Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anan nextweek nima zandawo idan asiya tagama bikin qanwarta saimu tahoma da ita kafin nan tadan sake sbd tana cikin matsanancin hali yanxu.

Kallon Barr yayi danshi tuni ya manta da wata Jidda sai yanxu ya tuna.
Babbar damuwarsa itace idan zaid yaji rasuwar dady zaice zai dawo to ya zaiyi da wannan village wahala da aka maqala masa sbd yasan sarai zaid baya zama gurinda ire irensu suke barema rabonsa da Nigeria tun yana primary to yanxu......
Katse masa tunani Barr yayi da cewa,
Idan kaga da matsala zaka iya tafiya da itafa.

No babu matsala barr kawai dai akoya mata tsafta pls.

Ba damuwa za'a koya mata komaima Allah ya tsare hanya bara nazo nakaika airport.





***************
Yau kwanansu abbanta shida da rasuwa kuma duk iya mamaki tabawa mutanen gidan dan kuwa ta dangana ta miqa alamuranta ga Allah ta maida himma gurin yi musu addua.


Tuni ta washe ta 'dan canza sbd canjin sutura da samun lafiyyan guri hadi da abinci mai kyau.
dan kuwa kudi bashir ya fitar yasiyo mata sutura akwati biyu.


Anty asiya ma matarsa tana iya qoqarinta gurin ganin ta lurar da ita mahimmancin tsafta da qamshi.
Dama Jidda mai tsaftace sosai rashi ne yamaidata tamkar almajira.

Kwanansu takwas suka koma abuja dan dama Barr da matarsa a abuja suke biki yakawosu yolar.

Hankalinta ya 'dan kwanta zamanta da Anty asiya saidai tana nan yanda take babu farin ciki ko kadan atare da ita dan kuwa tuni sukayi hannun riga.
Murmushi kuwa zata iya cewa tafi shekara biyar bai hau fuskartaba.

Yanxun ma ahaka take bata murmushi,bata dariya bata farin ciki kuma bata kuka.
Koyaushe a zaune take tana tunani.

Kwanansu 'daya da dawowa bashir yakira taheer yafada masa zasu kawo Jidda.
Saurin katsesa yayi da cewa,
No Barr bana nan nayi tafiya zuwa Lagos sai next week zan dawo ka qara riketa agurinka kafin nadawo.
To kawai Barr yace badan ya yarda da taheer din baya gariba.



1 *week later*

Barr yakuma kiransa nanma wata qaryar ya shimfida masa Barr yace,
Tunda dai maigadinka yana nan gobe zankaita idan kadawo kasamu matarka a gida.
Yana gama fadar haka ya kashe wayarsa.


Washe gari da daddare asiya ta shirya mata komai na kayanta a akwatinanta suka tafi kaita gidan.

Wani mahaukacin mansion suka shiga bayan an wangame musu gate.

Parking sukayi asiya nabin gidan da kallo ln tsoro sbd kyansa haryayi yawa.

Part biyu acikin gidan suna kallon juna kuma komai nasu iri data ne gashi kowanne upstairs ne.

Part din farko suka qwanqwasa saiga Cook din gidan sanye da kayansa na cook ya bude musu qofar palon.






Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[21:30, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA._*

漏 *Mamuh geee*

_Bismillahir-rahamanir raheem_
_

_Godia Mara adadi ga dukkanin masoya,makaranta da marubuta masu kira da turo saqon nuna qaunarsu,.ni Mamuh geee nagode..luv you too all_ 馃拫


13-14
Kallonsu yayi cikin girmamawa yace,
Welcome sir.
Thank you"Barr yace tareda cewa,
Is your boss around?
Yes sir but he's in his room upstairs and I don't go there.

Shigowa palon sukayi suka zauna a lafiyayyun royal kushins din dake Palon.
A qasa jidda ta zauna tana jiki a sanyaye dan duk da bata nutsu ta kalli gidan dakyau ba tundaga gate tasan rayuwarta batada gurbi ko qalilan a irin wannan rayuwar.

Abbana Allah yaji qanka kaida daddy dasu inna,
Allah yabani qarfi da juriyar rungumar ko wace irin qaddara dazata zomin anan gaba.


Anty asiya kuwa kalle kalle take a palon saboda iya rayuwarta bata ta6a ganin hadadden gidan da aka narkar da uwar dukiya kamar wannan ba bare da Barr yace mata duk haduwar wannan palon batayi haduwar 6angaren qanin taheer dinba wato zaid.
Jitayi tanason ganin wannan zaid din da mijinta yace yafi taheer a komai duk da tsanani kyau da dukiya irinta taheer.

Sundau minti talatin a zaune saiga qarar saukowar taheer din daga bene.

Gabantane ya fadi da qarfi sbd tsananin tsoron mugun kallon dayake mata na qiyayya da kyama a duk lokacin dasuka hadu.

Zama yayi yana gaisagawa da Barr kafin ya kalli gefen datake yace,
Bakya gaida mutane ne ke?
A ladafce tace,
Ina wuni?
Bai amsa ba yakira Samuel cook dinsa yace yadau kayanta yakai mata bedroom din palon.
OK yace tareda sungumar kayan yayi hanyar dakin dasu.

Kama hannunta Anty asiya tayi sukabi bayan Samuel zuwa dakin.

Gyara zama Barr yayi yace,
Taheer dan Allah kaji tsoron Allah ka taisawa marainiyar nan ka riqeta amana.
Iya abinda zanfada kenan.
Miqewa yayi tareda kiran asiya.

Miqewa tayi tareda kallon Jidda tace,
Jidda kadaki manta Allah aduk lokacin da kikaga Sabon alamari yasameki.,ki zama mai juriya da takawakali.

Jajayen idanunta ta dago ta kalli Anty asiya cikin dauriya tace,
Nagode.

A Palo ma cikin danne damuwarta takalli Barr basheer tayi godiya tana kallon qasa.

Har bakin mota ta rakasu suka wuce.

A sanyaye ta juya tashigo palon cikin nutsuwa.

Baya palon yakoma dakinsa dake sama.

Dakinta tashiga tareda zama a bakin gadon dakin tana kallon dakin.

Gado ne kawai sai wardrobe aciki sai toilet.bayansu babu komai aciki.

Kiran sallar ishai taji ta tashi tashiga toilet din tayo alwala tazo tayi sallah.

Xamanta tayi a daddumar bayan ta idar.
Shiru tayi cikin dogon tunani har qarfe sha biyu ta buga bata saniba.

Ahankali ta zame tayi kwanciyarta a qasan tana rintse ido cikin kewar abbanta.


Qarfe biyar ta tashi tayi sallah tacigaba da zama agurin.


Hargari yayi haske tana gurin zaune.
Qofar dakinta aka qwanqwasa ta miqe ta bude.
Samuel tagani tsaye sanye da kayansa na gida bana cook ba.

Sunkuyar dakai yayi yace,
Oga nakiranki.
Biyosa tayi gabanta na faduwa.

Zaune yake a kan one sitter yana karanta news paper.

Daga nesa kadan ta tsaya tareda sunkuyar dakai.

Baqin cikintane yazo masa iya wuya ya juyo a hasale ya kalleta a wulaqance yace,
Naga alamar daqiqanci da qauyanci tareda rashin tarbiya sunyi miki kanta.,
Toki bude tosashiyar kwakwalwarki da kyau kiji abinda zan fada.

Ni taheer ba sa'anki bane,babu abinda yakawoki rayuwata sai tarin baqin ciki da wahala.

Samuel kaje na sallameka daga yau.

To yace a sanyaye tareda ficewa.

Kekuma ki daga yau ke zaki ringa aikin kicin,da gyara koina a cikin gidan nan hakama wankin cars dina da bawa flowers ruwa tareda share harabar gidan nan gabaki daya danyau na sallami duk yan aikin gidannan maigadi kawai na bari.

And one last thing idan kika kuskura kikayimin kuskure ko banna tareda qazanta saikinyi danasanin zuwa duniya..stupid village girl.

Wuce ki fara aikin tun yanxu.

Jiki na rawa tashiga kicin ta tsaya tana tunanin mai zatayi.
Gudun laifi yasata fitowa ta tsaya nesa dashi kadan tace,
Me zanyi?

Tasowa yayi tareda wuceta ya haye samansa yana cewa,
Kitabbatar dakin hadamin breakfast kala biyu kafin na shirya na fito.




Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[21:30, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA_*.

漏 *Mamuh geee*

_Bismillahir-rahamanir raheem_


15-16
Jikinta har 6ari yakeyi sbd sauri tahau aikin.
Ba sosai ta iya aikinba shiyasa ta hada Abu mai sauqi.
Daya tasoya masa da egg sai plantain da ruwan tea.

Daya sauko baiciba saima mugun Marin Daya zabga mata sbd magin dayayi yawa a egg din.


Tana hawaye ta share palon tas tareda mopping dinsa takoma kicin tayi wanke wanke ta gyare kicin din.

Harabar gidan ta kalla nan take wasu marayun hawaye suka gangaro mata sbd masifar girmansa harta baci.

Fara shararsa tayi tana share hawaye.
Dakyar ta iya miqewa tsaye daidai bayan tagama sharar.
Motacinsa guda hudu tahau wankewa saida suka wanku kafin takoma kan flowers tafara basu ruwa.

Ana kiran azahar tana gamawa tana jiki da qyar tashiga palon tayi dakinta tana nishi da qyar sbd yunwa ga qafuwanta dake rawa sbd wahala.

Zata zauna kenan ta tuna da yace azahar zai dawo.
Da Sauri tayi kicin tana 'dingisa tahau aiki.
Taka tsantsan tahauyi gurin girkin cikin ikon Allah kuwa komai yayi daidai baiyi yawaba baiyi kadanba.

A dining ta jera masa tayi dakinta tana hawayen yunwa dan yace muddin baidawo yaci abinciba kadata kuskura taci koda yunwa zata kasheta.

Wanka tayi tayi sallah tazauna jiran yadawo ya sanmata abincin tasamu taci ko hanjinta sa daina kuka.



馃寱馃寫馃寱馃寫馃寱馃寫

Rayuwa tayi mata mugun tsanani,
Azaba kuwa harta fara sabawa da ita.
Yanxu ta saba da sabuwar rayuwar rashin jin dadi da yanci data zo mata.

Kullum idan ta tashi zata share gidan tsaf tayi mopping ta share hatabar gidan tabawa flowers ruwa.

Kyawawan mari kuwa kusan kullum saita samu dan taheer mutum ne mai zafin hannu.

Tsabar azaba,wahala da yunwa kuwa tuni suka samu matsuguni a hanjinta dan Jidda tuni ta koma kamar qwarangwal sai manyan idawanta dazasu baka tsoro.
Fatarta kawaice tayi kyau sbd samun lafiyayyen guri.

Taheer kuwa dama bai cika zama ba dan yanxu kullum cikin tafiye tafiye yake dama can ko yana gari ba ruwansa da ita iyakacinta girki da wahalar gidan gairkinma saiya ga dama yakeci idan kuwa tayi ba daidai duka takesha Wanda har jinya saiatayi.
Shiyasa idan yana gidan to bata wani kwakwaran motsi sai abinda yace
Ka'daici ma tun tana kuka tanajin tsoro harta saba Rana zama itakadai a gidan ta yini ita kadai ta kwana ita kadai.


**************

Yau asabar tunda ta tashi ta gyaro dakinta ta share falon taje sama ta gyaro dakinsa da palonsa dan baya gari yayi tafiya kusan kwana biyar.
Harabar gidan ta gama sharewa tana bawa flowers ruwa taji qarar bude gate gabanta ya buga da qarfi dan tasan daga yanxu zuwa ko wane lokaci idan tayi wani qwaqwaran motsi zata iyacin duka.

Yana fitowa daga motar tayi saurin duqar da kanta tace,
Sannu da zuwa.

Wani wawan mari taji ya sauka a fuskarta daya gigitata amma bata 'dagoba saidai hawaye dasuka 6alle mata.

Ke 'yar matsiyata almajirai dan kinci darajar mahaifina nabarki kina zama gidana harkin samu guts din gaidani kaman daga tsaye kaman wani sa'anki.

Durqusawa tayi ahankali cikin tsananin jin ciwon kalaman tace,
Kayi hakuri.
Qafa yasa ya ingizata ya wuce yana fidda hucin baqin cikin ganinta dayakeyi.







Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[21:33, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA_*.

漏 *Mamuh geee*

_Bismillahir-rahamanir raheem_


17-18
Ruwan datake bawa flower ne suka zube jikinta gaba 'daya sbd ingizar da yayi mata.

Tana hawaye ta miqe zata shiga dan canza kaya harta sako qafarta 'daya tajiyo muryarsa yana cewa,
Kadaki shigo saikin bushe dan banason warin dau'da idan tajiqa da ruwa.

Komawa tayi ta ra6e jikin filawoyi tana jinjina baqar wahalalliyar wulaqancin datake ciki kuma tasan aciki zata dauwama sbd rashin kowa a duniya.
Ahaka rana ta busar da ita tareda sakar mata da wani irin zazzabi mai qarfi.
Tashi tayi tana Jan qafafu tashiga.
Dakinta ta nufa ta tube ta xanza zuwa wata ko 'daddiyar doguwar Riga dan gabaki daya kayanta sun ko'de sun tsufa wasu harsun fara 'barkawa.

Zama tayi bakin gado tana rawar sanyi ga qarin yunwa data lauye mata hanji.



*************
Lokaci yaja sosai jiddah yanxu tazama cikakkiyar budurwa danta cika samanta da qasanta fatarta tayi kyau ga gashi mai tsawo da kyau saidai uwar rama da wahala da azabar rayuwar gidan yasata ta dafe sosai kamar ba farar fata garetaba ga suturar sawama sun gagareta gashi rabonta da barr tunda yazo yafada mata zaiyi doguwar tafiya kusan shekara kenan.

A zahiri taheer kyakkyawane sosai,fatarsa chocolate amma Hutu Dajin dadi yasa fatarsa tayi haske tana wani sheqi,
Taheer dogone yana dan da jiki kadan,
Yanada zafin rai da saurin fushi sannan ma aboci tafiye tafiye ne dan idan yayi tafiya wani lokacin yakanyi sati biyu ko uku har wata ma.

Abunda ta lura dashi shine babu abinda yake matuqar so a duniya kamar qaninsa *zaid*dan yanda yake yawan kiransa da lalla6asa.


*********
Girkin dare take shirin dorawa taji yakira
Da sauri ta nufi palon dan gudun laifi ta durqusa qasa tace gani.

Batareda ya kalleta ba yace,
Gobe kidau keys a lokan Palo ki bude wancan 'dayan 6angaren dake rufe ki gyara ko ina har toilet sannan ki nutsu gurin gyaran,
Kadaki kuskura ki canxawa wani abin guri.,
Zaid zai dawo gobe dan haka daga yau ki ninka wanka da tsafta sbd zaid bayason qazanta da hayaniya,
Hakama idan zakiyi shara ki ringa yi ahankali dan bayason abinda zai saka masa ciwon kai.
Aikinki kuma daga yau ya ninku dan shima kullum saikin gyaro 6angarensa hakama abinci duk abinda yakeso shi zaki dafa masa.,
Idan kinason kanki to kiyi qoqarin kiyaye abinda zai 6ata ran zaid a gidanna harya gama hutunsa ya koma.

Ajiyar zuciya tasaki ahankali tareda cewa,
Insha Allah zan kiyaye.


Tunda sauran duhun asuba ta dauki mukullai tayi sashin na zaid ta bude tareda bismilla tashiga.

Mamaki tayi sosai na ganin kayan palon sunci uban na palon taheer.
Qamshi mai dadi palon keyi duk da shekarun da akayi ba'a shigesaba.

Stairs ta taka ahankali shiga bedroom dinsa,
Qamshi mai sanyi da dadi irin na palon taji ta lumshe ido tana kallon dakin dan ko ina tsaf yake 'yar qurace kawai.

Gyara tahauyi tundaga toilet har dakin da Palo har kicin din dake palon.

Nan take komai yayi tsaf sai qamshi yafara tashi, light din 'dakuna da AC ta kukkuna ko ina ya fara daukar ra6a ta tazo 6angarensu tadau katon din ruwa Dana drinks tazo ta jera a fridge din palonsa na qasa Dana sama tukun ta rufo 6angaren takoma nasu.

Kicin ta nufa kai tsaye ta fara aikin abinci.
Awa biyu ta kammala komai tayi 'daki ta zube a gado tana matsar hawayen jikinta da hannuwanta tareda qafafunta dake zizar ciwo sbd aikin wahala.





Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[21:38, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA_*.

漏 *Mamuh geee*

_Bismillahir-rahamanir raheem_


19-20
Da qyar ta iya Jan jiki ta fada toilet tayo wanka tareda alwala.
A zaune tayi sallah sbd tsananin ciwo da jikinta ke mata ga yunwa da zazza6i nacinta.

Tana idarwa taji kiran sallar la'asar tayi sallarta.

Wata kodaddiyar batik datayi laushi ta 'dauko tasaka sbd itace mai sauran mutunci acikin kayanta.

Zaunawa tayi a qasa tana jiran tsammani.
Qarar shigowar motoci taji hakan ya tabbatar mata da baqon ya iso.

Bata motsa daga inda take zauneba dan batason tayi laifi komai qanqantarsa da zaisa taheer ya wulaqantata ko jibgarta agaban mutane
Dan ko masu gadin gidan sunsan ba wata darajace da ita agidanba danko agabansu marinta yake.

Hayaniya tajiyo a Palo tasan anan gefen suka fara yada zango kenan bacan 6angaren zaid dinba.

Hakanan taji gabanta na faduwa sosai tasa hannu ta dafe qirjinta tana kiran sunayen Allah.

Wayar landline dake dakinta wadda taheer yasa dan kiranta idan tana daki dan ko qofar dakinta bai taba zuwaba tun zamanta a gidan.

Bata qarasa tunanintaba tayi saurin dauka gudun laifi.
Kifito ki kawowasu zaid da baqinsa abubuwan dasuke buqata.
Yana fadar haka ya kife wayar.

Kallon Jikinta tayi taji tausayin kanta yakamata sbd yanda kaf kayanta sunyi mata kadan dan sbd tsawon data da girma.
Dan qaramin hijabinta ta jawo tasaka akan 'dangalalliyar doguwar rigarta data wuce qwafrinta kadan.,
Daka ganta kaga 'yar aiki Zak,ko acikin 'yan aikin to irin marasa gatan nan.

Ahankali take tafiya kanta na qasa ta qaraso palon ta raku6e gefen kujera ta durqusa cikin sanyin murya ta gaishesu.

Babu Wanda yakalleta bare ya amsa gaisuwarta firarsu kawai sukeyi cikin jiqa dasukayi da boko gamida dukiya.
Miqewa tayi takama hanyar kicin cikin sanyin jiki,
Ruwan sanyi da drinks tareda glass cups ta jero a tray takawo ta aje musu akan center table dake tsakiyar palon
Ta juya zata bargun taheer yasakar mata wani mugun kallon da ba shiri ta zube qasa tareda fara zuzzuba musu a cups.

Cikin nutsuwa ta dago ta miqawa na farko
Ya kar6a batareda ya kalletaba subata firarsu da taheer.
Na biyun tana miqa masa yace,
No thanks,

Ta ukun mace ce tana miqa mata itama tace,
No am ok.
Juyar da hannunta tayi zata miqawa na qarshen budurwar tace,
No zaid bayashan any drink just give him water.
Sosai tayi mamakin jin Hausa a bakin yarinyar dan kwata kwata batai kama da hausauwaba bare musulmai dan ta dauka baturiyace sbd farinta da shigarta.
Yarinyace kamarta siriryace tanada tsawo saidai batada cikar qirji ko kadan,kyakkyawace daidai misali.
Sanye take da maroon pencil jeans da farar handless top sai heels masu shegen tsini a qafarta gashinta kuwa wani maroon scarf ne akanta ta daure a gefe.

Aje drink din tayi tadau wani cup ta zuba ruwan SWAN aciki ta dago dan miqa masa dan tunda tashigo palon bataji muryarsa ba.

Ya salam,ta fada jikinta na wani irin mazari dan yanda gabaki daya kallo daya datai masa yasakar mata zazzabi da faduwar gaba mai tsanani.

Zaune yake kusada yayansa taheer ya jingina bayansa a kujerar dayake zaune wayarsa yake daddanawa dan ga dukkan alamu baya cikin firar yasu saima fuskarsa data nuna firar tasuma damunsa takeyi.
Farine tas ga fatarsa datasamu da kayan amfani masu tsadar gaske.
Sam taheer ko rabin kyansa da haduwarsa baiyiba.
Sanye yake da wandon suit black da farar longsleev sai baqaqen shoes a qafarsa.

Dogon hancin asalin Fulani garesa tareda wasu irin oily eyes masu daukar hankali ga wata 'yar qasumba da aka aske amma kasancewarsa fari ana ganin duhunta duk da an aske kuma hakan ya taru yaqarawa fuskarsa kyawu.

Duqar da kanta tayi cikin sanyi tace,
Ga ruwa.

Ba tareda yakai kallonsa akantaba yakai hannunsa cikin rashin sa'a ya Dora hannunsa kan nata.

Wani irin zazzafan shocking taji ansakar mata ya haddasa mata sakin cup din ruwan suka zube masa gaba daya ajiki.





Mamuh geee馃寫馃寱馃寫馃寱
[11:18, 1/2/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 漏 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 馃悇


馃寫馃寱 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

漏 *Mamuh geee*

For you my *zinnie*


21-22
Gabaki 'dayansu suka miqe
Budurwar kuwa tuni tasaka handkerchief tana goge masa tareda fadin,
Oh my god,the water is cold bby pls go and change before you catch cold.
Wani irin wawan mari taheer yasakar mata da qararsa Tasa dukkaninsu maida kallansu akanta suna jiran suga ta sume amma ga mamakinsu sai sukaga ko motsi batayiba idan kacire hawayen dasuka 6alle daga idanunta.
Yakuma daga hannu kenan zai daketa zaid ya daga masa hannu yace,
Its ok Yaya taheer hayaniyar ya isa haka.

Janye hannun budurwar yayi daga jikinsa ya bar palon yanufi 6angarensa.
Bin bayansa taheer yayi suma sauran abokan zaid din suka bisu aka barta daga ita sai budurwar nan da itama take cikin rashin jin dadin abinda zaid din ke mata na nuna ita din ba kowa bace agaresa duk da yasan tsananin son datake masa.
Jiki a sanyaye itama tabisu 6angaren zaid din.

Tattara gurin tayi cikin sanyin jiki tana hawaye.
Taheer ne yadawo palon cikin zafin rai ya cafkota tareda sharara mata lafiyayyen Marin da saidata kife a qasa tana fidda kuka mara sauti batareda ta dafe kumatunta ba.
'Daga hannu yayi zai kai mata wani dukan saiga budurwar nan tashigo da 'yar siriyar muryarta zatayi magana amma ta kasa ta tsaya tana kallon yanda ya dunkule hannu zai naushi Jidda kamar namiji zai daka.
Sakinta yayi yana huci yace,
This should be your first and last,idan kuma kikayi kuskuren haka takuma faruwa zakiyi mamakina stupid village girl.
Afusace ya juya ya haye stairs yana tsaki.

Itakam budurwar jikintane yayi tsananin sanyi dan itadai a iya saninta zaid yace brothern sa ne da matarsa a gidan amma wannan 'yar aikin kawai take gani gashi kuma taheer din sai azabtar da ita yakeyi.

Motsin jiddane ya katse tunaninta tayi saurin dubanta saitaga taga ta matso cikin ladabi tana goge hawayen dasuka qi tsayawa tace,
Kina buqatar wani abune?
Ajiyar zuciya tasaki ahankali kafin cikin sanyin murya tace,
Eh zaid yana buqatar hot coffee yanxu and muna buqatan abinci dansu farouk zasu tafi so pls ki kawo komai yanxu.
Tana gama fada ta juya tabargun cikin tausayawa Jidda.

Kicin tashiga cikin nutsuwa ta jera kayan duka a manyan tray guda biyu tadau 'daya tafara kaiwa.

Cikin nutsuwa ta murda kofar tashiga da 'yar siriyar sallarta,
Dukkaninsu suna palon banda zaid
Dining table ta nufa ta jera komai takoma ta 'dauko dayan tray din ta jera ta bude fridge ta dauko ruwa da drinks ta aje kafin takoma kicin ta 'dora masa coffee din.
Ha'di na musamman tayiwa coffee din dan gudun tayi laifi taci duka danko yanxu xaxxabi takeji amma ba damar kwantawa.
A cup ta juye ta 'Dora a qaramin tray ta nufi palonsa
Wannan karon dukkaninsu suna dining din hardashi
Ta qarasa ahankali ta aje agabansa tareda juyawa da sauri ta fice.

Suna gamawa ta dawo ta tattara kayan ta gyare gurin tsaf.
Tana tattarawa abokanansa dataji ankira dasu farouk suka tafiyarsu
Macen kawai aka bari itama 'dakin dake palon tashigewarta.

Cikin fargaba ta matso ta tsaya nesa dashi kadan tace,
Mai za'a dafama da daddare?
Shiru yai mata yana amfani da wayarsa batareda yasan da tsironta agunba.
Tsawon lokaci ba amsa sai tayi tunanin baijiba ta qara cewa,
Mai kake buqata da dare?
'Dagowa yayi ya watso mata idanuwansa tai saurin sadda kai qasa jikinta na rawa.
Cikin wata irin murya mai sanyi yace,
Banacin abinci da daddare only fresh fruit so will you pls excuse me.
Aiko da sauri tajuya tabar gurin hartana tuntu6e.

Kai tsaye kicin ta nufa tayi wanke wanke ta zauna ta cinye 'dan sauran abincin dasuka rage ta gyare kicin din tayi 'dakinta ta kwanta dan wani irin rawar sanyi datake sbd zazzabi.


Kiran sallar magriba yasa ta tashi tana rangaji ta fada toilet tayo akwala tazo tayi sallah.
Tana gamawa kicin ta nufa ta bude fridge ta 'dibi fruits dan tuni taheer yacika fridge da fruits sbd sanin su 'dan lelensa kesha da dare
Gyaresu tayi ta dakyau ta yayyanka ta zuba a qaramin tray tareda fork ta dauka ta nufi sashensa.
Da sallama tashiga bakowa a palon taje ta aje saman dining harta juya saiga fareeda budurwar zaid din tafito daga dakin dake palon tace,
Inason kidafamin indomie da carrot amma banason pepper.

Cikin minti goma tagama takawo mata takoma daki tayi sallar isha tayi kwanciyarta.





Mamuh geee
[11:20, 1/2/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 漏 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM* 馃悇


馃寫馃寱 _*ZUCIYARMU 'DAYA.*_

漏 *Mamuh geee*

For you my *zinnie*


23-24
Da safe tana tashi kai tsaye tahau gyaran sashinsu taje taba flowers ruwa takoma kicin ta hadawa zaid breakfast ta dauka takai 6angarensa ta jere a dining.
Tana cikin gyaran palonsa saigasa ya sauko daga dakinsa cikin kayan baccin dasukai masifar yi masa kyau.
Duqarda kai tayi tace,
Ina kwana?
Kai kawai ya 'daga batareda yakalli koda gefen datakeba.
Harabar gidan ya nufa yana cikin harshen turanci da zazzaqar muryarsa.

Yana tsaye ta fito ta share harabar gidan tas tundaga gate din farko harna biyu
Tadawo ta wanke duka motocin gidan harwainda ba fita za'ayi dasuba.
Tana cikin wanke ta qarshene taheer yafito yana waya shima ya nufi motar qarshe ga dukkan alama fita zaiyi.
Saurin durqusawa tayi tace,
Ina kwana?
Maimakon ya amsa sai yace,
Kin hadawa zaid breakfast?
Kai ta daga da sauri.
Yace, tafiya zanyi idan kinga dama kiyi abinda zaibawa farhan ciwon rai kiga yanda zanyi dake.
Yana fita ta miqe tana share hawayenta tacigaba da aikinta.

Shikuwa zaid

2 Comments On ZUCIYARMU DAYA
avatar
aishatu-5

1 year ago

Reply

Nice

avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment