Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaci abincin ka kawai mu tafi dare nayi.
Nan ya jayo trayn abinci ya ajiye a gaban su, bintu ta d'ibar masa a plate tuwon semo ne da miyar ku6ewa d'anya sae qamshi ke tashi tasa hannu tana bashi a baki yana ci.
Yace"ke bazaki ci ba?
Tace"um um naci tare da mami"
Komai bai sake cewa ba taci gaba da ciyadda dashi har sae da yace ya ishe shi snn ta bashi lemu da ruwa yasha,yasa tissue ya share bakinsa ya kama lallausan hannunta ya share mata shi tas.
Duk abinda suke mami na tsaye a bakin qofa tana kallon su,
tana mae qara jin son bintu a cikin ranta er qarama da ita amma ta iya bawa miji kulawa.
Sallama ta musu da suka amsa snn ta qaraso daga ciki, bintu ta d'auki tray zata fita dashi zuwa kitchen
Mami tace"Aa kawo d'auki mayafi kuyi ku tafi goma har da mintina ga anguwar taku da d'an jayawa.
Bintu bata bata tray d'in ba tace ta bari kawai takai
Mami bata musa mata ba sbd tasan ko kad'an bintu bata so ta ganta tana wani aiki tace"to jeki kikai amma halinki ne na sani Fatima kin ga damar kice sae kin wanke kwanikan dan Allah kar kiyi hkn ki barsu Hajjo na nn zata wanke kinji,cewa da mai aikin ta.
Bintu tace"to" snn taje ta kai kwanikan bata fito kitchen d'in ba sae da tasa handwash ta qara wanke hannunta.

Da zasu fito Mami ta rako su suka shiga mota suka tafi snn ta koma daga ciki.


Washe gari da asuba waheed ya tashi bintu sae miqa take tayi dan ba kad'an ba waheed ya saukar mata gajiya a daren jiya.
Rumfa ya mata idanunta cikin nashi tana kallon shi cikin shagwa6e fuska tace"uhm yaya agajiye nake wlh kuma bacci bae ishen ba har ji nake kmr kar inje school yau"
Gefen fuskar ta ya shafo da kulawa yace"am sorry muje muyi wanka idan munyi sallah sae ki d'an qara yin bacci koh.
Tace"to yaya break fast fa"
Kar ki damu muje muyi wanka tukun.
Ya qarashe mgnr ne had'e da miqa mata hannu ta kama hannun nasa ta tashi suka tafi bathroom.

A nan inda sukayi sallah ko hijab bata iya cirewa ba tayi pillow da cinyoyin sa ta soma bacci.
Sae da baccinta ya d'anyi nisa ya cire mata hijab snn ya zame jikinsa a hankali yaje ya d'auko mata pillow ya kwantar da ita akai,shi kuma ya tafi kitchen ya soya musu arish da qwai da ruwan zafin tea.

Duk da yana gudun kar suyi letti bai yi saurin tada ita ba har saida ya kwatanci ta d'an sami yin bacci snn ya tashe ta suka shirya byn sunyi break fast suka bar gidan in time ba tare da sunyi letti ba.

Tunda qarshen sati yazo bintu ta soma shirye shiryen zuwa kebbi ta kuma tanadi tsarabar ta mae yawa da zata kai musu sbd wancan karon fushi bai bar ta musu tsarabar komai ba.
Kuma wannan karon tafi yin farin ciki sosai sbd Antin ta Hafsa da Antin ta nafee suma sunce mata a qarshen satin nn zasu je kebbi,rashin jin dad'in ta d'aya yayan ta Abdallah baya nn yana can zariya inda yake karatu.
kuma qarin damuwar ta shine wani babban yayan su mae suna Abbas dake aiki abuja yana nn yazo gida gashi ko kad'an basa shiri ita da dashi sbd rashin jinta komai tayi gwasale ta yake sam baya bari ta shaqata amma tunda aka kusa auren ta ya soma d'an d'aga mata qafa ko tayi wani abun rashin ji sae yayi kmr ma bai ganta ba.

Ranar juma'a da yamma suka tafi kebbi gida ya cika sae murnar zuwan su ake dan kusan lokaci d'aya suka isa dasu Antin ta Hafsa da nafee.
Iyayen su zeenah wato matan sauri ga umma ba murna a tare dasu sae tsegumi suke tayi suna ta maganganun banza da habaice habaice marasa kae dan kawai su samu a tanka su amma ko d'aya basu samu wanda yace dasu uffan ba har bintu kuwa da duk cikin su tafisu fad'a kuma tsaf zata iya ci musu mutunci ba ruwanta da matan qannan mahafin ta ne acewar ta tunda basu d'auki girman su ba itama bazata basu girman su ba.
Ko yanzu dan umma ne kawai yasa taqi tanka su sbd akoyaushe umma sae tace komai zasu ce su sa musu ido kawai kmr ma basuji ba sbd umma mace ce da bata son tashin hankali da anyi ance kuma ba yau ba tasan halin matan saurin nata rigima kawai suke nema ayi ta fad'ace fad'ace sam basa son suga mutum ya zauna lafiya dan har tsakanin su ma idan suka tashi ba ragawa juna suke ba.

Wannan karon mahaifin su yana nn sae murna yake da zuwan su yana ta sa musu albarka kan irin tsarabar da sukayo dan kaf gidan ba wanda basu mae tashi tsaraba ba.

Duk da cewa wnn karon bintu bata had'u da yayanta Abdallah ba sosai taji dad'in kwana biyun da sukayi sbd yayanta Abbas da take shakkun fad'an shi sam bae takurata ba sae ido kawai ya zuba mata tana abubuwanta.

Bayan sun koma sokoto ne rnr Monday da yamma bintu ta fito daga wanka taje gun dressing mirror ta zauna had'e da yaye towel d'inda ke jikinta ta d'aura tafin hannun ta a hnkli kan nipples d'in ta dake mata masifar ciwo da ta rasa gane dalilin hakan dan tun ba yau ba ta fara ji amma sae ta share bata d'auka ciwon zae ci gaba ba.
Janye hannunta tayi a hankali tana tunanin da kamar tasan cewa ciki yana kawo ciwon qirji.
Ras gabanta ya yanke ya fad'i ba makawa ciki ne da ita dan yau kusan three months knn rabon da taga tayi period gashi zuwan nn da tayi kebbi kowa sae cewa yake ta qara haske da kyau waheed kuma sae gaya mata yake qirjinta yana cikowa wanda tabbas ta fahimci hkn amma sam bata kawo ciki ne da ita ba sae yanzu.
Idan kuwa hakane ya zatayi da cikin nn dmn dae bata shiryi kar6ar sa ba tafiso sae ta qara shekaru dai dai ta kammala karatun ta.
Kwallah ne suka ciko tap a idonta a yanda take da qananun shekarun nn in tabar cikin nn zata iya kamuwa da ciwon yoyon fitsari kmr yanda su zeenah suka gaya mata.
Karar bud'e qofar da taji ne yasa ta maida towel a jikinta ta d'aura tana mai kallon waheed da ya shigo d'akin har ya qaraso kusa da ita yaja stool ya zauna d'auke da damuwar da ta bayyana a fuskar shi ya kama hannuwanta ya riqa yana mae kallon idanuwanta da suke cike tap da qwallah muryar sa a natse yace"me yake faruwa ne my lady?
Girgiza kanta tayi tare da saurin share hawayen da suka gangaro kan kumatun ta,
muryar ta can ciki mae cike da jin kuka tace"ba komai".
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*







*_page 11&12_*
Aa fatima da akwai komai gaya min mene ne.
Ba komai yaya ta fad'i hkne tare da neman alfarmar dan Allah ya barta tana son kasance wa ita kad'ai.
Ba yanda waheed ya iya ya tashi jiki sanyaye ya bar d'akin.
Haka ma Bintu jiki sanyaye ta tashi ta nemi er doguwar riga ta saka snn taje kan bed ta kwanta cike da tunanin mafita.
Tun lokacinda waheed ya fita d'akin bae sake dawowa ba sae guraren qarfe tara na dare da shigar sa d'akin,
bintu dake kwance cikin shirinta na bacci tayi saurin sa hannu ta share hawayen fuskar ta.
Waheed yazo kusa da ita ya zauna a natse sae kallonta yake har ta tashi zaune snn yace"fatima gaya min me kike ma kuka"
Kanta qasa ta girgiza kanta a hnkli murya can ciki tace"ba komai"
Shiru waheed yayi yana kallon ta ya shiga tunanin
shi kuwa me yake damun fatima da bata son gaya mishi.
Can yace"to tashi muje muci abinci"
Tace"um um na qoshi"
Me kika ci da har kika qoshi?
Ba komai amma na qoshi.
Aa hkn ba zae yiyu ba fatima tashi muje muci abinci kuma kar kimin gaddama.
Sosai taji ya takura ta dmn sam bata jin cin abinci damuwar da take ciki kad'ai ta ishe ta,amma ba yanda ta iya dole ta tashi suka tafi amma duk da haka ta kasa cin wani abincin kirki sae waheed ne yaci koshi ba sosai ba.

Daren yau sae ya zamo ma waheed ba dad'i sbd yanda bintu taje can nesa dashi ta kame guri d'aya cikin damuwar da take d'auke da ita amma kuma tausayin waheed na ranta dan tasan dole bazai ji dad'in yanayin da take ciki ba gashi kuma ya saba kullum idan baya sameta ba sam baya jin dad'i amma ya ta iya,
tana jinsa ko bacci ma ya kasa yi sae juyi yake tayi da qarshe ya tashi ya tafi bathroom ya d'auro arwala ya shiga yin nafilfli.

Washe gari haka ta tashi ba wani qwari a tare da ita komai a sanyaye take yin shi har suka bar gidan.
waheed ya ajiye ta school snn ya nufi gurin aikin shi cike da tunanin me ke damun fatimar shi da bata son snr dashi,
bcos ko da safen nn ma sae da ya tambaye ta tace mishi ba komai.

Bayan sun gama lectures ne suna zaune a bakin classes ita da su zeenah sun sata a gaba sae tambayar ta suke abinda ke damunta ko sunyi fad'a ne ita da waheed.
Tace"in fad'a ne da sauki akan abinda nake ciki"
Zeenah tace"Ayya mene ne kike ciki gaya mana idan wanda zamu baki shawara ne sae mu baki shawara.
Sae da bintu ta fitar da numfashi a hnkli snn tace"ina d'auke da ciki kuma bana son kowa yasan dashi sbd ban shiryi kar6ar sa ba"
Kallon juna sukayi sarah tace"meyasa baki shiryi kar6ar sa ba?
Sanin kanku ne a iya shekaruna banko isa ace na kammala secondary school ba dan anyi sakko sani makaranta ne yasa nayi saurin kammala ta amma har yanzu still en tsarana na can basu kammala ba.
Shiyasa nace muku ban shiryi kar6ar cikin nn ba sbd qananun shekaruna nafi son sae nn gaba tukun.
Zeenah ta nisa snn tace"ae kam dama nasan haka zata faru, ciki ba.....um um kar ki soma zeenah ni shawarar ku nake so ba wasu qananun maganganu ba.
Zeenah tace "har wata shawara ce kawai ki zubar da cikin mana"
Da sauri sarah ta kalli zeenah bintu kuwa tayi saurin girgiza kanta tace"Aa ni bazan iya ba ina tsoro"
Zeenah tace"au daa a tunanin ki me zakiyi idan baki zubar ba byn da kanki kince baki shiryi kar6ar cikin ba"
Nima ban sani ba zeenah kuma ina tsoron zubarwa amma ko kad'an wlh bana son cikin nn.
Hm tsoron me to kece farau ko ko akanki aka fara.
Ni ba haka ba ina tsoron kar in zubar wata matsala ta biyo baya.
Kawai kisa a ranki ba abinda zae faru.
To idan yaya waheed yaji fa?
A ina zaiji bayan kince ba wanda yasan da cikin sae mu kad'ai da kika gaya ma yanzu,kuma sanin kanki ne indai mune maganar nn baza ta ta6a fita ba.
Haka ne na yarda daku amma duk da haka ina tsoro da kmr bazan iya ba.
Zeenah tace"to tunda kina tsoro ae sae ki bar cikin amma ina ji maki tsoron kamuwa da ciwon yoyon fitsari sbd sanin kanki ne kinyi qanqanta da haifuwa kuma da idonki a nn asibitin kinga masu fama da irin wnn lalurar mafi yawan su duk qananun yara ne irinki da akayiwa auren wuri.
Bintu tace"nima abinda nafi jin tsoron sa knn kuma ko ba komai nafi son sae na kammala karatuna tukun dmn bana jin lokaci d'aya zan iya lalurar renon yaro da kuma karatu.
Nima shi nake jiye maki amma kije kiyi shawara tukun.
Tace"shikenan zanyi shawara"
nn ta tashi had'e da fad'in ni zan tafi gida a qafa nake son in taka yau.
Nan sukayi sallama da juna ta wuce.
Rae 6ace sarah ta kalli zeenah tace"haba dan Allah zeenah kan me zaki bata shawarar ta zubar da ciki,ae da kin barta dashi in yaso karatun ta ya ta6ar6are kowa ma ya huta.
Hm sarah ke karatun ta ya dama ni burina in lalata rayuwar ta gabad'aya ta kasance ba inda zata saka kanta taji sanyi,dan haka ki zuba min ido kawai idan bazaki iya ba danke na fahimci qaramar qwaqwalwa ce dake.
Shiru kawai sarah tayi bata ce komai ba.
Bintu kuwa tana isa gida shigar ta keda wuya waheed ya kirata a waya yana tambayar ta meyasa taje gida a qafa bata kirashi ya turo mata driver ba.
Tace"yaya ba komai haka kawai naji ina son in taka a qafa"
No Fatima bana so kar ki sake dmn na tabbatar kafin ki isa gida kin sami wani ya tare ki a hanya.
Shiru tayi sbd hkne d'in wani ya tare ta a hanya sae dai bata kula shi ba ta wuce,haka take fama kusan duk lokacinda ta fito ita kad'ai sae wani ya tare ta a hanya yace yana sonta shiyasa sam waheed baya son fitar ta ita kad'ai,rnr ma tare suka fita amma sae da wani ya tare su a hanya yace da waheed dan Allah ina son er qanwar nn taka kuma wlh da aure nake sonta,sosai waheed yaji kishi a ransa amma hkn ya jure ya masa bayanin cewa matar sa ce ba qanwar sa ba, haquri mutumen ya bashi waheed bai kula shi ba yaja bintu suka bar gurin.
Waheed ya katse ta da shirun da tayi yace"fatima kimmin shiru wani ya tare ki a hanya knn koh?
Bata ce mishi eh ba sbd bata son ranshi ya 6aci sae ce masa tayi yayi haquri.
Yace"ae baki min laifi ba Fatima kawai dai ina so ki kiyaye kinji"
Tace"inshaa Allah zan kiyaye"
Daga haka suka tsinke wayar bintu ta rage kayan jikinta,ta zamo daga ita sae vest da d'an guntun wando tsayin sa iya cinya.
taje kitchen ta d'aura musu abinci bayan ta gama taje tayi wanka ta shirya abinta cikin qananun kaya sae zuba qamshi take amma kallo d'aya zaka mata kasan cewa tana cikin damuwa da tunani sbd tun lokacinda ta baro school cike take da tunanin shawarar da zeenah ta bata.

Koda waheed ya dawo gidan ya same ta zaune a falo tayi shiru ga Tv na aiki amma hankalinta baya gurin.
Kusa da ita yaje ya zauna,
a sanyaye bintu ta d'ago ta kalle shi had'e da yi mishi sannu da zuwa.
Shima jikin nasa a sanyaye ya amsa dan dae ba haka ta saba yi mishi sannu da zuwa ba,da murnar ta take zuwa ta rungume shi cikin so da qauna ta mishi sannu da zuwa.
Numfashi ya fitar a hnkli snn ya tafi da ita zuwa cikin sa muryar sa a natse cikin kulawa Yace"Fatima dan Allah gaya min meke damunki kinji.
Kae tsaye taji qwalla sun cika mata ido sbd tambayar ta da yake yana qara saka ta a cikin damuwa gashi kuma bata iya snr dashi cewa ciki ne da ita kuma bata shiryi kar6ar sa ba.
Waheed dake kallon ta yasa hannu ya share mata hawayen da suka silalo kan fuskar ta.
Snn yace"tashi muje d'aki inji mene ne"
Bata musa masa ba yaja hannunta suka tafi d'akin shi cikin lallami da rarrashi yake tambayar ta amma bai gane komai ba sae ma kuka ta ajiye mishi kan dole yabarta.

Haka ta kwashe sati d'aya kullum cikin tunani da damuwa ta kasa yarda da shawarar zeenah dmn tana tsoron kar wata matsala ta biyo baya amma sam bata son zaman cikin,
gashi bata san wa zata kira ta sanar matsalar da take ciki ba a cikin antin ta Hafsa ko Nafee dan tasan fad'a zata sha na qwarai har sae ta gwammaci bata fad'a ba d'in dan har umma zasu iya snr ma idan kuwa umma taji kashin ta ya bushe.
Ga ciwon qirjin nn sae damunta yake wani lokaci da qyar ma take samu a gama lectures ta dawo gida.

Da yake yau weekend ne suna zaune a d'aki suna fira ita da Antin ta Hafsa waheed bai san da zuwanta ba sae da ya shigo d'akin ai kuwa da murnar sa suka gaisa yace"wlh dama ina son ganin ki hafsa tun washe garin rnr da muka dawo garin nn gabad'aya na rasa gane kan Fatima kuka take yi in na tambaye ta tace min ba komai duk satin nn haka ya qare min cikin damuwa ba yanda banyi da ita ba ta fad'a min in nayi mata wani laifin ne sae in bata haquri amma taqi ta gaya min wai ita ba komai.
Anti Hafsa ta kalli bintu wacce tun lokacinda waheed ya fara zancen sa ta sadda kanta qasa.
Tace"hm"kafin take maida dubanta ga waheed tace"kasan ina shigowa gidan nn kallo d'aya na mata na gano cewa tana cikin damuwa kuma duk tabi ta rame amma dana tambaye ta cemin tayi ba komai dan ta tashi daga bacci ne, duk da ban ganmsu da abinda tace min ba amma sae ban matsa mata ba sbd ban sani ba ko wata matsala ce a tsakanin ku da bata son kowa ya sani shine kawai yasa na basar muka ci gaba da fira, a niyar in zan tafi in bata shawara kan koma mene ne ta riqa haquri ta daina saka damuwa da yawa a ranta haka, sae gashi ashe kai d'in ma baka san meke damunta ba.
Wlh kuwa Hafsa kuma in nace in matsa tambayar ta kuka take ajiye min snn abincin kirki ma ta daina ci kuma ta daina bacci a d'akina shine nace inaga dae ni na mata laifi ban sani ba.
Bintu ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace"wlh yaya ni baka min laifin komai ba"
Yace"to meyasa kika qauracewa d'akina kika daina bani duk wata kulawa da kike min amma tun da kin rantse kince ban miki laifi ba kuma baza ki iya gaya min abinda ke damun ki ba ina son dan Allah ki snr da Hafsa damuwar ki dmn ta baki shawara a sami mafita in samu in daina ganin ki a cikin damuwar nn fatima wlh bana jin dad'i ko kad'an kuma kin sani. Bintu tace"yaya na gaya maka ba komai"
Rai 6ace Anti Hafsa tace"wlh zan mareki in kika sake fad'ar ba komai d'in nn very stupid kin maida mu qananun yara ne da bama gane damuwa ko me!
Kuka bintu ta fashe dashi
Waheed yace"Aa Hafsa dan Allah ki mata a hankali.....wane irin na mata a hankali bayan kace ba irin lallashin ta da baka yi ba amma taqi gaya maka.
Kiyi haquri dae dan Allah ki lallashe ta har ki samu ta gaya miki ni bari in fita.
Bai jira amsar ta ba ya fita.
A natse anti Hafsa tace"haba bintu kince ba komai kuma kince waheed bai miki laifin komai ba to me kike so kice damu ki dubi yanda bawan Allah nn duk yabi ya rame lokaci d'aya sbd damuwar da kika saka kanku a ciki shin ba kya jin tausayin sa ne idan ya miki wani laifin ne a rashin sani ki gaya masa mana sae ku sulhunta kanku.
Bintu tace"wlh Anti bai min laifin komai ba"
To gaya min me yake damun ki kuma kar kice min ba komai.
Damuwa ta d'aya ce Anti test6 d'in da mukayi last week shine naji ance da dama ba'a ci wani abin qwarai ba shine duk nabi na damu kar in kasance cikin wa enda basuci abin qawarai ba.
Ajiyar zuciya Anti Hafsa ta sauke tace lallai bintu son karatun nn naki yana neman zautar dake hm kai ni ban ma yarda da zancen nn naki ba har kece zaki saka damuwa har da su kuka akan jin tsoron fad'uwar test keda sam ba kya wasa da karatu bare kiyi tunanin fad'uwa.
A d'an daburce tace"Anti ni gaskiya na gaya miki kuma komai dagewa ta akan karatu ae sae Allah ya cishe ni snn ko zanci".
Au kin san da haka shine baki roqi Allah ya cishe ki d'in ba zaki wani saka damuwa a ranki har dasu kuka,ni ban yarda ba gaya min gaskiyar abinda ke damunki ko kuma wlh in snr da umma.
Ganin antin ta na son gano ta tashi cike da kukan shagwa6a tana fad'in"haba Anti Hafsa gaskiya ni ki daina min haka ae kinsan bazan miki qarya ba ko umma kika kira wlh abinda zan iya gaya mata knn uhm uhm....ta bar d'akin cikin kuka ta nufi falo,
waheed dake zaune a falo ya taso cikin sauri ya qaraso gurinta ta fad'a jikinsa tana ci gaba da kuka.
Kafin yace komai sae ga anti Hafsa ta fito cikin damuwa yace"haba Hafsa keda nace ki mata a hankali shine zaki sake saka ta kuka Allah dai yasa ba dukan ta kikayi ba"
Murmushi Anti Hafsa tayi tace"ae kasan halin bintu ni ba abinda na mata daga kawai ta gaya min damuwar ta nace ban yarda ba shine fa, kaji kaji kaji ta gaya masa duk yanda sukayi da bintu.
waheed yace"to Hafsa ae kinsan karatun secondary school da wnn ba d'aya bane, wnn yafi wuya nesa kinga dole ta d'an saka damuwa a ranta har dai yanda akace mutane da dama basu ci ba.
Anti Hafsa tayi murmushi tare da fad'in to ae shikenan na yarda sae ki daina kukan.
A hnkli waheed ya shafo gadon bayanta d'auke da murmushi a fuskar sa bakin sa saitin kunnen ta yace"kinji anti Hafsa tace ta yarda daina kuka hk kar kisa baby na yayi baqin rai.
Da sauri ta d'ago cikin fargaba tace "wane babyn"
Hancin ta ya lakato snn yace"babyn ina fata mana"
Dukan shagwa6a ta kai masa a qirji snn ta rungume shi tana sauke ajiyar zuciya a hankali.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 13,14,&15_*
Saurin d'agowa tayi daga kan qirjinsa sbd tuna cewa Antin ta Hafsa na tsaye a gurin sae dai koda ta duba bata ganta ba ashe ta tafi d'aki tace"yaya bari inje inga anti Hafsa tace min ba jimawa zatayi ba akwai inda take son taje.
Ya gyad'a mata kae ta tafi ya hard'e hannuwan sa a qirji sae kallon ta yake har ta shige d'aki snn yayi murmushi had'e da girgiza kansa yace"fatima iyayen rigima Allah ya nuna min kin haifa min baby inga ya renon zae kasance er zan kama ko mamar.

Koda bintu ta isa d'aki ta samu har anti Hafsa ta d'auko jakarta zata fito bintu ta 6ata rae tace"haba Anti ba dai har zaki tafi ba"
Tace"Bintu kinsan na gaya miki sauri nake ba jimawa zanyi ba na biyo ne kawai in ganki"
To anti me zaki ban kafin ki tafi?
Er dariya tayi tace"kmr ya me zan baki"
Anti ina wani turaren da kika ta6a bani mae dad'in gaske d'in nn ya qare min kuma wlh ina son shi ya za'ayi?
Yako za'ayi qwara d'aya kacal nake da shi yanzu hk,ta ciro shi a cikin jaka tace kin ganshi kuma shine nake aiki dashi ba kuwa zan baki ba sae dai in nemo maki.
A shagwa6e tace "Plz anti ki bani shi sae ki samar ma kanki wani"
Tace"Aa kedai zaki haqura har in samar maki dan gskiya bana son wnn turaren ya katse min.
Uhm haba dae Anti dan Allah
Hm ni kinga tafiya ta nasan

Please Login or Register in order to submit comment