Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waya wasun ko kuma suna yi man textmassege wasu kuma suna yi man magana ta whatsapp akan baku ga 11&12 ba, tom kuyi hakuri mistake nayi wajen rubuta number amman idan kuka fahimci labarin yana tafiya dai dai ba'a tsalake wani waje ba, abunda nike so na gaya maku shine babu page 11&12 sai dai 13&14 nayi mistake ne sai ayi mana hakuri duba da abubuwa da suka yi man yawa shiyasa aka samu wannan akasin, Ina godiya kamar yanda kuke cewa kuna tare dani Nima haka ina tare da duk wani masoyina a duk inda yake🥰*

Karku manta *Yar'mutan kankia taku ce ❣️* ina godiya byeeeeee🤝🏻

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

    _STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_19&20

Tunda Rumaisa ta tashi bacci ta shirya ta wuce gidan aiki, sai da ta gama komai sanann ta wuce room din Fadila kwance ta tadda Fadila tana danna waya cewa tayi yana zama."Kawata gaya man matsalarki, naga kamar kina cikin matsala."? Murmushi Fadila tayi sannna ta tashi zaune tana cewa."Eh Rumaisa, amman ba wata matsala bace mai girma ba, amman abun yana damuna."kallon Rumaisa tayi yana mamakin wannan abun da yake damun ƙawarta cewa tayi tana mai dafa Fadila."Ayya maiye ke damunki har haka? Inasan naji komai ne wannan abun Fadila."girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace, cikin damuwa."Rumaisa, wani saurayi nayi kwannan, yana sona, amman nidai sai naga kamar bamu dace ba."kallonta Rumaisa tayi tana mamakin kalmar basu dace ba, ce mata tayi."Kamar ya baku dace ba? Bai da hali mai kyau ne? Ko kuma kawai bai yi maki ba Fadila."? Murmushi mai ciwo Fadila tayi sannan tace."Ko daya Rumaisa, Abdullah yana da kirki, duk da wannan zamanin baka yaban halin mutun koda ko uwarku daya, amman ina yi ma Abdullah kyaun zato."numfashi Rumaisa ta sauke sannan tace."Maiye to matsalar, da har kika ce *BAKU DACE* *BA* ? Abun da mamaki Fadila, tunda kince yana da hali mai kyau."kallonta Fadila tayi, sannna tace."Hmmm ba zan boye maki ba, inason Abdullah, abokin yaya Fadil ne, shima yana sona, saboda ya dade yana dakon sona, dan ni daga baya yake baiyana man sirin da ke cikin zuciyarshi,Abdullah yace yana sona, har nayi accepting din shi, mun fara soyayya, sai shekaran jiya wata yarinya ta turo man wani text marar dadin karanta wa, wai Abdullah yake yi mata kalar wannan maganganu banza, wanda basu da dadin ji,u
yace yana sonta,sun jima suna soyayya sai kawai taji labari gun abokanshi wai ni yake so yanzun ba ita ba, bayan ya gama yaudararta, ya gama bata mata rayuwa, shine yanzun zai juya mata baya ya dawo wajena, shine abun ke bani mamaki, wallahi abun yana damuna, bansan ya zanyi ba, shine nike neman shawarki Rumaisa na kyale Abdullah ko kuwa na cigaba da son shi."? Numfasawa Rumaisa tayi sannan tace."Uhmm, gaskiya dole kiyi mamaki, sannan kuma dole kiji kishi, amman a tawa shawarar shine karki rabu da Abdullah, a hankali in dai halinshi ne watarana dole a sirin shi ya tonu nidai a nawa tunanin kenan, dan kuwa komai yake dole watarana ki gane Fadila."Shiru Fadila tayi tana tunanin maganar Rumaisa sannan tace."Shikenan, Rumaisa yanda kika ce haka zanyi, tabbas Rumaisa ke din yar'uwata ce kuma aminiya, ina ma hmmm... MurmushibRumaisa tayi sannan tace."Ina ma mai kena? naji kin fara magana kinyi shiru."? Dariya Fadila tayi sosai sannan tace."Bakomai watarana Insha Allah zani gaya maki."cewa Rumaisa tayi.ok shikenan ni na wuce gida kinga mangarib har tayi." "ok byeee."
Haka Rumaisa tayi Sallama da Hajiya maryam ta gama gabanta zuwa gida, gidan nasu na *HAYA* mai mutane kala-kala..
Wani kallo Lami tayi ma Rumaisa tana dariya  sannan tace."Bita zai-zai kenan, har mundawo kenan Hindatu daga aiki."? Dariya Hindatu tayi sannan tace."Ai'haiye na naye, Lami kenan, mun dawo zamu shiga daki mu zauna kamar wasu mararsa gaskiya haha haha."dariya Lami tayi sanann tace."Yo daman gaskiyar ke gareki Hindatu?  anfita tun safe antafi wajen maza, sai yanzun aka dawo mana da nadasa a cikin gida ai dole ki shige daki."dariya sosai Lami tayi sannan tace."Ke dai bari Halimai, haka za'akare dai, ba'a gun wancen katon, ba'a gun wancen gardin ina ma amfani."cewa Halimai tayi."babu anfani Lami, Allah yasa mu gane dai."
Ita dai Rumaisa inda suke basu isheta kallo ba, ta shigewarta daki suka ci abinci tayi sallah ta kwanta suna labari da Mama suna cikin labari Baba ya dawo nan suka zauna sukayi fira sannan suka kwanta bacci..
Washe gari, yau Rumaisa ta tashi da wani zazzabi marar dadi, Wanda ya hana ta zuwa gun aiki..
Mama ce tace."Sannu Rumaisa, gaskiya kina jin jiki, kodai mu tafi asibiti."? Girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace."Aah Mama ba sai munje ba na fara jin sauki."cewa Mama tayi."Aa Rumaisa kidai tashi muje a duba lafiyarki, har yanzun ace mutun baya son ya asha magani."cewa Rumaisa tayi."naji sauki Mama, insha Allah ma zuwa anjima zani isilamiya."cewa Mama tayi."To shikenan Allah ya baki lafiya, bari na tashi na dama maki fura ki sha, sai ki sha magani."cewa tayi. "to shikenan Mama."Mama tace."Kwanta bari na tashi."girgiza kai tayi sannan tace."sanyi nike ji sosai Mama."Mama tace."to bari na lulubaiki, Allah ya baki lafiya kinji yar albarka."

*********************
Fadil ne yace ma Umma."Umma."..  "Naam Fadil wannnan kiran fa."? Cewa Fadil yayi."Wai ena Rumaisa ita nike jira tun dazun, amman har yanzun bata gama yi maku aikin ba."? Kallon shi Hajiya maryam tayi tana mamaki yanda Fadil yake nuna damuwarsa a fili a kan Rumaisa cewa tayi."Au ai duk yau bata shigo ba, inajin wani abu mai mahinmanci ne ya tsada ta shiyasa bata shigo ba."shiru yayi yana mamakin abunda zai hana Ruma zuwa yau, amman adduarshi Allah yasa lafiya, cewa tayi."To shikenan Allah yasa dai lafiya,mai kuka yi mana breakfast."?cewa tayi." Soyayen Irish mana Fadila tayi mana, gashi can dinning in zaka ci."
Cewa yayi."Nidai bani son Irish, ina awarata?  ita zanci kawai, amman gaskiya na koshi da wannan Irish din."kallonshi Umma tayi sanann tace."Shin kai dai kasani Fadil, tashi Ka ban waje ni, ka kira Fadila ta soya maka warar, kai ka dauki ta duka ka maida ta gunka, ka ringa soya abunka da kanka."cewa yayi."Ummma yanzun ita Fadilar bata soya man."? Cewa tayi."Eh gaskiya, dan yau Fadila ta gaji sosai ita daya tayi aikin gidan fa."tashi yayi yana cewa."to shikenan ni zan wuce na soya kayana, tunda ni na damu."cewa Hajiya maryam tayi."kai dai akeji Fadil."

*********************
Mama tace ta shigo tana cewa."Tashi kisha fura, ga magani nan sai ki sha."cikin jin raɗaɗin ciwo Rumaisa tace."Mama ni.... "ke mai Rumaisa, wahala zaki bani ko? Ke dai in baki lafiya shikenan baki kara cin abinci balle magani, haba ai yanzun kin girma, tashi ki ansa kafin raina ya baci."tashi tayi tace."to Mama."murmushi Mama tayi tace. "yauwa ko kefa.."haka taci abinci sannan ta sha magani ta koma ta kwanta, koda dare yayi Babanta ya dawo cewa yayi."Sannu Rumaisa."cewa tayi."yauwa Baba, ka dawo lafiya."? Cewa yayi."Lafiya lau ya jikin."?cewa tayi."Da sauki Baba."dafa koshinta yayi sannan yace."Allah ya baki lafiya."kallon Mama yayi sannan yace."Maman Rumaisa gobe Insha Allah ki kai ta chemist din Bala ko allura yayi mata muga yanda hali zaiyi."cewa Mama tayi."to shikenan Allah ya kaimu goben Lafiya." "Amin ya Allah."

*********************
Fadil ne ya shigo part din Hajiya maryam, zaunawa yayi ya fara gaida Mahaifiyar ta shi sannan yace."Umma." kallon shi Umma tayi sannan tace."ina jinka, lafiya."?Sosa ƙeya yayi sannan yace."Eh to Umma, amman kinga duk yau Rumaisa bata zo ba, Allah yasa lafiya."Murmushi tayi sannan tace."Amin ya Allah, nima abunda nike tunani kenan, abunda Rumaisa bata taba yi ba, in bata zo yau ba,  gobe sai muje muga ko lafiya."cewa yayi."To shikenan Allah yasa dai lafiya."cewa tayi."Amin tashi kije ki kwanta dare yayi, nima sai da safe."
Cewa yayi."ok Umma byeee tooo."






_*Ina masoyana suke😘masoyan yar'mutan kankia, wanda suke fadin yar'mutan kankia itace tauraruwa a social media, nice dai yar'mutan kankia wanda ta kawo maku NANA JAWAHEER, karku manta irin soyayyar da aka sha da Sadiq da Nana, sannan kuma ta sake kawo maku shahararrin litafin nan nata wato GIMBIYA HAKIMA inda aka zuba soyayya Hakima da Hakim, sannan kuma ta kowo maku SANADIN LINK, inda Sofy ta cancaɗa soyayya da Aliyunta, ba tayi ƙasa a gwiwa ba tazo ta kawo kamu IZZAH KO MULKI, inda kukaga yanda ake mulkin zalinci, sannan kuma kuka ga yanda ake makirci iri iri, ga ban tausayi dai dau abubuwa a cikin Izzah ko mulki.*_

_*Yanzun kuma take kawo maku A GIDAN HAYA, wanda A GIDAN HAYA aka fara wasan dan ko ba'ayi komai a cikin shi ba😁, uwa uba kuma ga SADAUKIN BURHAAN, wowowoho!!!! SADAUKIN BURHAAN kenan karku manta cigaban Izzah ko mulki ne, inda zakuji ina Sadauki yaje? Wata kallar fansa Sadauki zai dauka? Abubuwa da dama fa😘, To Masoyana anan zaku nuna man soyayyar da kuke cewa kuna yi man, domin ku masoyana, zan baku GARAƁASA! GARAƁASA!! GARAƁASA!!!  Daga yau 10/9/2020 zan sakar maku da Sadaukin Burhaan akan naira 200kacal, karku manta naira 300 nasa shi to duk domin ku masoyana mai doshi 200 daga yau tara ga wata zuwa ashirin da ɗaya ga wannan watan na satuba 31/9/2020 an single kenan, yan vips kuma nai maido maku shi akan naira 400,karku manta daga yau 9 ga zuwa 31 ga watan September din nan insha Allah.*_

_Wata GARAƁASAR kuma masu bukatar karanta Izzah ko Mulki yanda zasu ji dadin karanta Sadaukin burhaan su fahimci ida labarin ya dosa zaku bada naira 100 kacal ba baku document din sa, kunga kenan idan single ki saya Sadaukin burhaan zaku bada naira 300 duk da Izza ko mulki, idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada dari 200 kawai, idan kuma vips ne zaku bada naira dari 450 duka biyun kenan sadauki da izzah ko mulki idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada naira 400 kawai  Masoyana karku manta tana nan ne kawia zaku nuna man kaunar da kuk cewa kuna ma NOVELS dina, sannan kuma Hausawa sunce sayan na gari mai da kudi gida😍, ina maraba daku MY GUYS🥰_

*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
   _Jameelah jameey_

*yar'mutan kankia ce❣️*       

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannnan page din naki ne Auntyna, Wato BINTA UMAR ABBALE, Allah yabar kaunar da zuminci, Allah ya kara nisan kwana Aunty Bintu🥰*


Page_21&22

Har yanzun jikin Rumaisa sai dai addu'a dan tana dan jin jiki ba laifi, kwance take sai ga Mama ta shigo tace."Tashi mu tafi Rumaisa, ayi maki wannan allura ko mun dawo."kallon Mama tayi sannan tace."Wayyo Mama wallahi ban son wannan allura nike ba, dan Allah kayi hakuri kice ma Baba anyi mani kawai kinga daman ai naji sauki sosai."wani kallon banza Mama tayi mata, tana mamakin yanda Rumaisa bata san allura da magani cewa Mama tay."To bada ni za'ayi wannan rashin hankalin ba, inke baki da hankali ni inada hankali, a haka zamu sama maki ido baki lafiya amman muki baki magani, ai duk da sauki na gun Allah, amman Allah yace in baku lafiya kunsha maganin."sannan cigaba da cewa mama tayi."Dan haka tashi mu tafi tun muna mu biyu, kafin raina ya baci, Allah sai na bata maki rai."cikin irin tausayin nan Rumaisa tayi duk dan Mama taji tausayinta tace."Yi hakuri Mama yanzun zan tashi mu tafi, amman nidai tsoro nike ji sosai, bani son  wannan allura ko kadan Allah."hijab dinta Mama ta dauka ta bata sannan itama tasa tata hijab tana cema Rumaisa." Kinji dashi yar'nema, ke dai Rumaisa mijinki zai sa fama, ace mutum bai shan kagani kuma bai son allura, sai dai kawai aka ce mashi sannu ya ansawa, to ni Hadiza ba haka nike ba, dan haka tashi maza mu tafi wallahi na kusa sa maki bulala Rumaisa."tashi Rumaisa tayi tana cewa."yi hakuri na tashi mu tafi Mama."nan suka fito a tsakar gida, nan Mama tace ma yan mutan gida."To  mutan gidan nan mun tafi chemist sai mun dawo, za'ayi ma Rumaisa allura bata jin dadin jikin ta."cewa Mama A'I tayi."Ayyya Rumaisa Allah ya baki lafiya."cewa Mama tayi tana murmusi."Amin ya Allah Maman A'I."cigaba da cewa Maman A'I tayi."To Maman Rumaisa, adawo lfy."cewa Mama tayi."Allah yasa Maman A'i, A'i abincin ake ci ba'a bani, mun wuce."
Shewa Halimai tayi tana dariya tace."Allah yasa dai ba abun kunya aka dauko mana a cikin gida ba."dariya Lami tayi sannan tace." Amin Halimai nima abunda nike  tunani kenan, dan jiya cikin kunnena naji tana amai da dare, Allah ya kara ma."Hindatu ta bushe da dariya sannan tace."sai ku gaya man, bari mu fara tara kudin raggon suna, da kayan mai jego."kallon su Maman A'I tayi tana mamakin mugun hali iri na su Halimai sannan tace masu."Yanzun ku wai maiyasa baku gyale Yaya Hadiza ita da Rumaisa su sha numfashi a gabanku?Ace mutun shi kullun ba alkwari a cikin zuciyarshi sai Shari, ku baku yi mata ya mai jiki ba, amman kun sama mata ido cikin gida, kuma baku hada komai dasu ba *GIDAN* *HAYA NE* ya hadu amman kuna kishi da baiwar Allah."wata rin ashar Halimai tayi sanna tace."Wai Maman A'i maiyasa kike shiga abunda bai shafeki ba."?Lami ce ta ansa maganar tana cewa."Ke dai kyaleta Halimai, abun nan yana bani haushi sosai, ke dai bamu Sanyo ki ba cikin hidamarmu ba,amman kin sama ido a gida, wallahi ki fita a harkarmu Maman A'i muna ganin girman ki."Hindatu tace."kin dai gaya nata Lami, na lura Maman A'i tana son shiga hancinmu da gudundune, dan haka kiyi harkarki muma muyi tamu cikin gidan tunda nagadai gida ba na mijin kowa bane a cikin mu, gida dai naga *GIDAN* *HAYA NE*."kallon su Maman A'i tayi, taga yanda duk suka tadda jijiyojin wuya cewa tayi."Allah ya baku hakuri, bansan zaiyi maku zafi har haka ba da bansa maku baki ba, amman insha Allah daga yau na daina, kuma Insha Allah watarana zaku daina."cewa Halimai tayi."Wannan kuma ke kika san shi, hakuri ba, baki san mu ba mu san wata kalma wai ita hakuri ba, yau muka fara jin ta kuma daga cikin bakin ki muka ji ta, mudai kawai zaman lafiya a gidan nan shine ki fita a idonmu mu kulle."tashi Maman A'i tayi bata ce masu komai ba ta wuce dakinta,suko Rumaisa tunda suka tafi take hawaye dan tana tsoran Allura sosai, koda akayi mata allurar kuka ta tashe dashi sosai Mama ce tace."Rauguwar banza, ke da kike mace, watarana haihuwa zaki yi fa Rumaisa, amman kike yi ma allura wannan ihun sai kace wanda aka cika ma wuka a wuya, Allah ya kiyaye dan wannan rauganci ba Kara in mamaki kika bani ba."cewa tayi tana goge hawaye."Allah Mama baki ji yanda nike ji ba, gashi allurar shegin zafi ne da ita, ni nasa ma na mutu."tsaki Mama tayi sannan tace."Eh kin mutu dawowa kika yi yar'nema, yanzun allurar ita ake cema wa kamar an mutu, duka minti nawa ne akeyi, Allah dai ya sawaka maki."cewa tayi." Amin Mama ni nama samu sauki, gobe zani koma bakin aiki  na, dan nagaji da kwanciya har jikinka yayi ciwo."kallon Mama tayi sannan tace."Allah ya kaimu lafiya, amman dan kar a kuma yi maki allura shiyasa zaki koma aiki." Cewa tayi."Amin Mama, kinsan nayi missing din Fadila sosai, itama tana can tana missing dinna."cewa Mama tayi."kudai keda Fadila Allah ne ya hada ku."murmushi Rumaisa tayi sannan tace."hakane ko Mama."haka suka kama labari har suka iso gida suka shige room din su.

***********************
"Fadila! Fadila!! Fadila!!! Wai wannan wani kallar shiri ne kike kin barni tsaye, kamar wata dogarin sarki? Kin fito ko sai mun tafiyarmu, ga Fadil can ya fara dan na mana uban horn shima marar hakuri kawai."Umma ce ke cema Fadila haka dan tun dazun take jiran Fadila ta fito su tafi, amman ta tsaya kwaliya, Fadila ce tace."Umma gani nan, hijab na dauko shiyasa."cewa Umma tayi."kedai kika sani, shiga kitchen ki dauko cooler abincin na nan da zamu tafi da ita."ta fitowa tayi ta wuce kitchen sanna tace."to Umma, mu tafi na dauko." Suma fitowa Fadil ya wurga ma Fadila wata uwar harara sannan yace."Fadila daga yau karki sake ki ƙara ɓata ma mutane lokaci in zamu yi tafiya, inba haka ba wallahi sai dai ki hau motarki ki iske mu, ba wanda zai tsaya bata lokaci gun jiranki, fatan dai kinji ni."? Lura da yanda ranshi ya ɓaci Fadila tayi sumi sumi tace mashi."Naji yi hakuri Yaya Fadil, da gyale na dauko sai naga ya dace ace hijab nasa shiyasa na koma na nemo wanda zata hau da kayana."cewa Umma tayi."Allah dai ya sawaka, yanzun ace Fadila ku yanmatan zamani komai zakusa sai kunyi tomarch da komai naku."cewa Fadila tayi."Ai Umma mun fi kyau in munyi tomarch."shi dai Fadil bai ce masu komai ya cigaba da driving din shi,cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

*********************
"Rumaisa tashi ki shiga wanka ko."? Cewa tayi."to Mama yanzun nike son na tashi ko na kara jin dadin jikina."cewa Mama tayi tana murmushi."yauwa tashi mu wuce, shiga kiyi sauri ki fito, nima  shiga zanyi kina fitowa."cewa tayi."to shikenan."

********************
"Umma mu fara zuwa shoprite muyi masu shopping ko."?cewa Umma tayi."Nima abunda zance kenan bai ka mata muje daga mu sai cooler abincin ba." nan su Umma suka biya shoprite suka yi ma Rumaisa shopping kanan suka kama hanya gidan su Wanda ake kira da *DAKI GOMA*.

***********************
Rumaisa na fitowa wanka ta tsare ma Mama ta shiga Mama na fitowa zasu tafi Mama ce tace ma Rumaisa."wuce ki shirya sai ki kwanta, tunda mun samu munyi wanka."cewa Rumaisa tayi."to Mama."Rumaisa taji an watsa mata fitsari a jiki, kallon Lami tayi sanna tace."kai Lami ni zaki watsa ma fitsari a jiki bayan kuma gaban idonki nayi wanka."harararta Lami tayi sannna tace."An watsa maki fitsarin sai kiyi abunda zakiyi in zaki iya, banza dake kazama."sosai Mama taji haushin abunda Lami tayi ma Rumaisa cewa Mama tayi." Yau da ni za kuyi cikin gidan nan, ni uwar Rumaisa ba Rumaisa ba, na fahimci gidan nan baku san zaman lafiya,kunfi san ayi yar rashin mutunci."cewa Lami tayi tana dariya."Abu mai sauki, sai muyi dake din ai ba tsoran ki nike ba, da zaki wani daure kirji kina yiman wani jan ido."Cewa Mama tayi."Ai daman nasan karnikanci abu mai sauki ne a wurinki."da sauri Maman A'i ta fito tana cewa."dan Allah Maman Rumaisa kiyi hakuri ki gyale ta,  laifi dai tayi amman dan Allah kiyi hakuri."
Parking din motarsu kenan a kofar gidan su Rumaisa Umma tace."Ji nike kamar hayaniya  a cikin gidan ko."?cewa Fadil yayi."Umma nima naji kamar hayaniya Allah yasa dai ba mutuwa akayi ba."cewa Fadila tayi cikin tashin hankali."Amin naji kamar ana kiran Maman Rumaisa, Allah yasa muji alkhari."cewa Fadil tayi."Amin Fadila ku shiga mana, dan Allah kunyi tsaye."daurewa Umma tayi tace ma Fadil."gidan ku Fadil, ba'a, ko baka ga niyar s shiga muke ba."cewa yayi."yi hakuri Umma."nan su Fadila suka tafi suka shiga sallama sukayi."Assalama Alaikum....





_*Ina masoyana suke😘masoyan yar'mutan kankia, wanda suke fadin yar'mutan kankia itace tauraruwa a social media, nice dai yar'mutan kankia wanda ta kawo maku NANA JAWAHEER, karku manta irin soyayyar da aka sha da Sadiq da Nana, sannan kuma ta sake kawo maku shahararrin litafin nan nata wato GIMBIYA HAKIMA inda aka zuba soyayya Hakima da Hakim, sannan kuma ta kowo maku SANADIN LINK, inda Sofy ta cancaɗa soyayya da Aliyunta, ba tayi ƙasa a gwiwa ba tazo ta kawo kamu IZZAH KO MULKI, inda kukaga yanda ake mulkin zalinci, sannan kuma kuka ga yanda ake makirci iri iri, ga ban tausayi dai dau abubuwa a cikin Izzah ko mulki.*_

_*Yanzun kuma take kawo maku A GIDAN HAYA, wanda A GIDAN HAYA aka fara wasan dan ko ba'ayi komai a cikin shi ba😁, uwa uba kuma ga SADAUKIN BURHAAN, wowowoho!!!! SADAUKIN BURHAAN kenan karku manta cigaban Izzah ko mulki ne, inda zakuji ina Sadauki yaje? Wata kallar fansa Sadauki zai dauka? Abubuwa da dama fa😘, To Masoyana anan zaku nuna man soyayyar da kuke cewa kuna yi man, domin ku masoyana, zan baku GARAƁASA! GARAƁASA!! GARAƁASA!!!  Daga yau 10/9/2020 zan sakar maku da Sadaukin Burhaan akan naira 200kacal, karku manta naira 300 nasa shi to duk domin ku masoyana mai doshi 200 daga yau tara ga wata zuwa ashirin da ɗaya ga wannan watan na satuba 31/9/2020 an single kenan, yan vips kuma nai maido maku shi akan naira 400,karku manta daga yau 9 ga zuwa 31 ga watan September din nan insha Allah.*_

_Wata GARAƁASAR kuma masu bukatar karanta Izzah ko Mulki yanda zasu ji dadin karanta Sadaukin burhaan su fahimci ida labarin ya dosa zaku bada naira 100 kacal ba baku document din sa, kunga kenan idan single ki saya Sadaukin burhaan zaku bada naira 300 duk da Izza ko mulki, idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada dari 200 kawai, idan kuma vips ne zaku bada naira dari 450 duka biyun kenan sadauki da izzah ko mulki idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada naira 400 kawai  Masoyana karku manta tana nan ne kawia zaku nuna man kaunar da kuk cewa kuna ma NOVELS dina, sannan kuma Hausawa sunce sayan na gari mai da kudi gida😍, ina maraba daku MY GUYS🥰_

*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share
Comments
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
      

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_23&24

Da sauri Hajiya Maryam ta ida shigowa cikin gidan su Rumaisa, nan ta fara magana tana cewa."Subuhanalillah, lafiya mutanan gidan nan? nike jin hayaniya tun daga kofar gida."? Murmushi Mama tayi sannan tace mata."Hajiya lafiya lau, sannu da zuwa, anzo lafiya."?Itama Murmushin tayi sannan tace."Lafiya lau, nace lafiya duk naga mutanan gidan nan kowa ranshi bace."?
Cewa Maman A'i  tayi tana murmushi."Lafiya lau Hajiya, an dan samu sabani ne tsakanin lami da Maman Rumaisa."kallon Lami Hajiya Maryam tayi sannan tace."ikon Allah mai ye ya hada su."?
Maman A'i tace mata."Eh to Lami ta watsa ma Rumaisa fitsari, bayan ta san Rumaisa bata dade da fitowa daga wanka ba, gashi kuma bata lafiya."wata irin uwar harara Hajiya Maryam tayi ma Lami sannan tace tana kallonta."Subuhanalillah, ashe Lami yar yanzun baki da mutunci, yarinya bata lafiya amman kika watsa mata fitsari."?
Murguɗa baki Lami tayi, tana girgiza tana huce tace ma Umma."Eh din Hajiya, an watsa mata fitsari, ai shine nace ayi abunda za'ayi, zaki wani zo kina gaya ma mutane magana son ranki."
Murmushi Umma tayi, dan batayi mamakin maganar da Lami tayi mata ba, dan tasan su farin sani ba mutunci suka cika ba, ammman sai Maman A'i tace ma Lami."Yanzun Lami Hajiya Maryam kike gaya ma wannan maganar."?
Tsaki Lami tayi sannan tace."Angaya mata, inji bugu ko kuma na gan ni a offishin yan sanda, sai kace wata gold da, naje na gaya maganin abun."murmushi Hajiya Maryam tayi sannan tace ma Lami."Shikenan bakomai Lami, banyi mamaki ba dan kinyi man haka, abunda yafi haka ma kin iya yin shi."cewa Lami tayi."Oho dai, nagode Allah ina da zuciya, duk kudin mutun sai na gaya mashi ta cikina, koda da kudi yake yin mafashin kai, bai damaini ba sai na kalli idon mutun nagaya mashi abunda nayi niya eheeeey."Maman Rumaisa ce tace ma Umma."Hajiya dan Allah kiyi hakuri, ku shigo daki mana, munbarku a tsakar gida tsaye."kallonta Umma tayi, taji ta kara kwanta mata rai, dan babu shaka duk halinta Rumaisa ta dauko, cewa Umma tayi."Bakomai Maman Rumaisa, kuta hakuri da halin su dai,  ke Fadila zo mu shiga ciki, kinyi tsaye a nan."cewa Fadila tayi."To Umma, amman bari na gaya ma yaya Fadil ba abunda ke faruwa, nasan yanzun hankalinki tashe yake."cewa Umma tayi."To yi maza kije ki gaya mashi, sai ki shigo da cooler din kinji."? Cewa tayi na fita."To shikenan, insha Allah Umma."tana zuwa tace."yaya Fadil."kallonta yayi yace jiki duk a sanyaye."naam ina fatan lafiya dai, ba abunda ya faru da Ruma."!? Kallon shi Fadila tayi tana murmushi, dan ta lura yayan

Please Login or Register in order to submit comment