Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Lawan Dana Amina ba karamin tashi yayi ba sosai aka hau neman Aliyu cikin samu ganinsa ba addua kawai suke akan Allah ya bayyana musu shi rashin Aliyu yasa Amina ta Dan fara rashin lafiya a cikin irin wanan Halin Naseer yaje neman Auren Naeema da kansa a wajen Lawan Inda farkon ganin da Lawan yayiwa Naseer yaji Naseer din bai kwanta Masa kamar yanda wani abdullahi yafi kwanta Masa a maneman Naeema ba Dan har a zuciyarsa yafi San Abdullahi ahaka iya shi ya yarjewa Naeema take kulawa sabida yabawa da yayi da hankalinsa Dan Naeema nada manema da yawa daga Samari zuwa manyan masu kudin sai dai ya lura kamar Naeema tafi San Naseer Kuma baya San yayi Mata dole.

A takaice ahaka Mallam Hassan yazo ya nemawa Naseer auren Naeema bisa jagorancin Mallam Ibrahim daya sakarwa Mallam Hassan ragamar komai.


Cikin mutunci akayi komai bayan Lawan ya danyi bincike akan Naseer da a garin Jos yayi binciken nasa bai San suwaye asalin iyayen Naseer ba.

Naeema kuwa kawayenta sai tayata murna suke da samun miji kamar Naseer Dan Naseer San da yake yiwa Naeema baya b'uya.

Wata uku aka saka bikinsu.

Inda matan Mallam Hassan su suka Dan had'a Masa lefe aka Kai lokaci kawai ake jira.


Naseer kuwa tuni ya Gina katafaren gidansa a garin Jos.

B'angaren Hajara kuwa haikan ita da yan kungiyarta suke neman Inda Mallam Ibrahim yaje ya b'oye Naseer Dan har lokacin Hajara na zuwar wa Mallam Ibrahim akai akai akan a nuna Mata Inda danta yake.

A cikin irin wanan lokacin Ana saura wata daya auren Naseer da Naeema .

Naseer da Mallam Hassan suka tafi Modobi wajen Mallam ibrahim.

Dan shima Mallam Hassan akwai wani kanin mahaifinsa dake garin Modobin dayake San duba jikinsa.


Suna zuwa aka musu tarb'a Mai kyau Mallam Ibrahim sai murmushi yake Yana bin Naseer da kallo a Ransa Yana tunanin a yau zai Dan bashi labarin Mahaifiyarsa Amma bazai Gaya Mata wacece ita ba.

Zai dai bashi wasu adduoi ya ringayi na kariya daga sharri duk da Yana tunanin duk hatsabi bancin uwa bazata tab'a danta ba.

Wajen karfe hud'u suna zaune gabadayansu a k'ofar gida har da yayyen Naseer da ke zuwa wajen mahaifinsu haka da yamma duk da ba uwa d'aya ce ta haifesu ba suna da balain had'in kai.


Cikinsu kuwa har da Mallam Hassan

Kamar wacce aka jefota haka suka ga Hajara a gabansu.

Dan shugabarsu ce tagano Naseer ta mudubi shi da Mallam Hassan hakane yasa tayi saurin gayawa Hajara shine ta bayyana gabansu afujajan.


Mallam Ibrahim Sallati ya saki a lokacin da ya ganta ya hau addua a Ransa.

Mallam Hassan shima Yana ganinta yasan itace duk da bai taba ganinta ba.

Hajara kuwa Naseer kawai ta zubawa Ido tana kallonsa tamkar yanda yake kallonta yanajin wani iri a jikinsa

Hajara kuwa da Sauri ta dauke idonta daga kansa data ga katon tabon Sallah Goshin Naseer nata shigar Mata Ido haka kawai taga kamar kallonsa na neman haddasa Mata ciwon Kai.

Ranar wanka ba a boye cibi inji Mallam ibrahim "wanan itace mahaifiyarka Naseeer"

Naseer mik'ewa yayi da Sauri ya Isa gabanta ya tsugunna har kasa ya fara gaisheta Hajara kuwa kamar ta Kama da wuta sabida tsananin bakincikin ilimin addinin data ga ya ratsa Mata d'a Dan har ga Allah hakan na iya zame Mata barazana.

A takaice a ranar Hajara ta kebbe da Naseer tana Masa masifa bai tab'a nemanta ba hakuri kawai yake Bata Yana shima bai San dalilin daya sa Mahaifinsa yak'i Basa labari game da ita share maganar tayi ya hau Masa fadan da yanzu basu had'u ba sai dai yayi aure batare da sanin ta ba.

Anan mmaki ya rufe Naseer Dan yasan bai mata zance aurensa ba Kuma tunda tazo bai ga ta kebb'e da wani ba ballantana yace anan taji labari.


Hakuri kawai ya bata

Ita kuwa tayi murmushi tana "Ai matar da zaka aura kyakyawa ce ba laifinsa"

Kara dagowa yayi cikin mamaki Yana "Kinsanta ne"?

"Sosai ma nasanta dazu duk naji labarinta da zuwanka gurin mahaifinka Kai yanzu dai kafisan mahaifinka akaina ko shiyasa baka tab'a nemana ba Dan haka yanzu gobe zanzo na d'aukeka muje gidana ka Kuma ga 'yan uwanka"


"Murmushi Naseer yayi Bai ce komai ba Yana Dan Jin wani iri a jikinsa kasancewarsu waje daya data zo tafiya kuwa sai data bi Mallam Hassan da wani irin kallo tayi kwafa tayi tafiyarta.

Bayan sallar isha Mallam Ibrahim ya d'an fara yiwa Naseer hannunka Mai sand'a da Naseer ya bashi labarin Hajara zata zo gobe su tafi yaga gidan da take zaune.

"Naseer ka dage da Addu'a mahaifiyarka Tana cikin kungiyoyi da yawa nima bansan wacece ita ba sai Dana aureta zama Bai Kama ka ba Dan kaima baka wuce ta sako ka a gaba ba Dan su ba basu San Allah bama balle suji tsoron sa a zuciyarsu basu San Mai tausayi ba ballantana suyi Imani"


Watarana zaka ganewa idonka watarana zaka San wacece mahaifiyarka tun sanin Dana Mata Bata baccin dare bansan a wane matsayi zan sakata ba Mayya ce ko matsafiya Allah kadai ya barwa kansa sani Allah kadai ke kareni sanin wacece ita yasa na dauke ka tun kana jariri na kaiwa aminina Sabida ya kularmin da Kai Ina tausayinka Naseer a cikin yarana kafi kowa hakuri Kaine Kuma bakayi dacen uwa ba tun a yanzu ka dage da Addu'a Naseer.


A takaice ire iren kalmomin Nan ya koma Yiwa Naseer da Naseer ya haddace Gam a kansa Amma a akaran kansa ji yayi ya kasa gasgasta zancen mahaifiinsa a wajensa mayyu apperance dinsu daban yake Dana mutane Amma zai dage da Addu'a kamar yanda mahaifiyansa ya bashi shawara....


Share

dis page is fiction gaskiya Dan wacce ta bada labari Bata San ya mahaifiyarsa ta zama matsafiyya ko Mayya ba but tunda novel ne hakane yasa zamu Nemo yanda ta zama mayyar


Next page zamu tsunduma cikin labarin gdan gadan insha Allah ur comments give me strength d more u comment d more na samu kwarin gwiwa tnk u
[6/26, 6:15 PM] Buhari Yusuf IBr: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*



*Page 4*


Washegari Naseer suka d'au hanyar Calabar shi da Hajara da a fad'arta tazo ne Dama Wajen wani kawunta a modobi taji labarin zuwansa.

Kwana biyu Naeeer yayi a Calabar a cikin kwana biyun da yayi ya ga abubuwan mamaki da Al ajabi daya d'aure Masa Kai ya Kuma kasa tunkarar Hajara da tambayar daya dank'are Masa a zuciya.

Farko suna Isa gidan ya tarar da kannensa Tijjani Wanda yake da shekara Ashirin a lokacin Sai Safiyya da take da Sha bakwai sai Lami da take da Sha uku a palon gidan a zaune Hajara batayi Sallama ba da suka gidan hakane yasa shi Kuma yayi Sallama ga mamakinsa babu Wanda ya amsa mishi sallamar da zaiyi magana sai ya fasa Hajara kuwa cikin washe baki tace musu ga yayansu Nan da take basu labarinsa kadaran kadahan suka gaishe shi shi ma ya amsa musu Yana Dan karewa palon da aka rataya wasu irin Abubuwa a kowane kusurwar palon har da su Kaho haka.

Muryar Hajara dake kwallawa Tijjani Kira yasa ya maida hankalinsa kanta har Yana mamakin ya za'ayi ga Tijjani a gabanta Kuma ta ringa kwalla Masa Kira haka.

Da Sauri yaga wani datijjo ya fito daga wani daki dake Gefen palon kallo daya zaka mishi kasan Yana balain Shan wuya har wani irin furfura ne suka yayame fuskarsa.

Yana isowa gaban Hajara ya zub'e Yana Mata sannu da zuwa.

Naseer kuwa tsananin mamaki yasa ya saki baki Yana kallon ikon Allah.

Hajara kuwa Bata amsa gaisuwar da yake Mata ba tace "Naseer ga Babansu Tijjani Nan ku gaisa"


Da Sauri babansu Tijjani ya isa wajen Naseer yana neman durk'usa Masa.

Naseer kuwa ya mik'e cikin tashin hankali da Alajabi ya taro shi ya kalli Hajaran Yana "kina nufin Wanan shine Mahaifinsu Safiyya ma'ana mijin da Kika Aura da kuka rabu da Abbana"?

Hajara d'auke idonta tayi daga kansa ta watsawa Tijjanin wani irin kallo.

Shi kuwa jiki na rawa yayi waje da Sauri har Yana tuntub'e Yana zuwa Dab da kofa tace Masa ya shiga kitchen ya tuka musu tuwon Massara da miya.

Da Sauri ya gyada Mata Kai ya fice yana sharar hawaye.

Tunda ya Auri Hajara yasan ya aurowa kansa balai bashida ilimin addini da zai Kare kansa daga Sharrinta baya iya ketara umarnin ta Yana ji Yana gani ya rabu da matansa biyu Yana ji Yana gani ta watse Masa Yaya suka shiga duniya Banda biyu da suka rasu da yake zargin itace ajalinsu ya Riga da yasan wacce ya aura ya Sha yunk'urin guduwa tana kamoshi sosai suka d'aure shi da tsark'a har addua yake mutuwa ta d'aukeshi da irin rayuwar da yakeyi da ita.


Naseer kuwa bayansa yabi da kallo har ya fice ya dawo da kallonsa Kan Hajara data balain had'e Rai hakane yasa ya kasa Maganar dayake da niyyar Yi ya koma ya zauna tunani barkatai na zuwar Mishi

"Abba bazai min karya ba duk da ban tashi nasan wacece mahaifiyata ba ni akaran kaina nasan itace mahaifiyata Amma wane irin Abubuwa nake gani haka ta yaya Mahaifina da yake Shahararren mallami zai auri wacce ake zargin matsafiyya ce ko Mayya Astagafurullah Mahaifiyata ba Mayya bace ba matsafiyya bace insha Allahu Ina dai tunanin tana da fad'a.

Naseer duk ke maganar a zuciyarsa.

"Karka manta Naseer Allah Kan fitar da matacce a cikin Rayyaye ya fitar da Rayayye a cikin matacce Ka yarda da zancen Mahaifinka ka dage da Addu'a.

Maganar Hajara ne ya dawo dashi tunaninsa

"A Ina zaku Zauna Kai da matar taka"?


"Zamu zauna a garin Jos ne Umma anan na siyi fili har na Gama gini"

"Toh ban yarda ka zauna a Jos ba kaji ko ban yarda ka zauna da Dan iskan abokin babanka da ya d'aukemin Kai ko fuskarka ba'a Bari nagani ba ka Kara ma mu'ammalla dashi Naseer sai na tsine maka daga Yau ba Kai babu shi Dan babu yanda zanyi ne Dana ce har mahaifinka ban yarda ka cigaba da mu'ammalla dashi ba
Ban yarda ka ringa b'oyemin komai ba da yanzu a gabana ka girma da duk bazaka zama wani susu su haka ba"

Naseer rusunawa yayi a gabanta cikin tashin hankali Yana "Umma Abba fa shi ya Raine ni ya rik'eni tamkar Dan daya Haifa a cikinsa Dan Allah Mai yasa kike so ki rabamu Dan Allah kiyi hakuri nasan anyi Miki laifi Bai Dace a rabamu ba tun Ina jariri Dole zakiji ba dadi Amma Dan Allah kiyi hakuri Umma wannan matakin da kike San d'auka a kaina yayi tsauri Umma"


"Toh sai dai ka zab'a ko Ni ko shi Naseer idan Kuma ka zabe shi Banga abinda zai Hana nayita tsine maka ba daga yau babu Kai babu shi ko Jos d'in ma bana so ka Kara zuwa zamanka a wajensa ba alheri bane a gareni sai Sharri"


Sosai Hajara ta ringa bambamin fad'a har tana neman yiwa Naseer baki.

Shi kuwa Naseer sosai hankalinsa ya tashi Sosai da rabashi da Hajaran ke neman Yi da Mallam Hassan Wanda ya Masa abinda ko Mahaifinsa Bai Masa ba tun daya taso ya fara wayo ya fuskanci irin Kaunar da Mallam Hassan ke Masa ba k'aramin jajircewa Mallam Hassan yayi a kansa ba ko Sana'ar da ya farayi da kudin Mallam Hassan ya fara kafin Mallam Ibrahim ya turo Masa kudi ya Kara Jari Taya Sama ta Ka shekara da shekaru da suke tare ace lokaci guda mahaifiyarsa tace su rabu har tana barazanar tsine Masa.

Tunda ya taso Abu bai tab'a d'aga Masa hankali kamar yanda rabuwa da Mallam Hassan ya d'aga Masa hankali ba hakane yasa ya dage ya cigaba da rokar Hajara ita kuwa ta cigaba da Shan alwashin tsine Masa matsawar Bai bi umarninta ba.

Kiran Sallah ne yasa Shi mik'ewa ya fita waje ya d'aura alwala ya nufi Massallaci yayi Sallah azahar.

Yanda zuciyarsa ta cunkushe da tashin hankali yasa ya d'auki Qurani daya gani a Massallacin ya fara karatu ahankali yaji ya fara samun nutsuwa a Massallacin yayi zamansa har akayi Sallar ishai Dan Bai San Mai yasa yaji yafi samun nutsuwa da iska Mai dadi a Massallacin akan gidan Hajara ba.


Hajara kuwa sosai hankalin ta ya tashi da yanda taga Naseer nada ruk'o da addini Dan taga alamar bazata iya mallake shi yanda take so ba duk da wani Abun zai iya tasiri akansa Amma zai na sakin shi nan da Nan sosai tayi ta tsinewa Mallam Hassan da Ibrahim Dan har yan kungiyar sun so tab'a Mallam Hassan Wacce taje Masa a Siffar Mujiya ya watso Mata ruwan rubutu Wanda ya k'ona Mata Rabin Fuskarta Sosai shugubarsu ta fusata suka Kara d'aura damaran ganin Bayan Mallam Hassan da suka lura idan basuyi da gaske ba zai iya cin Galaba Akansu Dan a tsaye yake sosai duk jifan da suka masa baya kama shi da alamar shima Naseer din kusan hakan ne


Hakane yasa Shugabarsu Hajaran ta cewa Hajara lailai ta raba Naseer da Mallam Hassan.

Wani Abu suka bawa Hajaran akan ta dafawa Naseer abinci dashi indai yaci zasu Dan ci Galaba akansa wajen Mallakeshi.

Sai dai har ta Gama girkin Bai shigo ba har dare yayi.

Naseer kuwa har Sha biyun dare Yana Massallacin har zai bar Massallacin Kuma ya koma ya zauna daya ga wasu su biyu sun shigo da alamar kwana zasuyi suna karatu aikuwa tuni ya koma ya zauna ya shiga cikinsu suka kwana suna Karatu Sabida biyan bukatar gabansa yasa ya tashi da azumi.


Sai washegari ya koma gidan Hajaran data cika tayi Fam Dan duk yanda taso ganin Inda yake ta cikin mudubi,Bata samu ganinsa ba illa haske kawai data ke gani anan ta Kara sanin Naseer ya karantu akwai Kuma dafai a jikinsa.

Dak'yar ta amsa gaisuwar sa ta hau surfa Masa Balai shi kuwa yayi ta Bata hakuri sai data Gama Dan kanta tace ga abincinsa Nan ya tashi ci.

Wani irin kallo ta watsa masa lokacin da yace
Mata azumi yake.

A takaice duk yanda Naseer yaso shawo Kan Hajara abin yaci tura ahaka ya Mata Sallama ya taho Modobi zuciyarsa a cunkushe Dan ta rantse Masa idan Bai rabu da Mallam Hassan ba sai ta tsine Masa ta Kuma ranste bazai zauna a Jos ba yaje ya siyar da gidan ya dawo Calabar yayi gini su zauna.


Allah yayi wa Mallam Hassan baiwa sosai na gane Abubuwa Wanda har idan wani mummunan Abu na neman far'uwa dashi Allah Kan nuna Masa a mafarki shi Kuma sai ya dage da Addu'a idan ma abin zai faru zai zo Masa cikin sauki ya Dade da sanin irin harin da Hajara take kawo masa hakane yasa yaci damarar Kare kansa ko tafiyar da Naseer yayi da mahaifiyarsa sai daya dage da Addu'a cikin Mafarki Allah ya nuna Masa komai ya Kuma Godewa Allah.

Hakan yasa yak'i komawa Jos ya zauna zaman Jiran dawowar Naseer Dan ya Kara Masa wasu adduoi.

Naseer kuwa a lokacin daya iso kasa magana yayi da Mallam Hassan Yana Jin kamar lokacin Hajara ke rantsuwar Yi Masa baki indai ya Kara kulashi sosai kirjinsa ya Masa wani irin Nauyi ya hau zubar da hawaye Bai San maanar tashin hankali ba sai daya ga Hajara na neman rabashi da Wani b'ari na jikinsa.

Murmushi Mallam Hassan yayi a lokacin da yaga idon Naseer ya kad'a yayi Ja ya sunkuyar da kansa ya kasa Bari su had'a ido.


Mallam Ibrahim kuwa wani irin ajiyar zuciya ya sauke da yaga Naseer ya dawo ba abinda ya same shi.


"Karka damu na Riga da nasan Komai D'ana Ni nasan zatayi haka Dan Bata da makiyin daya wuceni Uwa ba Wasa bace kabi Umarninta Dan Allah sai dayace kabi Uwa sau uku kafin a ambaci Uba Abu daya zan Gaya maka karka sake da Addu'a ka dage da Addu'a dan Mahaifiyarka shu'uma ce ta gaske ta wuce tunaninka Sabida Kai yasa nak'i bud'e Mata wuta Amma da yanzu an shafe labarinta ita a tunanin ta idan ta rabamu shine zata iya cin Galaba a kanka tun kana jariri ban barka haka ba Naseer sai Dana Dage maka da Addu'a Kuma Alhamdulillah gashi ka girma cikin kariyar Allah a yanzu ne zaka fara fuskantar kalubale a rayuwarka domin Mahaifiyarka itace kaddararka duk lalacewa dai mahaifiyace Amma addu'a na iya canza komai idan rabbi ya sota da Shiriya zata shiryu kafin lokaci ya Kure kayi Mata biyayya ba zan fasa maka adduar dake daga mata hankali ba Kai yanzu ba yaro bane tunda baifi saura makwani ka Rayya Sunnar Ma'aiki ba Naseer ba kanka kawai zaka dagewa da Addu'a ba ka fara saka matar da zaka Aura a addua domin rayuwata itama Tana cikin hatsari karka tab'a kwanciya babu alwala Naseer daga Kai har iyalinka a yau da ba Hajara ce ta haifeka ba ace wani daban ta Haifa wlh Tallahi sai na kawo karshen tsafinsu Allah ya Kan Arawa bawa Dama yayi ta shagalinsa Wala Ala a gaba ko zai gane abinda yake Yi ba daidai bane ya gyara kafin lokaci ya Kure maka Amma Hajara ta Riga da tayi nisa ba Kuma ta Jin Kira Allah ya shiryeta ya ganar da ita gaskiya Bata isa tayimin komai ba sai dai idan Allah ya kaddara ta silarta zan tafi dawowar ka kawai nake jira Dama da tuni na tafi Amma duk da haka a yanzu zan d'au hanya Allah ya kareka da karewarsa ya baka ikon cinye wanan jarrabawa."


Daga haka Mallam Hassan ya mik'e ya jawo jakar kayansa Naseer kuwa duk dauriyarsa a matsayinsa na d'a namiji sai da ya fara zubar da hawaye kamar mace Yana kallon Mallam Hassan ya fice daga d'akin Mallam Ibrahim na rokarsa ya kwana gobe ya dau hanya ya dage sai ya tafi.

Motarsu Bata tashi ba sai wajen karfe biyar na yamma


Yan kungiyarsu Hajara kuwa Suna kallon komai ta cikin Mudubi hakane yasa Motarsu na d'aukar hanya duk suka rikid'e suka koma siffar Mujiya suka tashi lokaci guda kusan su dari.

Mallam Hassan kuwa tunda ya hau motar ya rufe Ido Yana tayiwa Annabi Sallati Bai ankara ba yaji an driver yataka wani irin birki Sakamakon Mujiyoyin da suka cike gaban glass din motar Wanda hakan yasa driver ya daina ganin gabansa har ya Kai shi da buga wani katon dutse dake Gefen hanya Motar ta kife.


A takaice mutane biyu ne suka Rayu a Hatsarin Motar ahaka Mallam Hassan ya amsa Kiran Allah Inda sai da Mallam Ibrahim da Naseer suka yi kwana uku a asibiti Sabida yanda mutuwar Mallam Hassan ya gigitasu.


(Allah ya jikanka Baba Ibrahim Allah yasa Aljanna ce makomarka a gaske akayi hatsari ya Kuma rasun Inda da yawa ake zargin yan kungiya ne suka haddasa Hatsarin Sabida biyu daga wayanda basu mutu ba suka bada labarin yanda Mujiyoyi suka rufe gaban motarsu Allah ya tsare Mana imaninmu Ameen)


Har Mallam Hassan ya samu sati biyu da rasuwa Naseer bai dawo daidai ba haka Mallam Ibrahim Dan tunda akayi rasuwar yake kwance ya Kuma daina magana.

Dak'yar Yan uwa da abokanan arzkiki suka samu rarrashi Naseer ya fara dawowa daidai Yana yiwa Mallam Hassan addua da yake ganin kamar zaa tashe shi ace mafarki yake ba mutuwa yayi ba Ashe duk maganar da yake Masa a ranar na bankwana ne daya sani ya rakashi daya Sani ya tashi ya rungumeshi kafin ya tafi.


Hajara kuwa sosai sukayi kwana bakwai a daji suna abubuwa na murnar Mutuwar Hassan Dan Dama shine ya zame musu karfen k'afa.


A takaice bayan Sati uku da rasuwar Mallam Hassan aka daura Auren Naeema da Naseer ba'ayi komai ba bayan daurin Auren Dan har a lokacin Naseer ba wani dawowa daidai yayi ba San ma dayake yiwa Naeema da San mallakarta ne yasa ma yake Dan samun relief.

Kamar yanda Hajara ta tsara ya nemi gida a Calabar haka ya samu karamin gida ya siya gidansa na Jos kuma ya zuba 'yan haya.


Hajara duk da gidan karami ne daki biyu da Palo sai kitchen da toilet gani take gidan yayi wa Naeema girma ita kadai

Sosai idanta ke Kan komai da Naseer zaiyi naira Hamsin ma da Naseer ya biya Sadaki a wancan lokacin sai data nemi ya rage Dan Naira Ashirin shine highest din kudi a time din dak'yar ya samu ta barshi ya bada naira Hamsin din.

Naseer Sanin darajar uwa da masifar dake tare da Bijirewa uwa yasa yake balain yi Mata biyayya ba Kuma yasan tayi fushi dashi zuwa Lokacin ya fuskanci Rashin ilimn da basudashi gabadaya a Kuma iya saninsa baiga Hajara ta tab'a sallah ba balle Kannensa.

Wani zubin yakan so ya gasgata Abinda ake zarginta dashi Amma kyakyawar zuciyarsa sai ya ringa zata Mata zato Mai kyau.


Sai da akayi Sati da Daurin auren Naeema da Naseer ta tare bayan Mahaifinta Lawan ya damka amanar Naeema a hannunsa ya kuma rok'esa daya riketa Amana Bata da kowa sai shi tunda sunyi nisa da juna zasu ringa aikawa Juna wasika ta Fax suna sanin halin da suke ciki.


Mahaifiyarta da tun b'atan Aliyu Bata Kara samun cikakken lafiya ba itama sai datayi kukan rabuwa da Naeema Dan har ga Allah bataso Naeema tayi Mata Nisa haka ba taso Aurenta tayi a garin ko a kusa da garin Kar abin ya.mata yawa duka yaranta biyu babu Wanda take gani addua kawai tayi musu itama ta roki Naseer daya rike Mata amanar Naeema kamar bazasu rabu ba aka fito da Naeema dake Jin kamar ta hakura da auren Naseer tana fitowa ta fara k'ewan Iyayenta.


Makotan arzikine suka Rakata har Calabar Lawan Kuma yace idan an kwana biyu zai saka shima a rakashi ya gano Inda suke zaune.

Wayanda suka raka Naeema washegari da suka kaita suka juyo bayan ya Naseer ya musu goma sha Tara ta arzki shima a b'oye Sabida Kar Hajara ta gani tayi Magana.

Sosai yake dokin kasancewa da Naeema Sabida tsananin San da yake.


Gida uku ne tsakanin gidan Hajara da gidan Naseer din

Hakane yasa Dan Abubuwan daya siyo ya siya guda biyu ya fara shiga wajen Hajara Dan ya Mata sai da safe.

A palon ya tarar da ita a zaune ta Sha dogon Jar Riga har kasa ta rambada kwalli Tana ta karkada kafa Fuskarta a had'e gefenta Kuma Mijinta ne.tijnani ya sada Kai kasa kamar Mai neman yafiya.

Wani irin tausayinsa ne ya rufe Naseer wanda hakan yasa Naseer danne nauyin Hajaran da yake ji bayan sun gaisa da Hajaran dake Masa wani irin kallo tana mamakin shakkarta da ta ga Naseer ba yayi idan tayi shigar dake saka hantar mutane kad'awa ko had'a ido baa iya Yi da ita intayi Shigar meeting d'insu.

"Umma Miji shugaba ne a wajen matarsa sai mace tabi mijinta take samun Aljanna Umma bana jin dadin yanda nake ganin Baba bana Jin dadin yanda yake neman maidaki shugabarsa Umma Dan Allah banyi magana Dan na b'ata Miki Rai ba bana San ki shiga fushin ubangiji"




"Kaiiiiiii dakata wa'azi zakamin har ka Isa kazo ka tsaya a gabana kana gayamin abinda ya dace da Wanda Bai Dace ba Ni Hajara baayi Wanda zan bishi ba daga yau karka Kara tarata da magana irin wanan wlh ranka zaiyi mumunan b'aci duk abinda zanyi idone naka kawai Kuma daga yau karka Kara tilastawa yayana suyi Sallah ai kowa na da raayinsa ko karka zo ka cusa musu abinda basuyi niyya ba ka dai ji na Gaya maka wanan ledojin daka shigo dasu na menene"?

Naseer dak'yar ya hadiye yawu sabida b'acin Rai dayaga yanda baba Tijjani jikinsa ke balain rawa da Hajara ke magana


"Kayan marmarine da kaza na siyo shine nace Bari na fara kawo miki kafin na wuce gida"

Karbe ledojin tayi gabadaya ta d'auko iya ledar Ayaba da lemon ta mik'a Masa tana "Zaka iya tafiya Kazar Kuma zan bawa kannenka suci ai Suma suna bukata"

Naseer baice komai ba ya karbi ledar ya mik'e ya Mata sai da safe.


Yana fita ta dakawa Baba Tijjani tsawa Akan ya tashi ya Bata wuri.

Waje yayi a rude Inda ya tarar da Naseer ya zubawa waje daya ido da ledar lemonsa a hannu.

Baba Tijjani baice Masa komai ba ya wuce shi Naseer ya fara binsa a baya.

Sai da suka jere ya fara magana Yana "Ka dage da Addu'a

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment