisa."
Harararta Fadil yayi sannan yace."Sai dai ku ku tafi,Amman Ruma ta nan zata yi aikin lada." dariya Abdullah yayi sannan yace."ko ba aikin  lada ba, Sweety mu tafi mu dan gaisa ko."
Bayan su Fadila sun fita suka bar Fadil da Rumaisa suna soyayarsu, cewa Fadil yayi."Ruma dan Allah ki saki jikin ki dani pls Ruma, bani son wannan daridarin da kike yi dani, ni fa zan aureki."cewa tayi."Yaya Fadil, dan Allah kayi hakuri."murmushi yayi sannan yace."Ruma ni baki yi man komai ba, kuma ke Amarya ce, Amarya bata laifi."cewa tayi."ko da na kashe dan masu gida."? Dariya yayi sannan yace."Ai inkin kashe dan masu gida kice ta farko gun yi asara...
*Yar'mutan kankia ce ❣️*
Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________




*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page_47&48


Sai da Rumaisa ta samu Fadil yaci abinci, ya koshi, sannan hankalinta ya kwanta, Murmushi Fadil yayi sannan yace."Ruma." kasa ɗago kanta tayi balle ta kalleshi, wasa take yatsun hannunta, dan kunyar abunda tayi mashi take, bude dan karamin bakinta tayi, tace."Naam." Fadil ya fahimci Rumaisa kunyarshi take ji, kuma shi baya jindadin wannan kunyar tashi da take ji, langwaɓar da kanshi gefe yayi cikin wani irin sallon soyayya yayi maganar kasa kasa kamar mai jin bacci yace."ki dago ki kyaleni mana Ruma, ina son ki kyale ni ido cikin ido, na gaya maki kallar SON da nike maki Ruma." sosai maganar ta shiga cikin jikinshi Rumaisa dan ko tsikar jikinta sai ta fara tashi, cikin zuciyarta tace."wash yau zan mutun da salon wannan mutum." abunda bata sani Fadil ji ne dashi yaji abunda tace, Murmushi yayi sannan yace."maikika ce Ruma."!? Sauri ta dago kanta tana kallonshi, sunburo mashi baki tayi sannan tace."ni bance komai ba fa." dariya yayi sanann yace."naji Madam bakice komai ba, nace ki kyale ni sosai na gaya maki irin son da zuciyar Fadil yake maki." cikin shagwaɓa tace."Yya Fadil..."Shsss Ruma." ya daura yatsa akan lips din shi, yana mai sauko wa bisa bed din ya duka giwa biyu a gabanta, yana mata wani irin kallon soyayya dan ji yake kamar ya haɗiyeta dan son da yake mata, cewa yayi."Ruma kin san bani son musu, dan haka dago ki kyaleni gani gaban zan nemi wata alfarma." da sauri Rumaisa tta sauko itama ta tsuguna tana cewa."Yya Fadil, dan Allah ka tashi tsaye, ban san na ganka a tsugune a gaba, inba haka na nima ba zan tashi ba.'' Murmushi Fadil yayi, sannan yace."Ruma wallahi ba zan tashi har sai na yi abunda nayi niya, kuma kema yanzun nike son ki tashi ki zauna." bata da zabi, tasan tunda yace baya tashi to ba tashin zaiyi ba, tashi tayi ta zauna, cewa yayi." yauwa kina jina."!? Kallonshi tayi kamar yanda ya bukata sannan tace."Eh ina ji." ƙara matsowa yayi yana cewa."yauwa RUMAISA."kasa cewa komai Rumaisa tayi, dan yanda taji yace Rumaisa, kuma tana tsoran abunda zaice mata raurau tayi da idanu sannan tace."Naam." Murmushi yayi, dan ya fahimci Rumarsa ta tsorata, dan zaiyi magana da ita, cewa yayi."Rumaisa! Rumaisa!! Rumaisa, kinji na kira sunanki sau ukku ko."?...."Eh."..."Rumaisa ina sonki, ina kaunarki, ina tausayin ki, dan Allah ki daure ki ban masauki a cikin zuciyarki, Wallahi zan kula dake ba zan yarda na saki kuka, zan rayu dake, zan mutun dake, ina son ki zamo uwa ga ya'yana." numfasawa yayi sannan ya cigaba da cewa."Ki man alkwarin duk runtsi duk wuya ba zaki zuya man baya ba, ki man alkwarin bazaki hukuntani da laifin da ban nayi shi ba, ki man alkwarin zaki rike ni Amana zaki bani kula ba zaki yarda kiga bacin raina ba." hawaye ta fara sharewsharewa, tasan batayi ma kanta adalci ba, da ta huka masoyin gaskiya har haka, tasan bayan iyayenta bamai son kamar Fadil, cewa tayi." Yaya nayi maka duk wannan alkwarin da kace man, yaya Fadil zuciyar Rumaisa ta dade da dakon sonka, kaga ko ba za ta yarda ta zuya maka baya ba, inasonka yaya Fadil, kaine gishirin rayuwata, inbaka nima bani, dan haka bani fatan naga ranar da ranka zai baci, ko da ya baci, ni Rumaisa sai na sashi farinciki, na gusar da wanda bakin ciki, ba zan iya sa masoyiyina kuka ba, kasani kaine rayuwata dan soyayyarka a jinin Rumaisa take." Wani farin hankichif, ya fiddo ya miƙa ma Rumaisa yayi mata alamun da ta goge hawayen fuskar ta, sannan yace."Nagode Ruma, Allah yayi maki albarka Matata." Murmushi tayi mai haɗa da kuka tace."Amin ya Allah Yayana." Hararar wasa yayi mata yaji tace Yayanta, tashi yayi yana cewa."Ruma to tunda ana sona sai abar ce man *YAYA* *FADIL* , ke kice Fadila tace, nidai gaskiya ke ki chanza man." ya karasa maganar cikin shagwaba,sai kace karamin yaro dan goye, Murmushi kawai Rumaisa tayi, cigaba da cewa yayi." Dan haka daga yau na dawo *PRINCES* , ni kuma zan ringa ce maki *PRINCESS* , haka yayi maki? In bai yi maki ba sai mu chanza wani sunan ko masoyiya." tana dago ta kallashi ya ɗage mata ido, yana mata wani kallon mai wuyar fassara, da sauri ta dukar da kanta kasa tana dariya sannan tace." Haka yayi man my princes, sunan yayi man dadi, dan haka daga yau insha Allah ka zama Princes." cewa yayi."wwoow my princess thank you very much, ilov uh,yauwa wai mai ya samu wayarki Princess."!? Cewa tayi a hankali."Bakomai lafiyarta lau." Murmushi yayi sannan yace."dan kawai nasha wuya shiyasa kika kulle wayar kenan."? Cewa tayi."Uhmmm, amman ba haka bane." cewa yayi."tom naji princess gaya man ya abun yake."? Yar dariya tayi marar sauti, sannan tace."Kawai princes bakomai jin dadi." cewa yayi."to Allah ya kara maki jin dadin princess."
Umma ce ta shigo tana cewa.to kai patient sai ku tashi mu tafi gida ko."? Saukowa yayi daga bisa gadon yana cewa."To Umma, da man ni tuni naji sauki, ko princess."? Nan dai Rumaisa ta dukar da kanta kasa tana wasa da hannunta, dan ita yanzun bala'in kunyar Umma take ji, lura da hakan Umma tayi tace."Kaji dashi dan nema, ku taso mu wuce, kaga magrib tayi, mu aje Rumaisa gida, kar hankalin Mamanta ya tashi kaga har yanzun bata dawo gida ba." cewa yayi."alright Umma."
Nan suka shiga motar Umma, aka bar ta Abdullah wani mai gadi zai maida masu ita gida, Umma ce tace." Fadil kana jina."!?.."Eh Umma." cigaba da ce mashi Umma tayi."sai ka rage yawan tunani, indai kana son lafiyarka da kuma kwanciyar hankalin mu." cewa yayi."insha Allah Umma, ni yanzun ai bani da matsala balle har nayi wani tunani, tunda princess ta yarda da soyayyata." dakuwa tayi mashi tana cewa."sannu shugaban masu kunya, a gabana kake princess ko."? Dariya yayi yana cewa."To Umma laifi ne in mutun ya nuna ma matarshi So, matsala hausawa kenan wallahi komai kunya, sai kunyar ta cucesu, nidai gaskiya bani da kunya a kan princess." kallonshi Umma tayi, tana mamakin Fadil, soyayyar Rumaisa tasa ya chanza hali sosai, Fadil din da ko magana bata damaishi ba, amman yanzun magana yake, cewa tayi." To naji, mai princess, a yi hakuri karda naji duka." rufe baki yayi yana cewa."rufaman asiri Umma." waigowa baya Umma tayi sannan tace."to Rumaisa mun iso gida, sai gobe ko."? Duk kunya ta isheta abunda Fadil yace a cikin mota, cewa tayi."Eh Umma nagode sosai." cewa Umma tayi."Dan Allah Rumaisa ki gaida man da Mamanki, kice ina gaida ta gobe Insha Allah zani shigo muyi magana,

Please Login or Register in order to submit comment