Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa karya ya tafi ya barmu,
kinga da bai tafi ba da sai ya nuna muna hanyar fita wannan daji, anan meenat tayi
murmushi tana mai cewa, ai tafiyarsa nada amfani garemu, kaga yanzu sai mu cigaba da
binciken wannan littafin har sai mun ganshi, anan bafferh ya harareta, ya za ayi muga
wannan littafi, bayan mun barosho cikin kogo, kuma hanyar da zata kaimu wurin ta lalace
balantana mu bita. inji bafferh.
To naji, yanzu sai kazo muje wancan gidan da muka hango, domin shine naga fotonsa a
cikin wannan littafin, daga nan suka fara tafiya xuwa wannan gida, suka manta da gargadin
mafarauci.
To bayan sun kawo gidan, sai sukaga an ajiye motoci kala kala, bayan sun zo gaf da
motocin, sai sukaga mutane na fitowa cikin motocin, daga ciki harda aunty balkisu da
daddy, anan mamaki ya kamasu meenat, koya akayi sukazo wannan daji?to me ya kawosu?
Aunty balkisu ce ke tafiya cikin rangwada har ta kawo wurinsu, marin meenat tayi har sau
biyu, sannan ta jawo kanta ta buga ga glass din mota, har sai da glass din ya fashe.
KU DAURE MIN SU!!!
Taba wasu samudawa umarni, anan aka daure meenat da bafferh, wata kaca ce aka dauresu
da ita yadda ko motsi basa iya yi, daga nan sai ta fara tambayarsu, ina littafin da kuka
sace?
Anan meenat ta kalli bafferh, daga nan suka done kai kasa ba tare da cewa uffan ba, cikin
fushi aunty balkisu ta amso wata karamar bindiga daga hannun masu tsaronta, "pistol"
halbawa tayi sau uku domin ta nuna musu cewa akwai harsashi ciki "bullets" daga nan sai
ta aza bindigar saman kan bafferh, zakiyi magana ko sai na fasa kan saurayin naki!!! inji
aunty balkisu, shi kuma daddy kallonsu yake ba tare daya ce kome ba, daga nan sai
meenat ta fara magana, haba daddy ka taimake mana, kana ganin abunda aunty ke shirin
yi? daga nan sai daddy ya fara magana, bazan iya taimakwanki ba meenat, face idan zaki
fada muna inda kuka aje wannan littafin, domin nima ina bayan auntin ki.
Wani kallo aunty balkisu tama meenat, ke, ki sani ni ba mahaifiyar ki bace, kije can ki bidi
mahaifiyarki ta gaskiya, wannan magana tasa hawaye sun zubo a idanun meenat, haka
shima bafferh tausayinta ya kamashi, to wacece mahaifiyata ta gaskiya? meenat tambaya,
yauwa, kinga sai ki fadamin inda kuka ajiye littafin kafin na baki wannan amsar, inji aunty
balkisu.
Kusan minti sha biyar meenat batayi magana ba, daga nan sai daddy ya bada umarni a
kaisu cikin wannan gidan a kulle, hako ko akayi, ita kuma UMMI sai kallonsu take, wani
matsiyacin duhu ne a cikin gidan, daddy da aunty balkisu na a cikin daki daya, haka suma
mutanen da akazo dasu duk an basu masauki.
To bayan kowa yayi bacci a cikin gidan, meenat ita kadai ce cikin wani wuri mai mugun
duhu, gashi ba wuri guda ne aka ajesu tare da bafferh ba, saman kujera take daure da
kaca, kawai sai taga an bude kofar dakin, ashe ummi ce rike da yuka, anan ta bada yukar
tana mata umarni data yanke kacar ta gudu, anan meenat ta shiga yanke kacar, ita kuma
ummi sai ta fita a guje domin kada a ganta, to bayan meenat ta yanke kacocin, sai taga
duhu yayi yawa, saboda haka sai ta fara kiran ummi domin ta kawo mata mata fitila.
UMMI,UMMI, UMMI, wai ko batanan, anan taji shiru, cikin sauri meenat ta mike,a hankali ta
fara takowa kasan benen domin ganin ko meke faruwa, tsoro ya dabaibaye zuciyarta, kuma
matsanancin duhu daya mamaye wurin gaba daya, takawa takeyi guda guda cikin tsoro,
tana cikin wannan tafiya sai ta hango wani abu kamar mutum, a lullube cikin bakaken
kaya, anan jikin meenat ya dau rawa, ta rasa abunyi, juyawa tayi da nufin komawa, cikin
mamaki sai ta kara ganin irin wannan halittar a bayanta, to a wannan lokaci tsoron dake
jikinta ya ya harzuka mutuka,batasan lokacin data fadi ba, a haka ta cigaba da mirginowa
kasan benen har ta kawo kasa, a wannan lokaci dakyar take nishi, to bayan ta tashi,
abunda ya daure mata kai shine bataga wadannan halittun bakake ba.
Anan ta cigaba da tafiya a hankali tana kiran ummi, tana waige waige saboda tsoro,bata
ganin ko tafin hannunta, sannan abunda ke ke damunta shine me yasa duk fitillun gidan
sun mutu? kuma ita ummi inata shiga ne? a haka ta cigaba da tafiya har ta shigo wani
daki, shogowarta keda wuya sai taga fitila, anan ta kunna, jin dadi tayi saboda ganin wani
fanfo,cikin sauri takunna fanfon domin shan ruwa, ihu tayi domin jini ne ke fitowa maimako
ruwa, juyawa tayi da nufin fita, kawai sai taci karo da karamar yarinya, laa ummi, ina kikaje
ina neman ki, anan taji shiru, kuma gata rike da wani gatari, kuma idanunta duk sun juye
zuwa ja, da karfi meenat ta kaucema saran data kawo mata, anan ta fitabdakin a guje, cikin
wannan gudune sai taci karo da wani abu, anan ta fadi, ahankali ta dago kanta domin
ganin ko meye, anan ta gane cewa wadannan halittun ne bakake data gani dazu, ihu tayi
sannan ta nufi wani daki a guje, kullewa tayi tana nishi, shigarta keda wuya sai ta kara
ganin wannan halittar baka kirin, a guje ta nufo kofa da nufin guduwa, to kafin ta kawo ga
kofar, sai taji anan bugunta da gatari, wato anaso a ballata da karfin tsiya a shigo ciki,
taga ta leka da nufin guduwa, sai taga duk itatuwan dake dajin sun zagaye gidan yadda ba
wurin gudu, a wannan lokaci wannan halittar ta kusa cimmata, haka kuma kofar dakin ta
kusa karyewa saboda bugun da tasha da gatari, anan ta hango watarijiya a cikin dakin rufe
da marfi, kawai sai taga an budeta, ashe bafferh ne, to anan ya mata umarni da ta shigo
ciki, rijiyar kamar hanya take, wai ya akayi ka kubuta bayan da suka daureka anan, inji
meenat, anan ya bata amsa da cewa ai ummi ce ta kawomin yuka domin in taimaki kaina,
anan taji mamki to meyasa ummi keson kasheta? suna cikin gudu sai suka hadu da aunty
balkisu tare da jama arta, wato kunaso ku gudu ko, to ku sani bazaku tona sirrin da muka
binne shekaru da dama ba, anan ta bada umarni da aka masu, to kafin a aiwatar, kawai sai
kasa ta fara girgiza, tana tsagewa, anan wadannan mutanen suka fara fadawa ciki, sai
kuma wasu kibiyoyi da ba asan inda suke fitowa ba suka fara kashe jama.a, idan kibiyar ta
shiga jikin mutum, sai dai aga yayi kunburi ya fashe.
MEYE KARSHEN WANNAN LABARI?
ZAMU CIGABA....

GIDAN FATALWA 3
kashi na uku
Written by
abdul king article
TUNATARWA DAGA NA BIYU:
A cikin littafi na biyu, mun tsaya inda bafferh da meenat suka hadu da aunty balkisu tare
da jama arta wato matsu tsaronta a cikin wannan rijiyar mai kamar hanya, a inda ta bada
umarni a kamasu, to kafin a aiwatar sai kasa ta fara girgiza, haka kuma wasu kibiyoyi da ba
asan ta inda suke fitowa ba suka shiga kashe jama a, wanda idan kibiyar ta shiga jikin
mutum, sai dai aga yayi kunburi ya fashe.
CIGABAN LABARIN:
Bala i yayi bala i, domin ta koina kibiya fitowa take, saboda haka hanjin mutane sun
yawaita a kasa, jini sai malala yake tamkar ruwa, to a wannan lokaci aunty balkisu ta rude,
domin mafi yawan masu tsaronta sun mutu "security agents" to ana cikin haka sai wasu
daga cikin mutanenta suka zo da wata shawara, cikin sauri suka fito da garkuwa domin
kare wadannan kibau, "protector" cikin dubara suka hada wani sahu, daga nan sai su
aunty balkisu suka koma bayansu, meenat ko magana bata iya yi saboda tsoro, haka suka
cigaba da tafiya cikin wannan sahu, duk kibiyar da tazo sai dai ta tsaya ga garkuwar, an
dauki lokaci wadannan kibiyoyin na fitowa kafin daga bisani su dauke gaba daya, to bayan
kibiyoyin sun dauke, sai dakarun suka aje garkuwowin, suna duban inda kibiyoyin ke
fitowa, basa ganin kome face tsananin duhun daya karwade wurin gaba daya, anan wasu
daga cikinsu suka fara yadiya da fitila " torchlight" sai dai fitilar batada haske sosai,
saboda haka duhun ya rinjayi fitillun, daga nan sai suka fara jin wani ruri marar dadi,
wanda hakan yasa kowa ya like kunnuwansa, kuma abun mamaki basa ganin mai yin rurin,
da sun haska wurin sai dai suka ga duhu, gaskiya ni bazan iya zama a wannan gida ba,
tsoro nakeji!!! inji meenat.
Yi shiru, banza, ai duk kece kikaja, yanzu zamu cigaba da tafiya domin mu samu hanyar
fita, aunty balkisu ta fadi cikin fushi, to daga nan sai suka cigaba da tafiya cikin wannan
rijiyar "underground" suna waiwaye waiwaye, kowanensu idanunsa sun fito saboda tsoro,
domin ji suke a kowane lokaci za a iya kawo musu hari, to suna cikin tafiyar sai suka kawo
wani wuri da anyi zane zane a bangon wurin, anan suka fara kallon zane zanen domin da
fenti ja aka yishi, wasu kwarangwal din mutane ne aka zana, sai kuma wata mata mai siffar
dodanni tana kalaci da naman mutum, anan suka cigaba da kallon wadannan zane naban
mamaki, shi kuma bafferh kome ya kaishi, hannunsa yasa ya shafi wani zane, yin haka
keda wuya, sai suka fara jin wani rugugi, kamar ana magana amma basajin abunda ake
cewa, cikin rashin tsammani sai sukaga wani abu mai kamada maciji, sai dai jikinsa dauri
gareshi, kuma bayada kafafu balantana idanu, cikin sauri wannan abu ya laulaye daya daga
cikin dakarun aunty balkisu, haka wannan mutumi ya fara ihu yana neman taimako, amma
ba mai iya zuwa wurinsa, kafin kaceme wannan abu ya wuce da wannan mutumi, cikin
minti biyu sai aka jefo musu gangar jikin wannan mutum, kai daban, hannaye daban, kuma
kafafuwa daban, duk an masa guntu guntu ba kyan gani, wannan abu ya mutukar tayar
musu da hankali, anan suka fara gudu, kowa na ta kansa, aunty balkisu ce ke basu umarni
inda zasu shiga sai kace tasan gidan, wannan abu yaba meenat da bafferh mamaki, anan
suka fara tunani wai ko batada nasaba da wannan gida?
To suna cikin wannan gudu ne sai wannan abun ya dawo, cikin sauri ya kara laulaye wani
daga cikinsu ya wuce dashi, abokin wanda aka laulaye ya kasa hakuri, saboda haka ya bi
shi domin cetoshi, anan su aunty balkisu suka rikeshi suna bashi hakuri, amma ina ya
kasa jurewa, sai kuka yakeyi yana kiran sunansa, AL AMEEN, ihun al ameen din sukaji tare
da ganin guntattakin jikinsa, anan suka tashi kowanensu yacigaba da gudu, suna cikin
gudu sai suka kawo ga wani wuri mai matattakala, a can saman wurin akwai wata kofa
wadda zata fiddasu daga cikin rijiyar, cikin sauri kowanensu ya fara tattakawa yana kokarin
fita, turanni in tureka suke, suna cikin wannan hali sai wannan abun ya kara dawowa, wani
ya laulaye sannan ya wuce dashi, ganin haka yasa kowanensu ya kara himma ganin cewa
ya fita daga wurin, cikin kuzari meenat ke kutsa kai ganin cewa ta fita, amma a duk lokacin
data tunkaro wurin sai wani yasha gabanta ya wuce, haka meenat ta cigaba da kokari
amma duk a banza, kafin kaceme kowa ya haye ya barta, anan ta fara kokarin hawa cikin
tsoro tana waige waige, fara takawarta keda wuya sai sukayi ido biyu da wannan halittar
mai kashe mutane, anan jikin meenat ya dau rawa, sukuma wadanda suka samu damar
hawayewa sai suka fara yi mata magana, suna bata umarni da tayi sauri, haka meenat ta
cigaba da takawa jikinta na rawa, shi kuma wannan halittar kokarin cimmata yake, anan
yayi wani tsalle ya riko rigar meenat, to a wannan lokaci tana gab da fita, shi kuma bafferh
yana ganin abunda ke faruwa sai ya zaro wata karamar yuka, rigar meenat ya fara yankewa
har sai da katse wurin da wannan halittar ya rike rigar, daga nan sai ya jawota da karfi,
tana fitowa suna kulle kofar, ji kake baaaam.
Anan sukayi tsaye suna nishi, kai da gani kasan sun gaji, daga nan sai suka cigaba da
tafiya har suka shigo wani daki, inda sukaga daddy da ummi na bacci, wannan abu yaba
meenat mamaki, anan ta tuno lokacin da ummi ke binta tana kokarin kasheta, kuma gashi
yanzu ta sameta tana bacci, to ya haka?
Aunty balkisu ce ta matsa da bugunsu har sai da suka tashi, ku bakuji abunda ke faruwa
damu neba? anan suka amsa da basuji komeba, anan meenat taja ummi gefe tana
tambayarta, ke da kika bani yuka nida bafferh ina kikaje? meenat ta tambayeta, anan ummi
ta amsa da cewa, bayan na baku yuka domin ku kwance kanku keda bafferh, anan dakin na
shigo na tarar da daddy na bacci, daga nan sai na kwanta nima na fara bacci, daga nan
ban dan abunda ke faruwa ba sai yanzu da kuka tasheni, inji ummi, anan meenat ta shiga
mamaki, kenan waccan ummi data gani tanason kasheta bata gaskiya bace, wannan itace
ta gaskiyar.
Bayan kamar minti goma, sai aunty balkisu ta dauki fitila da niyyar zuwa ban daki, anan ta
fita, cikin tsoro take tafiya tana waige waige, kamar ana tafiya bayanta takeji, anan tayi
tsaye cif ta kasa motsi, rike take da fitila jikinta na makarkata, kuma ta kasa juyawa baya
balantana taga ko meye, ana cikin haka sai taga jini na zuba ga kafafunta, anan ta juyo a
hankali, ihu ta buga, wani hannu ta gani duk kassa, ba tsoka a ciki, a guje tayar da fitilar
ta nufi dakin data baro, anan ta fara kwankwasar kofar domin a bude mata, amma ina
basaji, can kuma sai ta hango wani haske, wata mata ce a cikin hasken sai dai bata ganin
matar da kyau, domin dushi dushi take gani, anan ta cigaba da kwankwasar kofar domin a
bude mata, shi kuma wannan hasken mai dauke da matar ya cigaba da nufota, wata juwa ta
fara gani, kafin kaceme ta fadi, batasan inda take ba.
Mutane ne kewaye da wani gado, a saman wannan gado aunty balkisu ce, fita ake mata
domin ta farfado, daganan sai ta fara bude idanu a hankali, can sai ta budesu gaba daya,
da karfi ta tashi.
INA TAKE? abunda ta tambaya kenan.
HALA WACECE? daddy ya tambayeta, anan aunty balkisu ta kankane jikinsa tana kuka, ashe
bata mutu ba, dama tana raye, ta fadi cikin kuka, ki gayamin wacece mana?
MUHIBBAT!!! inji aunty balkisu.
Ina bazai yiwu ba, inji daddy, domin ni na turbudeta da kaina, kuma yanzu an fi shekara
goma da mutuwarta, anan dai aunty balkisu ta kara kankane jikinsa tana kuka, nidai na
tuba, kuma yanzu inaso ka nemo muna hanyar fita cikin wannan gida.
Wannan magana taba meenat mamaki, domin kaka zuwaira ta taba yin magana akan
muhibbat, a lokacin da daddy yazo mata da labarin cewa guguwa ta kashe mutum dari
biyar, kuma ta taba ganin an rubuta sunan MUHIBBAT a wannan littafin data tsinta cikin
akwati, to tambaya anan shine wacece muhibbat? haka wannan tambaya ta cigaba da
damun meenat, anan ta kasa samun sukuni sai da ta gabatar da ita gaban daddy.
Wato ki sani meenat bazan iya amsa miki wannan tambaya ba, sai yanzu zan kira kaka
zuwaira domin ta bayyanar dake abunda ke damunki na daga wannan tambayar, anan
daddy ya dauko laptop dinsa, kunnawa yayi, daga nan sai ya kira aunty zuwaira, fuskarta
ce ta bayyana ga screen din laptop din, daga nan sai daddy ya fada mata abunda meenat
ke son sani, murmushi kaka zuwaira tayi, su kuma sai kallon fuskarta suke, daga nan sai ta
fara labari kamar haka:
Tun kafin a haifeki meenat, babanki wato daddy ya sayi wannan gida da kuke ciki a yanzu,
domin yasa amaryarsa a ciki, wannan amarya tasa itace mamarki, kuma itace ake kira
MUHIBBAT, na masa fada a lokacin da ya sayi wannan gida, domin gidan ya kasance tilo a
tsakiyar daji, amma haka babanki ya kanne akan yanason gidan, to bayan an daura aurensa
da muhibbat, bayan wani lokaci, sai ya hadu da aunty balkisu, wadda suka far soyayyar
boye da ita, ita kuma balkisu batasan yanada mata ba, wata rana sai ta kawo masa ziyara,
a wannan lokaci kuma bayanan, to anan taci karo da muhibbat, daga nan ta gane cewa
yanada mata, rikici ne ya kullu tsakaninsu harda buge buge, to a cikin wannan fada ne
balkisu ta samu nasarar buga ma muhibbat tangaram, anan muhibbat tace ga garinku, to
bayan daddy ya dawo, anan ya rasa abunda ke masa daddy, ke kuma lokacin kina jaririya,
domin kwananki hudu, to anan daddy ya yi kokarin turbude muhibbat a cikin wannan
gidan, haka ko akayi, a nan ya gina mata kabari cikin gidan, daga nan kuma sai ya auri
aunty balkisu, to wannan shine takaitaccen labarin muhibbat, inji kaka zuwaira, wannan
labari yasa meenat ta mutukar bayyana haushinta ga aunty balkisu, domin ji take kamar ta
kasheta.
To menene ke bamu tsoro a cikin wannan gida? meenat ta tambaya, daga nan sai kaka
zuwaira ta bata amsa da cewa, idan aka rufe gawar mutum a gida, to hadari ne zaman
wannan gida, domin ruhin mutumin kan iya zamar muku matsala, sannan wannan gidan da
kuke gani, na dade inajin labarinsa, yafi shekara dari gine, asalinsa na wani mai kudi ne,
shi ya gina shi, amma saboda yawan tsoron da ake bashi, dole yabar gidan, haka wani ya
saishi, shima dakyar yasha, dole yabar gidan, daga nan sai mahaifinki shima ya saya,
kinga tun asali wannan gidan ba mai kyau bane, daga nan sai laptop din ta dauke saboda
rashin caji, daga nan sai daddy ya basu umarni dasu tashi su samu hanyar fita daga gidan,
gaba dayansu suka tashi, anan suka fara tafiya cikin tsoro, basuyi nisa ba sai wannan
halittar ta dawo, cikinsu ta dauke wani, yana karaji ta wuce dashi, to a wannan lokaci sun
kawo daf da kofar fita, amma kuma taki budewa, to anan aunty balkisu tayi tsintuwar wata
takadda wadda aka yi rubutu da jini kamar haka: SAI NA KASHEKI.
hankalinta ya tashi, amma haka ta daure, wani irin mugun bugu daddy yama kofar, daga
nan sai ta bude, budewar kofar keda wuya sai wannan halittar ta fito, anan ta laulaye
mutum biyar ta wuce dasu, wato saura daddy, aunty balkisu,ummi,bafferh, da meenat,
sauran security agents duk sun mutu, kusan su hamsin.
Suna fitowa daga gidan, sai wani haske ya bayyana a kofar gidan, wata mata ce a cikin
hasken, kawai sai aunty balkisu ta tsaya tana kallon hasken, a wannan lokaci wannan
halittar ta dawo, kafin kaceme ta laulaye aunty balkisu, ita kuma ummi ta fasa wata irin
kuwa ganin mahaifiyarta cikin wani hali, anan ta sheka a guje da nufin kai mata dauki,
meenat ce ta riketa don kada taje ta halaka, kiyi hakuri meenat, bazan iya rayuwa ba idan
bada momina ba, injita, daga nan ta kubce ta nufi wurin halittar, aiko tana zuwa itama aka
laulayeta, shi kuma bafferh zuciyarsa ta kawo, anan yayi wani tsalle da nufin kai dauki,
halittar ce ta cabe shi, daga nan sai halittar ta shiga dasu cikin gidan suna ihu, ita kuma
wannan matar a cikin haske murmushi tama meenat kafin daga bisani ta bace, anan meenat
ta gane cewa matar tayi kamada wannan data gani cikin littafi, bako shakka itace
muhibbat, wato mahaifiyarta, anan meenat ta nufi gidan a guje, tana zuwa kofar gidan na
kullewa, haka ta duka tana kuka, gashi kuma tanajin ihun su bafferh a ciki, anan daddy
yazo wurinta yana lallashinta, daga nan sai yaja hannunta suka shiga cikin mota, wato su
biyu kawai suka rage cikin taron jama a, a haka daddy ya fara tuka motar yana fita kokarin
fita daga dajin, to bayan sun isa gida ne, sai kaka zuwaira ta fara lallashinta, su bafferh
basu mutu ba, kada ki damu meenat, anan meenat ta fara kallonta cikin mamaki, daga nan
sai kaka zuwaira ta cigaba da bayani, wannan littafin da aka rubuta labarin muhibbat ta
dauko, laa ya akayi kika sameshi? meenat ta tambaya, ai ali sarki baka ya kawo min shi,
wato ki sani meenat, a binciken da nayi da nayi, na gano cewa mahaifiyarki muhibbat bata
mutu ba, domin a lokacin da a lokacin da aka turbudeta, ashe wannan hakittar ce ta tona
kabarinta ta cinyeta, saboda haka sai ruhinta ya fita daga gangar jikinta, to wannan ruhin
ne ke baku tsoro, kuma shine kuke gani matsayin haske, akwai wasu ruwa da ake cema
RUWAN SIRRI, da zaran an ba halittar wadannan ruwan, to ba ko shakka zata amayo duk
abunta ta hade, to a cikin wannan amai ne zamu gansu, sai dai ruwan basu cikin wanan
duniyar da muke takawa, suna can wata duniya daban, aiko duk inda suke sai na nemosu,
inji meenat, daga nan sai kaka zuwaira ta bata wata sarka, wannan sarkar tsari ce, ki riketa
sosai, kuma da itace zaki iya dawowa wannan duniyar, daga nan sai kaka zuwaira ta bude
wannan littafi, anan ta fara karanta wadansu kalmomi marar ma ana, wani bacci ne mai
nauyi ya dauki meenat, daga nan kuma sai wata guguwa ta fito ta dagata sama, anan
wannan guguwar ta cigaba da tafiya da meenat sama domin kaita wannan duniyar da zata
nemo RUWAN SIRRI. kaka zuwaira da daddy sai daga mata hannu suke har ta bace suka
bar ganinta.
WANNAN SHINE KARSHEN LABARIN GIDAN FATALWA, SAI DAI ZAMU HADU A WANI LABARI
MAI SUNA ( RUWAN SIRRI ) WANNAN LABARI SHINE CIGABAN GIDAN FATALWA, KUMA A
CIKINSA NE ZAMUJI GWAGWARMAYAR DA MEENAT TASHA DOMIN SAMO RUWAN, DA KUMA
YADDA SU BAFFERH ZASU TASHI, MUNA BAKU HAKURI DOMIN LITTAFIN BAZAI FITO BA SAI
BAYAN SALLAH, AMMA YANA FITOWA ZAMUYI POSTING DINSA, MUNA GODIYA.
abdul king article
To be continue in ( RUWAN SIRRI)....

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment