Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na bige waccan yarinyar banci abincin kirki ba "Hajja B tayi murmishi kana tace "ya kamata ka sami wani abu kaci , Nany! Nany! "Hajja B ta ƙwalawa ƴar aikinta kira wacce zatayi sa'ar Delu , da gudu ta shigo tare da sunkuyawa tace "gani "cikin bada umarni Hajja B tace "asamawa babana abinci mai kyau " angama "wacce aka kira da Nany tace "tare da miƙewa taje gaban MK ta gaishesa ta wuce kicin.
MK na fita Delu tahau bincike ko ina bincikawa take , drowa ta buɗe tana ƴar rawarta , abinda ta gani a ciki ne yai matuƙar razanata ta daka tsalle tare da hayewa gado tana ci gaba da tsalle tana ihu mai sauti tana cewa "gurguwa ki taimakeni yaya bature ka taimakeni naga abinda yafi ƴarfin ƙwaƙwalwata ".
Hajja B ce ta farajin ihun Delu tace " babana naji kamar kuka kuma ina tunanin na yarinyar nan ne ",
A hankali MK ya miƙe cikin takunsa na ƙasaita ya nufi ɗakin da yakai Delu , ya tura ƙofa ,yana zuwa yaganta tana tsalle tana yarfe hannaye ,bata ma san ya shigo ba ,
Tsawa ya daka mata wacce takejin tana barazanar toshe mata dodon kunne .
A hankali yace "nitsu nan ba ƙauye bane bama buƙatar hayaniya ,menene ?"
Da sauri Delu ta nuna drowa tare da ƙara ja da baya , MK yaje da zafin nama ya buɗe drowar tare da kallon kayan ciki yace "to ai banga komai ba "
Da hannu Delu tayi masa nuna tace "bagashi nan ba yana turo baki "
Duk da shiɗin bamai yawan dariya bane yafi yin murmishi amma sai da yayi dariya sosai kafin yace "yanzu ke wannan teddyn kike tsoro ?"
Hawaye shaɓe-shaɓe a idon Delu tace "wlhi bana ƙaunar gani "
MK ya rungume Teddyn tare da ficewa dashi yana dariya ,
Yana fita ta share hawayenta ta kwanta gabanta na dukan uku-uku.
(A ƘAUYE)
Har magriba tayi Barira bataji ɗuriyar Delu ba ,cikin damuwa da tashin hankali ta fice daga gida ta nufi inda ta aiki Delu niƙa .
Sallama tayi kana ta tambayi mai ingin ko Delu ta kawo niƙa nan ?.
Girgiza kai mai ingin yayi kana yace "gaskiya batazo ba sbda tun safe yana gurin.
Tun Barira na shiga gida-gida har ta koma gonaki neman Delu amma shiru, data gaji da yawo ta dawo gida ta rushe da kuka tare da cewa "na shiga uku yarinya marainiya gashi ban ganta ba " bayan anyi isha'i wani yaro yayi sallama ,
Maman Delu dake zaune a kan tabarma a tsakar gida ta amsa sallamar tare da cewa "kai ko anga Delun ne ?
Yaron yace "wlhi Barira naga Delu a tashar mota ta zuwa Kano ɗazu da naje tallan gyaɗa ".
Da sauri Barira ta miƙe tare da dafe ƙirji tace "wayo Allah na ka ganta da niƙa a kanta ?"
Yaron yace "a'a babu komai a hannunta".
Barira tace "to shikenan na gode "ko aikoka akayi ?yaron yace "a'a dama nazo gaya miki ne " ya fice.
Barira kam sai bacci ɓarawo ne ya ɗauketa sbda jimamin Delu gata yarinya gashi bata taɓa zuwa Kano da ita ba .
Washe gari.
GIDANSU MUHAMMADU
Tunda labari yazo masa akan cewar Delu taje Kano ba'asan inda take ba ,ya kasa ci da sha sbda tunanin halin da zata shiga ,
Da Azhar ya haɗa kayansa a buhu ya fito tare da shiga ɗakin Innarsa , samunta yayi tana sallah ya nemi guri a kan wani buhun shinkafa dake gefe ta kusa da bayan ƙofa , bayan tayi sallama ta shafa adu'a ta kalleshi tare da cewa "wannan uban kayan daka loda a buhu fa ina zaka ? gaban inna ya dawo tare da cewa "dan darajar iyayenki inna ki barni inje Kano nemo Delu ,Inna kinsan fa mariniyace mahaifinta.."dakata Muhammadu !kace sun gama min dakai ,soyayyar taku kai da ita har takai ga sadaukar da rayuwa? , to sadaukar da rayuwa mana ,da har zaka wani dinga yimin ƴar murya akan inbarka zuwa Kano ,to idan kaje gidan ubanwa zaka dosa ?eh nace gidan ubanwa zaka ?! kan Muhammadu a ƙasa yace "Inna kiyi haƙuri ki barni dan Allah wlhi zan iya mutuwa".
Saukar mari yaji a kumatunsa tasss wanda ya gigitashi da sauri ya miƙe tsaye tare da dafe kumatunsa ya kalli Inna yaja buhun kayansa yayi waje.
Ɗakinsa ya shiga ,wanda yake ɗauke da katifar yayi gefe kuma gatari ne da lauje sai buta dake kusa da randar ƙasa.
Dafe kansa Muhammadu yayi banda hoton fuskarta babu abinda yake gani ,daya buɗe ido sai yaga kamar zai ganta ,da sauri ya tashi tare da ɗaukar buhun kayan ya fice ba tare da yaje ɗakin Innar tasa ba .
Sai da yayi nisa sosai yama kusa zuwa tasha yaci karo da Haladu yana tafiya akan keke , har zai cigaba da tafiya Haladu yace "Muhammadu tsaya muyi magana "
Cak Muhammadu ya tsaya Haladu ya ƙaraso inda yake yace "ina Delu ?" Muhammadu na shirin magana Haladu yace "ku yi masa jina -jina shine silar ɓatan matar dazan aura"
Cikin ƙanƙanin lokaci sukayi masa lilis ko tashi baya iyayi karku manta ,hausawa sunce sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi , sai uban nishi yake , Halatu da tun tuni ya riga yabar gurin suma wanda suka daki Muhammadu suka watse ,
Har akayi la'asar yana gurin a kwance ko motsi baya iyayi .
Malam Usaini ne yazo wucewa yaci karo da Muhammadu kwance cikin jini ,a tsorace ya fara cewa "innalilahi wa inna'ilaihir raji'un "ya juya da gudu tare da ƙwalawa mutanen da suke zaune a bakin wani shago nesa dashi kira ,cikin sauri suka taso su biyar tare da zuwa gurin malam Usaini , nuna musu Muhammadu yayi yana kuka "ɗaya daga cikinsu yace "aje a kaishi asibiti jini na zuba "malam Usaini yace "a'a maganin gida za'ayi masa zaifi naga jini ya zuba da yawa "wani a cikinsu mai suna Jabir yace "baba Usaini so samu akai bawan Allahn nan asibiti "
Kasancewar shi Jabir yayi karatun boko mai zurfi .

Malam Usaini yace "kull ba boko mukeso a nuna mana ba ,kayan yahudu mai zuƙe jinin bil adama meye asibitin sukeda shi wanda mu bamu dashi ?"
Wani ana ce masa Garzali yace "baba mallam Usaini kodai bakason biyan kuɗin asibitinne ?...!
Masu comments nagode

😍😍😍
*Ina kuke masoya littafan mom islam wacce ta saba nishaɗantar daku a zafafan littafanta , to yauma gashi tazo muku da bajakolin ƙarshe shekara,zaku sami documents na littafanta cikin rahusa*
YARINYA MAI TAƁARGAZA (400 )1,2,3

SIRRIN ZUCIYA 1&2 (300)


ƘANIN UBA (200)

MACEN SIRRI (200)

Ga mai so zata iya yimin magana ta numberta 08141799224 karku manta siyan nagari 😘.


MOM ISLAM

🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂



*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_



Wlhi ina ganin comments d'inku a grp-grp godiya nake Allah yabar zumunci🙏

Page 11-12


Malam Usaini bai ƙara saurar masu magana ba ,aka wuce da muhammadu gidan Inna.

Tana zaune a tsakar gida taji ana cewa ku kauce a shigo dashi ,

Sam batayi tsammani ya fita ba ,sai gani tayi an shigo da mutum jini na ɗiga.

Ajiye Muhammadu sukayi a gabanta tare da cewa "a hanya muka ganshi a haka "
Wani dake riƙe da buhun kayansa ya ajiye gaban Inna .
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga fuskar Inna ,tasa tafin hannunta ta share tare da cewa "haƙiƙa saɓawa maganar iyaye bata da amfani ,ni da kaina nace ya haƙura ban amince yaje Kano ba ga abinda gardama ta haifar "
Malam Usaini yace "yanzu kam duk ba wannan ba kai Garzali jeka gidan malam Aminu kace ya baka rubutun da nayi masa bayani "Garzali na shirin fita yaci karo da yaro da gora a hannunsa da ƙullin magani ,nan aka shiga bashi da kuma barbaɗa masa a ciwo .

KANO

Washe gari da ana kiran sallahr asbha Delu ta tashi taje toilet ta kunna famfo tare da yin alwalah , rawa ta hau yi tana cewa "wlhi mai korata a gidannan sai ya shirya ,sukam ko wuyar jan ruwa da guga basayi taɓɓ ,fitowa tayi ta shimfiɗa darduma tare da cewa "astagfirullah , karatun sallan ma ba wani iyashi tayi sosai ba , sai mis mis mis kawai take cewa har ta idar ,
Nany ce ta shigo hannunta riƙe da bokiti da abin yin mopin tace "barka baƙuwa ni sunana happiness "dariya Delu ta sheƙe da ita tare da cewa "ke nifa ko baki faɗa ba nasan sunanki amma na ƙarya kika faɗamin ko ?nasan na asalin LAMUNDE ne koh? waro ido Nany tayi kana tace " true wlhi "Delu tace ko kuma Lantana dan wannan kwaya kwayan zanen fuskar taki sai wannan sunan ga sharɓeɓen leɓe da kikedashi hanci kamar na saniya "
Tasss Nany ta wanke Delu da mari tare da cewa "ke baki da kunya ne ?wlhi zan gyara miki zama duk da banajin hausa sosai nasan duk abinda kike faɗa "da gudu Delu ta taho ta cakumo wuyan Nany tare da cewa "inba tsoroba muje filin kaci uwaka wlhi sai kin dawo da fasashen baki "

Sallamar da taji ne ya sata yin shiru dan ko ba'a faɗa mata ba tasan shugaba ne.
A nitse ya kalli Nany kana ya kalli Delu yace "meke faruwa naji hayaniyarku ?da sauri Delu tace "wlhi cewa "tayi wai nayi kama da arniya kuma wai ni aljana ce shiyasa tunda nazo ba'a kaini ko ina ba...!

😂😂😂😂

Afuwan nasan yau na ɓata muku rai typing babu yawa ,wlhi bamu da nepa ne Pls kuna raina.

MOM ISLAM
🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂



*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_



Page 13-14


MK yayi murmishi wanda ya baiyanar da dimples ɗinsa yace "Nany maza ki kama aiki ke kuma wama kikace sunanki ?"

Murguɗa masa baki Delu tayi kana tace "gurguwa sunana"

MK da bai fahimci abinda take nufi ba yace "ke ina wasa dake ne ?
Ring ɗin da wayarsa tayi ne ya sashi katse ragowar maganar da yake shirin yi mata ,ya zauna a kan gado tare da amsa kiran ,a speak out yasa .
Yace barka da safiya habibiyata uwar ƴaƴana nasan kina nan kina tunanina ko ?kinga jiya ban kiraki ba "
Daga can ɓangaren wace yake waya da ita tace "haba my man wlhi sam hankalina ya kasa kwanciya amma yanzu komai normal dai ko ?",

Eh MK yace .

Budurwar tace "yanzu kana ina ne ?"

Kallon ɗakin da yake yayi kana ya kalli Delu da Nany ya rufe musu baki tare da gimtse fuska yace "ina Abuja ne dadyna ya turani wani aiki kinsan bashi da lafiya "

Cikin ɗaga murya Delu tace "ke wlhi karki yarda yana Kano shine ma ya bigeni a mota in gaya miki gashi a ɗakin gurguwa wata fara lutiya mai baƙin baki ƙilama taba take...bupp taji an bige bakinta tare da wanketa da kyakkyawan mari , Nany da jikinta yaɗau rawa da sauri ta gama gyara ɗakin ta fice zuwa ɗakin Hjja B .
Dafe kumatun ta Delu tayi kana tace "Allah ya isa ban yafeba wlhi sai na rama bakasan inkiyata bane a ƙauyenmu to sunana *DELU HATSABIBIYA*
MK da tuni ya riga da ya kashe wayarsa ya riƙe hannun Delu sukayo palo ya kaita gaban Hajja B yace "yau ɗinan wannan yarinyar sai tabar gidannan ".
Hajja B tace "kaifa ka kawota ya za'ayi kace tabar gidannan bacin tace ita marainiyace ?"
Dafe kansa MK yayi cikin faɗa yace "Hajja B ki gafarceni gaskiya nayi ganganci sbda ko binciken danginta banyi ba na kawota gidannan ni kar azo ma aljana ce ko maiyya tacinyemun ke cikin dare ".
Zaro ido Delu tayi tare da cewa "dani maiyya ce ai kai zan fara cinyewa tunda kasani a gaba kamar wuta da auduga "
MK yace "Hajja B kinji ko ?batada tarbiya ko kaɗan wlhi nayi dana sani amma ko yanzu ma bata ɓaci ba ,

Ya ruƙo hannun Delu dake kuka tana shure-shure yace "tashi muje "
Dakatar dashi Hajja B tayi kana tace "yanzu idan muka barta ta faɗa wani gurin bamusan rayuwar da zata fuskanta ba ,tunda dai ita marainiyace mu riƙeta da aminci bakomai yarinya ce gaba zata gyara.
Fakar idon Hajja B Delu tayi tayiwa MK gwalo tare da ƙara fashewa da kuka tace "nagode Hajiya Allah yabaki lafiya kamar kowa Allah yasa kishiga aljannah kuma insha Allah gobe da yardar Allah zaki taka da ƙafafunki "
A razane MK ya kalli Delu shida Hajja B cikin haɗa baki sukace kina bada magani ne ?
Girgiza kai Delu tayi kana tace "Babana ne yake badawa nidai ina tayashi ne "
MK yace "ke bamason surkulle "
Hajja B tace "babana ka ƙyaleta duk abinda Allah yayi duk mai kyau ne "
A zuciya MK ya fice sbda gani yake wannan Delun kamar aljana take.
ƘAUYE
Barira taci kuka ta godewa Allah dan tasan ko babu komai Delu waraka ce ga duk mutanen ƙauyen amma mai yasa ta zaɓi tafiya ta barsu gashi mahaifinta baya raye ?
Ƙara fashewa da kuka tayi , kowa yazo yi mata jaje sai yace ta rage kuka ta cigaba da adu'a amma ta kasa sbda tsananin damuwa data shiga.

Tunda su Haladu suka yiwa Muhammadu duka suka bar gari , dama bawai son Delu yakeyi na haƙiƙa ba ,kawai dai yana son wani abu a gurinta ne ,yasan komai daran daɗewa Muhammasu zai iya faɗar gaskiya .
Alhmdulilh Inna ta faɗa ganin Muhammadu ya fito sallahar asbha ko ɗingishi bayayi , Inna tace "a dawo lafiya Muhammadu na insha Allah zasu haɗu da gamonsu da yardar ubangiji".
KANO
Zuwa dare Hajja B ta kasa bacci gashi har ƙarfe 11:pm idonta ko alamun jin bacci beyi ba ,maganar Delu keyi mata amo a cikin kunuwanta,da rake cewa "da yardar Allah gobe zaki taka da ƙafafunki "tashi zaune tayi a fili tace "babu inda bamuje ba akan ciwonnan munje india munje egypt makkah kai garuruwa dai barkate sun tabbatar mana da babu tabbacin gyaruwar ƙafata sai Allah.

MK ma a nashi ɓangaren idonsa biyu dan tunani maganar Delu yake , sbda idan har Hajja B ta warke to zai yiwa Delu muhimmiyar kyauta ,idan kuma aka sami akasin hakan to wlhi na lahir

a sai yafita jin daɗi ,sbda sai ya wahalata fiye da tunanin mai tunani ....!


Tofa wasa farin girki akwai gwarama a gaba ya kuke gani , anjima zanyi typing insha Allah zuwa ƙarfe 4:pm


MOM ISLAM
🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂



*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_



Page 15-16

Washe gari

Da sassafe bayan anyi sallahr asbah da misalin ƙarfe 6:50am , MK ya shiga ɗakin Hajja B da sallama , samunta yayi zaune akan sallaya tana adu'a ,zama yayi a gefen gado tare da cewa "yaro man kaza "bayan Hajja B ta idar da sallah ta kalli MK kana tace "babana ka shigo kenan ? eh MK yace tare da cewa "ya ƙafar dai ? Hajja B tace "to alhmdulilh ta miƙe tsaye ta tako har zuwa inda yake ,rufe ido MK yayi ya buɗe ya kuma rufewa ,a ganinsa kamar bada gaske bane ,dan tafiyar Hajja B ta koma kamar wacce bata taɓa ciwoba ,hawayen farinciki ne suka zubo a fuskar MK yace "Hajja B kin warke "Hajja B tace "todai gashi da izinin ubangiji ina tafiya tunda na kwanta naji kamar ana jamin ƙafa ,dana tashi sallahar asbha naji ƙafar ta miƙe "da gudu MK ya fice ya nufi ɗakin da Delu take ,kasancewar yana cikin farinciki ya sashi dukan ƙofar ta ɓuɗe ,jin haka yasa Delu tashi zata gudu taji ya cafkota tare da cewa "dama haka kike kodai keɗin aljanah ce ?anya ke mutum ce kuwa ? Delu da ko sallahar asbha batayi ba ta galla masa harar kana tace "ka mance dodo ceni ka wani dami mutane kai da kakeson inbar gidanku ai wlhi sai na rama " MK yakasa jin haushinta yace "taso muje in siya miki duk abinda kikeso kokuma bari sai zuwa anjima "
Taɓe baki Delu tayi kana tace "wlhi idan ka ganni a lahira maza suka kaini ba mata ba ,da hankalina in bar wannan aljannar duniyar wlhi kome za'ayi bazan fita a gidannan ba garama a ƙyaleni " MK yace "kyauta zanyi miki ta musamman sbda kin samu farinciki saura su momyna da Nafisat suzo su tayamu "
Delu kam batasan inda zancen nasa ya dosa ba tace "uhm oho dai nan gani nan bari gidane bazan fita ba"
Tsawa MK ya daka mata tare da cewa "naji bazaki fita ba amma kizo Hajja B na kiranki "
Miƙewa tayi tare da rufe gwaguyayyen kanta tace "nifa banason sa ido ku haka kuke da kunga ƴan mata ku wani dinga yi musu murmishi sai kace kunga ranar auranku " MK kam dariya ce ta suɓuce masa harda riƙe ciki yace "kekam sometimes baki sanin abinda kike cewa naga alama "
Au ka mayar dani mahaukaciya kenan wlhi yau sai nasaka gwale-gwale .
Gimtse fuska Mk yayi sbda yana ganin yawan sake fuskar da yake yimata ne yasa take faɗa masa magana iya san ranta .
Muryar Hajja B sukaji na cewa "babana ina yarinyar baka kirata ba "
Caraf Delu tayi cikin sauri sbda kar MK yayi magana ta fashe da kuka tare da cewa "ka mareni wlhi kaida gurguwa "
Hajja B da kejin abinda Delu take cewa tace "ai na zamo mai ƙafafu "ta tako har zuwa ɗakin tana murmishi .
Shafa kan Delu tayi kana tace "tabbas akwai wasu sirruka dake tattare dake masu yawa amma kafin nan menene asalin sunanki ?
Cikin nuna damuwa Delu tace "dama nace insha Allah zaki taka sunana kam bazakujishi ba kalan azo nemana za'a kasheni wannan , ta nuna MK tace "wannan ya nunani "
Waro ido MK yayi kana yace "yau saikin bar gidannan ba sirri ba ko menene sai kin bar gidannan zamanki bashi da amfani "
Hajja B tace "ku dakata ke yarinya wannan ,ta nuna MK tace ya zamo yayanki ke kuma banda raini nagode miki gaskiya ke alkairi ce a tare damu , inane ƙauyenku?..!
Delu kam taga tasku tunda yanzu an fara bibiyar garinsu da sunanta tace "Hajiya nifa bani da gari wlhi idan kukaci gaba da matsamin cikin ikon Allah ƙafarki zata karye dan haka komai kukaga nayi ku ƙyaleni inba hakaba ,kamar inda Allah yasa ƙafar ta gyaru haka zata karye "waro ido Hajja da MK sukayi tare da cewa eyeee kiyi haƙuri muntuba " Delu tasa dariya tace "yau so nake kuyimin tuwo miyar kuka ke Hajiya kiyi miya shi kuma wannan me tafiyar matan yayi tuwo wlh kuyi sauri ko in karya ƙafar...!



MOM ISLAM

[3/19, 5:49 PM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂



*Zainab Habib(Mom Islam*



_Elegant online writers_



Page 17-18

Harara MK ya galla mata tare da cewa "ke bafa tsoronki akeji ba ni kinga tafiyata gidanmu Hajja B kici gaba da kula da ita wlhi bazan iya ba "
Ruƙo hannunsa Hajja B tayi kana tace "babana kaima taimakon kanka ne idan kayi aure basai kasha wuya ba "
Tuntsirewa da dariya Delu tayi kana tace "zan bika gidanku "
Waro ido MK yayi tare da cewa "muddin na sake kikaje gidanmu sunan danginmu matattu "
Fashewa da kuka Delu tayi lokaci ɗaya ta kalli Hajja B tace "Hajiya kinajin abinda yayana ke faɗa "
Shiru Hajja B tayi taja hannun MK suka wuce kitchen ,
Nany da tun ɗazu ta gama aiyukanta ta kwanta ,tanajin motsi a kitchen ta fito kasancewar ɗakinnata a jikin kitchen yake "sannunku Hajiya "Nany tace tare da tambayar suna buƙatar wani abu ne ? harara MK ya galla mata tare da cewa "ke kauce ki bamu guri bamason gulma "sum-sum tabar wajen.
Gas biyu Hajja B ta kunna tare da ɗora ƙananan tukwane lamba biyu tasa MK ya zuba ruwan zafi a ɗaya ,ita kuma ta markaɗa kayan miya ta soya manja ta zuba kayan miyar da su maggi da daddawa da , MK na tsaye ruwan ya tafasa Hajja B ce tayi masa talge ko kallon gurin beyi ba ,ji yake kamar yana shiga ɗakin Delu ya shaƙeta ta mutu , har talge ya dahu Hajja B ta tuƙa tuwo ta ƙada miya ,bai sani ba yana ta tunani ,sai ji yayi ance "miƙomin leda in kwashe, zaro MK yayi tare da cewa "harkin gama ne ?"
"Eh"
Hajja B tace a hankali tana gudun kar Delu taji aikinsu ya koma baya , bayan ta kammala komai tasa MK ɗaukar tuwo ɗaƙyar ya ɗauka sai da ta nuna fushinta sosai ,ita kuma ta ɗauki miya suka kai mata,suna shiga suka sameta tana ƴar gala-gala tana waƙa , Hajja B tace "ƴar albarka gashi "
Batare da Delun tace "komai ba ta karɓi na hannun MK ta ajiye ta karɓi na hannun Hajja B ta ajiye tace "sannunku "
Har MK zaiyi magana sai ya fasa .
Zasu juya wayarsa tayi ring a hankali ya ciro wayar daga aljihu tare da dannawa ya kara a kunnensa ,sallama yayi tare da cewa "momyna yau insha Allah ina nan zuwa ,wai Hajja B ta gaya miki ƙafarta ta gyaru kuwa ?cikin murna momyn tace "mun fara magana da ita jiya muma yau zamuzo "
"No karkuzo Hajja B bata nan taje anguwa sbda da wuri ta fita "
"Okay "
Momyn tace "sai mu bari zuwa gobe insha Allah "
Ya ajiye wayar.
Hajja B dake kallon MK tace "babana ban sanka da ƙarya ba meyasa zakace bana nan ?"
Dafe kansa yayi kana yace "wannan masifar wallahi ita tasani ƙarya idan momyna tazo zata iya juyar musu da hankali shiyasa ,kinga kafin gobe zan samo mafita "
"Yau za'ayi bura uba "
Delu tace tana ɗaure ɗankwalinta a kwankwaso .
Hajja B ce tace "ƴar albarka me ya faru ?Delu tace "duk halaccin da nayi miki Hajiya akan gyara ƙafa shine kika bari yana kirana da masifa ?"
Rungumota Hajja B tayi kana tace "kiyi haƙuri sam bai iya magana ba kuma ma dai yaro ne "
A fusace MK yace "Hajja idan kika sake ganina a gidanki kiyimin abin da kikaso ya fice ransa a ɓace.

Kai tsaye motarsa ya buɗe tare da zama a mazaunin driver , yanzu nema yakejin hankalinsa bai gama kwanciya da yarinyar nan ba ko kaɗan ,
Cikin fushi yaja mota yabar gidan .
Hajja B kam takasa cewa komai ,tana tsoron tayi magana ran Delu ya ɓaci karya ƙafa .
Bayan Hajja B tabar ɗakin Delu ta sauka ƙasa ta mimiƙe ƙafa ta fara zuba lomar tuwo , sai da taci tayi nak sannan ta miƙe tana tura ƙirji ta nufi palo ,
Tana zuwa taga Nany na zaune a ƙasa tana kallo a tv tace "ke tashi kihau kujera " Nany tsintar kanta tayi da cewa "to sbda itama tsoro take kar a ɓalle mata ƙafa ,kalle-kalle Delu ta fara ta hango fridge tace "ke wannan meye ?Nany tace "abin ajiyar ruwan sanyi ne "da sauri Delu ta isa gurin fridge ta buɗe , ganin drinks kala-kala yasa Delu cewa "munafuka ai ba iya ruwan sanyi bane a ciki da zanenki kwaya-kwaya kamar an tsaga da kifiya "Nany dai batace komai ba
Delu ta ɗauko faro ta ɗauko viju ta ɗauko pepsi ta lodasu a gefen zaninta ,tace "wlhi idan kikaji ana cigiya kikace nice daga yau kin gama zama a gidannan "
"Bazan faɗa ba Nany tace "

Driving MK yake amma hankalinsa na gurin momynsa ya matsu yaje ya gaya mata masifar dake gidan Hajja B .
Ring wayarsa tayi ,ya ɗauka tare da karawa a kunnensa yace "momy gani nam zuwa fa "
Daga can ɓangaren momyn tace "ai Hajja ta kirani ɗazu tace wai wasa kake tana nan shine muka taho nida Nafisat yanzu haka ma muna bakin get".
" Whattt!!!"
MK yace tare da juyo da akalar motarsa ya fara sharara gudu ....!


Kuyi haƙuri kunjini shiru fans


*Ina masoyana 😍ina mai yi muku albishir da zazzafan littafina mai cike da darrusa da nishaɗi kana da kuma ban dariya bugu da ƙari soyayyya mai sanya zuciya cikin farinciki ,dama gareku masoyana ,littafin na nan fitowa bayan sallah insha Allah ,kada ku bari a baku labari littafin shine SAHIBUL AMRAT*.


MOM ISLAM
[3/20, 3:50 PM] Mom Islam Ce: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂



*Zainab Habib(Mom Islam*


Masu kirana da masu comments Allah yabar zumunci 😘

_Elegant online writers_




Page 19-20
Lokacin da yakai bakin get ɗin gidan Hajja B baiga kowa ba hakan ya tabbatar masa sun shige ciki , sitiyarin motar ya daka tare da cewa "na shiga uku temako na nemam halakani zata iya haɗamin masifa a gurin momyna "
Fitowa yayi ya buɗe get ɗin kana ya koma cikin mota ya shiga gidan , bayan yai parking ya shige da gudu har yana shirin faɗuwa , sallama yayi har zai wuce yaji maganarsu a gefensa sbda idanunsa sun rufe ba sosai yake kallon abin dake gabansa ba " Hajja B ce tace "ɗan saurayi ka dawo ?"hararta MK yayi kana yace

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment