Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

al'umma sun
ganshi sai su rude , su razana suna fadin fatalwar
wane ta fito.
Shuraih Usman
Ko kuma idan mutum yana hulda. Dasu,kuma jama'a
sun san hakan kuma ya mutu,sai shi masu rikida da
siffarsa,su rinka razana wadanda suka sanshi.
Ubangiji yayiwa aljanu baiwar rikida daga wata siffar
kuma su wadan su irin halittu na da burinsu kawai su
cutar da mutane ,su kuma jefa su cikin rudani.
Sai dai abin dubawa shine ,babu yadda za'ayi aljani
idan ya rikida a siffar mutum,ya bayyana da
cikakkiyar kama ba tare da ansami tawayaba .dole ne
idan suka rikida kasamu wani bangare jikinsu,baiyi
dai dai da na mutane ba ,komai kyan siffar da suka
bayyana.
Wasu idan suka fito a siffar mutane zaka samu
idanunsu na mage ne,ko kura ko kuma sauran
namun daji ,ko kuma ka ga kafafuwansu irin na
doki,ko daya tafi daya girma da dai sauransu.
Amma mafi yawancin sunfi rikida amunanan siffofi.
Kamar mummunan tsohon dake cikin matsanancin
talauci,ko kuma siffar halittun tsoro. Shuraih Usman
Nayi shiru ina fargaba da mamakin,rikirkitaccen
al'amarin daya faru akaina,wanda da wani ne
yafadamin ba mamaki zuciyata takasa gaskatawa.
To amma ni ai banga wasu kamanni jikin
farida,wadanda ba su dace dana mutane ba sai dai
matar dake tare da ita,wacce kwata-kwata na tsani na
tuna kamanninta a zuciyata.
"Fatima! Wani abune ya girgiza rayuwata"
Kamar wani abu kenan"cikin doki ta bukata .
'Jiya ne bayan antashi daga wasan Nejeria da costrica
a Lagos ,sai muka hadu da yarinyar dake jikin hoton
dake hannunki.
Mun yi hira da ita ta fadamin sunanta, da kwatancen
gidansu a kaduna ,nakuma bata zoben nan dakika
bani yau bayan antashi daga wasa naje gidansu
kamar yadda ta kwatan tamin.
Ina ganin kamwarta da babarta ,naga kamarsu
daya,ba wani bambanci, dana nemi akirawo min ita
sai suka tabbatar min shekarunta uku da mutuwa.
Da farko ban yarda ba sai da suka gamsar dani da
hujjoji.
Lokacin da aka kaini kabarinta ,sai na ga zoben dana
bata akan kabarin.
Wannan hoton da kike gani cikin kundin hotunanta na
dauko.
To waishin wannan da me ya yi kama?
Kuma na duba jikinta tsaf,babu abin da bai yi kama
dana mutane ba.
A takaice ma har taba jikinta nayi"
Ta kurawa hoton ido wasu lokuta,ta dawo da
hankalinta kan zoben dake hannuna,sannan ta zurfafa
atunani.
Shuraih Usman
"Shakka babu ,wannan al'amari ne babba ,kuma da
aljana ce ina ganin ba zata fito cikin taron jama'a ba .
Koda yake to idan ba aljana ba ce ,yaya mutum zai
mutu shekaru uku kuma aganshi a wani waje daban?
Gaskiya al'amarin da rikitarwa"
A dai dai wannan lokci sai Ahmad doga dan baki
kakkaura fari kyakkaywa sanye da farin boyel
doguwar riga da wandonta .
Bayan fatima ta cire masa takalmin kafarsa ,ta
kwance masa agogonsa,ta sumbaci fuskarsa,sai ta
harhada tawagar abincinsu akan tebur.
Ko da yaushe tare suke cin abinci.
Shi kansa daya samu labarin al'amarin ya girgiza shi.
"Wannan sai yayi dai da labarin *_SHAKKA-BABU_*"
A gaskiya al'amarin kunshe yake da riktarwa.
Ahmad yafada.
Kwarai kuwa abinday faru akaina yaso yayi dai de da
labarin BABBAR MAGANA.
Har fatima da ahmad suka gama cin abinci suka shiga
harkokinsu,ina zaune zuciyata makil da tunani
,al'amarin sai faman kai kawo yake cikin
kwalkwalwata .idan na kalli hoton Farida sai naga
kamar moysi take yi, don gudun kada na zautu ,sai
najuya bayan hoton.rubutu ne dara-dara ajikin hoton
REST IN PEACE.
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 8
By Shuraih Usman
D
5~3~'99
*_ LITTININ_*
Shakka babu , al'ummar kano na matukar kishin yan
kwallon kafar england.
Zuciyarka zata iya gamsuwa da hakan idan ka halarci
wasan da aka buga tsakanin AMERIC da ENGLAND,a
dakin wasa na *_GENERAL SANI ABACHA_*,daka
kofar mata .
Wajen yadinke da dimbin al'umma bakamar lokacin
da aka buga wasa tsakanin camerou da japan ba .
Shakka babu dakin wasan ya yi haduwar ,da ba za a
kushewa wadanda suka yi aikin ba .
Har aka gudanar da wasan farko babu cikakkiyar
nutsuwa,a zuciyata da ruhina da kuma kwalkwalwata .
Idan har farida aljana ce mene ne dalilin yin kuka
,har da zubar da hawaye ?
Mene ne baiyi kama da halittan mutum ajikin
taba?.....
Bana mu'amala da da namiji"
Me wannan kenufi ?
Nasan baza yarda da abin dana fada ba ...... Ni kaina
ba'ason raina hakan ya kasance ba "
"Sai dai babu yadda zanyi"
Shin wadannan zantuttuka ke nufi ?
Shin farida mutumce ?
Idan mutum ce yaya ta mutu ta dawo?
Nayi iya bakin kokarina don samawa wadannan
tambayoyi amsoahinsu,yayin da kwalkwata da kuma
tunanina .
suka gaza don samar da amsa tambayoyin.
Da har yanzu dada rikitar da rayuwata sukeyi.
Shakka babu na hadu da farida ,nayi hira da ita
,wannan ba mafarki bane $
To kuma na samu gamsassun hujjoji kuma kwarara
cewar farida dana gamu da ita shakka babu ta mutu.
To mene ne wannan?
Wanne suna ta dace aradawa al'amarin?
Wannan suma tambayoyine ma bukata amsar dazat
gamsar da tunani.
Shuraih Usman
Da ga ranar dana hadu da'ita izuwa yanzu ,idan
kasanni kallo daya zakayiwa fuskata ka tabbatar
shakka babu rama ta ziyarceni.
Saboda tsagwaron kaduwa da rudewa ,da tunani da
hankalina suka yi,wanda hakan ya haifarwa da
kwalkwalwata nutson bazata cikin rudu da
matsananciyar birkita.
Duk don faruwar birkidadden al'amarina.
Shakka babu dolene tunanina ya zurfafa ,rayuwata ta
girgiza,hankalina ya galaibaita .
Ka gamu da mace jiya kuyihira ido da ido,kabata abu
ta karba ,ka tambayeta ,ta baka amsa ,karewa ka
tabata ,sannan kana daya kacal da haduewar ka daita
ka samu tabbacin mutuwarta ,shekaru uku da suka
gabata.
"Shin wace mummunar matar dake tare da farida"
Mene ne hadinta farida?
Mene ne dalilin da yasa take takurawarayuwarata ."
Shuraih Usman
Babu abin dana fiso a rayuwata irin hora da
namiji,sai dai bani da wannan damar arayuwata
"banda maganganun da mukayi da farida ,kwata
kwatakwalkwawata ba ta tuna wasu muhimman
al'amura . Shuraih Usman
Kwatsam! Sai naji farida ta a zuciyata.
Babu abindayafi ban mamaki irin tun dana ganta
,sonta ke dada ruruwa a rayuwata .
Maimakon idan tunanin matacciya nakeso,sai ya
ziyarci zuciyata na kori son,sai son yakara bunkasa.
Kiri kiri,ina ganin ana shiga dakin wasan,yadda za'a
fafata tsakanin England da USA,kuma ni kaina ina
matukar ra'ayin wasan ,na hakura natsaya a waje
,kuma nakasa tafiua ko ina ,idan ka ganni tsaye ko
tunanin gajiya banayi,na kurawa dakin wasan ido ,sai
ka dauka so nake nashiga bani da kudin shiga .
Shine na kasa daurewa na tafi , nake kallon masu
damar shiga.na shiga ,nikuma ina kallon takaicin
babu yadda zan yi.
Sai dai da ace wani zaizo inda nake ,zai san na zurfafa
a tangamemen tekun zunzururutun zuzzurfan tunani.
Da ace nasan awajen wani al'amari zai kara
faruwa,har ya girgiza rayuwata,fiye da yadda na
tunzura jiya da yau ,da ban tsaya tsimayin faruwar
tsorataccen al'amarin ba.
Amma ina gama ya gama ,uba yayiwa yarsa ciki.
Al'amarin yariga. Ya faru.
Tun lokacin da na zari hoton farida ,har zuwa wannan
lokaci,duk lokacin dana kura mata ido, ina mai maita
tambayoyin da amsarsu bazata samu awajena ba,ina
dago kaina sai naji zuciyata ta yi tsayawan wucin gadi.
Shuraih Usman
Kamar lokacin nafara ganinta ,ranta amatukar bace
,kodaddiyar fuskarta ta kara muni,har yanzu
idanuwanta jawur suke kamar tira su take yi.
Sanye d katuwar rigar shan iska da matan turawa ke
sawa,hannun ta rike da makullin mota tana dan
karkadawa.
Ina ganinta tsoro da matukar fargaba suka lillbe
zuciyata ,dukkan jikina ya dau rawa tamkar mutuwa
ta na ke gani;
Babu abin da ke bani mamki irin yadda nake matukar
tsorata da zarar naga matar.
Shakka babu na tsani mummunar matar,bana
bukatar ganinta a rayuwata.
Cikin tsoro ina tunanin guduwa daga wajen ,sai farida
sanye da shudayen kwat riga da siket,ita ta fito daga
dakin wasan .hankalina yayi matukar girgiza,tunanina
ya dagule ,zuciyata bugun ta ya tsananta sannan jinin
jikina ya zafafa.
Farida ! Shin ba wannace akace tamutu ba ?shinyanzu
ma mafarki nake yi?idan dai har aljanu basa rikida
batare da na sami wani bangaren jikinsu , Shuraih
Usman da baiyi kama dana mutane ba ,farida ba
aljana bace .ko ina ajikinta irin na mutane ne
,wannan ko shakka babu.
Domin kura mata ido nayi,babu inda ban kalla a
jikinta ba .
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 9
By Shuraih Usman
Kyan fuskarta ya dada karuwa akan nada ,sannan
amintaccen murmushina bayyana adan karamin
kyakkyawan bakinta "MINAL JINNATI WAN NAS"
Abin da kawai narinka fada kenan.
Sannu ahankali ta rinka nufo wa inda nake ,har nayi
niyyar cika wandona da iska ,ga mamakina sai
kafafuwana suka nauyaya ,ba zan iya gudu ba .
A dai dai lokacin da ta zo daf da ni sai ita da hasken
suka bace,A ranar kwana nayi ina wuridi don na
razana bacci yayi hijira daga idanuna
Shakka babu ina cikin rudu babba.
Shuraih Usman
F
LARABA
7~3~'99
Mahaifiyata Nana safiyya ta kasance ma'abociciyar
turare ce ,
Aduk lokacin da zatayi maka gagarumar kyauta
turarene
Duk lokacin daka hadu da ita ,hancinka zai wadatu da
kamshin hadadden turare.
Fatima ce babbar yarta.
Sannan ni,sai kuma karamin kanen mu sadiku.
Kuma shine yafi farin jini a gidanmu sakamakon
baiwar hikimar zance da zuzzurfan tunani daya
mallaka.
Wata rana mahaifinmu da abokansa na
hira,kowannen na fadin wanda yafi tsana
arayuwarsa,da dalilin daya saya ya tsane shi,kamar
wasa sai daya daga cikin abokan mahaifinmu
yatambayi sadiku dake zaune kusa da mahaifinmu
"Sadiku wanene babban makiyinka aduniya ?"
"Sulman rushdie"ya amsa masa
"Musamman ya wallafa littafi yasa masa suna ayoyin
shaidain(SATANIC VERSES),
Acikin littafin yakirawo fiyayyen ANNABIN RAHAMA,
Mayaudari mazinaci,ya kuma ambaci tsarkakkan
matansa da Allah yakirawo IYAYEN MUMINAI,da
cewar karuwai ne.
Sannan yanuna cewar yayan gidan ANNABI(SAW)
yayan zina ne,
Musulmi da suka rasa rayukansu a yak-yaken
daukaka kalmar ALLAH,ya kirawo su batattu.(Kai
amma Allah ya tsine ma sulman rushdie- kowa ya
tsine mai)
Shuraih Usman
Shaidan salman rushdie bai tsaya nanba ,sai daya
kirawo littafin ALLAH mai tsarki al'kur'ani da cewar
ayoyine na shaidan.
Ayanzu shine littafin dayafi kowanne littafi tsada ,
Wannan abu da shaidan salman rushdie yayi,ko
fir'auna baiyi wannan bakar aniya ba .
Azaba mai matsananciyar radadi,da la'anta mai
matukar yawa ,su tabbata ga shaidan salman rushdie
da yan barandansa"
Abokan mahaifinmu sai dai suka shawarce shi ,da ya
wadata sadiku da wataccen ilmi,saboda nan gaba zai
zama malami mai wadataccen tunani.
Aduk lokacin dana saya mata turare,takan dade tana
nuna farincikinta ,ganin haka sai na mai dasaya mata
turare dabi'ata .
Aduk lokacin da nake bukatar daddadan turare ,kai
tsaye NAFISATU FASHION nake tafiya .
NAFISATU FASHION kayataccen tangamemen waje ne
da mata ke matukar alfahari da ziyartarsa.
Sakamakon zunzurutun kayan kyale-kyalen,mata
masu matukar kyau sai dai tsada .
Koda yake nafisatu ta tabbatar musu cewar arha bata
ado,kuma sayen nagari mai da kudade gida.
Kuma dimbin matan dake narkar da kudinsu a
nafisatu fashion sun dade da yin amanna da wannan
maganar
Shuraih Usman
Idan kana bukatan kayan mata masu kayatarwa,ko
kuma mace na bukatar hadadden gyaran gashi ,ko
tsararren tsari da salo salon kitso,ko kuma
amintattun zanannun furanni(Flowers) a hannu da
kafa ,idan ta ziyarci nafisatu fashion zuciyarta zata
samu gamsuwa daga masana akan sirrin harkokin.
Karfe sha dayan rana na tsaida motar honda civic a
kofar nafisatu fashion sanye nake da kubta riga da
wando ruwan kasa,kaina da hula.
Kamar yadda nasir yafada cewar ya gasgata al'amarin
daya faru gare nine ,ganin yadda kamannina suka yi
mutukar birkita cikin kankanin lokaci tundaga ranar
dana hadu da farida.
Hakama Ahmad da Fatima suka kara maimaitamin,
Kuma ni kaina shakka babu na shaida akan hakan.
Dayake unguwar gadonkaya da gidan Ahmad babu
yawan mutane ,
Kuma ni da shi mun kasance masu yawan zirga zirgar
daukar rahotanni ,bani da abokai kamar unguwar
Albasa da gidan mahaifiya ta yake.
SIRRINSU
Littafi na daya
Chapter 10
By Shuraih Usman
Na san da zarar naje Gandun albasa abokaina na
ganina sai sun tambayeni game da ramar da keyi.
Na samu dogon lokaci ina zaune cikin motar,
Amma na kasa fitowa saboda zurfaffan tunani da na
yi.
"Nan ne gi dan su dela din?
Yanzu ku dama shegantaka. Kuka kulla min?
Ina zaune lafiya kuka yimin karya kun san ba gidan
delar zaku kaini ba !
To mene ne nufin ku da yin hakan?"
Wata yamutsastsiyar murya da kaji kasan wacce ta
mallaketa ,
Shekaru sun wada ceta aduniya ta kaste min tunanina
.
Ina waigawa sai na ga wata tsohuwa ce sanye da riga
da zani na atamfar English,
Tayi wani irin baudadden daurin fatala.
Sannan zanen ma maimakon yatafi daidai sai ya
kauce kamar arazane yake ,sakamakon wani irin
dauri da tsohuwar tayi masa.
A tsaye daf ta wata marsandi ruwan toka ,
Fuskarta da idanuwanta amsoshi ne na cewar ta dade
aduniya.
Kusa da ita wasu kyawawan 'yanmata ne guda biyu,
Babba da karama kana ganinsu kaga ya da kanwa,
Farare sal dasu.
Babbar sanye take da burgujejiyar riga da wandon
wani zani mai kyalkyali a jikinsa ,
Kanta babu fatala.
Karamar kuma bakin wandon jeans ne ajikinta ,
Da kuma farar rigar yadi mai hudahuda,da yake
baiyanar da bakar shimin dake jikinta ,tayafa katon
bakin fatala a kanta.(Tambaya dan Allah mata mene
fatala don ni bansan shi ba Shuraih Usman )
Tsohuwar da ke tare dasu duk ta rude kamar tana
nuna alamun sato ta sukayi.
"Wannan shegantaka har ina ?
Kawai ku tashi ku zunbuda min karya ,wai gidan su
dela zaku kaini,
Shikenan sai ku kawo ni wata uwa duniya ku ajiyeni!
Kunsan ba son shiga mota nake yi ba,
Wannan dinma dan kunce gidan su dela zaku kaini
ne"
Tsohuwar take fada lokacin datake kokarin tafiya
daga inda yaran suke .
"Tsaya kiji Goggo"
Babbar tafada .
"Gidansu delar zamuje ,
Mun tsaya anan ne muyi saye-sayen biki,
Mukuma gyara gashinmu a kuma zana mana flowers.
Sannan kema tunda gobe biki sai a gyara miki gashin
ki,
Gobe ba sai ki fito fes ba"
"Ban gane a gyaramin gashiba !
Da me za'a gyara min gashin nawa ?
Kai kunga bana son iya shege da wasu tsarabe-
tsaraben banza dana wofi.
To ina ma hausar a gyaramin gashi ?
To ama gyara min gashi kamar ya ?
Shuraih Usman
"Kinga Goggo cigaba aka samu ,
Wani irn inji nasara ya yiwo musamman don gyaran
gashi.
Za'ayi matukar wanke miki gashinki ,afitar da
kowanne irin datti,sannan sai ki zura kanki a cikin
injin ya gyara miki gashinki ya rinka sheki ,
Ya kuma canja miki duk irin fasalin da kike bukata "
Ita kanta budurwar sai da ta fada ta gane kuranta.
"Allah ya sitiri bukwui!
Yanzu don Allah ,Don annabi ina zaman zamana kuka
yaudareni babu sidi babu sadada,
Wai na zura kaina cikin inji!
Wato ya markade min kaina kenan?
To idan kun gaji dani alhaji bai gaji da ni ba".
"Na zura kaina cikin inji akan wane dalili?
Tsohuwar ke fadi lokacin data bar inda matan suke ,
Ni kuma a daidai lokacin na fito daga motar na fara
nufar nafisatu fashion.
"Kubarni Allah yakawo wanda zai mayar dani gida,
Babu ruwana daku,kuje tsiyarku ta kare akanku
,nazura kaina cikin inji turkashi!"
Karamar yarinyar tayi saurin tasha gabanta,
Ta fara lallaminta ni kuma adaidai lokacin nazo zan
gifta.
Bawan Allah kaji zancen nanfa"
Tafada lokacin dakai tsaye take fuskantar fuskata(
Shuraih Usman )
"Cewa sukayi na shirya su kaini gidan kanwata
,shikenan sai kuka woni nan waina zura a inji,
Wai acanja min fasali"ina jin yadda injin makotanmu
ke burari,
Sannan yanzu don sunana saratu na garkama kaina
cikin injin nasara ,
Ina ruwana da wata gayyar tsiyar nasara".
Kafin nayi magana karamar yarinyar tarigani.
"Goggo ba markade miki kai zaiyiba ,
Mutane nawa akayiwahakan?
Yanzu zamani ya canja ,
Abin da babu shi da yanzu an samu bawani abu
tattare da hakan?"
"Zamanin banza dana wofi,haka kawai garin neman
gira a rasa ido.
To wai mene ne yayi zafi gira ke hayaki,idoke cin
wuta"
"Shakka babu tafiku gaskiya ,yaya ga abin da mutun
ya saba dashi ,haka kawai rana tsaka ,yarinka
nemowa kansa abin da bana saba.
Tun da dai ku kuna bukata kuje kuyi,
Ita dabataso tayi zamanta a mota, idan kuka fito ku
kaita gida.
( Shuraih Usman )
Nafadi hakanne don na kwantarwa. Da tsohuwar
hankali.
"Sannu dan gari•haka kawai babu gaira babu
dalili,kilu ta jawo bau"
Tafada lokacin da tafara komawa wajen motar.
"Kaduba rannan ina zaune lafiya suka kawomin wata
tsinanniyar aba wai ita talabijin,
Dalbijin ko masifa?
To inbanda masifa kawai sai gani nayi wannan ya
cakawa wancan wuka.
Wancan ya sari wannan da takobi,a duko bindiga a
zunduma wa wannan ,kaga tsiya ! Mutum yafadi ya
mutu.
Can kuma sai wuta ta kama zaal! Zaal! Zaal!!!"
"Kwanana uku ina mafarkin wannan masifar,kuma
tun daga ranar nace in Allah yayi duniya don dan
Abdullahi ni da talbijin munyi sallama .
( Shuraih Usman )
Tafada lokacin data shiga motar,'yanmartan sai
faman dariaya sukeyi suna kallon fuskata.
"Ni dadina da Goggo ,haryanzu kanki yaki wayewa "
Babbar tafada cikin zolaya .
"Fatalar uwarki!kan nawa bai wayeba kullum kike
zuwa ki ce na koya miki yadda zaki mallake mijinki ki
hana shi fita ?"
"Ahayye ! Ayyururi ! Kyale su haka Goggo"
Suka fada suna shewa, lokacin da suka shiga Nafisatu
fasion ,ina biye da su a baya .
Mata ne dinke cikin nafisatu fashion,kowacce na kai-
kawo,
Don zabin abin da suke bukata .
Dayake na san abin daya kawon,kuma nasan inda zan
sami turaren kaina tsaye ban tsaya bata lokaci ba na
nufi matattarar turarikan.
Ina zuwa wajen tirarikan 'yan matan suma suka zo
inda nake .
"Zainab !
Ni ma fa ina bukatar turare"
Babbar ta fada wa karamar,lokacin dasuka fara
duddubawa.
"Kaima turaren zaka siya ?'
Zainab din ta tambayeni.
"Shakka babu "
Nafada ina murmushi.
"Na zaba maka"
"Zaki iya yin hakan"
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 11
By♥ Shuraih Usman
Queen da heart da kuma daimond ,
Sune turarikan da zainab ta zaba min.
Shakka babu ,nayi matu kar yaba zabin da zainab ta
tayi min ,domin tsarin kwalaben kadai sun gamsar
idanuwa .
A dai dai lokacin dana rike ina dada dudduba , sai
naji wata irin daddadan dariya ta diki dodon kunnena
.
Kwalaben turaren suka kubuce daga hannuna suka
tarwatse a kasa,
Tsarwatsewar da ta jawo hankalin matan cikin kantin
kaina .
Hankalina a birkice ,
Tunanina arazane ,bugun zuciyata yayi matukar
tsananta lokacin danaga wacce nake gani ,
Shakka babu farida ce ,
Kasancewar nafisatu fashion tangamemen wajene
akwai tazara tsakanina da su.
Babu abin daya fi tunzurani fiye da komai,
Irin duk inda naje sai na ganta .
Shakka babu ,
Dole hakan ya tunzura rayuwata,
Dole rayuwata ta rude,
Dole rayuwata ta gigita,
Tun ranar da Nigeria da costrica,suka yi wasansu a
lagos ,
Kullum sai mun hadu da farida ?
Kuma bayan na samu tabbacin mutuwarta .
( Shuraih Usman )
Sanye take da kayan babe bari dogwaye har kasa,
Ta nannade jikinta da dogon kayataccen mayafi,
Kamar dama zuwanta kenan daga maiduguri.
Abin daya dada jan hankalina gareta ,wannan lokacin
cikin farin ciki da nishadi farida take,
Bakamar ganina da nayi mata a sani abacha stadium
da kuma hawan dabar gidan sarki ba .
Saboda kada na kara gamuwa da ita, Ahmad yatafi
Lagos don dauko rahoton wasan Nigeria da
Germany.sannan kuma zai wuce ibadan don halartar
wasan gwana da argentina .
Babu yadda bai yi dani don mutafi ba ,
Na dage akan gaskiya na hakura ,
Kawai do tsoron haduwata da Farida .
Wannan lokacin ma tare suke da ko daddiyar matar
,ita ma sanye da zurma zurman bakaken kwat riga da
siket.
A lokacin nake kollosu,kudin sayayyar da sukayi
mayar ke biya .
A lokacin dana yi yun kurin zuwa inda suke ,
Saboda na ga suna kokarin fita sai naji hannuwa sun
rikeni.
Ina wai gawa saina ga wasu rusa-rusan karti guda
hudu,
Kowanne fuskarsa a tirbine suna yi min kallon rashin
yarda.
Sai daga baya na fahimci masu tsaron nafisatu
fashion ne .
Ai a anan na dawo hankalina na fuskanci ta'adin
danayi .
Har yanzu zainab da yayarta na tsaye suna
mamakin,yadda cikin kankanin lokaci na birkita .
Kwata-kwata sai kunya ta lillibeni,dana waiga inda su
farida suke tuni sun fice daga wajen.
Shuraih Usman
Bayan nanemi afuwan ta'adin danayi ,
Na biya kudin tirarikan sai na kara sayen
wasu,sannan cikin sanyin jiki da kunya na nufi inda
motata take .
Na sami dogon lokaci cikin motar ,
Na kasa tukawa na tafi.
Shin menene dalilin da duk inda nayi sai na hadu da
farida?
Tambayar da zuciyata tayi ta maimaitawa kenan,
Na rasa amsarta har sai da wata murya a sanyaye
tace;
"Hala wani abu ya tunzuraka?"
Zainab ce an matukar kayata gashinta ,
Sannan hannunta data dora akan murfin motar,
Shima ya kayatu da kyawawan furanni lokacin dana
waiga.
Bayan nayi ajiyar zciya sai nayimata murmushin
gaskiya kin-hadu-zainab.
Ganin haka ita ma sai ta yi murmushin.
Mahaifiyata tayi farincikin turarikan dana kai mata ,
Kuma ta tambayeni dalilin rama da nakeyi .
Ban boye mata ba ,
Na sanar da ita komai,
Kuma shakka babu tayi matukar mamki kamar yadda
duk wanda na gayawa sai yayi mamaki.
Shuraih Usman
Sannan tabani addu'o'in da zan rika yi don neman
tsari,
Sannan kuma ta shawarceni da kada na aiwatar da
wani yunkuri da zai iya kaini ga halaka ,ko kuma ya
cutar da rayuwata.
Abokaina ma sai da suka tambayeni halin dana ke
ciki.
Shi kansa mahaifina sai da yayi min tofin wasu ayoyin
AL'QUR'ANI a dukkan jikina ,sannan ya tofa min wasu
aruwa na sha.
Ya kuma umarceni da karanta QUL'HUWALLAHU uku,
FALAQI uku,
NASI uku,idan nayi sallar asuba.
Sannan idan nayi sallar magriba ,
Da kuma idan nazo bacci .
Ya kuma kara umarta ta da karanta AYATUL KURSYU
da kuma suratul YASIN.
Bayan na dawo daga gandun albasa wajen
mahaifiyata ,a ranar idan na runtse ido saina ga
kaman farida tana kuka ,
Idan na bude sai na ganta tana murmushi.
Sai dana samu dogon lokaci ina zubar da hawaye
sannan na fahimci kuka nake yi.
"NA SHIGA UKU"
Kalmar dana yawaita fada kenan awann rana.
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 12
By♥ Shuraih Usman
G
ALHAMIS
8~3~'99
Mata ne dake tinkaho da ilmi,
Masu takama cewar mazansu masu fada ajine ,
Suka dinke dakin taron na makarantar Rumfa College,
Don gudanar da taro na musamman akan tallafawa
iyali.
Maimuna isa kwantagora matan ,kantomar jihar
kano,ita ce tayi jawabi na karshe a taron.
Kamar yadda Ahmad ya umarceni don na dauko
muhimman abubuwa a taron ,
Na cika wannan umarnin, domin na halarta.
A burin Ahmad duk wasannin da za ayi a dakunan da
Nigeria ta tanada don gudanar da wasan cin kofin
matasa na duniya sai mun halarce su.
Da farko nayi matukar farincikin hakan,
Amma daga baya na fatattaki farin cikin daga
zuciyata,don matukar tsoron kara haduwa da farida.
Sanye na ke da farin jeans riga da wando,kafata
daure da kito baki
Wasan da za ayi tsakanin cameron da England a
kano,
Bashine a gabansa ba .
Wasan japan da USA da za ayi a bauchi,
Da wasan zambiya da spain daza a gudanar a
calabar,da kuma wasan honduras da brasil da za ayi
a por shine abin daya dame shi.
Kuma babu yadda za,ayi ya halarce su rana daya
,shine babban abin bakin cikinsa da kuma kekasa
kasa danayi nacewa bazan kara halartar kowane
dakin wasa ba .
Shakka babu baiso hakanba ,don matukar shakuwa
da mukayi da shi.
Bayan na gama gudanar da abin daya kawoni ina
kokarin tafiya hausawa sabon titi,in da kamfanin
jaridar Ahmad take ,sai na'urar daukan hoton ta
subuce daga hannuna ta fadi.
Da farko na bayar faridace,sai daga baya na karbo
ashe mahaifiyarta ce ,
Ita ma tana daya daga cikin matan da suka halarci
taron.
Nayi matukar girgiza da mamakin ganinta ,wanda ita
kanta ta fahimci hakan rubuce a fuskarta.
Kuma ita kanta tayi mamakin ganina a wajen
Har muka gaisa da ita gabana na faduwa ,shakka
babu idan kaga mahaifiyar farida kaga farida .
"Da ma anan kake"
Tafada cikin mamaki.
Shuraih Usman
"Wallahi anan nake "
"Daukar rahotanni kake yi?"
"Da man kai ma'aikacin jaridane?"
"Shakka babu"
Nafada .
"A wanne kamfani kake aiki"
"Dankari"
"Dankari?"
Tasake maimai tawa.
"Shakka babu"
"Kana nufin jaridar dankari wanda dimbin al'ummma
ke alfahari da karantata?"
"Shakka babu"
Na maimaita.
"A gaskiya shakka babu ,ta shiga bakinka "(nima haka
daenagani)
Tafada tana murmushi.
"Shakka babu"
Nima nafada cikin murmushi.
Murmushin datayi sai ya koma dariya ,
Nikuma a wannan lokacin zuciyata a farida take
daukanta .
Duk da cewar tafi farida kaurin jiki da shekaru,gani
nake yi zata rikide ta koma farida.
"Ina nasir?"
Na tambayeta don katse dariyar da takeyi . Shuraih
Usman
"Tare muka taho,har ma da meenat ,duk suna
tarauni"
"Tarauni wajen ina "
Na bukata .
"Don inason gaisawa da nasir"
"Kana zuwa daidai masallacin juma'ar tarauni,ka
tambayi shagon askin sulaiman ,agidansu sulaiman
din muka sauka .sai gobe zamu koma yace yana son
ganin wasan England."
Abin dayabani mamki har muka rabu bata yi mani
zancen ganin farida danace ina yiba .
Wanda hakan na nufin TASAN FARIDA TA MUTU
,KUMA TASAN SHAKKA BABU WANDA YAMUTU
KAWAI YAMUTU.
WACCE NAKE GANI A TUNANINA ,ALJANACE TAKE
FITO MIN A SIFFAR FARIDA.
TO AMMA ABIN TAMBAYA ANAN WACECE WANNAN
KODADDIYAR MATAR
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 13
By♥ Shuraih Usman
Bayan naje hausawa sabon titi na bawa ma'aikata
rahotannin dana dauko , sai na wuce gida nayi wanka
na sauya kayan jikina , da shadda riga da wando
launin sararin samaniya ,sai na shiga wata motar
Ahmad din TOYOTA CAMRY sai tarauni.
Kamar ta kwatanta min,ina tambaya aka nuna min
shagon askin sulaiman.
Sulaiman farine amma ba dogo ne sosai ba,yana da
yawan fara'a da 'yar saurin magana.
Kaset din wa'azin AHMAD DEEDAT ne ke tashi a
katuwar rediyon dake shagon yana yi wani yaro aski.
"Don Allah nasir dayazo daga kaduna nake nema"
Na fada bayan ya rage karar sautin rediyon.
"Ok,kwarai yana gidanmu.
"Nasir ko?"
Hakika yana nan.
"Don Allah barina gama askin sai mutafi,dama ina
zon zuwa gida"
Cikin saurin magana yafada,yana sauri don ya gama
wa yaron askin.
"Bismillah,zauna mana ,nakusa gamawa ,saura
kadan"
Yafada lokacin da yayi min nuni zuwa ga kujera .
Bayan ya gama askin,ya kulle shagon,sai muka nufi
gidansu.
"Tun dana ganka nake tunanin,kamar na so na sanka
"
Sulaiman yafada lokacin dana tsayar da motar a kofar
gidansu"
"A ina fa ?"Na bukata
"Shin ko kataba yin karatu a 'yargaya ?"
"Shakka b babu"
"Haba ni fa tun dana ganka ,nake ma kallon sani,nima
a 'yargaya nayi karatu"
Shuraih Usman
A daidai wannan lokaci sai nasir,sanye da farar riga
ya dora mata bakar falmaran ,da wando launin kwai
ya fito daga gidan.
"Aah! Habib! Yaya aka yi kasan ina nan ?"Cikin
mamaki yafada ,lokacin daya nufo in da muke.
"Nasir!" Na kirawo sunansa bayan mungaisa.
"Ya yi habib ,wallahi ina da saurin mantuwa,mama fa
ta fadamin kun hadu dazu a rumfa college "
"Shakka babu"
"Ok sai anjima ,nizan shiga daga ciki"sulaiman ya
fada.
"Nagode sai anjima "na amsa masa.
"Nasir! Kasan kuwa farida tana kano?
Domin jiya sai da nakara haduwa da ita ,a nafisatau
fashion dake nan kofar nasarawa.
Kuma shakka babu. Bani kadai nake ganintaba
,jama'a da yawa suna ganinta ,kawai dai don basu
san tabane "
Nafada
Shuraih Usman
"Habib wannan al'amari yana da matukar mamaki da
rikitarwa.
Ni kaina idan na tsaya nayi tunani,sai zuciyata ta cika
da al'ajabi.
Ni dai nasan farida ta mutu,kuma inhar mutum ya
mutu ,shakka babu tasa takare .
Kuma gashi kai kana haduwa da farida ,abinda yafi
mamaki ma ai dole kwalkwalwa da zuciya suyi"
Cikin matukar mamki yafada .
"Kasan abin dayafi dagula min lissafi nasir? Farida ba
aljana bace ,kamar yadda masana SIRRINSU suka
sanar dani.
Dole idan aljani ya rikida asiffar mutum ,sai ansami
alamun daza su tona masa asiri cewar ba mutum
bane .
Na ga farida har sau hudu,kuma shakka babu ,babu
wata alama a jikinta da bata dace da mutane ba".
Kuma babu yadda za'ayi aljani yarinka bayyana a
bainar jama'a yana hulda dasu .
Duk ganin da nake yiwa farida acikin jama'a nake
ganinta ".
Nasir yayi shiru na wasu lokuta ,nikaina na san tunani
ne ke birkita kwalkwarsa.
"To shin habib idan wacce kake gani ba aljana bace
,kana nufin farida kake gani, wacce muka binne kuma
wacece?"
Shuraih Usman
"Nikaina wadannan tambayoyin ina matukar
kwadayin amsoshinsu"cikin sanyin jikinafada.
"To ai sani zaka sake nema daga masana akan
SIRRINSU"
"Shakka babu,ina ganin abinyi kenan"
Bayan mun tattauna akan wannan da waccan,sai
naga yadace nakoma .
"Habib ,zaka halarci wasan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment