Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Camerou da England
kuwa"
"Shakka babu , na kauracewa halartar kowanne
kallon wasa,don matukar tsoron haduwa da farida"
Ya dan kalli fuskata ,kallon dana so nasan abin da
yake nufi.
"Ba mamaki kaima kuhadu da ita acan"
Nafada ina kallon fuskarsa,bai yi magana ba amma
yanayin fuskarsa na nufin shakka babu da mamaki.
Shuraih Usman
A daidai wannan lokaci sai zuciyata takara kadawa
sabida ganin meenat sanye da atamfa,riga da zani
ruwan madara,ta nufo in da muke .
A wannnan lokaci dana ganta sai dana tsorata ,a
tunanina farida ce ta rikida takoma karama ,domin
idan ka san farida,kana ganin meenat ka ga kanwar
farida.
Ta na zuwa ta rakabu da jikin nasir,tana kallon
fuskata.
"Habib ! Ko zan sami kasa-kasan fim din hausa a
wajenka?" Nasir ya bukata.
"Shakka babu,amma sai dai a gida ,idan kanaso zamu
iya zuwa"
Dani dashi da meenat muka nufi Gandun Albasa.
"Habib mama ta gayamin wai a kamfanin jaridar
dankari kake aiki"
"Shakka babu"
"A jaridar ne ake buga labarin BABBAR MAGANA ko ?
Agaskiya akwai matukar rikitarwa ,da jefa mutane
cikin rudani,kuma kagaya yi daidai da abin dake
faruwa akanka "
"Shakka babu ,maganarka ba musu"
Nafada lokacin dana shigar da motar haraban gidan
ahmad.
"To mene ne dalilin dayasa kai baza ka buga wanda
yanzu yake faruwa akanka ba ?"
Nasir yafada lokacin da muka fito daga motar.
Shuraih Usman
"Saboda babu wanda zai yarda da ni"
"BABBAR MAGANA ma da farko mene ne jama'a
basu fada akansa ba "
Har sai lokacin da aka karanta karshen labarin"
Bayan munci abinci saina bashi MUNKAR da
TSUNTSU MAI WAYO da kuma SAI DAI MUTUWA.
"Baka da NAIRA DA KWABO?' Yabukata
"Wallahi bani da shi nasir ,sai dai nahada ma da
littafin SAI DAI MUTUWA da kuma WUYA BA TA KISA"
Fatima na ganin meenat tace kanwar faridace,haka
ma faruk(BBJJ) da bala Barde,muna fitowa zamu tafi
suka ce meenat kanwar faridace .
Abokaina ne kuma sunga hotonta a wajena .
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 14
By♥ Shuraih Usman
Abin mamaki da rikitarwa ya farune adaidai KANO
LINE a kan hanyarmu ta komawa tarauni don kaisu
nasir gida.
Kwata-kwata nasha'afa babu wadataccen mai amotar
,kawai sai ga ni nayi malejin mai nayin nuni cewar
mai yakare ,yayin da motar ta tsaya .
A lokacin karfe biyu da rabi,ina sauri na kai su nasir
gida don ganin wasn England da yake da niyyar zuwa.
Sanin cewar akwai 'yan cuwa-cuwa a diga ,sai muka
nufi can don sayowa ,nasir rike da hannun meenat.
"NASIR ! NASIR !! KAGA ! KAGA !!
Arazane meenat ta rinka fada ,tana nuna wata mota
kirar volvo da mata biyu keciki.
""FARIDA ! FARIDAAAAAA......"
Shima Nasir arazane ya rinka fada ,idanuwansa sun
zazzaro ,farida ce ke tuka motar,kodaddiyar matar
agefenta kuma titin sabo bakin zuwo suka nufa ,inda
muma zamu.
Lokacin danayi kokarin duba lambar
motar,zundumemiyar harafin "L" ne a makale.
Shakka babu meenat da nasir sunyi matukar razanar
da tunda suka shaki iskar duniya basu taba razana
fiye da haka ba.
Shuraih Usman
Cikin gaggawa jikina na rawa ,na tsayar da wata taksi
babu kowa aciki .
Don kada ya bata mana lokaci nazaro damin kudi na
bashi, na nuna masa motar ta fara nisa ,nace duk
inda tayi yabita .
Na saka meenat wadda duk ta fice daga hayyacinta a
motar ,sannan shima nasir afirgice na kama
hannunsa muka shiga motar.
Cikin zumudin da na ba shi ,direban ya zaburi motar
cikin matsanancin gudu.
A daidai lokacin da muka isa garesu ,sai motar ta
shiga matan fada road,kuma adaidai lokacin danja ta
tsayar da mu.
Cikin matsananciyar gaggawa direban ya kutsa kan
motarsa, GARAM!!!
Yakade wani dan acaba da zai gifta ,dana duba
motarsu farida sun bace.
"Shit!" Na fada lokacin dana daki kan motar.
A ranar kallon wasan da nasir bayyiba kenan sai da
aka masu allurar bacci sannan suka sami nutsuwa.
(Lol sun karyata sun ga zahiri)
Duk da ina kara razane,sai son farida yadada karuwa
a zuciyata .shakka babu ina matukar sonta.
Shuraih Usman
H
JUMA'A
9 ~ 3~ '99
Juma'a babbar rana , wannan juma'ar shakka babu
,koda wani bata zama babbar rana agareshi ba ,a
wajen Al'ummar kasar Nigar babbace .
Domin da sanyin safiyar juma'arne ,shugaban
kasarsu BA'ARE MAINASARA, ya koma ga
mahaliccinsa .
Sakamakon ruwan harsashi daya fuskanta daga
jami'an tsaronsa.
Fantsamuwar labarin a duniya keda wuya ,Ahmad
yaga muma yadace musamawa jaridar DANKARI
kanun labaran tun da dumiminsa.
An katse gidajen rediyo,an hana jirage tashi a kasar
Nijar, wanda hakan na nufin dole muyi amfani da
mota idan muna bukatar shiga kasar.
Kada ka dauka mun samu shiga kasar cikin
sauki,bayan nune-nunen shaidar cewar mu
ma'aikatan jarida ne ,saida wasu kudade daga
aljihunmu sukayi balaguro zuwa ga aljihun masu
tsaron boda.
Shuraih Usman
Bayan munyi yanzirga zirga nan da can ,mun kalato
abin da muka dawo kasar Nigeria .
Duk da cewar Ahmad yayi tukin motar , jikina ya
samu wadatacciyar gajiya .
Karfe hudu da mintuna takwas,muna cikin birnin
dabo a wannan lokaci rana tafara sanyi sai dai babu
wani alamar sanyi a zuciyata da kwalkwalwata .
Har muka je Nijar muka dawo,zuciyata taf take da
tunanin farida ,da kuma tunanin halin da meenat da
nasir suka shiga .
A wani bangaren zuciyata na so faruwar hakan
saboda shakka babu Nasir,da meenat da kuma
mahifiyansu za su fi gaskata al'amarin,domin gani ya
kori ji.
Bayan nayi sallah naci abinci wanka yabiyo baya
bansan lokacin dana zurfafa a zuzzurfan kogin bacci
ba .
Ba don fatima ta tasheni ba, daban san lokacin
farkawata ba .
Saboda wadataccen baccin danasamu darana ,da
daddare sai barci yayi hijira daga idanuwana.
Karfe tara daidai naji ina matukar sha'awar fita
yawan shakatawa,SULJAM PALACE shine wajen da kai
tsaye yayi ungulu a zuciyata.
Shuraih Usman
Sai dai da nasan akwai mummunan al'amarin da zai
sake faruwa akaina dana hakura .
Sai bayan dana samu wasu lokuta zaune wajen su
nasir ,don ganin halin da suke ciki.
Ina fitowa da niyyar tafiya tarauni ,sai ma'aikacin
wajen ya zaburo a guje yagaya min wai wasu mata na
kirana a ciki.
"Wasu mata?"
Na rinka maimaitawa har lokacin dayanuna min inda
suke zaune .
Sannu a hankali zuciyata na mamakin kiran na karasa
inda suke.
"Wa nake gani kamar habib ?"Daya daga cikin mata
uku dake wajen ta tambaya.
"Idan dai ba wanine yayi kamama dani ba ina ganin
shakka babu nine "na fada lokacin dana fahimci
raqeebah da saratu da kuma jameelah ne
,dukkaninsu 'yan unguwarmu ne .
"Dama kana zuwa irin wadannan wuraren?"
Saratu ta bukata ,lokacin data kurbi tataccen lemu.
"Ku yakamata nayi wa wannan tambayar " nafada.
Lokacin dana zauna kusa da su raqeebah.
Shuraih Usman
"Saboda me kafadi haka ?"
"Saboda da namiji yana da yancin irin wadannan
wuraren musamman ga irinmu marasa aure ,amma
ga mace ziyartar gidajen kawayenta zaifi mata
martaba akan irin wadannan wuraren"
"Kiji son kai" jamila tafada .
"Wato ku maza ku zo ku nemi mata koh? Mukuma
mata mutafi gidajen kawayenmu?kana nufin kenan
mu muje muyi soyayya atsakaninmu ko? To waye
baya son hutu ! Koda dutse aka halicci mata ?"(Kujifa
yan'uwa)
Dukkaninsu sai suka kyalkyale da dariya .
" Baki fahimci abin danake nufi ba ,ina nufin kamar
yadda yake al'ada ,idan har akaga namiji a irin
wadannan wuraren,kawai ana daukarsa mai neman
matan banza.
Koda kuwa ba hakan ne ya kawoshi ba .to ina ga
mace ?da zarar an ganta cewa za'ayi 'yar harkace
ma'ana mazinaciya ce"
Shuraih Usman
Wannan hirarce ta jawo mana musun da ya sha'afar
dani harsai dana fahimci daya da rabi na dare
,sannan hankalina ya tashi ,banzo da abin hawaba .
Nafito cikin hanzari ina tunananin komawa gida ,sai
motar da muka gansu jiya aciki VOLVO,haryanzu
zundumemyar harafin "L" din na makale ,suka gifta ta
daya bangaren titin.
"Farida !"A kidime na kwala mata kira ,sai dana kirata
na fahimci gaba dayan gilasan motar arufe suke ,ina
rufe bakina sai dan-acaba ya bayyana .
Kamar yadda nayi wadan taksi,shima sai naba shi
kudi ban san nawa bane , na sanar dashi yabi
dukinda motar tayi.
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 15
By♥ Shuraih Usman
Hikimar yin hakan zaka ga kasamu biyan bukata da
wuri ,don kada a bata lokaci wajen tsadancewa
,sannan idan da zargi a zukatansu,kudin zaiyi saurin
fatattakarsa.
Ratar dake tsakaninmu bata da yawa sosai
,kasancewar babur dinsa Yana da ingancin inji
,sannan Kuma farida ba gudu take sosai ba.
Babu abinda yayi saurin bani mamaki ,irin yadda na
gane su farida nan da nan.
Suna zuwa wajen wasu yansanda dake tsattsaye kan
titi ,mummunar matar ta mika musu kudi ,suka Kuma
kyale su suka wuce.
Don gudun kada muma su batamana lokaci ,tun kafin
mu karasa na zaro kudi ,muna zuwa wajensu na mika
musu muma suka kyale mu muka wuce.
Haka muka yitayi,duk yansandan da msuka taremu
sai mun basu kudi ,
Har sai da motar su farida ta shiga harabar VILLA
GUEST INN .
Kai tsaye na umarci dan-acaban, shima ya shiga ciki.
Cikin sauri Dan acaban yafice daga wajen bayan na
sauka ,don gudun kada nabukaci ,wasu daga kudin
Dana bashi.
Sai da mummunar matar ta fito daga motar ,sannan
na fahimci a matukar buge take .
Ganin yadda take tangadi, har sai da farida ta rika
taimakamata.
Suna shiga reception din, ma'aikacin wajen ya mika
wa farida makulli ,wanda na nufin makullin dakin da
suke ne.
Nayi sauri na zaro kudi daga aljihuna ,nanufi inda
yake.
Shuraih Usman
"wannan kyakyawar yarinyar nakeso ,Kuma na tsara
ta yarda ,Amma wannan matar da suke tare ta kawo
mana cikas .lambar dakinsu zaka gaya min"
Nafada lokacin Dana mika masa kudin .
Kafin na san me yayi tuni ya rarume kudin daga
hannuna ,kamar yadda kadangare ke yiwa kuda
cafkar bazata .
"No. 11, dakin dake fuskantar yamma ,daga hannun
damanka "
Ga mamakisa sai yaga na fice daga wajen ,har na fito
Yana lekena .nasamu dogon lokaci ina tsaye ina
tunani.
"shin menene hadin farida da wannnan mummunar
mata ?
Nasir yabani tabbacin basu da wata yar'uwa datayi
kama da wannan matar ,kai kanta kallo daya zaka yi
wa matar kasan babu abin da ya hada ta da farida .
Ganin farida danakeyi kullum Akano ya tabbatarmin
suna Kano .
Abin tambayar shine ,shin akwai wajen dasuke zaune
musamman ? Kokuwa tun farko anan Villa guest inn
din suke ? Wannnan tamabayar ma'aikacin yadace
nayiwa.
Banyi mamaki Dana tambayeshi yace yaune zuwansu
na farko ba .
Kuma sannan kudin kwana daya kawai suka biya ba.
Motocin dasuke shiga ina suke samunsu ?farida ta
mutu, Kuma kullun suna tare da wannan matar.
shakka babu akwai wani kullallen al'amari tattare da
matar nan .domin kana ganin matar ,kasan ba
mutuniyar kirki bace ,yanzuma ba acikin Maye
nagantaba?
Shuraih Usman
Kuma kana ganin farida kasan bata yi kama da
mutuniyar banzaba .
Wani bangare na zuciyata ya shawarceni da kai tsaye
na wuce wajen yansanda na sanar dasu cewar ,ina
zargin wannan matar da sace farida .
Tun da iyayenta da kannenta na Kano .
Kuma zasu gane yarsu ,tunda dama sunganta sun
ganeta ,shiken sai azo acafke matar .
Daga nan Sai a sani shin faridar data mutuce
kokuwa ?
Wani bangare na zuciyata ya bijirewa wannan
shawara da cewa na fara sanar da mahaifiyarta .
Mu zo mu kama .
Sai mu tuntubi hukuma .
Kuma da wannan shawarar na yarda , nayi ta jiran
Dan-acaba .
Har sai Dana fitar da rai da samu
Shuraih Usman
A daidai lokacin da tsinken agogona ya tsaya akan
biyu da minti dudun dare ,saina hangi hasken fitila na
nufo ni, sai daya kusa zuwa na fahimci babur ne .
Babu Irin daga masa hannun da banyiba ,don ya
tsaya ammma ko alamar tsayawa bai yi ba .
Inda Allah ya taimakeni sai a she sabi'u ne da muke
kira [lastman].
A wajensa ne muke sayen katin duk wani wasan
kwallon kafar da ake gudanarwa indai anan Kano ne.
"lastman!lastman!! Na rinka zunduma masa kira har
sai da jiyo sannan ya Dan tsaya .
Abin daya sana tsayar da shi ,na sani sani sokoto
road yake , tun dani tarauni zanje sai na yi farincikin
hakan .
Komai dare komai dare nayi niyyar sanar da
mahaifiyar farida inda farida take .
Don gudun kada na tafi gida kaddara tasa na makara
,kafin naje tarauni su Kuma su kama gabansu
"Dan Allah wasu muhimman takardu ne na manta su
a tarauni ,Kuma a Daren nan ake bukatarsu ,ka
taimaka ka ajiye ni a nan sokoto road din sai na
karasa"
Na yi masa karyane don gudun kada ya cikani ta
tambayoyin me zan je yi atarauni?bayan ya san
unguwarmu .
Shuraih Usman
'bawani abu hau mu je "
Yafada kafin yarufe bakinsa na dare Vespa din,
Saboda ,matukar kaguwa Dana yi ,na ganni a tarauni.
Har muka zo sokoto road bamu sokoto road bamau
hadu da yansanda ko daya ba .
"tarauni wajen ina zaka ?"ya tambayeni.
"kasaukeni anan na karasa"
Ba wani abu na karasa dakai "
"masallacin juma'a na tarauni zani" nafada.
ya ajiyeni adaidai masallacin sannnan ya juya .
"nagode " nafada .
"bawani abu ,Allah ya bamu alkhairi."
Banda haushin karnuka da ke tasowa nan da can ,
babu wani sauran motsi da kunnena ke iya ji .
Dayake na gane hanyar da muka bi jiya da sulaiman
,sai na bi har kofar gidan .
Koda irin 'yan tauran dake yawon dare , ban gani a
layinba ,kowa ya garkame kofar gidansa,kamar har
abada bazasu kara budewa ba .
Nayi ta faman kwankwasa kofar gidan har na gaji ,in
da kasan kofar makabarta nake kwankwasawa, babu
wani motsi da ya biyo baya .ganin haka sai na hakura
,da niyyae zuwa bakin titi na samu babur na koma
gida, nayi matukar kokari na dawo da asubah.
Ina zuwa daidai masallacin juma'a .sai wata bakar
Peugeout ta tsaya a gabana ,tun kafin su fito na
fahimci.........................................
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 16
By♥ Shuraih Usman
Ina zuwa daidai masallacin juma'a .sai wata bakar
Peugeout ta tsaya a gabana ,tun kafin su fito na
fahimci ,yansanda ne ,Kuma nayi matukar bakin cikin
manta I.D. CARD dina a gida .
Subiyu ne a motar , mai kakin 'yansanda ajikinsa
shine ke tuka motar ,fari kakkaura mai gashin baki .
Nakusa da shi Kuma baki kakkaura Mara gashin
baki,sanye da fararen kaya.
"hey !daga ina ! Zaka ina a wannan tsohon Daren?"
Kafin na amsa masa tambayoyin da yayi min, bakin
ya fito ya cafi kuguna .
"shegiya ! Barawo ,sata zata " yafada lokacin da yake
kokarin turani motar .
"officer" nafada ,ina son yimusu bayani.
"close your goddam mouth" bakin yakara zunduma
min tsawa a sukwane ,lokacin Dana shiga motar .
"in banda barawo , me mutum yake a waje har yanzu
bai kwanta ba ? "
Dansandan mai kaki ya fada , wanda sai daga baya na
fahimci ashe D.P.O ne .
Shuraih Usman
Ni dai bance musu komai BA ,kawai ni dai abin daya
dameni, kada su farida su kubuce min .
Yanzu idan aka kulle ni kafin mana fiti kawai su farida
sun min adabo.
Kai tsaye D.P.O ya nufi kasuwar tarauni kamar akwai
abinda yake nema ,ya zazzagaya kasuwar , sannan ya
tuka muka hau titin maiduguri, kana ahankali ya
gangara da motar muka shiga layin farko na kusa da
lambun tarauni.
Ya tsayar da Motar a daidai shagon wani gida ,da
wani saurayi sanye da gajeren wando ke shan sigari.
D.P.O na fitowa saurayin na fahimta dan sandane .YIP
" yafada shagon a tsorace tamkar wanda yaga
mutuwarsa .
D.P.On bai tsaya bata lokaci BA yabi bayansa, yayin
da dayan ya fito daga motar ya tsaya Yana gadina .
Babu yadda D.P.On bai yiba don Yafito da saurayin
Amma abin ya faskara .
Sai ya fito bakin kofa ya umarci dayan ya shiga ya fito
da shi.
Shuraih Usman
Bayan ya shiga , sainaga kwata-kwata hankalin D.P.On
ya tattara akan shagon, sakamakon bololon da
saurayin keyi.
"baba! jamilu ! Wayyo niba barawo bane "
Kai idan kaji burarin dayake cikin tsakar dare ,sai ka
zata ana kai shi harbe shi za'ayi.
Sannan a hankali jikina na rawa ,
Na bude motar na rufa aguje kamar zantashi Sama .
Na sami dogon lokaci ina gudu , sannan na hango
hasken fitilar motar na haske min gaba . Nayi
matukar gajiya , zuciyata kamar ta faso kirjina ta fado
,sannan tsabar haki yariga ya gama da ni ,Kuma
nasan idan har suka kama ni hukuncina sai yafi da
tsananta .
Saboda babu abin da 'yansanda suka tsana irin su
kamaka ka Kuma gudu.
Da kyar na sha wata kwana kamar zan kife , ina shiga
kwanar dabara tazo min nashiga cikin wani katon
tanki dake ajiye kofar wani gida .
Sai Dana shiga na fahimci shara ake zubawa a cikin .
Sun dade suna zazzagaya unguwar don nemana ,ni
kuwa ina cikin tankin gabana na dakan sittin sittin ,
hankalinsu bai zo gareni Ba.
Sai dana tabbatar babu wani sauran motsi dA
kunnena ke iya ji, sannan jikina manne da shara na
fito, gabana na faduwa .
Na fara 'yar tafiya kenan ban yi tunanin ,shin yanzu
takamaiman ina. Zani ba , sai na kara hango hasken
mota na nufo inda nake banyi tunanin kara komawa
cikin tankin dana fito ba ,na kara rufawa aguje .
Ina dada gudu gunjin motar na kara kusantoni,har
sai lokacin dana zo.
titin makarantar sekamdiren tarauni.
Sai da motar ta gifta ni, sannan na fahimci honda,ce
kuma wani mutum ne shi kadai a ciki.
Duk da haka ban tsaya ba sai lokacin dana kai daidai
gindin gawo ,ina kokarin tsayawa sai nayi tintiben
daya wuntsilar dani har kasa.
Shakka babu, naji matukar zafin buguwar da kaina
yayi.
Kamar ajiyeta aka yi a gabana ,sai ganin motar,sai
ganin motar nayi ta tsaya , har 'yansanda hudu sun
fito daga motar kowannen su rike da bindigarsa
ahannunsa.
Ka-ka-ka-Kaf! Karaf !"
Shuraih Usman
Naji bindigogin sunyi shirin yin ta'addanci,sannan
suka cuccuna minsu akaina da bayana .
Da kyar na dago kaina motar ,zuciyata takasa tuna
komai saboda tsoro.
Inter-state-Anti-crime-patrol.
Abin dake rubuce kenan ajikin motar, can. Sai naji
wata murya kaman na taba jinta tace.
"Don't move ,you are under arrest"
Babu yadda zanyi kawai sai narufe idanuwana ,jikina
kamar ba laka na koma na kwanta ,shakka babu na
kamu.
'Ka daka aiwatar da wani yunkuri da zai iya kai ka ga
halaka ,ko kuma ya cutar da rayuwarka "
Na tuno da gargadin da mahaifiyata tayi min.
Anan muka kawo karshen Book 1
sai kun jini a book 2 mai taken
MUN-JI-MUN-GANI
Authour: Maje~el~hajeej Hotoro ( ya hajeej)
Written: Shuraih 99%
Shekarar bugu : 1999
Post by: Shuraih 99%

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment