Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya taimaka ya kawo kasuwa." "Amin." Yace sannan ya fita, fitowa Mama tayi tsakar gida, taddasu Halimai tayi zaune sun hada kai waje daya sai magana suke a hankali ga dukan alamun gulma suke, kallon banza sukayi mata a tare sanann suka kauda kai, bata damu da kallon da sukayi mata ba murmushi tayi sanann tace." Sannunku da hutawa ina kwanan mu."!?  Tsaki Halimai tayi sannan tace." Ke hutu ya gani, kuma da bamu kwana ba da kin ganmu."? Dariya Mama tayi sannan tace." Hakane kuma Halimai, daman zuwa nayi muyi sallama yau zamu tashi daga gidan nan zamu koma gidan Hajiya Maryam da zama." Take fuskokinsu ta chanza, bakin cikine kwance kan fuskokinsu, tsaki Hindatu tayi sannan tace." Andai ji kunya wallahi, kinsan Allah Lami da nayi roko da bara kwara na mutun cikin gidan haya, amman da yake wasu ba su da zuciya anje anyi fadanci an samu anba miji aikin gadi,har ana shirin kome." itadai Lami cewa tayi." aiko dai Hindatu, ni banga amfanin zuwa wani yi mana sallama ba, mu daman anzo anyi mana bakebake cikin gida, ai mu dadi mukaji za'a tafi a barmana gida." itako Halimai bakin ciki yasa ta kasa magana, sai ma kallon Mama da tayi tace." munji dan Allah wuce ki bamu waje Allah ya raka taki gona." itadai Mama murmushi tayi sanann ta koma suka cigaba da hada kayansu, daman Rumaisa ta gaya ma Fadil dawowar tasu yau, aiko suma sukaje suka gyara masu part din da zasu zauna, Baba na dawowa suka kwanshe kayansu nasawa kawai kujerun dakin da gado harma wasu kayan sawar da kwanonin cin abinci, Mama su Halimai taba tace su raba,haka suka tafi suka barsu da kayan bakin ciki, kuma bayan tafiyarsu, harda fada akayi tsakanin Hindatu da Halimai akan kayan da Maman Rumaisa ta bar masu, dan ita Lami cewa tayi ta barmasu su raba, dan taga sun fita bukata tunda ita mijinta ba abunda baya sayar mata.

Su Mama sun dawo gidan su Fadil, da zama suna zaman su hankili kwance, amman duk da haka Baban Rumaisa ya na zuwa neman kudin shi, dan yace shi dai a barshi ya nema na kanshi, ba dan Hajiya Maryam taso ba ta barshi. 
Yau ta kama ranar da Alhaji Khamis zai dawo cikin iyalenshi, dan haka kowa ya tashi da shirin tarbarshi....

__________________________________

     *WUDIL-KANO*

"Malama." Wanda aka kira da Malama naga ta dago tsuhuwar fuskarta, dan da alamu ta tsufa sosai, dan dai bafulatace kuma tana da jiki mai kyau shys ba'a cika gane tsohanta ba sosai, cewa tayi."Naam Malan, ya na ganka haka? Kamar wani marar lafiya."! ? Numfasawa tsohon yayi, dan da alama da kaganshi kasan mijinta ne, cewa yayi."Lafiya lau, sai dai kwana biyu hankalina ya tafi wajen Fadil, ban san yanzun ko yana wani hali ba." Shiru Malama Fadila tayi, dan mijin nata ya soso mata inda yake mata kaikayi, amman bata zabi daurewa tayi sannan tace."Hakane Malan, shiyasa nike nuna maka, rashin dacewar hukuncin da ka dauka, ai in Khamis ya gudu ya barmu, bai ka mata ace muma mun tafi  mun bar dan karamin yaro, saboda san zuciya Irin tamu, mun tafi mubar yaro wanda bai wuce shekara goma ba a duniya, yanzun ko Yana wani hali? Allah kadai ya sani." Cewa Muhammad yayi."Tabbas Malama, mun tabka baban kuskure, wanda in bamu gyara shi ba, mu ka bar duniya, gaskiya sai mun hadu da hushi ubangiji,  ya bamu amana mun watsar mun tafi mun barta." Girgiza kai tayi sannan  tace."Yanzun mai abun yi Malan."!? Tashi yayi yana cewa."Abun yi shine yanzun ki tashi, ki hada kayan ki, dan yau insha Allah a Kano zamu kwana." Itama tashi tayi tana cewa."to shikenan Malan."

_____________________________

     *KANO*

Alhaji Khamis ne ya shigo compound din gidan shi, parking yayi yana murmushi yanajin farin cikin dawowarshi cikin iyalanshi, duk da  abunda yaje nema bai samu, hawaye ne suka fara zubo mashi, dan da ya tuna tarin dukiyar da yake da ita, kuma ya tuna daginshi basu tare dashi, baisan a wani hali suke ba, baisan suna da rai a halin yanzun ba ko kuma basu da shi, yana cikin wanann hali , yaji an rungume shi ana cewa."Oyoyo, Abba sannu da zuwa." saurin goge hawayenshi yayi sannan ya jiyo yana murmushi, yace."Yauwa Fadila, ya na samai ku Auta."? Cikin Murna tace."Lafiya lau Abba, sai dai munyi missing dinka sosai." lakutar hancinta yayi sannan yace."Nima nayi missing dinku." Fadil ne ya taho yana cewa."Abba sannu da zuwa ya hanya."!? Rungumo Fadil Alhaji Khamis yayi, sannnan yace."Lafiya lau, Son, fatan kana cikin koshin lafiya."? Shima kara rungumar Abbanshin yayi yaga cewa. "Lafiya lau Alhmdulh, sai dai missing dinka da nayi sosai."shafa kanshi yayi sannan yace."Allah sarki barisster, Nima nayi missing dinka sosai." Hajiya Maryam ce tsaye tana kallonsu cikin farin ciki, cewa tayi."To masu uba, ai kun kyale man miji haka ko? Ku barshi ya huta, kun hana  ko gani na yayi." Sakin yaran nashi yayi yana dariya sannan yace."oyoyo da girman kujeranki, uwargida ga Khamis Muhammad Dako." Murguda baki tayi sannan tace."uwargida kawai."!? Dariya sukayi tare sannan yace. "Aah Amarya ga Khamis Muhammad Dako."  nan Umma ta shige jikin mijin nata tana yi mai sannu da zuwa, tana sheda mai yanda tayi missing din shi, nan suka kwasa suka shiga ciki, sai da Alhaji Khamis, ya gama cin abinci yayi wanka ya huta, sannan Haji ya Maryam ta fara magana...
"Abban Fadil." Kallonta yayi sannan yace."Naam Umman Fadila, lafiya na ga tun dazun, kamar da akwai magana a wannan bakin naki." Kamo hannunshi tayi tana murzawa sannan tace."eh ina san na gaya maka da man, na taimaka wasu suna zauna cikin gidan nan, basu da gidan zama shine nace su dawo nan ita da mijinta." Kallonta yayi, yana mamaki sannan yace." Kina gani ba matsala Hajiya."!? Kwantowa tayi jikinsa sannan tace."Eh ba matsala, ai yarinyarsu ma Fadil zai aura, da man jira nike ka dawo, sai a sa bikin nasu baki daya harda Fadila." Dariya yayi yana shafa jikinta yace."To To, masha Allah gaskiya naji dadin wannan labarin, insha Allah gobe zan gaisa da shi mahaifin yarinyar, sai musan yanda za'ayi komai, daman inasan naga Fadil yayi aure." Cewa tayi."To Allah ya kaimu goben Amin ya Allah."


_____________________________

    *WUDIL KANO*

Malan Muhammad ne tsaye yana jiran Malama Fadila yana cewa."Shin Malama fito mu wuce ko."fitowa tayi tana cewa."to gani nan fito Malan, wai na tsaya yin sallama da Mutane ko."? Cewa yayi. "To kinyi kokari mu tafi, kin san garin mu da dan-nisa kadan." nan suka  je tasha suka hau motar Kano..

________________________________

    

*KANO*

Bayan mota ta sauke  su, suka tafi bakin titi domin tsada nape, suna tsaye Baban Rumaisa yaga iyayen nashi,  nan ya tsada napen , ya fito ya rungume Malan Muhammad yana kuka yana cewa...
"Maiyasa! Maiyasa!! Maiyasa? Mai nayi maku har haka? Kuka yanke man wanann hukuncin, kuka tafi kuka barni ni daya."!? Kallon Baban Rumaisa, Malama Fadila tayi sannan tace."FadiiiiL, kaine dana."!? Cewa yayi. "Eh nine Inna." Sake cewa Baban Rumaisa yayi."maiyasa kuka tafi kuka barni."!?  Dafashi Malan Muhammad yayi sannan yace."yanzun fadil, labarin nan ka bari sai mun zauna, zamu gaya maka dalilin tafiyarmu muka barka.
Nan fa Baban Rumaisa, yasa ma iyayen nashi kaya cikin napen, sannan suka shiga suka kama hanyar gida.


Alhaji Khamis ne yace ma Hajiya Maryam."Hajiya, je kiyi man magana da Baban yarinyarnan Rumaisa." Cewa Umma tayi."Haba Alhaji, ai ka matayayi ka tashi mu tafi tare ka gaisa da shi." Cewa yayi."To shikenan,tashi mu tafi." Fadila tace."Abba nima zani." Kamo hannunta yayi yana cewa. "to Auta, taso mu tafi, iya karmu dai cikin gidan nan ba wani guri ba." suna fitowa napen na shigowa cikin gida, Alhaji Khamis tsayawa yayi yaga waye ya shigomai da napen a cikin gida, kuma napen din baiga ansa KHAMIS DAKO ba a jiki, ai Fadil yana fitowa suka fara kallon-kallon shida Alhaji Khamis, suna cikin haka suka ji Malama Fadila suna ta salati ita da Malan Muhammad...
Da sauri Alhaji Khamis ya ida isowa wajen su Baban Rumaisa yana cewa."Fadil, kune idona ke nuna man."? Shima Baban Rumaisa rungume Yayan nashi yayi yana cewa. "Yaya Khamis, Ashe da man nan ne gidanka? A gidan nike zaune ban sani ba." Shima kara rumgume kanin nashi yayi yana cewa."Eh nan ne gidana dan-uwana, Inna dan Allah ku ya fe man." Kallonshi Malama Fadila tayi sannan tace. "da kata Khamis, kai Fadil da man gidan Khamis zaka kawo mu shiyasa ka shigo da mu motarka."!? Rike Mamar tasu Baban Rumaisa yayi sannan yace. "Aa Inna ban san shine mai gidan ba, ni dai nasan ance man mai gidan yayi tafiya, amman dan Allah kuyi hakuri, ku shigo, kunga inba nan ba, bansan ina zan kaimu ba." Wani Kallon banza Malama Fadila tayi ma Khamis sannan tace."ka ci darajar Fadil, ba dan Fadil ba, ba abunda zai shigo dani a gidan ka."
Nan su Malan Muhammad suka shiga cikin part din Umma, baki daya family din, da man shi  Fadil bai yi mamaki ba shida Rumaisa, dan sun dade suna tunanin Babanta shine wanda Baban Fadil yake nema shekara da shekaru...
Bayan kowa ya zauna, Khamis ya tashi ya bude taro da addu'a, sanann ya fara magana kamar haka...
"Ina neman afuwarku ya ku iyayena, hakika na san ni mai laifine babba a wajen ku, da na iya hada kaya na tsarlakeku na tafi na barku, nayi hakan ne dan naje na nemu kudi, na sani,indan nace maku ku barni na nemi kudi, cewa zaku yi Aa shiyasa na tafiya ta, da niyar indan na samu kudin zan dawo gare ku, bayan na samu kudin ba inda ban je neman ku ba, amman ban sa mai ku, yanzun haka kwana na daya da dawo wa daga WUDIL ne man ku, ance man anga Baba a kasuwar Wudil." kallonshi Malan Muhammad yayi sannan yace."Tabbas, kai mai laifine Khamis, dan kaine sillar faruwar komai, muma masu laifin ne, saboda dalilin tafiyarka,  a ranar dana wayi gari baka gida, ba inda banje neman ka ba, nine ban dawo gida ba sai bayan isha'i, nayi kuka da bakin cikin talauci, na san cewa da ina da kudi ba inda zaka tafi ka barmu, balle kai kake ciyar mu, ni na sama kai na mutuwar zuciya, domin babu maraya sai raugo, wanna bakin cikin yasa muma muka bi dare ni da Innarku, baka bar Fadil yana bacci, bai san abunda ake ba, haka muka tsarlake shi muka barshi, lokacin dan shekara 10,amman bamu  tausayinshi ko kadan ba muka tafiyarmu, muka je wudil, a wudil na samu aikin gadi,  a cikin gidan gadin muke kwana nida mahaifiyarku, munyi zaman lafiya da amana, sai yanzun da muka shigo Kano dan mu nemi Fadil, na sha ganinka a wudil kuma na san mu kake nema, saboda bamu da kowa a garin wudil balle kace gunsu kazo, ni ban san ka dawo ba ma, kuma ban gaya ma Innarku ba na ganka, dan karta tada hankalinta tace sai na kaita ta ganka." 
Kallansu Baban Rumaisa yayi sannan shima ya basu labarin wahalar da ya she a rayuwa, bakin daya falon ba wanda bai yi kuka ba, ba kamar Khamis da yake ganin shine sila, bayan sun gama suka tambayi yanzun ina Ba'ba Rumaisa take, nan yake gaya masu ta rasu, bayan rasuwar Khamis, sun masu fatan rahama...


*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share


🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
       

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page_55&56

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, suna rayuwa cikin mutunta juna, dan yanzun a part din Inna ake cin abincin, sai bayan sun gama cin abincin, Rumaisa da Fadila suke gyara ko ina a gida, dan Inna tace abarsu suyi aiki sosai tunda aure za'ayi masu, ba kamar Fadila da bata da jurumin aiki sosai, amman yanzun ta Saba.
Yau Abdullah zai zo zance, dan haka yau tun safe su Rumaisa basu zauna ba, dan yau harda kunshi da salon suka je, kallon Rumaisa Fadila  tayi sannan tace."Kawata dan ki fiddo man da kayan sawa kafin Dear ya ce na fito, kinga yana wajen Yaya Fadil tuni." tashi Rumaisa tayi tana cewa "to shikenan,, kema ki shiga wanka mana, matsala da ke wallahi saurin rudewa, yanzun da yace ki fito zaki rudeman ke baki shirya ba, bayan kinsan tun dazun yana cikin gidan nan." tashi tayi tana cewa."Yauwa Kawata, bari na shiga." kayan sawa Rumaisa ta fiddo mata, tana gama Fadila na fitowa cewa tayi. Yauwa kawata bari na shirya kuma." tashi Rumaisa tayi tana cewa."ok nima bari na shiga wankan kafin ki gama shiryawa, kin san yau zamu fita da prince." "ok." Fadila tace ta cigaba da shiryawarta, fito daga wanka Rumaisa tayi, kallon Fadila tayi sanann tace."Wow Kawata, sai kace yau ne bikin? Ina da ranar bikin sai kinsa Abdullah ya rude baki daya kenan." kallonta tayi ta mirror sanan tace. "Uhmm ke dai ake ji Kawata, amman ai kin san duk kyau na ban kai ki ba, ni na wuce yana part din Inna, yana can yana jirana." dariya Rumaisa tayi sanann tace."ok ki gaida shi, sai na shigo."


Nan fa Rumaisa ta zauna ta fara tsara kwaliya taji da gani, dan harda jan baki ta sama dan karamin pink lips dinta, bayan ta gama wata arniyar atamfa ce ciganbi ta dauko tasa, dankin riga da sicket simple style ne, sai dai an fiddo shape a dikin sosai, dan breast dinta sun zauna sosai a cikin breastcup din rigar, sannan ga sicket din yayi mata dai-dai hips din su zauna sunyi das dasu, bayan ta gama sa kayan ta murza daurin dankalinta irin wanda ake yayi, ta dauko agogonta rolel ta daura ma hannuta, sannan ta dauko gyalenta ta yafa, ta dauko turarenta ta fashe jikinta da shi, sannan ta dauko glass dinta Gucci ta manna ma fuskar ta, masha Allah ba karamin kyau Rumaisa tayi ba, sai ta biya tayi ma su Umma sallama zasu fita ita da yaya Fadil, sanann ta fara biya wa part din Inna ta gaisa da Abdullah sannan ta wuce part din Fadil, tunda ta shigo Fadil yake kallon, cewa yayi."Princess, Woow masha Allah, gaskiya princess kinyi kyau ji nike kamar na maido bikin mu gobe,dan wallahi bakiji yanda nike ji ba."murmushi Rumaisa tayi, sannan tasa yatsan hannu a bakinta tace."shssss Prince mai kake ci na baka na zuba."!? Matsowa yayi kusa da ita suna kallon juna, dafe sitin zuciyarshi yayi sanann yace."Son ki nike ci princess kaunarki ke zuba." kiss ta hura mashi tana dariya, ka she mashi ido daya tayi sannan tace."I love you prince, ina kaunarka ina kishinka, akan sonka ba abunda ba zani ba masoyina." wani irin dadi ya kama Fadil sannan yace." Ilov uh too Princess, insha Allah ba ba abunda zai rabu dake inba mutuwa ba, masoyiyata karki manta dani ko babu raina ina fatan ki ringa yawan tunawa dani kina yi man addu'a." murmushi kawai take sanann tace." tabbs Princess komai lokacine, muma namu ya kusa mu zama miji da mata, kamar yanda kace kar na manta dakai, nima ina fatan haka, masoyina dan Allah karka manta dani ko babu raina ka dunga yawan tunawa dani." lumshe idanu yayi yaa budesu a kanta, hula yaje dauka ta riga shi dauka, matsowa yayi kusa da ita sannan ya dan duƙa dan yafi tsawo ba laifi, sa mashi hular tayi sannan ta dauko turare ta fesa mashi, Murmushi suka sakarma juna a tare sannan yace." Princess ki sani sonki a jinin jikina yake yawo, ina kaunarki sosai Matata,  yanzun mu tafi sun wa'ance sun iske mu in sun gama soyayyar." murmushi tayi sanann tace."ina zamu wai princes nidai kawai kace na shirya."? Lakutar hancinta yayi yana Murmushi, dan tayi mashi kyau sosai shigar da tayi maganar, cewa yayi."Crossing din Major Aliyu mana, wani friends din mu ne." langabar da kai tayi sanann tace."ok mu wuce, dan Allah prince ka bani nayi dreving naga zai yi man kyau." murmushi yayi yana kama hannunta suka fito, sannna yace."ai princess ba driving kadai ba, ke komai kika yi kyau yake maki, gaki chocolate colour."murmushi kawai tayi, bude mata mota yayi ta shiga sannan shima ya shiga, mika mata key yayi nan Rumaisa ta ja motar har inda za'ayi crosing,
Sunje crossing anyi crossing lafiya, anci ansha, sune basu dawo gida ba sai karfe 10pm, suna dawo wanka Rumaisa ta fara shiga, bayan ta fito taje garden inda suke haduwa da Fadil basu rabuwa sai 12am sannan suke sallama kowa ke wuce wa makwancinshi.


Washe gari, bayan sun tashi, sun gama aikin komai, Umma ke gaya masu za su tafi England su hado kayan furnitures, ita Rumaisa harda lefenta, tunda bikinsu yanzun saura sati biyu, dan gobe za'a kawo lefen  Fadila.

Washe gari, kowa ya tashi da aiki dan yau za'a kawo lefen Fadila, sun shirya komai yanda ya dace, dan part din Inna za'a anshi lefen, ita kuma Fadila ita dasu Rumaisa sun fita, sunje diner din Major Aliyu.

Woow, wasu yan-mata biyu na hango a hall din dinner, ko wace tana tare da saurayin ta suna ta zuba soyayya, yan matan nan anko din wani materials suka yi, Army green, su duka material din nan yayi masu kyau duk da ba hasken su daya ba, dan Fadila fara ce sosai, ita kuma Rumaisa ruwan tarwadace, Amman colour din tayi bala'in yi masu kyau, su Fadil ne suka tashi suka barsu, ai suna tashi wani handsome guy ya taso yazo wajen ssu Rumaisa ya zauna, kallon su Rumaisa yayi sannan yace."Yan mata sannu fa, Am Nasir Abu-turab, dan Allah ki bini lokaci na gaya maki abunda nazo dashi izuwa gareki." ita dai Rumaisa bata ce mai komai ba, yayin da Fadil ji yake kamar ya shake wuyan Nasir da man tunda suka zo wajen nan yaji guy din bai yi mashi ba, dan da man ya lura yanda ya nuna maitarshi a fili a kan princess din shi...
Nan take Fadil ya isge hannun Rumaisa yana janta, tana cewa."princes ka matse man  hannu fa, da zafi sosai fa." yana jinta amman yayi banza ya kyale ta, sai kara ma matsa hannun da yayi sosai, ba ajeta ko ina sai cikin mota, ya shiga ya ma motar da gudun bala'i nan take Rumaisa ta fara kuka, ba tayi tunanin zasu iso gida lafiya ba, koda su iso gida, bude motar yayi ya wucewarshi cikin part din shi, dan haushin Rumaisa yake ji sosai, biyo shi tayi tana kuka, tana shigowa ta kara rushewa da kuka tana cewa."Prince dan Allah kayi hakuri, wallahi ban san shi ba, hushinka zai iya haifaman da matsala babba, kayi man ko wani hukunci amman banda kalar wanann, amman kasani ni ban sanshi ba, ban ma taba ganinshi ba." kallonta yayi yana cewa."eh na san baki san shi ba, amman mai yasa kika sakar mashi fuskar har yazo wajenki, da kinji yanda naji da ko kallon fuskar shi baki balle har yazo wajenki."
Kuka take sanann tace."bai dace kayi man haka ba, amman kayi hakuri bazan sake ba." matsowa yayi kusa da ita yana share mata hawaye sannan yace." komai ya wuce princess, amman ki sani komai kika nayi duk sonki ne sila." dariya tayi mai hada da kuka sannan tace." nagode da kayafeman, nima sonki ba zai bar ni na kula wani ba inba kai ba."


An kawo lefen Fadila akwati  18 da gana biyu, an ma dangin Abdullah tarba ta mutuncin, sun koma gida suna yabon tarbiyar gidan su Fadila, dan gaskiya Abdullah yayi dacen mata.


Washe gari jirgin su Rumaisa ya tashi zuwa England, sun yi abunda ya akaisu, dan itama Rumaisa akwati 18 aka yi mata da gana biyu, sannan furnitures da komai iri daya aka yi masu set daya duka white in colour, sai set daya kuma brown and milk, ko wane set biyu aka yi mashi, sun dawo gida Nigeria lafiya, sunyi fresh sun kara kyau sosai da ka gansu ka ga amare,  bayan sun dawo su duka suka koma part din Inna da zama nan ake yi masu gyaran jikin,  dan har wani glowing suke dan tsananin gilka da halawa da suke sha.

Yau biki saura kwana uku, kuma yau, za'ayi diner, sun dauko makeover zata yi masu kwaliya da gyaran gashi, masha Allah, gaskiya duka  Amayarnan biyu ba karamin kyau suka yi ba, sunsa gown brown and white, an daura masu head sunyi bala'in kyau, nan aka saka kowa motar da angonta ke ciki yana jiran ta, domin suje meenet event.

"Princess, kinyi kyau sosai." waigowa tayi yana murmushi sannan tace. "kayi kyau sosai prince." kamo hannunta yayi yana cewa." flower din nan tayi man kyau gaskiya princess, princess wannan wani turarene kika shafa."!? nan ya janyo ta jikanshi yana sunsunan kamshin jikinta, itako sai tureshi take, da taga abun ya fi karfin ta ta sa mashi ido😁, tana cikin tureshi taji ya hada bakinsu waje daya yana kissing dinta, shiru tayi ta kwantar da kanta a kafadunshi, dan ta da yanda zatayi dashi lumshe idanu kawai tayi yana jin yanda Fadil yake tsotsar mata harshe kamar ya samu sweet, ba su san an iso meenet event ba, sai  dai Mubarak yace suyi hakuri, hakanan mai suke ci na baka na zuba🙈.


Itama Fadila, tunda ta shiga mota, Abdullah ya matsa mata da ya mitsa, shine ya taba can ya lasa can sai da yaga zata yi mai kuka sannan ya daga mata, suna iso suka jera bakin dayansu suka shiga, anyi diner yanda ya dace amare sun yanka cake, an tashe kowa ya koma gida...
Washe gari, aka yi bridel shower, tsaya wa gaya maku kyau da Amare suka yi bata lokacine, amma kyau ko anyi masha Allah...
Sai Washe gari a kayi wa'azi, Malama juwairiya tazo tayi wa'azi a kan yin biyeyya ga miji da kuma shi auren mai ye shi, tayi wa'azi mai shiga jiki, dan su Rumaisa sun sha kuka...


Yau ta kama daurin aure....

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls


🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia  ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar  da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page_57&58


Yau da misalin karfe 2pm aka daura auren FADIL KHAMIS  MUHAMMAD da Amaryarsa RUMAISA FADIL MUHAMMAD a kan sadaki naira dubu Dari, sannan aka daura auren ADBULLAHI ABUBAKAR SULE da Amaryarsa FADILA KHAMIS MUHAMMAD akan sadaki naira dubu Dari, bayan an gama daura auren aka wuce reception aka ci aka sha..
Bayan nan sun Fadil suka yi pictures da abokanansu, sanann ya samu ya turama Rumaisa message..
Gidan cike yake da yan'uwa da abokan arziki, su Rumaisa suna part din Inna ta shirya su, dan har anzo daukar Fadila, tana basu wani jiko da ta anso masu,kallon Rumaisa Inna tayi sannan tace."wai Rumaisa zaki ansa ki sha ko sai muyi ta dake cikin gidan nan."turo baki tayi tana cewa. "Inna wallahi na gaji da shan wannan abubuwan naki, su ba wani dadin kirkiba." Cikin fada Inna tace."ai da yake bani zan ji dadin abun ba keda mijinki zaku ji dadin abun ku, lokacin ni banma san inda kaina yake ba,ku kuwa kina can kuna murzar juna, dan dagake har shi Fadil din ba hak'uri gareku, yanda kuke rawar kan nan ai dole sai da gyara." Rufe fuska Rumaisa tayi, tana cewa."ni dai Inna bani na sha yanzun zaki fara kallar wanann maganar taki ba dadin ji,ki tasa mutun yana jin kunya." ai Rumaisa tana cikin sha taji message ya shigo wayar ta nan ta fara karantawa..

_Yau din na kin zama tawa halak malak, inyi yanda nike so da yarinya ba mai ce man dan mi, congrats Rumaisa Fadil, yau kin zama matar Aure.._

Nan take Rumaisa ta fasa ihu, da man mai neman kuka, an gaya mashi mutuwa☺️,kallonta Inna tayi sannan tace. "ooo ni Fadila yau ina ganin zamani, shine kika kama kuka, daga anshi kisha? To ajiye ki tashi mujo gun iyayenku su yi maku fada, tunda ba ku za'a tsaya jira ba."

Please Login or Register in order to submit comment