Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

SAI NA GA RAHMA SADAU
Marubuci
Imam abdullahi usman
Publish by:-http://fb.com/hausaebOoks

SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Dedicated to Sulaiman Ibrahim Azlan
Posts by SHURAIH 99%
Part 1
FARKON LABARIN
.
zaune nake a kofar gida, bisa kan benchi. Yammaci ne
misalin karfe 4 da 'yan mintuna.
Nazari nake gami da tunanin lbrn da zan soma wallafa.
"assalamu alaikum" muryar wani matashi ta katseni,
"wa'alai kassalam" nace gami da dagowa na kalleshi.
"yauwa wlh dama ni bakon kane, nasha wahala kafin in
samu gidanku, wuni nai ina yawo.
Yace dani

na sake dubansa, tabbas duk inda aka je, aka zo
bakauyene, kuma ba bafulatani bane.
"gashi kuma bangane kaba, anya kuwa ni imam din kake
nema ? Na ce dashi.
Ya gyara tsayuwa gami da cewa "tabbas kaidin dai,
wannan me rubuta lbr a yanar gizo, koba nan ne
unguwar matsango ba ?
Ya fada gami da jefamin tambaya.
"maraba da zuwa, tabbas nine, na fada gami da mikewa,
nace muje daga ciki.
Daki na na kaishi, gami da dauko masa ruwa da guntun
abincin rana. Na bashi waje, sai da ya gama sannan na
dawo.
"da farko ina maka barka da zuwa, sannan zanso sanin
kai waye da dalilin zuwanka" nace dashi, dai dai lokacin
da zauna bakin katifa.
Bakon yai ajiyar zuciya gami da cewa " sunana rabi'u
amma anfi sani na da rabe, nazo ne daga kauyen dalli nan
karamar hukumar shira, akwai wani abokina dan
makaranta, da muke kwana daki guda da shi, shi ke
karanta mana lbrn ka, gaskiya muna jin dadi. Yanzu haka
takaici nake da ban iya karatu da rubutu ba, tabbas da
ace na iya, da saina kwace maka dukkan magoya
bayanka, da zarar na rubuta lbr daya.
Nai murmushin rainin wayo gami da cewa "ina maka
barka da zuwa, kuma nayi farin ciki, ashe kaima kana da
ra'ayin rubu2 ?
Ya gyara zama "ai kai dai kawai ka bari, allah ne ya ragewa
aya zaki, yanzu dai ka karkada kunnuwanka, kasha lbrn
soyayyata da rahama sadau.
"comedy kenan, na fada araina, yanzu wannan ba kauyen
har ya isa ya tsara wani lbr ? Jifa tsabar shirme wai shi da
rahama sadau. Amma a zahiri sai nace "inajinka" {ko ba
komai ai zansha nishadi dan lokacin completly ali
artwork na dauke shi}
rabe ko ince rabi'u ya soma da cewa....
¤¤
malam barau da gwoggo tani sune mahaifana, babana
bai da wata sana'a face noma, ita kuwa gwoggo tani
dinkin tabarmar kaba take. Ni ka daine dansu, dagani ba
kowa, hakan yasa suka shagwa6ani, bana kallon kowa da
mutumci duk girmanka yanzu zan maka tijara, in
takaicema lbr ko su iyayen nawa ma ban ganinsu da
daraja. Na dago idanuna na kalle shi cikin mamaki.
"karkai mamaki na bawan allah, su suka raine ni da
hakan, kuma na dau course.
Ya cigaba "shekara ta 18, amma bansan ko bihim ba,
abarma maganar boko kam, dan ko A ban saniba. Wayar
da babana ya siyamin ban cika ta da komai ba, face fina
finai da wakoki gami da fotunan rahama sadau. Dan haka
na taso mai kaunar wannan baiwar allah, awancan
lokacin inason rahama sadau fiye da kowa a duniya....!

Bari in takaita haka, in soma fada maka, musabbabin
lamarin.
Karfe 8 da 'yan mintuna, na fito daga dakina rike da wata
tsohuwar jakata, ba komai ciki face 'yan tsummo kara na.
Mahaifiyata dake fama da wutar dumame ta dago ta
dubeni, "dan baba ina zaka da tarin kaya haka ?
Sai da na gama garkame dakin, na dubeta nace "neman
rahama sadau" a zabure ta dubeni, tuni idanun ta sun
kawo ruwa, "dan baba ka rufa mana asiri, dan allah karka
fada uwa duniya.
"wannan kuma ya rage naki gwoggo, amma yau kwana
sai kano. Nace gami da rarumar 'yar jakata na aza a ka.
"wayyo allah malam na shiga uku. Tafada da karfi
babana ya fito daga daki. a rikice taimar bayani, ya ruga
da gudu da nufin ya taroni.
"kai dan baba" naji yana kwadamin kira a sa'ilin har nayi
nisa, na kusa cimma tasha, na tsaya gami da jiransa.
"wlh baba saina tafi nemanta, ai yanzu da hankali na niba
yaro bane. Nace dashi ina huci.
Mahaifina yana kuka, yana roko na, gami da rikemin
jakata. Akan na hakura da tafiyar nan, amma haka na
fizge jakata har sai da ya fadi, naje tasha na hau motar
azare, daganan na shiga ta zuwa kano, da zumar haduwa
da rahama sadau.
Direban motarmu, ya kure totir, gami da jan motar
aguje.......!
¤¤
port 2 na loading
¤
www.facebook.com/hausaebooks
SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Dedicated to Kingboy Isa
Posts by SHURAIH 99%
Part 2
.
motarmu ta shalla kan titi, zakai mutukar razana idan
kaga yadda direban mu yake, jan motar da gudu, kai kace
ba rayukan al'uma bane aciki.
An saukemu a wata tasha, da na mance sunanta,
passingers kowa ya soma sanin inda dare yai masa.
Nima jakata na dauka, gami da mikewa nai gabas, sai da
dai 'yar ubansun tafiya sannan na yanke shawarar yin
tambaya, tunda hausawa sunce matambayi bashi 6ata.
Wani mutumi na hango, akallah zaikai shekaru 28 yazo
gilmawa ta gabana.
"malam dan allah tambaya nake" nace dashi
yaimin kallon banza , gami da cewa "ina jinka" na gyara
tsayuwa na ce "dan allah inane gidan "yan film din
hausa ? Ya dubeni a wulakance gami da cewa "ka gamu

da aiki ai shasha, anan zakai ta gararamba" yana gama
fadin hakan yai tafiyarsa.
Na bishi da idanu gami da jijjiga kai, lokaci guda naji
hajijiya na damuna, sakamakon cikina dake min korafin
yunwa.
Sannu ahankali na bude baki gami da kiran wata yarinya
mai sai da gurasa da ruwansha.
Haka na ci gura sar nan, tana shakata ina korawa da
ruwa.
Nakoma jikin wata inuwa na dan huta. Daga bisani na
kuma daukan jakata, lokacin rana ta take.
"malam dan allah ni bakone, tambaya nake. Na ce da
wani mutumi da nake kyautata zaton zai kai 30.
Ya dubeni cikin sakin fuska " yauwa inajin ka" cikin
kwarin gwiywa nace "wlh ni bako ne, daga jihar bauchi
nazo wajen "yan film ne, ina son ganin RAHAMA SADAU.
Mutumin yazaro idanu gami da yin murmushi cikin farin
ciki yace "alhamdullah, ka godewa allah, tazo gidan sauki,
allah ya takai tama, sunana YASEEN AUWAL". Cikin
zumudi na dubeshi, kana nufin daraktan film din
RARIYA..? Ya jinjina kai gami da yin murmushi, yace
tabbas kuwa "yanzu haka na kai mota ta gareji ne.
"dan allah malam ka taimakeni, dan allah kaimin hanyar
ganinta, wlh dan ita nazo. Nace dashi cikin sigar rarrashi.
Ya dubeni gami da dafa kafadata yace "zan tai ma keka,
kasa aranka kaga PRIANKHA, ni dai kawai bukatata kayar
da dani.
"malam na yarda dakai wlh, nace dashi cikin zumudi.
Nan ya tara mana adai dai ta.
muka shiga, aka kaimu wata unguwa.
Kasan me yaban mamaki imam ? Na jijjiga kaina. yace "
gidan da ya kaini amatsayin gidansa, bawani gd ne na
kuzo, mu gani ba, dan gidan kansilan kauyenmu ma ya
fishi.
Daki dayane ciki da falo, balaifi akwai tv da "yan kujeru a
falon, dakin kuma katifa dayane.
Bandaki ya soma nunamin yace naje nai wanka, yana
zuwa. Na dade ina wankan, daga bisani na fito. Na tarar
da shi zaune, a bakin katifar ga wata kodaddiyar kula a
gabansa.
Da kyar na iya sanya kaya, duk ya kureni da wasu
idanuwansa, niko ba sabawa nai ba. Ya sani agaba sai da
naci abincin.
Daga nan hira muka dingayi, yana bani lbrn wuyar da
suka sha a shooting din RARIYA, nayi mamaki da wani
abokinsa ya kawo masa ziyara, naji yana kiransa NURA
AJI DADI, amma banda halin tambaya.
Da daddare an kawo wuta, tun kusan 8 ya kunna mana
kallo, anan yake sanar dani cewa RAHAMA SADAU taje
daukar wani film za suy kwana 6 su dawo.
Ni kuma na yarda.
Da daddare muna kwance....!

Rabe yana zuwa nan ya fashe da kuka, na dago gami da
kallonsa cikin kaduwa nace meya faru? Ya jijjiga kai gami
da share kwalla yace..... Ashe....!
¤¤¤
page na loarding
¤
¤
SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Dedicated to Jidda Abdullahi Usman
Posts by SHURAIH 99%
Part 3
.
rabe ya tsai da hawayen dake gudana a idanuwan sa, yace
ashe..! Mutumin nan yaudarata yai, mutumin banza ne,
fasiki, macuci, ji nai ya sanya hannun sa a al'aurata...!
"Innalillahi shine abinda na fada cikin tashin hankali, nace
ya aka kare ?
Rabe ya jijjiga kayi gami da share wasu hawaye, lokaci
guda wasu suka biyo baya.
Muryarsa adashe yaci gaba, "haka inaji, ina gani, ba barci
nake ba, ya karishi wasan sa dani...!
Rabe na zuwa nan ya kuma fashewa da kuka, na matso
kusa dashi gami da dafashi, ina mai bashi hakuri.
Ya cigaba da bani lbr, "imam bani da mafita a wannan
lokaci, sabida a wannan lokaci idan nai wani yunkuri,
komai zai iya faruwa. Da gari yawaye har kusan 7 bai
tashi daga bacci ba, cikin sanda na hada na dau jakata,
gami da ficewa daga gidan, wani kuka ne, ya su6ucemin
lokacin da na tuna abinda wannan tsinannen bawan allah
yaimin.
Na dubi rabe gami da cewa "ba yaseen auwal din bane ba
kenan?
Ya dubeni cikin takaici, "haba imam yakake tambayar
abinda ka sani ? Kaima kasan kawai ya yaudareni ne ya
cuceni.
Nai tsam, dani dama tunda ya soma bani lbrn na gano
wannan mutumin 6atagari ne, baida nasaba da'yan
wasan hausa.
Inajin ka malam rabi'u nace dashi.
Ya cigaba "jiki na yana rawa, na gaggauta barin layin, sai
da na danyi nisa, na sami waje na zauna gami da soma
risgar kuka, hawaye nata kwarara a idanuwa na.
"malam tun dazu nazo wucewa, na tarar da kai kana ta
kuka lafiya ? Wani matashi da nake zaton zai kai 20
yaimin wannan tambaya.
Na dago da jajayen idanuwana, na kalleshi, koba komai
ina bukatar taima ko.
"dan allah ka fadamin damuwarka, musulmi dan uwan
musulmi ne, kuma daga gani kai bakone" yace dani cikin
sigar lallashi.

Nan take na juye masa lbr na, da duk wani abu da yafaru
dani.
Ya tausayamin sosai, sannan ya dora da cewar " wancan
gidan ba gidan mutanen arziki bane, an dade dama ana
zarginsu da naiman juna, allah ya kyauta. Idan bazaka
damu ba, kabiyoni muje wajen uwargijiyata, wata
matace mai saida abinci, nasan bazaka samu matsala ba,
inyaso kadan zauna na wani lokaci kafin ka ta samma
komawa gida, tunda kaga ga yanayin da ake ciki.
Nan nabi wannan bawan allah, ya tara mana adaidaita
muka nufi kasuwa, domin dama siyayya zaiyowa ogarsa.
Nikam duk da wannan bala'i da nagani, ina nan da kudiri
na na SAI NAGA RAHAMA SADAU.
A hanyarmu ta zuwa wurin abincin nasu, yake shaidamin
sunansa ali, asali shi almajiri ne, tun yana yaro ya 6ige da
yiwa wannan mata aiki. Acewarsa yunwa ce tasa shi
guduwa da makaranta, kuma an kawo shi tun yana
kankani ne, zuwa yanzu malamin nasu ya mace, shekaru
12 da suka gabata, kuma bai san garinsu ba, dan haka
uwani mai abinci itace uwarsa da ubansa, dan tai masa
abinda iyayen nasa basu masa ba. Acewar sa kenan.
"rabe zakaji dadin gurin mu, dan akwai wata kawata a
wajen, itama mayyar rahama sadauce, zuwa yanzu
sunanta ya tashi daga hanne ya koma SADAU, dan haka
zaka samu bayanai da dama awajenta. Alin keta koromin
wannan bayani, dai dai lokacin da adai daitan keta tsala
gudu, gaskiya wajen nasu da nisa na fada araina.
" alokuta da dama nakanji haushin, HANNE SADAU idan
naji ta fiye maganar wannan fitsararrar yarinya rahama.
Nai murmushi cikin zolaya nace, "ba'a zagin sadau a
wajena" yaduben cikin raha yace "SAI KAGA RAHAMA
SADAU"
murmushi kawai nayi.
Wurin abincin nasu wajen garine, rumface sai dakuna
langa langa, guda uku. Mai adai dai ta ya sauke mu, gami
da dire kayan har harabar wajen, gayyar doyace da
shinkafa gami da sauran tarkace.
Wata siririyar matashiya na gani, wanda ko kadan bata
more mayin bilicin ba, domin ita da taima 6ata mata
fuska yai, ta zama 2 kala. Tana zaune tana tsintar wake.
Ga iyayen tukwane guda uku a murhu.
Wata gajeriya mummuna, mai mici mici idanu, tafi to
daga cikin rumfar ta nufomu.
"shegen sama ka dawo ne? take fada dai lokacin da ta
karaso garemu.
"Eh wlh hajiya" aliyu ya bata amsa
"ina ka samo wannan dan shilan kuma ? Ko shima ya fito
ne ? Matar ta kuma tambayarsa.
wannan siririyar matashiyar dubo yadda muke aka ron
farko gami da watsamin harara....!
¤¤
page 4 is loading

¤
¤
journalist din kune.
SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Posts by SHURAIH 99%
Part 4
.
ali ya dubi uwani mai abinci gami da cewa "hajja rahama
sadau ya fito nema.
Hajja tai wata shu'umar dariya irin tasu, ta gogaggun 'yan
duniya tace "da haka muka soma, wai kuturu yaga mai
kyasbi. Ta dubeni na dan lokaci tace da aliyu "shegen kai
shi da kinka, in mun gama aiki, sai inzo in dora masa
karatu"
ali ya dubeni gami da cewa "muje ciki" na bishi a baya.
Har yanzu wannan siririya mai kama da kilaki tana
watsamin harara.
Wata macacciyar katifa ce a ya she, cikin dakin sai
tabarma guda daya gami da dan tarkace da ba'a rasaba.
"nan ne dakina, anan zamu zauna, har zuwa lokacin da
zakai gaba" shegen sama ko ince ali ke koromin wannan
bayani, bayan mun shige dakin langa langar madaidaici.
Na ajiye jakata gefe gami da tsayuwa ina karewa tsohon
langa langan idanu.
"Ka zauna mana, muryar ali ta katseni, zamanai a kan
tabarmar dake yashe.
Da karfi aka banko kofar cikin fusata, hajja ce tana huci,
ta malmalo ashariya "banason shirme shege, kazo kai
aiki, ka wani kule dakin dan uwarka, musamu mu
kammala, bayan kasan kwanan zancen. tafada tana zare
mici micin idanuwanta, bakinta har kumfa yake tsabar
masifa.
Shikam shegen sama, tun lokacin da ta soma sirfa masifa
jikinsa ke ta rawa. A gaggauce ya fice tabi bayansa.
Nai ajiyar zuciya gami da kwantawa kan katifar, sai
alokacin na tuna mahaifiyata gwoggo tani, alkah sarki
mace mai sanyi maras hayaniya, baki na ta6e gami da
runtse idanuwa, bacci yai awon gaba dani.
Bansan iya lokacin da na dauka ina bacci ba, na dai farka
naga wata madaidaiciyar kula a gabana da ruwan sha a
kofi.
Wata matashi wanda itama nake kyautata zaton
ma'aikaciyar hajjace, ta shiga ba tare da sallama ba. Sai
dai ga dukkan alamu tasan yadda ake bilicin tunda ita
kam yo kodar da ita, kamar yadda take bida, duk da
kasancewar ta kakkaura.
"hajja tace kaci abinci, ga ruwansha, zata zo kuy magana.
Tana gama fadin hakan ta nufi kofar ficewa, "dan allah
ina aliyu ? Na jefe ta da wannan tambayar "wai shegen
sama kake tambaya ? Ai ya tafi naiman arziki" matashiyar

tace dani, dai dai lokacin da ta isa bakin kofa ?
"naiman arziki ? Na tambayeta cikin mamaki
ta kalleni gami da yin wani shu'umin murmushi tace "kar
ka damu, zaka gane da zarar hajja tazo, ta dora maka
karatu" tana gama fadin hakan tai ficewarta.
Zulumi tare da juyayi suka ziyarci kwanyata, daga bisani
na bude abincin domin ina fada da "yar gusau {tofa
katsinawa} shinkafa jalofiya harda namanta tana kamshi.
Banyi wasa da abincin nan ba, haka na ringa sanya shi
acikina, sai da na koshi. Na kora da ruwa.
Na koma na kwanta, inajin hayaniyar mutane a wajen,
daga bisani hayaniyar ta dan ragu wajejen mangariba.
Hajjo ta shigo dakin wannan karon wani leshine ajikinta,
harda "yar kwalliyarta, sai dai abinda na fahimta ga hajjo
shine, ita muninta na musamman ne domin da tai
kwalliyar maimakon tai kyan gani, a'a sai kwalliyar ta fito
mata da asirin siririn kan da ke gareta.
Ta karaso ta zauna gefen katifar da nake daf dani, har
munajin numfashin juna.
Tai ajiyar zuciya gami da cewa, "ka saki jikin ka dan shila,
dama irin ku nake nema, kana da kyau ka godewa allah
tun daga nan ya baka jari. Abinci muke sai dawa kamar
yadda ka gani anan, a kallah munkai mu 13, duk a
karkashina suke, ciki kuwa harda mai mana gadin wajen
nan, sakamakon da daddare mukam fita naiman abin
rufawa juna asiri, kasan dai wannan abincin da muke
bazai kwashe mana duk bukatun mu ba, kasan rai da buri
muna son tara arziki.
Yanzu haka shegen sama {ali} hajiyarsa tazo ta daukeshi,
taimin balance idan ya kare kwanaki biyun zatai masa
nasa balance din, kayar da ka zauna damu, ka tara arziki,
ita da kanta RAHAMA SADAU zata nemeka. Yadda kake da
kyan nan, bazan saka a kasuwa ba, zan barwa kaina kai ni
zannayima ka balance din, a duk lokacin da kaimin aiki.
Hajja ju ta kworo wannan uban bayani gami da mikewa,
tai hanyar fita gami da cewa, zumu fita naiman arziki, sai
gobe zamu dawo sassafe, kafin nan kai shawara da
zuciyarka, duk da nasan bawanda yaki kudi.
Tana gama fadin hakan tai ficewarta ta barni a daskare...!
¤
¤
¤
part 5 is loading
¤
¤ina da group a facebook IMAM ABDULLAHI USMAN
HAUSA NOVELS GROUP za ku iya yin searching kuy
joying, domin kasan cewa da littafaina kala la. Bugu da
kari ina da page IMAM ABDULLAHI USMAN tanan zaku iya
kasancewa dani kai tsaye duk dai a facebook.
Ngd
¤
journalist din kune.

SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Posts by SHURAIH 99%
Part 5
.
nadade azaune ina daskare, duk abin duniya yabi ya
sheni, tabbas yau ina ganin ta kaina ya 6arawo a hannun
mata.
A haka har dare ya tsala, ina nan zaune, daga bisani na
mike tseye gami da ficewa daga dakin.
Babu kowa a harabar wajen, duk hayanir nan ta shude.
Ga uban duhu daya dabai baye wajen.
Kukan karnuka na tashi daga wani waje da bansan ko ina
ne ba.
"Bako ka fito kenan" aka ce dani da wata iriyar murya.
Na waiga kusurwar da najiyo muryar, zaune akan benci
yana rike da sigari yana karawa sama hazo. Duk da duhun
daren bai hanani ganin saba.
"haba dai kar dai tsoro kaji ? Nine megadin wajen nan.
Yace dani, dai dai lokacinda na nuna alamar tsoro.
Na karasa wajensa gami da zama akan bencin. Sai da
yagama zuke sigarin ya kashe wutar gami da
cewa,"Bawan allah, kai kuma wacce kaddarar ce ta jefoka
karkashin Hajjaju mai abun dadi ?
Kalaman nasa suka doki zuciyata na gyara zama, gami da
fuskantar sa nace "banda amsar tambayarka!
Yayi jim daga bisani yace "ga dai alamun ka kamar ba
ficacceba, bawan allah idan kasan kai ba tayar gaban keke
bane ka gaggauta nisantar wajen nan"
na jingina da jikin langa langa gami da cewa "meye kuma
tayar gaban keke ?
Mutumin da nake kyautata zaton zai kai shekaru 30 ya
sheke da dariya, gami da cewa, "kana nufin bakasan
wannan jaririn yaren ba ?
Na dirice na nuna masa kauyan cina a fili.
Shiko ya karkace yake ta shekamin jawabi, ban boye
masa maganganun da hajjaju ta fadamin ba, anan ya
warwaremin zare da abawa.
Ashe alin da ya kawoni nan din shima gogeggen dan
duniyane, fasikanci ba irin wanda ba yayi da sunan naima
arziki.
Ita kuwa hajjo karamin aikin ta shine karuwanci, acewar
sa takan dauko yara 'yan sha 17,18 zuwa 20 tana lalata
dasu, abar batun sauran matan dake gabanta wadanda
sukan idan kaso musu adalci shine ka kirasu da karuwai.
"kaga bawan allah idan dai kasan kai ba na banza bane,
yan zun nan ka dauko jakar ka, in nuna maka hanya, wlh
banda yau hajiya tayi kamu ba, da i yanzu kuna chan tana
fadama mecece duniyar."
mai gadin ya karkare surutansa da bani wannan
shawarar.

Cikin mintuna 2 naje na dauko jakata, naiwa dakin kallon
karshe, na nufo wajensa.
Mikewa yai gami da haska fitilar da ke hannunsa yace
muje zuwa.
Yai min rakiya mai nisa, daga bisani muka soma hangowa
hasken gari, yaja tun ga ya tsaya, ya sanya hannu a aljihu
gami mikomin kudi yace "gashi dubu biyu ce, nasan zata
isheka komawa garinku, bawan allah ka koma ga
iyayenka ka naimi gafararsu karabu da batun wata 'yar
wasan hausa."
na kar6a gami da yi masa godiya, mukai bankwana, na
kutsa kai birnin kano.
Abakin titi na kwana, washe gari na shiga tambayar ina
zanga RAHAMA SADAU ?, kai gaskiya ranar naga wulakanci
da yawa, wasu mahaukaci suka daukeni.
Sai daga karshe wani yake sanar dani cewa rahaman 'yar
kuduna ce, dan haka kadunan zan nufu, a cewarsa ba
abun da ke kawota kano face aiki.
Nai masa godiya gami da daura aniyar tafiya kaduna.
Tuni na samu mota, duk da dare ya soma yi, motarmu ta
wulwula hanyar kaduna.
Naga saurin isarmu, direba ya watsar da mu a tasha
nasoma naiman hawajen kwana domin na kudurta
araina cewar gobe SAI NAGA RAHAMA SADAU.
Tunda gani a kd
arumfar wani maishayi naji wasu matasa suna maganar
shahararre wajen kwalliyar mata da rahama sadau ta
6ude.
Faduwa tazo dai dai da zama kenan, tabbas idan naje
shagonta nasan samunta abune mai sauki.
Nai murmushin nasara gami da ajiyar zuciya.........!
¤¤

.
.
Last page is loading

.
¤
journalist din kune.
SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Posts by SHURAIH 99%
Part 6
KARSHE
.
A bakin titi na kwana, aranar, washe gari kuwa, naci gaba
da sana'ata. Wato tambaya, sai dai tambayar ta yau ta
bambamta da wacce nake a baya. Tunda da tambaya
nake ina zanga RAHAMA SADAU ? Yan zu kuwa kai tsaye,
nake tambayar jama'a dan allah inane SADAU BEAUTY ?

Hakan ma na jima ina tambaya bansamu kwakkwarar
amsa ba, kai kace ba'a kadunan nake ba.
Cikin tambaye tambayen nawa ne, na tambayi wata
matashi "yar kwalisa. Kai da ganinta kaga "yar swag.
Gaskiya imam nayi mamakin saukin kanta, dan cewa tai
dani "gaskiya shagon ba'a unguwar nan yake ba, sai dai
kuma yanzu hakama chan zani. Idan ba damuwa muje in
sau keka sai na nu na maka wajen.
Cikin azar6a6i na amince, sai dai nayi mamakin nisan
wajen, sai da mukaje kusa da wajen wurin sannan ta
nunamin shagon gami da ajiyeni. Gadiya nai. Ta karamin
jawabi da cewar kaga yau asabat tana nan ma, insha
allahu zaka sameta.
Bakina cike da azar6a6i na nufi hanya domin tsallakawa
nai arba da rahama sadau. Imam naga kaddara ko ince
alhakin iyayena dana taho na baro. Na dubi rabe gami da
cewa mai yafaru ? Rabe ya gyara zama gami da cewa "ai
mota ce taimin diban karan mahaukaciya daga nan
bansan inda nake ba"
sai budan idanu nai na ganni a garin mu, cikin gidanmu.
Na dubi rabe cikin rashin yarda nace kamar yaya ?
Yace "cikin hikimar ubangiji ashe lokacin da lamarin ya
faru akwai idon sani wato dan garinmu, shi yaiwa na allah
jagora suka dawo dani har gida.
Na roki gafarar iyayena. Nai zaman jinyar karayar da nai
a hannu da kafa.
Bayan nasamu saukine na soma daukar karatun addini
awajen wani malami. Imam a yanzu nayiwa kaina
karatun ta nutsu, ina zaune zaman mutumci da iyaye.
Kaji lbrn da nake dauke dashi.
Rabe yace dani.
Nai jigum ina nazarin wannan labari.
**
Alhamdullah
**
karshe
**
ngd fans
**
Imam Abdullahi Usman


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment