Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi sai cutarwa. Habib! Ka san
menene ke tsorata ni fiye da komai?" Yafada
yayin dayayi shiru,ni kaina sai na tausaya masa.
"Aduk lokacin da mai sihiri ya mutu,jeka ka
tona kabarinsa idan har kana da karfin yin
hakan. Abin da zaka gani ciki ba zaisa kayi
sha'awar kasancewa cikin wannan hali ba. Habib!
Ni kaina ina son na daina sai dai ina!shaidan
yayi alkawarin batar da duk wanda baifi karfin
zuciyarsa ba" Ya samu dakiku biyar kawai ya
kurawa kwalbar ido,tamkar yana mamakin
ganinta a hannunsa. "Ka taya ni addu'a habib"
Lokacin daya fada hawaye ne a
idanuwansa,amma yana rufe bakinsa sai ya kafa
kwalbar giyar a bakinsa ,yaci gaba da zazzaga
ruwan a tumbinsa . Tun daga lokacin bai kara
cewa uffan ba ,haka zalika ni ma bance masa
komai ba . Har sai lokacin da anas ya idar da
sallar ya karaso inda muke. "Yanzu dandash
mene ne abun yi ?" Ya bukata. Batare da
dandash yayi magana ba ya buda jakarsa ya fito
da wani sumulmulen farin dutse ya dora shi a
hannun hagunsa,kana sannu a hankali yafara.
Shashshafa dutsen da hannun damansa. Bai
dade yana yin hakan ba sai mukaji yanayin
magana da farko ba mu samu fahimci meke
faruwa ba ,sai da muka ga ya tattara hankalinsa
ga ruwan,sannan nima na kalla. Cikin sauri na
dauke idona a razane nan da nan bugun zuciya
ta ya tsananta,cikin kankanin lokaci gumi ya
rinka keto min,take jikina ya rinka tsima kamar
mazari,ba na son kallon abinda na gani . Fuskar
mummunar matar dana gansu, tare da fareeda
ce ta bayyana akan ruwan. "Yaya sunanki?".
Dandash ya bukata . Taki yin magana . Yakara
tambayarta shiru,sai ya matsa dutsen dake
hannunsa. "Sunana G-A-R-M-O-D-A!" Tafada
cikin shakakkiyar muryA. "Ina farida" wannan
karonma taki magana ,shima sai ya kara matsa
dutsen. "Tana taredamu" alokacinne na fahimci
ta hanyar matsa dutsen ne ya ke tirsasa ta take
magana . Kamar yarda masu yin (ruqiyya) ke
tirsasa aljanu suyi magana ta hanyar karanta
Alqur'ani. "Bamu labarin komai" dandash ya
bukata. "Shugabanmu ne yakawota,kuma yafi
sonta fiye da kowacce macen dake tare damu.
Shine da zaiyi tafiya ya bani umarnin kula da
ita,cewar duk inda zani kafata kafarta.
@mr:shuraih 99% Nikuma dama aikinane
dukinda ake gagarimin taro indai na mata ,zan
rika bi ina dauko kyawawa daga ciki. Ina kawowa
shugabanmu. Sanin cewar kyawawan mata zasu
halarci wasan kwallon kafar da za agudanar,
(nigeria 99) shine na tafi da ita . A lokacin
danake kokarin dauke wata kyakkyawan
yarinya,shine habib yahadu da ita ,sukayi hira
yabata zobe,ta kuma kwatanta masa gidansu.
Zoben daya bata shine na mayar,kan kabarin da
jama'a ke tunanin gawar farida na ciki. Nayi
hakanne don kawar da zarginsa Idan yagani
kada ya dauka farida mutunce, alokacin dayake
kan hanyarsa ta zuwa gidansu na tura da zoben.
Ganin bai hakura ba yana neman bayyano sirrin
shine naso na zautashi ta hanyar baiyana cikin
haske siffar fareeda ,yayinda yake tsaye akan
kabarinta karo na biyu. Addu'ar dayayi itace ta
zamar masa garkuwa ,daga wannan sharrin dana
tasamma yi masa" Alokacin dana ji wannan batu
, nayi matukar mamaki da tuni na zama zararre.
Anan kuma na kara fahimtar,wannan hira da
dandash keyi da Garmoda,taso tayi daidai da
wani abu da turawa keyi wa mutumin da yayi
wani abu kwata kwatakuma ya manta. Idan anso
ya tuna sai ayimasa wani abu da suke kira
(hypno analysis) @mr:shuraih 99% "Wanene
shugaban naku? Ta yaya kuke daukar mace ? Me
kuma yakeyi da matan?" Dandash ya katse min
tunanina . Wannan tabyar da yayi .rufe bakinsa
keda wuya,kamar walkiya ta baiyana ta bace ,sai
kwatsam !ganinmu mukayi a wani irin gida
,yayin da ruwan yayi ambaliyar ba-zata da mu.
A razane na kalli anas da shima tuni ya rude
,dandash kuwa ya fice daga hayyacinsa . A
sannane na fahimci Garmoda ta yiwa dandash
,abinda baiyi tsammani ba. Kuma da dukkan
alamu a Fadar shugabansu muke . Can sai wani
jibgegen kato kamar wanda yahada dangantaka
da samudawa ,kyawawan matan zagaye da shi
ya nufo wajenmu. Farin kyalle ne daure a
jibgegen kansa,anyi daran rubutu da bakin fenti
BARBUSHE.
9"Aaaah!"Nafada yayin da jibgegiyar kafarsa ta
dira a timbina .Yakara tallafo fuskata ya gabza
min mari,wannan karon kasa yin ihu nayi.Ya
cakumo kwalar rigata da jibgegen hannunsa har
sai d fuskata tazo daf da tasa.Ya kura min ido da
jibga-jibgan idanuwansa,masu kama da
garwashin wuta.Bazan iya hada ido da shiba
,kawai sai na rufe idanuwana .Ina jin zazzafan
numfashinsa na bugun fuskata.Ban dade da rufe
idanuwana ba sai jin bugu. Nayi a kirjina
,"Uuhhh!" Cikin halin jin matsanancin radadi
nayi kug.Alokaci guda kuma ya cillar dani
.Matukar zogin danaji yayin dana gwaru da
bangon dakin shi yatabbatmin kasusuwan
bayana sun kakkarye.Das! Jibgegiyar kafarsa
tayi dirar ungulu a kwanyata .Nazata raina ne ke
shirin ficewar daga jikina ,A lokacin dawasu irin
taurari suka ziyarci ganina .Sai daga bayane na
fahimci ashe suma nayi.Cikin halin matsanancin
ciwo da azabbabben radadin dake azabtar da
duk wata gaba dake jikina .Kwalkwalta kamar ta
tarwatso daga cikin kokon kaina,saboda
masifaffen zogi.Da kyar da jibin goshi nadan
bude idanuwana.@mr:shuraih 99%A halin jina
jina naga Anas da kuma dandash ,shine ya
tabbatar min suma sun sha dan karen bugu
kamar yadda nasha.Na lura da yadda jininmu ya
fantsamu nan da can ajikin bangon
dakin."Nhmm....". Cikin halim yar karamar
murya mai cike da tausayi ,shima anas ya
farfado.Bayan ya bude idanuwansa ya fahimci
halin da muke ciki,sai yadaga hannuwansa,yafa
ra Addu'a. .A duk halin da bawa yasamu kansa
babu abu mafi alkhairi gare shi irn fadawa
ubangiji bukatunsa nikaina sai na fara
Addu'a.Bayan mun gama addu'a sai dandash
shima ya farfado.Duk dani kaina a galabaice
nake sai na da tausaya masa ,yayin dana kalli
galabaitacciyar fuskarsa .Ya kalle ni kana
Anas,sannan ya umarcemu da mu matsa kusa
da shi.Bayan ya kwanto wata doguwar siririyar
fata daga kugunsa.Sai yakara mayar da fatar
kugunsA ya daura sau daya ,sannan ya rike
hannun anas dake bangaren hagunsa ya kure da
jelar fatar.Ni maya kama hannuna da daya jelar
fatar ya daure tamau.Kawai mu dai munzuba
masa ido ne ,domin munsan akwai al'amarin
dayake shirin aiwatarwa.A daidai wannan
lokacin sai kofa tabude.Barbushe da aka rubuta
balo-balo da bakin fenti dake daure a jibgegen
kansa shine ya shigo dakin .Kamar lokacin
farko,wannan karon ma kyawawan mata ne
hagunsa da damansa,daban kirga adadinsu
ba.Bayan ya shigo dakin sai kuma garmoda ta
shigo,kallo daya zakayi wa mummunar fuskarta
kasan arazane take.A bayanta sanye da bakin
kwat da siket din dana fara ganinta dasu a
rayuwarta .farida ce.@mr : shuraih 99%Shiru ya
mamaye dakin tamkar mutuce ta ratsa ,in ka
dauke zuciyata dake barazanar faso kirjina ,don
matsanciyar bugun da takeyi.Na kalleta sama da
kasa ,naga shakka babu farida ce,saina ji wani
irin ni'imtaccen sanyin soyayyarta ya keta
zuciyata.Wanda har na manta da ciwon da zogin
dake addabata.Tunda ta shigo dakin babu wanda
ta kalla,kawai dai ta sunkuyar da kanta ,ta
tattara hankalinta ga kyakkyawan zaren da ke
hannunta,kamar lokacin farko da muka
hadu.Dana lura da hannuwan sauran matan,duk
akwai irin wannan zaren,kuma irinsa ne suka
manta a villa guest inn.Jibgagen katon yakalli
dandash da anas,sannan ya dawo da hankalinsa
gareni.Ganin ina kallon farida yasa yayi mini
wani irin kallo,wanda fal kallon yake da
matsanancin kuna ,kasancewar yana son farida
fiye da komai,kamar yadda garmoda ta
fada.Dukkaninmu muka yi jugum, kamar
berayen da kyanwa ta ritsa.Ganin na dauke
kaina sai ya mayar da hankalinsa ga garmoda
.Babu abinda ke bani mamki da shi irin tun
daya fizgo mu zuwa fadarsa, har zuwa yanzu ban
ga motsa bakinsaa ba ,ballantana yayi
magana.Cikin kankanin lokaci gaemoda ta fice
daga hayyacinta ,yayinda kai tsaye barbushe ke
kallon cikin idanuwanta.Jikinta gabadaya ya
rinka kakkarwa,kamar wacce ake gasawa da
wuta .Tun tana dan daurewa dan kada tafadi
kasa,Amma ina !sai data yanke jiki tafadi kasa
wanwar . Akwai wani lokaci dana taba ganin
wata kyanwa ta kura wa kadangare
ido,kadangaren makale yake ajikin katangan
wata kango,inda. Babu yadda za ayi magennan
ta riskeshi,kuma dan motsawa kadan zaiyi ya
gujewa magen ta daina ganinsa .Amma cikin
wani hukunci na ubangiji kadangren ya kasa
zuwa ko ina,kawai sai ya tsaya yana ta
makyarkyata ,har sai daya fado magen ta dauka
.To shine yayi daidai da abin da abin danake
gani yanzu¤¤¤¤
Kiri
kiri a idonmu ,garmoda ta fadi tana
makyarkyata ,kana ganin yaddda mummunar
fuskarta ke ya mutsewa cikin kunci,kasan ranta
ne ke shirin barinn jikinta.Wani abu daya dada
girgiza tunanina shi ne narkewa da ta ringa yi
tamkar yadda dalma ke narkwa a kan wuta.Ina
ganin lokacin da anas ya makalkale jikin
dandash, yayin daya dauke idonsa daga kallon
abin al'ajabin dake faruwa.Wannan shine yayi
daidai da lokacin da garmoda tazo min da siffar
farida yayin danake tsaye akan kabarin
farida.Shakka babu wannan sihirine
mabaiyani.A daidai wannan lokaci sai dandash
ya tube hukar dake kansa,yaciro wani kambu
dake damtsen hannunsa na dama yasaka acikin
hular,cikin halin saurin baki ya ringa fadan wasu
yamutsasstsun kalmomi yana yawu akambun
dake cikin hulat.Basai wani ya fassar min
meyake shirin aiwatarawa ba,sihiri zai yi
ahankali sai hayaki yafara tashi daga cikin
hular.Dana mayar da hankalina ga barbushe
,yana nan yadda yake tsaye akan garmoda dake
narkewa cikin haske.Kamar daukewar wutar
lantarki, babu wani abu da yayi saura daga
gareta ta narke .babu ita sannan babu wata
shaidan da zata tabbatar dazu ta tsaya
awajen.Bazan iya tuna hakikanin yadda
al'amarin yafaru ba ,ni dai kawai abinda zan iya
tunawa naga hayaki na fita daga cikin hular
dandash ,lokacin daya cilla ta daki fuskar farida
.Cikin abin da baifi dakika ba gabada dakin ya
turnike da hayaki,tamkar ilahirin gidan ne ke
shirin gobarewa."Alelujah" jibgegiyar muryar
barbushe mai kaman fashewar nakiya ya
gauraye ilahirin dakin ,yayin dayayi wata irin
faduwar bazata .Kamar daukarsa akayi aka fyada
da kasa .Sai tsintar kaina nayi har yanzu
hannuna daure tamau ,ga dandahs da kuma
anas dukkaninmu ya janye mu daga fadar
barbushe zuwa tsibirn dazu.Babban taimakon
da muka samu abakin gaba muke.Cikin abin da
baifi dakiku uku ba ,muka fito waje haryanzu
jakar fatar dandash da kuma kwalaben giyarsa
guda biyu na nan a wajen.Daya ya shanye ,daya
kuma akwai ragowar 'yar kadan.@mr:shuraih
99%Ba sai dandash yayi bayanin halin dayake
cikiba kallonsa kawai zakayi ka fahimci ya fimu
jigata .Don sai da muka taimaka wajen fito
dashi daga ruwan.Yayi yunkurin kwance mana
hannayenmu amma sai ya kasa.Ganin abin daya
ke nufi sai muka kwance hannayenmu.Anas na
kwance hannunsa sai ya durkusa akan
gwiwowinsa ya fuskanci gabas ,kana yadaga
hannayensa sama alamar rokon Allah yakeyi
.Cikin karfin hali dandash ya yafito ni, alamar na
kai kunnena bakinsa."KASHE KANTA ZATA
YI" .da kyar maganar ta fito daga bakinsa ,yayin
daya yi min nuni da hannunsa.Ina kallon abin
dayake nuna min sai hangar farida nayi ta jike
sharkaf alamar ita ma ruwan ta fado,kamar
yadda muma muka fado.Sai dai ita har ta riga ta
fita kuma ta rufa aguje,kamar wacce ke shirin
tashi sama."KASHE KANTA ZATA YI". Maganar ta
kara daidai tuwa a kwalkwalwata."Farida"
muryata ta cika dajin cikin tsohion daren
lokacin da raina kamar zai fita don gudun hana
ta yunkurin kashe kanta,da take shirin
aiwatarwa.Domin sai daga bayane na fahimci
wani tangamemen ramine ,dake nesa kadan
daga inda take ,shikuma ta ke shirin
fadawa.Gudu take yi,Gudu nakeyi.Tana dada
kusantar ramin,ina dada kusantarta.A daidai
lokacin da take shirn taka takun karshe ,wanda
daga shi sai
мυη ~ ĵι~ мυη ~ gαηι
¢ιgαвαη ѕιяяιηѕυ
ωαяηιηg : вα'α кαяαηтα Ļιттαƒιηηαη đα đαđđαяє
ѕαвσđα gυĵєωα мυgαуєη мαƒαякαι
αυтнσυя: мαĵє єĻ нαĵĵ
ωяιттєη : ѕнυяαιн υѕмαη
¢нαρтєя : 10
Kiri kiri a idonmu ,garmoda ta fadi tana makyarkyata
,kana ganin yaddda mummunar fuskarta ke ya mutsewa
cikin kunci,kasan ranta ne ke shirin barinn jikinta.
Wani abu daya dada girgiza tunanina shi ne narkewa da
ta ringa yi tamkar yadda dalma ke narkwa a kan wuta.
Ina ganin lokacin da anas ya makalkale jikin dandash,
yayin daya dauke idonsa daga kallon abin al'ajabin dake
faruwa.
Wannan shine yayi daidai da lokacin da garmoda tazo
min da siffar farida yayin danake tsaye akan kabarin
farida.
Shakka babu wannan sihirine mabaiyani.
A daidai wannan lokaci sai dandash ya tube hukar dake
kansa,yaciro wani kambu dake damtsen hannunsa na
dama yasaka acikin hular,cikin halin saurin baki ya ringa
fadan wasu yamutsasstsun kalmomi yana yawu akambun
dake cikin hulat.
Basai wani ya fassar min meyake shirin aiwatarawa
ba,sihiri zai yi ahankali sai hayaki yafara tashi daga cikin
hular.
Dana mayar da hankalina ga barbushe ,yana nan yadda
yake tsaye akan garmoda dake narkewa cikin haske.
Kamar daukewar wutar lantarki, babu wani abu da yayi
saura daga gareta ta narke .babu ita sannan babu wata
shaidan da zata tabbatar dazu ta tsaya awajen.
Bazan iya tuna hakikanin yadda al'amarin yafaru ba ,ni
dai kawai abinda zan iya tunawa naga hayaki na fita daga
cikin hular dandash ,lokacin daya cilla ta daki fuskar
farida .
Cikin abin da baifi dakika ba gabada dakin ya turnike da
hayaki,tamkar ilahirin gidan ne ke shirin gobarewa.
"Alelujah" jibgegiyar muryar barbushe mai kaman
fashewar nakiya ya gauraye ilahirin dakin ,yayin dayayi
wata irin faduwar bazata .
Kamar daukarsa akayi aka fyada da kasa .
Sai tsintar kaina nayi har yanzu hannuna daure tamau ,ga
dandahs da kuma anas dukkaninmu ya janye mu daga
fadar barbushe zuwa tsibirn dazu.
Babban taimakon da muka samu abakin gaba muke.
Cikin abin da baifi dakiku uku ba ,muka fito waje
haryanzu jakar fatar dandash da kuma kwalaben giyarsa
guda biyu na nan a wajen.
Daya ya shanye ,daya kuma akwai ragowar 'yar kadan.
@mr:shuraih 99%
Ba sai dandash yayi bayanin halin dayake cikiba kallonsa
kawai zakayi ka fahimci ya fimu jigata .
Don sai da muka taimaka wajen fito dashi daga ruwan.
Yayi yunkurin kwance mana hannayenmu amma sai ya
kasa.
Ganin abin daya ke nufi sai muka kwance hannayenmu.
Anas na kwance hannunsa sai ya durkusa akan
gwiwowinsa ya fuskanci gabas ,kana yadaga hannayensa
sama alamar rokon Allah yakeyi .
Cikin karfin hali dandash ya yafito ni, alamar na kai
kunnena bakinsa.
"KASHE KANTA ZATA YI" .da kyar maganar ta fito daga
bakinsa ,yayin daya yi min nuni da hannunsa.
Ina kallon abin dayake nuna min sai hangar farida nayi ta
jike sharkaf alamar ita ma ruwan ta fado,kamar yadda
muma muka fado.
Sai dai ita har ta riga ta fita kuma ta rufa aguje,kamar
wacce ke shirin tashi sama.
"KASHE KANTA ZATA YI". Maganar ta kara daidai tuwa a
kwalkwalwata.
"Farida" muryata ta cika dajin cikin tsohion daren lokacin
da raina kamar zai fita don gudun hana ta yunkurin kashe
kanta,da take shirin aiwatarwa.
Domin sai daga bayane na fahimci wani tangamemen
ramine ,dake nesa kadan daga inda take ,shikuma ta ke
shirin fadawa.
Gudu take yi,Gudu nakeyi.
Tana dada kusantar ramin,ina dada kusantarta.
A daidai lokacin da take shirn taka takun karshe ,wanda
daga shi sai....................
Zanci gabaPart 11
Last page
Tana dada kusantar ramin,ina dada kusantarta.
A daidai lokacin da take shirn taka takun karshe ,wanda
daga shi sai ramin adai dai lokacinne hannuna yayi nasarar kamota
.
LAST PAGE ERROR
.
Jama'a dayake kunsan wannan littafi tsohon ajiya ne , toh yanzu dai karashen littafin ya yage
Amma ga abun da karashen fallen littafin ya kunsa
*******
Mun yi nasarar tseratar da Farida da kuma karya Asirin da Barbushe yai mata,
Daga nan sai dandash yayi sihiri muka bace a cikin dokar dajin nan muka bayyana a gida
*****
Jaridan Dankari jaridace ta mijin yayana Ahmad, a jaridan tayi suna da karbuwa sosai a wajen al'umma inda mutane suke jiran fitowarta duk sati
.
Wannan karon Jaridan na dauke da firgitaccen labari wanda mutane da dama bazasu taba yarda da shi ba, a shafin Farko na jaridar an sanya hotona dana farida cikin manyan launi, a saman hoton an rubuta
(......) Na manta abun da aka rubuta friends
.
Wannan yasa jaridan na wannan satin ta samu karbuwa sosai mutane da dama da suka sanni suka runga zuwa wajena muna gaisawa suna yimin barka
,
******
Yan sanda sun samu nasarar kama barbushe da dukkan mukarrabansa ma'abota tsafi
********
Tangamemen falone mai madaidaicin girma, iyayen farida da iyayena suna zazzaune akan wasu dogayen kujeru masu matsakaicin tsayi, a gefe daya kuwa Anas,Dandash da insfekta Sagir suna zazzaune suma akan kujera mai mazauna uku, ni kuma ina zaune akan kafet din tsakar dakin fuskana na kallon kafet din,
Mahaifin farida ne ya fara bude taron da Addu'a sannan ni na tashi na fara kawo labarin tun farkon haduwana da farida , har ta kwatanta mani gidansu, da zuwana gidan da nayi aka tabbatarmani ta dade da mutuwa da sake ganinta dana ke a wurare dabam dabam,
Har zuwa lokacin da na hadu da anas muka je garin su dandash
,
Dandash ya mike ya fara bayani, akan mutuwan sihiri, da yadda ma'abota tsafi suke sanya mutum yayi doguwan suma bayan an bizneshi suje kabarinsa su ciroshi su maye gurbinsa da wani abun daban
,
**
Godiya sosai mahaifan farida sukai mani,
Bada dadewa ba aka sanya Ranar Aurena da farida,
***
Abubuwa sun daidaita yanzu dandash ya musulunta,
Bayan haka da mukaje muka tone kabarin Farida sai muka tarar da tarin itacen giginya ne a ciki
.
Alhamdulillah
MAJE EL HAJEEJ HOTORO 1999
.
Anan muka kawo karshen littafin MUN JI MUN GANI cigaban SIRRINSU,
Ya Allah duk wasu kurakuren dana tafka cikin littafin Allah ka gafarta mani
,
JIN JINA GA
Ilyas ishak gundutse
Muhammad Maiyi ninko
Yarima a gangariya
Sadeeq Shehu Shareef,
Matukar jinjinawa gareku na jmiri da jiran Postin dina
ILYAS ISHAK GUNDUTSE
MUHAMMAD MAIYO NINKO
SHAMSU A BAITI
ALHASSAN ADAMU ALA
Usman Ubale SafUs Rano
Shaheedah Fahat Ma'aji
Da sauransu
.
FATAN ALKHAIRI GA AHALIN
Taskar Gidan Littafi
Tsangayar marubuta
.
Littafin da zan kawo maku na gaba shine
AJALI daga Gidan Littafi
.
Littafin yazo maku ne daga shafin http://hausaebooks.cf
A kowani yanayi, ko wane lokaci zaku iya shiga shafin don dauko wasu littatafan masu kayatarwa


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment