Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alokacin karfe goma da rabi na dare
domin shafiu na barin otal din gidansu Aisha ya wuce kai tsaye da yake uwar rikonta kande ta
dauke daya daga cikin atamfofin da shafiu yabata ba'a sami wata matsala ba wajen fitowar aisha.
Abin mamaki kande ce ma turo ta da kanta.
Yi sauri ki fita mana sai wani nuku nuku kikeyi wannan yaro ai ya isa dan arziki wallahi ga shi daga
zuwansa har ya fitar damu daga cikin tsummokara.
To aisha kefa nake jira kinyi shiru.
Aisha ta dubeshi a tsorace tace wallahi shafiu tsoron kiran Aljanar nan nakeyi kaga....
Shafiu ya ya daga mata hannu menene abin tsoron bayan tace bazata cutar da ke ba?
Aisha tayi batace komai ba.
In kuma kina ganin dai tsoron bazai barki kiyi kiranta ba to kirawo ta mana yanzu tunda ina tare
dake.
.
Aisha tayi ajiyar zuciya in dai kana tare dani bana tsoron komai shafiu bari na kirawota ta bude
jakarta ta fara laluben farin dutsen abinda bata sani ba shine tuni cikin shafiu ya fara kugi domin
shima a bala'in tsorace yake to amma da yake ransa yana kan dukiyar dake binne saiya dake
zuciyarsa amma gumi tun daga goshinsa har zuwa kan babban dan yatsan kafarsa zuba yake.
Aisha ta dauko dutsen daga cikin jakar ta dorashi akan tafin hannunta ta lumshe idanu sannan
ahankali saita fara murza dutsen a tafin hannunta.
Shafiu yayi mutuwar tsohuwa ko kwakkwaran numfashi bayayiShafiu yayi mutuwar tsohuwa ko
kwakkwaran numfashi bayayi.
.
Wata guguwa mai karfin gaske ta turnuke zagayen motar sannan sai sukaji motar ta fara girgiza
kamar za'a dauke su sama tsawon lokaci ana girgiza motar sannan kwatsam sai balbelar ta bayyana
a gaban motar.
Matasan biyu suka zura mata idanu cikin kaduwa
Kada kuji tsorona ku tambayi duk abinda kuke so daman nasan zaki neme ni ta dubi Aisha.
San..nu da...zuwa aisha tace bakinta na rawa
Yawwa aisha yi sauri ki fadi abinda kike son fada ina BIRNIN SIN fa kuka kirawoni sauri nakeyi
zan koma na baro yarana acan.
Aisha ta dubi shaiu sannan ta dubi balbelar cikin hali So...muke mu san inda aka binne akwatin.
Balbelar ta girgiza kafadunta sannan ta dubi shafiu tace Ramin daka shiga dazun nan anan akwatin

take kasan akwai wani bawana dana ajiye shi yayi gadin akwatin yau shekara dari da shirin yana
zaune agurin yana gadinta. Ko dazu ma saida ka taka shi baka ganshi ba.
Shafiu ya dubi aisha duk da yake a bala'in tsorace yake saida ya daga mata gira to in bakuda wani
abu kuma da kuke son tamaba ni zan tafi
Mun...gode Madalla sai kuma wani jikon Aisha tace bakinta na rawa.
Balbelar ta dubi shafiu tace idan Allah ya kaddara auranka da ita ka riketa da kyau yarinyar kirki ce
sannan ta bace.
Matasan biyu sukayi ajiyar zuciya lokaci guda shafiu ne yafara magana to sai yaya kuma? Saiki
shirya gobe warhaka muna can in Allah ya yarda ko sha biyun dare bazatayi mana acan ba zamu
dawo da dukiyar
kana nufin har dani zamu tafi? Aisha ta tambaye shi a tsorace.
Shafiu ya fashe da dariya cikin farin ciki yace Haba Aisha kiyi amfani da hankalin ki mana ai idan
bakya agurin akwatin bazata dauku ba don bana tsammanin karama ce maiyiwuwa mai nauyin tsiya
ce.
Kuma ni me zan iyayi ina mace?
Shafiu ya dubeta kana ya matsa dab da ita har tanajin numfashinsa afuskar ta yace Bakiji abinda
tace ba? Akwai wani bawanta dake gurin yana gadin akwatin shi zamu sa ya janyo mana akwatin
daga karkashin kasa.
Aisha ta bude baki cikin kaduwa.
Shafiu kada fa son abin duniya yasa ka zarewa in banda abinka a ina zamu ganshi Aljani ne fa
shafiu ya sake fashewa da dariya wannan shine dalilin daya nace dake zamu tafi idan munje bakin
ramin saiki murza dan dutsenki idan balbelar ta bayyana saiki roketa alfarma tasa wannan bawan
nata dake gadi agurin ya zaro mana akwatin ko kuwa ya kika gani?
Aisha ta dube shi da murmushin farin ciki adaidai lokacin ne to Aisha ta kula da kansa Kai shafiu
yaushe ka aske wannan gashin naka?
Shafiu ya fashe da dariya sai yanzu ma kika lura?
Aisha bata iya bashi amsa ba saitaci gaba da kallonsa sama da kasa Alokacin ne ma ta lura ashe har
zako zakon faratan dake hannunsa duk ya yanke.
Wallahi daka aske gashin saika zama kamar ba kai ba.
Shafiu yayi murmushi sai nayi muni ko?
Aisha ta girgiza kai tace haba dai ai haka ma wallahi kafi kyau inama ace ina iya kallon ka sosai
batareda jin kunya ba
SUKA FASHE DA DARIYA.
** ** ** **
Washegari tun da asuba shafiu ya tashi yayi sallah. Wannan shine karo na farko acikin shekaru
goma sha takwas da shafiu ya tashi sallah da suba rabonsa da sallah tun yana dan shekara goma
aduniya alokacin bai gagari mahaifansa ba.
Mahaifin shafiu zaune a dakin shakatawa suna karin kumallo sai suka ga shafiu ya shigo falon
ahankali kamar maiyin sanda mahaifan suka kura masa idanu cikin kaduwa domin sun san shafiu in
har ba makaranta zashi ba babu abinda zai tashe shi da karfe takwas na safe.
Mahaifinsa ALHAJI SADIQ ya kalle shi sama da kasa cikin kaduwa domin ya lura da cewa
dugunzunzum din gashin nan da yayi matukar tsana shafiu ya aske shi.
Ina kwananku shafiu ya gaishe su a durkushe
Lafiya lau shafiu... Suka amsa baki daya cikin mamaki tsawon lokaci babu wanda yace kala can sai
Alhaji sadik ya dubi dansa yace a sanyaye shafiu yau kuma shiriya ce Allah ya kawo ma?
Shafiu kansa a durkushe yace Eh baba.
Zuwa ma nayi na roke ku gafarar abinda nayi muku abaya. Nayi muku alkawarin daga yau nabar
shirme da sakarci mahaifiyar shafiu ta fashe da kukan farin ciki Mun yafe maka shafiu.
Allah sadik ya tashi tsaye sannan ya dubi dansa cikin farin ciki Na godewa Allah daya shirya min
kai kuma tunda Allah yasa shiriya tazo maka saika nemo wacce kake so ayi maka aure.
Shafiu ya dago kai cikin farin ciki yace Gobe in Allah ya kaimu zan zo muku da ita baba
mahaifansa suka dubi juna sukayi murmushi toh ai shikenan shafiu kuma indai naga ka zarce ahaka

zan mika ma ragamar harkokina ahannunka duk da yake dai ba wani abu nake dashi kamar da ba
amma In Allah yakaimu jibi za'ayimin wani tsohon biyan bashi na kusan naira Milliyan hudu da
zarar an kawo min su kai zan Dankawa.
Wannan wani abu ne daga Allah lallai babu abinda yafi komai dadi aduniya irin bin hanya
madaidaiciya shafiu yace cikin zuciyarsa duk da wannan alkawarin da akayi masa na wannan
makudan kudi zuciyar shafiu bata daina tunanin dukiyar dake binne a karkashin kasa ba.
** ** ** **** **** ****** ******* *****
.
Wani katon gyare yayi tsalle yafada faskeken kunnen daya daga cikin yansandan dake bobboye
abayan bishiyoyin suna nazarin bakin ruwan.
.
Dansandan ya kaiwa kunnen mari katon gyaren ya tashi dansandan ya mari kunnensa a banza.
Kai wannan masifa dayawa take dansandan yace cikin zuciyarsa sau dayawa yakan zargi kansa da
kansa amatsayin mahaukaci domin wai in ba mahaukaci ba wane ne zai shiga aikin dansanda aikin
da akullum bashida wata riba sai ta bakin jini kullum kana gadin jama'a da dukiyoyinsu sukuwa
nabinku da tsinuwa.
Shekarunsa ashirin da biyu yana aikin dansanda amma haryanzu bai wuce sajan ba idan karshen
shekarar yazo yake sa ran yin ritaya.
Wannan dansandan sunansa AUDU ada can baya yasha niyyar barin aikin dansandan amma sai
wani abokinsa yace dashi Haba audu kada ka jahilci aikinka mana wannan aikin da kake rainawa fa
babu abinda yafishi muhimmanci domin daku yansanda da malaman makaranta idan babu ku babu
gari kaidai abinda zakayi kawai shine ka tsarkake zuciyarka ka nemi Halali acikin aikina sai Allah
yabaka lada yakuma albarkaci aikin Amma zancen wai kabar aiki wannan duk bata taso ba.
Wannan kalami na abokinsa shi yasa audu kaiwa har tsayin wannan lokaci yana aikin Dansanda
daga inda Audu yake fake yana iya hango duhuwar sauran abokan aikinsa su bakwai duk a rabe
dauke da bindigogi suna nazarin bakin ruwan
Audu na nan a makale zuciyarsa tana yi masa sake sake domin matarsa nada tsohon ciki kuma
awatan zata haihu haka nan har izuwa wannan lokacin bai sayi koda buzu ba.
Audu ya lalubi aljihunsa ya zaro kwalin taba cikin damuwa.
Dan cin hancin ma da muke karba anyi mana bakin ciki gashi dai ba wani kyautata mana akeyi ba
amma saboda bala'i kuma ance wai duk hancin wanda mukaci yakaimu Kara...
Tunanin audu ya katse adaidai lokacin daya hangi hasken fitilar mota ta nufi bakin dam din abinda
yabashi mamaki domin tunda aka kawo su adaren jiya kimanin karfe goma sha biyun dare har zuwa
yanzun nan basuga motsin wani mahaluki abakin ruwan ba. To me yakawo mota kuma?
Cikin sauri jikinsa na rawa audu ya fito daga inda yake labe bindigar dake hannunsa ta dada nauyi
in har akwai abinda audu yaki jiki shine akaishi aikin da za'a iya yin bata kashi kullum addu'arsa
itace Allah yasa yagama aikin dansanda ido biyu kafa biyu hannu biyu.
Kamar audu sauran yansandan ma sun ga zuwan motar don haka sai suka firfito daga inda suke
make kamar yadda aka umarce su sukabi cikin duhun kamar aljanu suka nufi inda sukaga motar
tayi.
.
Shafiu yafito daga cikin motar ya rufe sannan ya zagaya ya budewa aisha itama ta fito amma jikinta
na rawa kamar mazari da za'a tsaga jikinta alokacin zaiyi wuya a sami wani digo na jini.
Shafiu ya zaro wata katuwar cocila sabuwa daga aljihunsa sannan ya haske cikin ramin lokaci guda
kuma ya jiyo ya dubi aisha yace toh Aisha aiki ya rage naki ga ramin nan munzo Ya dada haska
mata cikin ramin da cocilan.
Aisha ta kurawa ramin idanu na tsawon lokaci har yanzun nan takasa imani da cewa wai shekaru
dari da shirin da suka wani daga cikin kakanninta ya binne dukiya acikin wannan ramin.
Kinga ma bishiyar giginyar da nake fada miki keda ganinta ai kinsan ta dade dubi fa saboda tsayi
harta lankwashe kamar macijiya.
Aisha ta zubawa bishiyar idanu na yan dakiku sannan saita dawo da idanunta cikin Ramin.

Toh aisha yi maza kiyi kiranta koma koma gida da wuri naga sha dayan har ta gota Aisha ta sauke
jakarta daga kafada sannan ta bude jakar shafiu ya matso kusa da ita cikin sauri ya haske cikin jakar
da cocilan hannunta na rawa ta dauko dutsen sannan ta murza shi atafin hannunta
Sabanin yadda sukayi tsammani guguwa zata tashi awurin awannan karon lokaci guda balbelar ta
bayyana abakin ramin ta kada fiffike tace Ai ina nan kusa daku bama sai kinyi bayanin komai ba
duk shawarar da kuka yanke jiya ina nan tare daku inajinku In banda abinku ai ni ma ina iya dauko
muku akwatin don baku san irin kaunar da mahaifinku ya nuna min bane shiyasa kuma nayi masa
alkawarin isar da duk wani sakon nasa.
.
Tana gama fadin maganar sai tayi girgiza nan da nan kamar budar ido sai kasar wurin ta fara
tsagewa sannu ahankali sai sukaga akwatin ta babbako daga cikin kasa ita kadai kaikace raine da ita
sannu ahankali ta sauka akusa da inda motarsu take.
Balbelar ta kada fuffukanta sannan ta dube su tace Shikenan kwadayinku ya kwanta?
Aisha da shafiu suka gyada kai lokaci a tsorace domin abinda suka gano yayi matukar girgiza su.
To ni zan tafi sai kuma mun sake haduwa. Kafin kiftawa da bismilla ta bace. Shafiu ya dubi aisha.
Aisha ta dubi shafiu jikinsu na rawa cikin sanda shafiu ya matsa kusa da akwatin ya dallara hasken
cocilarsa kamar yadda yayi tsammani haka ya ganta to saidai bata kai girman dayayi tunani ba duk
jikin akwatin jajur yake da tsatsa tun da yake bai taba ganin irin akwatin ba ko da kuwa a hoto ne
domin wannan akwatin a dunkule take sunduki sunduki.
Haka nan akwai wasu abubuwa masu kama da madauki ajikin akwatin har guri shida awannan
lokacin ne to aisha tayi abinda ta baiwa shafiu mamaki......Hakanan akwai wasu abubuwa masu
kama da madauki ajikin akwatin har guda shida awannan lokacin ne to Aisha tayi abinda ta baiwa
shafiu mamaki domin yana tsaye akan akwatin sai yaga Aisha ta matsa kusa da akwatin ta durkusa
sannan saita sa hannu ta dafa akwatin tsawon lokaci tana nan a durkushe duk da yake baya iya ganin
idanunta amma jikinsa yabashi cewa kuka take yi.
Kukan me kikeyi Aisha?
Babu komai. Tace dashi bakinta na rawa sannan saita mike tsaye ta dube shi tace Tayaya zamu iya
sa ta acikin mota?
Shafiu ya bude baki kenan zai amsa sai wata bushashshiyar murya daga cikin duhun tace da can
lokacin da kukayi satar bakuyi tunanin hakan ba?
.
Aisha da shafiu suka juya a firgice sannan ne to sukayi ido biyu da yansandan kowannensu rike da
bindiga suna zazazare idanu.
AISHA TA KWALLA IHU A RAZANE.
** ** ** **
Yansandan suka dubi juna a rude cikin tsananin mamaki sa'ar da Aisha ta gama basu labarinta.
Lokacin da yansandan suka ritsa su sun yi niyyar tafiya dasu ofishin yansandan gaba dayansu har da
akwatin to amma kukan da aisha tayi ta rafsawa a tsorace tana magiyar cewa abarta zatayi bayani
shiyasa INSFETA ZAKARI ya amince sannan yasa yansandan suka kawo motarsu bakin ruwan aka
jefa aisha da shafiu aciki sannan aka nemi dasuyi bayanin abinda sukeyi abakin ruwan da wannan
uban daren kuma dasu fadi inda suka samo akwatin in dai ba sato ta sukayi ba.
Don haka sa'ar da aisha tagama basu labarin sai sukaji abin kamar almara Insfekta Zakari ya harari
aisha gamida buga mata tsawa yace Ke kada ki raina mana hankali yanzu ke kina nufin mu yarda da
wannan tatsuniyar da kika fara mana?
Aisha ta fashe da kuka wallahi ba karya nakeyi ba ai ga akwatin nan gakuma takardar wasikar nan
ma agurinsa ta nuna shafiu wanda ke zaune bayako motsi saboda tsabar tsoro duk da wayewarsa
babu abinda yake matukar tsoro irin DANSANDA.
Yanzu idan nace inason naga ita takartdar da kakan naki yabaiwa aljanar tabaki zaki iya nuna
mana? Insfekta zakari ya tambayeta cikin sauri.
Aisha ta dubi shafiu tace Basu takardar nan shafiu.
Jikinsa na rawa ya lalubo takardar daga aljihun wandonsa ya mikawa Insfekta zaka.

Insfekta Zakari ya zurawa rubutun ajamin idanu. Dayake wani zamani daya wuce yataba karatun
Allo rubutun ajamin bai wani bashi wahalar karatu sosai ba amma duk da haka da kyar a daddafe ya
hada bakaken sannan ya karanta wa sauran yansandan A Fili.
Jami'an tsaron sukayi shiru na tsawon lokaci sa'ar da suka fahimce ashe akwatin dake nan dab dasu
acike take da dukiyar Milyoyin Kudi.
Insfekta zakari yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi Aisha da shafiu yace na yarda da abinda kuka fada
amma fa hakan baya nufin bazamu iya cazar ku da laifi kwata kwata bane kunga dai kayan nan da
kuka dauko suna da hadarin gaske tunda ko shima kakan naki dukiyar ba tasa bace sata yayi.
Saboda haka kinga dolene hukuma tayi bincike akai mai tsayin gaske kafin a gano wanda ya
mallaki dukiyar nan tun tsawon shekaru dari da ashirin. Ya danyi shiru.
Aisha taci gaba da shishshikar kuka hakan ya daya gani yayi matukar faranta masa rai don haka sai
yaci gaba da cewa amma duk da wannan hadarin da kuke ciki idan kuna so zan iya taimakon ku.
Aisha da shafiu suka dubi juna a tsorace Muna....so suka amsa baki daya
Insfekta yayi gyaran murya yace to abinda nake so daku shine kuyi gum da bakinku kada ku sake
wani yaji labarin akwatin nan sannan kuma zan rike wannan wasikar agurina zamuci gaba da
bincike har zuwa lokacin da zamu gano mai dukiyar ku kuma kuyimin alkawarin zakuyi shiru da
bakinku idan kukayi haka zan sallame ku yanzun nan ku tafi gida idan kuka sake labari ya riskemu
cewa kun bada labarin acikin gari to zamuyi muku kamun Yan Fashi kun yarda?
.
Cikin sauri su aisha suka gyada kai insfekta zakari ya kunnewa sigari wuta cikin farin ciki sannan
ya lalubi aljihunsa ya dauko Albashinsa cancakat da aka biya shi awannan ranar ya mikawa Aisha
yace ga wannan yan mata kya rage bacin ran da zaki shiga nasan tuni kin gama kasafin abinda
zakiyi da dukiyar kakanki ko? To hukuma bazamu amince da haka ba domin shima ba nasa bane
sata yayi da'ace wasikar ta nuna cewa dukiyarsa ce to da babu abinda zai hanamu baki kayanki.
Aisha ta karbi kudin a tsorace shafiu kuwa ji yake kamar zuciyarsa zata fashe domin yanaji yana
gani an raba su da milyoyin kudi an basu dubun naira
.
Ku tashi ku tafi ku kuma iya bakinku kunji? Insfekta zakari ya umarce su
Jikinsu na rawa suka nufi marsandin shafiu har suka shiga motar suka tafi babu wanda yace da wani
QALA
tafiyarsu keda sai Insfekta Zakari ya dubi sauran yansandan ya fashe da dariya sannan yace to ku
saurara da kyau kuji yau Allah yakawo karshen wahalar da muka dade muna sha shekara da shekaru
ina fatan kowa daga cikinku zai iya bakinsa domin wannan wata kyautace daga Allah ina ganin
abinda ya dace kawai shine mu sa bakin bindiga mu bude akwatin nan mu kasafta dukiyar dake ciki
kowa tasa ta fisshe shi ko kuwa ya kuka gani? Kunsan dai ba aikin kama barayi aka turo mu baki
ruwan nan ba kwantar da tarzoma muka zoAudu ne yafara cewa haka za'ayi yallabai sannan sai
sauran ma suka amsa baki daya mintuna biyar da faruwar hakan yan sanda suka sa bakin bindiga
suka balle daddiyar akwatin yar shekara dari da ashirin a karkashin kasa.
.
Insfekta zakari yakoma cikin mota ya dauko cocila sa'ar da aka bude tsohuwar akwatin yansandan
guda takwas suka zagaye ta kowa na hadiyar yawu zasu kwashi banza daga inda suke tsaye suna iya
hangen wasu abubuwa manya manya acikin akwatin.
Koda Insfekta zakari yataho dauke da cocilan sai yansandan suka dada marmatsawa domin su ga
zinare da lu'u lu'un dake ciki Insfekta zakari ya haske cikin akwatin nan da nan yansandan suka
dauke Numfashi lokaci guda cikin kaduwa da abinda suka gani.
Insfekta zakari yaji kamar hanjinsa ya tsinke.
A ajiye acikin akwarin GUMA-GUMA dasu har guda biyar wasu manya manyan duwatse ne kan
kura.
.
Cocilar dake hannun insfekta zakari ta kwace ta fada cikin akwatin fus ta fashe ya juyo bakinsa a
kafe ya dubi Audu yace Mun dauki adireshin yaran nan kuwa ?
Audu ya girgiza kai cikin kaduwa gami da

GODEWA ALLAH DA BA KUDINSA AKA BAWA 'YAR KYAKKYAWAR NAN BA yace.
Bakace mu dauki adireshinsu ba yallabai.
** ** ** **
Washegari misalin karfe hudu da rabi na yamma shafiu yayi fakin da bakar marsandinsa a kofar
gidansu aisha zuciyarsa cike da bakin cikin ta leko ta koman da suka gani adaren jiya.
Ga mamakinsa lokacin data fito saiyaga ita ko ajikinta wai an mintsini kakkausa
(ASMA'U MATORI)
domin cikin farin ciki ta tare shi tana murmushi
SANNU DA ZUWA MY ONE.
Shafiu ya dubeta fuskarsa a murtuke yace na fahimce ke Aisha ko jimamin asarar da kikayi bakyayi
Aisha ta dube shi gamida girgiza kai daman ba rabona bane shafiu haka allah ya kaddara domin
idan abu ya kasance rabonka ne Allah yabaka duk duniya babu wanda ya isa ya hanaka shi haka nan
ma idan ba rabonka bane to fa babu wanda ya isa ya baka.
Ina fatan zaka manta da komai musa abinda yake gabanmu acikin zuciyarmu Ta danyi shiru sannan
tace babu abinda nake kauna aduniya fiye da kai Shafiu wallahi dukiya dana rasa ajiya bata kai ko
rabinka ba agurina Nagodewa Allah da bakaine ka kubuce min ba.
.
Hakan datace shi ya tausasa zuciyar shafiu tayi fari tas don haka ya saki wani fatalwan murmushi
yace Haba ai abin ne da ciwo...to amma dai ta bakin naki domin duk dukiyar da zan samu aduniya
banza ce idan babu ke Aisha.
Aisha ta lumshe idanu naji dadin abinda ka fada wallahi harkasa zuciyata tayi sanyi.
Yanzu ma ai shiryawa zakiyi mu tafi Aisha ta bude baki cikin mamaki ina zamu?
Mahaifana ne suke son su ganki jiya nabasu labarin ki.
Aisha ta rufe idanu a kunyace tace
'kai haka da wurwuri?
Shafiu ya harareta yace haba aisha shekarata nawa ina kaunar ki? Don Allah je ki shirya kifito mu
tafi suna can suna jiran isowarmu.
.
Gani nan zuwa my one ta ruga gida aguje shafiu yabita da kallo sannan ya girgiza kai cikin
murmushi
'Karfe biyar na yamma suka isa gidansu Shafiu aisha ta caba ado da daya daga cikin leshin da shafiu
ya saya mata ya kuma sa akayi mata dinkin gaggawa duk da yake duniya ta juyawa mahaifin shafiu
baya saida aisha ta rude da ganin yadda aka tsara farfajiyar gidansu shafiu.
Shafiu ya bude mata kofa ta fito sannan sai ya dubeta da murmushi yace zo muje bayan mota nabaki
abinda na sayo miki domin ki basu amatsayin kyautarki ta musamman ga iyayena.
Aisha ta rike baki duk duniya banida mai kula dani kamar ka.
Shafiu yayi murmushi sannan cikin farin ciki sai ya zura dan makulli abayan motar domin bude but
din motar don ya dauko kyautar.
Yana bude bayan motar sai yayi tsalle gefe guda a tsorace
aisha ta rike kafadarsa a firgice tana duban bayan motar sannan ta karkada fuffuke tace
KUYI HAKURI NA TSORATA KU KO? Ina son ku sano ba nufina na cuce ku ko na tsorata ku ba
nazo ne domin na baku dukiyarku da akaso a zalunce ku adaren jiya yau Allah ya nuna min ranar da
zan cika alkawarina dana dauka tun tsawon shekara dari da shirin da suka wuce.
Ku leka ku gani dukiyar ku tana bayan motar nasan jiya kwana kukayi bakuyi barci ba kun hadu da
azzalumai bata gari ai nayi maganinsu danasa musu GUMA GUMAN DUWATSU ACIKI.
.
Balbela tayi shiru sannan sai ta dubi aisha tace To Aisha sai watarana daga yau bazaki sake ganina
ba tana gama fadin haka saita bace.
Shafiu ya dubi aisha murmushi ya subuce masa tun kafin ma ya leka bayan but din motar ya hangi
haske da walkiya na tashi aciki.
Jikinsu na rawa suka leka numfashinsu ya dauke cak sa'ar da suka ga but din motar cike da wasu
irin kananan duwatse masu kyawun gaske suna haske da walkiya.

.
Dukiyarmu ta dawo aisha shafiu yace sannan yayi tsalle sama ya dire yayi ihu cikin murna ga
mamakinsa saiyaga Aisha ba murna takeyi ba maimakon hakan ma sai hawayene ke zuba daga
idanunta
Kukan me kuma kikeyi?
Aisha ta goge idanu tace shafiu kada fa ka manta da cewa wannan dukiyar ba hakkinmu bace domin
shima kakan nawa.KARSHE.
THE END
.
Kukan me kuma kikeyi?
Aisha ta goge idanu tace Shafiu kada fa ka manta da cewa wannan dukiyar ba hakkinmu bace
domin shima kakan nawa SATO TA YAYI.
.
Shafiu yaji kamar Aisha ta kwada masa guduma a kirji To yanzu me kike nufi? So kike mu dauki
dukiyar aka mu shiga gari neman wanda akayiwa sata shekaru dari da shirin da suka wuce ko me?
.
Ganin ransa ya baci sai Aisha ta matsa kusa dashi ta dafa kafadarsa akaro na farko tace a tausashe
Shafiu abinda nake son ka fahimta shine wannan dukiyar ba tamu bace bamuda hakkin taba ta
kanaji fa abinda yace shima sato ta yayi.
Shafiu ya dubi asiaha a fusace yace To Idan dukiyar ba tamu bace ta wacece?
Fada min mana aisha dukiyar wacece aduk fadin garin nan?
.
Aisha ta fashe da kuka sannan ta girgiza kai tace
WALLAHI NIMA BAN SANI BA.
Shafiu ya matsa kusa da ita yace kada ki sani ciwon zuciya Aishata Yaya Arziki yana binki kina
gudunsa ?
.
KARSHE.
.
NAZIR ADAM SALIHI (Nas)


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels

Please Login or Register in order to submit comment