Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Auwal, yanzu na girma na fahimci illar yin haka gareni,,shikenan na fahimta kin amince da zarar mun koma lagos na nemi aurenki agurin abi tayi shiru ta kasa cewa komai "kice wani abu mana , Allah ne yajefawa zukatanmu soyayyar juna, tayi mugun tsaresa da ido tace "ni fa bance ina sonka so irin na aure ba fa,ina dai sonka so na 'yan'uwanta"you can't deny it muwaddat I know you love me so much ..so ki daina wahalar da kanki da soyayyarmu ,zaki aureni har ma ki haifa min ya'ya masu kama dake duk duniya idan akwai Wanda ya cancaci ki aura to muhammed Auwal ne, zaki aureni koda baki sona ni zan koyar dake yadda zaki soni, ke koma me zakiyi sai dai kiyi amman auwal shine mijin aysha ....
Yadda yayi maganar cikin karfin hali da isa yasa ta kasa daina dubansa, Auwal daban yake acikin maza har ma da sauran mutane ,yadda yake gudanar da alamuransa cike da isa da gadara sosai yake bata mamaki, da sake dilmiyar da zuciya cikin kogin kaunarsa cikin zuciyarta ,take ta shiga maganar zuci "Anya kuwa itama bazata fito fili ta bayyanawa iyayensu abinda ke ranta ba ,auren Auwal da muradi mallakarsa take so a halin yanzu ..
"Kina tunanin yadda zaki fito ki bayyana soyayata ga iyayenmu ko ?
Yayi mata tmbyr yana tsareta da idanunsa.."karki damu duk Auwal zai d'auki alakin hk ,ni zan fad'a musu muna son juna .
ta Mike tsaye "ni dai babu ruwana kuma ban aikeka ba, ta juya ta bar d'akin kugunta yabi da kallo yana lasar lips, shi kansa ya kan rasa me yasa yake mata irin wannan zazzafar soyayyar shi da mata ke bi a London suna rububibi akansa ,wani lokacin ma har da fad'a bai ta'ba tunanin sauraransu ba, amman dubi yadda ake garasa....
Mmn sudais ce....

DEDICATED TO~

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

alhamdullahi am back again.

warning!!!

for the first time !!!! i will like to say," don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ......wannan shine.


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 16


..tsaye yake acikin lanbun shakatawa na cikin gidan hannuwansa duka rungume a saman kirjinsa yana tafiya ahankali ahankali yana lumshe tsumammun idanunsa saboda sanyayyiyar iskar dake ratsa jikinsa ..
kmr ance ya bud'e idanunsa kawai yaga faiza tsaye a gabansa tana fuskantarsa cikin mayunwacin halin da shi kansa bazai iya misaltawa ba,
ya d'an tsura mata ido yana Kare mata kallo na wani lokaci , sam itama bata da munin da zai kita, sai dai shi sam baya jin sonta acikin zuciyarsa, dan matukar muwaddah na rayuwa a doron kasa ba zai iya rabar wata mace da sunan soyayya ba, bare aure,tsawon minti goma suna haka sannan ya juya ahankali ya soma d'aga zara zaran yatsun kafafunsa cikin isa da izza ,tabiyo bayansa da sauri tana kiran sunansa yaya bunayya! yaya bunayya !!"dan Allah ka tsaya ka saurareni bakasan yadda nake jin zuciyata ba akanka.
ko tsayawa bai yi ba bare ya nuna alamun amsawa kuma tabbass tasan yana jinta tayi saurin tarar gabansa tana ware masa hannuwanta duka "wai yaya bunayya me yasa kake min haka ne?
"me yasa kullun kake tsanata kiyayya gareni?
"ina da komai da za'a so mace dan shi ,to me yasa ni bazaka soni ba? tsayawa yayi kawai yana kallonta tmkr bai santa ba bare wata danganta dake tsakaninsu illa dogon tsakin daya jaja da karfi yabi gefenta ya wuce tayi saurin riko laulausar tafin hannunsa cikin karfin hali wanda hkn datayi yasa har taji wani azababben ciwon kai ...

cikin wani irin tashin hankali ya daka mata tsawa "kina hauka ne da zaki rike min hannu?"ko kin fara shaye shaye ne bansani ba ?
cike da kuzari da karfin zuciya tace " an rike maka hannu me zakayi?
" muhammed auwal bari na gaya maka lokaci yayi da tsawarka ta daina firgitani ,lokaci yayi da kowa dake cikin danginmu zasu san abinda ke tsakanimu da kai ......
tasss tasss taji ya saukar mata wasu gigitattun maruka har guda biyu akan fuskarta "ki kyaleni faiza ...ki rabu dani faiza, tunda nace ki kyaleni ,ki kyaleni mana ko ana so dole ne?
in soyayya ce nace bana yi ana so dole ne?
bari kiji daga yau karki sake takura min akan wannan shirmen saboda bana sonki bana sonki ba kuma zan ta'ba sonki ba ..yana gama fad'ar hk ya juya fuuuuuuu a fusace ya kalleta anan .

tabi bayanshi da kallo fuskarta cike da tsansar damuwa da nadamar rike masa hannu datayi watakilla da bai kai hannunsa jikinta da sunan mari ba, hawayen dake boye acikin kwarnin idanunta suka samu nasarar gangarowa bisa kuncinta, tasa hannu ta goge wasu na sake zubowa cike da matsanancin sanyi jiki ta bi hanyar baya dan kar wani ya ganta cikin damuwa ,most especial aunty'nta muwaddah wacce kwata kwata bata kaunar ta ganta cikin damuwa, koda faiza ta shiga d'akinta sai ta rushe da wani tsumammen kuka ,kwantanta damuwar data shiga baya fad'uwa duk yadda take tunanin M. A ya wuce nan,, ya wuce da tunaninta sam ba itace agabansa ba, "to ita yanzu ya zatayi da rayuwarta.. ?
"hakika bata san yadda rayuwarta zata kasance nan gaba ba matukar M. A yaki amincewa da soyayyarta ,"shin me yasa bazai sota ba ya rabu da aunty'nta tunda itace daidai shi ba muwaddah ba?
har yammanci rana tana kwance a d'akinta taki fito dan batason kowa yasan halin datake ciki ..


zaman M. A a gidan yasa faiza ta nemi takurawa rayuwarsa ,dan kuwa baya samun damar ke'bewa da sanyi idanunsa yadda yake so, duk abinda yake idanunta na kansa ,dan hk a daren ranar daya cika sati biyu da zuwansa ,ya kudurci a niyyar komawa lagos a washegari , lokacin da yake sanarwa dady zance komawarsa tana gurin, aiko taji haushi ma ganarsa, taji tmkr ta d'aura hannuwanta duka bisa kanta ta rusa ihu ne dan bakinciki tunda tasan saboda ita yasa zai koma.. ranar dai bata samu ishashen baccin kirki ba sbd tsananin tunanin M. A.
tun da garin Allah ya waye yasa awanke masa motarsa .
yayinda shi kuma yana can makale da muwaddah yana romacing dinta da sunan sallama ,yaso kwarai su koma tare ,amman taki sai daya gama tsotse mata baki da laguda mata jiki zuwa kirjinta sannan ya barta ya d'auki hanyar birnin iko..

da daddare suna zaune su duka a parlour'n dady ban da faiza dake kwance a d'aki cikin bargo tana fama da zazzabin tafiyar M. A ,ana cikin hira ala'meen ya shigo gayar da dady Wanda kaida ne kullun daren duniya zai shigo gurin dady su gaisa kmr yadda yaga yaya akram nayi, ihsan tace" yaya ala'meen d'azu na hau samanka ban sameka ba ,nayi zaton ko zance ka tafi gurin latifa ya cilla mata muguwar harara "to idan can naje sai me kin ganki ko mumy ... ,wallahi da ba dan ke din mai sunan mahaifiya bace dana shuka miki rashin mutunci yau..
Suka kwashe da dariya "ai kuwa da munganku arana inji cewar eiman ...
ihsan tace "bama za'a ganmu arana ba ,daman sako zan bayar ka kai mata,"sai ki bari idan zani ,eiman tace yaya ni kuma ina son zuwa gurinta ta min lalle da kitso , ala'meen yace "Allah idan kuka dameni da zancen wata latifa zan mazgeku yanxu, kun ji min yara da tonon silili kowa sai yasan da wata latifa..

suka sake kwashewa da wata dariya har dady ,wanda cikin dariyar yace ",ku rabu dashi zan sa direba ya kaiku sai kuje har muwaddat itama ta gano gari ala'meen ya dubi inda take zaune tana waya ,magana take kasa kasa a waya Amman babu mai jin abinda take fad'i ,saboda a hankali take magana ya tsura mata idanunsa yana kallonta yana magana da kannenta, kallo daya tayi masa ta d'auke kanta tare da gaisheshi ",ina yini maimakon ya amsa gaisuwarta sai yace ya zaman bakunta ?"lfy tace akaitace bai sake cewa komai ba ya samu guri ya zauna yacigaba da kallonta .

M. A datake waya dashi yace "Halan wannan tsohon mayen ne ?"nifa Allah zan masa rashin mutunci akanki dan me zai dinga shiga tsabgarki, kema har da wani gaishe shi ya k'arasa fad'ar mgnr yana Jan tsaki"cool dawn kanina babu komai fa atsakaninmu, ka cire zargi zuciyarka "karka manta shi da kai duk abu guda ne agurina kmr yadda zan mutuntaka haka yazama dole na mutuntashi sannan na girmama shi ...
"tsaki ya ja " ki shirya next week zanzo in tafi dake sannan ya kashe kiran ..
Tayi shiru ta d'ago idanunta ahankali suka had'a ido da ala'meen yayi sauri kawar da fuskarsa gefe yana cigaba da hirarsa "hanyar d'akin ta nufa kar dai zargin Auwal ya tabbata al'amen sonta yake ?

"kai impossible hakan ma bazai ta'ba yiwuwa ba ,shi da yake da matar da zai aura ..shi kuwa al'ameen binta yayi da wani shu'umin kallo zuciyarsa na sake bun kasa da soyayyarta da tayi masa kamun kazar kuka .


Washegari da safe bayan an gama kalaci duk yaran gidan suna parlour'n mumy ,dady ya shigo gabad'aya yaran suka kaceme da hayaniya, kowa da abinda yake fad'i muwaddat ce kawai tayi shiru ta kama kanta saboda tun jiya da M. A yayi fushi daita akan yaya ala'meen ta rasa samun kwanciyar hankali da natsuwar zuciya dady ya dubeta yace "muwaddat ki shirya direba ya kaiki yawo ki d'an ga gari eiman tayi saurin cewa "Amman dady har damu ko? Dady yace da dai kun bari an kaita ita kad'ai idan kuka fita tare zaku dameta da hayaniya" kai dady yau fa week ce babu makarata kabarmu mu fita tare itama zatafi jin dadi ko aunty ?
Kafin muwaddat ta bata amsa dady yace "ko babu makaranta malamin lesson dinku zaizo an jima ..

Ana cikin haka sai ga ala'meen yashigo a shirye cikin shirin fita ,t shirt ce ajikinsa da bakin wando jeans, dady yace" yauwa tunda yayanku yau yana gida bama sai na had'a muwaddat da direba ba ,ala'meen ga kanwarka nan ka d'an fita daita taga gari, Dan tun zuwanta ba inda taje .


Ala'meen yayi shiru yana kallonta soyayarta na sake huda zuciyarsa, yana da inda zashi Amman hakan bazai hanashi bawa wannan fitar mahimmanci ba ,
Cikin rawar jiki yace ,"to dady ta shirya mana ai sai mu fita ya kalli eiman " fushin me kike yi ?


ihsan tace "wai Dan dady yace ba damu za'a je ba saboda lesson din zaa yi mana , alameen ya harari eiman "ai ko babu lesson bazaki shigar min mota ba sai dai ku fita direba ..

Dady yayi murmushi" wai me ke had'aka da eiman ne sam kafi biyewa faiza da ihsan akanta?
"dady yarinyar ce bata da kunya "eiman tayi saurin cewa "wai dady Dan akan aunty Ltifa tayi min waya ta tambayeni yana gida shikenan tun lokacin ya tsaneni ,dady yace to kai meye abun jin haushi ba kai da kanka ka nuna kana sonta ba nima fa na lura a yan kwanakin baka zuwa gurinta kmr da ala'meen ya shafa sumar kansa yana murmushi "babu komai dady kawai ina hutawa zata janyo azo a dameni bayan nayi mata gargadi ko abokaina suka zo nemana karta kuskura tace ina gida sai dai idan ta tambayeni amman dayake mara jin magana ce da an xo nemana sai tace ina gida dady yace "ke eiman kinji abinda kikayi daga yanzu in ana nemansa kice yayi balaguro eiman tace "to dady ai shine yake cewa idan mutane sunzo nemansa su tambayeni kuma haka kawai sai na dinga yi karya,byn karya babu kyau ala'meen cikin wasa yace"zaki rufewa mutane baki ko sai na bubbugeki ,tayi shiru tana gunguni ya d'an waiga bai ga muwaddat yace "wai ina wace zan fita daita ne ?

Faiza tace bari na dubota tana ciki tana shiryawa tana shiga d'akin ta iske muwaddat kwance a d'akinta mamaki yakamata tace ",kai aunty ke da ake jira za ki fita yawo tare da yaya ala'meen shine kawai zaki zo ki kwanta .


Muwaddat ta d'an yatsina fuska ",nifa wallahi banason fita haka kawai ,ni bancewa dady ina son ganin gari ba A6mman dan rigima wai wani sai an kaini yawo "ko dai da yaya ala'meen ne baki son fita ?
"amman ina laifin a fita dake kiga gari tunda har yanzu bakigama sanin garin ilori ba ..

"Ke nifa ban iya fita da wannan magananne mutumin wallahi sai yasa Kan mutu ya d8auki caji Sam Sam maganarsa bata da limit "ke ina ruwanki da maganarsa ,tunda ke ba mai magana bace bare kice maganarsa ta dameki?
"Kuma ba surutu garesa ba ,wallahi idan kikaji yadda a waje ake complain din rashin kula mutane da bai yi sai kinyi mamaki agida kam ya kan 'bata lokacinsa akanmu, kuma yanzu kinga fita nashi uzurin zai yi dady ya sashi"
"Kin fahimcesa ba daidai ba shiyasa naga kin sauya fuska lokacin da dady yace ya fita dake yawo ..

"Kinga faiza banson dogon turanci kema yanzu na kula zama dashi yasa kin dawo aku kuturu , abinda za'a yi yanzu kawai kije kice kaina ke ciwo shiyasa nashigo na kwanta .

"Gasky aunty bazan iya ba kawai ki taso idan kika ki kmr kin wulakanta dady ne muwaddat ta yarda da shawarar kanwarta ta tashi ,ta sauya kaya jikinta ta shirya tsaf ta fito cikin wani had'adden material mai maseefar tsada kayan sunyi mugun kama jikinta tayi kyau sosai kana kallonta kasan yar Hutu ce ba'a kashe kudi a banza ba hatta jaka da takalmi kace domin kayan aka kerasu ta d'an yafa Gyalenta ,kana ta fito parlour'n dady ya dubeta yana driya "kai yar gidan daddy wannan irin kwaliyar haka kar fa ki gigita mutane gari gashi babanki bai tashi miki aure ba .
Ta dan yi murmushi saboda wasan da dady yake mata ala'meen kuwa idanunsa kyam akanta yana son yaga yadda zatayi magana zata ce mishi su fita ko kuwa Jan aji ba zai bari tayi mishi magana ba ,koda yake ta cancaci fiyye da hakan yacigaba da kallonta saboda kwaliyarta ta burgeshi, shiyasa sam ya kasa d'auke idanunsa akanta ,lokuta dayawa mace mai yanga tana burgeshi amman baya son Jan aji yayi yawa kuma bai fiyye shiri da shagababbiya ba ,yana daya daga cikin abinda yasa yake gwasale eiman shagwabatar tayi yawa kmr itace auta idan tana wasu abubuwan ko sabir k'aramin kaninsu baya abinda take yi .
tun muwaddat na yarinya yasanta da shagwa'ba saboda gata da yayi mata yawa ,Yasan dole ne ta zama sangartacciya domin gata mugun abu ne kuma gata guba ne agurin wasu ya'ya Dan bakowanne Dan gata yake samun ingantacciyar tarbiya ba ,tun sanin dayayiwa muwaddat tana yarinya har yau da wannan fuskar yake kallonta ,shi yasa lokaci datazo yayi kmr bai Santa ba domin bayason yashiga harkokinta bare yasha haushi, amman d'an zaman datayi yanzu a gidan ya kula kmr tana da kamun kai ,domin yanayin halayenta suna burgeshi bata da son hayaniya kuma bata da yawon surutu sannan akwai natsuwa ,illarta girman kai da Jan aji, gashi shi yanzu zuciyarsa ta kamu da matsanancin soyayyarta....

Muwaddat tayi zamanta da Jakarta a hannunta shi kuma yaki yace mata tashi su tafi, sai dady yace "ku tafi mana tunda kin shirya ,zaman me Kuke?

Ala'meen ne ya fara mikewa batare idanunsa na akanta ba yace "ki sameni a mota bata amsa ba ta Mike tabi bayansa ,Kafin ta k'arasa gindin mota shi har yashiga ya zauna ,tasa hannu jikin motar tana kokarin budewa sai taji shi gam a kulle , bazata iya ce masa ya bud'e Mata ba ,kawai sai ta matsa ta bud'e gidan baya ta shiga ta zauna ala'meen ya d'an waigo kawai ya kalleta baice komai ba ,yayi zaton ko ta kasa bud'e gidan gaba zatace a bud'e mata ,Amman sai yaga ta kame a gidan baya ,a zuciyarsa yace lallai ma wannan yarinyar direba zata maidani ko me?

Ya dai daure ya tada motar suka tafi suna hawa titi ya fara sharara gudu ban da kidan zamani ba abinda ke tashi acikin motar ,glass din motar ya saita gefenta domin yasamu damar kallonta adaidai wannan lokacin wayarta tayi k'ara ta d'auka tana magana da abi Sai wani magana take cikin shagwa'ba.


Alameen ya natsu sosai ahankali take magana Amman ya fahimci da Wanda take waya ,har wani lallaminta t
yake "haba yar gidan dady menene abun fushi kuma ?
"Cikin zumbura baki tace "to abi bayan kaine yau baka tasheni a bacci ba shiyasa har na makara banyi sallah da wuri ba yace "kiyi hakuri abinda yasa tun asuba Dana shiga massalaci ban fito ba sai da gari ya waye sosai shiyasa ban bugo na tasheki daga bacci ba, na yi zaton idan umminki ta tashi zata tasheki Amman kibari in Allah ya yarda zan cigaba da tashinki da asuba ince dai idan na ta dake kiyi sallah kina min addua kullun ?

A marairace tace " haba abi ina maka mana taya daman za'ayi in yi sallah ban wa babana addua ba "yauwa yar diyata nasan zaki min ina fatan kina jin dadin zaman ilorin?
"Abi babu laifi garin akwai dadi "da fatan hajara bata takura miki don nasanta da zafi akan yaro "dady wannan karon bata matsa min ba da yake tasan halinka Dana ummi "to fatan dai baki da damuwar komai "wallahi abi babu wata damuwa,sai dai gaskiya ni abi ina son na dawo "ki k'ara zama tukunna har yanzu da sauran lokaci kafin ki koma makarata ki dai dinga duba litattafanki saboda kinsa da kun koma zango karshe zaki shiga kuma zamanki anan zaki fi samun nasuwa saboda takurawar bunayya .

"Shikenan abi tunda kace haka na amince zan zauna Amman nayi kewarku ban da bunayya ,abi yayi murmushi "mu ma muyi kewarki ,bunayya daman wani kewarsa kikayi bayan kuna tare duk kwanakin nan ince yau kwanansa uku da dawowa, nan da sati biyu masu zuwa zai koma London take gabanta ya fad'i yashiga dukan uku suna hira da abi cikin nishadi shi kuwa ala'meen tukinsa yake Amman hankalinsa na gurinta sai lokacin ya gano yawon amsa wayoyinta datake yi ashe ba wayoyin samari bane da iyayenta take ko da wancan miskililin yaron da baya ganin mutunci mutane shi Sam yaron baya burgeshi ..
Satar kallonta yacigaba dayi wato Dan tsananin gata har tashinta suke daga bacci ,bayan daren da suke rabawa suna waya ita dasu .

Bai rage gudu ba sai da suka shiga ciki wata unguwa sannan ya rage gudu ya karya kwana yashiga cikin layin a kofar wani madaidacin gida yayi parking ya bud'e murfin mota ya fito ya Dan jira ko zai ga ta fito daga cikin motar Amman sai ya lura bata da niyyar fitowa wata wayar ma take amsawa sai ya tuna ashe bai gaya mata cikin gidan zasu shiga ba ,sai daya bari tagama wayar sannan ya bud'e mata murfin motar "bisimillah ki fito muje ki gaida matar abokina ya tsira mata idanu ko zatace wani abu batayi magana ba ta zuro kafafunta ta fito daga cikin motar suka jira suka shiga cikin gidan .


minal ce ta fara tararsu da faraa ta kaisu parlour'n ta tana fad'in "kai alameen sai yanzu tun dazu ake jiranka Amman ka shanya min miji ,yayita kokarin nemanka a waya bai sameka ba .


"Al'amen yace ku ya femin madam wallahi wani Dan uzuri ne ya tsaidani, ya fad'a yayinda yake kokarin zama a daya daga cikin kujerun kushin din parlour'n ya d'an dubi muwaddat sannan ya cewa minal "madam gafa bakuwa na kawo miki .


Itama ta dubi muwaddat cike da faraa yayinda ta nuna mata wurin zama da murnarta da komai ta karbeta sai kace tasanta muwaddat taji dadi sosai da irin tarbar da minal din tayi mata ,suka gaisa a mutunce ta fara tsokanar al'ameen in ce sabon kamu akayi shiyasa tutar latifa ta fara dusashewa ?

Cikin murmushi yace "no wannan kanwatace a lagos take ta d'an zo mana Hutu ne ina angon naki ?
"Yana ciki gajiya yayi da jiranka shiyasa ya shiga ya Dan kwanta bari na tasoshi .


Tana shirin shiga sai gashi ya fito daga bedroom dinsu ganin ala'meen tare da muwaddat ya sashi washe Baki da yake ya taba ganinta sau biyu dayaje gidansu cikin fara'a yace "a she ba kai kad'ai bane ,cewa zakayi yau muna da babbar bakuwa ya fad'a yana kallon muwaddat.

Ta dan kirkiro murmushi dole kana ta gaida shi minal kuwa sai rawar jiki take tana nan nan da muwaddat kafin kace me duk ta zagayesu da abubuwan motsa baki al'maen Yasan ba lallai bane muwaddat taci abubuwan da aka kawo mata Dan haka yayi hanzarin cika cup da ruwan lemu ya tura mata gabanta ,abun mamaki sai yaga ta d'auka tasha suna ta hira minal sai tsoma muwaddat take cikin maganar dole sai da muwaddat ta saki jiki tashiga cikin hirar ,ta dinga saka baki jifa jifa, ala'meen zuba mata ido yayi saboda lura dayayi yadda yarinya ta iya lafazin iya magana cikin natsuwa tare da kwantar da murya da gogewar harshe hakan ya tabbatar mishi da tasan abinda take ,ala'meen ya dubi minal sannan yace "madan Dan Allah zan barta anan saboda inda zamu da oganki idan mun dawo zan kaita taga gari kmr yadda dady ya bukata minal tace "babu damuwa ya Mike ya kada mukullin motar dake rike a hannunsa tare da watsa idanunsa akan muwaddat Amman ita Sam bata kallesa ba asalima hankinta na can gurin turawa M. A sako .
Yace "ayshatul muwaddat ki zauna anan kafin muje mu dawo muryarsa ta ratsa cikin dodon kunnenta da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido saboda yadda yakira complete name dinta ya razana zuciyarta domin tun tasowarta babu Wanda ke kiranta da wannan sunan bayan Auwal dinta sai yanzu dayayi mata ,da muwaddat akasanta kuma dashi kowa ke kiranta, ita kanta mantawa take da sunanta na gasky saboda ba'a kiranta dashi sakamakon sunan uwarsu ummi ne daita, suna girmama sunan babu abinda yabata mamaki kmr yadda ala'meen yayi amfani da sunan gurin kiranta ..

Ahankali ta gyada masa kai kawai Amman batayi masa magana ba, har ya fice daga parlour'n suna hira da minal saki fuska da fara'ar da minal ta nuna mata ya burgeta da kuma kyakkyawan tarba da rawan jikin datayi daita yasa taji tana son minal .

Minal dai yar wani fitaccen d'an siyasa ne anan garin ilorin ba'a Jima da yin bukinsu da Hisham ba Wanda ya kasance babban aboki agurin ala'meen tare suka kare karatu a Rasha har yanzu minal karatu take ,ayanzu haka tana karatunta a jamiar ilorin, hira ce ta balle tsakanin muwaddat da minal tamkar sun dade da sanin juna muwaddat ta saki jiki sosai har kowa ya labartawa kowa tarihin rayuwarsa.

Anan muwaddat ta wuni cur a gidan minal sai kusan yamma sannan ala'meen suka dawo daga unguwar da suka tafi suna cikin mota akan hanyarsu ta dawowa ala'meen yace bari in kira yarinyar nan ince mata gamu nan zuwa zan d'an zaga daita yawo sai mu koma gida .


Har ya fiddo wayarsa da niyyar zai kirata sai kuma ya tuna bashi da number ta ,yayi tsaki ya maida wayar aljihunnsa hisham ya dube sa yace "Anya manage babu wani abu tsakaninka da yarinyar nan?
Ala'meen ya Dan hararesa yace ",me kagani ?
"Ni Kan haka nan naji zuciyata na zargin akwai wani abu koma ince akwai soyayya mai karfi tsakaninku "kai rufa min asiri ai wannan ba irin tamu bace "saboda me kace haka ala'meen byn akwai zumunci mai karfi tsakaninmu ?
"nasan babu yadda za'a yi ka furtawa iyayenta kana sonta suki baka ,sannan ka daina ganin tafi larfinka..

Ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske "duk ba haka bane yarinyar ce yar shagwa'ba kai kanka kasan bana shiri da yan shagwa'ba ya fad'i hk yana waskewa ,zuciyarsa na dokawa ,domin a yanzu ma dayake maganarta wasu wurare a kirjinsa sake bud'ewa sukayi soyayyarta na kara nikaya aciki .

Hisham yace "Amman ni kuwa yarinyar batayi min kalar shagwababbiya ba..
"Eh to wani lokacin ni kaina ina mamakin yadda take magana a natse Amman shagababbiya ce gurin daka ganta ,iyayen goyonta sun sangartata ainun kar mutun yaje yasaka kansa cikin tasko."ai kuma ba daga nan take ba bakowa gata yake lalatawa ba ,akwai wasu

Please Login or Register in order to submit comment