Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce,tun daga bakin falon na tabbatar cewa na daeo gida,hakanma farfajiyar hajiyah saleema,dan komai da gindinsa yake zaune a falon,duk da babu datti amma fah babu tsari ko kaɗan irinna na ɗakin ƴa mace.
Fitowa tayi daga ɗaki muna haɗa ido da itah,babu sannu da dawowa bare yah hanya sai ƙorafi dayah min sallama,na kashe mata wayah danayi.
Dan takaici ba tsaya yi mata wani bayani ba nayi hanyar ɗakina,ina jinta tana biye dani har sannan bata daina ƙananan maganganu ba,jin abin zai min yawa goma da ashirin yasani dakatar da itah,tareda cewa,
"Dan allah saleema ki barni na huta tukunna koma menene sai tambayeni ,amma yanzu bakya ganin daga hanya na dawo,babu sannu da dawowa bare ruwan sanyi sai aukin ƙorafi,wai yaushe zaki sanja ne?"
Jumbura daki tayi irinna sakalai kafin tace cikin muryar shagwaba,
"Haba honnnney,yanzu hakama zaka ce dan gaka ina damuwa da kai,fisabilillahi tun yaushe ka bar garinnan,sannan tun kwana uku da suka wuce yakamata ace ka dawo,amma baka dawoba sai ma kashemin waya dakayi bayan na ƙiraka,wai meyasa kake min hakane "
"Ni babu abinda nayi miki saleemah,kawai akwai abinda yasa na tsaya ne,kuma idan kikayi haƙuri inna zauna zan sanar dake,domin kema yah shafeki"
Daga haka na juyah na wuce ɗakina ina riƙe goshina,wanda nakejij kaman zai iyah darewa a kowanne lokaci.
Wanka na shiga naji ɗan dama dama,ina fitowa na samu saleema a bakim gado tana jirana,ban yi mata magana ba sai da na shiryah kafin nazo na zauna,anan na kula ashe abinci ta taho dashi,ta wannan bangarenne kawai take burgeni,dan idan na faɗamata abu tanayi,sannan kuma bata fiye yimim musuba,barta dai a shagwaba kam har da ta siyarwa.
Jawo kwanon abincin tayi tah juba,duk raina bayaso saboda na ƴan aikine,ita kuma babu dama tah dafa abinci da kanta,wannan sam ya zama abinda tah maidashi haramun a gareta.
Kaɗan naci kafin na ajiye cokalin ina kallonta,wanda tunda nafara cin abincin ta tsura min ido tana kallona,
"Uhm ......dama saleema akwai abinda nakeson baɗamiki,kar lokaci yaƙure ban faɗamikiba kice ban kyautaba"
"Uhm ina jinka honey mai yah faru ne?"
"Da farko kinsan ni mijine ke mace sannan kuma an halattamin auren mata guda huɗu idan ina da dama koh?"
"Tsaya tsaya haka,banason jin wanann bayanin gaskiyah,dan wallahi babu kishiyar dazaka yimin ana zaune kalau,nasan ma bazaka yi ba ai,dan haka a bar wannan zancen"
"Amma yah kamata ki dunga tsayawa kina jin karshe magana,dan aure ba zancen za'ayi bane an riga anyi ne,dan yanzu haka ma amaryar jibi za tare kuma samee.............."
"Karka cigaba da faɗin abinda kunnuwana bazasu iyah ciggaba da jiba sameer,me kake nufi,aure!!!,kuma ma har an daura,nan da wasu kwanaki matar zata zo ta zauna a gidana,kuma itama tah mallakeka kaman yanda nakeyi,inaaaaaa hakan bazai taba yiyuwa ba kama canja zance amma ba wannan ba ............kasan mai kake faɗa kuwa??"
"Nasan mai nake faɗa mana salee............"
Tun kafin nagama magana ta watsamim wani kallo wanda tunda nake bansan ta dashi ba ta bar ɗakin da sauri tana bugomim ƙofar ɗakim kaman zai karye.
"Yah salam"
Shine kawai abinda na faɗa,dannasan shikaɗai zai kawo min mafita akan abinda yake shirin tunkaroni.

💎*Sameemah a madubin gani*💎


Lokacin da mai lallen ta zo ma kaman bazan tashiba,da jinake wani baƙin ciki yana taruwa a cikin kirjin lokaci zuwa lokaci,samun waje tayi tah zauna ba kin katifar sameerah ta da,tana sunkuyar da kai kaman mai tsoron haɗa ido dani,ƙoƙarin katse shirun ɗakin nayi tah hanyar cewa,
"Miye sunanki?"
"Hamiddah"
"Karki yimin mai yawa,shima dan babu yanda zanyine kawai shiyasa zanyi"
Tasowa tayi tah fara haɗa kayan yin lallen,har tah gama.
Wata shawara ce tah kawo kaina cikin ƙanƙanin lokaci,aikuwa nayi shu'umin murmushi.
Bamu daɗe da farawa ba muka gama,dan cewa nayi tayimin zanen da tasan ba'ayi a lalle kaman zanen kwari da na su ƙadangare,kallona take da mamaki kafin tah fara abinda nacemata,dayake ta iyah zane kuwa,sosai hotunan ƙwarin suka fito kaman suyi magana harda kala ta saka musu,ɗaga hannun nayi ina kallon zanen yamda yah fito raɗau a hannuna,dan duk mai tsoro ƙadangare da kuma su dandoriyah to yana gani nhannu na zai fita da gudu,daɗi ne yah isheni koba komai zuciyahta tayi ɗan sanyi danayi tsiyah.
Tana gama lallen koh nace zanen tayi shiru tareda ɗan matsawa gefe,sai kallon abinda yake hannuna da kuma ƙafata takeyi.
"Ai baki gama ba,ina so kiyimin zanen maciji ya nannaɗe wuyana,ina zaki iyah?"
"Eh zan iyah anty"
"Yawwa toh yimin yayi biƙi sosaifah"
"Toh anty"
Ina gama faɗan hakan na cire rigata nabar iyah zani ɗaurin kirji,lallen da sake haɗawa kafin ta fara zanen
Wanann sai da ya ɗaukemu lokaci domin so nake ya fito kaman na gaske,aikuwa nima kaina sai da naga kyau na macijin,rai na fari tass yayi ganim abinda nake shirin aikatawa yah fara tafiyah yanda nake so.
Kuɗin aikinta na bata ta tafi,kitso kuma shagon gyara nake son zuwa saboda kawai abinda nake son aiwatarwa.


💎*Saleema a madubin gani*💎


Tun naji furucin daya fito daga bakin sameer mai kama da dafin maciji na tashi na tsaya,ji nake duniyar tana juyamin duk illahirin jikina rawa yakeyi ga kuma wani tashin hankali da baƙin ciki da suka taru a ƙirjina,numashina har sama sama yakeyi.
Ɗakina na nufah ina haɗa hanya dan ko hanyar idanuwana basa gani sosai,babu abinda yake amsa kuwwa a cikin kai na kalmar da sameer yah faɗa ta,aure aure kishiyah kishiyah.
Da ƙyar nasamu damar sakawa Zuhra riga(mai sunan mahifiyar saleemah,hajiyah Fatima)na sunkuceta sai bakin motata,shikuwa farouq bai dawo daga makaranta ba ta isilamiyya,idan yah dawo ubannasa yasan yanda zayyi dashi.
Ikon allah ne kawai yah kaini gida,sa'a ta ɗayah babu nisa duk a cikin barikin sojojinne,saboda girmansane yasaka ni ɗaukar motar dan idan na ce zanje a ƙafa toh zam iyah yin kusan wata a ganina ban ƙarisaba.
Ina kashe motar na fitah daga motar da gudu zuwa cikin gidanmu,har na kai bakin ƙofah na tuna nabar ƴata a cikin motah,da gudu na koma na ɗaukotah kafin na shiga cikin gidan.
Akan kujerar falo na dire zuhra dan ita haushinta nakeji ubanta yah shafamata,mai aikin gidan nagani zata wuce madafar abinci.
"Ke zo ki ɗauki yarinyar nan ki kula da itah sannan ki bata madara"
Zuwa tayi tah ɗauketa ni kuma na yi ɗakim mommy da gudu har ina tuntube,babu abinda nake buri sai,wanda zan samu na faɗawa mai yake faruwa,sannan kuma da wanda zai rarrasheni.
Ina shiga na faɗa kan mommy wacca take naɗe kayan ta ƙanana akan gado,kuka na rushe dashi wanda dama na daɗe ina riƙeshi,sai yamzu yah samu damar kwacewa yah fita.cikin shshshekar kuka nafaɗamata abinda yah faru.
Tana gamajin labarin tah tureni daga jikinta tareda cewa,
"Dallah ni matsa kiban waje,dan mijinki zai ƙara aurenne kike wannan kukan kaman wata sakaryah,ke kuwa kina hankali kuwa?,kai kai wallahi alhaji yajiƙa aiki daya shagwabaki,ya maida ke bakisan kinemi abu ki rasa ba,sanann ya maidake bakisan kiyi haɗaka da wani ba akan abin duniyah,saidai yanzu alhamdulillahi gwanda da yayi auren koba komai zaki koyi darasin haɗa abu da wata,kuma zaki san duniyah ba kullum abinda kake so kake samuba koh ake yi maka ba"



Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.


💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎





*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}



💎9~10💎



Matsawa nayi daga jikinta na bar ɗakin,da wanne zanji da kishiyar da akayimin koh kuma da faɗan da takemin,idan tana wani abun saikace ba itah ta haifeniba matar ubace,nidama nasan batasona kaman yanda abba yekiyimin,kullum cikin yin faɗa take da hantarata.
Kuma wallahi ban haƙuraba daddy yana dawowa zan faɗamasa,bazan bar gidan bama anan zan zauna har sai ya saketa tukunna kaman yamda ya aureta.

Ɗakina na gidan na nufah,ina kuma danna ƙiran wayar SUHAILAH,tsuka naja ganin tana ta ringing amma bata ɗaga ba sai daga baya kafin ta ƙirani.
"Sully kina ina ne wai,ina ta kiranki baki ɗauka ba,akwai matsala fah"
"Matsala kuma wace iri,banganeba mrs major,fayyacemin naji mai ake ciki"
"Hmmm ke miyema bai faruba aikawai sai kinzo,dan zancen baxai yiyuba a waya"
"Toh shikenan gani nan zuwa,dama yamzu na dawo daga makaranta,cin abincina kenan,bari nayi wanka nazo naji mai yake faruwa"
Ajiye wayar nayi bayan nagama wayah da suhaila,nasan ana jimawa zan ganta,safa da marwa na fara a ɗakin tsakanin kujerar madubi da kuma bakin gado,duk abin duniyah yah isheni,lokaci ɗaya har na rame na fitah hayyacina,dama haka mata suke ji idan za'ayimusu kishiyah?,tabbb gaskiyah abin babu daɗi,dole ne muyitah,koh ni koh itah,duk da bansan ma wacece ba.
Sai kusan magriba kafin suhaila tazo,ita kanta nasan a lokacin uzuri takemim saboda babu laifi tasha madifa tafi cikim kwando.
Itama bata wani bani shawara gamshashshiyah bah,duk daga nayi kwalliyah,na dunga jan ajina,sai kuma kar na bari tah rainani,kallon suhaila nake lokacin da take faɗan hakan,lallai bata san me ake jiba idan akayi maka kishiyah,dan taga batada mijinne bare kuma zancen yimata kishiyah,toh yaushe ma zan zauna da itah har nafara wannan shirmen na jan aji da kuma kwalliyah.
Ita kanta surayyah ganin nayi mata shiru yasa itama ta kama tura saƙonta a wayah,ni hakan ma yafimin da wanann zance nata.
Daddy yana shigowa tun kafin yah zauna na fito daga ɗakim ina haɗe fuska,kallona yayi da alamar damuwa a fuskarsa ganin yanayin dana ke ciki.
"Ƴar daddy mai yasameki haka?"
Kallon mommy nake wanda take zabgamin harara kaman idonta zai fito,hakan bai dameni ba saima ɗauke kaina danayi ina kallon inda mai sona yake wato daddy,
"Daddy inadai wai sameer ne yaƙara aure....."
Ina gama faɗin hakan hawaye ya fara zuba a idona,daman yau kam ai idon cike yake da hawaye.
Cikin razana da kaɗuwa daddy yafara magana ransa a bace,
"Aure kuma,daga aura masa ke kawai sai yahsake aure,ni naga ga mahaifiyarki nan ban sake mata abokiyar zama ba,sai shi ne zai wani yi miki kishiyah da yarintarki kawai dan ya bata miki rai"
Ina jin haka na sake rushewa da wani kukan ina ɗora kaina a kafaɗarsa.
Dan tsabar takaici dayah shaƙi mommy buɗe baki kawai tayi tana zubawa sarautar allah ido,dan kam abin yah fara bata mamaki.
"Kutt yanzu alhaji abinda zaka ce kenan,kana ganin tah baro gidanta ta dawo gida sai tijara takeyi da girmanta ,ba ƴar yayeba harda ƴaƴa biyu,da a ƙauyene ma tah kusa auren ƴarta shine kake wani rarrashinta harda ɗaure mata gindi dan kawai mijinta yah ƙara aure?,toh wallahi bazan yarda da hakanba,yau ɗinnan basai gobeba zata koma ɗakinta,idan kuwa tah kwana a gidannan akan wannan abin,toh kuwa zanyi fushi da itah"
Binta mukayi da kallo nida abban,wanda shima bai ji daɗin mommyn tace ba,saidai babu yanda zayyi tunda ta faɗi hakan toh bazata sanjaba tana nan akan bakanta.
Dadare na fara da kafafuna ina kiran daddyn,ganin hakanne yasashi ɗaga wayah ya ƙira sameer akan yazo yana son ganinsa,nikuma yah lallabani na tafi ɗaki kafin sameer ɗin yah ƙariso.


💎*Sameer a madubin gani*💎


Tun lokacin da saleemah tah bugamin ƙofar ta fitah ina jinta har tashin ƙarar motarta,wanda dama nasan sai hakan tah faru,abu ƙaramima take kaiwa ƙararsa bare kuma al'amari irin wannan.
Baccine ya ɗaukeni na wahala a wajen,dan kaina ji nake kaman zai sare gida biyu.
Sai can wajen magribane naji ƙarar buɗewar ƙofar dakinnawa,farouq ne ya shigo da kayan islamiyyah a jikinsa,kaina yah ɗale da sauri yana dariyah,nima wani sanyi naji yah jiyarci zuciyata,dan rabona da ɗannawa nayi ɗan kwana biyu,muna nan zaune sai kuma na tashi nayi masa wanka kafin najashi muka shiga madafar abinci.
Taliyar yara na yimasa,dan dama kowane yaro yana sonta,da farinciki kuwa yah karba ya nufi falo da gudu.
Nima bin bayansa nayi ina murmushi,sai surutu yakemin maganar bata fitah,wani nagane na bashi amsa wani kuma saidai kawai na kalleshi,*yara manyan gobe*
Waya tace tayi ƙara ina dubawa naga abban saleemah ne,nasan *za'a rina wai an saci zanin mahaukaciyah*
Ɗauka nayi tareda yin sallama cikin girmamawa,cewa yayi na sameshi idan anyi isha a falon sa,amsawa nayi da toh kafin na kashe wayar.
Wajen anty talatu (nanny ɗin farouq)nakaishi bayan yagama cin abincin nikuma na wuce masallaci.
Lokacin dana dawo anyi isha,farouq na dauka a motah muka nufi gidan su saleemah.
A falo nasameshi a zaune,saleemah tana gefensa idonta yayi luhu luhu,na ɗan ji tausayinta a raina amma kuma ta wani bangaren dama inaso tayi hankali,tasan ba kullum ake kwana a gadoba.
Zama nayi akan daddumar da take kasan falon tareda gaishe da alhajin. Dadai lokacinne itama hajiyah Fatima ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi,daga gani alhaji Musa bai so shigowar ta ɗakinba saidai baice komaiba.
"Yawwa sameer ina jinka,yarinyah tah daho tana kuka wai tacemim ka ƙara aure,ɗazu ka faɗamata sannan kuma amaryar jibi zata taro,wani abu saleemah tayi maka ne"
"Babu abinda tayimin,sannan abinda tah faɗa gaskiyahne,nayi aure kwana uku da suka wuce,jibi za'a kawota m"
Ina gama faɗan hakan na basu labarin nima jinayi kawai an ɗaura auren bayan an gama ɗaura na ƙannena wanda naje nasu ɗaurin auren.
Jinjina kai alhaji musa yayi kafin yace,
"Yanzu yah ake ciki kenan,gida ɗayah zaka haɗasu?"
"Eh hakan nake da niyyar yi,dan a tsarina banason yin gida biyu gaskiyah"
"Ammma.........."
Hajiyah fatima ce tayi saurin katse alhaji musa daga maganar dayake son yi tace,
"Shikenan sameer munji duk abinda kace,munayi maka fatan alkhairi allah ya tayaka riƙo ya kuma baka ikon yin adalci a tsakaninsu,yanzu kaje ka jira ta,nasaka ta ɗakko zuhrah da kuma jakarta yanzu zata fito ku koma".
Har a raina naji daɗin yanda hajiyah fatima ta taƙaita maganar,dan har raina nake yaba irin halin dattako da sanin yakamata irin na hajiyah fatima,matar ta kwanta min a rai,ganinta nake tamkar mahaifiyata.
A hanyar mu tah dawowa gida kuwa babu wanda yayi wa wani magana tsakanin nida saleemah,dan ko kalllona batayiba,idonta yana kan titi,farouq kuwa yana kulata zata zabga masa harara shima dayaga hakak sai ya cigaba da wasansa a gefe ,ni dariyah ma tabani.


💎*Sameemah a madubin gani*💎


Mutane sai taruwa akeyi ƴan ina da biki,zuwa yanzu kowa yasan alaƙata da sameer,cewa ni ba ƴar inna hajara bace riƙeni tayi,saidai babu wanda yafaɗawa kowa su waye iyayena,kowa idan yagam kwakkwafin yaga bai gano komai na sai ya haƙura.
Ina jinsu suna tah hidimarsu da mutane a cikin gida saidai koh inda nake babu wanda yake zuwa barekuma ayimin tsokana irin tah amare.
Kaman yanda na faɗa nabada ɗinki kuwa haka akayimin,wannan duk hidimar surayyah ce,dan itah kadaice take shigowa ɗakin tah gama yimin tsiyah ta fice,tun da safe burgu yah kawota akan idan aka yini tah kwana washagari a tafi kaiwani da itah,hmmm lallai aure manya,zasu san sun sakani cikin masu aure kuwa.
Riga ce jah ta yadi mai tsada,saidai anyi mata ɗikin buɗaɗɗen wuyah,sai kuma tah matse kunkumi tah zuba a kasa ,lokacin dana faɗamata yanda za'ayi rigar bata so a yi irinta ba,amma yanda na bayar dole haka za'yi ina haka na kuma na fitah da kaina na kai ɗinkin.


~~keee mai taurin kai,koyaushe kina cikin karya mana doka koh,mun ce kinuna ƙin amincewar ki akan aurennana amma kikayi biris da zancen,idan san samune ki kawo mana jinin mijinnaki ana kaiki gidan,sauranki jinin guda uku ki hau kan karagar mulkinki,wanda dama lokaci yake jira,idan kuma kika ƙi aikatawa ............

Bazan aikata ba daman,karku bata lokacinku,koh kasheni zakuyi bazanyi abinda kuke so ba sai abinda nayi niyyah,tsarinku daban nawa na daban,sannan sau nawa nake faɗa muku banason kiran ruhina da kuke batareda ixinina ba zuwa duniyar mafarki,idan har kuka cigaba da aikata hakan,toh zan samo hanyar yin abinda bakwaso kodah kuwa yah zama koni koh ku ne.~~~~~

Tashi nayi daga kan gadon ina kallom rufin ɗakin wanda nagama kwanan na na ƙarshe a cikinsa,tareda tunanin mutanen mafarkinnawa,ruwa na ɗauko a gefena na fara sha saida na shanye shi tass,natsani ƙishirwar dasuke sakani ina ji,wayonsu shine su ɗaɗe dani a duniyar mafarkin har sai na buƙaci shan jini a wajensu idan inaso naji dadai,saidai sun makaro,domin na koyi fitowa daga wajennasu koda suna so koba su so,nasan hakan bai yi musu daɗiba saidan babu yanda zasuyi ne.
Bankoma bacciba sai ƙoƙarin hada canjin wajen aiki da nakeyi,dan burina shine ina zuwa can na nemi aikina na cigaba dayi.

Washagari tun da hantsi motoci guda uku suka tsaya a ƙofar gida,ina jin dirinsu na tuno da motar alhaji bala dana ɗauko,wanda jiyah nasa burgu ya mayar masa kayarsa,dan dama banida niyyar riƙeta din din,saboda bana ra'ayin mallake abinda ba nawaba,dama na taho da itah ne dan yaji haushi.
Wanka na shiga nayi,kowa idan zan wu ce sai bina yake da kallo,kome suke kallo oho.
Saida nagama shiryawa na saka rigar dana bayar akayimin,surayyah ce ta nace sai tayimim kwalliyah,hakanne yasa na barta tayimin amma kuma baƙi yafi yawa a kwalliyar,dan jam bakimma baƙiƙƙirin aka saka hakama gira da kwalli,bataso yamda na bata kwalliyar ba saidai yazatayi dani.
Muna cikin yine saƙo yah taddani cewar baba umaru yana ƙirana,
Abinda ya tsana kenan wannan wa'azinnasu na munafurci,banda munafurci sun san fah mutum ba sajawa zayyi a sakanniba imdai har girmansa bai canja ba,kawai a damu mutum da iyayi kawai.
Lifayar kayan da ɗauka na yane jikina dashi kafin na fito zuwa dakim baba umarun,a zaune yake akam dadduma yana jan carbi,sallama nayi ciki ciki tah dole,shima murmushi kawai yasan dan dole nayi sallamr ba da san raiba.
"Toh sameemah allah ya kawoki lokaci kema zaki ɗakinki kaman sauran ƴan uwanki,ina miki fatan alkhairi allah ya zaunar daku lafiyah ya baku zuri'a dayyaba,ina yimiki nasiha da ki bi mijinki sau da kafa,sannan yi nayi bari na bari,banda musu da kuma tairin kai,dan nasanki sosai,saidai naga kaman kwannan kinyi hankali kaman ba lokacin baya ba,dan haka a zauna lafiyah ........"
Surutunsa yake tayi ina jinsa,da ni mai saurin dariya ce ma dana tuntsure da dariyah,saidai kasshh ba komai bane yake sakani dariyah,yasakani a gaba yama wani surutu kaman ya samu yar shekara biyu,hmmmm.
Tun yana maganar a marmari har yafara gajiyah,rufewa yayi da addu'a,yana ƙara cewa na zauna lafiyah,inna rabice dake gefe take ɗan matse wata ƴar ƙwallah,tabbb lalllai mutanennan nifah suna bani mamaki,tashi nayi ganin innna rabi batada niyyar tashi nayi hanyar fita daga ɗakim ina yiwa baba umaru sallama,toh mezan tsaya nayi bayan yagama surutun.
A hanyah inna rabi ta isoni da ɗan sauri,batacemim komai ba dan itah yamzu abin yah fara daina bata mamaki.
Motar da aka kawo muka nufah,sauran motocin duk an cika su sai wanda zamu shiga nida inna rabi ce tah saurah.
A gidan baya muka zauna ina tsaƙiyarta itah da wata mata,wai naji suna kanwar iyah mai kalwace.
Maganganun da baba umaru yayi minne suke dawowa cikin kwanyah tah.

Me baba yake nufi ma tukunna,ai shikenan nayi hankali saina zauna a gidan sameer lafiyah?
Inaaaa hakan bazai taba yiyuwa ba,waisu nan a barikin sojoji,ai shiyasa aka haɗani dashi ana ganin babu abinda zan iyah,sai kuwa san ya kaini cikin gidansa,dan sai yah gagareshi samun kwanciyar hankali,ballanta kuma matarsa,dama naga rainine da itah,dan haka itah zan fara gyarawa zama tukunna,sai azo ta kan mazauannan gidan,duk wanda ya taboni koh bindiga ce shi ba sojaba saina saita shi.
Natsani zama da wasu,a gida ma zaman dole nakey ,shine harda suka min aure koh,hmmm bazance yasakeni na amma zanyi masa abinda dakansa zai gaji da zama dani.
Lallai basu san wacece sameemah ba,wasan yan zu za'a fara bugawa kawai.

Ina cikin tunani na saƙar zuci bansan lokacin da muka shiga garin porthacourt ba sai gani nayi mun doshi babban barkin sojojin mai kama da gari guda a girma,ko kalle kalle banyiba saboda wanann ba shine karona na farko a ganin barinkin sojojiba,naga wanda suka fi wannan ma girma da komai, sabani sauram mutanen ƴan tafiyar musamman ma wanda dama basu taba zuwa birni kaman hakaba.
Ba laifi yana da girma sosai dan saida muka ɗanyi tafiyah kafin muka zo bangaren gidajen manyan ma'aikatan.
Buɗe murfin motah kowa yayi yah fito yana tah wawware ido dan bawa idonnasa abinci.
Wani sojane ya taho yana wani taƙama da ƙasaitah,uniform ɗinsa na kalla kawai nasan wane muƙami ne dashi.
Murmushi nayi tareda cewa,lallai akwai aiki anan wajen sosai.




Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎





*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}



💎11~12💎




Wuceshi nayi nice ma ta farkon shiga cikin gidan,saboda su sun tsayah ɗari ɗari da kuma bashi amsa,hannu yaɗaga mim akan meyasa na wuce,kallo ɗaya nayi masa dana juya kafin na wuce ciki.
Da sauri inna rabi tah taho ta riƙe hannuna tareda yimin kallon tah gaji da halina,ko a jikina sai ma ɗauke kai danayi.
Babban falone yayimana salllama yasha kayan alatu irinna ƙyalelen duniyah.
Wasu manyan matane masu kama da hajiyoyi a zaune akan kujerun ɗaya bangaren,mukuma muka zauna a wanda suke kallonsu.
Dayake kafin mu shigo inna rabi ta sakamim baƙin ƙyalle a fuskata dan haka bana ganin fuskarsu saidai maganar su kawai,tsinkayo maganar wata daga cikinsu nayi wanda take cike da gadara da kuma isa.
"Toh da farko masu kawowa amarya barkanku da zuwa,saidai ina son sanar daku cewa nan gidan saleemah ne dan ita aka zo aka samu,karkuga cewa wai dan itah tana ƴar uwar miji ta nemi yi mata iko koh gadara,toh hakan bazai faruba,dan itah kanta dukiyar da sameer yake da itah da kuma ɗaukakar da kuka ganshi da itah har kuka laƙaba masa ƴar ku,duk mallakin mahaifin saleema ne,yanzu amarya zata buɗe mana kanta mugani kafin kuma mununa mata ɗakinta,kafin sannan kuma........."
Jin maganar nayi tah isheni haka zuciyata da kunnuwana baza su iyah cigaba da jin irin wannan kalar rainin hankalin.
Saurin yaye alkyabbar nayi ina kallonta ido cikin ido,ganin ɗan razanar da tayi ne tanan kallon lallen dayake hannuna na hotunan ƙwari da majicai na baƙin lalle anyi musu ado da jan lallene yasata zare idanu,su kansu wanda suka taho tareda dani basusan mai yake jikinba sai yanzu,surayyah ce kawai ta sani,ɗauke alkyabbar nayi daga jikina gabaɗaya nayi wurgi da itah a ƙasa,hoton macijin dayake wuyanane yah fito fili,zanen kansa yana kwance akan kinrjina wanda akayiwa ɗinkin mai buɗaɗɗen wuyah.
Tun daga kan kwalliyar da take fuskata da kuma irin nau'ina lallen dayake jikina mutum zai ɗauka daga cikin duniyar ifiritai na bayyano.
Kallon saleema nakeyi wanda tayi suman tsaye,da alamun bata san waye a cikin gyalenba sai yanzu ta tabbatar da wa zatayi zaman wani abu wai shi kishi.
Mayar da kallona nayi kan wacce take feso magana sakkanni kaɗan da suka wuce,ganin kallon bazai isheta bane yasa na matsa har inda take ina ɗora ƙafa ta ɗayah mai tsinin takalmi a kan hannun kujerar da take kai,dan dama ni ban cire takalmina ba daza mu shigo.
Fuskata nakai har wajen fuskarta,dan baifi tazarar yatsa ba na bari a tsalaninmu,ɗaga girar hagun nayi tareda kanne ido ɗaya sannan nace ,
"Ke....mekika ce maimaita naji,bazanyi taƙama da abin gidannan ba?,ke wacecs toh a gidan?da har kika samu ƙwarin gwiwar fadamin hakan,toh bari kiji na faɗamiki,tun daga kan itah matar tasa da kuma shi babu wanda ya isah yah takani,barekuma wani can banzar bazara baƙo a gidannan,itah kanta wacce kikeyiwa wannan aikin wato matar gidam ta fiki sanin wacece ni,ke bakisan komai ba a kaina,dan haka ina jan kunneneki da idan goda wasa watarana kikazo gidannan kikayi zancena ,sai na cire harshe fiyattttt ma kuwa,.............dan haka yanzu zaki iyah nunamin ɗakin dazan zauna ɗinne koh kuma har yanzu baki shiryah faɗan suanan ɗakin ba?"
Tsayawa nayi na bata ɗan lokaci saboda ta samu damar jan numfashin da ta riƙe shi tun ɗazu,ga kuma gumi dayake keto mata,duk da sanyin Ac din ɗakin.
Da hannu ta ɗaga tah nunamin ɗakim da takasa cewa komai da bakinta.
Matsawa nayi daga kanta domin tasamu ta sha iska,murmushi nayi mata tareda miƙe hannuna nayi wata miƙa kaman hannuna zai balle gida biyu,juyawa nayi na kalli mutanen da muka zo dasu wanda suma sukayi tsitt suna bina da ido.
"Kuje su nuna muku ɗakin dazaku zauna dan wancan nawane,kuma bacci zanyi na huta dannagaji,idan kuma wata tazo tah tasheni hmmmm"
Jiyawa nayi nasake kallon matan da suke gefen saleema,
"Sauran kuma na tashi naji kun cigaba da watsawa wanda muka zo tare magana,wallahi ko mai gidan bai isa kwatarku a hukuncina ba,zai fi mukuma na tashi na samu kun bar gudan"
Saida na zare ido tareda haɗe fuska kafin na faɗi hakan,har na fara tafiyah na juyo na kalli surayyah wanda itama mamakinnawa takeyi,duk da tasan hakan kadanne daga halina.
"Ke kuma zo mutafi dakinnawa akwai abinda zan faɗamiki"
Da sauri tah tashi zata biyoni,inna rabi tagumi kawai tayi,ba ko gigin biyoni ba,dan yamzu itama tasan halina.
Muna shiga ta maida ƙofar ɗakin tareda cewa,
"Yanzu anty sameemah me kikayi haka kenan?ƴan uwan ogan mijinki ne fah,amma kika yi musu haka daga zuwamki"
"Toh yan uwansa ƴan uwanane,kema ba surutu na ƙiraki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment