Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiyimin na,yanzu dai ciro mun kaya a cikin wajen kayannan tukunna,sannan idan kin ciro ki je ki dubamin matannan,duk abinda suakyi kizo ki fadamin,dan ba yarda dasu nayiba,ƴan tuƙa tuƙa kawai"
Surayyan ta buɗe baki zata sake cewa wani abu nayi saurin shigewa banɗakin.
Dan banson yawan surutun yanzu,ina jin dariyarta a ɗakin har kuma tayi shiru.
Cika bahon wanka nayi na shiga na kwanta,gaskiyah nayi kewar ƙasar palastine dan rabona da danayi wanka na cikin baho tun ina can.
Saida na kusa awa guda kafin na fito daga bandakim,shima ina fitowa na samu surayyah ta fitomin da kayan,dan haka ina sakawa nabi lafiyar gado.
Bangaren masu aikin gidan aka kaisu dan shima wajene mai zaman kansa,sun mafi sakewa a canɗin akan dakina,dan wallahi babu da matar da zan kwana tunda bani na gayyatosu ba ai.


💎*sameer a madubin gani*💎


Tun dazu nake zaune ina aiki amma nagaza tabuka wani abin kirki,daga na fara tubutun da shigar bayanai sai na ajiye,ni kadai na jera tsuka tafi cikin kwando ina zaune.
Na rasa ma abin da yake min daɗi,ni kaɗai nasan irin ƙalubalen dana ke shirin fuskanta na rayuwa da sameemah a cikin gida guda,kirjina sai bugawa yake yi lokaci bayan lokaci.
Ga saleema tun lokacin dana daukota daga gidansu tah daina yimin magana,ko na kulata ma saidai ta bar wajen,abin duniyah duk yah isheni.
Sallama akayi tareda bugo ƙofar office ɗinnawa,ina ɗaga kai mukayi arba da Ahmad babban abokina wanda tare muka yi karatu da kuma tafiyah service a Russia.
Miƙomin hannu yayi muka tafa kafin yace,haba mutumina kana ango wanda za'a kawo masa amaryah yau amma kuma kake aiki,wai yama naganka da damuwa a fuskarka,kamata yayi yau ka yini cikin fatin ciki ai"
Hmmmm kawai nace,dannasan idan nayi masa magana ma bazai fahimta na sam,dan haka babu ma wani zancen tsayawa bata lokaci akan maganar.
Wasu abokan aikimmune suka sake shigowa,sai tsiyah suke min,dole babu yanda zanyi na ajiye aikin tareda ta fiya gida.
Gidan su Ahmad muka wuce,dan shine zai auri suhaila ƙawar saleema watan jibi.
A dakinnasa yada zango,akan zasu rakani zuwa dare,saboda nace bazan yi komaiba dan haka dole suka ƙyakeni tunda basu san dalilina ba na ƙin yin komai ɗin.
Wajen ƙarfe goma na dare muka shigo cikin gannawa kowa a cikin motarsa,nidai binsu kawai nake duk abinda suka ce,dan karsu gane halin da ake ciki.
Falon babu kowa kaman ba bu mutane a gidan,ɗakin saleemah muka fara nufa wanda yake bangaren dama yana kallon wanda sameema take ciki.
Nufar ɗakin saleema muka farayi tukunna amma ƙofar ta ƙi buɗuwa tah kulleta,ɗan jimm nayi kaman mai tunani kafin na koma inda su ahmad suke,ɗan yaƙe nayi wanda yah fi kowa ciwo.
"Ina ga tayi bacci kaman"
Ɗaga kai sukayi alamar sun fahimta duk da basu yarda da abinda nace ba,ƙarbar ledar dayake hannun ahmad nayi ina yi musu murmushi.
Fatan alkhairi sukayimin kafin kowa yah shiga motarsa yah nufi gidansa.
Ajiyar zuciyah nasake ganin yanzu niƙadaine a cikin cakwakiyar nan babu kuma mai tayani yinta.
Ɗakin sameema na tura na shiga,a zaune na sameta ta saka kayan bacci gefe kuma tana ƙurbar tea a kofi,duk wanda ya kalle ta sai yayi zaton dama gidantane kuma ta daɗe a ciki,dan batayi kama da maryar da aka kawo yau ba.
Daga kai tayi ta saman system ɗin datake gabanta ta kalleni kafin na ɗauke kanta,daga nan bata sake cewa komaiba sai ma cigaba da aikinta da ta cigaba dayi.
Nima banyi mata magana ba,sai ajiye ledar nayi a kan drawar gadon da nake kusa da itah,juyawa nayi na fita daga ɗakin,har na fita naji muryarta tana cewa,
"Baka rufemin ɗakina ba,sannan kayi na farkone amma daga yanzu in wani abune ka fada nazo na ƙarba,banson a dunga shigomim ɗaki babu izini"
Jijjiga kai kawai nayi na koma falo na zauna,yazanyi allah ya hadani da mata,mabanabanta,daga wacce sakalcinta yayi yawa sai wacce sakalcin matan ma bata iyaba kaiiiii.

Ina nan zaune na kunna kallo amma hankalina kwata kwata baya kan kallon,yana kan yanda zamyi na magance abunda yake shirin faruwa a gidana.
Alamun wulagawar mutum nagani yah shiga kicin,wanda ban ma kula sanda ya wuce ba,saida tah fitone na kula a she sameemah ce ta ɗauko plate daga kitchen ɗin.

💎*sameerah a madubin gani*💎

Har dare yayi amma na gagara bacci saboda halayyar umaruje tun ba a je ko ina ba ta fara canjamin,dan yanzu nakula akwai wacce yake so,suke wayah kullum,idan na tambayeshi ne kawai gani gashi Bayamin musu,amma idan abu a wayane cewa yake cewa bai sani ba ɗin,danaga hakanne na fara lallabashinsa dan a zauna lafiyah,saidai naga abin kaman gaba yakeyi ba baya ba,
Yanzu ma zaman jiransa nakeyi tun safe bai shigo gidan ba har yanzu,gashi gobene tafiyar sa Dubai,abin takaicin waccen shegiyar uwartasa.
Ina cikin safa da marwan na juyo kenan muka haɗa ido dashi sai layi yakeyi na maye,ga kuma zagi dayake da ɗurawa,takaicine yah kamani ga warin giyah,na rasa ma da wanne zanji,ni gsni nakeyi gwada ma salma koba komai alhaji bala baya shan giyah,sannan ba itah mijinta zai tafi yah bari ba,dui da itam da itah da babu duk ɗayah ne a cikin gidan,dan hajiyah mairo tafi ƙarfin tunanin mutum.
Tallafoshi nayi tareda tsinke tunanin danakeyi ganin yana ƙoƙarin hawamin gado a haka,tureni yakeyi yana maganar da ni kaina banajin mai yake faɗa.
Daƙyar allah yabani iko na cire masa rigar jinsa da takalmimsa kafin ya kwanta.
Bakajin komai sai minsharinsa kawai,dan baccinsa yafara hankali kwance,hmmm ga kuɗi da jin daɗi amma babu kwanciyar hankali kwata kwata.
Da safe da wuri na tashi nayi abinda zanyi na tafi madafar abinci,dan yanzu duk mune muke komai na gidan kaman yamda hajiyah mairo ta faɗa.
Har nagama abinda zanyi na fita umaruje bai tashiba,nima ban tasheshi ba na bar ɗakin zuwa aikin dazanyi.
A wajen nasamu salma wanda tarigani zuwa yau ba kaman kullum ba,kallonta nayi ban cemata komaiba,itama bata kulaniba da babu wanda yake yiwa wani magana kaman bamu san junaba,kowa tasa ta fishshsheshi.
Kayan abincin muka fara haɗawa,dan ma yanzu aikin yaragu saboda babu na ƴan sadaka,mu kaɗaine kawai.
Bamu kai minti ashirin ba a wajen muka kammala tsaff,nice na wanke kwanukan da mukayi aikin yayinda ita kuma salma ta kai abincin wajen cin abinci.
Saida muka gama kafin muka jiyo hayaniyar hajiyah mairo itah da alhajin suna saƙƙowa,gaishesu mukayi kafin muka ja kujera kowa ya zauna.
Har an fara zuba abinci hajiyah mairo tah kalli kujerar umaruje babu kowa akai,wani kallo ta watsamin kafin tace,
"Ke ina mjinki ban ganshi a wajen cin abinci ba?"
"Uhmm dama mommy yana baccine,tunjiyah daya dawo yana maye na giya bai tashiba"
"Mtsww baki san yanayin kulada mijiba bare kuma sirrinsa"
Tashi nayi nayi hanyar sashenmu domim tashinsa,dama da gangan na faɗi har da giyar dayasha dan taji haushi,duk da nasan ba komai zasuyi mar ba daga itah har ubannasa.

Lokacin danaje tashinsa har yah tashi ya shiga banɗaki sai ƙarar ruwa dana ji kawai.

💎*sameemah a madubin gani*💎


Lokacin dana buɗe idona daga bacci samun kaina nayi kwance a kan sabon gadon da aka mallakamin a matsayin nawa.
Hasken rana ne yake shigowa ta windon ɗakin da alama hantsi yayi duk ina bacci,dama kuma ban kwanta a da wuriba ina tah shirye shiyen yanda zan kai takardar neman aikina a nan garin,wanda jira nake ayi kwana uku na fita neman aiki kar lokaci ya ƙure.
Surayyah ce ta shigo ta tiren abinci a hannunta,a jiyewa tayi tana murmushi,wani lokacim har mamaki take ban,bata fushi abinda koyaushe tana cikin murmushi.
Gashi tayi haske abinta saboda ƙaramin cikin da take dashi,kallonta nake yanda take zuba shayi akofi tana kuma gulmar su inna rabi sun cinye abinci mai yawa kuma basu ƙoshiba,saikace masu cikin rumbu kalan su jawo mana magana a wajen mutaneen gidan.
Bance mata komai ba akan zancennata dan ba abin mamaki bane zasu aikata,musamman ƴan ƙauyen da baba umaru yah nace sai an taho dasu.
Bayan mungama karyawa nne na shiga wanka,dan yamzu wankana zai dawo saboda ga ruwa ko wanne lokaci,dama na saba da wanka akai akai,rashin sa ne a gida yasa nake yin guda ɗayah.
Wasu fararen kaya nasaka acikin kayam da aka sakamin a cikin ɗakin,dogon wandone da riga iyah gwiwa sai kuma ɗan mayafi.
Lokacin dana fito zanje sashen da su inna rabi suke ma'aikatan gidan sai kallona sukeyi har na isa wajen.
Banyi sallama na shiga kawai nayi,gabadayah a iyah kwana ɗaya duk sun birkice falon,kallon wajen nakeyi da mamaki,da guntun biredi ruwan shayi akan kujera harda yaro mai fitsari.
Dan takaici koh magana banyiba,inna rabice da kwarin gwiwarta tace,
"Amarya bakya laifi,yah kwanan baƙunta kuma,ya mijinnaki da abokiyar zaman,ɗazu yazo nan muka gaisa ai zai fita aiki,yace ma mushiryah motoci su mayar da mu"
"Toh ashe kin ganshima kuma kike tambayata ya yake,ni babu wanda na haɗu dashi dan tashina kennan,itama da kike tambayata itah ban ganta ba,yanzu dan tsabar nuna hali kuga yanda kukayimusu da muhalli,kaman awaki sunyi kalacen safe?"
Wata ce daga can gefe da kofi a hannunta tace,
"Lahh wai waje,bamu kohiii ba ma,gahii masu aikin sunƙi karo mana,dan sunga muna ƴan uwan amaryah,hiiine nace tunda kinzo me zai hana ki ƙaro mana,wajene ina ba ta ziri ba bazaka ƙara dawowao ba bare kaci mai daɗi aradun allah"
Kallonta nake kaman na shaƙetah.
"Baku kohii ba,toh karku kohiiin ƴan kohin uwa kai,nabi kohin da gudu,wallahi banga laifinta ba taƙekin kuzo mata gida,ku kalli yanda kuka maiida wajennan,kallai uban kulolin da aka ciko da abinci kaman na mutum hamsin,amma ku iyah goma kun tashi dashi,toh wallahi naji wacce tace bata koshinba,kuma kuna gamawa babu mai barin gidannan saikuna gyara wajennan tassd,bari ma ku gani na karbo muku tsintsiyah"
Tashi nayi na daure fuska,saida na surfesu tass,kowa tayi tsuru tsuru taan jina,haba mutum bai san komaiba sai ci kawai,kaman jaki.
Fita nayi zuwa ɗakko musu tsintsiyah kowa saitattare na gabanta takeyi,mai ɗan ta kuma da yayi fitsari ta tafi nemo ruwa.
Hmmm karutai kawai aka ce basaji.......


Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎





*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}



💎13~14💎


Komawa ɗakina nayi nikaɗai ina tsuka,haba irin wannan halin ai dole komai ma a fada muku.
Bayan sun kammala inna rabi ce kawai tazo mukayi sallama,sauran wai haushina sukeji,itama ciki ciki mukayi magana,a raina nace ai sai kuyi babu dama mutane basason gaskiyah kwata kwata.
Ina jin ƙarar tashin motar tasu,dan daga window na ma ina ganin kokuwar da sukeyi akan shiga motar.
Yau kwana na uku a gidan sameer,rabona da ganinsa tun lokacin da yakawomin kazar amarci,ko nace kazar al'ada,matar gidan kuwa rabona da ita tun a falo sanda aka kawoni,ina jin motsinta a falo da kicin,duk da yawancin muryar wata nakeji a ketchen ɗin daban.
Ganin zaman ɗakin ya isheni ne kwana uku yasa na saka wata doguwar riga bayan na fito daga wanka,babu abinda na saka a fuskata haka na fita zuwa falon.
Babu wanda na samu sai kallo shikaɗai yanayi,wajen abincin na wuce na zubo masa da miyah taji hanta na dawo falon wajen da kallon yakeyi.
Ina jiyo hayaniyar saleema ita da wani,da alama mijinnatane yake nan.
Can wajen kamar minti uku naga sun fito daga ɗakinnasa,sai shagwaba take yimasa shikuma yana biyeta kaman wata yarinyah,ta wani lafe a ƙirjinsa tana bubbuga ƙafa,
"Uhm uhm honey wallahi nikam zan bika mutafi,kayimin akawarin waccar tafiyarfah amma shine zaka cemin wai bazanje wannan ba"
"Kai saleemah da rigima kike,da da yanzu ba ɗaya bane,lokacin baya ke kadaice amma yanzu kinga ku biyune koh"
"Ahah ni bazan yaddaba,naga ita ba sonta kake ba auren dolene kawai da cika wasiyyah,dan haka nikam muyi tafiyarmu kawai"
Shiru yayi na ɗan wasu lokaci da alamun bai so ta faɗi hakanba saboda sun san ina jinsu,ita kuma da gangan ta faɗa dannaji haushi,kuma take mammanne masa dan ta nunamin ita kaɗaice a wajensa.
Kallonta yakeyi da alamar meta aikata haka,ita kuwa harda wani murguɗa baki alamar tayi ɗin.
Duk abinda suke ba iyah jinsu nakeba harda kallonsu,saidai ba kowane zai kula ina kallonsu,saboda na kware a wajen satar kallo da kuma ɗauke magana.
Ƙarasowa sukayi cikin falon har sannan tana maƙale dashi,wanda duk da ba damuwata bin ka idaba amma nasan ka idar amarya itace da miji,amma daga dukkan alamu a ɗakinta na kwana,kuma ma dannasam hakanne yasa ta shigaba da faɗar.
"Honeey jiya fah muna kwance da daddare na fada maka cewa,ni bazan yi sharing falo da wata ba,kuma baka ce komai ba,gaskiyah saidai tah koma ɗayah bangaren kawai"
Kallon fuskarsa nayi wanda yake min wani kallo da niyyar yana jiran yaga mai zanyi,bai san koda za'ayi shekara suna zancensu bazan yi magana ba saidai idan sakani sukayi a ciki.
Tashi nayi na nufi kitchen domin kaiwa plate ɗin danaci a binci a ciki.
Lokacin dana dawo suna dinning wajen cin abinci,cigaba nayi da kallon labaran da akeyi a ƙasar iraq cikin harshen larabci na ƴan ta'adda da suka kai hari.
Hankalina ya tafi gabaɗaya wajen labaran da ake yi,banzata ba sai gani nayi an sanja tasha zuwa ta zee world.
Kallon mai wannan aikin nayi,saleema ce a ɗaya kujerar da take gefena ta saka idonta akan tv,ga kuma remote a hannunta tana jijjiga ƙafa wanda tasa ɗaya kan ɗaya.
Dan takaici ma bansan abinda zance ba,dan ko kaɗan banida ra'ayin yi mata magana a lokacin bare kuma faɗa.
Shima kansa sameer yana kallon abinda yake faruwa,amma ko ƙala bai ceba.rintse idona kawai nayi domin tunano mai ma zan mata wanda zan huce.
Sauke idon nayi a kanta wanda nasan koba madubi a gabana nasan sun sanja kala daga yamda suke.
"Ko ki mayar da tashar da takeyi ɗazu ko kuma nayimiki abinda ba kya tsammani,sannan idan na ƙirga goma baki mayar ba,shikansa tv to daga yau yah tashi a aiki bazai ƙarayiba,sannan duk wanda yaje gidannan abinda zai biyo baya bazai yimasa daɗiba.
Sanann abu na ƙarshe ina baso kike na karya ki karal ki tashi daga aikiba toh karki kuskura a zantukanki kisake sakoni a ciki,dan abin bazai yi miki kyauba"
"Heee me kike tunanin zaki iyah yimin,toh dama jira nake ki tanka dannaji ɗazu kinyi shiru,toh idan baki saniba ba'a shigo sansanin zaki a taba ɗansa a fita lafiyah,dan haka ke ba komai bace a cikin garinnan ma bare kuma gidannan,dan duk abinda yake gidannan toh ki sani mallakina ne nikaɗai,komai kika taba alfarma aka yimiki,dan haka dole nayi yanda naga dama,babu abinda zaki iyah,idan ba hakaba kuma nasa a hukuntaki kuma babu mai ƙarbar ki a hannuna koda kuma mutum zai saida gidan gandu"
Zuwa yanzu maganar na kula bada iyah ni kaɗai take ba harda shikansa uban gayyar,dan taga kissar bazata kaitaba sai ta koma gargaɗi kawai.
Murmushin gefen baki nayi,ita ana ta tunanin ƙananan sojijin da ubanta yasa suyi gadinta,wasuma a cikinsu koh training cikkeke basuda shi sune zasu iyah yimin wani abu,saidai nayi mata uxuri ai zaman yamzu aka fara zata yi abinda bazan ƙyaletan ba.
Kallon agogon falon nayi wanda yah nuna goma dadai,mayafin kai na na gyara kafin na koma ɗakina domin ɗauko takardun aikina,akwai abinda nakeson yi banida lokacinta.
Lokacin dana fito daga ɗaki na fita waje sameer yana ƙoƙarin tayar da motarsa zai fita.
Kallon kallon muka sake yi,sannan ma bai yimin magana ba,nima kuma banyi alamar zanyi masanba,yana fita da motarsa nima na fita daga gidan zuwa office ɗin ƴan vigilantee na garim porthacourt.

💎*zainnb a madubin gani*💎

Kallon zanin dayake jikina nayi wanda yayi duƙun duƙun dashi kaman an tono ni a cikin toka,dam takaici ta kuma wuyah inaga nayi kuka yafi cikin kwando daga kawoni gidan yunusa,wanda koh wata ɗayah banyiba,gashi jiyane tun waccan satin yakamata naga al'adata inaga ma cikine dani,wayyo allah na da wanne zanji haka.
Wallahi ji nakeyi kaman na gudu a rasani gabaɗaya ma.
Muryar inna laraba naji daga cikin gida kaman goge tana ƙirana,tun safe nake gindin murhu har gashi la'asar tayi amman koh gyaran ɗaki banyiba,gashi miji na maidashi sabatoto,naje anyi masa asiri bashida aiki sai cemin toh duk abinda nace kuwa.
Amsawa nayi a ƙasan maƙoshi kafin na gita dan jin menene dalilin ƙiran.
"Wai a Ina kika makalene tun d'azu nake kiranki kaman an aiki bawa garinsu"
Shiru nayi ban bata amsaba,toh mai zance bayan tagama fadanta kuma.
"Kowa yunwa yake ji kizo ki raba abincinnan mana,ko so kike ki kashemu da yunwa dama kin washemu,ga altine ma yar mijinki tazo,ƴaƴanta sai yunwa suke ji,kizo kobasu abinci dan basu saba da yunwa ba"
Takaicine ya isheni,mai take nufi kenan,ni na saba zama da yunwar ne aka fadamata kome?
Dan babu yamda na iyha haka na je gaban ƙatuwar tunkuyar na fara zuba shinkafar,jajir da itah bata da maraba da dawa,daɗinta daya ma banice da tuwon dareba,zan samu na nakwanta na huta kafin wani jiƙon kuma.
Ina gama rabon na ɗebi nawa na tafi ƙofata,dan dama nikaɗaice a ƙofar yunusa yah tafi aikin ƴan sanda an turasu garin darazo a jihar bauchi.
Burina bai wuce yah samu sugama training ɗinba yasamu aiki a wani garin na bishi,ko na huta da wannan uƙubar da ko yanzu aka barni da itah na azabtu yanda yah kamata kuwa.
Tsabar gajiyar danayi koh abincin dana shigo dashi banciba,ina kwance ina ta tunani har bacci yah ɗaukeni bansaniba.

💎*sameemah a madubin gani*💎

Ina fita bakin titi na samu mai adaidaita sahu nayi masa kwatancen office ɗin ƴan vigilantee,mun dan dade muna tafiyah kafin muka iso wajen,a bakin wajen na sauƙa na bashi ƙudinsa kafin na wuce zuwa cikin wajen.
Bansamu wani wahala ba na ganin shigaban kasancewar babu layi kaman office ɗin dana je a baya.
Wani na samu aciki ana sallamarsa da alama aikin yazo nema shima,dan ƙaramin matashine mai jini a jika,bai dade da shigaba sai gashi yah fito yana murmushi da alamun yayi nasara,nima shiga nayi na zauna a kujerar da take kallon shugaban.
Karim farko takarduna ya ƙarba,ya dade yana dubawa kafin ya dauko wata takardar a gefen sa ita ma yah duba,ɗagi kai yayi yana kallona kafin yace,
"Sameemah umar koh?"
Daga masa kai nayi alammar ehh,zare glass ɗin dayake fuskarsa yayi kafin yace,
"Saidai kiyi haƙuri,amma ma'aikata sun cika a nan bazai yiyu mu baki aikiba"
"Hmmm yallabai kenan,waye ya hana a bani aiki anan wajen,sannan menene dalilinsa"
Tun kafin yabani amsa na tafi wani tunani,irin kallon da sameer yakemin lokacin dana zo fitowa daga gidan,sannan shekaran jiyah naji kamshin wani turare a dakina wanda ba nawa bane,tabbacin wani yah shiga ɗakina kenan,wato yah plan ɗina na cigaba da aikina shiyasa ya min haka.
Dakatar da shugaban nayi tareda cemasa,
"Karka bata bakinka,nariga nasan wanene yasaka ka hanani aiki anan wajen,na gode da bani aron lokacinka"
Takarduna na ɗauka na fice daga office ɗin.
Tun daga bakin titin na danna ƙiran burgu a wayah.
Ringing biyu tayi yah amsa,duk hayaniya ma da alaamun yana kan hanyah,saidai tunda yana jina shikenan.
"Kai burgu"
"Na'am shugaba jar wuyah amarya a wajen major yah akayi ne"
"Ba surutu na ƙiraka kayimin ba,ina so kaje anguwarmu inda na bada ajiyar su bingo,kasaka minsu a manyan motoci su kawomim su garinnan,yau ba sai gobeba,so nake zuwa gobe sun iso wajena"
"Amma shu......."
Kittt nayi saurin katse wayar dan banason wani dogon surutu kuma.
Alllah allah nake gobe tayi su bingo su kariso,so nake na koma ainihin sameemah da kowa ya sani,banason hakurinnan danakeyi da kuma yin shiru akan abu,zuciyata batajin daɗin hakan,saboda bada wannan sameemah na daceba sam.
Shikuka sameer zai san yahana a bani aiki,badai zaman gidansa yakeson nayiba ,zai san yah sakani zaman gida kuwa.
Wani mashin ɗin na hau zuwa gidan,tun daga bakin ƙofar shiga falon nakejin murayar wata a falon,koh sallama banyiba na shiga.
Haɗa ido mukayi da wata wacce bazata wuce sa'a taba,daga yanda suke zance mutum zai san abokiyarta ce.
Har nakai bakin ƙofar ɗakina naji tayimin magana,hakanne yasa nadawo daga shiga ɗakin,
"Amaryar bakyaa laifi,babu maganane,sunana suhaila budurwar Ahmad abokin mijinki,koba komai zaki zo mugaisa koh"
"Toh koh shi Wanda kika ƙira da sunan saurayinnaki ban sanshiba,ko na sanshi ma ba tsayawa zanyu mu gaisa ɗinba,bare kuma ke da kike matsayin budurwarsa"
Ƙarisa maganar nayi ina kallon cikin idonta tareda da ɗaga girata kuda ɗaya dan tasan ma da gaske nakeyi,sakin baki tayi tana kallona da mamaki,bantsaya jin mai zata sake cewa ba nayi cikin ɗakina.


💎*saleema a madubin gani*💎


Tunda aka kawo sameema cikin gidana akayi kwana uku naga babu abinda yake shiga tsakanin sameer da sameema sai hankalina yah kwanta,sai kuma nafara ɗaura ɗamrar mallakewa mijina niƙaɗai ,dan na nuna mata ita bata isa ta ƙwacemin shi ba.
A falo ma duk abinda mukayi nayi zaton zata tabani ko kuma tayimin wani abu,dama na shiryah ɗaureta zan sa ayi a ɗakin horo har sai kammanninta sun canja,sai kuma ta shafawa kanta ruwan sanyi batayi komaiba,sai ma ficewa da tayi daga gidan.
Ina zaune niƙaɗai a ina bawa zuhra nono,ina kuma chatting a whatsapp sai ga suhaila tah shigo,da tayi nayi niyyar mushige daki amma sai muka yada zango a falon kawai.
Tafawa mukayi bayan na faɗa mata abinda na aikata da safen.
Muna cikin hakanne sai gata ta shigo,da alama wani waje ta je,signa suhaila tayimin nima nayi mata lokacin da sameemah ta kusa shiga ɗakinta.
Ina jin duk maganar da,sukayi da kuma amsar da sameemah ta bata,nidai bance komaiba sai gyara ƴa ta danakeyi wacce take bacci a cinyata.
Kama baki suhaila tayi tana kallona jin irin amsar da sameema ta bata.
"Ke kiji wannan matar,wannan magana haka,kaman ana bata action,uhmmm gaskiyah kin gamu da aiki daga gani,sai fah kin dage,dan ma kincemin baya kulata,amma duk da haka saifah kin dage,ba a shaidar ɗan kuturu sai yah shekara da ya tsunsa tukunna"
Murmushi nayi kawai,danni kaɗai nasan irin abinda na shuka zam aiwatar a gidannan,duk abinda zanyi na kori sameemah a gidana to zanyi,domin itah ɗin hatsarine zaman ta cikin gidan.
Hirar mu muka cigaba da suhaila kuma duk bata wuce akan sameemah bane.
Sai wajen magriba kafin suhaila ta tafi gida,lokacin sameer ya dawo daga aiki suka gaisa ma a waje.
Tare muka shigo dashi,ina kalllonsa yama kallon gefen ɗakin sameema,haushine yakamani duk da nasan ba komai ne a tsakaninsu ba,jakar hannunsa na karba tareda kamo hannunsa cikin tattausan hannuna duk dan na ɗauke hankalinsa daga tunanin ta,kallona yakeyi da idonsa da sukayi ɗan ja saboda yawan aiki.
Nima sansanyan kallo nake aika masa wanda nasan yana narkar da zuciyarsa a duk lokacin danayi masa,musamman idan yana a yanayi na buƙata.
Ɗakinsa muka shiga yah rage kayansa yah shiga banɗaki,nikuma na ajiye jakar tareda zuwa ɗauko abincin da kareematu mai abincina tayi.
Lokacin dana shigo ɗakin har yah fito daga banɗakin yah saka ƙananan kaya marasa nauyi,hada ido mukayi dashi,lokaci ɗaya na karanci duk abijda yake kwance a cikin idonsa,kirjina yabada ƙarar bugawa fatt,saboda nasan in yana wannan yanayin bana karewa da ɗadin jiki,dan sai nayi gashin jiki tukunna.
Kawar da tunanin hakan nayi a raina na cigaba da zuba masa abimcin,saƙƙowa yayi inda nake zaune daff da dani,ɗan matsawa nayi kaɗan domin bashi damar cin abincin,saidai daga fuskarsa nagane bahakanne a gabansa ba.
Ko kuma mai yah tuna sai kuma naga ya jawo plate ɗin abinci yah fara ci.
Lokacin dayah gama an ƙira sallahr magriba,dan haka alwala yayi yah tafi masallaci,yayinda nima nayi nawa ɗakin.



Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment