Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a Kurna hankalin mu kwance, sai dai mu Kaima Ba'ba Rumaisa ziyara duk randa babu Isilamiya don na shiga Isilamiya a nan Kurna."
"Na shiga primary school,Lokacin Babana ya bar sana'ar Ruwa, ya koma hayar machine, wani Alhaji  sanusi ya siya mashi, yana bashi balance, tun rana...









*yawan comment yawan typing, dan gsky ba zan dunga yi maku typing mai tsawo ba, ku bakuyin comment dan haka ga wannan*

*Yar'mutan Kankia ce❣️*
Share
Comment
Vote
And
Like
Pls


🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
___________________________________

      
            
*am back nagode sosai da addu'oinku, sannan kuma jiki da sauki Alhmdulh, karku manta yanzun muka fara wasan ku cigaba da biyoni a cikin a gidan haya kuma kuna surburbuɗo man ruwan comment💃❣️*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_31&32

"Haka mukai ta rayuwa hankalinmu kwance, ba abunda ke damun mu, kuma kullun sai Babba ya  kai balance din ci nikin da yayi wajen Alhaji Sanusi."
"Ina primary 5,mama ta haifaman kani, ranar Suna Yaro yaci sunan KHAMIS."
"Khamis sunan yayen Babane, aka sa mashi , wanda suka tafi suka barshi shi daya, bayan anyi sunan khamis da kamar wata biyu, sai Mamana ta fahimci khamis bai da lafiyar kai, nan ne fa hankinta ya fara tashi."
"Saboda taga kullun kai shi girma yake yi, nan suka fara zuwa chemist, aka bashi paracetamol na yara, nan aka fara bashi magani, aga ko za'adace."
"Khamis yana da wata shidda a duniya , amman bai fara zama ba, balle akai da sa ran rarrafe, ga kuma kanshi sai girma yake."
"Don ba'a goya shi da zane daya sai biyu ake goya shi, daya ake tare kanshi sai dayan kuma a goya shi."
Kallon Fadil Rumaisa tayi sannan tace."Yaya Fadil lokacin sallah yayi."shiru yayi na wani dan lokaci sannnan yace."to Ruma, muje muyi sallah ki cigaba ko."?murmushi tayi tana wasa da zoben hannunta sannan tace."Aah sai gobe indan Allah ya kaimu."cewa yayi."A'ah Ruma please ki ida man yau mana."cewa tayi"Yi hakuri Yayq Fadil, amman ya dace ace na koma gida yanzun, Mama nacan tana jirana dan Allah ka bari dai sai goben."cewa yayi."to shikenan Allah ya kaimu, ammam ba dan naso ba zaki tafi Ruma, dan kawai Mama itama tana bukatar ki shiyasa zan barki ki tafi."cewa tayi."hakan ma ai nagode sosai."kallonta yayi sosai yakejin tausayinta balle yanzun da ya fara jin labarinta cewa yayi."gaskiya labarin ki yana da ban tausayi, Allah ya kaimu goben ki iya da bani labarin, ina san naji  ina khamis yake, don banji kina kiranshi ba."cewa tayi tana mai miƙewa tsaye."Allah ya kaimu zaka ji yanda komai yake, sai da safe."cewa yayi."To shikenan, amman bari na dawo mosque sai na kai ki gida."cewa tayi."to shikenan, kafin kadawo nima nayi sallah."
Bayan Fadil ya dawo daga mosque ya dauki Rumaisa ya kai ta, yace ta gaida mashi Mama, sannan kuma zasu yi waya.
Tana shiga cikin gida ta tadda Mama tana jin redio, zaune ita ɗaya zaunawa tayi kusa da Mama sannan tace."Mama yau bacci nike ji sosai, gashi Baba bai shigo ba har yanzun."kallonta Mama tayi sannnan tace."ai kin bari ayi isha'i sannan ki kwanta ko kasa uwar yan bacci."? Sunburo baki tayi sannann tace."Mama ai cewa nayi na gaji shiyasa zani kwanta, kuma ba naji ana kiran sallahar ba."murmushi Mama tayi sannan ta kalleta tace."tashi kiyi sallahr to, tunda baki cin abinci sai ai ta bacci."tashi tayi tana cewa."na koshi naci abinci a gidan Mami."tafiya tayi tayo alwallah sannan ta dawo tayi sallah, kallonta Mama tayi sannan tace."je kiyi baccin ki Rumaisa, ba yanzun Babanki zai shigo ba."cewa tayi taba mai tashi tsaye."to Mama sai da safe."har ta fara tafiya taji Mama na cewa."Au Rumaisa na manta ban gaya maki ba, gobe Maman A'I zasu tashi su koma gidan su na kansu."dawowa tayi ta zauna cikin nuna farin ciki tace."Masha Allah, gaskiya ina taya ta murna, sunyi gidan kansu, su huta da zaman GIDAN HAYA, Muma Allah ya nuna mana randa zamu yi gidan kaimu."cikin murmushi Mama tace."Amin Rumaisa."tashi tayi tana cewa."bari na kwanta Mama, gobe nayi mata murna."cewa Mama tayi."to sai Allah ya kaimu."..."Allah ya kaimu."
"Washe gari, bayan Rumaisa ta gama shirya wa ta biya tayi ma Maman A'I murna, ta wuce gidan aikinta...
Bayan sun gama yin komai ita da Fadila, suka kira Fadil suka ci abinci suka maida komai ma zauninsa, sannan ta wuce part din Fadil...
Sai da ta gama gyara part din tas, dan harda bedsheets ta chanza ma duka beds din da suke cikin part din nashi, ta wuce kitchen ta hada mashi tea ta juye a flask, ji tayi yana cewa."Ruma don Allah ki ajiye wannan aikin ki zo ki cigaba da bani labarin, baki san yanda na kosa ba."cewa tayi, tana mai tahowa."to gani nan, fara shan tea din mana sai mu cigaba."kallonta yayi yana murmushi kashe mata ido ɗaya yayi sannan yace."to bani nasha, amman Ruma kin iya haɗa komai kedai aa duniya."ajiye cup din hannunta tayi sannan tace."rufaman asiri, badai komai ba, Yaya Fadil duk santin ne kenan."dariya yayi yana ajiye nashi shima dan ya gama sha, yace."ai dole nayi santi, kedai komai naki daban yake Ruma, kin iya komai da komai."murmushi kawai tayi bace komai ba sannan ta cigaba da bashi labarin.
"Yauwa yaya Fadil, bayan ciwon khamis yayi tsanani, tunda baya zama sai dai kwanciya, nan fa aka fara kai shi asibiti GENARAL HOSPITAL, munyi kamar zuwa biyu su kayi discarded din mu zuwa AMINU KANO TEACHING HOSPITAL."
"Haka muka koma Aminu kano, aka bamu gado, amman shi gadon sai an bada kudin har dubu hamsin, sannan za'a bamu gadon da Khamis zai kwanta a asibiti."
"Ba inda Baba bai je ba, amman bai samu kudin ba, sai dai Mama ta sai da wani dan marakin sa din ta wanda ta gada wajen Babanta, aka biya kudin gado....


*karku manta ina kan bakana yawan comment yawan typing ❣️, much love uh all my fans*
*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan Kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Page_33&34

"Haka aka bamu gado,  nan aka fara yi ma khamis wankin kai, saboda sunce ruwa ne a cikin kanshi sosai."
"Sai da mu kayi kwana hudu a Aminu kano, a na yi ma khamis aikin kai, sai kawai watarana a kace mana mu bada DUBU DARI DA HAMSIM, za'ayi ma khamis aiki."
"Ba yanda ba'a yi ba su rage kudin aikin, amman suka ce haka zasu yi shi, shiyasa muka hado kayan mu muka dawo gida...
"Baba ya cigaba da neman kudi, ita kuma Mama ta fara aikatau  gidan Alhaji Sanusi."
"A na haka Allah yayi ma Ba'ba Rumaisa rasuwa, Baba yayi kuka kamar ba gobe, ga jikin khamis da sai gaba yake ba sauki sai wurin Allah."
"Watarana muna gidan Alhaji Sanusi, muka ji ana ihu cikin unguwa, muna leƙawa, muka ga wuta ta tashi gidan da muke haya."
"Allah yaso ba kowa a gidan, sanadin wutar nepa wutar ta tashi a gidanmu, munyi kuka sosai,dan ko komai namu sai da ya ƙone, haka muka barma Allah, lamarinshi muka anshi kaddaramu hannu biyu."
"Alhaji Sanusi ya bamu wani shago a kofar gidan shi yace ya bamu sati biyu mu zauna kafin mu samu wani gidan haya, saboda bai dace ba a ce muna kwana  a shago ba."
"A hankali muka samu wani sabon GIDAN HAYA, a cikin Kurna amman bayan airpot, haka muka had a kaya muka koma."
"Kullun nida Mama sai munzo aiki tunda uwar safiya a kasa da kafafunmu, dan ni makaranta nike wuce wa dan yanzun na kai jss2 a Secondary school."
"Haka muke ta rayuwarmu, Baba yana neman kudin aikin da za'a yi ma Khamis."
"Ciwon Khamis ya tashi abun ba kyaun gani, dole ta sa muka koma Aminu Kano, Likitoci sun ce aiki za'a yi mashi, kuma ba'ason aikin ya wuce yau zuwa gobe."
"Mun dun aikin ya wuce ranar sai dai Muyi hakuri da shi, nan hankalin kowa ya tashi, Baba ya je ya kwaso kudin da ya tara harda wanda ita ma Mama ta samu ta tara."
"Baba ya kwaso kudin baki daya, da aka lissafa duka kudin dubu saba'in ne, ba inda Baba bai shiga ba neman bashi amman bai samu ba,  haka ya hakura ya dawo asibitin...
"Ya gaya ma Mama baisamo ciko ba, nan Mama ta kwashe duk kayan dakinta ta sayar da su dubu  talatin, da aka hada kudi suka cike dubu dari."
"Saura dubu hamsin, muke nema cikon kudin aiki, ga khamis nan muna gani kwance babu kudin aiki, sai Alhaji Sanusi ya ba Baba kyautar dubu hamsin, nan aka hada aka bada sannann aka shiga da shi aiki...
"Bayan angama aiki lafiya, roba ce aka samai daga cikin kai zuwa wajen fitsarin shi, sun ce zai ringa fito ruwan da kai cikin kan shi a hankali har kan ya koma kamar na kowa."
"Bayan anyi aiki da shekara ukku, dan ba inda Khamis baya zuwa har magana duk nayi, watarana muka waye gari Khamis ya ce ga garinku, Allah yayi ma Khamis rasuwa😭😭."
"Munyi kuka, domin maganar gaskiya mutuwar khamis munji ta sosai, dan yana saurin shiga cikin zuciya, gashi nayi bala'in saba wa da shi , lokacin ina SS1 a secondary school."
"Bayan na gama secondary school ina da 18yrs, lokacin nayi saukar gur'ani mai girma, bayan nayi candy mai gidan da muke zaune na Kurna yazo shima ya ta damu."
"Yace mu barma shi gida, zai gyra shi, zai sa amaryarsa a cikin gidan, dan haka ya bamu sati biyu, cikin sati biyu Allah yasa muka samu gida a nan cikin unguwarku."
"Nasarawa, mun samu GIDAN HAYA MAI SUNAN DAKI GOMA, nan muka yi sallama da abokan Arziki, kafin mu tafi Alhaji Sanusi ya siya ma Baba KEKA NAPE, ace ya ringa kawo mashi  balance har ta zama tashi."
"Haka ko a kayi yanzun nape ta zama ta Baba, tunda muka dawo zaman gidan su Halimai bai da dadi, dan bamu san maiyasa su Halimai suka tsani rayuwarmu ba, dan duk zaman mu a GIDAN HAYA bamu zama da mutane sai wannan."
"Maman A'i ita tayi man hanyar aiki gidan ku."
"Kaji labarin RUMAISA FADIL MUHAMMAD."

my dear's Fan's dan Allah kuyi hakuri da wannan ina busy ne wlh.

*Yar'mutan Kankia ce❣*
Share
Comment
Vote
And
Like
Pls


🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
   _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

            

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page_35&36



Hawayen fuskar shi Fadil ya goge sannan ya kalli Rumaisa yace.""Ayya, yi shiru Ruma, yi hakuri pls, tabbas Ruma labarin rayuwarki tana da abun tausayi, Allah ya jikan Khamis, Allah yasa mutuwa ta zamu hutun shi."
Ɗago kanta tayi daga tsugune, kallon shi tayi,gira ya ɗage mata yana mata nuni da ta goge hawayen fuskarta, goge hawayen tayi sannan tace."Amin Yaya Fadil nagode sosai."murmushi yayi yana kallonta, dan natsuwarta tana kara mashi sonta, cewa yayi."Ruma yanzun haka kuke rayuwa cikin wannan yanayin?kuke zaune a cikin gidan haya."? Wasa take da yatsan hannunta, tana murmushi dan ita ai ta saba da gidan haya, ita da aka haifa a gidan haya ta taso a cikin shi ai ba abun mamaki bane, cewa tayi."Eh har ma ni nasa ba zaman GIDAN HAYA."shiru yayi na wani lokaci, dan parlourn shiru yayi kamar ba mutane a ciki, ji tati yace. "Allah sarki."kamar ba shi yayi maganar ba, dan wani waje yake kallo na daban, kallon shi Kawai take tana mamakin halin shi ace yayi magana kamar ba shi bane yayi taba, tana cikin tunanin taji yace."Ruma inasan nayi wata magana dake fa."kallonshi ta sake yi sannan tace."to yaya Fadil ina jinka, Allah yasa muji alkhari."murmushi yayi Wanda ya ƙara mashi kyau da haiba da kwarjini, waigowa yayi yana kallonta sannan yace."Eh alkhari ne Ruma, amman banson ya zaki dauki magana ta ba, da man ba wata magana bace, uhmmm Ruma."ji yayi ya kasa maganar ma, amman yasama ranshi duk rintsi yau sai ya gaya mata abunda ke cikin ranshi, shima ya dan huta, cewa tayi."Naam yaya Fadil ina sauraranka."murmushi yayi ya sake daga inda yake yaje ya haɗo masu black tea mai zafi,wanda bai cika sugar ba, dawowa yayi ya zauna sannan ya bata yace."anshi nasan zaki bukaci wannan Ruma."dariya tayi sannan tace."ina godiya sosai Yayana."ansa tayi ta dan kurɓa sannan tta ajiye a gabanta tana kallon shi, tana jiran abunda zai ce mata, murmushi yayi da ya kalleta dan ya lura ta ƙagu ya gaya mata abunda yace zai gaya mata ko zata tafi gida, shi kuma bai san  tace zata tafi, daurewa yayi yace."Ruma ina sonki."zunbur tayi tana kirma sosai sannan tace."Yaya Fadil."abun dariya yaso ya badashi yanda ta rude cikin minti ɗaya, tea ya dauka ya bata rike tea din kawai tayi amman ta kasa sha, fahimta yayi da ba sha zatayi ba yace."eh Ruma ina sonki, ina kaunarki Ruma, rasaki shine barazanar dauke war numfashina."tashi tayi tana girgiza kai sannnan tace."Yaya Fadil, amm.... "tabbas Ruma."katseta yayi, sannnan ya cigaba da cewa."Ruma ba mafarki kike ba, da gaske ni ne Fadil durkushe a gaba ina nema samun mazauni  a cikin birnin zuciyarki, ki taimaki ne ki anshe ni hannu biyu please RUMAISA."
Kallon shi tayi duƙe a gabanta, nan fa Rumaisa ta tashi ta fita da gudu tana kuka, ita dai shin farin ciki zata yi ko mai, haka ta shiga dakin Fadila da gudu tana kuka, kallonta Fadila, sannan ta tsinke wayar dasu da Abdullah, tace ma Rumaisa."Lafiya? Rumaisar Mama, naga kin shigo da gudu kuma kina ta kuka."?ƙara rushewa da kuka Rumaisa tayi sannan tace."Fadila na shiga ukuna, na lalace shikenan na gama aiki a gidan nan." dirowa tayi daga bisa gadon, taje wajen Rumaisa jijigata tayi tana cewa."na bani ni Fadila, Rumaisa wa ya mutu? Gaya man dan Allah Rumaisa."kallonta tayi ta kwanta bisa cinyar Fadila, tana hawaye sannnan tace."Fadila ba wanda ya mutu, amman Yaya Fadil ne."ƙara ruɗewa Fadila tayi, taji ance Yaya Fadil, cewa tayi."Yaya fadil kuma?wani abu ya samaishi ne? Na boni ni Fadila."girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace."Aah Fadila ba abunda ya samai shi, kwantar da hankalin ki."numfasawa Fadila tayi sannan tace."to gaya man lafiy? duk kin sani cikin damuwa, da ruɗini Rumaisa."kuka ta sake tashewa dashi sannnan tace."Fadila, wai Fadil yace yana sona." ta ida fadi tana kuka sosai, dariya Fadila ta fashe da ita sannnan tace."haha daman dan wannan abun kika shigo duk kika tada man hankali."? Cigaba da cewa tayi tana dariya."Ai da man tuni na gaya maki yaya Fadil Sonki yake, amman sai ke kice man ba wani kawai jininku ya hadu, to ai yanzun kinga haduwar jinin ko Rumaisar Mama?  hahhahhahha."tashi tayi tana goge hawayenta sannan tace."Amman Fadila... "shhhhh, yi man shiru na baki shawara a matsama na yar'uwarki, Rumaisa karda ki kuskura ki gyale yaya Fadil, ki anshi Soyayyarshi, in kuma kika tsaya kunya da wasa, to kina nan zaki ji ya samu wata ya aura,dan haka shawara ta rage naki."kallon Fadila tayi tana girgiza kai sannan tace."Fadila, yaya Fadil ba sa'ar aure na bane, yaya Fadil yafi ni komai, shi dan hutune dan masu hannu da shuni, karki manta ni yar'aikin gidan ku ce, kinga bai dace ace na buge yin soyayya da dan masu gida ba, ku......"Rumaisa, ashe matsayin da muka ba ki a gidan nan ke ba haka kika dauke shi ba? Rumaisa mun daukiki yar'uwa bamu nuna maki banbanci, amman duk da haka kina yi ma kanki kallon yar'aiki a gidan nan."? Zatayi magana Fadila ta katseta ta cigaba da cewa."A she yaya Fadil bai da arzikin da zaici darajar Umma ki aminta da Soyayyarshi ba, tabbas Rumaisa baki yi mana adalci ba, kuma banji dadin jin haka daga bakin ki ba gaskiya."saurin rufe mata baki Rumaisa tayi sannan tace."Fadila dan Allah kiyi hakuri, wallahi banyi tunanin rainki zai baci har haka ba, nima na baku matsayi mai girma a rayuwa, har abada ba zan manta da hallacin ku daga gare ni ba, kawai dai sai naga kamar banga dacewar mu ba da yaya Fadil."kallonta Fadila tayi sannan tace."Mungode da matsayin da muka samu, Rumaisa kinga na tsuguna giwowi na duka biyu in ma kina so zan dafa kafafunki ki taimaka ki Aminci ce Yayana."ɗago ta tayi tana cewa."Subuhanalillah, Fadila dan Allah ki mike tsayi, wallahi kin fi garfin komai a wajena, ai bun kunya ne naki dan uwanki, naso wani, Amman ina san ki bani dama nayi shawara da su Mama."murmushi Fadila tayi sannan tace."To shikenan Rumaisar Mama, Allah yasa muje alkhari, Amman dan Allah ki tausayama Yayana."tashi tayi tana cewa."to ni Fadila na wuce gida sai gobe." tashi Fadila tayi, ta tafi wajen Umma tana cewa."Umma albishirinki."? Kallonta tayi sannan tace."Goro."cewa tayi."fari ko ja."? Cewa Umma tayi."Fari tas da shi ma."dariya tayi sannan tace."to Umma yau dai yaya Fadil yace ma Rumaisa yana sonta."murmushi Umma tayi sannan tace."Alhmdulh Allah nagode maka, gaskiya na baki kyautar MOTA cikin new motors din da aka kawo jiya, amman ita Rumaisa mai tace mashi."?cewa."nagode Umma, ita bata ce komai ba, wai sai tayi shawara da Mama."cewa Umma tayi."Da kyau bani son ta bashi ansa dan yanzun har sai na ida tabbatarwa da kallar son da yake mata, dan ni na haifi Fadil na san waye shi, shi mutun ne mai wuyar fahimta."dariya Fadila tayi, sannan tace."To shikenan Umma, haka za'ayi, zan sa ta gara shi yanda ya dace, shima ya san yanda ake san wuya wajen neman aure."cewa Umma tayi."yauwa albarka haka nike son ji da man."
Tunda Rumaisa ta koma gida, ta kasa yanda zatayi, daurewa tayi sannnan tace."Mama da man ina son na gaya maki wata magana."kallonta Mama tayi sannan tace."wace magana ce haka Rumaisa? Fadi inajinki." kallok Mama Rumaisa tayi sannan tace."da man Fadil ne."kallonta Mama tayi sannan tace."Fadil ne mai wani abu ya sa mai shi."?cewa tayi."Aa da man ce wa yayi yana sona."tashi Mama tayi sannnam tace."Yana sonki fa Rumaisa."? Kallon Mama tayi sannnan tace."Eh Mama."zaunawa Mama tayi sannan tace."Rumaisa kiyi hakuri da Fadil, dan Fadil ba sa'an aurenki bane, ko ke baki lura ba."?cewa tayi."Mama ni ma haka nace ma Fadila, amman sai ta nuna bacin ranta, wai ashe ban dauki matsayin da suka bani ba, har da tsugun nawa tayi kasa tana neman alfarman na so Yayanta."shiru Mama tayi, dan itama ta hango hallacin mutanan gidan, take jikinta yayi sanyi sannnan tace."To shikenan Allah yayi maki albarka, Allah yasa shine alkharinki."cewa tayi."Amin Mama, ni zan kwanta sai da safe....
*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

   _STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Page_37&38


Yau Rumaisa tana gama aiki, ta wuce gidan aiki, bayan ta gama duk aikin da take Hajiya Maryam ta kirata ta fara yi mata magana.
"Rumaisa."sai da ta kalli Umma sannna tace."Naam Umma." Murmushi Haji ya Maryam tayi sannna tace."da man ina san nayi wata magan dake."cewa tayi. "to Umma."cewa Hajiya Maryam tayi."Rumaisa, naji Fadil yace yana sonki, amman sai naji wata magana wanda kwata kwata bata yi man dadi ba."numfasawa tayi, sannan ta cigaba da cewa."Yanzun Rumaisa da man baki dauke ni a matsayin uwa ba."? Sauri dago kanta Rumaisa tayi sannan tace."Yi hakuri Umma, amman ba haka nike nufi ba."murmushi yayi sannan tace."to shikenan Rumaisa bakomai,Ki dauke ni a matsayin uwa, yanda nike daukar Fadila, haka ke ma nike daukarki, zan baki shawara tsakani na da Allah."
Cigaba da cewa tayi."Rumaisa, na san Fadil na san halinshi duk da baka yabon dan yanzun, Fadil yana da wuyar sha'ani, na san kin san da haka, Fadil wani kallar murderden mutun ne baka gane gaban shi balle bayan shi."
Murmushi ta sake yi, sannan ta sha tea sannan ta cigaba da cewa."To ke taya zaki gane gaban shi? Shin taya zaki iya fahimtar halinshi? Taya zaki gane kallar son da yake maki? Dan haka Rumaisa kina da aiki sosai a gaban ki, amman kafin nan indai har baki son Fadil ki fidda kunya ki gaya man, domin mai iya zama da Fadil sai ya shirya."
Kallon Umma tayi sannan tace."Umma  ina son yaya Fadil, sai dai nima ina tsoron kalar zaman da zamu yi da shi a matsayin ma'aurata, duk da akwai shakuwa tsakanin mu ni da shi yaya Fadil din."shiru Umma tayi sannan tace."Tabbas haka ne naji dadin wanann maganar Rumaisa, yanzun zan gaya maki yanda zaki fahimci komai na Fadil, da yanda zaki ci ribar zama da shi a matsayin miji in Allah ya yarda."
Cewa tayi."Rumaisa Fadil mutun ne mai bala'in son kwaliya da tsafa, Fadil yana da musulkilanci sosai, amman kin san mai Rumaisa."? Girgiza kai tayi sannan tace."Aah Umma."..."to Rumaisa zama da miskillin mutun dadi ke gare shi amman in kin bi abunda yake so, to ba abunda ya fi zaman kalar masu halin Fadil dadin zama,sannan ban yarda ki gaya ma Fadil kina son shi ba dan yanzun, har sai kin tabbatar da ya wahalu sannan ki bashi ansar kin yarda da Soyayyarshi, shi kuma wannan wahalar da ya sha zai sa ya rike soyayarki riko na gaskiya da Amana."kallonta Hajiya Maryam tayi sannan tace."Karki yarda ki nuna mashi tausiyi a lokacin da kike ba shi gashi a hannu dan wannan zai sa ki gane ina matsayinki ya kai a cikin zuciyarashi, sannan Rumaisa, daga yau duk wata hanyar da zaki san zata hadaki da Fadil ki kiyaye ta, wannan ma wani shirine babba, ta yanda zaka gane matsayinka wajen mutum,sannan duk lokacin da kika amince da Soyayyarshi, karki yarda dai-dai da yatsan hannunki ya taba, dan duk budurwar da ta yarda saurayi ya kama mata hannu nan gaba NONONTA zai ce zai taba, tunda ya ga hanya,yanzun soyayyar da rabin da kwatan yan-matan yanzun suke wato soyayyar MINTI, ke kin saki jiki kin barmai yana ta tabawa a banza babu sisin kabo, sai ya gama bata maki rayuwa ya gudu ya barki da citson yatsa, Allah ya sa mu dace."
Dukar da kanta tayi sannan tace."Amin Umma."sake cewa Hajiya Maryam tayi."sannan Rumaisa ina san ki kara zage danke wajen iya abinci sosai, domin Fadil yana son mace wanda ta iya abinci dan shi baya cin abincin waje,Ke koda shi mutum ne mai cin abincin waje, ai ke macece sai ki bi hanyar da zaki bi kiga kin hana shi wannan hali, shin Rumaisa wace hanya ce wannan? Hanya daya to shine kisa mu ki koyi iya abinci kala kala, tun daga kan na zamini har zuwa na gargajiya,dan haka daga yau keda Fadila ku zaku ringa yi mana girki a cikin gidan nan, dan ban sake shiga kitchen daga yau."murmushi tayi sannan tace."To shikenan Umma insha Allah, zanyi ko kari  na bi shawarar da kika bani da yarda Allah."
Murmushi Umma tayi sannan tace."To Rumaisa, Allah yasa."..."Amin Umma, ni Umma zan cigaba da yin aiki kafin lokacin Isilamiya yayi, dan yau muna da Isilamiya."..."to Rumaisa Allah ya taimaka."... "Amin ya Allah."



Fadil ne zaune a office yana tunani duk abun duniya yayi mashi yawa, Abdullah ne ya shigo, tun dazun yana ma Fadil magana, amman bai jishi ba, bugasshi yake yana cewa."Fadil!  Fadil."firgigi ya dawo cikin haiyacin shi  yana cewa. "Naam Abdullah."kallon shi Abdullah yayi yana cewa."lafiyarka kalau kuwa."?ƙaƙaro murmushi yayi sannnan yace."Maika gani, ko nima baristancin za'ayi man."!? Dariya Abdullah yayi sannan yace."haba Fadil ai da an kalleka ansan baka cikin natsuwarka, Lafia mike damunka."?
Shiru yayi sannna kuma yace."Abdullah, Ruma ce."nazari Abdullah yayi sannna yace."mai ita Rumaisar tayi maka, har haka."?shafe zufar da ta fito mashi a goshi yayi, yana murza koshin shi sannnan yace."Abdullah ina son Ruma, akan Ruma ba abunda ba zanyi ba."ajiyar zuciya Abdullah yayi sannnan yace."To kaje ka gaya mata mana, sai kabar abu yana ci maka rai."Murmushi mai ciwo Fadil yayi sannan yace."Abdullah baka fahimceni ba, tun jiya na gaya mata, tun daga

Please Login or Register in order to submit comment