Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata magana a tswa ce tace.

" ke munafuka! Ke munafuka!".


Jikin tane ya fara rawa da sauri tayi ƙasa da kanta ta k'asa komai dan ba abinda ke mata zuba inba hawaye ba.


Zainab ce ta tashi ta fara tako d'aya bayan d'aya wajan da Fatima take taƙarasu ga banta sai data yi mata kallon sama da ƙasa kana tace.


A rayuwata ban taɓa ganin jaka kamar kiba inba da kike jaka ace ki rasa wa zaki aure sai mahaifina, kece k'arya wadda aka haifa ba jini aji kinta sai da a kasa mata manja to bariji".

Har zatayi magana Momy ta ɗaga mata hannu tace. "Zainab k'yaleta dan yanzu fita zanyi dan haka kuje ku nuna mata aikin dake garemu kada rana tayi".

Tana kaiwa nan ta yafa mayafin ta tace musu tafi.

Sai da suka saka k'yayarta gaba suka bata aiki mai woya sannan suka barta, tanayi tana kuka..





Momy na fita driver ta kira tace ya kaita gidan Hajiya Shafa, koda suka isa gidan har Hajiya Shafa ta fito da nufin tafiya, sai ga Momy tazo dan haka tace to suje, haka ta shiga mota Hajiya Shafa taje suka tafi.



Basu tsaya ko ina ba sai wannan mogon daji, sai da suka aje motarsu wani wajan kana suka ƙarasa da ƙafa kamar yadda suka ji kuka wancen lokaci ko yanzo haka sukaji amma saboda taurin zuciya irin tasu haka suka k'arasa.



Suna ƙarasawa cikin wannan bokkar tasa yasa kar musu dariya mai ban tsoro, saida ya gama dariyarsa kana ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba, wani ƙullin magani ya mik'ama Momy yace, gashi ki tabbatar da ya shiga gida da hayakin maganin zai fara cin karo, sannan ya bata wani k'ulle yace.

"Wannan kuma a zuba masa cikin ruwan lipton masu zafi a zuba wannan maganin a ciki, yana shigowa gida bayan yaci karo da wannan haƙin kafin wannan abinda zaiji ya sakeshi sai ki bashi wannan ruwan lipton ɗin. yadda yaji bata son haƙin, haka zaijin bata son komai kama da ita, kuma yadda yasha ruwan lipton masu kunar masa zuciya haka zaiji zafi idan ya tuna komai kama da ita kuma ko bai sake taba zai manta da ita har abada, da fatan dai koyi yadda a kace kuyi dan haka ku tashi ku tafi".


Kuɗi masu yawan gaske suka ijje masa kana suk afito cike da farin ciki.





*By Sumy ✍✍*





*Comment*
Nd
*Shere*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦




*KAWAR* *'YATA* *CE*




®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*Story & written*
By
*Sumy*


Dedicated to...
*My sweet Shemah*❣❣💖




*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHAM*



~Vote & Follow 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~


*Page* 2?9?


*__________📖* Haka suka dawo gida ciki da farin ciki.


Shiko Daddy yana fita daga gida bai tsaya ko inaba sai gidan yayarshi Hajiya Sa'a.




Koda yaje tayi murna sosai da ganin sa, bayan sun gaisa take tambayar shi ina Fatima yace,



" gobe zankawo miki ita kiganta, dan gobe koda nace ki araman ita zaki bada".


dariya tayi irin tasu tamanya kana tace, "nasa kana kulada ita dan gashi kaima naga kayi ƙiba tubari kallah".😃yace,



"Yaya sai ma kinga ƙanwar taki zakigane ina kula da ita".


Tace, "gashi yau zanyi tafiya zowa germany, kasan Abban su Mufida za'ayima aiki shiyasa yau zanje". yace,


"Yaya abun har ya kai haka to Allah yabashi lafiya, ta amsa da "ameen".



ya kara da cewa idan kin sauka zan ga yamiki lokaci da zamu zo dubashi." tace,



"to yayi sai nakiraka. tambayar sa tayi tace, kaje wajan Gwaggo kowa? yace, "yanzo dana fita wajan ta zanje".


Tace, to ka gaidamin ita nima zan biyo kafin na wuce. haka dai sukaci gaba da fira tana bashi labarin auren ƴan uwanshi da ikayi bayanan, daga baya yayi mata sallama ya wuce gidan Gwaggo.



Koda Gwaggo ta gansa tayi murna sosai daganin ɗan nata, bayan sun gaisa take tambarsa ya gida dasu Fatima. yace, "duk lafiya qlau suke"fira sukayi sosai kana yayi mata sallama yatashi zai fice bayan yasa asauke kayan daya zo mata dasu tayi murna sosai kana yayi mata sallama ya fice.


Da fitarsa bai tsaya ko inaba sai gidan iyayin Fatyna shi.



koda yaje Kaka Amo yasa aka kira masa tayi masa jagora har gidan Baba Babba.


bayan sun gaisa yayi musu shatara na arziki, dan mafi yawan dangin Fatima saida yayi musu alhairi, dan har Ummata da Babata wannan lokacin saida yabiya musu umura, sannan yayi musu sallama yawuce office.



Har yafara aiki yaji yana sun yaji Fatyn shi, wayar sa ya ɗauko yakira ta, tana ringing ba'ayi piking ba har sada yayi miss call fiya da goma ba'a ɗa gaba, kana ya iji wayar zuwa ajima yakoma kira yaga ko zata dauka.



Ita ko bata masan yana yiba dan tana can tana ɗawainiya da aikin da suka sata tanayi tana hawaye tana tuna zakin da Zainab tayi mata.



Ita ko Momy tunda tadawo gida tafara shiri yadda komai zai kasance mata cikin natsowa, lokaci-lokaci sai takira Daddy tana tambayar sa karfe nawa zai dawo, hardai taci riba yafaɗa mata yanzu zaI dawo dan gashi nan ma ya kamu hanyar gida.




Itako Fatima saida tagama Ai kin dasuka sakata kana takoma part ɗinta, wanka tayi tayi sallah, bayan tagama ta shitayi domin ta gyara jikin ta, wayar tace tafara ruru sunan da taga yana yawo saman screen ɗin wayar ne yasa da sauri tayi pinkig.



Sallama tayi tari da faɗin, "Ummata yakike.saida ta amsamata kana tace, "lafiya ƙalau Fatima, ya gidan naku inafatar kuna lafiya?Fatima tace, "lafiya muke Ummu bayan sun gama gaisawa Umma tace, "Fatima baji mawaba Mijinki yazo ya gaishe da iyayyinki har yayi muna abin arziki dan har Umura saida ya biya muna nida mahaifinki, dan haka nace bari nak'iraki na gayamiki kimasa godiya sosai kinji, kuma kiyi ta hakuri da yadda kika samu kanki kinji".


saida ta numfasa kana tace, "tau Umma insha'Allahu zan masa". saida suka sha fira daga baya sukayi sallama.


Har cikin ranta taji daɗin abinda yawa iyayyin ta, dan haka tayi ƙudirin sai ta faran ta masa.dan haka cikin hanzari ta ƙarasa jikin mirrow ta ɗanɗasa kwaliya daba ta taɓa irinta agidan ba, kana ta murje dukkan jikin ta da turarukka masu kamshi gaske.


dogowar riga tasanya ta materi, rigar ta karɓe jikinta gashi taɗeme mata jikin sosai tyi kyau, gashi abuga mai kyau, ɗaurin ɗan ƙwali ta murza gashi ita gwanace a wajan, ita kanta tasan tayi kyau bana wasaba.


sai da tagama koma tafara tunani yadda zata fita taje part ɗin Daddy a haka, tunani tashigayi can dai tace, "tasan zaizo dan haka ko sauka ba zatayiba bare suyi mata kallon banza, tana wannan magane ita kaɗay. dan haka tasamu waje ta zauna kafin ya ƙarasu.




Momy ko tana jin yace ya kama hanyar gida tazo tafara turarin ta sai da ta turare gida gabaki ɗaya, kana tahaɗa ruwan lipton tasaka wannan magani kana takuma wajen harabar gate ta zauna, tana jiran ƙarasu war sa.



Ba jimawa da zaman ta sai gashi inayi horn, da sauri maigi yaje yawan game gate ɗin, hanci motar driver yasanyo ciki harabar gidan, wajan da aka tanadar domin picking ɗin moto nan yazo yayi picking, Momy ko tana ganin sun ƙarasu da sauri tayo wajan da suke, ƙarasuwar ta tayi dai-dai da fitowar Daddy a cikin Mota, yana fitowa yaji wani baƙon alamari yazo masa tari da wani ɗuwi da bai taɓa jin irinshi ba, aikowa kakarin amai yafari kamar zai amaye ƴan cikinsa.





yana cikin haka Momy ta ƙarasu gareshi da sauri tana faɗin,


"Alhaji lafiya? komai bai cemataba dan haka taɓuɗe cup ɗin da tazo dashi na ruwan lipton tace, ƙarɓe kasha zaka daina".


Ba musu ya ƙaraɓa ya kai bakinsa, hankali yafara zuwa makoshin sa har ya kai zuwa ƙirjinsa har yazo zowa zuciyar yarsa, aikowa yana kaiwa ga zuciya yarshi sada yasaki wata ƙara tari da faɗin, "ya Allah".



Sai da ya shanye shi tas kana ta janye cup ɗin daga bakinsa, hannusa tariƙa ta ƙarasa dashi part dinsa. sai da ya zauna yajima kansa na kasa, ahankali yafara ɗago kansa yasauke gareta.


Ido ya kefeta dasu yana kallon ta, dan wani kyau ne yaga tayi masa wanda bai taɓa gani haka ba sai a yau, har wata yarinya yaga takoma mishi, gawani sonta da yaƙara zomasa wanda bataɓa jin hakaba atari da shi ba.



Tunda taga ya kifeta da ido tafara sakar masa murmushi maita yar da hankalin ƴan maza slow-slow tafara takonta har takawa gareshi, jikinsa ta faɗa tana faɗin,




"dear nah sannu da zuwa"



sai da ya ƙarasanya ta jikinsa sannan yace,



"yauwa sweet heart ɗita, ya gida".


Tace, "lafiya ƙalau".


Tashi zatyi yakara sakata jikinsa, murya ƙasa-ƙasa yake faɗin ina zakije? ".


A hankali ta furta cewa, "ruwan wanka zan hadama sai kayi wanka kaci abinci dan nasan akwai gajiya atari da kai".


Ba musu yace, "tau Hajiya tah duk yadda kikayi dai-dai ne".



Wani daɗin ya ziyarcr Momy wanda ba tasan lokacin da ta rungumeshi ba tana fad'in I love Alhaji nah".



Haka dai sukaci gaba da soyewar su suyi wanna suyi wancan har dai yayi wanka yaci abinci ya kwanta, amma koda wasa baiyi tunani wata Fatima aranshi ba.



Itako tanan zaune tana jiran Daddy har magarba ta gabatu ba Daddy babu alamunshi.






*By Sumy ?*






*Comment*
Nd
*Shere*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦




*KAWAR* *'YATA* *CE*




®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*Story & written*
By
*Sumy*



```Dedicated``` to.....
*My family* 💖🥰





~Vote & Follow 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~


*Page* 3?0?



*__________📖* Tana gama sallah tunani tashigayi ko dai Daddy bai dawo ba.



Har taso taje part ɗinshi tagani ko ya dawo amma tana tsoron abunda zata tarar, haka ta hak'ura badon taso ba tace bari ta ɗau waya ta gwada kiran sa taji ko lafiya.




Waya ta ɗauka domin ta kira shi amma sai taga miss call d'in shi kusan har goma, dan haka cikin sauri tadanna masa kira, tana ringing amma ba'ayi picking ba. Saida tayi mishi kusan miss Call uku ba'ayi picking ba dan haka tace bari ta dakata zuwa anjima ƙila baya kusa da wayar.



Har goma ta kusa ta kuma kiranshi, Amma abin mamaki yanzu wayar ma akashe take.



hankalinta ya soma tashi, don bai taɓayi mata haka ba, kuma tana son ta fito amma ta kasa.




dan haka ta hak'ura tace inbai zoba da safe taje tagani ko lafiya.


Da haka ta hak'ura taje ta kwanta.



Momy ko tana ganin ya samu bacci takoma part ɗinta ciki da farin ciki.






Tana ƙarasawa wayarta ta ɗauka takira Hajiya Shafa.


Ringing da bai wuce uku ba ta ɗaga.


bayan sun gaisa Momy ke faɗamata abinda yafaru, aikuwa murna awajanta ba'acewa komai, dan har rawa saida ta taka kana tace, "gobe insha Allahu a gidanki za'ayi meeting, dan haka kisa ta haɗa mana lunch mai kyau".



Momy tace, "angama Hajiya tah kada kidamu tunda safe zata tashi ta ɗora".



Haka nakeso kafin itama tabar gidan taci ubanta,gobe ko wani taga zai auri ɗaya daga cikin mazajenmu nasan bazata bashi shawara ba".


Momy tace, "sosai kuwa, ko Zainab da take goyon bayanta yanzu ko ta daina dan haka sai gobe ma idan kunzo".



Tace, "ba damuwa sai munzo".



Sallama sukayi Momy tayi wanka ta koma part ɗin Daddy.



Koda gari ya waye da zazzaɓi ta tashi dan ko baccin kirki bata samu ba dan sai gaf da asuba ta samu bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta.



Tana cikin bacci ta mai daɗi dan ko sallah asuba bata samuyi ba,cikin barci taji anayi Mata knocking da ƙarfi kamar za'acire ƙofar.



Tashi tayi da addu'a abakin ta, yadda take jin jikin ta kamar ba zata iya tashi ba amma saboda bugun ƙofar yayi yawa dan haka tayi ƙarfin hali ta tashi ta fara tafiya ahankali har takawo ƙofar dan har jiri take gani.



A hankali ta murɗa handle ta buɗe ƙofar, Momy ta gani tsaye fuskar ta haɗe, jikinta ne yaɗau karkarwa batasan lokacin da ta furta cewa,



"Momy dan Allah kiyi hakuri wallah yanzu na farka daga barci".



Sai da Momy tayi mata kallon sama da ƙasa kana ta yatsine fuska sannan tace,





" haɗa mana breakfast yanzu, indan kuma kika gama ki maida sanwar Rana saboda muna da baƙi yau agidan, Kinji ko bana son asamu matsala don haka tun yanzu kije kifara".



Cikin muryar masu zazzaɓi tace, "to momy bari nayi sallah dan yanzu na tashi".



Momy tace, "ba ruwana kije can idan kin gama sai kiyi dan mijina yanzu zai fita dan haka kiyi sauri ki haɗa mana breakfast kafin ranki ya ɓaci".



Ba musu ta raɓa ta gyafin Momy ta wuce kitchen.



Momy sai da taga ta shiga kitchen kana ta koma ɗakin Daddy ta kwanta suka cigaba da barcin su.




Ita ko koda taje kitchen rasa abinda zatayi tayi,duk tunanin ta Yana Kan Daddy,watau jiya gida ya kwana,to amma me ya hana shi zuwa dubata? kodai dan ya kira ne banyi picking ba? Tambayoyi take tayi barkatai acikin zuciyar ta.



Sallah ta farayi kana ta fara haɗa breakfast tanayi tana zama tana hutawa dumin yadda takejin jikinta ba ƙarfi, saida ta kammala sannan ta jera saman dinnig sannan ta wuce part ɗinta. tana zuwa saman gadu ta faɗa saboda yadda jiri ke ɗibarta ko gani batayi sosai dan haka ta kwanta domin ta huta.



Momy ita da Daddy sune basu farkaba sai 10:am, kana sukayi komai atare sannan suka fito domin suyi kalaci.




A falo suka same su Zainab, dan Ummi da Kulsum su sunje school tun safe.


Zainab ce ta fara gaishesu sannan Nabila, zama sukayi sukayi breakfast ɗinsu cikinsu babu wanda yayi maganar Fatima har shi kansa Daddy haka sukayi breakfast ɗinsu su kaɗai bayan ya kammala yafita ba tare da ya nemi Fatima ba, dan shi a yanzu gabaki daya ya manta da ita.



Haka momy tayi masa rakiya har wajan motar sa,sai da driver yaje sannan tadawo tasame Su Zainab suka cigaba da firarsu.


Momy ta dubi Zainab tace,"kije kitchen ki duba man ko yariyar can tayi akin dana sata".



Zainab tace, "to Momy bari na duba".


Tashi tayi taje kitchen taga bata nan dan haka tazo ta faɗama momy bata kitchen.


Momy tace taje part ɗinta tagano ko tana can? tashi tayi ta tafi a hankali take tafiya har takai part ɗinta,knocking tayi mata jin ba'ayi magana ba yasa ta tura ƙofar ta shiga ciki.



Cikin bargo ta sameta tayi rufa dashi tana makyarkyatar sanyi.



A hankali take takowa har tazo gab da ita, tsawa ta daka mata "tace hala bakiji ana knocking bane kinyi banza da mutane eh? ".



A hankali taɗago kanta ta kalle Zainab tace, "haba Zeey kiyi hakuri wallahi banji ba kuma ko naji ba iya tashi nakeba".



Zainab tace, "ba ruwana da baki iya tashi dan haka ki tashi kije ki ƙarasa aikin da aka saki kinji ko".



Komai batace mata ba dan ko magana bata sonyi, da Zainab taga bata ce komai ba dan haka taje ta gayama Momy wai tace baza tayi ba dan ita ta gaji, aikuwa ba shiri Momy tacema Nabila taje ta gayamata duk ta yadda tasame ta sai tayi dana sanin zuwan ta gidan.



Kafin momy takai ƙarshen zancen tuni Nabila ta fara tafiya.



Tana zowa da ƙarfi ta buga ƙofar ta shiga bako sallama ba komai, yadda Zainab ta barta haka itama tazo ta sameta, da zuwanta bata tsaya komai ba tayaye bargon da ke rufe ajikinta, ido Fatima ta ɓude tace dan Allah Aunty Nabila kuyi hakuri wallahi banda lafiya".



Aikuwa bata kai da rufe bakinta ba taji saukar mari har guda biyu hago da dama.



Kallon ta Nabila tayi tana huci kana tace, "har kin isa momy tasaki abu ki k'iyinsa? to wallahi bari kiji ko mutuwa zakiyi sai kinyi aikin da aka saki dan haki tun ranki bai b'aci ba kitashi kije ki ƙarasa".




Tana riƙe da kuncinta komai bata ce mata ba,tashi tayi tafara bin bango tana tafiya har ta kai bakin ƙofa jiri ya samu ɗibarta har zata faɗi tayi sauri ta riƙe ƙofar.

sai da taji dama-dama kana taci gaba da tafiya har ta ƙarasa kitchen d'in.


Nabila ko tana ganin ta shiga kitchen taje ta gayama momy ta tashi har ta fara aikin sannan itama momy ta koma part ɗinta dan ta shirya tarbar baƙinta.




Ta jima zaune tana nishi kana tayi ƙarfin hali ta tashi ta kunna gas ta fara haɗa musu abinda sukace.



Tunda ƙamshin girkin da takeyi ya dake hancinta ba shiri zuciyar ta tafara tashi aikuwa tafara ƙoƙarin tayi ammai, amma ta kasa dan ba komai acikinta.



Tajima kafin abun ya saketa dan ta wahala sosai kana ta tashi taci gaba da aikin da suka sata.



Bayan ta kammala girki, tana cikin tsaftace kitchen sai ga Momy tazo tace mata taje ta gyara gida dan baƙin ta na kan hanya. To Fatima tace mata.




Sai da tagama gyaran kitchen kana ta taje ta gyara dukkan gida tanayi tana share hawaye tana tunanin ina Daddy yaje mi tayi masa da ko wayar ta bai kiraba. Haka dai tayi ta magana a zuciyar ta har ta gama ta koma part ɗinta.




Wanka tayi da ruwa masu ɗumi ko zataji ƙarfin jikinta haka kuwa ya kasance da taji jikinta ya mata sauƙi sosai dan haka ta shafe jikinta da mayuka masu k'amshi kana ta kwanta.



Wayarta ta ɗauka tadanna kira Daddy tana ringing amma ba'ayi picking ba, har saida tayi mishi kusan miss call biyar bai ɗagaba. wayar ta tayi jefa da ita tana Mai fasa kuka cicin k'arfnta,kukan da takeyi irin kukan Nan ne Mai cin zuciya.



Tana kuka tana faɗin, "Allah kabani ikon cin wannan jarabawar daka ɗoramin".




Shiko Daddy koda ta kira bai ma saniba dan baya cikin hayacinsa, dan yau yafaɗa kaidin Hajjiya kulu.




dan baijima da zuwa office ba Hajjiya Kulu tazo wajansa taci kwalliya sosai gwanin ban sha'awa gawani ƙamshi mai sanyaya zuciya tare da sanya nishaɗi musamman ga wanda yaji ƙamshin.



Knocking tayi masa,aka bata damar shiga.

ahankali ta turo ƙofar ta shiga, cikin ta kunta mai jan hankalinsa ta ƙarasa ciki, tun batayi sallama ba k'amshin ta yayi masa sallama,take yaɗago kansa ya kalleta, aikowa wani shu'umin murmushi ta sakar masa wanda yayi sanadiyar kashe masa duk wani ƙarfi dake jikinsa.



Idonsa ya kifeta dasu nan take yaga ta koma mishi wata irin kyakyawa, aikuwa bashiri yataso zuwa gareta.


A hankali yake tafiya har yazo wajan da take tsaye kamar wanda aka dasa waje ɗaya tana aika masa da shu'umin murmushi mai birkita ƙwaƙwalwa.



Yana ƙarasowa gareta jikinsa ya sanyata aikuwa tanajin ta jikinsa ta sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfin gaskiya, dan rabonta data jita jikinsa tun lokacin da ya fara neman auren Fatima.


Shiyasa duk duniya yanzu ba abinda ta tsana kamar Fatima, dan taso ya aureta amma yace a'a Fatima yakeso dan haka ita zai aura.

Hajiya kulu ba inda bataje ba dan kada ya auri Fatima amma da yake Allah ya ƙaddara ba wanda ya isa ya hana, dan haka taci alwashi duk yadda zatayi sai taraba shi da Fatimar shi. Ko yanzu atunanin ta abinda akayi mata ne yafara aiki dan haka tayi ƙudurin sai ta rabashi da duk wani wanda ke raɓarsa. Badan komai yasa tasa bokanta yayi mata aiki ba sai dan yazama mallakinta ita kadai.





Tunda taga yanayin da yashiga tafara jin wani sanyin daɗi ya rufeta.



Aikuwa tana gani haka ta janye shi daga jikinta cikin murya mai jan hankali da iya bariki tace, "sakeni koda ma nazo ne mu gaisa kawai, kuma gashi natarar aiki kakeyi".



Cikin muryarsa data fara dushewa yace, "kiyi hakura zan ajiye aikin har kitafi, kibarni mu gaisa please ".



Kamar baza tayi magana ba tace, "a'a bazan tsaya ba sai dai kazo muje gidana".


Ba musu yace, "muje to".



Wani farin cikine ya lubeta bata san lokacin da takai masa kiss a lips ba, shiko kamar jira yake yafara mayar mata da martani da ƙyar tasamu ya barta.


Ɗaya daga cikin ma'aikatan shi kira yace zaifita. adawo lafiya sukayi masa kana suka wuce shida ita.


Tunda suka shiga gidan ta tafara rikitar dashi gabaki ɗaya ya manta da kowa bare wata mai suna Fatima.



Dan koda ta kirashi bai masan a ina wayar take ba.




Bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita, dan ko dama har barci akwai acikinta.




12:pm dai-dai motocin group7,suka fara shigowa gida kowanin su cikin shiga ta alfarma suka fara shigowa, inda aka tanadar musu Momy ta nuna musu suka zauna d'aya bayan d'aya suka fara zuwa har suka kai su bakwai.




Ko wacce daga cikin su idan zata shigo sai ta rangwaɗa guɗa, Hajiya Hafsa ta dubi Momy tace, Hajiya Hadiza naga har ƙiba kinya fah mi yabaki daga jiya zuwa yau"tana mai sanya dariya.



Saida suka tafa kana tace, "komai ma yabani tunda yanzu sai yadda nace".


Aikuwa gabaki d'ayansu suka tafa sukayi wa kansu kirari suna faɗin, sai mu group7 bamu ba kishiya duk wanda yace zai ja damu yayi k'arya. amma idan zaka iya kazo ka gwada.



Haka dai sukayi tayiwa kansu kirari, daga baya sukaci suka sha har da taka rawa sannan sukace akira musu Fatima su ganta.



Momy Kulsum takira tace taje takira Fatima.




Koda Kulsum taje kwance ta sameta tana bacci dagani ba barcin daɗi ne takeyi ba.



Sai data ƙaraso gabanta tafara faɗin, "Aunty, Aunty, kitashi Momy na nemanki".



A firgece ta farka tana faɗin, Kulsum ina Momy take?".


Kulsum tace, "tana parlour tana jiranki".



Fatima tace, "to je yanzu zanzo".



Har Kulsum zata tafi sai kuma tadawo tace, "Aunty hala baki da lafiya ne"?



Har taso tace eh kuma tafasa tace, "lafiya ta ƙalau bacci daine bai ishe niba".



Kulsum tace, "to Aunty idan kika dawo sai kiyi ta barcin ki".



Gajiya tayi da maganar kulsum dan haka tace, Kulsum je kice mata gani nan zuwa kinji".



Aikuwa da gudunta tafice.



Itama Fatima tana ganin tafita tashi tayi da ƙyar ta saka hijab nata kana ta safko, tun bata karasa ba tafara jin hayaniya aikuwa ba shiri gabanta yafara duka uku-uku.



A hankali take tafiya har takawo cikin falon.



Tunda ta tunkaro su suka fara antaya mata harara,nesa dasu ta durƙusa tace, "Momy gani".



saida ta aikamata kallon banza sannan tace, "hala jakar uwarki bata koya miki yadda ake gaida mutane ba? ".



Idon ta tap da hawaye tafara girgiza kai hawaye na zuba a idonta.



Gaishe su ta farayi amma ba

Please Login or Register in order to submit comment