Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikin muryar kuka Bintu tace"mugun nufi kuma mami"
Mami tace"au a tunanin ki bamu san abinda kk shirin aikatawa ba,to bari kiji duk abinda kuke shirin aikatawa na jishi a kunne na dan hk dake har iyayen naki baku isa ku rabani da d'an nn qwaya d'aya tal da Allah ya bani ba idan ku mayu ne can kuci kanku Allah bazai ta6a baku nasara ba koma a ina kuka je.
Waheed ya miqe tsaye yace"haba dan Allah mami wnn wane irin zance ne kikeyi haka banbarakwai ba dad'in ji"
Cikin d'aga murya tace"yi min shiru waheed! kuma idan naji ka sake cewa wani abu a nn zan maka abinda baka ta6a tsammani ba wlh,shashasha kawai wanda bai san abinda yake yi ba! Ka rubuta mata takardar sakinta nace ka bata ko kuwa sae ka gama 6ata min rae ne iye!
Waheed yayi shiru kawai bai ce komai ba sae kallon takarda da biro yake da kmr ba zae iya rubuta abinda ta umarce shi ba.
Tace"ban isa ba koh!?
Yace"ko d'aya mami wlh ba haka bane amma dan Allah kiyi haquri na mata wani hukuncin ba wnn ba.
Cabd'i lallai inaga baka san abinda wnn yarinyar take shirin aikatawa akan ka ba shiyasa,ta nuna bintu tace"ka ganta nn bata aure ka dan komai ba sae dan dukiyar ka shiyasa duk cikin da ta samu bata barin shi take zubarwa kai d'in ma lokaci kawai take jira ta kawadda kae ta kwashi dukiya su gudu.
Waheed yace"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!mami a bakin wa kk ji wnn mgnr wa ya gaya miki da har kika yarda cewa fatima zata iya aikata haka a gareni bayan kinfi kowa sanin irin qaunar da take min.
Au qaunar da take maka ne yasa duk ta sami ciki take zubarwa.
Kansa ne ya kunce lokaci d'aya qwallah suka ciko masa ido haqiqa mami tayi magana a nn amma baya jin bintu zata iya cutar dashi ko nn da can da akwai dai dalilin da yasa take zubar mai da ciki dashi kansa ya kasa gane dalilin.
Idanun sa jajur ya kalli bintu wacce ke kuka cikin tashin hankali da jin zancen mami da ya qara rikitata.
yace"fatima ashe dama dalilin da yasa kika aure ni knn ba sona kikeyi dagaske ba!?
Cikin kuka tace"yaya waheed wlh na rantse maka ba haka bane ban aure ka dan komai ba sae dan qaunar da nake maka"
Yace"qarya kike ba kya qauna ta fatima kan me zaki ta zubar min da 'ya'ya na to gaya min ko duk cikin so ne!
Da sauri ta tashi daga durqushen da take taja da baya ganin yanda yake matsowa kusa da ita kmr zae duke ta bata iya cewa komai ba sae wani sabon kuka da ta fashe dashi dan bata san ma ta yanda zata mishi bayani ba.
Waheed sae kallon ta yake zuciyar sa na masa wani irin zafi da quna ba dan komai ba sae dan baqin cikin quncin rayuwar da ta jefa su a ciki suna zaman su mai dad'i tazo ta 6ata musu komai wanda shi ya tabbatar abinda mami ta jiyo ba gaskiya bane bintu bazata iya aikata shi ba amma ba yanda zai yi tunda bintun taqi tayi bayani.
Mami tace"kaga waheed bana son wani 6ata lokaci yi abinda na umarce ka kawai tayi ta bar gidan nn in daina ganinta idan kika tafi can kya yiwa iyayen naki bayanin bakuyi nasara ba Allah ya tonu asirin ku.
Waheed ya runtse idanun sa ko kad'an baya jin dad'in yanda mami ke sako iyayen bintu a ciki yafi son koma mene ne ta tsaya akan bintu.
Komai bai sake cewa ba ya rubuta takarda ya ba bintu ta kar6a sae kallon takardar take tana hawaye.
Mami tace"kuma kisani a cikin satin nn waheed aure zai yi dan haka ki tabbatar kin kwashe duk wasu komastsanki da kika san naki ne ki tafi dasu bana da buqatar ganin su a gidan nn"
Bintu dake kallon mami wasu hawaye masu zafi suka gangaro kan fuskar ta tasan dole abinda zae biyo baya knn,bata ce komai ba ta juyawar ta zuwa d'aki.
Mami ta kalli waheed wanda gabad'aya hankalin sa ya gama tashi da jin zancen ta dan yasan tun da har ta furta ba makawa haka ne d'in zae faru wanda cike yake da son ya mata magana amma bata bar yace komai ba taja hannun sa suka bar gidan.
Itama bintu ba 6ata lokaci ta bar gidan sae kuka take janye da akwati a hannun ta.

Motar kasuwa tabi cikin mota ta yanke shawarar ko taje gida baza ta bar umma ta sani ba zata ce kawai ganin gida tazo,ba don komai ba sae dan bata son ganin irin baqin cikin da umma zata shiga a ciki da kuma irin maganganun habaici da zata sha agun iyayen su sarah wa'enda burin su knn ko yaushe su gansu cikin matsala.

Byn isha'i suka isa garin birnin kebbi ta samu napep ta kaita gida, bata yi sallama ba dan bata son kowa yaga shigowar ta, taci sa'a kuwa har ta shiga d'akin su ba wanda ya ganta kowa babu a falo ta shiga daga ciki ta sami umma ta fito daga bathroom knn.
Da mamaki umma tace"bintu kece da daren nn da kuma uwar akwati haka ga kuma uniform a jikin ki ko cirewa bakiyi ba lafiya me yake faruwa?
Duk yanda bintu taso 6oye ma umma damuwar ta ta kasa ta saki akwati taje da gudu jikin umma ta fashe mata da kuka.
Umma taja ta suka je gefen gado suka zauna tana kallon ta da kulawa tace rashin jinki yasa kunyi fad'a da waheed koh?
Girgiza kanta tayi
Umma tace"to mene ne?
Ba komai yaya ne zae yi tafiya.
Umma ta girgiza kanta tace"to shine kike ma kuka haka awa wacce akayiwa mutuwa ina waheed d'in yake tare kuka zo ko kuwa"
Aa ba tare muka zo ba yana can.
To wace irin tafiya ce zai yi da bazai barki gidan mamin sa ba kmr yanda ya saba.
Zai jima sosai shiyasa.
To komai jimawar da zaiyi bintu ae bai kamata ace kin dawo ba keda kike aiki.
Na d'auki hutu ne....shi aikin asibiti ake d'aukar hutu haka kawai,hm mts ni narasa meyasa waheed yake biye miki da galihun nn ae gwanda kiyi aiki tuquru ki san halalinki kike ci.
Bintu tace"umma wlh ni tun lokacin da na fara aiki rana d'aya ban ta6a tsallakewa ba ko yanzu lalura ce ta kama.
Umma tace"to naji shi drivern da ya kawo ki yana ina ko a motar ki kika zo?
Aa ba a mota ta nazo ba, yunwa nake ji umma banci komai ba nazo"
To ae kinsan hanyar kitchen sae ki tashi kije ki sami abinda kika ci.
Nan ta tashi ta fita umma taja akwatin ta takai ta inda ta dace.

Bintu kuwa tea ta had'a tazo falo tayi zaune tayi shiru qwallah tap a idon ta sae motsa tea take tana tunanin duk rnr da umma ta gano gaskiya ya zatayi tasan kashin ta ya bushe gashi ko yanzu sae tambayoyi take ta mata wanda hkn ne yasa ta qirqiro cewa yunwa take ji dan ta samu ta ku6uta daga tambayoyin da umma ke mata amma halin da take ciki sam bata jin zata iya cin komai duk da irin yunwar da take ji kuwa.
Motsin da taji ne yasa tayi saurin share hawayen da suka gangaro kan kumatun ta.
Umma ce ta fito sae da taje ta kunna tv snn tazo ta zauna ta kalli bintu had'e da fad'in"keda kika ce yunwa kikeji baki ci komai ba shine baki ga abin had'awa ba sae tea byn akwai abinci"
A sanyaye bintu tace"umma ko tean ma naji kmr bazan iya shan sa ba"
Umma tace"ae tunda kika had'a shi sae kin shanye shi tas in gaya miki, nn ba irin gidan ki bane da kike 6arnar da kika ga dama.
Umma wlh ba 6arna bace shan sa ne bazan iyaba kuma so nake inje ko ruwa na watsa in cire uniform d'in nn duk sun isheni.
Umma tace"to sha ko kad'an ne sae ki tafi"
Yanayin fuskarta kmr zatayi kuka tace"Umma dan Allah bari in tafi.... ba inda zaki je fa sae kin sha ko kad'an ne idan kuma d'ure kike so in miki to a shirye nake.
Kan dole bintu ta kur6a kad'an ta ajiya ta tafi acewar zata dawo ta qarasa shanye sauran idan ta cire uniform wacce ta fad'i hkne kawai dan kar umma tace tazo sae ta qara sha.
Umma dae bata ce mata komai ba sae binta tayi da kallo dan ta fhmci duk ta fad'a ta rame.

Dama labarun Kebbi TV tazo kallo ana gama labarun ta kashe Tv ta d'auki tean da bintu ta ajiye ta tafi d'aki riqe da shi a hannunta, ta sami bintu cikin shirin ta na bacci zaune kan bed ta had'e kae da guiwa.
Kan bedside drawer ta ajiye tean snn ta zauna gefen gado kusa da bintu wacce sae a lokacin taji shigowar ta tayi saurin sa hannu a 6oye ta share hawayen fuskarta snn ta d'ago a hnkli ba tare da ta iya kallon umma ba.
Umma tace"ke shike nn dan waheed zai yi tafiya kibi kisa damuwa a ranki kmr wanda in ya tafi ba zae dawo ba"
A sanyaye bintu tace"umma zae jima sosai ne shiyasa "
Umma ta numfasa tace"duk da haka bintu kukan nn yayi yawa ki duba fa koda kika zo gidan nn duk idanuwanki a kumbure suke sbd kuka sae kace kece farau tafiyar miji ko da yake banga laifin ki ba waheed mutumin kirki ne da ko kwana d'aya kayi tare dashi bako so ya tafi ya barka, kece dai yini d'aya ma kin ishi mutum.
Komai bintu bata ce ba sae kallon umma tayi ta sake maida kanta qasa.
Umma tace"tsawon wane lokaci zae d'auka kafin ya dawo?
Hawaye ne suka silalo mata ta share hawayen snn tace"nima bai gaya min lokaci ba ya dai ce zae jima"
Cikin yanayin tausayi umma taja ta zuwa jikin ta tana shafa bayanta cikin rarrashi da haka har bacci ya kwashi bintu.
Umma ta kwantar da ita taja blanket zata rufa mata jikinta sae ta hango hannun ta dunqule da wani abu,a hankali ta ware hannun taga takarda ce ta ciro takarda ta bud'e zata karanta.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 24_*
Ta bud'e takardar zata karanta knn sae taji qarar wayar ta tana ringing sae kawai ta linke takardar ta jawo bedside drawer ta saka snn taje ta d'auki wayarta.

6angaren waheed kuwa suna isa gidan mami,mami ta zaunar dashi kan doguwar kujera taje ta d'ebo mishi abinci tayi zaune kmr wani qaramin yaro zata fara bashi a baki.
Bae kar6a ba yace mami ki barni inyi magana dan Allah.
Mami ta sake kae spoon a bakin shi tace"ci abinci tukun zamuyi magana kaji"
Yace"Mami bazan iya cin abinci nn ba wlh so nake kawai naji shin zancen aure nn kin fad'a ne kawai ko da gaske kike?
Mami ta numfasa tare da maida spoon a plate tace"ba wasa nake yi ba waheed da gaske nake kuma a cikin satin nn inshaa Allah nake so ayi komai dmn so nake ka manta da bintu kwata kwata a rayuwar ka ko tunanin ta bana so inga kanayi.
Waheed yayi shiru kawai dmn abinda mami ke fad'a ita kanta tasan ba zae yiyu ba,ba zae ta6a iya manta bintu a rayuwar sa ba har abada sae dae kuwa idan qwaqwalwar sa ce ta sami matsala.
Ya kalli mami cikin yanayin begging yace"Mami ki taimaka min dan Allah ki janye zancen auren nn wlh gabad'aya aure ya fita a raina nafi so in ci gaba da rayuwata ni kad'ai bana da buqatar wata abokiyar rayuwa.
Hm waheed knn bari kaji in gaya ma aure kam anyi an gama kuma a cikin satin nn inshaa Allah idan kae baka da buqatar abokiyar rayuwa ni inada buqatar inga en jikokina snn dan mace d'aya ta cuceka ae bashi zae sa ka tsani duka matan duniya ba dmn kowace mace da irin halinta kuma wacce nake son in had'a ku aure ka santa yarinya ce mae natsuwa da hankali wato Husna er gidan Hajiya binta wacce akae akae take zowa gidan nn tana kawo min ziyara ina ce ka gane ta?
Shiru kawai waheed yayi wanda ko kad'an baya son mami na masa zancen auren nn shi abinda yake matuqar damun sa ya kuma d'aure masa kae shine shin a ina ne mami taji cewa bintu ta aure sa ne dmn taci dukiyar sa"
Mami tace"wae waheed baka jina ne ina maka magana kamin shiru.
A hnkli ya numfasa yace"kiyi haquri mami so nake ki gaya min dan Allah a bakin wa kika ji cewa bintu ta aure ni ne kawae dan taci dukiya ta.
Mami tace"waheed meyasa kake son sae kasan wanda ya gaya min?
Sbd nayi mamakin yanda akayi har kika yarda da zancen nn mami.
Tace" Waheed ni kaina da farko nayi matuqar mamaki da jin zancen nn sbd nafi kowa sanin irin qaunar da bintu ke maka snn kuma a iya sani na ko 6atan wata bintu bata ta6a yi ba hkn yasa nace ba bintu 'yata ba kam sae dai ko wata can ce suke mgnr ta amma in kazo zan tuntu6e ka inji,sae gashi da kazo na tambaye ka kamin bayani dae dae yanda naji mgnr kaga kuwa dole in yarda tunda kae kanka kace baka san dalilin ta na zubar ma ciki da take yi ba,ko kun ta6a wani fad'a ne ka 6ata mata rae da yawa shiyasa take ramawa da hakan?
Ko d'aya mami a zaman da mukayi ban san munyi wani fad'an azo a gani ba.
To ko ta ta6a ce maka tana son kuyi planning sbd karatun ta kace mata a'a?
Aa mami asalima duk ta samu ciki ya zube sosai tafi ni shiga damuwa se tayi ta kuka sae ni zanyi ta rarrashin ta.
To ka gani duk nn zaka fahimci na munafurci ne kawai tunda cikin farko ma baka san ta same shi ba har ta zubar,dan haka nake son kar ka bani kunya waheed ka yarda ayi auren nn kmr yanda na buqata.
Idanun waheed ne sukayi jajur suka ciko tap da qwallah sam a tsarin rayuwar sa bai ta6a kawo zaiyi rayuwa da wata 'ya mace ba bayan bintu koda kuwa ace mutuwa ta rabashi da ita sae dai yayi rayuwar sa shi kad'ai amma yanzu ya zama dole yayi biyayya ga mamin shi ko dan kasancewar sa shi kad'ai ne d'anta a duniya da zata kalla taji sanyi wanda idan bai bi umarnin ta ba ya tabbatar zatayi matuqar baqin ciki shi kuma baya da burin da ya wuce ya ganta cikin farin ciki ko yaushe.
A hankali ya kwanta kan laps in ta tare da fashe mata da kuka ta d'ago shi sae share masa hawaye take tana fad'in "haba waheed kaifa namiji ne bai kamata ace kanayin kuka da hawaye irin haka ba komai na duniyar nn haquri akeyi ba kuka ba kaji yi haquri.
Yace"Dole inyi kuka mami dmn fatima ta cuce ni bata kyauta min ba meyasa zata min haka bayan tasan irin qaunar da nake mata.
Cike da tausayi Mami ta maida shi kan laps d'in ta ta kwantar sae shafa kansa take tana rarrashin sa.

6angaren su bintu kuwa washe gari da safe umma ta tashi bintu tayi sallah,bintu ta tashi taje bathroom bata wani jima ba ta fito tazo tayi zaune qasa gefen gado ta had'e kai da guiwa.

Umma da ta sallame sallah tace" zo nn bintu"
Bintu tazo jiki sanyaye kmr wata mara lafiya ta zauna kusa da umma wacce ke kallonta da kulawa tace"gaya min gskyr abinda ke damunki dmn bazai yiyu ace damuwar tafiyar waheed kad'ai ce ke damunki da har kika kasa yin baccin kirki.
Bintu tace" ba komai umma"
Umma dake kallonta muryar ta natse tace"bintu duk wanda ya kalle ki lokaci d'aya yasan akwai damuwa a tattare dake,ki gaya min idan har matsala kika samu da waheed inji in sasanta tsakanin ku kafin Abban ki ya dawo ki samu ki koma dan in yazo ya tarar dake a gidan nn zaku kwashi en kallo ne keda shi dmn muddin yaji ba zuwan gidan lafiya ne kikayi ba tofa mai qwatar ki a hannun shi sae Allah kin sanshi sarai soja ne mae baqar zuciya ba sae an gaya miki ba kuma gab yake da dawowa yau ko goben nn.
Shiru bintu tayi haqiqa tafi kowa sanin halin Abbanta shiyasa take matuqar jin tsoran sa dmn kan rashin jinta akwai wani d'an karan duka da ya ta6a yi mata har sae da aka fidda ran zata rayu.
Amma kuma tana jin tsoran snr da umma gaskiyar abinda ke faruwa dan ta tabbatar ba abinda bazae faru ba idan suka ji,Abba zae duke ta dukan tsiya umma kuma zatayi baqin ciki marar misaltuwa.
Tace"Umma bani da wata damuwa kawai ina jin kewar yaya waheed ne kuma baccin da na kasayi ciwon kae ne ya hana min.
Umma ta numfasa tace"to Allah ya sauwaqe tashi kiyi sallah ki sami abinda kika ci sae kisha magani"
A sanyaye tace"Fashin sallah nake umma kuma kaina ya daina min ciwo".
Umma tayi shiru tana kallonta tace"wae bintu har yanzu dae shiru ko 6atan wata"
Bintu ta sadda kanta qasa qwallah cike a idonta.
Umma tayi shiru tana kallon yanda hawaye ke silalowa a hnkli kan kumatun bintu ta fhmci duk tayi mata zancen haifuwar nn sae tayi kuka se taji dama bata d'auko zancen ba sbd bata son bintu tana saka damuwa a ranta.
Ta jata zuwa jikinta cikin rarrashi tana fad'in"ke yarinya ce bintu wacce kwata kwata ko shekara ashirin bakiyi ba har yanzu dan haka ki daina saka damuwa da yawa a ranki haifuwar nn ta Allah ce lokaci ne kawai bai yi ba idan lokaci yayi zaki haifu da yardar Allah kinji ki daina kuka.
Bintu ta gyad'a kanta tare da share hawayen fuskarta sae kuma da saurin ta ta kalli umma tace"umma jiya da nayi bacci baki ga wata takarda dunqule a hannu na ba?
Umma tace"na ganta tana cikin bedside drawer na saka miki"
Ajiyar zuciya bintu ta sauke ta tashi taje ta d'auki takardar ta 6oye a cikin akwatin ta umma dai sae kallonta kawai take tayi bata ce mata komai ba.

Guraren qarfe goma zaune suke suna break fast inda bintu cin abinccin kawae take cikin tunani can muryar ta a sanyaye tace"umma wae su zeenah na gidan nn kuwa naga tun jiya banji alamun su ba ko dan basu san nazo bane"
Umma tace"Ae yanzu su zeenah basa zama gidan nn haya suka kama can kusa da asibitin da suke aiki sae jefi jefi suke shigowa"
Cikin mamaki bintu tace"Haya kuma umma da wane dalilin?
Umma tace"Hm wae yafi masu sauqi ko a qasa sae suje asibiti ba sae sun hau mashin ba.
Amma umma wnn ba hujja bace shi kawai kud'in mashin zae sa abar su su kama haya a matsayin su na en mata kuma iyayen su suna a cikin gari gaskiya hakan bae dace ba kuma ba mutunci bane.
Umma ta nisa tace"ba yanda Abbanki bai yi ba bintu amma fafur iyayen su suka ce su sai dai abinda 'ya'yansu suke so za'ayi,ya kawo na gani ya saka musu,dan haka kema bana son inji kin musu wata magana da sunan shawara dmn bana son anyi ance.
Bintu tace"to"snn tace"yaya Abdallah fa yaushe zae zo?
Baice min ga yaushe ba yadai ce min idan ya sami lokaci zae zo.
Shiru kawai bintu tayi bata ce komai ba tana tunanin lallai idan ya dawo zata gaya mishi matsalar da take ciki ko zata sami mafita dan tasan shi kad'ai ne zae iya fahimtar ta har iya bata shawara.

*Sokoto*

Waheed ne kwance shiru yana jin gabad'aya gidan ya masa fad'i ba dad'i qunci da tunani fal a ransa duk ya rame kmr wanda ya jima kwance yana ciwo.
Doorbell d'inda yaji ne yasa ya tashi sannu a hnkli yaje ya bud'e qofa. maminsa ce ta shigo ya gaida ta suka je suka zauna takai hannun ta kan goshin sa tare da fad'in"ya jikin naka da sauqi koh"
Muryar sa can ciki yace"da sauqi "
tace"to Allah sauwaqe kaci abinci kuwa?
Kae ya gyad'a mata ba dan yaci ba sae dan baya son ta tasa shi gaba kan sae ya ci.
Tace"Alhmdlh zancen auren ka dai yana tafiya dai dai dmn nayima hajiya binta magana kuma ta amince ayi komai a cikin satin nn kmr yanda na buqata snn na gaya musu komai mu zamuyi da kanmu har kayan d'aki dan haka nake son duk wani abu na bintu zan turo a kwashe ae aikata mata komastsanta can bama da buqatar su.
Waheed ya gyad'a mata kae kawai dan ko magana ma baya sonyi
Mami ta numfasa dmn ko kad'an bata son ganin waheed cikin damuwa shiyasa ma take son ayi auren nn da wuri ko zae rage damuwar da yake ciki.
Tace"bari in tafi sauri nake amma dan Allah ka rage damuwar nn kaji"
Still kae ya gyad'a mata ta tashi ta tafi ya d'ago kansa sae kallon hoton su yake shida bintu inda suke sanye da qananun kaya iri d'aya ya goyata a bayan shi suna dariya, ya sauke idon sa a hnkli yasa tafin hannun sa ya share hawayen da suka gangaro kan kumatun sa.

*KEBBI*

Washe gari bintu ce zaune shiru riqe da magani a hannunta tana kallon umma dake harhad'a kayan wanki sae fad'uwar gaba take taji da ta rasa dalili ga kuma kanta dake mata masifar ciwo sbd damuwar da take ciki da kullum qaruwa take jin tana yi.
Umma ta gama had'a kayan wankin tace"bintu kisha magani mana ki kwanta kiyi bacci ko ciwon kan nn zae rage miki ni zan tafi inyi wanki bana son Abbanki ya dawo ya sami kayan dattin nn.
Bintu tace"umma ae naji sauqi bari in wanke miki kayan"
Umma tace"sha magani kawai ki kwanta zan iya da kaina kinji"
Komai bintu bata ce ba ta d'auki koko dake ajiye cikin cup kan bedside drawer tasha magani.
Bata kwanta ba sae kayan wankin da umma ta d'auka taje ta kar6a tace"umma bari in kai miki bana son ki d'auka da kanki".
Umma bata musa mata ba suka fito tsakar gida nn gurin fanfo inda kowa ke wanki bintu ta ajiye wankin dama da akwai kujeru gurin na tsakar gida ta d'aukowa umma ta zauna snn ta d'ebo ruwa a fanfo suka fara wanki umma keyin sa6in farko bintu nayin na biyu ta kuma d'aurewa ta shanya ba don umma taso ba sbd ciwon kan da bintu ke fama dashi amma bintu ta dage kan saita taya ta.

Suna cikin wankin ne suma iyayen su sarah suka d'auko nasu wankin sunayi dan kawai suyi su cika gurin shanya kar umma ta samu yanda take so ba don sunyi niyyar yin wankin ba.
Da bintu har umma ba wanda ya kulasu suna jin su sae fira suke a tsakanin su suna kekkewa da kuma habaice habaicen su da suka saba na neman magana.

Can kowannen su na cikin wankin sa kmr

Please Login or Register in order to submit comment