Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bawa siyamar hakuri taheer ya kifa mata mari zai fara magana siyama ta fashe da kukan munafurci.

Kama hannunta taheer yayi sukayi sama yana rarrashinta.

Ahankali siririn kukanta ke fita yana shiga kunnuwansa da zuciyarsa.

'Dagowa yayi yakai kallonsa gareta bayan tsawon lokaci.
Gabansane ya buga da qarfi sbd muguwar ramar dayaga tayi ga suturar jikinta duk a yage.

Marin da taheer ya kifa mata yadawo masa da yanda siyama ta tureta ta fadi.
Miqewa yayi da sauri danjin zuciyarsa na Neman fashewa ya fice daga gidanma gaba daya.




*3 days later*
Siyama ce tayi baqi zasu tafi ta fito rakasu nikuma ina harabar gidan ina bawa flowers ruwa.
Sunzo wucewa bansan dasuba sai ruwa ya'dan watsar musu.

Fizgoni siyama tayi da qarfi tana cewa,
Ke munafuka Mara gata da 'yanci harkin samu damar dazaki jiqani da qawayena,
To wallh saina Nuna miki ke bakowa bace.
Kar6e kuwan tayi tafara juyemin tun daga kai har qasa saida suka qare tayi wurgi da bucket din suka wuce suna dariya.

Banji haushi sosaiba sbd tasha yimin Wanda yafi wannan.
Juyawa nayi zan wuce kawai mukayi ido hudu dashi nayi saurin duqar da kaina,
Shikuwa rai a6ace yabar gurin sbd akan idonsa komai yafaru.


Da daddare sun zauna cin abinci na dauko fruits din zaid zan kawo amma kafin naqaraso Anty siyama tayi saurin 'daga murya tace,
Kadaki kuskura ki qaraso dan ganinki zai hanani cin abincin nan.
Taheer yayi saurin cewa,
Fruits din zaid zata kawo kuma kinsan sune abincinsa da daddare.
To amma my dear kasan idan tazo zan iya.....
Pls ya isa siyama dole tazo takawo dan abincin zaid ne.

Cikin 6acin rai da rashin kunya tace,
Idan har wannan jakar ta matso gurin nan wlh bazanci abincinba sbd banasonta banason ganin....
Shut up ,,,sukaji zaid din yafada da qarfi dan su duka ukun saida suka firgita.
Miqewa yayi afusace yabar palon.







Mamuh geee
© *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*




37-38
Tun safe yau taga siyama natakai kawon hada kaya harta gama tayi wanka tazauna a palon tanata kiran wayoyin yan uwanta da qawayenta tana fada musu tafiya zatayi itada taheer ta tsawon shekara a qasar Morocco.

Hayaniya suka jiyo daga harabar gidan siyama tayi saurin fita nikuma naci gaba da aikina,
Murya najiyo kamarta fareeda nayi saurin aje mopper na fita.

Ita kuwa 'dince durqushe kofar palon zaid tana kuka ahankali.

Da sauri na qarasa na riqota ta riqeni tana fadin,
Jidda iyayena aure zasumin nikuma zaid nakeso amma zaid yace,
Baya sona.

Daidai nan zai yakuma fitowa ya matso tareda kama hannuwan fareeda ya tada ita ya shafo fuskarta a ahankali yace,
Fareeda ina qaunar sosai kuma qaunar danake mikice tasa bazan aurekiba sbd qaunarki nake ba sonki nakeba,
Idan na aureki zan cutatar dake ta hanyar auro wadda nake so kuma zan iya tauyeki fareeda.
Trust me wannan shine d best thing for us,banason nasaki damuwa agaba fareeda wlh ina qaunarki kamar sister na,,kuma maganan gaskiya akwai wadda nakeso dan yau 'din nan ma zan koma US acan zamuyi aure da ita.

Ba fareeda da ake fadawaba koni saidana girgiza nayi sumar wucin gadi jin akwai wadda yakeso kuma yau zaitafi yayi auransa acan yayi zamansa yabarni da aurensa.

Hawaye ne suka 6allemin na miqe da sauri nayi daki nafara darzar sabon kuka.

Fareeda ma cikin dauriya ta miqe tareda cewa,
Nagode zaid kuma insha Allah zan dauki shawararka na zauna da duk Wanda aka auramin and promise you'll always be a gud friend to me.,

Share mata hawaye yayi yana gyada kai.

'Dakin Jidda ta nufa daganan sukayi bankwana da Jidda suna kukan rabuwa da juna bakamar Jidda dake kuka biyu dana rabuwa da fareeda mai taimaka mata da kuma kukan tafiyar zaid data samu kanta dayi,,
Taheer da siyama zasu tafi, fareeda zata tafi,zaid ma zai tafi ni Jidda ni kadai zanyi Rayuwa kamar mayya babu kowa.

Kuka fareeda take sosai tana sambatun soyayyar zaid datayi mata mugun kamu.
Jijjiga Jidda take tana kuka Wanda kukan jiddan ma haryafina fareeda dan ita batada kowa sai allanta.

Tashin motar zaid suka jiyo fareeda tayi saurin miqewa ta fito da gudu zuwa harabar gidan.

Yana hangota yayi saurin rungume taheer yace,
Yaya na tafi saimunyi waya.
Mota ya fada da sauri yaja yabar gurin.

Atare itada Jidda suka durqushe suna kuka.

Daqyar fareeda ta mike ta kamo Jidda tace,
Jidda nasan wata rana zamu kuma haduwa,ina miki fatan alkhairi,kuma ina miki fatan duk randa zamu hadu Allah yahadamu kina acikin wani Sabon yanayi,sabuwar Rayuwa.

Kai kawai Jidda ta gyada sbd kukan dayaci qarfinta.
Wannan shine karo na biyu data rasa mutane biyu datake so alokaci 'daya.
Sbd na farko ta rasa abbanta da dadyn lokoja a lokaci daya,
Yauma ta rasa zaid da fareeda alokaci daya.


Tun bayan tafiyar fareeda take kuka har shaqewa takeyi

Banko qofar 'dakinta taji anyi da qarfi amma bata 'dago kaiba sbd tasan siyama ce.

Kallonta tayi awulaqance tace,
Yau dai bazan 6ata raina abanxaba sbd lokaci yayi daxan yarda qwallon mangwaro na huta da quda.
Kamar yanda kika sani yaudai ko kuma nace yanxu zumu wuce nida mijina kuma na yanke shawarar bazaki zaunamin a ananba sbd shima Wanda yake aurenki ya tsallake yabarki muma bazamu barki kiyi mana sataba danhaka ki tashi yanxu ki hado kayanki ki fito zamu rufe 6angarenmu.

A tsorace ta 'dago tace,
Dan Allah Anty siyama kiyi hkr wlh banida gurin zuwa.

Kinga ki kwashe kayanki cikin arziki ko kisa nayi abinda banyi niyaba.

Durqusawa tayi tana hawaye tace,
Anty siyama kitausayamin wllh banida......
Cakumota siyama tayi tafara janta itakuma tana roqonta amma bata tsayaba saidata kai harabar gidan ta cillar da ita.
Kayanta ta 'debo ta watso mata takoma 'debo sauran tana watsowa taheer yazo da sauri yana cewa tayi sauri su wuce time 'din tashin jirginsu yakusa.

Maida kallonsa ga Jidda yayi yaga tana kuka ga kayanta a zube.

Lafiyarki kuwa?
Ya tambaya yana jiran amsarta.

Matsowa tayi gabansa ta durqusa cikin kuka tace,
Yaya taheer kaji tausayin maraicina kadaku koreni bansan ina zan dosaba.

Jikinsane yayi sanyi zaiyi magana siyama tayi saurin cewa,
Kadama kayi tunanin cewa abarta dan wlh bazam bartaba nadawo na tarar datamin sataba,
Sannan datake roqonka daka barta ta zauna nagama Wanda nauyinta yarataya akansa yatafi yabarta,
Kuma Allah ko aharabar gidannan bazan barta ta zaunaba fita zatayi gaba 'daya.

Taheer yace,
Siyama idan ta fita ina zataje?

Gidan karuwai,taje can dama shiyafi cancanta da ita dan dama karuw.......

Idon data hada da zaid ne ya datse zancenta ganin yanda yake cikin tsinanin 6acin rai yana aiko mata da kallon zallar tsana,
Sam babu Wanda yasan da zuwansa dan sunsan ya wuce airport gashi kuma ga dukkan alamu yaga komai daya faru da maganganun da siyama ke Fada akan Jidda.

A zafafe ya qaraso siyamar tayi saurin 6uya bayan taheer.

Ko kallonsu baiyiba ya damqo hannun Jidda dake durqushe tana kuka ya kalli taheer yace,
Daga yau na kar6i Jidda amatsayin mata dan haka daga yau tanada full right akan gidannan,
Haka kuma ka sanar da matarka matsayinsu daya anan gidan daga yau,
Bamai sake sakata koda dafa ruwan tea bare wani aiki,
And one more thing kada takuma kiran Jidda da sunan data fada.

Janta yayi suka bar gurin rai abace.
Mota yajefata yazagaya yashiga yaja motar aguje suka fice.
Wani Abu yadawo dauka amma 6acin rai baibarsa ya daukaba.

Airport ya nufa,
Suna isa Yakuma damqo hannunta kai tsaye boutique din dake cikin airport din ya nufa ya miqawa madam din dakedashi yace ta hadawa Jidda Mayan sawa a set din akwati akuma bata wasu tasaka kafin ya yanko musu ticket.

Tsuru tayi tana kallonsa cikin rawar jiki sbd ita tsoroma yake bata dan yau taga ainihin 6acin ransa data rasa sanin dalilin dayasa 6acin ran.

Doguwar Riga maroon matar tbata tasaka tareda mayafinta sannan aka shaqe mata akwati biyu da kaya tareda turaruka masu tsada da sanyin qamashi,hatta bra da panties saida matar ta zuba akayan.

Yana dawowa yabiya kudin komai fuska atamke suka wuce suka shige jirgin.





*Ina sonku kaman yanda kuke sona fans....*


Mamuh geee
m
© *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*

_This page is for you my sissy *Rahama nalele*_



39-40
Jin ana sanarwar sun iso lagos ne yasa ta fahimci Lagos sukazo,

Baqin glass yaciro ya sanya,
Yayi qasa da murya cikin tamke fuska yace,
Listen here,duk kika kuskura kikayi wani qauyancin dazaisa akallen wllh barinki zanyi natafiyata dan bakisan yanda kika wargazamun farin ciki.

Babbar motace tazo daukarsu suka wuce,
Wata anguwa Mara hayaniya aka bude musu gate din wani babban gida mai kyau suka shige.

Driver ne yadau kayansu yakai bakin qofar Palon bayan ya bude musu yayi wucewarsa.

Shigewarsa yayi nikuma jiki a sanyaye na 'dauki kayanmu na shiga dasu.

Babban palone daya tsaru iya tsaruwa fiyeda gidansu na can abuja.

Qofar bedroom biyu ne a palon suna kallon juna ya nuna mata qofar daya,
Yabude 'dayar master bedroom dinsa yashige.

Daukar kayanta tayi tashiga bedroom din daya nuna mata.

Bedroom din ya tsaru iya tsaruwa ga komai na room 'din is white.

Hotonsa ne dayayi masifar kyau a ajiye kan bedside drower cikin 'dan kyakkawan frame,.

Tsaruwar komai na gidan yasa jikinta yin sanyi tasaki ajiyar zuciya a hankali cikin tausayin kanta dashi kansa zaid dan tasan tazamar masa wata lalura data datse masa farin cikinsa da burinsa dan tasan wannan gidan yayi abinsane dan yayi rayuwa mai dadi da matarsa a duk lokacin dayazo lagos amma abin takaici ba matarsace dayayi buri ba tafara shiga gidan.

Toilet ta shiga shima komai fari gashi a tsare.
Wanka tayo tareda alwala tazo ta bincike kayanta tsaf babu wani dazata iya sakawa tayi sallah dan duka babu rigar arziki,
Daga iya cinya,sai wando iya gwiwa,sai mini skirt da bmshort.

Maidasu tayi tana mamakin yanda matar tasako mata irin wainan kayan dakuma tunanin yanda yanda zata iya sakasu.

Doguwar rigar data cire ta maida tareda yafa gyalan rigar tayi sallah.
Tundata gama sallah take zaune taqurawa hotonsa dake aje a dakin ida ko qyaftawa batasanyi sbd so take tagano abunda yasa idan taga taheer batajin abinda takeji idan taga zaid.

Qwanqwasa qofar da akayine yasa tayi saurin dawowa hayyacinta ta miqe ta isa bakin qofar ta bude duk da bawai key tasaba kawaidai ta rufene.

Suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kai.

Kallonta yayi tundaga samanta har qasa,
Gabansa ya buga da qarfi dan ganin yanda rigar tayi masifar fiddo da kyawun qirar da Allah yayi mata,
Gashi batada abin 'daure gashinta dan haka shima gashin abaje yake dukda ta rufeshi da gyalen rigarta amma kusan rabinsa yafito sbd tsawonsa na fulanin asali.

Wannan ne yasa aketa kallonta airport Ashe ni na 'dauka kallon bagidajiya suke mata.

Jiyayi ransa yayi mummunan 6aci ya ha'de fuska tareda 'dauke kai yace,
Akwai komai a kitchen zaki iyayin duk abinda kikeso amma Sam banason hayaniya ko wani babban kwarafniya.
Juyawa yayi harya fara tafiya saikuma ya tsaye batareda ya juyoba yace,
Kuma ni ba Yaya taheer bane I don't tolerate qazanta ko Yaya take,so ki ringa tsafta sosai dan bana iya zama da qazami bare ke kadaki manta taimakonki akayi.

Harya shige 'dakinsa bata 'dagoba sbd kalamansa sun shigeta sosai.
Saurin maida hawayenta tayi tana qarfafa komai na zaid zata iya jurewa.

Kitchen din dayace na nufa ban tsaya dogon tunaniba na 'Dora masa coffee tareda kunna fridge na zuba fruit ina rufe fridge din naji kiran sallar isha nakoma 'daki nayo nadawo tareda juye coffee din da fruits nakai dining,
Kicin nakoma Nima nasha fruits din kadan nawuce wata 'daki
Na duba kayan baccin dake cikin kayana naga babu wadda zan iya sakawa sbd sunyi tsiraici da yawa haka nabar rigar jikina nayi addua na kwanta a qasa dan bazan kwanta a gadonba na 6ata masa run kan yakawo matarsa ta so.




**************
Washe gari tana tashi sallah tafarayi kafin tayo wanka ta tsaya 'daure da towel 'din data Tatar a toilet 'din tana tunanin kayan dazata saka dan ta gwada kayan duka amma ta rasa Wanda zata fita dashi kada yakorota yace mata 'yar iska.

Ganin lokaci na qure mata yasa tayi tawakkali ta saka wani wandon jins fari iya gwiwa da rigarsa armless red colour.

Tana kallon kanta amadubi taji hankalinta yatashi dan Sam bazata iya fita ahakaba.

Ta jima tana saqawa da warwarewa amma babu mafita,
Ahankali ta miqe jiki a sanyaye ta yafa 'dan sirin gyalan rigar jiya ta fita.

Tana rufo qofar shima yana fitowa anasa 'dakin.

Saurin 'dauke kansa yayi ya nufi tsakiyar palon yana kunna wayoyinsa dasuka kwana akashe.

Cikin 'Dari 'dari ta fara shara amma takasa isa tsakiyar palon sbd kunya.

Lura da hakan yasa ya miqe yakoma 'dakinsa.
Sauri tayi ta gyare koina tayi mopping tareda kukkuna ac ta fesa airfresshnr.

Kicin takoma ta hada masa breakfast ta kai dining taje 'dauko ruwa a fridge tadawo saigashi yafito cikin black suits dasukayi maseefar yi masa kyau kasancewarsa fari sosai ga suit's din black.

Duqar da kanta tayi harya wuceta 'dauke da briefcase ya zauna a dining yana waya da taheer.

Batareda ya gama wayarba yace,
Zubamin tea kawai am in hurry.

Qasa qasa yayi mata kallon tsaf yanajin wata kasala na shigarsa sbd qamshin turaren da matar boutique tasako cikin kayan,
Qamshinta yacika gurin gaba daya yana ruguza duk wani kuzarin jikinsa.

Tana gama zuba masa ta juya zata bar gurin,
Murya qasa qasa yace,
Idan nafita ki rufe qofar idan nadawo zanyi knocking.

Kai ta 'daga tana kallon gefen qofar kafin tajuya ta wuce.




Godiya mai yawa ga soyayyarki *FATEE[truncated by WhatsApp]
© *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*

This page is for you masoya Mamuh geee musamman,
*My zinnie*
*Sistoh na rahama nalele*
*Fateema bintu*
*Queen billy*
*Maman Abba*
*Sis biebie*
*Sis zeetty(m hanan* )😍💋😘



41-42
Tunda ya fita ta rude qofar saita saki jikinta tana aikinta,

Da rana kuwa,
Cous cous da cabbage ta dafa masa tareda farfesun kifi mai ha'de da carrot sai fruits salad.
Jeresu tsaf tayi a dining takuma gyare palon ta feshesa da freshener mai sanyin qamshi sbd akwaisu a gidan different flavour jere akan console mirror dake dining area na palon.
'Daki takoma tayi sallar la'asar da ake kira,
Bayan tagama ta kwanta ta huta sai kuma ta tuno da garga'dinsa na tsafta.

Akasalance ta tashi dan harga Allah ba wankan takeji ba kayan sawar take tunani dan koshi kansa dayasan su matar tasako bazai biya kidinsaba.
Haka ta miqe ta fa'da toilet tayo wanka ta fito.

Man pureskin na oriflame tashafa tareda turaruka masu qamshi mai dadi ta jawo pant da bra tasaka tareda saka wata doguwar Riga iya cinya mai adon stones ako ina,gashi rigar black ce sai hasken fatarta ya yafito sosai a cikin rigar.
Turare takuma fesawa tana ajewa taji qarar doorbell
Da sauri ta tattara gashinta ta 'daure tsakar kai ta nufi qofar da sauri.

Cak ta tsaya bakin qofar tareda kallon kanta taga santala santalan cinyoyinta farare tas a fili ga rabin nonuwanta samansu abayyane.
Juyawa tayi da niyyar ko zanin gadone ta yafo amma taji ankara danna doorbell 'din harda qarin bugawa da hannu.

Juyowa tayi cikin tsoro ta bude masa qofar tareda matsawa gefe tana kakkare jikinta da hannuwanta.

Agajiye yake dan yanda idanuwansa ke lumshewa suna bu'dewa ahankali amma yana sawo kai cikin palon qamshinta dana palon dasuka gauraya da sanyin ac sai suka qarasa hargitsashi yakasa qarasawa 'daki kawai ya zube akan sofa palon yana sakin numfashi ahankali.

Ruwa taje kitchen ta 'dauko masa masu qaramin sanyi tareda cup ta 'dauro a qaramin tray ta kawo masa.

Kallonta yakeyi ido ciki ciki tundaga qasa har sama ya tsaida idanuwansa akan qirjinta yana kallon yanda numfashinta ke fita da sauri yana 'daga kirqinta tsabar tsoro.

Kar6ar ruwan yayi ya kwankwade ya rintse idanuwansa ya budesu a tsakiyar idanunta,batasan lokacin data durqushe agabansaba sbd wani irin magnet cikin idanun nasa.

Tashi yayi tsaye tareda sanya hannuwansa a aljihun wandon suit dinsa cikin qasaita da Jan aji tareda kasala yace,
Meyasa kike saka wa'innan kayan acikin gidana bayan nafada miki bakida wani 'yanci ko dama agidannan?

'Dagowa tayi cikin nutsuwa ta kallesa jiki asanyaye tace,
Duka irinsune matar tasanyo.

Kallonta yayi cikin tamke fuska dan yasan yana cikin wani hali muddin tacigaba da saka wa'innan kayan ga mugun turaren datake sawa Wanda yake Dana sanin bata izinin sanyawa sbd kasalar dayake sakar masa.

'Daki ya wuce batareda yace komaiba,
Wanka yayo tareda sallar magrib yafito palon sanye da black trouser da farar vest data bala'in fiddo da kyakkyawar farar surar damutsansa da tsafafen cikinsa.

Waya yakeda taheer cikin farin ciki sbd yana fada masane siyama Nada ciki danma tana asibiti an 'dan kwantar da ita.

Jikinane yayi sanyi sbd tausayin kaina daya kamani danjin inama zan samu nayi aure kamar ko wane aure Nima na haifi 'dan kaina,yazamemin 'dan uwa,aboki,amini,abokin fira nima na fara ha'da zuriata.,amma ga dukkan alamu banida wannan sa'ar.
Hawaye suka gangaro mata tayi saurin sharewa sbd zaid yace ko hawaye bayaso agidansa bare kuka.
Cikin rashin sa'a muka hada idanu lokacin danake sharewa,
Baice komaiba ya kashe wayarsa tareda nufar dining ya zauna.
A sanyaye na zuba masa abinci ka'dan tareda fruit salad na juya ina tunani na wuce.
Damuwa da tunanin data shigane yasa ta manta da steps din dake dining area 'din ta taka aiko akayi sama da ita,ka'dan yarage ta isa qasa taji an riqota sakin ajiyar zuciya tayi kafin ta bu'de idanuwanta data rintse ahankali ta 'dora akansa.

Rungume take ajikinsa yasaka hannuwansa biyu ya riqota,
Kallonta yake cikin tsakiyar idanunta,
Jikinsane yasaki gabaki daya itama tuni nata jikin ya mace sbd body contact dasuka samu dan babu mai rigar arziki acikinsu.

Shi yafara 'daure idonsa sbd ringing 'din da wayarsa tayi.
Zamewa tayi cikin tsananin kunya tana Jan rigarta data tattare ta kwashe.

Ha'de fuska yayi tareda 'daga wayarsa yana zama kan kujerar dining.

Hello farouk I was about to call you idan nagama dinner saigashi ka kira,
No ka gane I just need a favour inason idan khairat tasamu time tazo ta fita da yarinyar nan tasiyo mata kaya irin wa'inda take sawa I mean zannuwa dan wata gud for nothing mata nasaka take tasako mata....just dai idan khairat yasamu time tazo.

Dariya farouk yasaki sosai kafin ya 'dora da fadin,
Kai banda abinka my friend madam ta shiryoma kayan dazasu sa ka mori auren gatan da Yaya taheer yama shine kakeson khairat tazo asiya mata zannuwa sbd.......
Pls farouk am serious.
I know zaid that's why nake nake fada maka ka rungumi matarka idanma kanason wata ne zaka iya aurenta daga baya,just look yanda yarinyar take marainiya kuma very simple ga nutsuwa and she's very beautiful more than duka tarkacen 'yan matanka jst chill my friend kaci amarcinka.

Datse wayar yayi yana yamutsa fuska ahankali yace,
Zai sakarmin ciwon kai da dogon zancen nan nasa.





*****************
_1 month ltr_
Wata 'data kenan zuwansu garin amma kamar tayi shekara sbd canzawarta gabaki 'daya.
Tayi wani irin haske laushi ga wani irin kyalli da sheqi datake sbd asalin haskenta na asali yafito sbd Hutu da tsadaddun kayan amfani,
Ta ciko Samanta da qasanta shape dinta yafito sasai,
Idan kai mata kallo 'data saika qara sbd tsananin kyawu da 'daukar idon datakeyi ga uwa uba kwanciyar hankali data samu.

Ta 6angaren kaya kuwa tuni tasaba tun tana jin kunya tana 'Dari 'Dari harta saba free take yawonta cikin gidan da abinta.




Hmmmm da sauran Rina a kaba Jiddah kadakiyi saurin sakewa😭😭😭😭😭😭😭😭
Masoyan Jidda saiku tanadi tissue din share hawaye dan yanxu muka fara.



Mamuh geee
© *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*



43-44
Zaid kullum yafita aiki yadawo bai cika fitaba hakama baya shigowa da kowa palon iyakacinsa da baqinsa harabar tunda yasan batada kayan rufe jiki.

Shima kansa zaid yanayin garin ya kar6esa idan kacire tsantsar damuwar dayake ciki ta muguwar sha'awar data tarar masa dan haka yanzu bai cika zama apalo ba sbd Jidda.
Qamshinta,surarta,kyawunta da tsantsar tsaftarta sunyi masa mugun rauni sbd gaba 'daya yanzu bayada kuzari sai miskilancin nasa ya da'du sosai.


Yau da wuri yadawo dan wani irin zazza6i da ciwon ciki ke damunsa,
Driving ma kasawa yayi saida driver din farouk yaje ya 'daukosa,
Tun kafin su qarasa gida yakira doctor.

Zaune take a Palo tanajin shigowar motarsa ta miqe ta isa bakin qofar ta bu'de bata jira ya danna doorbell ba.

Doguwar rigace ajikinta iya cinya da dogon zip a gaban rigar tun daga sama har qasa ga rigar roba ce.

Kallonta yayi da idanuwansa dasuka rine tsabar azabar dayake ji,
Mararsa yaji ta qara qullewa wani irin amai yataso masa yayi hanyar 'dakinsa amma yana shiga 'dakin kan ya isa toilet jiri ya 'dibesa ya zube bakin toilet yana aman.

A ki'dime ta rufe qofar palon ta tura qofar 'dakin tashiga arude jikinta har wani rawa yakeyi.

Kansa tayi tana hawaye sbd zuciyarta bazata juri ganinsa a wannan halinba sbd ganinsa ahaka yana qona jinin dake jikintane.

Qoqarin miqewa yake amma babu kuzari ajikinsa kasancewarsa 'dan Hutu tayi saurin kamasa ya miqe duk da haduwar jikinsu na tsananta abinda yakeji ajikinsa itama anata 6angaren jitake kamar ta maqale a wutar lantarki.

Toile takaisa ta kunna masa komai ta fito,
Kafin ya fito ta gyare gurin tsaf ta qara feshe 'dakin da turare tayi kitchen dan ha'do masa hot tea.

Tana kawo tea din ta tarar dashi yayo wanka ya sanya kayan barci farare qal ya qudundune.

Tea 'din ta aje a bedside drwar tana tunanin yanda zata ce masa saitaji doorbell tayi qara saurin aje tray 'din tayi zataje budewa tajiyo muryarsa can qasa yace,
Ahaka zaki bude qofar babu indake suturce ajikinki?

Mamakinsane yakamata na yanda jikinsa ke kakkarwar zazza6i mai qarfi amma harya iya tunatar da ita kada ta bude qofa ahaka.
Da hannu ya nuna mata jallabiyarsa fara qal ta sallah yace tasaka.

Bayan tasaka rigar saidata yafa gyale kafin ta bude qofar.

Baqo tagani da briefcase ahannunsa yasaki fuska sosai yace,
Am Dr hameed, ur husb.....
Saurin basa hanya tayi batareda tabari ya qarasaba zancensa ba.

Ahakali yake takowa harsaida yakusa faduwa Dr yayi saurin tarosa.
Dubasa Dr yayi yabasa magunguna tareda 'yan shawarwari dan yafahimci abinda yake damunsa sosai.
Zai tafi saigata tafito daga kicin yace,
Ga magungunansa kibasa kan lokaci hakama idan irin wannan zazza6in mai qarfi yataso masa ki basa taimakon gaggawa ta hanyar rage masa zafin jiki da jiqaqqen towel mai tsafta idan baiyiba saiki rage masa ta hanyar ha'da jikinki da nasa idan yasamu body contact zai sauka insha Allah dan zazza6in barazanace ga irin lalurar datake damunsa.

Dr na tafiya yakoma 'daki ya kwanta,
Maganin ta dauka tabisa dashi da ruwa tana shiga cikin sanyin murya tace,
Ga tea kasha saikasha magani.
Ga mamakinta saitaga ya tashi zaune ahankali yakarbi tea 'din ya'dansha ya miqa mata hannu ta 'dora masa maganin tareda glass cup din ruwa yasha yakoma yakwanta.

'Daki takoma tayi sallah tasaka kayan bacci ta kwanta.

Daqyar tasamu ta 'dan rintsa sbd hankalinta Sam yaqi kwanciya sbd tsoran kada zazza6in yadawo masa tunda Dr yace barazanace garesa.

Qarfe biyun dare tayi wani irin rikitaccen mafarki da zaid a firgice ta tashi jikinta na rawa ta kasa samun nutsuwa da sauri ta fara kai kawo.
Ganin kai kawon bazai bata nutsuwaba yasa ta nufi 'dakinsa cikin san'da.
Ahankali ta mur'da qofar 'dakin saikuwa ta hangosa na'de kan gado yana jijjiga.
Batasan lokacin data qarasa gadon da guduba ta yaye bargon tana kiran sunansa arikice.

Wani tiririn zafi yadaki fuskarta lokacin data yaye bargon tsabar zafin jikinsa.
Toilet 'dinsa ta shiga arude ta jiqo towel da ruwan 'dumi kadan.
Cire masa riga tayi daqyar sbd gabaki 'daya jikinsa yasaki baya ya fice hayyacinsa.
Da sauri tahau goge jikinsa da towel 'din jikinta babu inda baya rawa.

Tana gamawa tashin hnkalinta ya ninku sbd jikin nasa daya ida rikicewa har numfashinsa na qoqarin 'daukewa.

Kuka tasaki tareda rungumo kansa kukan nata na tsananta.

Jikinsa taji yasaki zuciyarta tayi wani irin bugu da bata ta6a yiba nan take tahau mazari ta diro qasa ta wawuri wayarsa,da qyar wayar ta tsaya hannunta sbd rawar da jikinta keyi.
Sunan Dr ta lalubo takira,
Harta katse bai 'dagaba saidata masa kira Tara ana gomane ya 'daga.

Kuma ta rushe masa dashi yayi saurin mitsitsikewa daga bacci yace,
Kidaina kuka ki nutsu kimin

2 Comments On ZUCIYARMU DAYA
avatar
aishatu-5

1 year ago

Reply

Nice

avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment