Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna da kirki sosai, ni da ina yi ma Yaya Fadil kallon marar mutunci, ashe ba haka abun yake ba, Allah na tuba, Shiyasa ba kyau yin zato, gashi naga deal ai yanzun." haka dai har ta gama hada mashi tea da yaji kayan hadi, dan *TURKEY* *TEA* ta hada mashi, sannan ta kai mashi...
"Ga tea din nan Yaya Fadil."kallonta yayi sannan yace."To Ruma sannu da aiki, nagode sosai kinji Ruma."cewa tayi."haba Yaya Fadil, sai kace wani abu, da zaka ce ka gode, asha lafiya."murmushi kawai yayi yace."to Allah yasa." nan Rumaisa ta shiga cikin bedroom ta fara gyara shi dan yau harda new bedsheet ta sauya ma bedroom din, ta shiga bathroom shima ta gyara shi ta chanza new carpet don daman bathroom din ba wani baci yayi ba don Fadil ba daga baya ba wajen tsafa, sai da tagama gyara ko ina sannan ta dawo sitting room lokacin ya gama shan tea din yana ta game din shi....
"Yaya Fadil, zan gyra nan amman inka gama."cewa yayi."to Ruma bari na tashi, amman inkin gama ki yi man magana kafin ki wuce."? Cewa tayi."to shikenan, insha Allah." nan fa shima sitting room ta gyrashi tsaf da dashi ta chanza ma duk royals din nan waje tayi mopping sanann ta kunna boner nan take dakin ya gume da kamshi mai sanyaya zuciya, ta wuce kitchen ta gyra sannan ta fito, tace."Yaya Fadil na gama."cewa yayi."ok Ruma, gani nan zuwa, dan jirani kadan kinji."samun waje tayi ta zauna tace."to yaya Fadil."sai da ya ida gama abunda yake sannan ya fito yace."yauwa sannu da aiki Ruma."cewa tayi."yauwa yaya Fadil."zama shima yayi sannan yace."anshi wannan kin saya jan baki da za'ayi kwaliya."kallon kudin hannun shi tayi sannan tace."to ngd, amman don Allah yaya Fadil kabar kudin ka nagode."sosai Fadil yayi mamakin yanda taƙi ansar kudin, nan take ta ƙara shiga zuciyar shi cewa yayi."Ruma keki tambayeni na baki kudi."? Girgiza mashi kai tayi sannan tace. "Aah bani bace." daure fuska yayi tamou sannan yace."to bari kiji, in har kina san karda muyi fada daga yau in har na baki wani abu karki ce baki ansa, kin dai jini ko."? Cikin tsoro tace."Eh naji kayi hakuri."dan sakin fuskarshi yayi yace."naji karki sake Ruma, dan ni bani bada abu ace ba'a ansa, haka nike bani bada abu amai doman, tashi ki ka tafi, kaji mince zaki tafi isilamiya karda ki makara."tashi tayi tana cewa."To shikenan, nagode yaya Fadil."har ta kusa fita taji yace."Ruma."waigowa tayi tace."Naam."rasa abunda da zaice mata yayi ji yayi yana cewa."daga yau ki ringa dafa man tea di nan da yawa wanda zai kaini har safe kinji."? Cewa tay."Eh Insha Allah, sai anjima." shi ko Fadil bai son ta tafi doman bai son abunda zai yanke fira da ita dan yana bala in jin dadin muryarta ita dai Ruma da ban take cikin mutanan, komai ta iya haka Allah yayi ta dai.
Tunda ta fito daga part din Fadil take gode ma Allah da suka rabu lafiya dashi, zuwa tayi wajen Fadila tace."Fadila taso na yi maki ko na tafi."kallonta Fadila tayi sannan tace."wai Rumainsar Mama saurin mai kike har haka."? Ce mata tayi."Wallahi Fadilar Yaya Fadil, sauri nike yau Isilamiya zan tafi bani son na makara shiyasa."tashi Fadila tayi tace."ok to yi man sai ki tafi, ammn naso yau muyi fira sosai, amman bakomai, in kinzo munyi gobe."cewa Rumaisa tayi."to shikenan." nan Rumaisa tayi ma Fadila kalaba, sannan ta wuce gida, ta dauki abincin ta koda taje gida samun taje gida kwantawa tayi kusa da Mama tana cewa."wai Allah na, Mama yau duk nagaji sosai."kallonta Mama tayi sannan tace."to Rumaisa, sannun kinji, Allah yayi maki albarka."cewa tayi."amin ya Allah Mama, ga wannan kudin Fadil ne ya bani su."kallon kudin Mama take sannan tace."Rumaisa wannan kudin basu yi yawa ba."? Numfasawa Rumaisa tayi sannna tace."Mama sai da nace bani amsa amman yace sai na amsa na ni da yanda zani yi."jinjina ma Fadik Mama tayi sannan tace."mun gode, Allah ya kara masu bude."cewa Rumaisa tayi."Amin ya Allah, yanzun bari dai na tashi na wuce isilamiya karda na makara kin san halin malam Ahmed sai yace zai wulakantaka ba abu bane mai wuya agareshi."cewa Mama tayi."To tashi maza ki tafi, inkin dawo kinci abincin, dan nasan baki komai ba har yanzun."cewa tayi tana mikewa tsaye."to Mama na tafi."cewa Mama tayi."adawo lafiya."
Bayan Rumaisa taje isilamiya sun gama yin karatu, hanyarta ta dawowa ta gamu da Fadil a hanya shima,ji tayi yace."Ruma."tsayawa tayi tace."Naam Yaya Fadil, kai ne nan  da kanka."? Kallonta yayi ya kauda kai sanann yace.eh nine, daman nan wurin isilamiyarku take kenan."?ansa mashi tayi da."Eh nan ne, gama ta can."waigawa yayi yaga isilamiyar sanna yace."wai da itace kenan? Allah sarki, yanzun kuma gida zaki sannan ki huta ko."? Murmushi tayi sannan tace."Eh wallahi gida zani na samu na dan huta, kafin mu daura abincin dare nida Mama."cewa yayi."to shigo na kaiki gida mana."cewa tayi."Yaya Fadil na hutar dakai ai gidan ba wani nisa keda akwai ba."wani kallo yayi mata sannaan yace."wallahi Ruma daga na sake saki abu kika yi man gardama sai na ɓata maki rai, ki bari sai na saki abunda Allah ya haranta mana da muyi shi sannan kice bakiyi, oya come in Madam."hakuri ta bashi sannan ta shiga motar  sannan tace"to shikenan nagode."ce mata yayi."Sannu Ruma, kina kokari sosai."kallonshi tayi sannan tace."Yauwa Yaya Fadil, amman ba wani aiki bane mai wahala ba."cewa yayi ba tare da ya kalleta ba."daman kema nan ne unguwarku kenan."? Ce mashi tayi."eh mna unguwarmu daya da ku ai."murmusawa yayi sanna yace."to nuna man gidanku sai na ajiye ki nima na wuce."ce mashi tayi."kana shan wannan kwanar shikenan kazo gidan mu."sai da ya sha kwanar da tace mashi sannan yace."to shikenan, ai mun iso kenan."? Cewa tayi. "aiko dai, to nagode sosai."tadda motar yayi yana cewa."bakomai ki gaida man da Mama."cewa tayi."to zataji."tafiya ta fara yi taji ana cewa."Na boni, ni Halimai, mutanan gidan ku fito kuji ikon Allah, dan Allah duk ki fito, zargin da muke yau dai ya taibabata gaskiya."Hindatu ce ta fito tana cewa."lafiya Halima? zaki tadamu muna cikin hutu."? Cewa Halimai tayi."Ina fa lafiya Hindatu, ai wani baƙin gani nayi."Lami ce ta tashi har tana faduwa tana cewa."baƙin gani kuma Halimai."? Cewa Halimai tayi."Eh Lami baƙin gani, ki godema Allah da bake kika yi wannan bakin ganin ba."tambayarya sukayi a tare suna cewa."wannan wani kalar bakin ganine har haka."? Cewa Halimai tayi."Yanzun naga wani mutum ya sauke Rumaisa cikin wata bakar mota, kafin ta fito sai da tayi kusan minti 20, sannan ta fito tana gyra hijab dinta."wata irin dariya Hindatu tayi sannan tace." daman ke sai yau kika fara gani Halimai."? Kallonta Halimai tayi sannan tace."Eh Hindatu, kardai kice man kema kin gani."? Cewa Hindatu tayi."yo wani dare ne jemage bai gani ba? sau nawa ina kamata, ke ni nan har gani nayi wani gardin Allah yana yi mata kiss, yo da man ai ku ake yi ma alaye da sunan gidan aiki da isilamiya ba dai ni ba."kallonsu Lami tayi sannan tace."Ni fa duk kun sani a duhu, kuna nufin Rumaisa da gaske tana bin *MAZA*." ? cewa Halimai tayi."haba Lami, sai kace wanda bata waye ba, ai da kinga ido Rumaisa kinga idon Yan duniyarnan, wanda suka zama Yan hannu a cikin harka."cewa Lami tayia tana mamaki."Tabbas biri yayi kama da mutun, banyi mamaki ba, yanda suke cin abinci mai kyau, su sa kaya masu kyau, ai dole wanann harkar sai da bin mazan banza, dan ba kudin keke napen kawai ne zasu rike mutum ukku ba."
Cikin fushi da konar zuciya Rumaisa ce tace masu."Ya ishe ku haka...

*😂😂😂😂 ya kuke ganin next page zai kaya tsakanin Rumaisa da su Lami🤔,  sai naga ruwan comment dinku sannan zan baku next page😉*

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

Share
Comments
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey_
*Ƴar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
____________________________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannan page din na yan Team Rumaisa ne kuyi yanda kuke so da shi😂❣️*

Page_15&16

Shiga tayi ta wankr Lami da mari sannan ta cigaba da cewa."Lami nace ya ishe ku haka, zan iya jure duk wani abu da zaku yi man a cikin gidan nan, amman banda sharin bin maza, dan ku baku isa kuyi man sharin zina ba, ku baku ganin bala'in da yayi maku yawa amman kuna zagin wasu har kuna masu sheri wallahi ku kiyaye ni."
Lami dafe kunci tayi dan taji marin da Rumaisa tayi mata sai da tayi mutuwar wucin gadi sannaan ta dawo dai dai cewa tayi."kam bara'uban can, dan ubanki rashin kunyar taki har takai da kisa hannu ki mareni? Bayan Halimai da idonta tga ganki wani sheri mukayi maki? Wallahi baki mari banza, kedin banza kidin wofi, banza mazanaciya, ai dai yi abun kunya arasa wata sana'a za'a kasa a cikin gari sai sana'ar bin maza, dan kinga Allah ya baki kyau shine zaki zuba hannun jari da shi, andai ji kunya idan ansanta, kuma ni bazan rama marin dakika yi man ba, daman ance tabarmar kunya da hauka ake naɗeta."
Ƙara yowa kan Lami Rumaisa tayi, aiko Lami ta kauce ta wanka ma Halimai wani wawan mari, dan Halimai bata san lokacin da ta kurma uban ihu ba, marin ya shigeta sosai, dan so tayi ta zauce ma, nuna ta Rumaisa tayi da yatsa tana zare mata ido tana mata kallon tsana, dan ji take ta tsanesu su dukansu cewa tayi."ke ai kiga gani ko? To yau duk sai naci ubanku cikin gidan nan, matsiyatan banza matsiyatan wofi, ke har kike da bakin da zaki yi ma wani munufinci a gidan nan, ke idan akace za'a tona maki asiri a gidan nan wallahi magana baki sake fitowa kiyi shashar banza dake wanda bata ajiye komai ba a ranta sai bakin cikin da hassada kuma hassada ga mai rabo taki ce wawaye daku daƙiƙan banza daku, inba kuna jahilai ba yaushe ake irin haka? Wai ni zaku yi ma sheri na zina wallahi bazan kyaleku ba."
Ƙarfin hali Halimai tayi tace ma Rumaisa."Dallah malama yi ma mutane shiru, ke harda bakin magana ke gareki? bayan da idona na ganki cikin mota, kuma wallahi tinda har kika mareni kindaina zaman lafiya a gidan nan, kuma bazani fasa gaya ma kowa ba Rumaisa mazinaciya bace tana bin mazan banza."
Sheƙima Halimai wuya Rumaisa tayi, dan Halimai sai da idanuwanta suka fito waje ta fara kakarin mutuwa, sosai su Hindatu suka tsorata da lamarin Rumaisa, cewa Rumaisa tayi."Ni ko ke da bakin magana, dan kin ganni cikin mota shine aka ce maki wani abu mukayi."? Sakekin Halimai tayi, on-experting Hindatu taji Rumaisa ta sheƙeta, itama wanka mata marika hudu tayi lafiyaiyu, dan dama ita tafi jin ciwon maganarta wai tana ganinta namiji yana mata kiss dare ita da ko fitar dare batayi amman Hindatu ke cewa haka, cigaba da ce ma Hindatu tayi."ke kuma Hindatu da kike cewa kin ganni wani yana yi man kiss, ki kiyaye ni wallahi kin san nasan komai, idan kika kuskura kika sake yi man Shari wallahi sai na fasa kwan gidan nan kowa yaji, wallahi idan har na tona maki asiri a gidan nan, sai aurenki ya mutu, kema ai kisan da haka, kidahumar banza, bagidajiya kawai wanda bata da ilimi, inba ku jakkane taya zaku yi haka? Wallahi ku kiyayeni ku dukanku a gidan nan."
Cigaba da cewa Rumaisa tayi."Ko dan kunga muna sama ku ido cikin gidan nan? to haka ba yana nufin muna tsoran ku bane, Aa sai dai kawai dan mu zauna lafiya daku tunda *GIDAN HAYA* ya hadamu, bamu sanku ba,  kuma haka baku sanmu ba sai dan ta dalilin *GIDAN HAYA,* shiyasa muka san juna, dan haka ku kama girman ku, idan ko ba hak... Halimai da ta dawo dai dai ta tari numfashin Rumaisa ta hanata ta ida magana tace."Kam bala' in nan, ke har kin isa kizo ki gaya mana magana, har kina yi mana barazana? To barazanarki ba tsoro zata bamu ba, dan haka indan muka gani sai mun fadi ehyyeh."wani wawan kallo Rumaisa tayi mata, sannan tayi tsaki tace. "to ai ga fili ga mai dokinan HALIMAI nida ke shige ka fasa."
caraf Halimai tace tana girgiza girji sai kace wani abun kirki zata iya yima Rumaisa abunda yanzun ta gama kwasa masu tafi sun kasa komai sai yanzun take da bakin magana cewa tayi."Dan halal sai yanka, ko yar mararsa mutunci."? Tsaki Rumaisa tayi tana nuna ta da yatsa tace."ga ki nan wanda bata gado arziki ba, wallahi da kin gado arziki Halimai da baki yi wasu jakkanci ba, kuma harda rashin ilimin arabi da dana boko shiyasa kwalwarki ta tose jahila adai koma a nemi ilimi."Mama ce ta fito tace ma Rumaisa."Rumaisa Indai ni na haifeki to bance ki sake yi masu magana ba, ki shigo daki." wasu hawaye ne Rumaisa tayi sun zubo mata,kallon Mama tayi sannan tace."Amman Mama.. "yi man shiru amman ma? ni HADIZA ai nasan halin diyar da Allah ya bani ko? Kuma nasan abunda zaki iya dama wanda ba zaki'iya ba, dan haka shigo kici abincin ki."Mama tace ma Rumaisa cikin ɓacin rai, dan taga idan ba haka tayi mata ba, abun sai ya wuce tunanin su Lami, dan ran Rumaisa ya ɓaci sosai tana iya yi masu komai, kuma daga baya azo ana dana sani.
Sai da Hindatu taga tafiyar Rumaisa sanann tayi dariya tana cewa."Aikin banza, in ba tsoro ba kudawo mu cigaba mana."Halimai tace tana buga gaba tana cewa."har ni Halimai za'ayi ma barazana, babu wanda ya isa cikin gidan nan, gida dai ba na kowa bane eyyeh, gidan *GIDAN* *HAYA* ne, balle ayi mana wani iyayi."ita dai Lami bata sake cewa komai ba, tun marin da tasha, tashi tayi ta shige daki, dan kunya ma abun ya bata, dan ta tabbata su Halimai sheri sukayi ma Rumaisa, kuma ita ai gaya mata sukayi amman Rumaisa zata haɗa da ita taita kwasa masu mari kamar itace uwarsu.
Niko Jameey nace idan Lami zaki biye ma sabgar su Halimai wallahi yanzun kika fara ganin ɓacin rai 😎.
Koda su Rumaisa suka shiga ɗaki, kuka ta kama yi dan bata so Mama tayi mata haka ba, taso ta barta ta koya ma Halimai hankali, dan ta lura Halimai itace babbar yar'iskar sannan Hindatu, sai Lami yar'autarsu, amman wallahi a sannu zata koya masu tarbiya tinda taga basu da ita, ji tayi Mama na cewa."Kuka na mai kuma Rumaisa."?kallon Mama tayi tana kuka mai cin rai tace."Haba Mama kinajin abunda suka ce man fa, amman kin hanani magana, zina fa Mama, yau har abunsu ya wuce tunani na suna ceman mazinaciya, amman kin hanani anso haƙina." murmushi mai ciwo Mama tayi sannan tace."au ai maganar bata da anfani, domin ko mai zaki ce ba yarda zasu yi ba, tunda ba Allah a cikin zuciyarsu, amman Rumaisa motar wa kika hau."?shiru tayi tana goge hawayenta sannan tace. "Mama ba wani bane ba fa, Fadil ne dan gidan Aunty ya gamu da ni a hanya shine ya rage man hanya, amman kinji abunda suke ceman."abinci Mama ta tura mata a gabanta sannnan tace."Bakomai, barsu ga Allah, Rumaisa ko kin biye masu kunyi fadi ba wani riba kika ci ba, dan haka Rumaisa ki daina biye masu, su dai ba hankali ne dasu ba, babu ilimi shiyasa kika ga abun yayi yawa kinji?maza kice abincinki ma."cewa Rumaisa tayi."Eh Mama naji Mama, kuma na barsu ga Allah."kallonta Mama tayi, tana jin son yarta na shigarta cewa tayi."yauwa yi dariya mana, ko ke fa, inkika yi fushi baki yin kyau kinji, dan haka ki daina yin fushi."cewa Rumaisa tayi yana dariya."To Mama, daman dai raina ne ya baci sosai, yauwa Mama yunwa nike ji sosai bari na ci abinci ni, ko muyi abincin dare."mama cewa tayi."aci lafiya, amman yau ba muyi wani girki,wanan abinci ya ishemu har dare."cewa Rumaisa tayi."to shikenan."nan Rumaisa ta gama cin abinci ta wuce dakin Maman A'I ta yi ma Karin karatu, bayan sun gama Maman A'i ta fara yi mata magana."Rumaisa."cewa tayi. "Naam Maman A'I."kallon Rumaisa tayi sannan tace. "Dan Allah daga yau karki sake biye masu Halimai, su kawai bakin ciki suke yi maku, ba kamar ke da kike aiki gidan Hajiya maryam, don su duka Ukkun sun taba yin Aiki gidan amman suna farawa take korarsu, kuma sata suke yi mata, shiyasa suke bakin ciki ke har yanzun ba'a koreki ba, dan haka karki sake biye masu kinji."? Shiru tayi tana mamakin, ashe suma sunyi aiki gidan su Fadila shiyasa suke mata haka kenan? Numfasawa tayi sannna tace."To Insha Allah, ba zan sake biye masu ba, nagode sosai, ni zan wuce bacci zanyi dan inasan na tashi gobe da wuri Insha Allah." "to shikenan Allah yasa." tashi tayi ta wuce daki, kwaciya kawai tayi.


*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_17&18

Washe gari, bayan Rumaisa ta gama yi ma Mama gyaran daki da dan wanke-wanken su, sannan  tayi breakfast, ta shirya tace ma Mama ita ta wuce wurin Aiki, "Mama sai nadawo."cewa Mama tayi."a dawo lafiya." "Allah yasa."Rumaisa tace tana mai shirin fita, koda  tazo taho mu haɗa sukayi da Halimai, wani malalacin kallo Rumaisa take ma Halimai sai da hantar cikin Halimai ta kaɗa, dan har yanzun kumatunta zafi suke mata marin da tasha jiya a wajen Rumaisa, amman da yake Halimai ƙarfin hali ne da ita, sai da tayi ma Rumaisa kallon banza da tsaki sannan tace."antafi yawon ta zubar kenan?Allah dai ya tsare cutar ƙwanjamou."
Ita dai Rumaisa batace ma Halimai komai ba tabi ta gefenta tayi ta tafiyarta, amman maganar da Halimai tayi mata tayi mata zafi sosai, sai dai ba yanda zatayi ne, dole tayi hakuri ko dan farincikin Mama, koda ta shiga gidan su Fadila ta fara gaida Hajiya maryam.
"Aunty ina kwana."?kallonta Hajiya maryam tayi tana murmushi tace."Lafiya lau Rumaisa, ya Mamanki."?cewa tayi. "tana nan lafiya lau, Alhmdulh."nan ta tashi ta fara yin abun da ya kawo ta tana gama yin aikin gida, suka wuce kitchen ita da Fadila...
Fadila tace."Rumaisa, yau saboda muyi fira shiyasa na tashi da wuri."cikin jindadi Rumaisa tace. "dan Allah kawata? naga ai Kamar da magana a bakikin ki." Dariya Fadila tayi sosai sanann tace."au haka ma zaki ce kenan."? Itama Rumaisa dariya take sannan tace."Ehmna ai haka abun yake don tun jiya naga da magana a bikin ki."
Fadila tace tana murmushi."Aiko kin gano gaskiya, aiko maganganu a baki na, amman sai kin gyaro wajen Yaya Fadil sannan mu zauna muyi maganar, lokacin ba wani aiki da ke gabanki."murmushi Rumaisa tayi sannan tace."To shikenan Fadila, munyi saurin mu gama wannan girki tunda ba mai wuya bane zamuyi ba."kallonta Fadila tayi tana mamaki wai ba mai wuya bane zasuyi ce mata tayi."Aiko dai ba mai wuya bane, amman a wajenki yake ba ya da wuya amman niko tsakani da Allah *DAMBUN MASARA* da *ZOGALE* yana bani wuya,  ko dan daman ke na fara ganin kinyi shi, shiyasa har yanzun na kasa na koya."kallon mamaki Rumaisa tayi mata sannan tace."Haba Fadila, in banda abunki maiye abun wuya ga *DAMBU* ? Ai Kamar yanda kika iya yin *DAMBUN SHINKAFA* watarana hadda *GWAƊA* kuke sa mashi, to shima haka ake yin dambun masara shima."girgiza kai Fadila tayi tace."Niko Rumaisa, wallahi sai naga Kamar na masara yafi na shinkafa wahala, Rumaisa."Rumaisa cigaba da yanka albarsarta tayi sai da ta gama sannan tace."Ai haka zaki gani, tunda kinfi iya na shinkafar, amman nidai naga Kamar duk wahalar su daya, nima kafin na iya na shinkafa sai nace na masara yafi na shinkafa saukin yi, amman daga baya sai naga duk wahalarsu daya, ke ni baki daya ban daukesu wani aiki ba, tunda gashi har mungama yanzun, cikin dan lokaci kadan, albasa kawai zan kara sawa."cewa Rumaisa tayi."Eh gaskiya, haka ne nima yanzun na kara fahimta, kuma Kinsan Rumaisa sai kasa abu rai kake koyanshi, sannan kuma in ka sama ranka baka iya abu kaza to baka iya yinshi tunda kasashi a ranka,  shiyasa ni komai nike sama raina zani iya shi."dariya Rumaisa tayi."Eh hakane, amman kisan wasu matan basu dauki abun a haka ba, Allah yasa mudace, yanzun ni zan wuce na gyara ma Yaya Fadil part din shi sai ki juye dambun cikin cooler tunda mun gama."Murmushi Fadila tayi, dan ita har yanzun ta kasa yarda wai Yaya Fadil shi Rumaisa ke gyara ma apartment mutumin da ba kirki ya ishe shi ba ai tana kokari ma cewa Rumaisa tayi."To shikenan, sai kin dawo dan Allah kiyi sauri ki dawo ina son yin magana dake mai mahinmanci Rumaisa."cewa Rumaisa tayi."To shikenan, na wuce." nan fa Rumaisa ta wuce part din Fadil ta fara aiki da ya ke ta tadda baya nan.
Nan fa Rumaisa ta fara dafa ma Fadil tea, bayan ta gama hada tea sannan ta wuce ta fara gyaran dakin, ta na niyar fita dan ta gama suka ci karo da Fadil, wani irin yanayi ya tsinci kanshi dan ko sai da yace."wash."dabarbarcewa Rumaisa tayi nan ta fara matsa kwalla, dan gani take yau mai rabata da Fadil sai Allah, balle yanda taga yayi tsaye ya kasa ko motsi a tare suka fara magana, sai Rumaisa tayi shiru, shiko cewa yayi."sorry, bansan kina ciki  ba."cikin Mamaki ta ɗago ido tana kallonshi, aiko crab suka haɗa ido cikin ido, da sauri Rumaisa ta ɗukar da kanta kansa, dan bata iya jure kallonshi, shi ko kallonta kawai yake, dan natsuwarta tana kara mashi sonta a zuciya, cewa Rumaisa tayi."Aa ba komai yaya Fadil nice ya dace na baka hakuri, dan Allah kayi Hakuri."kallonta yake yana mamakin hali irin na Rumaisa shi yayi mata laifi amman ita ke bata hakuri ce mata yayi."naji nayi hakurin, yanzun ina zaki."? Cewa tayi."Da man yanzun na gama yin gyaran, ban zo da wuri ba, da yake yau mu muka yi sauwa nida Fadila, shiyasa, kuma tafiya zanyi."murmushi yayi sannan yayi mata alamun da ta koma ciki, koma tayi ta zauna shiga bedroom yayi ya ajiya suit dinshi sannan ya fito kallonta yayi sannan yace."Mai kuka dafa mana? Dan tunda na shigo da motana nike jin gidan baki daya sai kamshi yake buga wa."murmushi tayi tana wasa da yatsan hannunta tace."Ba wani abu mai dadi bane yaya Fadil, dambun masara ne da *ZOGALE* ."kallonta yayi sannan yace." *DAMBUN MASARA* kuma? Daman ana yin dambun masara, bayan dambun shinkafa da kus-kus."? Murmushi ne kwance a fuskar ta sannan tace."Eh mana, ai da dambun masara kawai aka sani, sai daga baya dambun shinkafa ya shigo, yanzun kuma naga harda dambun *KUS-KUS* duk ana yi."mamaki yake sosai, dan tunda yake bai taɓa ganin dambu masara ba, bai ma san anayi ba, ce mata yayi."Ikon Allah, amman nayi mamakin sosai fa."murmushi tayi tace."Ai ba abun mamaki bane, wannan zamanin ana yin kala kala, wani abincin ma yaya Fadil baka iya cin shi, amman mutanan da daga tuwo sai fura suka sani da dashishi, shiyasa suka fimu lafiya, domin yanzun ba kowa ke cin abincin gargajiya ba."kallonta yayi yanajin wani irin sonta na fisgar shi cewa yayi."Hakane, fatan kin da faman tea din ko."?cewa tayi." Eh na dafa, komai ma duk nayi, yanzun zan wuce gun Fadila muyi fira sannan na wuce gida."tashi yayi yana cewa."Ok shikenan kin gaida man da Mama inkin koma gida, nima yanzun wani file na manta ban fita da shi office ba kuma yau za muyi cases din shiyasa na dawo."itama tashi tayi tana cewa."Allah ya taimaka, Allah baku sa'a"cewa yayi. "Amin ya Allah."
Bayan Rumaisa ta gama gaisawa da Fadil ta wuce wajen Fadila domin sunyi magana da itace zasuyi.

*BUƊEƊIYAR WASIƘA*

*Buɗeɗiyar wasika zuwa ga masoyana masoyan litafin *A GIDAN HAYA* fatan kuna cikin koshin lafiya? Ya gida da kowa da kowa, Allah ya sa mu cika da imani Amin kuma muyi kyaukyawan karshe Amin ya Allah 🙏🏻*

*Dalilin  da yasa na rubuto maku wannan wasika shine, kuna ra tambayar  11&12,wasu na kirana

Please Login or Register in order to submit comment