Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonta yayi yana mamakin yanda take irin wa innan aikin daya kamata ace injin keyi.



*************
Rayuwa ta qara tsananta gareta dan wahalar datake ciki yanxu tafi tada dan zuwan zaid yazamar mata wani yankin azaba dan takoma kamar wata inji tsabar aikin wahala tun safe idan ta tashi batada wani hutu har dare.
Ta qarasa qanjamewa ta rafka uwar rama sai wuya da qasusuwa da manyan ido.

Abinda ta ura dashi shine zaid mutum ne mai tarin 'yan duniyar abokai duk dashima 'dan dubiyarne amma miskilanci ya boye nasa.,
Kullum gidan yanxu acike yake da abokanansa da 'yan mata dake haukar sonsa yana sharesu hargwarama fareeda dasukazo tare duk da itama nasha gani ya wulaqantata agabana har kuka takeyi.

Nikuwa duk wasu masu shige da fice a gidan sunsan dani amatsayin baiwa yar aiki wahalalliya.
Duk wahalar danakewa zaid da jamaarsa baita6a koda kallonaba da daraja bare nasamu wata yabo ko godiya.


Yaukam aikine dani dan zaid da kansa yabani umarnin nayi masa abinki sbd zaiyi baqi daga UK.
Farfesun kifi nayi musu da salad mai ha'deda hanta.

Bayan nagama nakai palonsa na jera a dining nadawo daki nai wanka nayi kwanciyata.

Har barci yafara daukata qarar wayar landline din dakina tayi qara
Natashi ina yamutsa fuska dan ahaqiqanin gaskia banso Tashiba ayanxu.

Salami alaikum"
Tafada cikin muryan bacci.

Wani irin yarrr yaji dan azahirin gaskiya duk duniya bayan iyayensa dasuka rasu baitaba kiran wani ko wataba akai masa sallama.

Ahankali yasaki ajiyar zuciya cikin cool voice yace,
Yaya taheer na nan kuwa?

Daburcewa tayi tana dan rawar murya tace,
Eh 'dazu ina aiki yashigo ya haye sama kuma banga saukowarsa.

OK kije kice baqina sun iso inaso su gaisa kuma wayoyinsa duka a kashe.
Dam gabanta ya buga da qarfi dan tasan wannan saqon nasa da wuya idan baija mata duka da zagiba amma yata iya kuma rashin isarda saqon ma wani balain ne.








Mamuh geee
[12:31, 1/4/2018] ‪+234 813 272 6929‬: © *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*

For you my *zinnie*
And *Maman abba*


25-26
Taka benen take cikin fargaba da tsoron abinda zai biyo baya dan ya hanata zuwar masa koda hanyar dakinsa.
Tsayawa tayi bakain qofar dakin tana jinjina alamarin dake shirin faruwa da ita.
Hannunta na karkarwa takai ahankali ta buga qofar cikin tsoro.
Shiru babu alamar motsi bare abude.
Tunanin baijiba yasa ta kuma qwanqwasawa harso uku.
Afusace ya bude qofar idanuwansa a birkice ga alama barci yake sosai.
Cikin sauri ta bude baki zata fadi saqon amma tuni yakai hannu ya doke bakin nata saikuwa ga jini ya 6alle.
Gashin kanta dake dunkule cikin hijab ya damqo yafara janta har zuwa qasa ya wurgar da ita tsakar palon tareda take yatsun hannunta yana cewa,
Wat did I tell you gameda zuwar min daki.
Cikin kuka da azabar hannunta daya take tace,
Yaya zaid ne ya.......
Shut up,zaid din zakiyiwa qarya,muje gabansa naji idan qarya kikayi masa wlh yau saikin bar gidan nan.
Sake damqarta yayi ya fara janta zuwa sashen zaid.
Daidai qofar palon ya watsar da ita saida goshinta ya bugu shima ya fara jini.
Zaid ne ya fito dan zuwa kiran taheer din da kansa
Saurin ja da baya yana kallon yanda bakinta da goshinta ke jini ga wani irin kuka mai tsima rai datakeyi.
6ata fuska yayi da 'dan qarfi yace,
What's this?pls take her away Yaya kukanta yana damuna.
Da hanzari baqin palon suka fito suna kallon Jidda kamar wadda tai hadarin mashin.
Zaid did you send this village girl to me?
Dafe goshinsa yayi yana yamutsa fuska yace,
Ohh god Yaya dama kadaketa ne sbd aiken danai mata.
Yes zaid I thought she was only looking for excuse to disturbed me.
But you should've ask me first Yaya taheer,for godsake she's ur wife.
Tsaki yaja rai Adan 6ace sbd kansama daya farasarawa ya juya ya shige palonsa.
Shima taheer 6ace da rai ya juya yabar gurin hakama sauran baqin.

Fareeda kuwa bayan kowa ya watse ta matso ahankali cikin tsananin tausayi da mamakin shin ina iyayen jiddan suke data kasa komawa garesu tabar wannan baqar wahalalliyar rayuwar.
Durqusawa gabanta tayi murya a shaqe tacewa jiddan,
Kina buqatar wani taimako?
Duk da tana cikin wani hali saidata dago da sauri ta kalli fareedar sbd wannan shine karo na farko da wani dan Adam yaji tausayinta tun bayan rasuwar abbanta da dadyn lokoja.
Wasu sabbin hawaye suka gangaro mata ta girgiza kai alamar aa ta miqe tanajan qafafu ta tafi.
Tana shiga daki ta sulale qasa tareda saikin wani ginshiken kuka.
Kuka ta dirza sosai na tsawon lokaci kafin ta lallashi kanta ta miqe ta fada toilet ta wanke jikinta tayo alwalar sallar magriba da ake kira.

Da daddare ta shirya fruits din zaid ta dauka tayi 6angarensa.
Tana shiga taci karo da wata budurwa mai masifar kyau fara sosai kamar baturiya
Sanye take da qananan kaya dasuka fidda qirarta sosai sai gashinta data saki har kafadu.
Zaune take amma Rabin jikinta gaba daya nakan zaid.
Saurin 'dauke kai nayi na nufi dining zan aje naji muryarsa mai tsananin sanyi yace,
Kai kawo min anan.
Najuyo kenan saiga fareeda daga daki tazo gaban zaid ta tsaya tace,
Zaid inason magana dakai.
Yana cigaba da latsar wayarsa yace,
Uhumm inajinki.
Cikin jin ciwon yanda yai mata tace,
In private nakeson maganar.
Kallonta baquwar budyrwarsa tayi tace,
Ki fada masa anan tunda yace ki fada.
Kallon zaid din fareeda tayi taga still baida alaman tashi sai hawaye suka 6alle mata tace,
Zaid son danakema ne yasa nakasa tsayawa nayi karatu acan ina binka kamar jela amma sbd wannan banzar kake wulakantani.....
Shut up ya fada yanda tashi tsaye,
Na taba cewa ina sonki?
Nataba cewa ki Bini?
In dazaki riqe son naki ki daina bina danafi murna,and dakike magana akan Nina she's my guest,tazo daga UK just taganni so should I just throw her out of d house sbd ke?unbelievable.
Ohhhhh you are driving me crazy..
Barin gurin yayi afusace yana girgiza kai.





Mamuh geee
[12:32, 1/4/2018] ‪+234 813 272 6929‬: © *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*



27-28
Washe gari nagama komai nayi breakfast na ajewa Yaya taheer nasa a dining nadau nasu zaid natafi kai musu.
Koda nakai tray din farko babu kowa a falon na byun ina zuwa na tarar dasu duka ukun a dining.
Na aje zan juya Nina takirani
Ina dawowa tace kadana kuma kawo musu abinci da yagaggun kaya dan ita tanajin qyanqyami.
Batareda ya kalli gefen da Jidda takeba yace kinji abinda tace karki qara.
To tace tareda wucewa simi simi.

Da rana tana kicin tana aiki taji ana knocking qofar palonsu ta aje yankan cabbage din datakeyi taje ta bude.
Fareeda ce da kaya ahannunta ta gaidata cikeda ladabi tareda matsawa tashigo palon.
Xama fareeda tayi tana qara kallon palon tareda jinjina tsafta irinta Jidda sbd qamshi tareda sanyin ac daya gauraya Palin.

A nutse tace,
Kina buqatan wani abune?
No fareeda tace tareda miqo mata kayan hannunta tana cewa kayana ne nabaki idan ba matsala.
Hannu biyu tasa ta karba dan tana tsananin buqatar sutura.
Nagode"tace cikin sanyin murya kafin takai daki tadawo.
Tareda fareeda suka qarasa aikin dan fareedar tace itama aikin zata koya.

Ahankali sukayi sabo da fareeda dan tare suke shiga kicin fareedar na koyon aiki agurinta.
Taheer ma dai babu abinda ya canxa ahalinsa dan yanxuma ko agaban fareeda jibgarta yakeyi saidai idan yagama fareeda ta rarrashet.



**************

Yau gidan tsit ba kowa daga ita sai zaid,
Taheer yayi tafiya,fareeda taje Lagos gurin iyayenta dan sun dawo daga tafiyar dasukai.
Falon zaid tagama gyarawa ta haye sama ta gyara dakunansa dan yana garden din gidan yana shan iska.
Toilet tashiga tashiga ta fara wankewa gurin kunna ruwa hannunta yataba shower ruwanta ya jiqa mata hijab.
Dan qaramin tsaki tayi tana cire hijab din tace,
Mitss bayan hijab ma harda gashina da fareeda ta gyaramin kafin ta tafi.
Zare ribom din tayi tana kakka6e gashin bayan ta dora hijab dinta a kan qofar toilet din dan yadan sha iska kafin tagama.

Zaid daya shigo dakin yaji baiji motsintaba saiyayi tunanin tagama ta fita.
Tubewa yayi tareda daura towel a qugunsa ya fada toilet din.

Sam batasan dashiba sai ganinsa tayi batasan sanda ta kurma ihuba.
Cikin zafin nama ya fizgota da hannu 'daya dayan kuma ya rufe bakinta.
Wata irin kasalace ta dirar musu lokaci daya atare.
Fuskarta yakalla tareda dogon gashinta murya a kasalance yace,
Kinason fasamin dodon kunne ne.
Ahankali tace,
Yi hkr naji tsorone.
Sakinta yayi tayi saurin fizgo hijab dinta garin sauri tsanci yajata qarfi..
Cikin sauri ya riqota amma kasancewar akwai ruwa ko ina a toilet din sai shima qafafunsa suka kasa tsayawa saiko gaba dayansu suka tub din wanka dake cike taf da ruwa.
Itace a qasa shiyasa gaba daya kanta yayi jagab da ruwa.
Wani irin kallo zaid kebinta dashi idanunsa na Neman qanqancewa sbd ganinta kwance acikin ruwa.
Da sauri ta miqe ta fito tub din tabarsa aciki zata fice,
*JIDDAH*" cak ta tsaya batareda ta juyoba cikin tsananin mamakin ashe yasan sunanta.
Fitowa yayi ya nufota tayi saurin rintse ido saitaji ya fice.
Ajiyar zuciya tasaki sai gasa yadawo da jallabiyarsa da 'dan qaramin towel na tsane kai ya miqa mata.
Rufe toilet din tayi ta cire rigarta data jiqe tana digar ruwa tasaka jallabiyarsa tareda nade kanta da towel din tayi saurin fitowa tabar sashen gaba 'daya.

Tunda ta fito palon zaid idanuwansa suke akanta dan dawowarsa kenan daga tafiyar dayayi kuma idan ba gizo idanuwansa ke masaba to lallai rigar zaid ce ajikinta kuma ga dukkan alama wanka tayo daga can.
Ras gabansa ya buga da qarfi sbd wani zargi mai qarfi daya dirar masa kafin ta qaraso yayi saurin shigewa Palo.
Tana shigowa tagansa tayi saurin durqusawa ta gaidashi.
Bari tsaya amsawaba ya fizge towel din kanta dan tabbatar da zarginza.
Aikuwa zargin nasa ya tabbata dan ganin gashinta a jiqe.
Shaqota yayi da qarfi cikin tsananin 6acin rai yace,
Me kikayi?
Meyasa kika cutatar dani adaidai lokacin da nayi nadama natuba zan karbeki amatsayin mata Ashe tuni hkrinki ya qare kike cutar igiyar aurena dake kanki.,
Kin cuceni kin cuci qanina dakika koyawa halinki na zina.
A razane ta 'dago ta kallesa zatai magana yasakar mata wani mahaukacin marinda jini ya 6alle ta hancinta da bakinta.
Ko motsi batayiba sbd wani irin radadi da zuciyarta keyi.


Janta yayi kamar kaya yayi sashen zaid da ita ya wurgar bakin qofa tareda kiran sunan zaid da qarfi.
Cikin nutsuwa zaid din yafito yana kallan Jidda fake bleeding ta hanci da baki daidai nan fareeda tasawo kan motarta gidan Aida gudu ta qaraso gurin tareda tallafo Jidda dake kuka riris ajikinta.
Fuzgota da qarfi taheer yayi tareda cillata gaban zaid cikin 6acin rai yace,
*Ni taheer na saki Jidda saki uku*
Sbd laifin cin amana Dana kamata dashi,
Wannan shine hukuncina na farko na biyun kuwa shine zan hadata aure da Wanda suke taren ako wane lokaci.

Yana gama fada yabar gurin yana huci...



Mamuh geee
[11:48, 1/5/2018] ‪+234 703 300 1537‬: © *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*

For you my *zinnie*



29-30
Ahankali ta fara rero wani sabon kuka tana fadin,
Fareeda wlh banyiba,bansan ma wani Abu daya shafi zancen dayake fada,bantaba zina ba,na rantse ban....kukane yaci qarfinta tacigaba da rero abinta cikin qonan rai.

Kukan datake rerowa ke shigarsa ahankali yana wargaza nutsuwarsa,rintse ido yayi da qarfi yacewa fareeda,
Take her away hayaniyar kukanta na damuna and pls kema I want to be alone.

Riqota fareeda yayi suka nufi dakin Jidda din.

Duk yanda taso daina kuka ta kasa dan ranar yau tana daya daga cikin manyan ranakun baqin cikinta.

Fareeda tayi rarrashinta daqyar kukan ya tsagaita amma banda hawaye dansukam ba ranar tsayawarsu gareta.




***************

3 month later,

A yau tacika wata uku cif da taheer yasaketa duk da babu wani wani alamari na aure daya shiga tsakaninsu.
Azaba kuwa yanxu ta ninku sosai,zagi kuwa ansamu qari dan yanxu har mazinaciya yake yake ce mata,
Duka ma yanxu ko babu laifi dan tunda yayi sakin baiyi tafiyaba.
Akwai ranar da yayi mata wani irin duka agaban zaid saida zaid din dakansa ya dauketa yakaita daki.
Fareeda da kanta tazo tayi kusan kwana hudu agidan tana jinyarta kafin takoma gida,nikuma dama agurina da daacan da yanxu duk dayane dan banta6a jina amatsayin mai aureba bare yanxu da babusa.

********
Yau juma'a tun safe nakejin sanyin jiki tareda faduwar gaba amma saina danganta hakan da weekend din daza'a shiga sbd taheer baya fita.

Taheer ne yayo ado cikin wata tsadaddiyar shadda fara tas harda babbar riga.
Kirana yayi na duqa gabansa ina gaidasa.
Bai amsaba sai kaya daya miqo min,
Farar Australian shadda ce mai masifar tsada tareda agogon diamond da sabbin takalimi masu kyau da tsada yace,
Jeki kikaiwa zaid kice ya shirya cikin wainnan kayan lokacin sallar juma'a yakusa.

Tana zuwa tayi knocking yace tashigo.
Kayan ta miqa masa tareda fadar sauran daqon ta koma.

Baiyi wani mamaki ko tunani ta shirya ya nufi palonsu taheer din yashiga yana baza wani irin qamshi mai sanyin dadi.
'Dauke da cooler ta fito kicin zataksi dining idanunta suka sauka akansa saidai lokacin shima nasa suka sauka anata.
Saurin dauke kai yayi yana kallon taheer daya sauko yana fadin su wuce kada suyu latti.

A hanyarsu ta zuwa cikin mota ya kalli zaid yace,
Zaid I'm sorry am saying it now,I just wanted to surprise you ne.,
Am getting married today.

Kallon mamaki zaid yayi masa cikin nunajin zafinsa yace,
Amma yaya taheer zakayi aure yau shine kake fadamin ahanyarmu ta zuwa daurin auren.

Sorry little brother abun ne yazo da sauri sbd program 'din dazani na one year a Morocco kuma ina buqatan zuwa da mata.

Idan hakane Yaya maiyasa ka saketa?

Zakasan dalilina nayin hakan bada jimawaba.

Suna isa babban masallacin jumaar akayi sallar juma'a ana gamawa aka fara daurin aure.

An 'daura auren taheer abdulhameed da siyama shitu,

Sai daurin aure nagaba da'aka daura za'a fada sunayen sai taheer yadau hankalin zaid batareda yajiba......




Mamuh geee
[12:30, 1/5/2018] ‪+234 703 300 1537‬: © *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*

For you my *zinnie*


31-32
An watse taro lpia amma ga babban mamakin zaid dukkanin friends dinsa dake kusa sun halarci daurin auren.

Gida suka wuce suna isa taheer yace zaid yabiyosa palonsa zaiyi magana dashi.

Suna shiga ko zama basuyiba saiga Barr basheer yashigo shima cikin shiga ta alfarma wanda ga alama shima ya halarci daurin auren.
Gaidasa yakumayi dasu ya 'Dora dayiwa taheer congrat.
Cikin farin ciki ya amsa tareda cewa,
Bismillah Barr zauna.
Murya ya daga ya kwalomin kira.

Cikin nutsuwa da sanyin jiki ta iso,tana ganin taheer wani masiffen dadi yakamata harsaida fuskarta ta nuna.

Durqusawa tayi tagaidasa ta miqe zata kawo masa ruwa taheer ya dakatar da ita.
Fara magana yayi cikin tamke fuska,
Barr jiya kana dawowa naje gidanka nayi maka bayanin komai na daddy kafin yarasu yace baiyafe a cire Jidda daga zuriarsaba,
Lura danai zaid zaifi iya riqe amanar dad yasa na yanke wannan hukuncin,kuma daliline yasa nayi haka sbd lura danayi suna buqatar hakan.,kuma ni babu ko wani kallon aure dana tabayi mata bare wani Abu yashiga.,dan haka kaima ka shaida yau auren da aka daura musu kuma na......
Wait pls Yaya taheer.
Yafada da qarfi.
Nifa bangane mai kake ta qoqarin fadaba.

Dafasa taheer yayi yana fadin,
Calm down my little b,idan ka kwantar da saurareni zaka fahimci zancena.
Abunda nake nufi anan shine kai zaid qanina da Jidda daddy yabarmin amanarku kuma wannan shine babban gatan dazan iyayi muku na daura muku aure ayau,Barr basheer yayi wakilin Jidda nikuma nayi naka, ayau muduka andaura mana aure dan haka inaga is better idan ta hada kayanta takoma 6angarenka dan anjima kadan za'a fara gyaran kawomin amaryata.

Babbar rigar jikinsa ya fisge taredayin cilli da ita yana fidda wani irin zufa yafara magana cikin qulewa,
Yaya na ta6a nunama wata mace aduniyarnan nace insaonta?
Nata6a fadamaka inasan nayi aure?
Dady tun yanada rai yasan dani amma ya aura maka ita,
Wannan shine amanar da dady yabar maka tawa?
Ka ruguza rayuwana ta hanyar dauramin aure da wannan abar?
Na ta6a nunama ina sontane,matarkace fa.....o oo wait wait oh my god Yaya kana nufin ni kake zargi da ita lokacin dakace tana...

Wani irin 6acin raine yataso masa zuciyarsa ta kawo iya wuya,idanunsa suka kada jajir
Ya dunqule hannu ya bigi center table din palon saidaya fashe shima hannuwansa suka fara tsiyayar jini.

Taheer da Barr atare suka miqe,taheer yayi saurin kamo hannun zaid din cikin ru'du yake cewa,
Wat do you think u're doing zaid? Pls ca.....
Yaya tun wuri ka warware wannan auren dan bana sonta,ban ta6a sontaba, and I swear ban taba aikata zinaba barega matarka.,
Kuma Sam wannan bata cikin tsarin matan danake iya so,bazan ta6a sontaba.,pls Yaya am....
Daga masa hannu zaid yayi cikin tamke fuska yace,

Zaid idan harni yayakane da kakeso to tabbas bazaka saki jiddaba,zaka bar wannan auren,inason naga idan zaka iyayin abu ko sadaurwa sbd ni kamar yanda nake sadaukarwa sbd kai ako yaushe.

Yana gama fadar haka yabar palon shima zaid a fusace yabar palon yanaji kamar zuciyarsa zata fashe.


Allah sarki Jidda yauko hawayen babu sai idanuwanta dasuka bushe sukai jajir.
Ahankali Barr ya matso tareda aje mata damin kudi yace Jidda ga sadakinki nan,
Kuma Jidda kiyi hkr insha Allah wannan auren zai canxa rayuwarki.,kici gaba da jure Rayuwa Allah na nan.

Harya gama magana ya fice ko motsi batayiba,
Ahankali ta miqe tayi daki tanajin zuciyarta na wani irin ciwo,
Kudin sadakin ta kalla sai kuka yazo mata mai cin rai.
Ni Jidda haka zanyi rayuwata kowa baya sona kowa guduna yakeyi,haka zan qare Rayuwa gurin bautawa 'yayan dadyn lokoja suna tangariri dani.

Kuka take sosai hartana shaqewa har jama'ar amaryar taheer suka fara zuwa dan gyara duk da komai najin dadi akwai a gidan.






Mamuh geee
[12:55, 1/9/2018] ‪+966 59 966 3591‬: © *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*


_Kuyi hkr two days I was very busy ne amma yanxu alhamdulillah_ .



33-34
Miqewa tayi da qyar tanabin bango sbd jiri ciwon kai na kukan data yini tanayi.
Toilet tashiga tayo alwala tazo tayi sallah tana cikin addua ne wayar landline din dakinta tayi ringin.
Murya a dashe ta daga.

Taheer ne yace,
Kifito baqin kawo amarya sunfara zuwa kiyi aiki kuma ki tabbatarda kinkaiwa zaid abinci dan kada 6acin rai ya hanasa cin abinci wani abu yasameshi.

Qurawa wayar idanu tayi bayan ya aje tana tunanin yanda ya damu da damuwar 'dan uwansa amma ita akai baya kawota.


Mutane se sosai agidan anata gyare gyaren sauran dakuna biyu dake palon qasa kusada nata.

Durqusawa tayi har qasa ta gaidasu babu Wanda ya kalleta bare ya amsa.

Kicin tawuce ta 'dorawa zaid coffee tareda yanka masa fruits ta jere a tray ta nufi 6angarensa.

Ahankali take buga qofar dan sanin bayason hayaniya bare yau da ransa ke 6ace.
Ganin tajima a tsaye a tsaye bai budeba yasa ta murda kofar tashiga ahankali tareda 'yar siririyar sallamarta

Dining ta nufa cikin san'da sbd batason su hadu.

Wata irin razananniyar tsawa ya dako mata
tayi saurin tsayawa tana kyarma.
Cikin tsananin fushi da 6acin rai yataso kamar zai daketa,
Tayi saurin aje tray din zata juya da sauri sbd tsoro
Ya shaqota ta baya tareda birkitota yafara magana cikin jin haushinta,
Ke kikafadawa yaya taheer kina sona dahar ya yankemin jin dadin Rayuwa ta hanyar dauramin aure dake.,
Kalleki ki kallen kinga nayi miki kama da mahaukacin dazai soki harya aureki?
Cikin tsananin karaji 'daga murya yace,
Badake nake magana ba?

Rintse idanuwanta tayi hawayen dake cike dasu suka gangaro.

Abinda zan fada miki daga yau shine kadaki qara bari naga wannan bakar fuskar taki,banason ganinki,so stay away.

Ahankali cikin sanyin jiki ido cikeda hawaye ta 'dago ta 'dorasu akansa tana masa wani irin kallon mai yasa kowa ya tsaneta.,
Duk rashin son da taheer ke mata batajin ciwo kamar yanda yanxu takejin ciwon zaid baya sonta.

'Dauke idanunsa yayi ya juyar da kai yace,
Stop looking and get lost.



*************

Lokacin kawo amarya yayi gida ya kaure da hayaniya da gu'dar kawo amarya.

Sam banyi tunanin fitowaba dan gudun laifi ga kuma azababben ciwon kai da qirji dake damunta.



Washe gari daqyar na iya tashi nayi sallah sbd ciwon daya fara cin qarfina.
Bayan gari ya gama wayewa wayar dakin tayi qara
Cikin dauriya na 'dauka,
Ki fito Palo yanxu zanyi magana.

Taheer ne yana gama fada ya kashe.

Hijab ta zura ta futo tana hada hanya.

Zaune yake a palon cikin adonsa na shadda sky blue tadayi masifar yi masa kyau matuka sai amaryarsa zaune akusa dashi tana wani yamutsa fuska.

Farace amma daga gani na kanti ne dan yanda fuakarta tayi wani kala kala,
Tsawo ne da ita sosai gata siririya sosai,ta 6angaren nonuwa da hips kuwa babu ko 'daya komai a shafe yake.,
Sanye take da Riga da skirt na wani tsadadden lace daya matseta shiyasama rashin qibar tata yafito fili.
















Mamuh geee
[12:56, 1/9/2018] ‪+966 59 966 3591‬: © *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 🐄


🌑🌕 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

© *Mamuh geee*



35-36
Nesa kadan ta durqusa ta gaidasu cikin sanyin murya.

Taheer kawai ya amsa cikin basarwa ya dora da fadin,
Jidda wannan matatace siyama,ki zauna da ita cikin girmamawa sbd zaki zauna anan ne na 'dan wani lokaci kafin zaid ya sauko daga 6acin ransa na aurenku,idan kikai ba daidaiba kuwa wlh tattarawa zakiyi kibarmana guri.

Kallon siyama yayi yace,
Zaki fada wani abu?

Kallon banza ta watsawa Jidda kafin tace,
No banida abun fada kawai ta tashi taje dan banason ganinta.


Daqyar na iya soya musu dankali da qwai,na dora ruwan tea a cattle naji wani irin jiri ya debeni kafin nayi wani yunquri sai amai ya biyo baya,
Tun inayi har qarfina ya qare daganan bankuma sanin komaiba.




***********
Sama sama nakejin muryoyi harna bu'de idanuwana suka sauka akan nurse 'din dake dakin.

Cikin sauri 'dayar nurse din ta matso tana fadin,
Sister jamila ta farka ki kirawo fareeda ko?

Basai ankiraniba gani na iso.

Juyawa sukai bakon qofa ,itakuwa dince ta qaraso ta zauna bakin gadon tace,
Jidda kin farfado bayan kwana biyu akwance.

Ware idanu tayi,
Fareeda tace,
Yes,naje taya yaya taheer murnar aure na tarar dake a kicin kin suma.,
Jidda bazakiyiwa kanki fa'daba kibar wannan wahalalliyar rayuwar ki koma ga iyayenki.

Hawayen baqin cikine suka 6alle mata babu shiri fareeda tabar zancen.

Kwananta hudu a asibitin kafin aka sallameta.
Su taheer kuwa babu Wanda ya damu da inda take bare suje dubata.

Gida suka nufa kai tsaye har 'daki fareeda takaita bayan wulaqancin da siyama ta zabga musu kafin tabari suka shiga.




Tundata dawo wahalarta ta dawo sabuwa ga tarin cin zarafi da wulaqanci daga siyama,

Itake share ko ina har 'dakunan siyama sannan ta girkin abinda siyama tace shi takeso,
Idan ta girkama saitaga dama take bata taci.,idan kuwa siyama tafadawa taheer Jidda tai mata laifi yanxu baya dukanta saudai mari.,
Fareeda ke taimakonta to itama din tadaina zuwa sbd wulaqancin da zaid ke mata.

Zaid kuwa zan iya cewa tun ranar daya koroni bankuma ganinsaba duk da yana shigowa har Palon gurin yayansa.


Yau su duka zaune suke a dining har zaid dan tun bayan auren taheer anan yakecin abinci tareda 'dan uwansa da siyama.

Na riga na Jere musu komai a dining din dan gudin zaid ya ganni tunda yace bayason ganina kullum da wuri nake Jere komai nashigewata daki.

Anty siyama ta qwalomin kira na fito cikin 'Dari 'Dari nace,
Gani Anty.
Yatsina fuska tayi kafin tace,

Jeki cikin fridge ki kawomin kunun ayar dana saki kiyimin.
Da sauri na juya na 'dauko gurin ajewa a dining tsautsayi yasa ya zubewa siyama gaba daya ajiki.

Ingizata siyama tayi da qarfi cikin 6acin rai,
Qasa ta fadi zata

2 Comments On ZUCIYARMU DAYA
avatar
aishatu-5

1 year ago

Reply

Nice

avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment