Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Haka duk suka d'auka suka tafi Shigar su D'aki Hansai tace nikam kayan sun Birgeni Karime tace "tab! yanzu shikenan Mundena saka kayan mu!?
Kande tasa Dariya kide zauna Surutu Cas kayan sukayiwa Hansai kyau gashi sun D'an kamata daga kasa kamar ba ita ba,shape dinta ya fito daram tsakiyan cikin ta ya d'ame ga kirjinta har dan fitowa yayi, dogon wuyanta ya fito ya dace da beautiful face d'in, tsaki tayi "jifa yanda kayan nan sukayi mini? ni kam dama tabarni Nasa Hijab d'ina."
Karime tace "kai Hansai duk yafi miki kyau"Kande tace "eh wallahi" Karime tace "duk gayunsu wallahi kin fisu kyau" Kande tace "eh dande tana rufe Jiki ne."
Nan suka fita Sumy na zaune tana kad'a k'afa suka zo suka tsaya tayi Dariya "ko kufa yanzu kuka dace da 'yan Aiki Musamm ke Hansai kinga Anty ta tsaya miki har Super Holland kike kwancen ta to Daga yau ta kau, oya kowacce ta tafi nata guri nan suka juya."
Bin Hansai da kallo tayi tab! dama haka yarinyar nan take! dole ta rufe Jiki d'an tsaki tayi ta mike.


*MANGALU*
'Yan Sanda ne ak'ofar Gidan Malam, Dije da sauri ta shiga ta kaiwa Gwamma tsogwami nan ta shige d'aki ta gark'ame Jiki na rawa Fad'an- Fad'an Delu tazo tace bari na shiga Gidan.
Tashiga tana k'wala Sallama Jummai ta fito Delu tace ina wan nan Muguwar ta fito wallahi yau ko ta ban kud'i ko atafi da ita."
Daga can d'aki tace "bazan fito ba Wallh" Delu tace "yo ai bafin k'arfin kikaiba nan ta Danna K'ofar nan kwa ta bud'u ta Janyo Gwamma tace "kudi ko tafiya" tace "ki bari Mudi zai yimin aike."
"Ban yarda ba." Gwamma tace "ke bafa tsoronki nake ki ba wallahi bazan ma bayar ba" a fusace Delu ta fita ta Sanarwa 'yan Sandan nan suka Shiga soron Gidan sukace Gwamma ta fito dak'yar ta fito tana yafa Mayafi suka tasa k'eyar ta har waje yara ne dam! a tsaye nan ta tsaya tana huci tace "Delu munsa k'afar wando d'aya dake."
"Tink'is -Tunk'is aka tafi da ita D'uu yara na binta.Jummai kuwa sai tafa Hannu take "oh! su Gwamma an fara tab'ab'arewa." Malam ya shigo Jin Labari da takaici yake tambayar Jummai ta sanar mai yanda akai yace "Al amarin Gwamma Sam ba Allah aciki, ta wulak'anta Rayuwar ta kuma wallahi ba inda zani Sanda sukai niya sa sako ta."
Jummai tace "Allah ya kyauta Malam yace "nikwa yau watan Hansai nawa?" tace "ina Kin Uku Malm" yace "Allah sarki Hansai muna Kewarta" Jummai tace "nima haka."

*ABUJA*
*Bayan wata d'aya*
Yau ya kama Sunday duk 'yan Matan na Gida suna zaune kowacce da abinda take Zuby ta kira hansai da yake Anty ta sai Mata wata Aitle shiisa duk wacce ke da aiki kir zata kira ta. Hansai tazo gani Zuby ta Aiketa ta had'o Mata drink ta tashi ta tafi ta d'auko Jitayi an watso Mata Bra Sady ce ke Jin wak'a tace "Jeki wanken" ta tashi ta tafi sai wash take Saboda tunda ta tashi suke sakata Aiki har ta gaji Allah yaso ma Aikin Anty bame yawa bane, dawuri take gamawa.
Tas taje ta wanke ta shanya k'aryar ta ta tashi har sai Sun gama bushewa San nan ta deb'e sai wajen 2 ta dawo rik'e da su,ta shiga wangamemen d'akin nasu duk Sunyi wanka Sun fece Sumy ta kalleta "ke anjima zaki rakani Shopping" Ruma tace "oh no! ku kam wai mesa kuka takurawa yarinyar nan komai ita duk baga su Karime ba."
Sady tace tab! wad'an nan k'azaman Ji Uniform din su kullum datti sai Dana sa Iya ta sasu suke wankewa kullum , kinga kuwa ita kullum nata agoge shiisa nafi san Aikin ta Ruby data k'urawa Hansai Ido tace "Gata kuwa so beautiful" Zuby tace "LOL" .
Sumy tace "nikam Anty Ruma Dady na nan? tace "eh mana yana garden" tace "nikam kayan make up D'ina ya k'are da perpums gashi duk nayi searchin new a Goggle" Sady tace !tab ai kuwa nima hakan."
Sumy tace "Nifa bansan gasa Sady tace k'afata k'afar ki" Sumy ta "kalli Hansai dake tsuggune ta Sunkwi dakai ke ki fa shirya zaki rik'en kaya". Hansai tace "to Anty Amma da wad'an nan kayan zani ? Dariya suka fasa su duka, Sumy tace "to da dame zaki? meye Amfanin ki ba 'yar Aiki bace ke? dole ki bada Alama da hakan."
Anty Ruma kam akwai Sauk'in kai tace "no baza ai haka ba, itama fa 'yar Adam ce taje kawai ta saka kaya masu kyau ,ke ba abin kunya bane aagareki ta tafi da uniform na aiki."
Sumy tace "kai Anty Ruma!" ta kalli Hansai "oya Jeki wanka kisa kaya me kyau."
Hansai tace "to" ta tashi a salub'e ta fita D'an sauri take Ojuku ya tsareta "pls baby Do you love me? Hansai ta harare shi "ni ka matsa meye ruwa na dakai, ka takuramin"
Yi hank'uri Baby me kyau" wucewa tayi yabi bayan ta da kallo yana mai wani had'e Ido, cigaba da Goge tiles d'in yayi yana wak'a baby love me ! love me."
Sumy da suka fito zasuyi part din Dady ta wullawa Ojuku key "pls ka wanken Motata saboda anjima zani Shopping" yace "Okay Maddam" Look ban. Hanaka cewa Maddam din nan ba?" yace "Sorry Hajiya" tsaki tayi Sady tace "ke komai fad'a" tace "nayi."
Part din Dady suka Shiga Sunkai tsakiya sukaga Anty tana magama "pls Dady's boys a D'aukarwa Mubarak me Lesson" yace "ba komi Amaryata" Sady tace "Aikin kenan komai boys, Don taga su Mama sun d'aga Mata legs" Da sallama suka shiga Sady da yake yar gaban Goshin sa ce da saury taje kusa dashi ta zauna "Dadyna" yace "Uwata ya dai?"
Sumy tace "Dady kayan Makeup d'ina ya k'are da Perpums" yace "kai Yaran nan bakwa Rabo da kwalliya Last 2 weeks na Baku fa" Sady ta Marairaice Don Allah Dady yace "oke Don worry" ya tashi ya bud'e kit ya curo bandir ya bawa kowa 20k suka had'a baki "Allah ya K'ara Budi Dady."
Suka fita nan ya juya yace "Maman Boys Insha Allahu Next week zai fara zuwa tace "Ngd Dadyn kids"


Please Login or Register in order to submit comment