Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"eh sannunki da haɗa guri "
Delu dake kwance kan cinyar momyn MK kasancewar shi bai ma san tana palon ba tace "yaya ai Mamanka tace "zataje dani gidanku " rai ɓace MK tace "momy wai meyasa kikazo ne ? nace ki huta amma kinƙi tunda ina hanyar zuwa "
Batare da momyn nasa tace dashi komai ba tayi masa murmishi wanda ya fito da ainihin kamar da suke shi da ita.
Wani babban tirai Nany ta ajiye a gabansu wanda yake ɗauke da kayan itatuwa kama daga su apple da abarba da sauransu ,Nafisat dake latsa wayarta ta kalli MK daya gimtse fuska tana son yin dariya amma babu hali kasancewar a gidansu ko haƙoransa ba kasafai ake gani ba .
Murya a cunkushe MK yace "ke lil sis yau gaisuwar ma ta gagara ko?"
Nafisat ta zare farin gilashin daya ƙarawa farar fuskarta key tace "bro naga kanata faɗa ne "
Caraf Delu ta karɓe da cewa "ɓera fa waccan me kamada aljanun tace maka "
Momy ta buɗe baki ,har zatayi magana hajja B tayi mata alama da tayi shiru .
Nafisat tace "bro kana jinta ko ?"
Ƙwafa MK yayi sbda yana tara abubuwan da zaiyi mata inhar taci gaba da kaishi maƙura.
Bayan anyi azhar momy suna shirye-shiryen tafiya ,Delu taje jikin momy tace "mama zan biki ni marainiya ce "
Kasancewar MK baya nan tunda ya fita masallaci bai dawo ba ,yasa ta dinga shararawa momy ƙarya harda cewa "dangin ubanta suna yunƙurin kasheta saboda Allah yayiwa doguwa kaf cikin ƙauyen gajeru ne , kuma tana da sa'a a rayuwarta ,babanta kafin ya mutu yace "duk mijin daya aureta zaiyi kuɗi na ban mamaki wanda Allah kaɗai yasan adadinshi "
Cikin tausayawa Nafisat tace "ayya ke abin tausayice ƴar uwa ,insha Allah zamu kula dake momyna ta zamo momynki kuma kin zamo ƙanwata ta jini dadyma zaiyi farinciki da ganinki "
Tausayin Delu ya gama kama momy sbda harda ƴar ƙwallah tayi .
Nafisat ta sa Delu shiga toilet tayi wanka , bayan ta fito ta shafa mai ,Nafisat tace "ina kayan canzawa "Delu tayi narai-narai da ido tace "bani dashi a titi ma na haɗu da wata mahaukaciya ta temaka min da kayan sawa ".
Hannunta Nafisat ta riƙe kasancewar ta mayar da kayanta wanda ta cire momy ma ta tashi suka nufi ɗakin Hajja B , momy ce ta kalli Nafisat tace "ku jirani a palo ina zuwa "
Kai saye suka dawo palo tare da zama a kujera ɗaya.
Momy tace "mama kina ganin mu tafi da yarinyar nan ?"
Nisawa Hajja B tayi kana tace "inaji a jikina yarinyar nan tana da wata ɓoyayyar baiwa dan kinga zuwanta Allah ya taimakeni na fara tafiya ko ɗingishi babu inaji a jikina waraka ce "
Momy tace "to shikenan zan tafi da ita sai ta fara zuwa makarantar islamiyar su Nafisat kafin a nema mata school ".
To Hajja B tace "kana ta miƙe tare da ɗibo musu dambun kasa a cikin wata farar roba mai hannu ta basu ,
Bayan sun fito suna tsaye a parking space MK ya shiga tare da kallonsu yace "momy ina motar da kukazo da ita ?"
Momy tace "ai danaga kana nan shine nace driver ya koma da ita "
"Okay "
MK yace "tare da shiga mazaunin driver momy ta shiga gaba Nafisat ta shiga baya , Delu ma ta shigo ,
"Wayo laushi kamar gadon aure na "
Da sauri MK ya kalli backside ɗin da Nafisat ke zaune yaga Delu na zazzare ido yace "wlhi sai dai a fasa tafiyar nan ni zaki rainawa wayo wlhi bazakije gidanmu ba ,itadai Hajjan dake sonki sai kuje ku ƙarata "
Hajja ta haɗe hannuwanta biyu tare da cewa "haba babana kayi haƙuri ko kwana biyu tayi na yarda ta dawo gurina ba'a takurawa maraya fa"
"Maraya ko ?"
MK ya faɗa tare da nuna Delu yace "ai marayun ba haka suke ba da hatsabibanci"
Momy da sai yanzu ta kuma magana tace "haba my M muje Allah yayi maka albarka "badan yaso ba ,yajasu sai dan farincikin mahaifiyarsa sbda baya iya yi mata musu.
Cikin ikon Allah suka iso anguwarsu Ɗorayi ,bai shiga da motar ba yayi parking daga bakin get ɗin ,ganin haka yasa momy ƙinyi masa magana sbda tasan sarautar ce ta motsa .
Nafisaat ce ta fara buɗewa tace "ƙanwata fito "tom "Delu tace ta fito ta tsaya gaban motar "MK ya zagaya ya buɗewa momy ,suka buɗe gidan suka shiga .
Wani azababben ihu Delu ta rangaɗa tare da tsalle tana nuna wani kare dake kwance yana hutawa , karen jikinsa duk gashi gashi ƙato sosai,
Tsaki MK yaja mtsw tare da cewa "ga irinta nan ai "
Nafisat taja hannunta suka shiga ciki .
Bayan sun huta momy da MK suka zauna a plo Nafisat ta kai Delu ɗakinta ,ɗakine madai-daici mai ɗauke da toilet mai kyau pentin ɗakin ruwan madara da ruwan toka ne yayiwa ɗakin keyau sosai , daga gefe kuma royal bed ne wanda aka shimfiɗeshi da haɗaɗɗen zanin gado mai laushi , zanin gadon fari ne tass haka ma filolin .
Sufa Delu tayi ta haye gadon tare da cewa "nidai na rasa ya akeyi ƴan binni suke kuɗi amma banda ƴan ƙauye "
Nafisat dake kallon Delu tace "komai fa daga Allah ne ,inyaso ya ganka a haka inyaso ya maidakai mai arziƙi "
Delu kam har wani lumshe ido take tana ƙarawa sbda laushin gadon Nafisat ga wani ni'imtarcciyar iska dake ratsa ko ina na jikinta "
Zuwa dare mai aikin gidan ta jere musu abinci a dinning ,bayan sunyi isha'i kowa ya hallara harda Delu , kallon MK tayi da yake ta kumbure-kumbure tace "mama yaya yana kuka cikin sa'a ya shammacesu ya kwasheta da mari mai shiga jiki ,
Faɗa momy ta kama yi masa akan marin da yayi ,Delu kam kuka take bil haƙƙi sbda jira take taji an ɓatawa MK rai ,

Nafisat ko tari batayi ba sbda a inda taga ran yayan nata ya ɓaci zai iya dukanta .
Momy tana gama cin abinci tabar su a gurin ta wuce ɗakinta ,MK yace "lil sis maza jeki kwanta " Nafisat ta janyo hannun Delu "maƙale kafaɗa Delu tayi kana tace "idan akwai daɗi nidai zan ƙara abincin , tsawa MK ya daka mata tare da cewa
"Ke mufa nan ba ƙauye bane da zamu dinga ajiyar abinci barkatai babu tsari ".
Nafisat dake dariya tace "bro akwai abinci fa "
Kallon da yayi mata ne yasata barin gurin batare da ta jira mai zece ba.

MK yace "muddin kikace zaki gawada surkullenki a kanmu wlhi sai jikinki ya gaya kiki saura kiyiwa momyna rashin kyautawa "
Turo baki gaba Delu tayi kana tace "amma dai bazan koma gida ba ko ?"
MK dake shirin kai mata duka ta kauce tare da zubawa da gudu ta fara zagaye-zagaye sbda ta rasa inda zata shiga , MK gani yayi tama gama rainashi dan haka yabar gurin tare da cewa zaki gane kuranki da ƙafarki zaki bar gidannan.
Delu kam ta rasa hanyar da zata sadata da ɗakin Nafisat ,wata hanya tabi ta buɗe ƙofar taga kitchen ne ,amma a nata tunanin tace "nan kuma ɗakin waye ?ga kayan abinci kamar ba'a so "
Dube-dube ta fara cikin sa'a ta buɗe ,gurin gasa kasa ,waro ido tayi sbda ganin gasassun kaji har guda biyu manya sai zuba ƙamshi suke amma babu zafi , kujerar dake kitchen ɗin ta hau ,kasancewar kujerar doguwa ce yasa ta zama tare da ɗaukar kaza ɗaya ta fara ci , tunowa tayi ashe dare ne sosai hakan yasa ta yagi naman ta ƙulle a gefen zaninta ta fito ,a taƙaice dai har yanzu ma ta rasa inda zata ,dan haka ta kwanta a doguwar kujerar dake ƙawataccen palon nasu .
Kasancewar dole idan mutanen gidan suka fito daga ɗakinsu dole su haɗu a palo.

Washe gari , an tashi da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya , kasancewar ana lokacin damina.
Kowa na gidan ya makara kasancewar daɗin bacci da mutan gidan sukaji ,ciki kuwa harda MK sai wajen ƙarfe bakwai sannan suka tashi a bacci.
Momy ce ta fara tashi taje tayo alwalah ta shimfiɗa sallaya ta kabbara sallah ,bayan ta idar tayi adu'ointa ta ninke tare da ajiye sallahar a mazauninta , batayi tsammanin MK bai tashi ba ,kai tsaye ta wuce ɗakin Nafisat bata lura da Delu dake kwance ba ,
Sai da momy ta fito daga ɗakin Nafisat sannan tahau dube-dube kasancewar bataga Delu ba , ganinta tayi a kwance kan 3sitter sai uban zuba munshari take , momy ta ɗan taɓata tare da cewa "ƴata gari ya waye fa "
Da sauri Delu ta tashi zaune sai kuma ta haɗe rai tace "ina cikin mafarkina mai daɗi za'a wani tasheni "
"Yi haƙuri momy tace "tare da kamo hannunta suka nufi ɗakin Nafisat ,Nafisat dake sallah bayan tayi sallama takai dubanta ga Delu ,taga kumatunta duk yawun bacci ,tuntsirewa da dariya Nafisat tayi , sai kuma ta hau istigfari.
Har toilet momy ta raka Delu tayi alwalah bayan ta fito Nafisat ta miƙa mata hijab ta bata sallayar , bayan Nafisat ta gaishe da momyn .
Bayan fitar momy Delu ta miƙe kasancewar ta idar da sallah tace "wai ku bakwa kai ziyara ne ?"
Nafisat da bata gane inda zancen nata ya dosa ba tace "kamar ya ziyara ?"
"Ina nufin gidan sababbin amare mana ko gidan tsofaffi "
Delu ta faɗa tana riƙe ƙugu.
Nafisat tace "gaskiya bana yawo kuma ai kinga yanzu ruwa akeyi babu halin leƙa koda ƙofar gida ,kuma yau dadynmu zai dawo "
Hangame baki Delu tayi kana tace "waye kuma dady wane sabon ƙyallen ne ?nagafa ku ƴan binnin nan fi'ilinku yafi ƙarfinku "
Delu ta ƙarashe maganar tare da taɓe baki.
Shiru Nafisat tayi ,a zuciyarta kam cewa take "anya zamu iya zama da wannan yarinyar kuwa wlhi ina "
Delu da taga ba'a bata amsa ba ta fice ta dawo kujerar data kwanta ta zauna tare da cewa "anyimin sata kodai lokacin da naje yin alwalah suka sace naman dana ɗibo ?",
Sai kuma tace "uum inma sun ɗauke ai nasu ne yanzu ina magana zan tonawa kaina asiri ko kuma wancan mai kamada mugun yace zai maidani gidan gurguwa ,dan ko ƙafar ta gyaru bazan dena cewa gurguwa ba ....!


Pls kuyi haƙuri nayi muku alƙawarin 6 banyi ba nayi baƙuwa ne anjima zuwa 8pm zanyi koda babu yawa inason mu gama kafin azumi insha Alla.

MOM ISLAM domin magana mai muhimmanci 08141799224.

[3/20, 6:56 PM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hasabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂


*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_


Page 21-22

Hango gurin da sukaci abinci jiya tayi , an cikashi da kuloli sunkai biyar , waro ido tayi tare da miƙewa saɗaf-saɗaf ta isa gurin kana ta buɗe foodflaks ɗin taga soyayyen dankalin turawa da wainar ƙwai a gefe , kunto ɗankwalinta tayi tasa wainar ta mayar da murfin kular ta rufe.
Da gudu ta koma ɗakin Nafisat tana rawa wai a dole fitsari takeji ,ganin haka yasa Nafisat cewa "meya faru ?"
Delu tace "fitsari kamar zai zubo "
Tana maganar ne tana yarfe hannaye .
Nafisat tace "baga toilet nan ba kishiga "
Kishigan kawai ta gane amma sam bata taɓa jin wani abu mai suna toilet ba.
Tana shiga ta ƙarewa ƙofar kallo ksancewar tana laluben inda ake sanya saƙata kar a kamata .
Fashewa da kukan ƙarya tayi tare da cewa "wayo Barira basir ɗina ta motsa
Nafisat dake zaune tana dane-dane tace "lafiya kuwa ?" sbda taji kamar ana kuka.
Jin tsit yasa Nafisa bata ƙara magana ba ,sbda abin da take a waya ya ɗauke mata hankali ,
Kunce ɗankwalin Delu tayi ta fara gutsirar soyayyan ƙwan tanaci tana cewa "daban ɗauke ba sai su iya yimin haramiya dan ba imani ne dasu ba" a hankali take maganar inda baza'a jita ba.
Bayan MK ya dawo daga masallaci ya shiga toilet yayi wanka tare dayi brush ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa ,janye ƙaramin towel ɗin dake rataye a jikin rake yayi ya goge kansa ,ya fito ya zauna kan bed, tare da sauke ajiyar zuciya ,kayan daya cire ya ɗauka yasa a washing machine ya nufi gaban mirror ,wata doguwar kujera yaja ya zauna tare da ƙarewa fuskarsa kallo ,a zahiri yace "wlhi na rame ,ko wannan masifar ma ta isheni "
Lotion ɗinsa mai matuƙar ƙamshi ya ɗauka ya shafe jikinsa ,ya ɗauki mataji ya tace kansa ya shafe kansa da wani mai baƙi mai fitinannen ƙamshi , bayan ya kammala ya wuce drowar kayansa wani lallausan yadi ya ciro mai kyau sai sheƙi yake kalar ruwan ƙasa ,bayan yasa kayan ya ciro baƙar hula da takalmi baƙi sau ciki yasa , gaban mudubi ya dawo ya ɗauki farin agogonsa dake ƙarawa fuskarsa kyau da haiba ,ya kalli kansa a mudubi yayi juyi ya daɗa gyara zaman hularsa , turare ya ɗauka mai ƙamshi ya feshe jikinsa ya kuma ɗaukar wani ya feshe jkinsa dashi ,ya ɗauki wayarsa dake kan bed ya zirata a aljihu ya fito palo ,
Da momynsa suka fara haɗa ido ,ta sakar masa murmishi Delu na kallo kasancewar ta riga da ta fito tunda Nafisat ta sanar mata da momy na kira aci abinci , karaf idonsa ana Delu tayi farr da ido a dole kalar abinda momy tayi masa itama tayi .
Tsaki MK yayi tare da kallon Nafisat dake shan shayi da cokali yace "lil sis a kullum sai dai a gaisheki ne ?
Langwaɓar da kai Nafisat tayi kana tace "afuwan yaya bazan sake ba ,daga haka suka gaisa , MK yakai dubansa ga Nany dake zaune a kan kafet tana cin indomie yace "ina dankalin da nace ki soyamin....!

Yau banga comments ba zanje hutun sati ɗaya Allah zuwa bayan sallah ma ƙarasa.


MOM ISLAM
[3/21, 4:32 PM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hasabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂


*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_


Page 23-24

Cike da ƙwarin guwaiwa Nany tace "yana foodflaks " okay good " ya isa kan dinning ɗin tare da jan kujera ya zauna ,yace "au na mance bamu gaisa da momyna ba "
Muemishi momy tayi kana tace "naga kamar kana sauri har dadyn ya iso ne ,kodai kunason ku ƙara yimana irin surprise ɗin da yayi ne next week ?
MK dake buɗe kular abinci yaga tsakuren dankali baifi guda goma ba ,ya ɗago ya kalli Nany yace "ke zonan " batayi zaton wani abu ba ta cire hannunta ,a abincin tazo gabansa , momy dake kallon yanayin fuskarta duk ta sauya izuwa ɓacin rai tace "yadai lefi tayi maka ?
Sai da ya kwashe Nany da wani gigitaccen mari wanda yai sanadiyar zubar hawayenta tashi ɗaya ,sannan ya kalli momy yace "momy jibi abincin da nasa ta yimin ".
Cikin rashin jin daɗin marin da MK yayiwa Nany momy tace "Son ba haka akeyi ba ,idan kuskure tayi sai kayi mata faɗa ta gyara "Nany dake riƙe da kumatu tace "wlhi momy harda ƙwai na soya guda biyar "cikin masifa MK yace "to ina yake ? Nafisat data gama nata break fast ɗin tace "yaya kayi haƙuri "ke tashi kibar nan kafin in fasa miki baki "MK yace tare da nuna Nafisat da yatsansa .
Inda sabo ta saba da idan yana faɗa bayason ana bashi haƙuri ta miƙe tabar gurin ,
Delu da take fitsari a wando ga hawaye nabin fuskarta sbda ganin fitinannen marin da akayiwa Nany tana tunanin idan yasan ita taci to zai iya sumar da ita "
Momy na shirin tashi daga gurin taji ta taka abu kamar ruwa "da sauri ta sunkuya ,zarnin fitsari da kuma ganin ta wajen Delu yake gangarowa ne yasata cewa...!
Kuyi haƙuri zanyi mai yawa gobe kaina ke ciwo yanzu.

Masu shar'hi daga grps grps nagani kuma na gode
MOM ISLAM

[3/22, 11:49 AM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hasabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂


*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_

_Writer of 👇_

ZAINABU ABU
ZAZZAFAR KISHI
LADIDIN ƘAUYE
JININ ABBANA
NANCY ƳAR ƘARYA
DIYANA
LAMARIN ƘADDARAR AURENA
YARINYA MAI YAƁARGAZA -paid
SIRRIN ZUCIYA- paid
ƘANIN UBA- paid
DOCTOR MARYAMAH
NIDA YARINYA
ZAƁIN SHI NE - paid
MACCEN SIRRI -paid
Now Mk MIJIN DELU
My new book *SAHIBUL AMRAT* is loading



Pls kushiga kuyi mana subscribe sannan ku danna ƙararrawa a wannan channel ɗin ,domin samun zafafan littafan hausa 👇

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg



Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====270
2GB@=====550
3GB@====800
5GB@====1,350

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*

_____________________

Page 25-26


"Ƴata ɓarin ruwa kikayi ne ?"
In ina Delu ta farayi
Tace "babbba..bafa...ni...ce....ba..karkuyimin sharri.
Ido waje MK yake kallonta a zafafe ya matso kusa da ita yana shirin wanka mata mari hannunsa ya maƙale !
Momy dake tsaye tana kallon ikon Allah bata ma lura da hakan ba sai da taji MK na cewa "momy lanƙwasa min hannuna "
Kallonta takai ga hannun nasa tare da cewa "wai meke faruwa ne ?MK yace momy bakya gani ne ? momy da kwata -kwata ta dena gani ko kaɗan sai haske wato dun dumi fari kawai take gani ,tace "son bana ganin komai "
Kuka MK ya fashe dashi kana ya kalli Delu da itama kukan take yace "ni bansan ma mezance miki ba ,wlhi nayi dana sanin ɗaukoki na kawoki familyn mu gashi kin zamo mana annoba gara kiwon kare da ajiyarki a cikin gida "wannan kalmar ta doki Delu ta share hawaye tace "yau zanbar muku gidanku yanzu ma "
Momy dake laluben inda zata bi ta iso gurin Delu ,ta fara tafiya tana cewa "kiwa ma'aikin Allah karki bar gidannan inda hali ma har kiyi aure .
Rufe fuska Delu tayi kana tace "ina son wannan mugun amma ina tunanin karya kusa illatani idan nayi masa laifi "
Momy dake neman mafita tace "babu illatawa aike bakya lefi karki damu yanzu dawomin da idona "
MK kam ya gama hassala abda banda hucu babu abinda ke fita daga bakinsa ,ga jijiyoyin hannayensa da suka tattashi ,da ƙarfi ya hambare Delu ta zube ƙasa tana mai ƙara rushewa da kuka .
Momy tace "wai son mai yasa kake haka ne ?wlhi idan har baka ƙyale yarinyar nan ba zan saɓa maka "
Suna cikin magana Nafisat ta fito sanye da dakakkiyar shadda ta isa gurin momy tana cewa "my momy dady harya kusa zuwa gida naga baki shirya ba "momy da bata ganin Nafisat sai dai jin muryarta tace " daughter kaini ɗaki bana gani " whattt!! Nafisat tace "momy garin yaya mekuma ya sameki "sai ta fashe da matsanancin kuka .
Delu dake sunkuye tana gursheƙen kuka tace "muma haka mukaga ta koma "MK yace "yau sai na kasheki ! alamun an buɗe door sukaji basiyi tsammanin shigowarsa ba ga mamakinsu sai sukaga dadyn yana takunsa wanda ya saba idan har yana tafiya ,
A al'adarsu idan ya dawo koda ƙofar gida yaja sai momy tazo tayi hug ɗinsa ,sai yau kuma yaga akasin hakan ,gashi dai saitinshi take kallo amma bashiɗin take kallo ba ,kuma bata ma san ya shigo ba,MK yaje gurin dady da maƙalallen hannu yace "barka da dawowa my dad "kallon hannun MK dadyn yayi kana yace " what happen ko kanaso ka zamo gurgu ne ?yakai kallonsa ha Nafisat dake riƙe da hannun momy tana kuka ta sanya hannun momy a na dady...!

Kuyi haƙuri uzurori sunyi min yawa

Sabon littafina mai fitowa insha Allah bayan sallah ,*SAHIBUL AMRAT* kada ku bari a baku kabari.
08141799224


MOM ISLAM
[3/23, 10:32 AM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hasabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂


*Zainab Habib(Mom Islam*



*Kuyi haƙuri masu comments wlhi ina gani aiyuka ne sukaimin yawa ,shiyasa kuke jina shiru amma ina karanta comments ɗinku a duk inda kukayi🥰.*


_Elegant online writers_


https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg

Pls ku shiga kuyi mana subscribe a channel ɗinmu dake sama👆domin samun zafafan littafan hausa mungode.


Page 27-28


Cikin kuka momy tace "wlhi wannan yarinyar ba alkairi bace a tare damu "momy ta nuna Delu datake durƙushe tana kuka ,sbda tasan yau inhar mutanen gidannan basu koreta ba to sunyi mata adalci.

Dady ya kalli Delu ya kalli MK mai maƙalallen hannu yace "a ina kuka samota kodai ba mutum bace ?"
Cikin sauri MK yace "dady nima na fara tunanhn hakan kaga har hajja B wannan yarinyar ya" nuna delu kana yaci gaba da cewa "ta gyara mata ƙafa ".
Da mamaki dady yace "kenan mai magani ce ko menene wai shin ma a ina kuka ɗaukota?" .

from A to z MK yaba dady labari harda ce musu da tayi ita marainiya ce bata da kowa .
Gingina kai dady yayi kana ya gyara zama a kujerar daya zauna ya daɗa kamo hannun momy da batace komai ba ,cikin tausayawa yace "afuwan hajiya insha Allah zakiyi normal barinji asalin yarinyar.

MK da Nafisat suka nemi guri suka zauna tare da zubawa dady ido suna sauraronsa ta inda zai fara magana , sudai fatansu karta maidashi kurma tunda ta iya hatsabibanci.

"Taso ƴata " dady yace cikin bawa Delu umarni da miƙa mata hannunsa na hagu kasancewar na daman yana riƙe da momy .

Tasowa Delu tayi tana share hawaye .

Dady yace "mahaifinki fa?"
Delu tace "ya mutu"
Dady yace "menene sana'arsa?"
Delu tace "babban malami ne sbda kaf ƙauyenmu shine yazo na ɗaya gurin iya sihiri iri-iri har zuwa tono gawa a kabar....."

"Shittt dady yace "ya isa haka , ya koya miki wani abunne dangane da magungunan da yake badawa ?"
Giyaɗa kai Delu tayi kana tace "eh sosai ma ,ya koyamin inda zan gyara karyayyu dakuma inda zan sami abu a lokacin da nakeso "
Dady yace "why kika karyawa yarona wanda ya taimakeki hannu ?
Delu tace "baba cemin yake aljana kuma ni ba aljana bace "

Dady yace "me mahaifiyarsa tayi miki ?" tsitt Delu tayi batace komai ba , dady ya kuma tambayarta ,sai a karo na uku ne tace "nidai ku auramin wannan mai sunnan arnan " waro ido dady yayi MK yace "wlhi zanci ubanki shegiya maiyy kawai "momy kam babu magana sai hawaye da take amma tana jinsu .

Dady ne yace "yanzu anan gurin inaso ki gyarawa kowa abinda kika nakasa masa "
Maƙale kafaɗa Delu tayi kana tace "zaka yarda in auri wannan "ta nuna MK dakeyi mata daƙuwa da ɗayan hannunsa .
Ba tare da dady ya kawo da gaske takeyi ba ,dan shi gani yake wannan ƴar ficiciyar batasan menene soyayta ba kawai wasa take ,dady yace "eh naji maza gyara musu komai.
Sudai suna zauna amma a zahiri basusan abinda tayi ba ,sai ga momy ta buɗe ido MK hannu ya miƙe "har zai tashi ya nufi gurinta dady ya tsayar dashi tare da cewa "abi komai a hankali....!


Ina ƙara baku haƙuri babu yawa


MOM ISLAM
[3/24, 8:38 AM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hasabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂


*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_



https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg

Pls ku shiga kuyi mana subscribe a channel ɗinmu dake sama👆domin samun zafafan littafan hausa mungode.


Page 29-30

Bayan Delu ta gyara komai dady yace "yanzu ƙauyenku nakeso ki faɗamin "
"Taɓɓ ɗijam "
Delu tace "tare da riƙe ƙugu tace "toni hatta sunnan ƙauyen ma na mance dan haka sai ku shafamin lafiya "
Waro ido dukkansu sukayi Nafisat da tazamo kamar gunki tace "dady wannan yarinyar wataran zata kashemu kaf ɗinmu "
Babu wanda yayi magana sai dady dake jero mata tambayoyi .

Zuwa dare bayan an Nany ta gyara gidan tsaff tasa turaren wuta ƙamshi ya gauraye ko ina ,Delu ta fito tana ɗan rangwaɗa tace "ke maza yimin miyar daddawa "
Nany kam bata san meye daddawa ba sbda batajin su momy suna yawan ambaton sunnan abun ,tace " meye kuma daddawa i dont know "
" Idi yana gidan uwarki !no kuma kinkira sunan nonon Uwarki badai na uwata ba dant kuma dalilin daga ƙauye na fito hatsabibiya " Delu ta ƙarashe magana tana harar Nany ,
Yau kam gidan babu wata walwala hatta momy dan dole take kula Delu gudun kar abinda ya afku ya sake afkuwa ,kowa a ɗakinsa yaci abinci Delu kam kitchen ta shige taci abinda ranta keso ta fito ta dawo ɗakin Nafisat da tarigada tayi magrib time ɗin isha'i yayi ta kwanta .
Zama Delu tayi kan wata ƴar kujerar roba dake ɗakin A fili tace "bazanyi sallah yanzu ba sbda kaina a cunkushe yake da zunubai kardai ma in kwanta in ace na mutu bana nunfashi kuma wuta za'a kaini ko ? waigawa tayi taga Nafisat na bacci harda munshari ,taci gaba da cewa "zan haɗa mangariba da isha'i da asuba sunfi zumunci sbda duk ƴan uwan juna ne "
Sai kuma ta miƙe tana zagaye ɗakin tana cewa "toni da nace inason waccan mugun anya auranshi bazai karya abun ba kuwa ? tabbas zai iya karyawa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment