Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da duk ruwan maniyyinta ba. Ta janye su a jikinta ta maidasu ta rungume su a gefe da gefen hannunta.



Littafin kuɗine
Regular 300₦ Vip 500₦ special 1000₦
Katin MTN ko ta nan bank ɗin 7782217014 ,Mohammed Hassana , Fcmb bank

Shaidar biya ta wannan Number 09065990265
_*YARON GIDANA*_💻
(My house boy)
3️⃣

الاسباب والعلاج تكون بين المرء و الصورة...هاذا حب جميل💝👍🏻😂

_Healthy Glowing face_
Zaki samu abubuwa kamar haka
•Madara
•Auduga
•Cow ghee (Man shanu)

Zaki zuba madarar ki a mazubi mai kyau ,sai ki ringa dangwalar madarar kina goge fuskarki dashi (cleansing) sai ki barshi yayi kmr 30 mns kafin kije ki wanke sai ki shafa wannan man shanun ki kwana dashi a fuskarki

Rxn a sati ɗaya zaki zama abun kwatance ,ki gwada ƴar uwa
NB masu oily face (maiƙon fuska) da masu pimples kar su shafa man shanu zai ƙara worsen ƙurajen fuskar.
__________________________
Washekari

Simple kwalliya Kausar tayi but sexy ,Jan riga ce mai yalwa ta saka da hoton ƙatoton ƙwallo a gaban rigar ,an masa kwalliyar fari da blue . Sai ta saka wando blue jeans ,da takalmi cambas ,shima anyi shi da ƙyallen blue jeans ɗin sai fararen igiyoyi .
Saida ta gyara yalwataccen gashinta ta kama da red ribbon sannan ta ɗaura farar Abaya mai yalwan duwatsu ta yane gashin kanta da mayafin Abayan ta shiga sport car ɗin ta ta wuce wajen aikinta .

Tunda ta shigo companyn El'ameen ke kallon ta ta glasses ɗin offices ɗin su ,tayi masa kyau kamar cartoon kuma sosai kwalliyarta ya dace da motarta ,haka kewayyiyar fuskarta da tulin gashinta da ta tara ta baya ya ɓoye shekarunta ya maidata ɗanya sharaf kamar ƴar shekaru 24 .
har ta kulle motarta ta hauro saman office ɗin ta ita yake kallo . Amma yina ganinta ya maza ya wani basar ya fara shafa laptop ɗin dake gabansa ,hakan ba ƙaramar ƙular da ita yayi ba

“Baka iya gaisuwa ba ko?”

Yi yayi tamkar a lokacin ya ganta “Good morning”

Banza tayi masa ta wuce cikin office ɗin ta .

Guntse dariya yayi ,shidai masifarta na burgesa wai ita lalai dole sai ta nuna masa ita ɗin fa gaba dashi take.

Saida ya bari ta shiga da kusan minti talatin sannan ya shigo ,kamar yanda ta basa umurnin tsayawa jiya hakan yasa yauma bai gigin zama a kujerun ba kawai ya tsaya a tsayen .

Ya ajiye mata tulin takardun da ta basa na jiya sannan ya ɗaura mata I_pad tablet ɗin da ya adana ayyukan da yayi aciki , a saman takardun.

Kallonsa tayi ta ballara masa harara sannan ta ɗauka ta fara duba zanen da ya firfitar a cikin tablet ɗin ,sosai sunyi mata kyau fiye da tunaninta .

Ɗagowa tayi ta kallesa bayan duk ta gama ganin ayyukan

Muɗuɗɗuke fuska tayi ta fara tsiyan ƙarfin hali

“Wani shirmen kenan wannan?” a mamakance ya ɗago yina kallonta .
kana ta cigaba“See, wannan shirmen da kayi sam baiyi daidai da abinda na baka a cikin script ɗina ba ,don haka kwashi tsiyarka ka tafi ,I can't present this trash to the company”

Tunda yake ba'a taɓa ƙona masa rai irin na yau ba ,duk kashe darensa da yayi don yaga yai aiki mai kyau tukuincin zagi dama zai samu?

Lumshe idonsa yayi ya lanƙwashe hannuwarsa a ƙirjinsa ba tareda ya motsa ba

Kausar kam janyo mouse ɗin jikin desk top computer ɗin ta tayi ta cigaba da scrolling new project ɗin tallace tallacen da zasu gudanar a satin nan a yanar gizo.

Jin shiru bai motsa ba ga inuwar mutum a saman kanta yasa ta ɗago ,shiɗin ne dai a tsaye,satan kallonsa tayi taga yanda yayi muɗuɗi da rai😡. Rasss ! taji gabanta ya faɗi

Sai kuma cikin tsiwa tace “wai da magana ne?”

“Uhm mamaki nake ta yanda zan iya wannan creative ɗin upheaded (Da kai)idan har ban duba format ɗin da kika bani ba”

Matse baki 😕tayi ta soma juyawa akan kujeran da take kai cikeda mulki ,kafin ta dawo ta dafa table ɗin da take kai tana kallonsa

“Mr. El’amin wahalar da kasha wajen yin creation ɗin ka ba shine damuwa na ba , efficiency ɗin aikin Ni shi nakeso don haka ko ka koma office ɗin ka ka sauya aikin nan ko dai ka tashin mun akai kar ka samun headache”

Ɗaukan I_pad ɗin yayi ya buɗe ƙofar ya fice a hankali jikinsa a mace .

Kallo ɗaya ta ma bayansa taja tsaki ta cigaba da aikinta akan computer.

Wayarta ne ya shiga ɓurarin neman agaji. Kallo ɗaya tayima wayar kawai ta washe baki ,ta danna wajen ɗaukan ta kara wayar a kunne

“Da girman kujeran ki giwan Gomna da kanta”

“ƙawata ƙawata ... To ya kike Abuja babes?"

Caɓe baki Kausar tayi “Gamunan muna maleji da rayuwar ,Affah kuna wata ƙasar ko ana ɗan chilawa a nigeriar”

“Ke dai ki share rayuwar so boring Mijina yina Cairo yaje amsar magani ,Ni yanzu haka ma ina Abj ɗin”

“Are You serious ? Bana son ƙarya ƙawata”

“Bana maki ƙarya wallahi nazo wani program ko zamu haɗu a Aso guest inn ƙarfe 7pm nasan lokacin kinada time”

Shiru Kausar tayi ,tana tunanin yanda iyayenta zasu barta ta fita bayan magrib .
Jin tayi shiru yasa ta fara tunanin rejecting don haka da sauri tace “Meye marabar maitama da Asokoro? Don Allah kizo” jan ajiyar numfashi tayi

“Ƙawata ina tsoron driving da dare me yasa ke bazakizo gida ba sai ma ku gaisa da momy”

“Nace maki taro akeyi banason in zauna Ni 1 don Allah kizo... Kuma driving ai ke kika so ma kanki yanda kike hot ɗin nan yaci kinada driver ko kuma companynku ta baki driver”

“Shikenan zan zo”
Godiya Raudha tayi ta mata kafin ta kashe wayar .
A hankali Kausar ta ɗaura wayarta a saman leɓenta tana tunanin maganarsu na ƙarshe da Raudha kan maganar driver ,Sam Bata son drivern gidansu yina tuƙata kamar wata tsohuwa dole ta nema yaron ta mai mata hidima.


*****
Karin maganar bahaushe
‘Duk yaron da yace uwarsa baza ta rintsa ba,shima kuwa ba zai barcin ba’

Abinda ya faru da Kausar yau kenan taƙi approving aikin El'ameen gashi ana jiran Advert ɗin a yau ga El’ameen yaje office ya ajiye aiki yaƙi gyarawa .
Har bayan Asr suna office sai azaban kira take sha daga wajen na sama da ita ,itakuma girman kai ya hanata kiran El’ameen tace in ya Gama gyare²n ya kawo.

Don haka cikin takaici ta fara gudanar da aikin da ta baiwa El'ameen yayi da kanta

6.30pm⏱️

Kausar ta gaji tulus don haka ta ma sakko daga kan table ɗin office ɗin ta koma ƙasan carpet da tarin takardun zanen da su computer ɗin da take fitar da Axel ɗin aikin a ciki ,ga drinks da ruwan da take sipping lokaci bayan lokaci ,ba abunda take buri sai taga ta gama aikin da takeyi kafin a kira sallar magriba bata son tai disappointing company da rashin kawo aiki akan lokaci.

Tuni ta cire Abayan saman kayanta ta cire veil ɗin da ta rufe gashinta dashi ta ajiye su a gefe yanda kasan tana gida ,sam bata expecting shigowar kowa office ɗin ta a wannan lokacin ,tana zaune daga ita sai kyawawan riga da wandon jikinta iskar fanka na karkaɗa gashin kanta da ya gaji da shan gyara . Batayi aune ba taji an turo ƙofar office ɗin an shigo .

Ɗauke wuta yayi ya manne jikinsa da ƙofar office ɗin shi bai shiga ba shi bai fita ba gashi ya kasa ɗauke idonsa a kanta .

Kausar ta firgita matuka ganinsa a kanta ba tareda tana cikin shiri ba,da sauri ta yayimo mayafin Abayan ta rufe gashinta ,sannan ta waiga ta kallesa yina ganin hakan yayi sauri ya ɗauke kai .

Ballara masa harara tayi cikin tsiwa ta fara fada “Meye na shigo mun office ba excuse ”

Lumshe sexy eyes ɗinsa da gazar gazar ɗin lashes sukai masa rumfa yayi

“I’m sorry ma,to check on you ne, sannan In nema izinin tafiya gida kowa ya watse a companyn saura mu kaɗai”

Wani maƙoƙon takaicine ya tokare mata a maƙoshi kawai sai ga hawaye ya fara bulbulo mata a ido

Cikin Muryar shagwaɓaɓɓun mata ta fara masa magana wai ita a dole tana masa faɗa ne cikin hawaye “Baka iya koman ka ba Alamin ,ka ɓata mun tarikhin aikina saboda zuwanka cikin rayuwar office ɗina ogannina sun samu incompitency ta wajena bayan i was totally innocent...Sai da kaga duk sun watse ban gama compiling result ɗinba ka wani zo mun zagwai zagwai kamar bush man,wai kana tsarona ne tun ɗazu...”

Gabaɗaya ta gama kashe masa jiki da yanda take magana ɗigon hawayenta jinsa yake kamar ruwan dalma ake kwarara masa a zuciya , shagwaɓaɓɓiyar muryarta lula sa yakeyi a wani duniya da bai taɓa riskar kansa a ciki ba,don haka kamar wawa yake Binta da ido ba abunda yanzu yakeso illah ya kamota ya rungumeta yasa halshe ya lashe mata hawayen da suke gangaro mata a fuska sannan ya kama kunnenta ya raɗa mata kalmar ‘Ta huta komai ya daidaita’

Bai ankara ba yaji ta wullo masa handkerchief ɗin ta aikuwa ya saukar masa a ƙirji .

Gigif yayi kamar wanda ya farka daga barci ,da sauri ya ƙanƙame handk ɗin a cikin ƙirjinsa yinajin kamar ita ya rungume ƙamshin turaren ta na ƙarasa haifar masa da kasala.

Cikin masifa tace “Am I not talking to being?Wai ko ba da mutum nake magana bane?”

Kallonta yayi da mayatattun idanuwarsa da basa buɗewa duka “Yes ma!”

Wani ƙululun baƙin ciki yazo mata wuya da sauri ta dafa kai “Owoooooo OMG ,Mr. young man aikin nan da aka baka yafi ƙarfinka don haka zan sa a kawo mun mutumin da ya Fika cancanta ,amma zuwa yanzu bazan Barka ka tafi empty handed ba ,zan baka damarka na ƙarshe na zama YARON GIDA NAH ”

Ido ya dildilo waje “Ma??? I'm not comprehending?”

Cikin tsawa tace “Kunne nawa gareka? Cewa nayi na koreka a aikin kamfani na ,yanzu zaka koma gidana ka koma tuƙani idan zani aiki ko anguwa,idan kuma haka ɗin shima bai maka ba,kwashi tsumman rayuwarka ka bar mun office ɗina”

Yanda tayi magana kamar boss lady yayi matuƙar basa dariya ,amma saboda kar ya ƙara ƙular da ita yasa yace “Ah wane Ni ince banaso ,bayan kin taimakeni nabar zaman banza! A hakan ma Ni ke da godiya godiya nike gimbiyata”

Miƙa hannu tayi ta ɗauko makullin motarta ta wulla masa a kusa da ƙafarta
Sannan cikin gadara tace “ya kamata ka gode mun with outmost humble Ni ba tsarar ka bace da zaka wani cemun gimbiyarka ........So get to work”

Duƙawa yayi ya ɗauka makullin ya haɗa da handk ɗin hannunsa yina shafasu ,suna ƙara sa masa jin Wani abu a kanta.

Saida ta fara hada tarkacenta duk yina tsaye bai motsa ba sannan ta ɗago ta kallesa “Young man meke damun ƙwaƙwalwarka?”

“Hajiya me nayi kuma?”

Riƙe ƙugu tayi tana hura hanci “Kana kallon boss ɗinka tana aiki kai kuma kana tsaye ,meye amfanin ka?”

“Sorry ma!” sululu yake tafiya kamar mara ƙashi a jiki ya duƙa a hankali yana haɗe takardun da ta bari dasu laptop ɗin ta waje guda . Tsaki taja

“Ni na fika zama mai mataccen zuciya , dallah ji yanda kake aiki salaala kamar ba mace ,tsaf saina wartsakar dakai...amma dayike rashin ɗa'a ne ai kasan ka shigo ma mutum office ba sallama bare ɗaukan izini”

Haka tana ta sababi har ta maida igiyoyin takalminta ta ɗaura abayanta ta fita bakin ƙofar office ɗin tana jiransa har ya gama haɗo kayan da sai tayi mayawa biyu zata gama kaisu mota shikuwa duk ya haɗa su a lokaci ɗaya ya riƙe da hannu ɗaya ,ya kulle mata office ɗin ya bi bayanta ,itakuma sai karairaya take tana tafiya a dole ga boss . Shikuwa hakan ba ƙaramar burgesa yayi ba ,dama zasu dawwama a haka har ƙarshen numfashinsa fa.....

A baya ya ajiye mata kayan taje owners corner ta hakimce shi kuma ya je wajen driver ya fara tuƙata ,a ransa yana cewa komai nata mai kyau ne sannan tsafta a jininta yake ta ƙara samun kaso mai girma a zuciyata.

“Hajiya dama Inaso don Allah in roƙe ki wani Alfarma!” Alamin ya tuntuɓeta da maganar idonsa na kallon titi

“Ina jinka. Allah yasa ba cewa zakayi shima aikin tuƙin na baka jidali ba don na ga yin komai kakeyi kamar wani ajebo ,nan kuwa ajekwali ne” wani ƙayataccen murmushi ya saki ,tana kallonsa ta mirror ya ɗan taune jajayen leɓensa da ya fi komai fari a fuskarsa kamar mai shafa masu pink ɗin jan baki. Sannan ya lumshe lumsassun idonsa ya buɗe su a hankali kamar mai zooming wani abu.

Tsikar jikinta ne taji ya tashin mata yarrrrr! a ranta tace yaron nan bala'i kyakyawane anya idan na ringa tafiya dashi bazai ringa spoiling mun market ba kuwa? Duk inda mukaje ya zama shi ake kallo ba Ni mace ba?
A sama taji yana bata amsa

“Ehhh ba maganar driving zanyi ba ,dama zan roƙeki ne don Allah ki daina sa wainnan kayan kina fitowa dasu waje ”

A ranta tace ga murya kamar tashin sarewa, amma a sarari sai cewa tayi

“Sannu ɗan bani na iya ,ko zan iya sanin dalili? ”

“Kawai naji kamar ina kishin haka ne”

“Kai😩🙄 bakada kunya ? Ni zakace kana kishi ,to ka ɗinko mun hijabai sai In dinga sawa ...mtsewww”

Murmushi ya sake yi a ranta tace banza gashi baya fushi ,tana ganin ya ɗaga baki zai sake magana ta maza ta dakatar dashi da hannu ✋

“Heyyy ya isa ,na gaji dajin gwalangwalasonka,ga kwanan layin namu nan” ta nuna masa hanyar shiga maitama phase 1.



Kunajin daɗin labarin???🙊🐱
Nasan Amsoshinku haka ne😘😍👍🏻👍🏻😂


To a ƙarfafa mun gwuiwa wajen siyan littafin nan tuni masu manufa sun fara siya
Katin mtn ta wannan Number
09065990265 ko ta wannan asusun bankin
7782217014 , Mohammed Hassana,Fcmb bank.




Enjoy your day😘💃
_*YARON GIDANA*_💻
(My house boy)
4️⃣

الاسباب والعلاج تكون بين المرء و الصورة...هاذا حب جميل💝😂👍🏻
__________________________
Kausar suna dab da isa gida sai ga wayar Raudha.
Kamar bazata ɗaga ba ,kuma ko mai ta tuna oho takai hannu ta latsa green ɗin wajen ɗauka gamida sa maganar kausar ɗin a speaker yanda ba sai ta kanga wayar a kunnenta ba zataji .

“Hello sisto” ƙarar tashin kiɗa kawai kakeji yina fita ta wayar sai hayaniyar mata ,dagaji dai ana holewa .

“Hello Raudha can You hear me? Kina jina kuwa?”

Cikin karaɗin murna tace “Kai babe you're missing wallahi ”

Caɓe baki tayi “Hmm I guess I do ”
“matsalarki miskilanci Kausar ,yanzu bazaki iya tambayata dalilin da yasa nace kin yi rashi ba?”

“Kawai ki faɗa ƙawata ,basai kin wahalar dani ba da yawan tambaya ”

“To Yanzu dai kina ina kiyi sauri ki ƙaraso Plz an gayyato mawaƙinki fa,crush ɗinnan namu sanda muna schl😂wlh yanzu haka shine on the stage ”

Komawa tayi ta kwantar da bayanta jikin seat din motar ,ta lumshe ido da wayar a hannunta ita yanzu duk shirmen nan ya fita a ranta su da sukai succeeding a rayuwa sune suke takan wani leasure.
,shikuwa El’ameen duk idanuwarsa na kanta ,ta mirror.


“Babe I'm tired.Yanzu nake hanyar komawa na gida daga office .So, Bazan samu zuwa ba sorry”

Lallaɓata ta farayi Amma Kausar ta botsare lallai bazata ba ,sosai ran Raudha ya ɓaci ,saboda ta gama yinma ƙawayenta kuri birthday babe na hanya

“shikenan in kin sauya Ra'ayi kinsan inda muke ” ɓit ta kashe wayar cikin ɓacin rai.
Kausar kam caɓe baki tayi "Banga ubanda zai sani zuwa wani party ba ,kin dade bakiyi fushiba becouse of your silly selfishness ,Ni in kashe kaina da gajiya ai bazai yuwu ba”

El’ameen yaji daɗin lafazinta kuma ta burgesa ,yinason matan da guguwar zamani da zugin ƙawaye basa tasiri a kansu,don haka tsilin ya tsoma mata baki .

“Da kyau ashe kinada hankali,sam zuwa irin wajen nan bai dace da Addininmu da tarbiyyar Hausa/Fulani ba ,inma banda shirme kuna mata kuna rawa da waƙa da magriba ɗin nan daidai lokacin da sheɗanu suke saukowa ,shi kansa party ɗin me ya daɗa ,in wani abun murna ne ya sameka sai kayi walima ka bada abinci sadaka ,sai Allah ya yi Alfahari dakai in mun tuna ayar nan da take cewa ‘La'in shakartum la axidannakum’...”

“Hey mr. Man wai wanene kake ma wa’azi? Wai Ni ? Shekaranka nawa? Ashirin da takwas ,a haihuwar awakai na kusa haifarka ,so sai naje partyn nan wallahi kuma kaine nan zaka kaini juya kan mota ,ka wuce dani Aso guess inn”

Wangale baki yayi “Hajiya ɗaukan gaskiya ba ruwansa da ya fito daga wajen ƙaramin yaro ,Plz karmuje,wajancan gayyar Iblis ne kinji antyna ”

“Innalillahi wainnailaihir rajiun...Kai wai ka manta da wacce kake magana ne? I'm your boss ka mun shiru ,can da munafurcin ustazancinka duk munsan irinku wa'inda in kunga masu kudi suna facaka da Naira sai ku fara masu baƙin ciki a fake da ƙalallahu ƙalar rasul ,bayan kuna samun kudin atimes ƙara'in da kukeyi yina fin namu...so bana son jin bakinka”

“Allah ya baki haƙuri ma!” ya karya kan motar zuwa inda ta umurcesa
Banza tayi masa ta danna Number mamanta tana kiranta a waya don neman izinin zuwa inda zataje.

****
7.15 na dare suka isa gaban wajen ,don haka Kausar ta kira Raudhat a waya

Da ɗan fushi a Muryar Raudha tace “Lafiya kuma”

“kaina bisa wuya giwar gwamna da girman kujeranki ,badai anyi fushi dani ba”

“No really”

“To gani a bakin wajen ina cikin sport car Yellow colour Amma gaskiya banyi kwalliya ba tun wankan safe ma,sai kisan yanda zakiyi dani”

Wani ihu tayi ta waya da yasa Kausar cire wayar a kunnenta da sauri tana rimtse ido .

“Gani nan zuwa”

Kashe wayar tayi tana murmushi itama ,El'ameen baice komai ba ya buɗe motar zai fita

“To ɗan ƙauye ina zaka daga zuwa ?”

“Zanje sallah”

“Karka fita ka jira ƙawata tazo tukuna mayb zaka kaimu near by boutique siyan kaya”

“Kiyi hakuri babu biyayya wajen saɓa ma mahallici zanje in sallah kar isha ya shiga kema ina baki shawara kiyi sallah kafin ki shiga wancan wajen” a dake yayi mata magana kamar wani ubanta ,ta kada baki zatayi masa bala’i sai ga Raudha da tawagar ƙawayenta sun dumfarosu ,tarrr ta ganesu a hasken futullun da ya haskaka ko'ina .

Da gudu ta ɓalle murfin motar ta fice tana ihuun jin daɗin ganinsu suma suna ihu, haka suka rungume juna kamar ba manya ba ,kafin suka fara mata,feshin shine shine a jiki suna cewa _Happy birthday Happy birthday_ Itakuwa sai gudu take tana kakkare feshin abun a jikinta suna Binta a karce kamar ƙananan yara.
wannan ya tuno mata da sanda suke makaranta in ɗayarsu na birthday a hostel kafin a yanka cake da safe ruwa ake dinga cikowa a bokiti ana watsa mata a jiki sai an jika ma mutum daki jagwab da ruwa .

lallai shine shine ɗin nan yayi reflecting mata watsa ruwan baya .

Haka suka janye hannunta suka shige da ita ɗakin taron.

El’ameen folding Hannunsa yai a ƙirji yina kallon bidiri,ashe dama mata duk girmansu yarane? Jibi yanda manya manyansu dasu suke aikin yara?

Program an cigaba on progress ,kausar,taji daɗin karan da ƙawayenta sukayi mata ,haka suka ɓincine hancin shamfen aka fara circulating ɗin sa da sauran snacks da drinks masu tsadar gaske .

Kasancewar Kausar itace uwar gayya don haka ita ta fara kai glass cup ɗin drinks ɗin bakinta,bayan sun haɗe glass cups ɗin dukkansu waje guda kowa ya daga sama... Shan ruwa tai ma drinks din ,saidai duk wayewar ta da tasowarta a gidan kudi bata taɓa ɗanɗanan irin wannan drink ɗin ba,mamakine ya kamata ,ta ɗan tsaida idonta akan glass cup ɗin da ta kusa shanyewa sannan ta waiga ta kalli Raudha

“Wani kalar drinks ne wannan?” dariya Raudha ta fashe dashi “Hehehe haba kamar ba babbar yarinya ba ,kike tambayata wannan kalar drink ɗin”

“To ai ban sanshi ba ,sam baimun kama da irin wanda na saba sha ba a sauran occasions da nike zuwa”

“Yes taron ƙananan kai kike zuwa nan na manyan kaine Bama shan drinks saidai stars”

Wangale ido tayi “Kai meye star kuma?”
Yanda tayi maganar a tsorace shi ya baiwa Raudha mamaki

“Haba Kausar wani star kika sani bayan wine”

Zumbur Kausar ta miƙe “Raudha kina nufin wai giya kuka bani nasha?.... Innalillahi wainnailaihir rajiun”

“mtsew to meye a ciki dallah ki saki jikinki wannan mai tsadar ne ko kwalban kikasha bazai bugar dake ba ,saidai kiyi ta barci”

Tauuuu! ta ɗauke ta da wani lafiyayyen mari a hanci aikuwa da gudu jini ya tsinke ya fara zuba ,dafe hancinta tayi ta shafa hannunta “Ni kika fasa ma hanci kausar”

“Na mareki kika sake wani magana ma dukan tsiya zan maki a wajen nan banza lalatacciya Allah ya isa da kika gayyatoni wajen nan” cacan baki suka somayi ,a take wajen ya hargitse,Shugabar mata tayi tayi su bari abun kamar ana zuba ma wuta fetur ,ganin haka kawai akayi calling off din taron ,don rirriƙe Kausar akeyi tana harin dukan Raudha...
Da kyar aka ƙwace Raudha akayi wani ɗaki da ita . Itakuma ganin hakan Kausar ta miƙe tayi hanyar waje itama ,tuni ta soma tangaɗi alamar giya ta fara mata aiki.

Al'ameen yina waje yaga mata ana fito dasu a rirriƙe suna layi ,waje fa ya soma zama haja haja irin na bariki dai ,a rude ya tunkari ƙofar wajen don yasan ko menene ake aikatawa a ciki to ba Alkhairi bane kuma


Yazo daidai bakin ƙofa ita kuma ta turo ƙofar zata fito ,cikin maye ta kallesa Idanuwarta a shanye kamar mai jin barci
“Muje ka kaini gida”

A tsorace yace “Kausar You drunk?”
Wani zagi ta lailayo ta ajiye ta soma tsinewa Raudha tana son labarta masa abunda ya faru amma tunɓele yasa baya ma fahimtar ta ,gashi sai cacumo masa wuyar riga takeyi tana neman fadawa jikinsa su zube a ƙasa duka .

Kama kafaɗarta yayi ,ya girgiza ta “Kausarrrr”

Wani lauuu tayi masa da ido kamar mai son yin masa fari ,kawai sai ta sakin masa murmushi “Yes handsome” ta kamo hannunsa “Muje ko?” cikin dubara ya zame hannunsa a hankali ya tallafota ta baya yanda kasan me tatata haka take gwama tafiyarta. Har suka kai mota ya buɗe mata a gaba ta zauna ya kewaya ya tada motan saida suka kusa kaiwa maitama sannan ya juyo ya kalleta

“Ammm ina muka nufa kinsan bansan gidan ba”

Lauuu ta kallesa kafin tace “Gidan mu zaka kai ni mana” Shiru yayi ya na tunanin mafita to shi ina yasan gidansu ,ga dare ya fara yi goma ta gota
Gyaran murya yayi ..

“Muje in kaiki Kisha coffee? ”
“me yasa? Oh no I'm so slouched”

“Oh come on! zai rage maki mayen da kike yi ,kar muje gida a haka a gane iyayenki bazasuji daɗi ba”

Kamo hannunsa tayi tana murzawa cikin nata ,tana kallonsa ƙasa ƙasa ,cikin sexy murya tace “Really?” ya kasa amsata saboda muryarsa da ya harɗe a maƙoshi ,itakuma kai hannunta tayi saman sajensa tana shafo sa a hankali ,ya kasa ce mata ta bari gashi yina ƙoƙarin rasa control ɗin sa ga dare yina yi.

Gyaran murya yayi daƙyar ya kai hannunsa akan hannunta ya rikesu duka aikuwa gaba-daya ta fada masa a jiki tayi pillow da cinyarsa .

Sosai yaji abar wandonsa tayi zillo da sauri ya matse cinyoyinsa waje guda ,amma bayi da zaɓin tureta don haka a haka ya cigaba da driving ,sun Gama kewaye iya inda ya sani a Abj amma ba wani coffee joint da suke buɗe ,ganin dare na daɗa yi yasa ya wuce da ita gidansa don ya haɗa mata shaf shaf ta sha ta ɗan dawo hayyacinta ta wuce gida .
Gaban wani wahalallen gidan bulo mai raunataccen ƙofa ya faka motar ya janyeta a jikinsa da sauri yaje yasa makulli ya buɗe sannan ya zo ya kamata ƙafafuwan ta ba takalmi ya shigar da ita gidan ,A falonsa yai mata masauki yai sauri yaje ya kunna camp gas ya dafa ruwan cofee ya kawo mata.

Yina dawowa ya ganta tayi rashe² a kujera sai gyangyaɗi takeyi ,tallafota yayi zaune ya miƙa mata mug ɗin coffen

Kai hannunta tayi zata karɓa amma Idanuwarta suna kakkafe cikin nasa tana masa wani kallon ƙasa ƙasa,har ta kama takai coffen wajen bakinta .

Wani daddaɗan ƙamshine ya doki hancinta da sauri ta lumshe ido ,sai sannan ya iya janye nasa idon a

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment