Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan ta samu dama, itama Mijinta Allah ya hore mashi yayi gidan kanshi.

_________

Ita ko Hindatu, mijinta ya kamata da karto har cikin daki suna lalata, yayi masu mugun bugu sannan ya saketa saki uku, yanzun haka Hindatu bara take a kan titi ga tana fama da cutarb HIV.
Watarana Rumaisa tana cikin driver taga Hindatu tana bara, parking din motar tayi., aiko da gudu masu bara suka doso wajen Hindatu ce ja gaba, zuge glass din Rumaisa tayi, sannan tace."Hindatu kece nike gani ko kuma mai kama dake ne."!?
Sai da Rumaisa tayi magana sannan ta gane Hindatu ta ganeta, kuka Hindatu ta fashe dashi tana cewa."Rumaisa yanzun kice kika zama Hajiya? Kaicona ni Hindatu kaico mai hali irin nawa, tabbs na biyema shirin zuciya da kuma zaga ta Halimai mukai ta wulakantaku muna binki da shirin zina, sai ga shi sheri ya fada mana, kinga yanda Allah yayi dani Rumaisa, na tabbata alhakinki ne ke binmu, dan Allah Rumaisa karki duba abunda mukayi maki, dan ko munsan mun cutar dake, ki yafemana saboda da Allah."
Kallonta Rumaisa tayi, sannan ta bude mata mota ta shigo suka tafi gida tare, ruwan wanka  ta hada ma Hindatu bayan Hindatu ta fito wanka kaya ta bata tasa Sannan Suka ci abinci tare, kuma tace ta yafe mata, gidan Halimai ta Kaita tace su su zauna tare, sannan tace ma Hindatu ta ringa zuwa tana ansar magani kuma duk wata tana aiko masu da abinci da kuma kudi.

______


Rumaisa ce kwance bisa cinyar Fadil, kallonshi tayi sannan tace."Prince." cewa yayi. " Naam princess." cigaba da cewa tayi "ya shara'ar Allah yasa ku kayi winner."? Murmushi yayi sannan yace."Eh Alhmdulh princess, mun gama cases  munyi winner, da man muke da gaskiya, ake ta bata lokaci ga gaskiya suna gani, amman su kulle ido su tsaya suna kare marar gaskiya a kan karya." cikin jindadi tace."hakane gaskiya, Allah ya kara taimakawa.".."Amin, gobe ne fa ake yinkarin girman nan." cewa tayi."eh duk mun shirya, Allah ya kaimu goben Allah."

Washe gari duka ahalin Mai *DAKO* suka hallara gun da ake ma *BARISSTER FADIL KHAMIS MUHAMMAD* *DAKO* Ƙarin girma,  taro ya ansa taro manya barissters na Nigeria sun zo inda aka nada barisster Fadil *CHIEF OF JUSTICE*  na *KANO STATE*,  baki daya...

Nan fa Fadil ya tashi yayi speak inda yake godiya da matarshi Hajiya *RUMAISA FADIL MUHAMMAD DAKO* , sanann ya maika godiyarshi ga iyayenshi da yan'uwa da abokan arziki..

Anyi walima, anci ansha, anyi hanikan,Fadil ne ya shigo cikin room din da Rumaisa suke ita da Fadila, Cewa yayi."princess zo kiga wani abu, kema Maman Deejat taso mu tafi." wani dakine ya kaisu nan suka tadda *SADIQ* yazo shida *NANA* *JAWAHEER* , sai *KHALID* da *ZAINAB* , sai *LUKMAN* shida *SALMA,na* *NANA* *JAWAHEER* 🧕 suna cikin murnar ganisu tana waigawa ta hango *GIMBIYA HAKIMA DA SARKI HAKIMA NA CIKIN GIMBIYA HAKIMA* suna cikin murna sukaji anyi gyran murya waigawar da zasuji sukaga  *SOFY* itada *ALIYU* Na *SANADIN LINK* 🙆‍♀️, abun dai ba'a magana dan harda *SADAUKIN BURHAAN* yazo shida *HUSNARSHI* DA *ZUBAINA* suma sunzo taya Fadil murna Karin girma da ya samu, nan su matan suka tafi bedroom din Rumaisa suka zauna suna labari da ba juna shawarwari, suma haka su Fadil suna labari da yanda zasu kugadanar da wani kasuwanci baki dayan su Anan kano, nan suka fito cin abincin rana, sun ci abinci cikin farin ciki da annashuwa...


*ALHMDULILLAH RABBIL* *ALAMIN*

Anan na kawo karshen wannan littafi mai suna *A GIDAN HAYA* ,kuskuren dake ciki Allah ka yafemin,abinda na rubuta daidai kuma Allah kabani ladan,nagode nice taku har kullum  Jameey yar'mutan kankia

semun hadu cikin sabon book dina me suna  *ƁARAWO NE* 


'''Ai da kunji ance ƁARAWO NE kun san akwai cakwakiya da sirkarkiya a cikin book din kudai ku biyo ni, 🤫karki sake a baki labari😍'''

*~KADAN DAGA CIKIN ƁARAWO NE~*

Karfe Uku na dare, gari yayi shiru bakajin motsin komai, sai kukan karnuka da mujijo, wani mutun ne na ga ya haura wani gida ya shiga, shigar shi keda wuya naji ana."Ihu barawo! Ihu barawo!! Ihu barawo."abunda ake cewa kenan, sai zunduma abun wannan ihun ake, suna neman taimakon mutanan unguwa Amman shiru kake ji ba wani motsi, jin shiru yasa nayi saurin shiga dan na kwaso maku rohoton abunda ke faruwa, ina shiga naji ana cewa."Kai Alhaji zaka yi man shiru ko sai na fasa maka kai da wanann bundugar? Na tarwatsa maka gwakwalwa." cikin karma da tsoro gami da firgici wanda aka kira da Alhaji yace." Nayi shiru, Amman Dan Allah mai nayi maka bawan Allah? Mai kake nema wajena." murmushin gefen baki wannan ɓarawo yayi sanann yace."Kudi! Kudi nazo ansa a wajenka, idan ka bani kudi shikenan zan tafi ba ruwana da kai." kallon bindigar da ɓarawo yasamashi bisa kai kawai yake, cikin tsoro yace."To! To!! To!!! Naji Dan Allah karda ka harbai ni da wanann bungugar, indai kudine ga su'nan." Allah Sarki, nan Alhaji Nura ya kwaso kudi masu yawa ya ba wannnan ɓarawo, Wanda ya boye fuskarshi da facemask shiyasa baiga kwayar idonshi ba.
Yana amsar kudin ya Kama gabanshi da sauri ya fita gidan Alhaji Nura, yana fita ya cire mask din fuskarshi.
Sannan ya shiga gidansu, wani gidane yanda kukasan kango dan baida banbanci da akirashi da suna kango.
Yana shiga, yaga mahaifiyarshi a tsakar gida, nan ya fara tambayarta cikin tashin hankali, dan baiyi tunanin zai taddata ido biyu ba, kuma yasan mudun ta ganshi waje zata tuhumaishi abunda ya fiddashi waje, cewa yayi."UmmiYa akayi naga kintada hankalinki? Ai nasa tuni bacci kike." cikin tsoro da firgici tace ma mashi."Mustapha Ina'ni ina bacci, ko bakaji anyi ihu ɓarawo ba a gidan Alhaji Nura."!?  Tayi mashi tambayar cikin tsoro dan tunda taji anyi ihun farko a cikin kunnanta akayi shi, shiyasa ta tada hankalinta, kallon Ummin tashi yayi, sannan ya kamo hannunta ya zaunar da ita cikin dakinta sannan yace."naji wallahi Ummi, ai shiyasa na fita Amman banga ɓarawon ba, dan da alamu ya Samu ya gudu." numfasawa Ummi tayi sannan tace."Kash!! Allah dai ya shiga tsakanin na gari da mugu, suma wannan ɓarayin Allah ya shiryasu, su gane hanyar gaskiya." kallonta Mustapha yayi sannan yace."Amin ya Allah Ummi, yanzun dai Ummi ki  kwanciyarki kinga dare yayi sosai." cewa tayi."To shikenan, kaima kaje ka kwanta, kafin Allah ya kaimu gobe musan yanda zamuyi akan wannan kudin na registration dinka Mustapha, abun yana damuna amman insha Allah zan fita na samo koda bashi ne." tashi yayi yana cewa."To ummi sai da safe." kwantawa tayi tana cewa. "Allah ya kaimu."
Bayan Mustapha ya shiga dakinshi da bakomai a cikinshi sai wata tsohuwar tabarma wanda da ita gwanma babu, ya zauna ya fara aikin kuka yana fadin..
"Na shiga ukuna ni Mustapha wanna wata kallar rayuwace na daukarma kaina? Wai ni Mustapha yanzun ni akeyi ma ihu barawo kaicona da wannan bakar rayuwa."
Yana cikin wannnan hali wata zuciya tace mashi inbaiyi sata ba ai da yanzun bai kai 600level ba, tunda baida kudin da zaiyi registration.
Haka Mustapha yai ta tunani yana tur'da hali irin nashi, domin shi ya san halinshi ba hali bane mai kyau..
Nan ya dauko kudin da ya sato wajen Alhaji Nura ya lissafasu yaga dubu dari da hamsin ne, nan yaji wani kallar dadi ya mamaye mai zuciya, dan sunkai yanda yake bukata harma sun wuce.
Dan haka shima gobe zaije yayi registration,  dan yaji ance sun kusa closing din portal dinsu.
Bayan Mustapha ya gama lissafa kudin registration ya tashi yayo alwallah ya fara sallah, yana kuka ya neman gafara wajen Allah, ya roki Allah ya kawo mashi karshen wanann wahalar da yake ciki.
Sanann ya kawo mashi mafita a cikin rayuwarshi, shine bai kwanta bacci ba sai da ya dawo daga sallahr asuba, sannan ya kwanta bacci bayan ya gama azkar din safe.
Shine bai tashi ba sai karfe goma na safe sanann ya tashi yayi wanka ya wuce wajen Ummi, zaunawa yayi sannan yace."Ummi ina kwana."? Kallonshi Ummi tayi tana murmushi sannan tace."lafiya lau Mustapha ga tuwanka can na ajiye maka tashi ka dauko ka ci." girgiza kai yayi sannan yace."Ayyya Ummi na koshi kedai ki dauka kici, dan nasan baki ciba kika ajiyeman." kallon ɗa'n nata tayi tana jin sonshi yana kara shigarta, domin yanason farincikinta cewa tayi."Kai dai kaci Mustapha waya gaya maka ban ci ba? Dan haka kayi maza kaci ni yanzun gidan Alhaji Nura zani nayi masu jajen wannan abun da ya samaisu jiya." murmushi yayi mata, sannan yace."Dan Allah Ummi ki tsaya kici , ni yanzun zan tafi wajen Kamal nasan zansamu abunda naci, sanann kuma daga nan zan wuce makaranta nayi registration na samu kudin." kallon mamaki tayi mashi, tana mamakin ina ya samu kudin registration, cewa tayi fuskarta babu wasa."Kudi Mustapha ina kasamu kudin registration."?  Shiru yayi ya fara inda inda, dan yasan sun saba wanann case din da Umminshi, mudun ya samu kudin registration tom ta dinga yi mashi tambaya kenan, dan tana tsoran kar yan iska suyi amfani da dama dan sunga baida kudi su bashi kudi suyi iskanci dashi, abunda take tsoro kenan, cewa yayi."Na manta jiya ban gaya maki ba, da man inasan na gaya maki wallahi jiya mantawa nayi sai da akayi Ihu gidan Alhaji Nura na tuna kuma dare yayi lokacin ga hankalinki duk a tashe yake shiyasa nace yau da safe na gaya maki."  cewa tayi."Mustapha ba wannan na tambayeka ba,  ina kasamu kudi har Naira dubu Tamanin."?


*nan fa akeyinta🤣, ƁARAWO NE kenan, wanda zaizo maku  13 ga wannan watan insha Allah, nan ne zakuji ansar da yake ba Ummi idan ya samu kudin, amman fa naga ruwan comment sannan zan fara posting 🥺*

*Sai kuma kadan daga cikin* *~BAYI MA YA'YANE~*
Shi  kuma ba yanzun zai zo maku ba🥴

Masarautar Daborah masarauta ce dake can cikin kasar Gambia,  yankin Afrika ta gabas masarautar ta shahara a fagen Sarauta wadda ta share sama da shekara Dubu Ukku da kafuwa a cikin duniya ba inda ba'asan labarin Masarautar ba, a cikin kasar Gambia harma da kewayenta.
Masarautar kwata kwata basu san kima ko darajar bayin su ba sun maidasu kamar wasu dabbobi wani bima har kwara dabbobi sun fisu ƙima a cikin masarautar Daborah, kuma sunyi suna wajen tarar abokan gaba daga ko ina a cikin sassan duniya, wanda suke da tarin makayaka masu karfin gaske, labarin su ya karade kaf nahiyar wannan dalilin yasa ake shayin haye masu, wannan kenan. 

Duke take tanata famar nakuda kamar zata mutu duk tagama fita hayyacin ta duk yan uwanta sun zagaye kofar saboda gudun kar labarin nakudar Binta tafita a cikin masarautar, kowa ajinin shi akan hakaifa sai uban zufa suke ketawa karma ace mijin Abdulmajid hakan bakaramin tada mashi hankali yakeba, itako Binta baiwar Allah sai addu'a su Jummai ke mata ciki ikon Allah ta surbudo kyakkyawar yarta santaleliya jajir da ita gwanin ban shi'awa, godiya taima Allah duk da tasha wahala hakan baisa hankalin ta ya gushe yabar jikin taba, kukan da jaririyar keya hakan yasa ya fita har waje da sauri Abdulmajid ta shigo ya dauke diyar ya boyeta, sannan yasa su Jummai suka shirya su, duk baki daya hankalin su yaki kwanciya.

Ladidi ce ta shigo sai haki take a cikin Turakar bayi ta shigo dakin su Binta duk sun raina gaskiar su, kowa yabita da kallan tuhuma ko lfy? Bude baki tayi tafara magana cike da tsoro duk ya mamaye ta."kin bani Binta wayace ki haihu a cikin wannan Masarautar? Ko kinsan kalar hadarin da kika jefa kanki?Kin manta da matsayinki a cikin wannan masarautar?Amman kikayi wannan gangancin."?  Maida kallonta tayi ga mijin ta fara cewa."yanzun kai Abdulmajid a matsayinka na uban bayi yaza kayi da wannan matsalar."?  Kowa ya kasa magana danko su jummai kuka kawai sukeyi sunajin tausayin Binta, karma ace yar jinjirar da batasan komai ba,  zuwan ta kenan a cikin duniyar ga baki dayanta ma, kukan da yar tasu takeyi shi yakara jefasu cikin tashin hankali hakan yasa Binta daukar diyarta tafara feeding dinta kila tasamu kodan jinkai ne a wajen yarta bayan rasa su, magana Abdulmajid yafara yace."Ladidi ko kinsan me kike fada, taya zamu kawar da abinda Allah ya kaddara mana, karfa kimanta munkai sama da shekaru Arba'in da aure muna neman haihuwar nan amman bamu samuba sai yanzun Allah yajikan mu yabamu sai mu yarda muce bamu so mukasan ko wacece wannan yarinyar nan gaba, kisani ni Abdulmajid koda za'a sare kaina bazan taba wofintar da kyautar da ubangijina yaimani ba,  bayan na bata sama da shekaru masu yawa ina nema kawai dan ina bawa sai in wulakanta wannan ni'imar mai girman gaske, amm...."Aa uban bayi ba nufina kenan ba nidai fatana Allah ya tsaremu daga sharrin makiya kuma yakare mana yar'mu." Ladidi ta katse Abdulmajid tana cewa haka, cewa sukayi."Ameen."itadai Binta ita kadai tasan halin da take ciki sai kuka takeyi tana addu'a Allah ya tsaremata yar'ta koda ace ba tare zasu rayuwa ba.

FA'DA, zaune take a saman karagar mulkin ta alfarma wadda tasha ado da ruwan gwal da arzurfa ta hakince sai takama takeyi da gadara sai fiffita ake mata cikeda izzah take kada yan yatsunta wa'anda suka sha gwala gwala saman kyakkyawn wuyanta shima yasha ado mai ban mamaki ta gyara gashin kanta da aka daura mashi crown sai shaining takeyi taji gwal baki daya farfajiyar fadar fadawa ne zaune a saman kujeran su a suka kewaye fa'dar sai tsakiyar fa'dar katon kafat ne wanda ya gaji da tsaruwa kujerar Sarauniyar ce a tsakiya sai sauran yan fa'da suka kewayeta inda akabari in anzo kowa zai duka saman kafat dinnan yakai gaisuwa wajen Sarauniya inta zauna sannan kowa zai zauna.

Ba abinda yaimata zafi ko magana ba tayi sai kaɗa kafar ta takeyi a hankali cikeda kasaita, jin Sarkin kofar shiga cikin fa'da yana dakatar da wata baiwa a cikin amintattun bayin ta, hakan yasa ta kalli wani dogari dake gefenta kallan sa kawai da tayi yasa shi tafiya da sauri yacema Sarkin kofa da ya budema wannan baiwar gate din shigowa cikin fa'da jikin shi na rawa ya bude mata ta shigo faduwa tayi saman tsakiyar kafat din fa'da takai gaisuwa wajen Sarauniya takai wajen minti biyar sannan Sarkin Zagi yace mata." Sarauniya ta amsa." kanta a kasa a jin maganar Sarkin Zagi yabata ikon dagowa ta kalli Sarauniya tace."Allah yataimaki inaneman izinin zanyi wata muhimmiyar magana mai mahimmanci aimin a fuwa tuba nike Allah yakara girma." a dakile ta daga mata hannu." Sarkin Zagi yace."angai sheki Mero Sarauniya tabaki damar magana." Cewa Mero tayi."Godiya nike Allah yataimaki Sarauniyar Daborah ina tafe da wani labari mai girman gaske lallai yau antashi da alhini a  cikin wannan Masarautar mai tarin albarka, yau a cikin Turakar bayi antashi da firgicin gaske yau dinnan Uwar bayi Binta ta haifi kyakkyawar yar'ta mace hakan yasa nace bari in hanzarta fada maki,  Allah ya huci zuciyar ki yakara daukaka."

Mikewa tayi cikeda gadara tana kaɗa kai cikin izzah da isa sannan ta bude baki tafara magana."Sarkin fa'da kaida Sarkin horo ku hanzarta zuwa ku kamomin dasu baki dayan su harda yar da iyayen baki daya kuma nabaku nan da minti ukku." tashi sukayi suna cewa."Allah yakara nisan kwana angama yanzun nan kuwa." fita sukayi da sauri duk cikin su ya duri ruwa, itako sai kai lawo takeyi cikeda da kasaita.

Dauke suke dashi a saman wani gado daya gaji da kayatuwa bayine guda hudu suke dauke da wannan gadon mai dauke da kayan ado na jauhar da lu'u lu'u, sai daukar ido yakeyi ga dogarawa sai dukan wadannan bayin sukeyi hakan yasa wani matashin Saurayi yayi magana  a hankali yana saman gadon duk da bazai wuce shekara goma sha biyar ba a duniya ba karamin bacin rai bane ya kama shi ba, suko wadannan dogarawan sai ahi sukeyi suna neman tuba cewa yayi."daga yau karku sake ku kara dukan su me sukai maku?  da zaku dinga zalintar su, ga aiki sunayi ga duka dame kuke son suji."!?  cewa sukayi."Allah yahuci magajin gobe tuba mukeyi Allah yakara maka lfy." haka sukaci gaba da tafiya dashi sai a lokacin bayin nan suka samu sukuni ba inda suka isa sai bakin kofar shiga fa'da, da sauri Sarkin kofa yafara koda wannan kyakkyawan Saurayin mai farin jini ga alumma Masarautar, a hankali yake tafiya har ya isa wajen zaman shi, nan ya gaishe da Sarauniya sannan ya zauna a gefen ta saman tashi kujerar duk danya fahimci ran ta a bace yake sai dai baiyi magana ba, ba dan yana san zuwa fa'da ba yasan ba yanda zaiyi dole yazo, gani yayi dogarawa nata dukan wasu bayi, kamar zasu kashe su ga jinjira a hannun su bakaramin taba ransa hakan yai ba, ba inda suka gurfana sai gaban Sarauniya  kowa yakawo gaisuwa jikin su sai uban ɓari yakeyi duk sungama tsorata,cewa Abdulmalik yayi. "Allah yataimakeki kiranki ya samemu kimana aikin rai."  tahowa tayi kusa dashi ta wasga mashi wani kalar masifaffan mari mai rudarwa, cewa yayi."tuba mukeyi Allah ya kara girma." Cikin Izza ta fara cewa."Uban me yasa kuna bayina zaku sake jiki har ku haihu a cikin masarauta ta?Har yaushe kukeda wannan yanci?Ku kuka kafara karyaman dokata kuma manyan bayi lallai kun raina dokar Sarauniya Zulaiƙha kenan."?  Cikin tsoro sukace."kiyi mana aikin rai haka Allah ya kaddara." wani kalar wawan kallo ta aika masu dashi, wanda yasa kowa yayi kasa da kanshi cikeda tsoro.
Sarauniya Zulaiƙha kenan wadda takasan ce ya'daya tilo a wajen Sarki Abduljabar wadda tagaji mulki mai girman gaske a cikin masarautar Daborah itace Sarauniya ta talatin dake gabatar da mulki a cikin masarautar Daborah, wannan shine kadan daga cikin nasabar Sarauniya Zulaiƙha.

kowa ya nutsu kamar ba dan adam a wajen danko Binta ko magana takasa jitake kamar tayi fitsari tsabar firgita ga tana fama da raunin haihuwa, jin maganar Sarauniya Zukaiƙha ya dawo da ita cikin hayyacin ta."Sarkin horo anshe waccen jinjirai kaje ka yanka ta sannan ka binne mani gawar ta, su kuma ka kaimin su gidan kaso aita dukan su sannan ajefe su har sai sun mutu." ba Abdulmajid ba duk wanda ke fa'dar nan saida gaban shi yai mummunar faduwa, haka Sarkin horo yazo ya kama jaririyar nan uwar ta rike daura mata mari yayi, hakan yasa ta saki sai kuka takeyi da sauri wannan dan Saurayin ya tashi yafara magana, jin maganar shi yasa Sarkin horo tsayawa."Allah yahuci zuciyar Sarauniyar Daborah, kiyimasu aikin gafara haka Allah yaso karki zartar da wannan hukuncin akan jinjirar da batasan me akeba na rokeki kiyimasu afuwa." ba karamin mamaki ya kama taba ace dan' data haifa shikejin tausayin bayi har haka kallonshi tayi sannan tace."lallai yau na yarda da kalar rashin sanin yakamatar ka kana jinina da'na ace kai zakaji tausayin wadannan kaskantattun mutanen wadan da basu da wani anfani ko daraja suna bayin wulakantattu abin yarwa, karka manta bayi fane."

Girgiza kai yayi sannan yace."Allah yabaki hakuri Umma, amman kiyi masu lamani ki yafe masu, kuma kuda suke bayi, *Ai BAYIMA YA'YANE* kiyafe masu, Yarima Abdulmalik kenan da'tilo ga Sarauniya Zulaiƙha ta dauki son duniya ta daura mashi, batasan abinda zai same shi ko kadan hakan yasa tasa ake koya mashi dabi'un Sarauta duk da bai anfani da kalar abinda takeso yafiye tausayi shiyasa take cewa ubansa ya gada, mahaifin sa Saifullahil islam Sulaiman, shi kuma babban dan kasuwa ne mai fa'da a ji cikin kasar Gambia harma da kewaye matarsa daya sai dan'sa Abdulmalik wanda suke kiran shi da MalikusSaifil islam ko suce mashi Malik wasu kuma sunai mashi inkiya da sunan mahaifin sa MalikusSaif, duk da ya tashi cikin gata hakan baisa ya dauki duniya da zafi ba, ga gaji da haduwa kyakkyawa ne ajin farko ya gaji da haduwa saidai farine kuma dogo ne jayant, duk da kyawunsa bai gama fita kasancewar yanzun yake girma bazai wuce shekara goma sha biyar ba a duniya.

Kallonshi tayi sannan tace."Malik Kasan me kake cewa kuwa? dan bayi na ya'ya bashi zai nuna suki bin dokata ba."Kallonta Malik yayi sannan yace."Umma karki manta bantaba neman alfarma ba bakimin ba, dan Allah kiyi hakuri kibar wannan yarinyar kinga daman banda kanwa kibari su kula da ita inta girma sai ta dinga yimin hidima ki taimaka man."

*Hmmmm shin Gimbiya Zulaiƙha zata amince da bukatar  Malik ko kuwa zata sa a kashe yarinyar da aka haifa a tsakar bayi? Sai dai kun biyoni a cikin shirin nan wato bayima ya'yane.*

laifin dadi karewa kadan daga cikin wannan kayataccen labarin na BAYIMA YA'YANE wanda ya kunshi zalinci da bakin mulki ku biyoni a sannu danjin yanda wannan labarin zai kaya duk da free book ne📚🖊️ ne, ina bukatar comment dinku na Yar'mutan kankia ne, sai najiku masoya💔🤝🏻


Karku manta shi ba yazn zai zo maku ba

*Yar'mutan kankia ce❣️*


Share
Comment
Vote
And
Like
Pls


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment