Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yawan lokuta samarin
unguwar suna bakin ciki da wannan al'ada
tasa, ta zama a waje, domin yana matukar
takura masu wajen ganawa da 'yar
kyakkyawar yarinya A'isha.
.
Bayan A'isha ta gama waigen kowanne
bangare na harabar, sai ta hango Nazifi a can
rakabe a jikin wata bishiyar dorawar turawa
da ke kusa da babbar kofar shigowa cikin
gidan. Yana tsaye a jikin bishiyar, ya jingine
akwalar kekensa a gefe guda. Hannayensa a
harde a kan kirjinsa, ya sako wani farin yadi
boyel, wanda ya dan fara zazzagawa
.
A'isha ta isa gare shi tana murmushi. Tun daga nesa da ya hango ta shi ma yake murmushi, har ta
kawo inda yake.
"Wallahi har na cire tsammanin zuwanka,
Nazifi."
.
Soyayya da dadi jama'a
Saide daga karshe.......
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 5
.
"Wallahi har na cire tsammanin zuwanka,
Nazifi."
Ya ci gaba da murmushi, ya ce da ita.
"Haba A'isha, ai ke ma kin san cewar tunda
dai har na daukar maki alkawarin cewar zan
zo, ai ba zan karya ba."
.
Suka sake yi wa juna wadansu sabbin
murmushi.
"Gaskiya na ji dadi wallahi Nazifi, ka san
yadda soyayyar ta koma yanzu. Wani lokacin
sai ka ga an kulla alkawura sama da dari,
amma da wahala ka ga an cika ko da goma ne
a cikin darin. Kai dai ka san cewar da a ce
yadda ake kulla alkawarin soyayya a duniyar
nan, haka ake cikawa, to da yanzu babu
sauran wani mutum wanda ba shi da
masoyinsa."
.
Nazifi ya yi dariya.
"Duk da haka dai A'isha, ai dole ne a samu
nagari, kin san ba zai yiwu a ce duk an zama
daya ba, duk da lalacewar da soyayya ta yi za
a samu mutane nagari da ke cika
alkawarinsu."
"To za ki fara ke ma ko...?"
Ta yi dariya.
"Ba haka ba ne, wannan ai gaskiya ce Nazifi,
domin kuwa ba wani zolaya don ka fadi
halayen masoyinka nagari."
.
Suka sake tuntsirewa da dariya a lokaci guda.
Nazifi ya fara cewa bayan sun gama dariyar.
"A'isha akwai abun da ke tattare da zuciyata, wanda
duk na kosa da ma in zo in amayar maki da
shi. Wallahi A'isha jiya ban yi wani barcin
kirki ba, domin kuwa ina komawa gida,
tunaninki ya dabaibaye mini zuciya, sannan
kuma ko da na samu damar yin barcin,
mafarkinki ne ya buwayi kyakkyawan barcin
nawa. Don haka nake so idan ba za ki damu
ba, ina son mu yi maganar aure in dai har da
gaske ne kina so na."
.
A'isha ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce da
Nazifi, "Na ji duk bayaninka Nazifi kuma na
matukar farin ciki, to amma ina son ka yarda
har zuciyarka. Nazifi wallahi ni ma duk
duniyar nan babu wanda nake so sai kai. To
amma da akwai wata 'yar matsala guda daya
da ke tattare da ni. Ina son idan na fada maka
kada ka karaya, domin kuwa wannan matsala
ba za ta hana mu gudanar da soyayyarmu ba.
Ta dan saurara sannan ta ce da shi.
.
"Nazifi saura kwana takwas kenan a daura aurena."
Saurayin ya rike numfashinsa cikin kaduwa,
sannan ya dafe kirjinsa, "Aurenki!! A'isha...ban fahimce ki ba."
.
Ta girgiza kanta "kwarai kuwa aurena Nazifi.
To amma ina son ka sha kuruminka, domin
kuwa ni da ma ba na son saurayin da za a
daura mana aure da shi, kawai mahaifina ne
ya takura min a kan al'amarin. To amma a
halin yanzu, tunda har Allah ya hada
soyayyarmu da kai, wannan zancen aure babu
shi, ya lalace, in Allah ya so kai ne mijina
Nazifi."
.
Nazifi ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da ita.
"To amma kuma iyayenki kuma fa A'isha,
kina jin za su amince?"
"Sun riga sun san komai Nazifi, domin kuwa
na fadawa mahaifiyata gaskiyar abinda ke
zuciyata, to amma ban samu goyon baya ba.
Domin kuwa a dalilin na ce ina kaunar ka
Nazifi sai da ta lakada min dukan tsaiya, da
kyar mahaifina ya yi mata magana ta rabu da
ni."
.
Suka kurawa juna idanu cikin jimami. Nazifi
ya ce "To amma kuma A'isha kina jin
al'amarin nan zai yiwu? Tun yanzun fa kenan
har kin fara fuskantar matsaloli, to ina kuma
a ce tafiya ta yi nisa a tsakanina da ke?"
"Me zai hana al'amarin yiwuwa Nazifi?" A'isha
ta ce da shi.
.
"Ni dai na daukar maka alkawari, duk rigimar
da za a yi ba zan amince a daura mini aure da
wannan wahalallen ba, don haka na riga na
gama tunanin komai a halin yanzu, kai kawai
nake jira, don in ji ta bakinka. In kana jin za
ka iya jurewa, kamar yadda ni ma zan jure,
komai wahala mu rike juna."
.
Nazifi ya sake yin doguwar ajiyar zuciya,
sannna ya ce da ita, "Kada ki damu A'isha, na
daukar maki alkawari, komai wahala ni ma
ina nan tare da ke, sai dai mutuwa za raba
mu."
.
A daidai wannan lokacin ne da suke ta
wannan doguwar hirar tasu ta masoya, kamar
an jeho shi, sai Alhaji Dage ya fito daga cikin
gida. Tun dazu yake zaman jira, yana
tsammanin jin sautin dankareriyar mota ta yi
fakin a kofar gidan, domin kuwa shi har
yanzu tsammani yake yi, sabon saurayin da
A'isha ta ce ta sake, wani hamshakin attajiri
ne wanda ya rude ta da zunzurutun kudi.
Fitowarsa ke da wuya, ya kai ganinsa inda
A'isha ke tsaye tare da saurayin a gindin
bishiyar. Alhaji Dage ya yi raunanannen
murmushi da ya hango wanda ke tare da ita,
domin kuwa ya dauka cewar masinjan
masoyin 'yar tasa ne, ya zo fadawa 'yarsa
A'isha cewar Alhajin ba zai samu zuwa ba.
.
Alhaji Dage ya nufi inda suke a tsaye. Ya
hango tsohuwar akwalar keken saurayin a
jingine da bishiyar, kamar dokin kara, nan da
nan sai ya ji tausayin saurayin ya kama shi,
domin kuwa yana matukar takaicin yadda
attajirai da manyan ma'aikata ba sa kulawa
da masinjojinsu, haka dai ya iske su suna
cikin hirar
.
Nazifi ya rage tsawo ya gaishe da
Alhaji Dage. Ya amsa cikin fara'a-fara'a akaici-takaici, kana ya ce da saurayin.
"Allah sarki! Kai ya turo kenan, bai samu
zuwa ba. In ka je ka ce da shi na yi zaman
jiransa, domin ina son mu yi wata 'yar
ganawa da shi a kan lamarin 'yata A'isha da ya
ce yana so"
.
dan saurayin da 'yar budurwar suka kalli juna
cikin tsananin mamaki. Ba su san me siririn
mutumin yake nufi ba, to amma shi bai
damu ba, sai ma ya ci gaba da zancensa kai-
tsaye.
"Idan ka gama fada mata sakon da ya aiko ka,
don Allah ka yi saurin janye akwalar keken ka
tafi malam, domin ina jin tsoron kada ka
tsorata mini agwagi da dawisu da wannan
tsohon keken mai shegen rakin tsiya."
A'isha ta dubi mahaifinta cikin damuwa, ta ce
da shi cike da kaduwa.
.
"Baba shi ne, ba aiko shi aka yi ba."
"Ban fahimta ba, shi ne wa?" Ya zazzaro
kwala-kwalan idanunsa da ke boye a cikin
kwafcecen-tabaron.
.
A'isha ta ce da shi cikin ladabi.
"Baba shi ne ai saurayin da nake so dama, shi
ne masoyin nawa." Tuni jikinta ya soma
kyarmar kaduwa.
.
Alhaji Dage ya kai hannu cikin razana, ya
ciccibo katon tabaronsa kaya guda, ya rike a
hannusa, ya kalli saurayin sama da kasa
sannan ya ce a sanyaye.
.
"Lallai A'isha tubarkalla na ga saurayin, ya
sunanka malam?" Nazifi ya sunkuyar da kansa
kasa, domin kuwa ya tabbatar akwai matsala
babba da ke shirin faruwa. To amma dai duk
da haka, sai ya kokarta ya bude baki ya baiwa
mutumin amsa.
"Sunana Nazifi" Alhaji Dage ya dubi A'isha ya
daka mata tsawa.
"Shige cikin gida kafin in zo in same ki `yar
banzar yarinya kawai"
.
A'isha ta juya cikin tsananin karaya, ta nufi
cikin gidan. lokaci-lokaci ta kan waigo don
ganin abin da zai wakana ga masoyinta. Nan
da nan ta soma addu'ar Allah ya sa dai kada
mafadacin baban nata ya buge shi, domin
kuwa ta san shi wajen saurin hannu.
.
Wannan na daga cikin abin da ya sa shi yin kaurin
suna a unguwar, domin kuwa ya sha marin
samarin da ke zuwa wurin `ya`yansa,
musamman ma idan a kasa mutum ya zo ba
a mota ba
.
Shigewar A'isha ke da wuya, sai ya tattara
hankalinsa gaba daya ya ce da dan saurayi
Nazifi.
"Ina son in yi maka gargadi na farko, kuma na
karshe, wannan yarinya `yata ce, ni na haife
ta, kuma saura kwana takwas kenan a daura
aurenta, ka rufawa kanka asiri ka fita daga
cikin harkokinta, domin kuwa A'isha a halin
yanzu ko kai aka sayar ba za ka biya abinda za
kai aurenta ba. Domin kuwa na san dai ba za
ka kai naira miliyan guda ba, don haka kar ka
jawo wa kanka bala'i dan saurayi."
.
Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da
ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo
akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in
ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki
zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a
wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka a duniya
.
Malam Nazifi abun tausayi
Talakan masoyi ya hadu da ma kwadaicin siriki
Its shuraih 99%AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 6
.
Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da
ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo
akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in
ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki
zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a
wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka, a duniya.
.
Alhaji Dage ya sake cewa da shi a fusace,kafin ya tafi.
"Ka rike a zuciyarka dan saurayi ba na magana biyu, haduwar mu da kai ta biyu babu dadin gani. Idan na sake ganin ko da inuwarka a nan gidan,kai ko sawunka na gani wallahi sai na aika polisteshan, an kulle min kai, shege beran masallaci."
________________________________
Wata dankareriyar mota mai tudun baya, ta garzayo a guje kamar kibiya, tana sheki a cikin hasken kwaleliyar ranar wacce ke ta faman gasa naman bil'adam. Jama'ar da ke zazzaune a bakin titin, suka bi motar da kallo, domin kuwa lokaci-lokaci sukan ga motar ta shigo cikin unguwar tasu, to amma kuma har yanzu babu wanda ya san takamaiman abin da ke kawo motar a kai- akai ba
.
Kamar kullum sai motar ta rage gudu sannan ta fara sigina, cikin abin da bai fi dakika biyar ba,har ta tsallako titi.
.
Saurayin da ke tuka motar ya daga musu hannu, wannan al'adarsa ce koda yaushe, da ma ya kan dago musu hannu in ya same su a zazzaune. Yawanci idan haka ta faru, su mutanen ba sa wani kula shi, ko a yanzun ma da ya dago hannu da kyar aka sami mutane uku da suka kula da shi, su ma kuma ba hannu suka daga masa ba, kai kawai suka gyada masa kamar kadangaru.
.
Me yiwuwa idan aka tona zuciyar mutanen unguwar watakila suna da gaskiya, domin kuwa tun ganin farko da suka yi wa saurayin ya shigo unguwarsu, duk da yake a cikin mota yake, ta gilashi suke hango shi, a matsayin suna kwararrun zauna gari-banza, sannan kuma masana akan ilimin sa-ido, sun fahimci cewar wannan saurayi duk inda ya fito ba mutumin kirki ba ne
.
Akwai wani mutum da ya taba cewa ma da ganin saurayin ya san cewar dan fashi da makami ne, shi yasa da zarar ya shigo unguwar suke hade masa fuska, kamar sun ga mutuwa.
.
Saurayin bai taba kula ta tasu ba, don kuwa ya
san cewar wata rana ma ba za su sake ganinsa ba, neman aure ya jawo mishi shigowa wannan unguwar mai cike `yan sa-ido, dazarar an yi aure kuma ta kare
.
Saurayin ya yi murmushi da ya tuno cewa nan da kwanaki hudu za a daura auren sa da A'isha rabin
ransa, Aisharsa da ya mace a kan kauna tsawon lokaci.
.
Ko da ya tsallaka titi sai ya shiga layin gidan
su masoyiyarsa A'isha wacce yake ta faman
ambatar sunanta sai kace mai bitar darasi. Ya
ci gaba da murmushinsa sannan ya daki
sintiyarin motar cikin farin ciki,
.
hakika komai yana da iyaka, ya ce a zuciyarsa. Ya dauki dogon lokaci yana nunawa A'isha soyayya, amma ta ki ta gane kullum sai dai kawai shi yake kidansa sannan kuma yake rawarsa,
amma ita ba ma ta tasa ta ke ba. To amma
dai yanzu ai wulakanci ya kare tunda dai ta
kusa zama matarsa, ko da a ce ba ta
kaunarsa, ai ya zame mata dole ne ta zauna
da shi tunda dai ya saye iyayenta.
.
Saurayin ya ci gaba da murmushinsa na
samun nasara, ya ce a zuciyarsa, "Hakika kudi
suna da matukar amfani a rayuwa," domin ya
san cewar da bai mallake su ba to da shi da
A'isha kyakkyawa sai dai hange daga nesa. Da
yawa daga cikin abokansa sun sha damun shi
da surutai a kan wannan soyayya da ya ke yi
wa A'isha domin kuwa ta sha ta kwabsa shi ko
a gaban wanene ko da kuwa yana tare da
abokansa ne
.
Akwai wani lokaci da wani abokinsa ya ce da shi.
"Don Allah Gali ka rabu da yarinyar nan tun
da dai ba ta kaunar ka, wai kai ina ma ka
taba jin inda aka yi soyayyar dole ne? Ya
kamata ka canza sheka haka nan, domin kuwa
akwai `yan mata kyawawa a garin nan, ba
A'isha ba ce kadai kyakkyawa"
Gali ya yi murmushin ya ce da shi
.
"Abokina kada ka ga laifina don na likewa
yarinyar nan, wani lokaci ni kaina nakan yi
kokarin ganin cewar na cire son ta a zuciyata,
don in huta wa rayuwata domin kuwa A'isha ta
zame mini kamar maruru ko sartse a cikin
zuciya, ba na minti daya a duniya ban yi
tunaninta ba sannna kuma ba na iya daina
son ta a zuciya ta."
.
Tun daga wannan rana mafi yawa daga cikin
abokan Gali suka shafa masa lafiya, wadansu
kuma suka ma bata da shi domin kuwa su a
ganinsu ya ba da sojoji, ba haka aka san
zuciyar soja ba. To amma kuma abin da ba su
sani ba game da lamarin soyayya shi ne, ta
kansa mutum ya makance ya dukufa akan
son wani abu, wanda sauran jama'a ko da
kudi aka hada su ba za su so wannan abu ba,
.
domin kuwa idan ba haka ba, babu abinda zai
sa babban ba'askare a cikin sojoji, wanda ya
shiga har kasashen turai, amma ya dishe da
kaunar wata yarinya `yar cikin gida ba kirar
waje ba, har kuma ta zo tana wulakanta shi,
lallai abin dai kam akwai takaici.
.
Gali ya yi ajiyar zuciya da ya tuno walhalun
da ya sha a baya na kaunar wannan yarinya
A'isha, ya ce a bayyane cikin rada-rada.
"Kin ba ni wahala A'isha amma ba komai na
kusa ramawa"
A daidai wannan lokaci ne ya karaso kofar
gidan, ya yi fakin din dunkulalliyar motarsa
mai tudun baya, ya fito yana sanye da
dogayen kayan shudiyar shadda, dinkin ta-
zarce, dogo ne kakkaura baki, yadda yake
haka zuciyarsa take bakikkirin domin kuwa
da ran mutum da na kiyashi duk daya suke a
wurinsa.
.
Shekarunsa za su kai talatin da biyar koma fiye a duniya. Ya shiga zagayen gidan
kai tsaye, ya tsaya a cikin harabar inda shuke-
shuken alfarmar suke. Bai dade ba a wurin
wata karamar yarinya ta shigo cikin gidan, ya
tsayar da ita, ya ce da ita.
.
"Kice wa Ai'isha Gali yana jiran ta a waje"
Ba a jima ba yarinyar ta fito ta ce da shi.
"Ta ce tana zuwa"
Ya zaro wazobiya sabuwa fil ya mikawa
yarinyar. Ta amsa cikin doki ta fice a guje.
.
Gali ya yi ajiyar zuciya ya fara nazarin
harabar gidan. dawisu da agwagin ruwa da
suka fi komai ba shi sha'awa suna ta yawace-
yawace, da kuma koke-koke abinsu. Ya yi
mamakin yadda mahaifin A'isha rabin ransa
ke matukar kulawa da wadannan halittu. Ba a
jima ba A'isha ta fito. Tun daga nesa ta
murtuke fuskarta da ta hango Gali tsaye
kamar gunki
.
Ta ce a ranta "Wannan
wahalallen banzan kuma yaushe ya dawo?" Ta
karaso wurin da yake ta tsaya, ko sallama ba
ta yi masa ba, ballantana kuma ta dube shi,
to amma shi da yake ya saba da wannan
dabi'a tata, bai damu ba sai kawai ya fara
aikinsa na surutu.
.
"Ai'sha ya kamata yau dai rana daya ki saki
fuskarki a gareni, domin kuwa ni da ke mun
zama daya, kin ga fa yau saura kwanaki hudu
kenan a daura mana aure
.
Bai kamata a ce mu yi aure kuma ya kasance ba wata kwakkwarar jituwa a tsakaninmu ba. A'isha
ya kamata ki hakura haka nan, bakin alkalami
ya riga ya bushe."
.
Ta juyo cikin izgili ta dube shi a yatsine ta ce
da shi.
"Kai da wacce kuma za a daura muku aure?"
Gali ya dube ta cikin kaduwa.
.
Ku jira part 7
_________
Yan mata kudaina wulakanta samari
Domin kuwa zai iya yiwuwa su zaku Aura
Izan ya kasance Saurayin da ki ka wulakanta wajen neman aurenki ya zama mijinki sannan ki ka kamu da ciwon sonsa a yayin da shi kuma ya fara Rama wulakancin da ki ka masa
.
Mutane masu tsananin fushi, masu rike abu a zuciya, basa taba manta wulakanci
.
Wani mawaki yace = in aka furta so gareka sai kai na'am a zuciya karka zagi Kauna,
= Masoyi yana da rana
= Masoyi yana da Rana
.
Sai mun hadu gobe
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 7
.
"Kai da wacce kuma za a daura muku aure?"
Gali ya dube ta cikin kaduwa.
.
"A'ah! ni da ke mana A'isha, ko ba ki gane ni ba ne? Ni ne Gali masoyinki."
.
A'isha ta yi murmushi, amma ko da ganin
murmushin ka san cewar a boye a bayan sa
akwai abubuwa marasa dadin ji bila'adadin.
.
"Wani lokacin ka kan ba ni mamaki Gal wai
kai don Allah wanne irin mutum ne a duniyar
nan? Ba tun yau ba na nuna maka a zahiri, na
furta maka baki da baki ba na sonka, ba zan
taba sonka ba kuma, to amma kai ka like
mini. Yanzu kai saboda Allah har sha'awa
kake yi ka auri matar da ba ta kaunarka a
duniya?"
.
Saurayin ya yi ajiyar zuciya ya ce da ita cikin
damuwa "A'isha kin dade kina wulakanta ni a
lokacin da ni kuma nake ganiyar nuna miki
tsantsar soyayya tagari. To amma kuma ke
mene ne dalilin da za ki ce ba kya kauna ta?
.
Dole ne ma ki so ni A'isha, don kuwa babu
dalilin da zaki ki so na. Me kike bukata ki
mallaka a duniya wanda ba ni da shi? Ke
kanki kin san cewar ina da abinda za ki so ni a
duniya.."
.
Aisha ta tsayar da shi ta hanyar jifan shi da
wani busashshen murmushi "Lallai ba ka da
hankali Gali kuma ba ka san soyayya ba,
tunda har ka iya bude baki ka ce wai kana da
abin da zan so ka da shi dole
.
Na san cewar ba wani abu kake takama da shi ba face dukiyarka, to bari in fada maka ni ba
dukiyarka ba ce a gaba na? Kai a haukanka shi
kenan don kana da kudi dole ne mace ta
soka wannan ba gaskiya ba ne ka sake
tunani, domin kuwa kai ka mallaki kudi
amma kuma ni ba na sonka. Ka ga kenan
ashe ko wannan ma ya ishe ka darasi, don ka
fahimci cewar kudi ba sa iya sayen soyayya."
.
Gali ya dubi `yar budurwar cikin harzuka,
tunda suke ba ta taba kule shi irin wannan
karon ba. Ya ce da ita a fusace "To ya isa
hakan nan mu bar wannan zancen, yanzu
mene ne shirye-shiryenki game da auren
mu? Na san dai ba za ki rasa bukatar wani
abu ba."
.
Tace da shi "Ina bukatar abubuwa da dama
amma kuma ba wurinka ba. Ina da bukatar
ne a wajen mijina da zan aura, ko ba ka san
cewar wani zan aura ba ne Gali?"
.
Ya dube ta a tsorace "Wai me kike nufi ne?
A'isha ni fa ban gane ba, duk kin ruda ni
wallahi."
.
Ta ci gaba da murmushinta sannan ta ce da
shi.
"Abin da nake nufi shi ne saura kwanaki hudu
a daura aurena da wani saurayi da nake
kauna a zuciyata, amma ba kai ba."
.
Gali ya ce da ita cikin rudani.
"To ai ni ma saura kwanaki hudu kenan
mahaifinki ya daura aurenki da ni, kuma har
ma na fara raba katin gaiyata, A'isha."
.
"Wannan matsalarka ce Gali, ni dai
kasancewar ban taba cewa in kaunarka ba
kuma ban taba amsar komai naka ba don
haka idan an daura aure sai a kai maka wata
amayar amma ba dai ni ba."
.
Tana gama furta kalaman sai ta juya ta shige
gida tan kunkunai hade da yin tsaki. Saurayin
ya bi ta da kallo har ta bace, maganganunta
na ta faman amsa kuwa da kururuwa a
kwakwalwarsa. Tuni har ya fara lissafo
mutanen da ke bukatar a sai musu likkafani a
cikin jerin wadanda zai aika barzahu, indai
har ba a kai masa amaryarsa daki nan da
kwanaki hudu masu zuwa ba
_____________
BABI NA UKU
.
Ba kasafai Nazifi yake barcin rana ba, domin
kuwa ko ba inda yake da bukatar zuwa, da
wahala ka same shi a kwance da rana tsaka
kai ko rashin lafiya yake yi bai cika kwanciya a
daki da rana ba,
.
bar shi dai ya fito kofar gida ya zauna a dakali ya karanta mujallun fina-
finai ko kuma littafan soyayya. To amma
kuma sabanin wannan halayya tasa da aka san
shi da ita shekara da shekaru, kwanaki biyu
kenan Nazifi yana wuni a gida a kwance, ko
lekowa waje ba ya yi
.
Mahaifiyarsa Tabawa ta yi iyakar kokarinta
don ya fada mata dalilin canjin wannan
halayya tasa amma kuma abin ya faskara, ya
ki ya fada mata, sannan kuma babban abin da
ya fi ba ta mamaki shi ne wai a cewarsa
lafiyarsa kalau, ba inda ke yi masa ciwo. A
cikin kwanakin biyun nan ko wurin sana'arsa
ta kafinta bai leka ba,
.
wanda abu ne mai wahala ko ma kuwa menene dalilin a ce
Nazifi ya ketare rana daya bai je wurin
wannan sana'a tasa ba.
To amma kuma abinda ya tsorata Tabawa shi
ne, wani lokacin idan yana kwance yana barci
idan ta leka dakinsa
,
sai taji yana ta sambatu a cikin barci, yana fadar sunan wata yarinya
wai ita A'isha. Sannan kuma wani lokaci sai ta
same shi yana ta murmushi
.
Ko da Tabawa ta lura da wannna bakon al'amari da ya sami danta Nazifi sai ta ce da shi a fusace a wuni na biyu
.
"Haba ai ni dama na san a rina ai ga irin ta
nan kullum kwanan duniya yaron nan sai na
yi fama da kai ka rika shan maganin miyagu
da kuma na mutanen boye, amma taurin kan
tsiyarku na `yan zamani ya hana ka Nazifi, ga
shi nan ai ka yi gamo da aljana za ta sabautar
da kai a banza."
.
Tun daga wannan lokaci Tabawa ta fara
shirye-shiryen kaiwa bokanyarta ziyara,
domin kuwa ta san cewar wannan aljana da ta
cafi danta guda daya da take alfahari da shi a
duniya, duk tsiyar aljanar in dai har ta kai ta
wajen kwararriyar bokanyarta Iya mai
dogari, to ko ba ta shirya ba sai ta fice daga
jikin danta Nazifi
.
To amma kuma shi Nazifi ya san cewar ko sarakan bori na duniya ne suka taru a kan shi ba za su iya maganin
wannan matsala tashi ba, domin kuwa duk
kwarewarsu akan wannnan sana'a ba za su iya
mallaka masa masoyiyarsa da ya kamu da
ciwon so ba, wacce saura kwanaki biyu kacal a
daura aurenta da wani saurayin can daban
....
CIWON SO kenan
___________
MASOYA AKIYAYE
Izan zaka so mutum to ka soshi daidai wa daida
Haka nan yan mata kada ku dauki son duniya ku daurawa saurayi/budurwa, daga karshe kuma ku rasasu, rayuwarku ta fada cikin garari
.
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 8
.
Kamar kullum a cikin kwanaki biyu yana
kwance sai mahaifiyarsa ta shigo cikin dakin.
Ya yi tsammanin zancen neman maganin ta
zo yi masa, to amma sabanin haka sai ta ce
da shi.
.
"Wata yarinya ce wai ta zo tana son ganin ka,
shi ne na ce bari in zo in sanar da kai."
.
Nazifi ya mike zumbur cikin mamaki, domin
kuwa inda haka nan ne banza sai a wuni ana
fama da shi ba zai tashi ba, kai a cikin
kwanaki biyun nan har lokacin sallah sai ya zo
ya wuce yana kwance ba zai yi ba.
.
Amma yanzu daga jin an ce wata ta zo nemansa, duk da dai bai san ko wace ce ba, amma a can
cikin zuciyarsa sai ya ji ya dokanta da ya fita
din.
.
Ya tashi da sauri kamar ba shi ne ke wuni
a nannade a gado ba, kamar wanda ake yiwa
karin ruwa. Lallai dai sha'anin yaran zamani
sai dai a bar su, Tabawa ta fada a zuciyarta,
ita ma ta fice daga dakin.
.
Fitar sa ke da wuya ya cikaro da ita a tsakar
gida tana sanye da atamfa shudiya da kuma
dan fingilin gyale. Hakika zatonsa ya zama
gaskiya domin kuwa wacce yake tsammani ce
ya gani. Suka yiwa juna murmushi, Nazifi ne
ya fara yi mata magana.
.
"A'isha da ma ashe ke ce...?"
Ta jefe shi da murmushin Allah kashe ni don
dadi, sannan ta ce da shi.
"Kai da wa kake tsammani?"
"Ban yi tsammanin ki ba, domin kuwa na
dauka cewar tuni kin mance da ni A'isha."
Ta sake jifan shi da wani murmushi.
.
"In ban da abinka Nazifi ka taba ganin inda
mace ta mance da mijinta? Ko ba ka san
cewar ni a matsayin mijina nake daukarka ba,
ko ka mance da alkawarin da na daukar maka
ne in dai ina da miji a duniya ai kai ne
Nazifi."
.
Ya lumshe idanu don farin ciki, a zuciyarsa ya
ce Allah ya sa haka ya zama gaskiya A'ishata,
sannan ya ce da ita.
.
"Zo mu shiga daga ciki A'isha nan ba wurin da
za mu tattauna matsalolinmu ba ne."
Suka shiga cikin dakinsa, rufin kwano doron
zabuwa amma kuma babu silin babu komai a
ciki idan aka tsame dan tsurkun gadonsa na
katako mai kama da makara da kuma wata
kujera daya ita ma ta katako mai kafa uku da
rabi. A'isha ta yi wa kujerar kallon nutsuwa
kafin ta sami mazauni a kanta, domin kuwa
tunda suka shigo cikin dakin ta dubi
rubabbiyar kujerar ta fara zullumin cewar da
wahala kujerar ta iya daukar nauyin mutum
dukansa
.
To amma kuma cikin sa'a sai kuma
ta dauke ta gaba daya, duk da yake dai takan
nemi ta turgude a dalilin nakasar da ta yi na
gutsurewar rabin kafa guda. Nazifi ya fada
kan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment