Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels





*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


💎°•° *WASA FARIN GIRKI* °•°💎 {cigaban gidan gandu}



💎1~2💎





💎*sameemah point of view*💎

Inajin duk abinda baba umaru yake fada akan wai na maida komai ba komai ba, kuma nayi tawakkali,saidai da yasan abinda nakeji a cikin raina a lokaci da bayyi gangancin yin wannan furucinba,dan ji nake kaman na sha'keshi yah daina motsi dan haushi.
Duk da gargadin danayi masa amma bai jiba sai ma cigaba da yayi da cewar,
"Nasan Har yanzu kina jin haushi da kuma shiga yanayin damuwa saidai ina so nasanar dake cewa,hakan yah kasance a zanen kaddararki yahke,sannan ni nacika alkawarine na matata hajara dana dauka,wanda tah bani kafin tah koma ga gidan gaskiya"
Saurin juyowa nayi na kalleshi jin yace wai wasiyyar ummah tah ce da ta bashi kafin ta rasu,kenan dama abinda ta fadawa baba umaru kenan ranar da ta ce mu fita tana shirin mutuwa,wannan tambayar ni kadai nayiwa kaina amma kuma banida amsarta.
Tashi nayi domin fita a dakinnasa dan a halin yanzu bana bukatar abinda zai hadani da wani ma tukunna,dan na gano duk tsawon shekarun danayi a rayuwata a cikin duhu kai da jahilcin rashin sanin mai yake faruwa nayi ta dukka.
Dakinmu na nufah koba komai naji dadin rashin ganin mutane a gidan domim kowa yah watse bayan kwana uku da biki.
Wanka nafarayi badan nasoba dai dan yanda naji jikina yana hamami,rabona da wanka tun kwana uku da suka wuce.
Kayan inna rabi nagani a gefen nawa kayan da alamun anan take zaune kenan tunda aka daura auren,kallon dakin nakeyi wani kululun bakin ciki yana cina a zuciyah,nayi niyyar gyarashi na zauna ni kadai ashe nima so suke su fitar dani a cikin gidan.
Duk da cewa yanzu ba wannan ne a gabana ba,burina shine na san mai yake faruwa tsakanina da sameer dan yamzu nasan shidin ba jinina bane tunda aka daura min aure dashi.
Kuma na dau alwashin nima bazanyi musu yanda suke so ba matukar basu fadamin mai yake faruwa ba.
Dukkan gidaje guda ukun na amare babu wanda yayi wani doki da zuwan amaryar tasa,saboda duk abinda yake mararin zai samu daga wajen ta daren farko dama ya riga da ya karba a waje tun da dadewa,daya kuwa ma bazawara ce dan haka baya bukatar yin wani rawar kafah.
Zainab ce tah kalli yunusa wanda yah ke kokarin saka kayan aikinsa na yansanda zai fita.
"Yanzu dan tsabar rashin mutunci irinna maza,daga kawoni koh satin amarci banyiba kace min zaka fita wani aiki,kuma itama waccar uwartaka hadda cewa yau nice dayin tuwon gidannan?,,t
Duk maganar da takeyi ta rike wani dan karamin kunkuminta mai kama da muciyah tana jijjiga shi,amma yunusa bai kukataba kaman tana magana da dutsi,sai ma cigaba da gyaran takalminsa da yayi.
"Yanzu yunusa inaa magaan amma kaaman ka bawa banza ajiyata,toh wallahi tun wuri kaje ka fadamusu ba zaman yi musu tuwo nazo yiba,toh in ma tuwonne haka kawai daga zuwana koh sati banyiba har za'a dameni da nazo nayi aiki,saikace an kawomusu jaka koh?,toh wallahi bazan yiba nikam"
"Ashe kuwa kema bazaki ciba,kuma ninan da kika ganni aradun Allah yau bazan sayo miki gurasaba,dan tah jiyama saida nayi bashi na sayo,kuma tunda na rakaki kwanan uku ai yah isheki koh,dan haka koh ki dafa su baki naki,ko kuma kice bazaki dafaba ki zauan haka kalass,danni kam bazanje nace musu ke ba jaka bace,amma tunda kina ganin sudin jakunai ne basu da iyaye koh kuma suma basuyi amarcin ba sai kije ki fada musu"
Yana gama kawo nan a zancen sa yah dauki hukarsa yayi gaba kaman ba shine mai daukin auren ba kwana uku da suka wuce.
Ajiyar zuciyah zainab tasake mai cike da takaicin abinda angonnata ya fadamata,dafe hannunta tayi akan goshinta dayan kuma ta rike kunkumi,abin duniyah duk yah fara isarta tun ba aje ko ina ba.
Ganin ba sarki sai allah ne yasata fitowa daga dakinnata ta nufi sashen surukar tata domin gaisheta.
Sun daga nesa take jiyo masifarta da babbar surukarta wanda duk cikin su tafi yi mata rashin mutunci saboda halinta na sanyi da rashin magana,
"Dallah can ta shi Kuban waje,dan mijinnaki yakawo kudi sai akace kuma a baki kiyi yanda kika dama dasu,wato dan baku kuke nemowa ba kuma zaune saidai kici kusha sai kuma kashi a masai,toh bazan bada jaka biyun ba,wazobiyah (hamsin)ga tanan ki sayo masa ja da yalo(tetracycline),yasha,ba duk ku kuke jawo gudawar ba,ko ina mutum yah wice banda kukdaje da wari babu komai,duk kun cika gida da kazanta"
Daga kai tayi tana kallon zainab wanda ta iso wajen ta zuba mata idanu sai masifah rakeyi babu full stop bare kuma comma,
"Ke kuma miye kikayimin shekeke akai kaman wata wanda tasaka wandon karfe iyee"
Saurin tsugunnawa zainab tayi tana jinjina masifa irin ta,inna laraba.
"Inna Ina kwana"
Saida ta yahtsina fuska kaman bazata amsaba kafin tace,
"Lafiyah,nikuwa kawuna(yunusa),yah fadamiki zancen yau zaki dora tuwon dareko,dan in bai fadamikiba toh bari ba nanata miki,yau kece da ciga magirka,dan kowacce yarknyah idan aka aurotah toh kwana uku takeyi saikuma tashiga layin dafa abinci,dafatan kin fahimta"
Saurin daga kai zainab tayi kirjinta yana bada lugufen duka,bata tsammaci abin haka yakeba sai gashi duk masifarta da raininta ta kasa yiwa inna laraba musu,sai ma wata karkarwa da jijinta yah debi yi.........hmm muje zuwa.

Kwass kwass kwass kakejin karar takalimi mai tsini yana sakkowa daga kan beni.
Hajiyah mairoce ta sha wasu arnan kaya ga kuma sarkar gold a wuyanta,tun daga bakin kofa salma ta kafeta da ido ganin irin shigar da matar tayi da kuma itah kanta tsadar suturar.
Wannan shine kallonta na farko da hajiyah mairon,dan tunda yan gidansu suka kawota suka tafi koh wata halittar bata sake gani tah shiga sashenta ba sai mai kai mata abinci kawai,bare kuka uwa iba mijinnata rabinta dashi tun hirar dasukayi lokacin ana gobe daurin aure,sai kuma aikan da akayi mata akan maigidan yana kiranta sashen uwar gidan.
Saida tah gama jijjuyawar ta kafin tah dawo kujerar da take facing salma tah zauna,wani kallo ta ke zifanta dashi na zaki sani yarinyah,tun kafin wani a cikinsu yah yi magana sallamar su sameerah da umaruje ya jiyarci dodon kunnesu.
Ba laifi kam sameerah tayi shar da itah na kyallin amare,sai murmushi takeyi,a kasan kujera suka zauna,sameerah har wani sunne kai takeyi itah ga mai suruka.
Dauke kanta daga kallon salma tayi ta miyar kan sanyi zuviyar tata da kuma matar da suka shigo tare,
"Ina kwana mom"
"Lafiyah son yakk"
"Normal mom,yah abokiyar zamanki?"
"Hmm gata gaka ai,saika tambayeni itah,ko duk aurenne yasaka ka haka"
"Ahah kawai na tambaya ne"
Itama sameerah ganin sun gama gaisawa ne yasakata cewa,
"Ina kwana mom(uhmm a dole anji wani yah fada,duk da halin bakin cikin da salma take ciki saida taji kaman tah tuntsire da dariya)"
"Lafiyah"
Daga haka hajiyah mairo bata sake kallon inda sameerah take ba bare kuma salma wanda dama tunda suka zo wajen bata kulata ba,sai cigaba da magana da sukayi da danta.
"Lah my son nikuwa yah tafiyah Dubai dinanan ne,yakamata kaje karisa karatunka sananan idan ka dawo maganata tana nan"
"Mommy amma da sameerah zamu tafi koh,tumda wata shida zanyi acan bandawo ba"
Wani sihirtaccen dadine ya jiyarci zuciyar sameerah jin inda zasuje ita da mijinnata,har ta fara hasasowa irin rayuwar dazasuyi acan din,bazama ta yarda su dawoba idan suka tafi can,maganar hajiyah mairoce tah katseta daga hasken tunanin da takeyi zuwa na duhun bakin ciki.
"Bada it ah zaku tafiba kai kadai zakaje,so kake ka takura kanka ka kasa more jin dadinka,da budurwace ma ko kuma irin matanann na nuna wa sa'a sai ku tafi,amma banda wanda bata san komai ba kam tayi ta baka kunyah.
Sannan maganar mu na auren ku da Suhaila yana nan sannan itama ta dawo Nigeria lokacin dazaka dawo,nariga na yanke hukunci nan da sati daya zaka tafi"
Emotions guda uku ne yake yawo a cikin falon,umaruje kunyah ce ta kamashi,dan baiso mamar tasa tayu maganar auren da zayyi a wajen ba,itah kuwa sameerah tunda uwarta ta haifeta,da kuma duk irin tujarar da suke yiwa kansu a gida,bata taba jin disgawar da akayimata mai ciwo kaman wannan.
Yayinda salma a bangarenta kuwa dadi yah kaman yah kasheta jin yanda kishiyar tata take cakawa sameerah magana mai zafi.
Kowa dawowa yayi cikin hankalin lokacin ma har ummaruje yayi musu sallama yah tafi wajen abokanansa.
Suma tashi sukayi zasu tafi hajiyah mairo tah tsaida su tareda cewa,
"Bangama dakuba ai,inaso na sanar daku cewa na sallami dukkan yan aikin gidannan,daga yau kune zaku dunga yin komai na gidannan,na abincin mu da kuma na wanda ake fita dashi sadaka,ke zaki iyah tafiyah saboda ina da iko dake,ke kuma ki jira wanda yah kawoki yah tabbatar miki kiji da kunnenki,duk kuma wacce taga bazata iyaba toh yau basai gobeba zata koma gidan tsofi"
Har salma tayi niyyar juyawa tayi mata musu sai taga tamkar zakine a gabanta yake bata umarni,hakan yasa jikinta yayi sanyi tah koma ta zauna,duk da bata ce komaiba.
Itakuwa sameerah rarrashin zuciyar ta tayi ta bar sashen,zuciyarta sai bugawa takeyi tsoronta dayah kar asirin da take dan takama da shi ya karye ta,shiga uku gashi yamzu da gaske ta fara son umaruje aranta tun daren farkonsu yah kama zuciyarta.
Basu fi minti uku a zaune ba bayan tafiyar sameerah alhaji bala ya fito daga dakinsa yana gyara hannun rigarsa,wajen hajiyah mairo yaje yah zauna yana wani yake hakorah.
"Afuwan uwar gida sarautar mata,na barki a zaune kina ta jirana koh"
Saida hajiyah mairo tayi wani rausaya da kuma kallon salma ta gefen ido wacce tah zama tamkar kungi ganin koh inda take alhaji bala yayi bare kuma yayi mata magana,"anya kuma shine koh kuma wani ne daban"tah fada aranta.
"Babu komai honey kawai dai kasaka ni zamane har nakusan awa guda,nayi zaton koh kaki wankanne irin jiyah,ina shirin tashi naje na tayaka kuma sai gashi ka fitoma"
Dad'i kasheni haka alhaji bala yaji kaman an saka shi a cikin lambun soyayya.
"Ahah ahah karki damu gimbiyah mai tafiyah da ragamar rayuwata ,ina na isah nasakaki aiki bayan jiyah na saka ki,menene yake faruwa?"
"Sakonna na umarnin daka kafa gidanna nake so kasanar da matarka dan taji da kyau,karma ta daukeshi da wasa"
Kallonta alhaji yayi rai a bace kaman yaga kashi mai wari,
"Toh ma saina sake fada mata,ai duk abinda kika zartar dadai ne kawai yin biyayyane aikinta idan tanason zaman gidan"
Baki salma tasake tana kallonsu,musamman ma yanda alhaji yake wani cuccusuwa a jikin hajiya mairon,kaman wani mai shirin shan nono koh kuma mai kokarin komawa cikinta,koh kunyah basaji sai ka ce wasu yara.
Cikin dashashshiyar muryah irin ta wanda yashaki bakin cikinnan salma tace,
"Toh idan kun gama bani aikin dazanyi zan iyah tafiyah"
"Eh kina iyah tafiyah,kaima alhaji yah kamata ka tafi aiki haka,nima fita zanyi yamzu"
"Angama Ranki yadade"
Dukkansu kowa barin falon yayi farinciki kal zuciyar hajiya mairo,burinta yana cika.Kiran hajiyah laila tayi tana fada mata aiki yayi kyau sosai,dan yanzu kaff mutanen gidan itace take da iko dasu.
Inna rabice tah shigo dakin tah samu sameemah tah daga kayan aikinta tana shirin sakawa,aikuwa abinda bata sone yah faru dan kwaredede tah hada mata ganin abinda take shirin aikatawa.
"Tabdijan lallai ma kam,ina kike kokarin zuwa haka da aurenki da komai,kina da hankali kuwa ? Toh idam baki tambayi baba karamiba(sameer) ba inda zakije a gidannan,dan shike da iko dake a yanzu ha............."
"Wallahi karki sake kicigaba da cewa shike da iko dani,babi wanda ya isa yayi iko dani,nice nan nake iko da kaina,kuma zuwa aiki ba bashi ya dad'e bai bani izinin ba ina ga kuma wanda zai hanani fitah daga gidannan idan yah isa"
Duk maganar nan da takeyi saida tah jiyo tah kalli inna eabi tukunna ta fada,dan ma tasan da gaske takeyi ba karyah ba.
Saurin fita daga dakin inna rabi tayi da sauri dan gani takeyi kaman sameemah dukanta zatayi.
Cigaba tayi da shiryawarta hankali kwance har ta gama tsaff kafin tah fito daga dakin,karo suka ci da baba umaru da kuma sameer wanda shima fuskarsa babu alamun walwala a cikinta,saidai hakan bai dameta ba dan shidinma haushinsa takeji kaman tah sha'keshi.
"Yah isa haka wannan boye boyen, inna rabi tah fadamin cewa wai kin ce saikin fita,toh babu wannan zancen,indai akam abinda yah farune shekarun baya inshaallah yanzu zan sanar daku basai gobe ba,saidai daga lokacin zaki bi mijinki ku tafi wannan shine burin ummanki idan har kin dauketa da daraja kaman yanda kika fada.

*fitowar farko kenan daga littafin WASA FARIN GIRKI(cigaban gidan gandu)*
Sannan littafin zai dunga zuwa da,MADUBIN GANI (point of view),wato duk wanda aka sakawa shine zai dunga bada labarin mai yake faruwa,da abinda yake ransa da kuma abinda yake gani.

Nashiryah fah tsaff domin kayatar daku fiyaeda littafin farko. Domin saida nayi nutso kana nayi linkaya kafin na fito muku da zakinsa coii.

Amma ba'a bawa wanda bashida jaka guda a wajensa(200),dan haka saikuyi harama domin mallakar naku a hannu.

Domin samun shigaban labarin dakuma yanda zata cigaba da kayawa toh ku biyoni tahanyar biyan kudinku nairah 200 kacal,ta wannan hanyar.
Masu turowa ta asusun banki:
3131951977
Masu biya ta katin wayah kuma:
09035784150

Muna jiran isowarku domin cigaba dulmiyawa cikin cakwakiyar da take shirin kunnowa kai,ina yimuku tabbacin baku biyha kudinku a banza ba.
Domin komai kuke bukata mun tanadar muku a littafinnan.
Tun daga kan rashin mutumci, artabu, cakwakiyah, sarkakiyah, soyayya tausayi, harma da saka ku kuka,duk na shiryah.


💎Sadi-Sakhna💎_______✍🏼



*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}



💎3~4💎


Kowa samun waje yayi yah Zauna a tsakar dakin harda sameemah wanda koh kayan aikinnata bata cireba,da alamun har yanzu bata hakura da zuwa aikinba.
Numfasawa baba umaru yayi kaman bayason fadin abinda yake sirrinne,saidai dolene yah budeshi yunda bukatar hakan tah taso.



💎*Baba umaru,a Madubin Gani*💎



Shekara talatin da biyar suka wuce,lokacin ina matashin saurayi mai neman na kansa,duk da yayuna da kuma babana suna iyah kokarin su akan komai naci da sha, har ma da aure idan mutum yaso niyyar yi.
Saidai ni ban yadda da hakanba don nafison nakasance ina neman abin kaina bawai na dogara da abin wani ba.
Hakan yasa na yanke shawara inda na fara bin babbaan yayanmu mai suna ABDULLAHI,ana ce masa malam Audu,wato shine kawunku kawu audu wanda yah rasu tun kuna kanana,sanadiyyar ciwon koda.
Shikuma sana'arsa shine saida kayan fulani a garin bauchi a kasuwar wunti. Bayan wani dawowarsane nace nima zan bishi mutafi koh taimaka masa saina dunga yi,baiyi musu ba kuwa saima dadi da abin yabashi.
Lokacin da muka tafi saida nayi shekara d'aya kafin na zo gida,inda anan ne na hadu da innarku hajara tana kawowa fura daga kauyensu zuwa garin mu,da farko nasha wahalar shawo kanta saboda macece itah mai kunyah dakuma sanin yah kamata.
Lokacin da muka daidaita kanmune muka sanar da manyam suka shiga zancen,da yake aurene ba irin na yanzu ba sai an ja lokaci,wata d'aya mukayi sai gashi mun tare a dakin Da'aka yimana da kuma dan zagaye.
Zaman aminci da ganin darajar kowa mukayi har tsawon shakera biyu kafin hajara tah samu ciki,
DA take ni ba anan nake ba ina wajen Audu bansan me ake cikiba,ashe hajara wahala yake ji a wajen mahaifiyar mu kasancewar bata sonta,tafi son na auri y'ar kawarta aminyarta wato Ramatu,saidai duk abinda yake faruwa hajara tah toshe duk wata kofah da zansan abinda yake faruwa,har saida tazo haihuwa ne lokacin nazo akace bazata iyah haihuwa lafiyah ba saboda karancin jini da kuma rashin samun ishashshen abinci mai gina jiki.
Abinne yaban mamaki ganin babu abinda aka fi karfinsa ,tun daga sannan na fara zargin ba lafiyah na musamma yanda naga tah rame tayi baki,mata fara da itah amma tah koma haka.
Allah cikin ikonsa dayah dubemu sai hajara ta haifi d'anta na miji wata ranar juma'a bayan doguwar nakuda da kuma jin jiki da tayi,har masu karbar haihuwar suka ce bazata sake haihuwa ba ma saboda yanayin laushi da mahaifarta tayi.
Ranar suna aka sakawa d'a suna SAMEER,bayan an yanka masa rago.
Kasancewar ina nan nazo gidan saboda haihuwar matata,sai hajara taji dadi har tayi wankan arba'in dinta cikin walwala da kwanciyar hankali,duk da bata fadaminba amma nasan taji dadin jama danayi a tareda itah batareda na tafiba.
Tun da IYAH taji cewar hajara bazata haihuba sai zakaminta nasan na auro inna ramatu yah tashi,aikuwa tun kafin haajara tayi arba'in tashiga ta fitah saida tah kawo ramatu gidannan,duk da bana son auren amma nayi na'am da cewar hakan yana cikin kaddarata.
A zama na da ramatu babu inda na banbanta ta da matata hajara saidai sha'nin mata dakuma in sun samu daurin gindi daga wajen uwar miji,sai hakan yakara hura wutar tsiyar ramatu a cikin gidan.
Tun kafin hajara tayi arba'in ramatu da samu ciki,wanda itah bansamu damar ganin haihuwar ramatuba sai saƙon haihuwarta daya sameni kawai.
Ban tashi dawowa gidaba saida sameer yayi wata shida yayinda shikuma dan inna ramatu (manjo )yake da wata huɗu.
Aikimmu kam alhamdulillahi yana karbuwa sosai,dan yanzu shagonmu yah cika da kaya,har na samu hayar daki ɗaya wanda zan iyah tafiyah da matata daya muzauna.
Nan ma wani artabun aka buga ina na yanke shawarar yin wata shida da kowacce sai kuma tah koma wata tazo.
Bayan shekara goma muna kasuwanci sai ciwo yah kama mallam Audu inda ya barmin kasuwamcin nakeyi,saidai nima banyi wata biyu ba akayi godabara kaya suka ce ɗibemu a hankali.
Hakan yasa nayi niyyar komawa gida saboda komai yah kare,wannan zuwan da ramatu mukaje sai masifah takeyi wai an koma yin abinci marar daɗi,nida jinta kawai nakeyi dan banida amsar dazan bata a lokacin.
Da muka isa gidanma wani tashin hankalinne yasameni, domin a kwance na samu hajara a ɗakinta rai a hannun allah,wai laulayin ciki takeyi tun wata uku da tafiyarmu,gashi bayason abinci barkatai sai wanda tah zaba tukunna.
Nan nafara jinyarta gashi kuɗin hannuna bashida yawa sosai,ana cikin hakanne wata hajiyah ta turo saƙo akam idan inaso naje zata bani aiki na gadi a gidansu,kuma ta yaba da hankalina saboda ina yawan sayar mata da kaya,mun saba a wajen cinikayyah.
Abinda nayi tunani shine aikin gadi sai an zauna a gidan,sannan indai za'a zauna toh fah wata rana za'a bata,idan kuwa na kuskura na tafi da ramatu toh a ranar za'a koromu,sannan kuma bazan iyah tafiyah na bar hajara a wannan halin ba,kuma halin da take ciki tana bujatar taimako sosai.
Hakan yasa na yanke shawara babu wanda yahsani na cewa ramatu aikin dako zan tafi yi a wani ƙauye,kuma bazan iyah tafiyah da hajara ba bata da lafiyah,tsalle tayi ta dire akan bazata je wajen wahala ba saidai na tafi da hajara kk kuka nasan yanda zanyi,lokacin kuwa ta yaye ƴarta sameerah.
Baƙaramin daɗi najiba dana samu nakashe wannan wutar.
A ranar na fara yimana shirye shiryen kayan ita dai hajara kallona kawai takeyi,dan nasan idan zanyi shekara ina abu indai ba faɗamata nayiba bazata tambayeni ba.
Ranar tafiyarne na kaiwa iyah kayan sameer saboda yana zuwa makaranta shi,kuma ma yayi girma a tafi dashi gashi bamusan wajen ba muma tukunna.
Mun daɗe muna tafiyah a mota sai gamu a garin bauchin yakubu,hajara kam duk tah galabaita saboda jijjigar mota ,gashi dama koba mota amai takeyi inaga ta samu dalili.
Mai adaidaitah sahu muka ɗauka zuwa anguwar rail way inda tayi mana kwatancen gidan.
Shima kansa mai adaidaitan baisha wahala ba saboda gidan ba a lungu yake ba,kan hanyane inda kowa zai gane.
Kuɗin na bashi kafin na ranƙwafo da hajara zuwa jikina muka fitah zuwa bakin gidan.
Duba takardar ta take hannuna nakeyi sannan kuma ina sake duba gidan,"anya kuwa shine?" nafaɗa a raina,dan gaskiyah giraman gidan bayyi kama da wanda za'a gayyaci kamanni cikinsaba.
Ganin ba sarki sai allah ga kuma matata tana bukatar taimako ne yasa kawai nayi shahada da tunkari kofar gidan,saboda mun riga mun zo kuma ai babu batu komawa.
Wasu inyamuraine masu kayan sojoji suka buɗe mana kofar gidan,saboda tsabar tsoro bansan lokacin dana mika masa takardar hannu na ba,saboda dama tace idan nazo nabawa ɗayah daga cikinsu,zasu barni na shiga.
Hakan kuwa akayi ina mika masa yabani hanya wuce ina mamakin toh wane irin aiki kuma zanyi,danni a iyah tunanin gadi nakawo da tace zata ban aiki a cikin gida kuka zan iyah zuwa da iyalina,toh kodai ba nan bane,dan nan kam suna da mai gadi,wanda koh kare bazai nuna masa gadin ba ,dan ga ganinsa a fuska ma zaka tantance.
Nidai ban sare ba muka cigaba da tafiya a hankali saboda yanayin tafiyar hajara da bata sauri saboda rashin karfin jiki.
A bakin wata kofah muka tsaya saidai itah karamace amma dai tafi kofar shiga ɗaki girma,da wata yarinyah muka,haɗu tah yimana iso zuwa ga matar gidan.
Shiga mukayi tareda itah bayan tah dawo tacemana mu shiga.
Tabbbb danƙari wani kayan sai amale aradu,ai ina arba da inda aka shigo damu na saddaƙar da cewa ba'a Nigeria nake ba kawai,dan wajen badai ado ba kam.
A ƙasan wajen muka samu waje muka zauna inda mai aikin tacemana mu tsaya.
Bata daɗe ba kuwa sai gata ta shigo bakaman sauran masu kuɗiba da zasu iyah barka a zaune har awa guda.
Sallama tayi mana tareda nuna mana kujera akan mu zauna,nidai duk hankalina bai kwanta da zaman kujerar ba saboda kar mu bata musu,amma kasancewar ƙasan da sanyi ga kuma yananyin jikin hajara sai muka koma kan kujerar.
Har ta gyara zama zata fara magana sai kuma tayi saurin kiran wata a cikin gidan,saida ta bayyana naga ashe wacce ta rakomu ce,
"Yawwa blessing kawo musu abin sha da abinci mana,kinga har na fara cikasu da surutu kafin na bansu wani abu(juyar da kanta zuwa ga inda muke sannan tah cigaba da cewa).
Afuwan malam umaru,naga mai ɗakinnka ma kaman batajin daɗi sainaga kaman ma ƙaruwa zamu samu,yamzudai bari na saka akaiku ɗakin dazaku zauna kuci abinci ku huta daga baya sai muyi magana koh?"
"Toh shikennan babu matsala duk yanda kika ce ranki yah daɗe"
"Kacemin madam kawai,itah kuwa tah kirani da sunana Maryam,allah bamu ikon zama na fahimatar juna"
Daga haka ta tashi tayi hanyar wan beni,itah kuwa hajara tun gaisawa da sukayi bata

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment