Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma daya taƙaitani shikenan komai akayimin sai dai in yafe ?ina bazan iya ba " na haƙura da auran nasa , can kuma ta nisa tace "kai to inhar na haƙura gaba wannan mai kamada shanun zai nemo ƙauyenmu auransa shine mafita ,inci kaji in more insha lemon kwalba mai sanyi .

************
ASALIN LABARI.
Alhji Usman shine asalin sunnan dadyn tunda ya auri momyn MK har yau bai ƙara aure ba ,ko sha'awar ƙarawa ma bayayi .
Burinsa shine ya dinga kyautata mata iya ƙarfinsa .
Watansu biyu da aure ta sami cikin MK kulawa ta musamman suka fara bawa cikin sbda suna tsananin son aihuwa dukkan su .
Kwanci tashi babu wuya har ciki ya isa wata tara da kwana goma ,cikin ikon Allah a safiyar lahadi ƙarfe (7:am) ta fara naƙuda , da sauri dady ya ɗauketa zuwa asibiti cikin ikon Allah da taimakon rabbi da taimakon likitoci ta haifo santalelen yaronta mai matuƙar kyau .
Ciƙin ƙan ƙanin lokaci aka gyarata ita da baby boy , basu suka dawo gida ba sai wajen ƙarfe biyu kasancewar an kaita ɗakin hutawa .
Sai da suka dawo gida dady ya fara kiran Hajja B da sauran ƴan uwansa dana momy.
Gidan baya rabo da jama'a sam sbda tayasu farinciki.
Ranar suna yaro yaci sunnan Hajja B wato muhammad Kabir su momy suke kiransa da MK wataran tace son.
Ranar sunnan momy ba ƙaramin kaya da kudaɗe ta samu ba,sbda inda bata zata ba ma sunzo .
Abokan dady kuwa daga mai 30k sai mai 15k sbda tayasu farinciki.

Kwanci tashi asarar mai rai cikin ikon ubangiji MK yayi wayo , yanada shekara uku dady ya buɗe katafaren shago a Kaduna na siyar da shaddoji da atamfofi da sauransu , ba irin ƙana nan kaya yake siya ba na manya mutane hhh.
Cikin hukuncin ubangiji Allah ya sanyawa dady albarka a dukiyarsa taci gaba da juyata ,shi kuma MK aka sanyashi a makarantar boko mai haɗe da islamiya dake nan layin nasu .
MK yana da shekara goma ,ita kuma ƙanwar momy tana ɗauke da ciki wata goma ,har abin ya fara basu tsoro gashi babu aihuwa babu dalilinta .
Washe gari ƙanwar momyn da MK yake kira da anty Nabila ta fara naƙuda, cikin ikon Allah batare da kowa ya sani ba , ta haifo ƴarta mace fara kyakkyawa ajin farko , momy da ke ƙwalawa anty Nabila kira kasancewar ta jita yau shiru ,kuma ta ɗaukota ne sbda ta dinga kula da ita ,kasancewar nauyin da cikin yayi mata yasa bata iya wani aiki mai wahala.
Shigowar momy keda wuya taci karo da anty Nabila kwance cikin jini ko nunfashi batayi , momy tsabar tsoro ta rasa inda zatayi ga abin da aka haifa a gabanta yan cikin riga .
Waro ido momy tayi da sauri ta yage rigar ,aikuwa sai kukan jinjiri ,momy bata tsaya duba meye ba ,ta ciro reza ta yanke cibi , kasancewar a tare mahaifa ta faɗo .
Momy kam ta rasa inda zatayi da rayuwarta ga jaririya babu wanka gashi babu mataimaki sai Allah ga dady ya koma KD shi kuma mk yana makaranta .
Driver tayiwa magana bayan taɗan goge jikin anty Nabila aka sata a mota suka wuce asibiti , da zuwansu aka karɓesu kai tsaye aka shigar da anty Nabila ɗakin gaggawa, ɗaya daga cikin likitocin ta karɓi jaririn hannun momy , likitar ce tace "mace ko namiji ?momy na kuka tace "wlhi bansan ko menene ba "
Cikin tausayawa aka gyara yarinya tsaf ,momy bata zo da kaya ba dan haka wata norse taje bakin asibitin ta siyo riga mai kyau aka sanyawa jaririyar da sai yanzu momy ta tabbatar da abinda aka haifa.
Wani babban likita ne ya fito yana yarfe zufar data karyo masa ya kalli momy dake kuka idanu sun kumbura yace " am sorry to say ...sai yayi shiru sbda tausayin momy ne ya kamashi , momy tace "sorry for whatt pls ka gayamin ta farfaɗo ne ?"likita ya juya baya kana yace "she ...dan girman Allah ka faɗamin " momy tace "tajijiga kanta, likita yace "wanda ya fimu so ya karɓi abinsa .
Innalilahi ,momy ta ambata sauran kalmomin kuwa sun maƙale a fatar bakinta .
Tun lokacin da momy ta kira mai gadi ,shi kuma ya kira dady ya sanar mishi ,a take a gurin dady ya shiga motarsa , yabar shagon nasa ,kasancewar shi a office yake zama,tuƙi yakeyi mai kamada tuƙin gangancin ,dan ikon Allah ne kawai yasa baiyi hatsari ba ,sbda baya bin go slow wucewa kawai yake Allah kuma ya taimakesa babu jami'an tsaro .
Yasha tafi sosai ,burinsa bai wuce ya ganshi a gida ba , tun yana lisaafin mintocin har ya koma wasu lissafai na daban ,
Cikin ikon Allah ya iso asibitin , muryar momy da yajiyo tana cewa "ashe bazakiga ƴarki ba shikenan kin tafi kin barmu "yasa dady cire hular kansa ya ƙaraso cikin asibitin kasancewr yana parking ya fito.
Gurin momy ya nufa ko bai tambayeta ba yasan rai yayi halinsa ,sbda ana yiwa yin kukan farinciki kana ana kuma na baƙinciki ,wannan kam yayi tsauri da yawa , momy ta juyo ta kalli dady tace "my sis ta tafi ta barni dama mu biyu ne shikenan yanzu idan hajja taji bansan ya zataji ba "
Kamo hannunta dady yayi cikin tausayawa yace "kiyi haƙuri kullu nafsin za'ikatul maut, dan haka muyi mata fatan samun dacewar ubangiji da kuma rahamarsa....!

MOM ISLAM
[3/25, 2:59 PM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hasabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂


*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_



https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg

Pls ku shiga kuyi mana subscribe a channel ɗinmu dake sama👆domin samun zafafan littafan hausa mungode.


Page 31-32

Bayan su dady sun biya abubuwan da akayi ya buƙaci a bashi gawar su koma gida da ita.


Bayan sun koma suka sami MK ya zauna a palo yana kuka sosai , harda majina ,momy da har yanzu bata dena kukan ba taje ta rungumeshi ,cikin muryar kuka tace "me kakeyiwa kuka ne son ? MK yace "momy nazo bakya nan kuma ɗakin anty duk jini "

Ba tare suka shigo da dady ba ,kasancewar ya sanar a masallaci da gurin abokan arziƙi.

Cikin ikon Allah aka yiwa anty Nabila sutura aka kaita gidanta na gaskiya ,tashi ɗaya gida ya cika da maƙota da ƴan uwa ,

Bayan mutanen da suka shigo sun gyara ɗakin da antyn ta aihu suka dawo palo gurin momy tare da karɓar kyakkawar jinjirar ,

Jin muryar Hajj B yasa momy jin gabanta ya faɗi ,sbda tana ganin kamar ciwon hajja B zai tashi , ga mamakinta sai taga bata nuna komai ba ,ko kukan zuci take oho.

Bayan anyi kwana bakwai ba ayi wani taron suna ba ,amma yarinya taci suna Nafisat wato yayar Hajja B ,lokacin da mutuwar anty ta isa kunnen mijinta yayi kuka sosao ,sbda ji yake koda yayi aure bazai sami mai hali irin nata ba , girmama na gaba ,biyayya tausayi.

**********

Haka rayuwa ta dinga juyawa ana bawa Nafisat madara da magunguna na ƙarin lafiya.

Cikin ikon ubangiji yarinya tayi ƙiba ta fara girma , lokacin da takeda shekara biyar shi kuma MK yana da goma sha biyar , basa shiri ko kaɗan ko meye dalili oho , Nafisat ta kasance fara sol kyakkyawa mai dogon hanci ga yalwar baƙin gashi har gadon baya ,bugu da ƙari ga kyan diri , lokacin data cika shekara goma sha biyar ,lokacinne ta zama budurwar cikakkiya abda cikar da ƙirjinta yayi naban mamaki , komai zatayi shi cikin nutsuwa take bata hayaniya irin ta sauran yara .
Lokacin da MK yakai 20yrs lokacin ya makarantar gaba da sakandiri ,ana nema masa wata dady ya ɗaukeshi zuwa KD sbda harkar kasuwancin da yake na siyarda kayayyaki ,MK bai wani jima ba ya dawo sbda ba sabawa yayi ba daga zaman gida sai shagon da dadyn ya buɗe masa a kantin kwari na siyar da wayoyi.
Nafisat kam ba wani shiga harkarshi take sosai ba kasancewar tasan tun tuni ne basa shiri .
Wata rana dady ya dawo gida Kano bayan ya huta momy ta kwanta gefen kafaɗarsa tace "inason muyi magana dakai "Dady ya shafi gefen fuskar momy kana yace "ina jinki sarauniya "
Murmishi momy tayi kana tace "dama so nake zuwa gaba a haɗa auran Baban hajiya wato (mk ) shida daughter "
Shima dadyn murmishi yayi kana tace "shine kike wasu ƴan kwane -kwane ai ni tun ba yauba na yanke hukunci su kammala karatu nake jira sai ayi komai , dama Muhammad ya fara cemin shi ya gaji da karatu nace to ya dage da zuwa kasuwa "

Rungume dady momy tayi cikin tsananin farinciki tace "nagode Allah ya barmu dare "dady yace "amin"

CIGABAN LABARI.

Bayan dady da momy sun koma ɗaki , momy ta kalli dady tace "wai me yasa ka biyewa aljanar yarinyar nanne ?
Dady yace " come down "
Ya kamo hannunta yace "zata bar gidannan dole insha Allah "momy tace "niko ina ganin da kamar wuya tunda kana gani yarinya ƙarama ta iya tsafi " shiiittt "dady yayi mata .
Washe gari , yau dady zashi gidan Hajja B cikin siyasa ya kamo hannun Delu yace "yawa ƴata zaki rakani gidan Hajiya amma daga nan zamu wuce kasuwa muyi siyayya "da murnarta tace "aiko naji daɗi tana tsalle ,sai kuma ta turɓune fuska tace "kayan NAFISA nake sawa bani da gyale " dont worry biyoni mota "dady yace tare da kashewa momy dake tsaye tana kallonsu ido suka fice .
Kai tsaye dady ya kaita parking space gurin motarshi ya buɗe mata gidan gaba ,bayan ta shiga ya kulle ya dawo ɗayan side ɗin gurin zaman driver yayi bismillah mancewa yayi bai buɗe get ba ,yaje ya buɗe ya dawo ya shiga suka fice daga gidan.
Sunyi tafiya mai nisa kana dady ya fara magana da zuciyarshi shin ya zanyi inyi mata magana ne ?zako ta amince ?
Wata aya, ya tuno wacce ake karanta ta lokacin da kake son wani abu a gurin wani ko kake so ka sami abu ku lizimci karanta (izaja'a nasrullahi ✌) sau biyu bayan kunyi salatin annabi muhammad s.a.w .
Cikin amincewar ubangiji ya tsinci kansa da cewa "ƴata ke ƴar wane gari ce ?"juyawa yayi yaga wacce yake tambaya ma bacci take haiƙan ,sai yayi murmishi yaci gaba da tafiyarsa .

Bayan sun isa kasuwa yayi parking a gefen hanya ya tasheta kasancewar taƙi gaya musu sunanta ,da sauri ta buɗe ido tana cewar har mun iso gidan hajjiyar ne ?".
Jin hayaniyar mutane ya tabbatar mata da ai kasuwa sukazo ,dady yace "fito kallon ƙirjinta daya fara fitar da ƙirgen dangi tayi kana tace "bani da hijabi " dariya ma taso bawa dady ,dole yaje gurin wani mai siyarda mayafi dake zaune a bakin titi yasiya mata ya kawo mata sannan ta fito suka shiga cikin kasuwar.
Suna tafe Delu na surutu kome ta gani sai ta taɓa ko kuma ta faɗa sun tsaya gurin wata bayerabiya tana siyar da robobi dady yace "nawa takalmin roba ?"
Delu tace "wlhi ba a gurin wannan lutiyar matar za'a siyamin ba jibeta kamar buhun gari ga zane kwaya -kwaya kamar na ƙwarya "
Tsawa dady ya daka mata tare da baiwa mai kaya haƙuri dole sukayi gaba sbda lallaɓata yakeyi .
Wani katafaren shago suka shiga mai ɗauke da atamfofi da materials da shaddoji masu tsadar gaske ,dady yace "ɗinkakku yakeso ,aka faɗa masa kuɗinsu ,bamusu ya ciro ATM ɗinsa a war
Walet ɗinsa aka ciri kuɗi aka bashi abinsa ,yayi wa Delu siyayya ta ban mamaki , ya siya mata ɗinkakkun atamfofi da leshi da shadda da kayan kanti ga kuma takalma da gyale da hijab ,haka aka lodasu cikin babbar leda dady yace a miƙawa Delu ,waro ido tayi kana tace "kai me kaya wannan kayan dukkansa yakai nawa? " mai kaya yayi murmishi yace "dubu ɗari da hamsin " bajewa Delu tayi a ƙasa tare da cewa "kuma Alhji ni ka siyawa wannan kayan ?eh dady yace yana kallonta yana dariya .
Ashha dama Barira kaba koda dubu goma ne kabar kayanka wlhi tana da buƙata "karki damu dady yace ,ya yiwa mai shago godiya sukabar gurin .

Kai tsaye gurin masu siyarda cosmetics sukaje dady yace ta ɗibi duk abinda yayi mata , aikuwa kamar hauka anan ma sai da aka kashe 20k ,dady bai damu ba ,shidai burinsa su rabu lafiya.
Bayan an gama siyayya suka shiga mota dady yace "kayan sunyi miki ko ?" Delu ta waro ido tare da cewa "ai wannan kayan da ka gani ,wlhi ko auran wata akayi a ƙauyenmu ba'a samun kamar haka "dady yana dariya yace "to ke gashi daga tafiya kinsamo wanda ya fishi "Delu tayi dariya kana tace "ai kuwa tafiya tayi amfani .

Jimm shiru ya wanzu na wasu ƴan mintuna dady yace "shin ke ƴar wane gari ne ? Delu dake cikin tsananin farinciki tama mance da auran MK da zatayi tace "ni ƴar DASHI ce "dady yace "dashi dai dana sani ?
Eh Delu tace "dady yace "kince mahaifinki ya rasu ko ?"delu tace "eh .
Dady ya kuma cewa "yanzu idan nabawa mahaifiyarki dubu ashirin zaki kai mata ? Delu na murna tace "da gudu ma ai tunda babanmu yake bai taɓa riƙe dubu goma tashi ta kansa ba , amma gashi mutuwarsa tasa har binni nazo kuma nasami arziƙi "dady yace "ko zamuje a kai mata inyaso kika ɗan kwana biyu sai ki dawo gidan namu " cikin amincewa Delu tace "aikuwa mungode "dady ya juya akalar motarsa zuwa Dashi , cikin ransa ko hamdala yake da basu sami matsala da ita ba ......!


Fans ya kuke gani ??


MOM ISLAM
[3/26, 9:33 AM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hasabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂


*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_



https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg

Pls ku shiga kuyi mana subscribe a channel ɗinmu dake sama👆domin samun zafafan littafan hausa mungode.


Page 33-34


Suna cikin tafiya tayi bacci ,gashi dady yazo wani ɗan ƙaramin ƙauye wanda shima ba saninsa yayi ba .
Parking yayi a gefen hanya kana ya tambayi wasu mutane dake zaune kan wani icce "
Dan Allah nan ina ne ?"
Dady ya tambaya yana nuna musu hanyar da ya gani tayi arewa .
Ɗaya daga cikinsu ne yace "ai nan Dashi kukazo barkanku "murmishi dady yayi musu kana ya ciro ɗari biyar ya miƙa musu ,
Tashin Delu daga bacci dady yayi ,idonta a rufe take amsawa dan batayi tsammanin sun iso ba .
Jin dady yace "gamu fa a Dashi "yasa Delu zabura tace "ai ga gidan namu can "ta nuna wani gida mai zagaye da karare dan ba wata katangar kirki bane a gidan .
Masha Allah dady yace "tare da buɗe murfin motar ya fito kana yace "ƴata fito "kallon kayan jikinta tayi kana tace "nayi ragon azanci dana sani na ɗibo kayan Nafisa wlhi inyita sawa in ɓoye waɗannan , koda yake ma ai wannan na jikina ba batashi zanyi ba "dady ya kalleta yace "wai maganar me kike ne naji kamar kina ƙus -ƙus "
Babu komai ,Delu tace "tare da yin gaba dady yabi bayanta , samarin dake zaune ne suka ƙwala mata kira Muhammadu har yana tuntuɓe ya rugo da gudu yana cewa "Delu na "
Juyowa tayi kalar inda Nafisat take idan sunyi faɗa da MK tace "nifa ban ganeka ba kai ɗin waye ?"
Dady dake tsaye ya kalli Muhammadu kana yace "kayi haƙuri bari ta shiga ta huta "Delu kam cewa "take Alhji ka mance kai da bakinka kace kayimin miji "dariya ma taba dady suka shige gidan Muhammadu jiki na rawa ya koma mazauninsa .
Da sallama Delu ta shiga kasancewar itace a gaba dady na baya , shima sallamar yayi suka ƙarasa cikin gidan , Barira dake fitowa daga wani ɗaki da gari a gannunta ,ganin Delu yasa ta saki ƙwaryar data ruƙo garin ƙasa taje da gudu ta rungune Delu tana cewa "ina kika shiga ?"
Ɗago kai barira tayi ta kalli Dady tace "sannu da zuwa kodai kaine ka tsintomin ita ?" murmishi kawai dady yayi ,ta shimfiɗa masa tabarma ya zauna , bayan sun gaisa Delu yace "Barira kawo ashirin a siyowa alhji ruwan piyawata "kunto gefen Zaninta barira tayi kana tace "wlhi iyakacin nera goma ce dani "cikin tausayawa dady yace "no karku damu a bani ruwan randa "
Allah sarki Barira ashe bata ma da goman kawai dai ta faɗa ne.
Miƙewa Delu tayi ta ɗibo ma dady ruwa a kwanon ɗan cena ,ga mamakinsu sai sukaga yayi bismillah yasha mai yawa sosai.
Bayan wasu ƴan mintuna dady yace "ƴata ki nemi yara ku shigo da kayan nan "
To Delu tace "tare da ficewa da gudu ya rage dady da Barira ,Dady ya ƙarewa Barira kallo kana yace "dama dalilin da yasa mukazo tare nida yarinyarki yarona ne ya taimaketa lokacin da mota ta kaɗeta " babu labarin da dady ya rage ciki harda samun lafiyar Hajja B amma bai faɗi nasu momy ba.
Daɗi Barira taji sosai kana tace "mungode Allah yabar zuminci "amin " dady yace.
"Nidai na dawo da ita gurunki ne badan komai ba ,sai dan ƙila kina buƙatarta amma a dinga lura da ita ,kuma maganar zumunci duk lokacin da zatazo gurinmu muna maraba "dady ya ƙare zancen yana ciro kuɗi wanda tun a mota ya lissafasu ya miƙawa Barira ya fito "koda ya fito baiga Delu ba ,yasan ta harɓa wani gurin.
Buɗe both yayi ya kwaso kayan ya kawosu gida ya ajiye gaban Barira , itako banda kuka babu abin da takeyi sbda wannan sha tara ta arziƙin da dady yayi mata bazata taɓa mancewa ba ,ga kuɗi ga kaya , godiya tayi masa sosai yayi mata sallama yaja mota , daga can nesa Delu na kan bishiya ta hango motar dady , durowa ma tayi Allah ne ya kare bataji ciwo ba , ta fara gudu tana cewa "ka tsaya alhji nifa bazan iya zaman ƙauyen ba "inaa Alhji yayi nisa dan ko ganinta beyi ba .
Dady hamdala yake a zuciyarsa gashi sun rabu da Delu cikin salama ,yayi nisa sosai yaɗan rage gudu ya ciro wayarsa a aljihu ya danna number MK ring ɗaya MK ya ɗaga tare da sallama yace "dady na fito na samu baka nan "
Murmishi dady yayi kana yace "naje mayarda mutuniyarka gida ne gashi har na juyo "mamaki ne ya kama MK yace "dady kuma ta yarda kai garin ya ?"
Dady dake dariya yace "idan na sauka lpy zan baku labari ina hanya ,na kira wayar momynku bata shiga ko lpy ? "eh lpy dady inaga babu chaji ne "dady yace "why a tayar da injin mana "to "MK yace "tare da zuwa isar da umarnin dady .

Ƙarfe (4:30 pm) dady ya isa gida , bayan yayi parking ya fito kai tsaye ya shigo sashen nasu , babu kowa a palon hakan yasa shi zama yana kallon TV yana murmishi sbda Delu ma gaba ɗayanta comedy ce .
Kamar momy ta sani ta fito tare da tsayawa cak sbda mamaki ne ya kamata ,momy tazo kusa da dady tace "wai ta yarda ta zauna kuma ?" murmishi dady yayi kana yace "eh man gashi na dawo ni ɗaya " miƙewa momy tayi ta buɗe fridge ta kawo masa ruwan sanyi da cup , bayan yasha yayi hamdala ,ya fara bawa momy labari , sai ga Nafisat nan ta taho tana cewa "dady barka da dawowa Allah yasa anyi nasara ?"dady yana murmishi yace "aikam tana garinsu "Nafisat tayi dariya ,Dady yace "gaskiya mahaifiyarta abin tausayice amma na bata wani abun .
MK kam daɗi ne ya kamashi a fili yace "Allah mun gode maka matsalatu tabar garinnan .
Washe gari da safe bayan kowa yayi sallah an hallara a dinning ,cikin kwanciyar hankali kowa yake breakfast ɗinsa sunayi suna hirarasu mai daɗi.
Ƙarfe 9:am MK ya shirya zuwa kasuwa , yana shirin shiga mota ,wayarsa ta fara ring .
Ganin number budurwarsa da rabonshi da kiranta tun ranar da Delu tazo gidansu ,ya ɗaga tare da cewa "baby nayi missing ɗinki "
A faɗace tace "babu wani miss wlhi kawai dai ka sami wata ka mance dani "MK yace "haba wazan samu ?"
Budurwar tace "to dama bansami damar kawo maka invitation ɗin bikina ba sbda haka shine na kiraka saura kuwana biyar nagode zan karya wannan sim ɗin ta kashe wayar ,
Rai a ɓace MK yabi kiran amma shiru a kashe ,ya daɗe a tsaye daga ƙarshe ya shiga mota ya tafi .

GIDAN HAJJA B.
Tunda Delu ta tafi Hajja B takeson tazo gidansu momy taji ya suka ƙare ,yau dai kam ta shirya koba komai taci dariya ta godewa Allah .

Bayan Hajja ta gama shiri ta fito hannunta riƙe da jaka da mayafi , ta nufi parking space ta fara kiran driver ,da gudu yazo tace "gidan su babana zaka kaini "to angama Hajiya driver yace "tare da tafiya da gudu ya ɗauko key ya shiga Hajiyan ma ta shiga aka buɗe musu suka fita.
Mancewa tayi da bata sanar musu ba ,ta ciro wayarta a cikin hand bag ta danna kira ,kasancewar number MK ta kira yasashi cewa "nifa bana gida "ya kashe wayar sbda har lokacin yanajin baƙincikin auran da matar daya ɗorawa buri zatayi.
Hajja kam tace "Allah ya baka haƙuri kai kam babana halinka sai kai "
Number momy ta kira ,momy na ɗagawa Hajja tace "yau dai gani nan zuwa gidanku dan munkusa ma "cikin murna momy tace "to aikuwa munji daɗi sukayi sallama .
Ba wani tafiya mai nisa suka ƙara ba sai gashi sun iso gidansu momy , kasancewar get ɗin a buɗe yake tunda goga ya fice bai rufeba yasa su shigewa .
Bayan driver yayi parking Hajja ta fito tare da ƙarasawa cikin gidan ,da sallama ta shiga momy da Nafisat da Dady suka amsa cike da fara'a , dady yana dariya yace "Hajiya da yau fa zanzo sai gaki "Hajiya tace "ai ni na biyo ƴata ne ina take ? momy tace "aiko kunyi saɓani dan wlhi takoma ƙauyensu "waro ido Hajiya tayi kana tace "ƙauyensu kuma ?wanne me hikimanne ya yaudareta har ta yarda ?"dady yace "aiko na kaita kuma lafiya muka rabu "
Daga nan dady ya bata lbri ,suka gaisa , kasancewar shirin fita yake , yayiwa Hajiya Allah ya kiyaye hanya ya fice, Nafisat tayi masa Allah ya tsare .
Momy da Hajiya sun daɗe suna hira ta tsakanin ɗa da uwa.
Zuwa yamma Nafisat da momy suka rakota amma saida tayi ɗiff ta cika cikinta da abinci .
Suna fita driver dake rusa gyangyaɗi ya tashi tare da mutsike idonsa ya gaishe da momy da Nafisat bayan sun amsa ya shiga mota Hajiyan ma ta shiga suka ɗaga mata hannu , sai da suka fice sannan su momy suka koma ciki .

A ƘAUYE .
Bayan data duro daga bishiya ta kira dady bai jita ba,ta koma gida ta baje a tsakar gida tana shure -shure ,Barira dake zaune kan sallahaya tana ƙara godewa Allah bayan ta idar ta fito tare da cewa "meye kuma ?"
"Ai kina sane wlhi kece kika hana su tafi dani kuma sai na koma nan mutum duk yayita ɗiban datti "eyeee "Barira tace tare da sanya hannunta a haɓa tace "ni tunda nake na taɓa ganin ɗan da yaƙi mahaifarsa ? Delu tace "nidai banaso " Barira tace "dama jiya su Muhammadu suka kawo kayan sa rana anyi miki baiko "zaro ido tayi kana tace "ba uban da ya isa yayimin auran dole ai ba shine ya haifeni ba "Barira tace "ko bashine ba amma ai wanda ya badake ƙanin babanki ne "jar uba "wlhi kunyi gwari ,idan kwaɗayin kayan aure kikeyi Barira gani da wanda yafishi "ta nuna kayan da dady ya siya mata ,
kana tace "idan kuma kuɗi ne ai nasan an baki wani abu "tsawa Barira ta daka mata kana tace "aikuwa Delu kin shahara gurin iya rashin kunya "
Harara Delu ta gallawa Barira kana tace"nidai nariga da nayiwa kaina miji MK zan aura inkiya (MK MIJIN DELU) A hayye Barira tace tare da cewa "aikuwa kina ruwa dan auranki bazai shige daminar nan ba befi sati biyu ba "
"Nashiga uku Barira bakyasona gashi ko zan gudu Kano bansan anguwar dazance ba ,shiyasa gara ka dinga kallon hanya da kyau gudu kar azo ranar da amfanin komawa ya taso ido ya raina fata "oho dai " Barira tace "tana dariya.
Zuwa dare Muhammadu yayi wanka yasha turare da rigarsa har ƙasa kai kace

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment