Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwandon abinci da saurin sa ya kar6i kwandon ya bata hanya ta shigo yana fad'in"amma mami ya baki zo da Hajjo ba ta riqo kwandon sae ke kika d'auko da kanki?
Sae da mami ta zauna snn tace"hajjo tana aiki ne shiyasa ina bintu take jikin nata da sauqi dae koh"
Da sauqi mami bari in kira miki ita tana daga ciki.
Yaje ya ajiye kwandon abincin kan dining snn ya tafi d'aki ya kirowa bintu suka fito.
Suna qarasowa da ladabi bintu ta zauna qasa kusa da mami tana gaida ta,mami ta dafi kanta da kulawa tace"ya jikin naki da sauqi?
Tace"naji sauqi sosai "
Yace min period pain ke damunki koh"
Bintu tace" Eh"
Mami tace"to Allah ya baki lafiya ya kuma yaye miki wnn lalurar"
Suka ce"Amin"ita da waheed.

Bata wani jima ba tace"zata koma waheed ya rakata tace"dama ina son ganin ka waheed kaddai tun da akayi auren nn kallon kallon kuke yiwa junanku ba abinda ya shiga tsakanin ku na auratayya.
Sai da ya d'an sosa bayan kansa irin na jin kunya d'in nn snn yace"me kika gani ne mami?
Gani nayi da dama masu fama da irin lalurar nn in sukayi aure shikenan sun rabu da ita amma gashi bintu har yanzu kusan wata nawa da auren ku.
Mami kinsan kowa da yanda Allah yayi shi amma ba yanda kike tunani bane ciwon ne kawai yaqi rabuwa da ita kuma sauqin abun da zarar tasha magani shike nn.
Ajiyar zuciya mami ta sauke tace"to ubangiji Allah ya yaye mata"
Yace "amin"
Mami ta shiga motar ta taja ta tafi snn ya koma daga ciki.

Washe gari sosai bintu taji sauqi dan har break fast ita ta had'a musu suka ci ta kuma yi shirin zuwa school suka fita waheed ya sauke ta ya wuce gurin aiki.

Kmr kullum sae da suka gama lectures snn ta had'u dasu zeenah sae mamakin ta suke dan basu d'auka zata iya shigowa school ba sbd ta kira su ta gaya musu tasha maganin har ma cikin ya zube.
Zeenah tace"anya bintu kinsha abotion pills d'in nn kuwa sae na ganki qalau kmr ba abinda ya faru.
Bintu tayi shiru kmr ba za ta yi magana ba dan har ga Allah ko zancen bata son a mata ciwo take ji dan tayi dana sanin zubar da cikin ba kad'an ba.
A natse tace"zeenah zan miki qarya ne,nasha maganin kuma cikin ya zube kae tsaye"
That's gud yanzu shawarar da zamu baki itace kiyi planing har sae kin kammala karatun ki tukun.
A hankali ta girgiza kanta tace"Aa ni bazan yi ba kuma ko na sake samun wani cikin bazan zubar ba koda kuwa karatuna zae ta6ar6are.
Zeenah tace"to amma ba kya gudun ciwon yoyon fitsari ki tuna fa ke yarinya ce bai kamata ki haifu yanzu ba.
Zeenah ba ciwon yoyon fitsari ba koma ciwon me zae same ni bazan sake kuskure irin wnn ba dmn banida wani babban burin da ya wuce in saka yaya waheed a cikin farin ciki koda kuwa rayuwata zata lalace wa dalilin shi,sae goben ku ni zan tafi.
Komai kasa ce mata sukayi har ta shiga mota suka wuce sbd suna cikin magana ne drivan ta ya iso.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 18&19_*
Washe gari waheed ne kan jikin bintu ya mata rumfa sae dariya take tana tura shi sbd cakulkulin da yake mata yana son zae kar6i abu a hannunta.
Qarar wayar sa ce ta katse su ba tare da ya sauka kan jikin nata ba yakai hannu kan bedside drawer ya d'auki wayar sa dake kai snn ya d'aga kiran.
Yana gama waya ya kalli bintu wacce cikin dariya tayi saurin 6oye hannun ta a baya sae faman sauke numfashi take tace"wayyo Allah yaya zaka kashe ni dan Allah ka sauka kan jikina haka"
Yace"bani abuna to"
Maqale kafad'a tayi baza ta bashi ba ae kuwa sae ya sake mata nauyin sa gabad'aya,ba shiri ta saki ihu tana fad'in"dan Allah yi haquri ka tashi wlh zan baka amma sae in zaka en min"
Dariya waheed yayi ya d'an d'aga daga jikinta kad'an snn yace"to naji bani"
Sae da ta tsaya yerjejeniya dashi kan in ta bashi fa sae ya en mata yace ya mata alqawarin zae en mata.
Ta bashi d'an yatsan ta suka qulla er alqawari snn ta yarda ta bashi, wani irin hadadden chocolate ne da gani zaiyi dad'i da tsada girman sa da shape d'in sa kmr qwai tana kallo ya 6are ledar chocolate d'in direct ya tafi dashi zuwa bakinta zae saka mata har ta bud'e bakin nata kawai ya ruga abinsa gabad'aya cikin bakin sa ya kuma tashi aguje ya bar gadon ta bishi cikin kukan shagwa6a sae zagaye d'akin suke yana mata dariya ta samu da qyar ta cafko shi suka fad'i a tsakiyar d'akin kan center carpet tasa yatsanta a bakin shi sae son take ta ciro chocolate d'in amma ya cije haurun sa gam ta yanda ko yatsanta baya shiga ae kuwa se ta fashe mishi da kuka ta kuma sa tafukan hannyen ta duka biyu kan qirjinsa tana dukan sa cike da shagwa6a,
ya kama hannayen ta ya riqe yana ta mata dariya,cikin fushi ta fizge hannayen ta taje zuwa tashi yayi saurin riqo ta ya ciro chocolate d'in yana fad'in"yi haquri kar kiyi fushi kar6i gashi ban cinye ba raba ki bani nawa"
Bintu wacce dama ba fushin gaske bane ta kar6i chocolate d'in kae tsaye ta d'ura shi cikin bakinta ta kuma tashi da sauri tana batun guduwa waheed ya damqo ta ta fad'o sae kan jikinsa da hanzarin sa ya mirginadda ita zuwa qasa ya saka bakin sa a nata bashi ya zare ba har sae da ya gutsuro rabin chocolate d'in yana ci sae dariya yake dashi har bintu sbd yanda chocolate d'in duk ya 6ata musu baki sae da suka cinye snn bintu tasa lallausan harshen ta a lips d'insa ta lashe masa kaf chocolate d'inda ya 6ata masa baki haka shima yasa nasa harshen ya lashe mata.

Da yake dama sunyi wanka har ma sunyi break fast qarasa kammala shirin fita kawai sukayi suka tafi gidan mami.

Bayan sun gama gaisawa da mami ne take cewa da waheed"kaida kace da sassafe zakayi tafiyar nn amma gashi har goma tayi maka a cikin garin nn"
Yace"wato mami na d'aga lokacin tafiyar ne kinsan ta jirgi zanbi.
Ok to ina drivern naka bashi kace zae kai ka airport ba?
Eh wani uzuri ne ya tsaida shi amma zamu had'u dashi can airport sae ya dawo da mota nn gidan in yaso da safe ya riqa zowa yana kai fatima makaranta idan kuma sun gama lectures sae ta kirashi ya maida ta.
Aa ka barshi nida kaina zan riqa kai 'yata school ina maida ta in ka dawo sae kuci gaba da inda kuka d'ora.
D'auke da murmushi yace"to shikenan mami godiya muke ni bari in tafi"
Nan suka fito su duka suka rakoshi ya shiga mota mami ta masa Allah kiyaye hanya amma bintu kanta qasa ta kasa ce masa komai sae shi yace"to fatima ni zan tafi a mana addu'a kinji sae na dawo idan kuma na mutu ki yafe min"
Daga haka yaje zuwa rufe ganbun mota tayi saurin riqe gabun tare da fashe masa da kuka.
Waheed ya fashe da dariya mami ta dunqule yatsunta biyar ta watsa mishi tace"ungo nn ya zaka ce mata haka salon kawai kasa 'yata cikin tashin hankli"
Yace"mami meye laifina ganin nayi tana sonyin kukan nn sae kace idan na tafi ba dawowa zanyi ba"
Mami tace"Au dan ma ka samu koh"
A d'an shagwa6e yace"Mami wlh ba hk bane bana son inga tana yin kuka duk damuwa nake ji kuma ta sani.
Mami tace"to ae yanzu laifinka ne kana gani sae fmn danne kukan nn take amma sae da kasa tayi.
Waheed bai ce komai ba sae fitowa yayi daga cikin mota yazo gab da bintu yasa hannu yana share mata hawaye yana fad'in"to yi haquri daina kuka idan baso kk in na tafi bazan dawo ba sae dai nayi sabon aure abuna in manta ki muyi ta soyewa abin mu nida amaryata.
Da sauri cikin shagwa6a ta buge hannayen sa da yake share mata hawaye ta kalli mami kmr zatayi kuka tace"mami kinji shi ko"
Hararar sa mami tayi ta janyota zuwa jikinta sae shafa kanta take cikin rarrashi tace"barshi ae idan har ina raye bai isa ba ni ke kad'ai ce 'yata ba wata wacce ta isa"
Cikin dariya waheed yace"au mami dad'in baki kk mata bayan gashi har kud'in sadaki kin bani kince inyi sauri in kae kar tace ta fasa a satin nn kk so ayi komai"
Cike da shagwa6a bintu ta sake fashewa da kuka, mami tayi saurin ciro takalmin ta zata doka mai da gudun sa ya shige mota har yana buga kansa yayi saurin sosa gurin cikin 6ata fuska kmr qaramin yaro zae yi kuka.
Mami tace"da kyau in ni abokiyar wasar ka ce hkn yayi dai dai gobe ka qara.
Baice komai ba sae sosa kansa yake yana kallon bintu dake ta mishi dariya har da su gwalo,da saurin sa ya d'auko wayar sa ya saito ta kmr zae jefe ta da gaske,ta saki qara tare da maqewa jikin mami.
Waheed ya ajiye wayar sa cikin dariya yace"matsoraciya kawai"
Daga hk yaja motar sa ya musu bye bye suma sae bye bye suke mishi har ya wuce snn suka koma daga ciki.

Tunda ya tafi bintu bata da wata kewa sae ta rashin sa a kusa da ita dmn duk dare kiranta yake suyi ta waya abinsu kyace saurayi da budurwa da suke cikin tsananin shauqin qaunar juna,hkn nayi mami dad'i ba kad'an ba wacce sam bata ta6a jin irin kishin da wasu iyayen keji ba idan d'ansu na matuqar bawa matar su kulawa sbd ita kanta shaida ce kan kulawar da bintu ke bawa waheed shiyasa take jin ita kam ta gama yin sa'ar suruka,yanzu babban burinta a rayuwa shine ta fara ganin en jikokinta.

Ranar da waheed zae dawo bintu da kanta taje kasuwa ita da hajjo sukayo siyayyar kayan abinci da na yin snacks.
Su dukan su har mami tare suka shiga kitchen dmn shirya mishi abinci kala kala kyace wani babban baqo ne zai zo.
Koda yake ba mamaki dmn a birnin zuciyar bintu shine kad'ai sarki babu wani mae mulki a cikinta face shi haka ma mami wacce duk soyayyar duniyar nn ta d'aura ta akan shi sbd waheed shi kad'ai ne d'anta qwaya d'aya tal a duniya wanda ta kwashe kusan shekaru goma da yin aure kafin ta sami cikin sa hkn yasa mahaifinsa yayi matuqar farin ciki har da su rabon kujerun makka sae dai kash duk irin farin cikin da yayi kafin a haifi waheed Allah yayi masa rasuwa sanadiyar had'arin jirgin sama da yayi garin zuwa siyayyar kayan baby,ba irin kukan baqin cikin da mami bata yi ba har ma ta d'auki alqawarin ko ta haifu baza ta qara yin wani aure a duniyar nn ba shiyasa da ta haifi waheed tasa masa sunan Abban shi tana kiranshi da waheed d only son knn na farkon kuma na qarshe.

Mami da kanta taje airport dmn d'auko shi ta bar bintu da hajjo dmn su qarasa shirya abinci.

Suna cikin jera abinci kan dining sae ga mami ta dawo daga d'aukar waheed sun shigo tare murna a gurin bintu ba'a magana dan kwana biyar d'inda yayi baya nn ba qaramin kewar rashin ganin sa tayi ba.
Dama sun kammala jera komai tayi tsaye cikin kyakkyawar kwalliyar da take d'auke da ita sae murmushi take masa tana kallon sa cike da so tana kuma jin kmr taje aguje ta rungume shi amma kash kunyar mami da hajjo sun hana mata yin hakan.
Haka ma waheed ba kad'an ba yaso ya jita a cikin faffad'an qirjinsa yana rungume da ita amma saqon murmushin ta kad'ai yasa yaji sanyi a ransa.
Cikin takon qasaita ya qarasa gurinta dae dai hajjo da mami sun bar falon ya rungume ta tsam ta bayanta tare da manna mata kiss gefen wuyanta bakin sa saitin kunnen ta cikin natsastsiyar murya yace"yau abun na rowa ne ko sannu da zuwa babu sae tsaye kawai kikayi kina kallona baki je kin tarbe ni ba"
A hankali bintu ta juyo ta d'aura tafin hannun ta kan kyakkyawan sajen fuskar sa tana kallon sa da kulawa tace"am sorry kunyar mami da hajjo ne yasa na kasa zowa in tarbe ka amma kayi haquri kaji i dnt mean to hurt u"
D'an kyakkywan murmushi ya sakar mata tare da d'aura mata kiss kan goshi yace"ba komai my lady sae dai wnn kwalliyar taki tana neman zautar dani dan a lokacinda na shigo na ganki ji nayi kmr shed'a ta zata fita idan banzo na rungume ki ba amma sae na tuna mami ta hana min tace in riqa natsuwa in daina yin komai a gaban kowa sbd akan bar halak dan kunya.
Bintu tayi murmushi cike da jin dad'in zancen sa
bata kuma ga laifin mami da ta hana shi ba dan waheed yayi qololuwar wayewar da in ta kama a gaban kowa zae iya rungume ta ya mata kiss ba tare da ya damu ba.
Tace"ae gwanda da mami ta maka haka dan kae ba ruwan ka na gani a gaban kowa zaka iya rungume ni kamin kiss ko meyasa?
Yace"kina son ki sani?
A hnkli ta lumshe idanunta tare da gyad'a masa kae.
Yace"to matso kiji"
Ba musu ta qara matsawa zuwa jikinsa se matso fuskar sa yake a hnkli har ya d'aura tsinin hancin sa a nata a natse ya lumshe ido tare da karkatar da kansa bintu da ta fahimci me zai yi tayi saurin girgiza kanta tace"no yaya mami zata iya fitowa yanzun nn ka sani"
Bae kulata ba sae jin bakin sa tayi a nata ya cafki harshen ta yana sucking a hnkli kmr wanda ya sami hadadden sweet d'inda baya son ya qare mishi,
haka itama ta biye mishi bata iya hana shi ba sbd cikin kewar sa take sosai.
Qarar bud'e ganbun da suka ji ne yasa sukayi saurin rabuwa mami ce ta fito ta qaraso gurin su d'auke da murmushi tace"waheed ya baka zauna kaci abinci ba?
kafin yace komai bintu taja masa kujera ya zauna ta kuma zuba masa abinci dai dai yanda tasan zai iya cinyewa,snn ta zuba musu nasu ita da mami sukayi zaune suna ci.

Bayan sun koma gida da dare waheed na kwance kan bed zir abinsa hankalin sa kwance kafar sa kan d'aya sae dannar wayar sa da yake can ya ajiye wayar sa had'e da d'an guntun tsaki yana kallon bintu dake jikin wardrobe d'aure da towel tana neman rigar bacci girgiza kansa yayi snn ya taso sannu a hnkli yazo gurinta tare da rungumeta ta baya bakin sa saitin kunnen ta yace"haba my lady wae me kk nema ne tun d'azu sae faman jiranki nake"
Ba tare da ta juyo ba ta shafo gefen fuskar shi tace"yi haquri rigar bacci nake nema"
Yace"wae duk rigunan baccin nn da nake gani baki sami wacce zaki saka a cikin su ba?
Ta juyo tace to ka za6ar min ni na rasa wacce zan saka a cikin su,
yace"um um my lady ni ko towel d'in nn bana son ganin shi a jikin ki bare wata rigar bacci,ni baki ga a yanda nake bane"
Bintu ta kalle shi d'auke da murmushi tace"uhm na ganka mana"
Yace"to haka nake so in ganki"
Shagwa6e fuska tayi tare da maqale kafad'a tace"to ni ka d'auke ni muje kan bed tukun.
Ba musu waheed ya d'auke ta cak ya tafi da ita sai kan bed da kanshi ya zare mata towel ya jefar snn ya kashe wutar d'akin suka shiga ba juna haqqin su.

Haka rayuwar su taci gaba abin sha'awa suna bawa junan su kulawa cikin so da qauna yayinda bintu ke ci gaba da karatun ta cikin kwanciyar hankali bata ta6a samun wata matsala a karatun nata ba har ta kammala ta kuma fara aiki abinta.

Durqushe suke gaban mami ta kirasu zatayi magana dasu duk sun natsu suna sauraren ta.
Cikin natsuwa ta soma magana.
Tace"waheed abinda yasa na kiraku shine a gaskiya na matsu in fara ganin en jikokina tunda Allah yasa bintu ta kammala karatun ta har ma ta fara aiki sae ku daina planning d'inda kukeyi haka ya isa.
A hnkli waheed ya numfasa yace"mami wlh ba wani planning da mukeyi lokacin haifuwar dai ne baiyi ba har yanzu"
Mami tace"Allah sarki ae ni duk a tunani na family planning kukeyi dan ka samu ta kammala karatun ta tukun shiyasa nayi shiru ban ta6a cewa komai ba sbd bana son abinda zae takura bintu duk da irin matsuwar da nayi inga en jikokina kuwa, amma in haka ne to bamu ga ta zama ba yanzun nn ka d'auke ta kuje asibiti a duba lafiyar ku da kae har ita aji meye matsala dmn a san abin yi.
Ba musu Waheed yaja bintu suka fito suna tafe cikin mota bintu ta kalle shi a sanyaye tace"yaya meyasa baka snr da mami cewa ina samun ciki amma zubewa yakeyi ba?
Hannun ta ya riqa yana kallonta da kulawa yace"bana son mami ta shiga damuwa ne amma yanzu kinga idan mukaje sae muji meye matsalar koh"
Qwallah tap a idonta ta gyad'a masa kae tare da fad'in"Allah yasa ba wata matsala ba ce"
Yace"amin"

Asibitin uduth suka tafi gurin wani abokin sa ya duba su.
Suna zaune a gaban shi suna jiran me zai ce amma ya kasa ce musu komai sae damuwa fal da ta bayyana a fuskar shi.
A sanyaye Waheed yace"Khalid ko baka fad'a ba na fhmci da akwai matsala gaya mana koma mene ne zamuyi haquri da qaddarar da ta same mu"
Khalid ya numfasa had'e da zare eyeglass d'in idonsa yace"kayi haquri da abinda zakaji daga baki na waheed a gsky mahaifar mtr ka ta samu matsala sosai sanadiyar zubar da cikin da tayi da farko ta kuma zo tana shan maganin da ko ta sami ciki ba zae zauna ba yake zubewa.
Zumbur waheed ya miqe cikin tsananin mamaki da firgici yana kallon bintu wacce a rud'e ta shiga girgiza kanta tana kallon Khalid kafin take kallon waheed tace"wlh na rantse maka ba wani magani da nake sha kuskure d'aya da na san na aikata shine zubar da cikin farko da nayi amma.......bata qarasa zancen ta ba taji saukar wani irin gigitaccen mari har sae da kunnuwanta duka biyu suka d'auka,ba shiri ta dafe kucen ta cikin tsananin rud'u tana kallon waheed da ya mare ta wanda lokaci d'aya duk ya fita hayyacin sa jikinsa har wani rawa yake idanuwan sa sunyi jajur sae huci yake kmr wanda zae je ya shaqeta abokin sa yazo sae haquri yake basa bae kulasa ba sae nuna bintu yayi da yatsa kmr wanda zae ce wani abu amma ya kasa sae fita yayi yabar office d'in da sauri.
Bintu sae kiransa take amma yaqi tsayi nn kawai ta durqushe qasa kan guiwoyinta ta fashe da wani irin kuka tana kallon Khalid ta had'e tafukan hannayen ta tace"Dr Khalid dan Allah ka taimaka min ka gaya masa gaskiya wlh ni ba wani magani da na ta6a sha kuskure d'aya nasan na aikata shine zubar da cikin farko da nayi amma sauran duk bani na zubar da su ba wlh.
Khalid yace"Bintu na rantse miki haka bincike na ya nuna min amma ba kuka zakiyi ba kije ki sami waheed ki bashi haquri ko Allah zae sa ya haqura.
Cikin kuka ta fito daga office d'in koda tazo inda suka faka mota waheed yaja motar sa ya tafi.

Ba yanda ta iya haka ta taka har gate ta samu keke napep ta shiga.

Koda ta isa gidan mami, ta sami waheed durqushe a gaban mami sae tambayar sa take me yake faruwa ne ina kabar bintu amma ya kasa cewa komai dan in yace yayi magana kuka kawai zaiyi a gurin.
Jiki sanyaye bintu ta qaraso kusa dashi ta zauna tare da sadda kanta qasa mami tace"bintu gaya min idan shi ya kasa gaya min waye mai matsala a cikin ku?
Qwallah tap a idonta ta d'ago ta kalli mami cike da niyyar snr da ita gskyr duk abinda ya faru.
Waheed yayi saurin hadiye kukan da yake ji yace"mami ba wata matsala bace kawai dai lokacin haifuwar ne bai yi ba"
Mami tace"amma shine naga kowannen ku cikin damuwa sosai kmr da akwai wata matsala gaya min gaskiya waheed bana son 6oye 6oye ka sani"
Waheed yayi shiru can yace"eh mami mahaifar fatima ce take d'an d'auke da matsala"
Mami tayi shiru tana kallon bintu dake kallon waheed hawaye na silalowa a hnkli kan kumatun ta tana mamakin meyasa zae rufa mata asiri bayan bata cancan ci haka a gurin sa ba,gwanda kawai ta gaya ma mami gaskiya koma me zae faru ya faru.
Ta kalli mami ba tare da ta iya cewa komai ba sae wani sabon kuka da ta fashe dashi.
Mami ta janyo ta zuwa jikinta sae rarrashin ta take tana fad'in"ki kwantar da hankalin ki bintu ko qasar waje ne sae munje an magance miki matsalar ki da yardar Allah zaki haifu baza ki gani agun wasu ba inshaa Allah.
Cikin kuka bintu ta girgiza kanta tace"mami na cuceku ban cancan ci haka a gurin ku ba"
Mami tayi saurin rufe mata baki tace"haba bintu daina fad'ar haka kar kiyi sa6o meye abun cutuwa a nn keda bake kika d'aurawa kanki wnn lalurar ba Allah ne ya d'aura miki dan haka kar in sake jin wata magana ta fito a bakin ki.
Bintu kuwa bata sake cewa komai ba sae kuka take ci gaba dayi mami na fmn rarrashinta.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 17_*
Zeenah tace"hm ai in tasan wata bata san wata ba tunda har ta riga ta zubar da na farkon nn wlh komai yayi zan qarasa sauran aikin da kaina.
Sarah tace"ae ni har na shiga tunanin yanda zamuyi da ita.
Kima daina tunani nasan yanda zamuyi da ita cikin sauqi kawo kunnen ki kiji.
Sarah ta tara kunne zeenah ta rad'a mata,sarah ta kwashe da dariya tace"zeenah kina wuta ina binki da fetur shiyasa nake sonki wlh"
Zeenah tace"amma kin san me zuwa gaba fa gaskiya aikin nn zae d'an yi mana wahala,wahalar ita ce harakan nn sae da en kud'i mu kuma ba wasu kud'i ne damu ba haka ma iyayen mu ko bokon nn qarfi duk da taimakon baban bintu ne ba danshi ba ma ae da tuni bokon nn namu ya ta6ar6are sae dai mu koma kan titi muna sana'ar toya qosai.
Hm ae taimakon dan ya zamar masa dole ne in bai taimaka musu ba ae zai ji kunya a matsayin sa na babban wa a gare su kawai kedai meye mafita yanzu.
Zeenah tace"gani nake me zai hana....ta qarashe mgnr a cikin kunnen sarah,
sarah ta dafe gaba tace"Anya zeenah ni kam ina tsoro...common dan Allah idan ba muyi haka ba to ta wace hanyar kk tunanin kud'i zasu riqa shigo mana yanda muke so.
Samarin yzn nn ba qwantuwa suke ba dole sae kana basu suke baka.
Amma to zeenah ba kya ganin da kmr had'ari...wane irin had'arin ae ba kowane gara ne zamu riqa haraka dashi ba sae wanda yasan kanshi.
To idan mukayi aure me zamu ce da mazajen mu?
Mtsw kar ki 6ata

Please Login or Register in order to submit comment