Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa zeenah tace"hm ke yarinya ce bintu baza ki ta6a gane illar d'a namiji ba sae nn gaba idan ya maki illah daga lokacin da kika fara haifa masa 'ya'ya ya daina ganin sha'awar ki kwata kwata sae dai ya kwaso miki er duniya wacce ta jiqu cikin boko ya aura suci gaba da soyewa abinsu ke kin zama uwar 'ya'ya ba'a da lokacin ki walaqancin yau daban na gobe daban,ke baki ga miji baki ga boko sai dai kiyi ta zaman renon 'ya'ya da ganin wulaqancin sa da kuma wulaqancin kishiya.
Rai 6ace Bintu tace" kunga ku dakata wlh bazan d'aukar maku ba iyayenku suyi da mamana nima kuzo kunayi dani,
to kusani ko mama ba tsoron iyayen naku take ji ba fa ta sa musu ido ne kawai.
Gabad'ayan su kallonta suke tunda ta soma zancen.
zeenah ta nisa tace"Allah huci zuciyar ki me kuma ya kawo zancen iyaye byn sanin kanki ne mu kan mu bama jin dad'in abinda iyayenmu ke yiwa ummarki,komu ma muna baki shawara ne ganin ki na er uwar mu"
Hm zeenah knn wnn baqin bakin da kuke min shine shawara a gurin ku,ko kuma auren ne kuke so in kashe in koma gidan ubana da zama ku gaya min.
Sarah tace"calm down bintu mufa ba muna baqin ciki da auren nn naki bane,muna baqin ciki ne kan rashin karatun nn da Abbanku baya bari kuyi,secondary certificate is nothing bazata amfane ki da komai ba, gashi namiji dai ba abin dogaro bane komai kud'in sa gwanda kiyi boko ki sami ilimi kina d'an aikin ki yafi, wasu en lalurorinki duk ba sae kin tambaye shi ba.
Zeenah ta gyad'a kae snn tace"kedai gaya mata abinda muke so ki fahimta knn"
Bintu ta nisa a hnkli tace"olryt ynx na d'an fahimce ku ina kuma yi muku albishir d'in cewa ni ynx am free Abba ya barni inyi karatu"
Da sauri suka kalli juna d'auke da mamaki snn suka kalle ta tare suka ce da gaske kk!?
Wlh kuwa zuwan nn da mukayi kebbi komai ya kammala zancen samar min admission ma yaya keyi ynz haka.
Sarah tace"ikon Allah ya akayi Abbanki ya yarda cikin sauqi haka?
Hm dama fa ashe Abba burin sa ya auradda mu tukun in mazajen mu sun yarda muyi karatu ba matsalar sa bace kawai dai yana mana fatan alkairi su anti duk basu fahimci haka ba dan bai ta6a nuna masu ba shiyasa da sukayi aure ba wanda yayi tunanin yin karatun a cikin su.
Zeenah tace"Iyye kinji dad'i mun miki murna sosai,wace school zakiyi apply?
School d'in ku mana kunsan burina inyi aikin asibiti koda a iya nurse ne.
Sarah tace"Hm toh mu dae bari mu d'an ci musha sauri muke zamu koma hostel muna da abin yi"
Nan suka ci suka sha sae fira suke guraren six suka ce sun tashi tfy bintu ta raka su har gate snn ta koma daga ciki.
Da yake gidan ba
nisa da school d'insu da qafa suka taka,suna tafe sarah ke cewa"hm nifa zeenah kinsan Allah wlh ko kad'an banji dad'in da aka bar bintu tayi krtn nn ba dmn ko kad'an bana sonta da qaruwa gata da shegen qoqari......hm ni ba wnn ne ya dame ni ba Sarah babban baqin ciki na shine auran nn da ta riga mu yi,shine nake son ko ta halin qaqa in lalata auren ta hanyar saka tsana a tsakanin su.
Ta yaya zeenah aure dai an riga da an d'aura kuma dukkan su suna matuqar son junan su bana jin zaki iya yin nasarar saka tsana a tsakanin su har ta kaisu ga rabuwa.
Hm sarah ki duba fa ki gani mun fa girme ta nesa amma har yanzu ba wanda yaxo da niyyar auren mu bare zancen mu tsayar,ae ko sune Romeo and Juliet sae nabi duk wata hnyr da zanbi na ganin cewa na raba su in yaso duk mu taru mu da ita mu zauna ba aure hkn ya fiye min dad'i a raina.
Sarah tace"Kinada boka a hannu ne?
Ko d'aya ba boka ba malam kawai kedai ki zuba ido kiga aiki da cikawa.
Aa zeenah nasan zaki iya amma da kin barta ko dan irin shirin da muke a tsakanin mu, idan lokacin mu yayi ae muma zamuyi auren.
Baki san irin abinda nake ji bane Sarah wlh duk lokacinda na tuna yarinyar nn tayi aure bamuyi ba sae inji zuciyata ta cika tap da qunci da baqin ciki duniyar nn inji tamin baqiqirin ba wani hasken rahama a cikinta.
Ni kaina zeenah naji baqin cikin hk sosai,a school tafi mu qoqari,idan muka shiga mutane dangi ne koma a ina ne kowa ita yake jin yana ra'ayi mu ko oho,hk samari sae rububin neman aurenta suke kmr wata er gold tana ta wulaqan tasu sae waheed ne ya ciri tuta har yayi nasarar aurenta da shima ina zargin ba don komai ta aure sa ba sae don kud'insa in ya mutu suci dukiya ita da munafukar uwar ta dake ta wani nn nn dashi.
Cikin dariya Zeenah ta bata hannu suka tafa tace"ashe kina da fahimta da farko har na d'auka ko baki san komai ba amma tunda na fhmci kin gane sae kizo mu had'a hannu mu 6ata musu duk wani shirin su,gashi da ita har ummarta sun gama yarda cewa mu masu qaunar su ne bama jin dad'in abinda iyayen mu suke musu kinga ta hk ne zamuyi nasara cikin sauqi mu lalata musu duk wani shirin su.
Sarah ta kwashe da dariya had'e da bawa zeenah hannu suka tafa.

6angaren bintu kuwa tana komawa ciki kae tsaye kitchen ta nufa dmn girka musu abincin da zasu ci da dare ita da waheed.
Koda magrib tayi ta kammala girki,
tayi sallah ba ita ta tashi ba har sae da akayi sllr isha'i tayi sll snn ta tashi ta fad'a bathroom tayi wanka ta shirya cikin qananun kaya,riga da wando,rigar fara ce handless anyi qatuwar pink heart a gaban rigar,hk klr wandon pink ne skinny yayi d'as a jikinta kmr er baby har dai yanda ta tufke gashin kanta da pink ribbon abun sha'awa sae zuba qamshi take taje falo ta kunna TV tayi zaune tana jiran dawowar waheed dan ce mata yayi sae bayan isha'i ko zae dawo sbd wasu en biye biye da zae yi a cikin gari.
Zaman ta keda wuya taji shigowar motar shi da saurinta ta fita ta tarbo shi suka shigo tana manne a jikinsa sae yaba kwalliyar ta yake.
Kae tsaye room d'inshi suka nufa ta bashi ruwa masu sanyi yasha snn ta taya shi ya rage kayan jikinsa tace "zakayi wanka ne ko sae munci abinci"
um um sae munci abinci tukun dan yunwa nakeji.
Nan taje ta d'ebo
musu abinci suka ci byn sun gama ne waheed ya nemi ta raka shi bathroom dmn ta taya shi wanka,a shagwa6e ta maqale kafad'a ita bazata ba wae bata so ta 6ata kwalliyar ta,bae bi ta kanta ba ya d'aga ta cak sae wuntsil wuntsil take da qafafu har ya tafi da ita bathroom ya kad'a ta tsumbul sae cikin bahon wanka bintu me zatayi ba kuka ba ta kuma d'ebi ruwa sae watsa masa take shi kuma sae dariya yake yana kare saukar dukan ruwan da take watso mishi, ya bita cikin bahon shima sae watsa mata ruwan yake yana ramawa sukayi ta wasa da ruwa kmr wasu qananun yara har sae da suka gaji dan kansu snn sukayi wanka.
Koda suka fito bathroom d'in ko towel babu a jikin su, kae tsaye kan bed suka fad'a, bintu ce qasa waheed na samanta ya mata rumfa bakinta cikin nashi sae kissing d'in juna suke cike da qwarewa kmr wasu turawa,d'akin yayi tsit qarar komai baka ji sae sautin numfashin su dake fita a hnkli suna ci gaba da aikawa juna saqonni ta koina har suka je ga babban aiki.

Washe gari kasancewar weekend ne waheed bai fita ba yana zaune falo shida bintu kan doguwar kujera tana kwance kan cinyoyinsa tayi pillow dasu tana game da wyrta,shima yana riqe da tashi wyr yana danne danne,cikin hk sae yi suke suna fira abinsu.
A cikin firar su Bintu ke cewa"yauwa yaya jiya na manta ban gaya maka ba byn ftr ka su zeenah sun zo da zasu tafi sunce a gaida ka idan ka dawo.
"Ina amsawa"
Shine kad'ai abinda yace yaci gaba da danne dannen shi.
Ko kad'an waheed baya son shirin su da bintu haka kawai yaji yaran basa birge shi kwata kwata amma ba yanda ya iya en uwanta ne dole ya hqr ya barsu.
Bintu dake kallon sa tace"yaya zancen makaranta ta baka tambaye ni wacce nake so ba"
Wace school kk so my lady gaya min.
Sunan da yake kiranta dashi knn wani lokaci kuma bintu na jin dad'in sunan.
Tayi murmushi snn tace"yaya ae kasan bani da wani za6i da ya wuce school of nursing dake nn kusa damu cikin uduth"
Yace"ni bana sonta ki canza wata"
A shagwa6e ta tashi zaune tana kallon sa tace"yaya meyasa?
Sbd kawai bana so
Uhm Plz yaya.
Fatima da akwai dalilin da yasa bana son kiyi krt a can nasan halinki da kin had'e dasu zeenah duk wata shiririta ta gamu.
a'a yaya da yardar Allah hkn ba zae faru ba nayi ma alqawari kuma kasan ni ae bana saka wasa a karatuna lokacin karatu karatu nakeyi.
Waheed yayi shiru sbd yasan gaskiya ta fad'a, amma sam baya son suyi school d'aya dasu zeenah duk da cewa su a year 2 suke ita kuma bintu yanzu ne ma zata fara krtn.
Bintu dake kallon sa kmr zatayi kuka tace"yaya plz"
yace"Shike nn naji amma zanyi waya da umma na gaya mata idan tace ta amince to kin yarda.
Eh na yarda kirata d'in,
Aa ba yanzu ba sae anjima tukun.
Uhm yaya ni ynzu nake son ka kirata.
Ba kati a waya ta.
Cike da shagwa6a ta d'an doddoka qafagunta a qasa had'e da fad'in"uhm wlh Allah ba za'a rasa kati a wyr ka ba sae dai in bazaka kirata ba.
Fatima ni as wa da baza'a rasa kati a wayata ba"
Cikin turo baki tace"Kae a manajan banki mana"
Waheed yayi er dariya snn yace"to dan ina manajan banki shikenan baza'a rasa kati a wayata ba"
Cikin muryar kuka tace"Eh mana sae dai idan bazaka kirata ba"
Waheed dake kallon ta yayi murmushi had'e da jan karan hancinta yace"naji iyayen rigima kar ki min kuka bari in kirata"
Bintu najin hk ta saki murmushi had'e da maqale masa kan jiki shi kuma ya shiga dialling numbar umma ringin d'aya biyu ta d'aga suka gaisa cike da fara'a snn yace"umma dama bintu ce ta ajiye min rigima ita sae mkrntr su Sarah take son in samar mata admission shine nace bari in kiraki in snr dake idan kin amince to ba matsala.
Umma tace"bani ita idan tana kusa"
Waheed ya bawa bintu waya sae dariya yake mata ciki ciki dan yana farawa umma bayani ta turo baki shaye da toka tana kallon sa dan ta riga da tasan gami ne ya mata da umma.
Tana kara wyr a kunnen ta umma tace kinaji na baza kije wnn mkrntr ba ya nema miki wata ae ba ita kad'ai ce school of nursing a cikin garin ba.
Bintu kmr tana ganin umma ta 6ata fuskar ta cike da shagwa6a tace"Uhm to Mama ae tafi sauqi dan ta fi kusa damu kuma gasu zeenah da suke year 2 sunce zasu riqa nuna min wasu abubuwa ta yanda zanji sauqin krt.
Owo!Ae dama nasan dalilin su zeenah kad'ai kk so kije wnn mkrntr in yaso ku taru duk ku soma rashin jin da kuka saba.
to bari kiji in gaya miki bake ba wnn mkrntr ya nema miki wnn d'ayar school of nursing d'in dake cikin gari kuma kar inji kince komai.
Kuka bintu ta fashe dashi sosai ta kuma cillar da waya kan kujera ta tafi da gudu zuwa d'aki.
Waheed ya d'auki waya ya kara a kunnen sa umma tace"kana ji waheed komai kukan da Bintu zatayi kar ka biye mata dan ita ba ciyon kanta ta sani ba.
Waheed yace"Aa umma ayi haquri a barta kawai taje mkrntr da take so tunda kinga bata wasa da krtn ta ko suna tare"
Kafin umma tace komai sae da ta girgiza kanta sbd tasan ba komai yasa waheed yayi saurin cewa abarta taje school d'in da take so ba sae dan ko kad'an baya son 6acin ran bintu.
Tace"amma Waheed inace ka gaya min ne sbd baka ra'ayin taje wnn mkrntr koh"
Eh to umma amma dama zanji ra'ayinki ne tukun idan kin amince shikenan a barta d'in ni a gurina ba komai.
Waheed wato halin bintu ne na sani idan ta had'u dasu zeenah sae ka gaji da qorafe qorafen mutane,ko lkcn ba islamiya ba,ba boko ba kullum in suka je sae an kawo mana qarar su kuma babbar uwar rashin ji a cikin su itace bintu su kuma sune masu shiga mata fad'a.
Mama ae yanzu kinsan girma ya kawo musu baza suyi wnn shirmen a high school ba.
To waheed Allah yasa dan bintu kam har yanzu tana fama da quruciya a cikin kanta tunda dududu ba wasu shekaru ne da ita ba su zeenah ne kawai suka soma yin hnkli suda suka fita shekaru amma idan har kana ganin ba wata matsala shike nn ka nema mata mkrntr su zeenah d'in fatana dukkan su Allah ya basu sa'a su kammala karatun su ba tare da sun sami wata matsala ba.
Amin amin umma mun gode.
Daga hk ya tsinke wyr yaje d'aki ya sami bintu kwance ruf da ciki kan bed sae rusar kuka take.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*






*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 6_*
A natse yaje gab da ita ya zauna tare da d'aura hannun sa kan gadon bayanta
cike da son ya rarrashe ta.
ture hannun nasa tayi ta kuma tashi zata bar masa gadon yayi saurin janyo ta zuwa jikinsa yana rarrashi cikin son yi mata bayanin yanda sukayi da umma,da sauri tasa hannuwanta duka biyu ta rufe kunnuwanta ita bata son jin komai daga gare shi tunda har ya mata gami da umma.
Bai fasa rarrashin ta ba cikin kalaman nn nasa masu dad'i da tausasa zuciya har ya samu yayi nasarar janye hannuwanta da ta rufe kunnuwanta yana fad'in"haba my lady na am sorry kinji bazan qara miki irin haka ba kuma albishirin ki"
A shagw6e cikin kuka ta maqale kafad'a ita bata son ji.
Yace"umma fa ta amince na samar miki admission a school d'inda su zeenah ke karatu"
Sake maqale kafad'a tayi tana kallon sa ita bata yarda da zancen sa ba wasa yake mata.
Yace"Allah my lady da gaske nake gaya miki na bata haquri ta kuma amince amma da sharad'in duk kika yi wani abinda ba dai dai ba in gaya mata shike nn sae a cire ki daga karatun gabad'aya ko wata makarantar ma baza a nema miki ba sae dai kiyi ta zama a gida kina kallo su zeenah naci gaba da karatu abinsu"
Bintu dake kallon sa idanun ta cike da qwallah tace"inshaa Allah yaya nayi alqawari bazan yi wani abinda ba dai dai ba"
D'auke da murmushi yasa hannun sa ya share mata hawaye yana fad'in "yauwa to shike nn yi shiru daina kuka"
Nan taje a hnkli kan faffad'an qirjinsa ta lafe abinta tana sauraren yanda yake shafar gadon bayan ta a hnkli cikin natsuwa kmr wata er baby.


*_1 month later_*
Tuni bintu ta fara zuwa school sae jin take yanzu gabad'aya bata da wata matsala a rayuwarta,
dama babban burinta shine tayi karatu kuma gashi Allah ya taimake ta ta fara abinda bata ta6a zato ba.

Tafe suke ita da su sarah sun rako ta zasu fito gate d'in uduth sae rarraba ido bintu keyi ko zata hango motar waheed tafe.
Zeenah dake kallonta ta le6ace baki snn tace"hm dama kin daina wani dube dube dan ga dukkan alama waheed ya manta dake"
Sarah tace"lallai dae kam ace tun d'azu da kuka gama lectures kin kirasa ya turo miki driver amma har yanzu shiru munyi zaman jira har gamu zamu fito gate ba alamar motar shi tafe gashi ba ko gida zaki je ba bare ki taka a qafa.
Bintu tace"shi ne wlh amma bana tunanin yaya waheed ya manta da akwai dai abinda ya tsaida drivern.
Zeenah tace"hm haka dai kk gani wata qil ko kiran sa ma baiyi ba yana can yana harkokin gabansa da suka fi masa muhimmanci.
Kafin bintu tace komai sae ga motar waheed ta faka a gaban su wato drivan nata yazo d'aukar ta,da saurin sa ya sauke glass yana fad'in"dan Allah hjy ayi haquri wlh go slow ne ya tsaida ni.
Bintu tace ba komai snn ta kalli zeenah tace"inace yanzu kin tabbatar nafi komai muhammanci a gurin yaya waheed kuma ba manta ni yayi ba ehe.
Ta qarashe mgnr ne had'e da mata gwalo ta kuma yi saurin bud'e mota ta shige sae dariya take sbd dukan da zeenah taje kaimata bata same ta ba.
Ta rufe ganbun mota snn tayi ma sarah hannu tana fad'in"Bye Sarah keda kk da d'an hnkli hnkli ke kad'ai zanyiwa bye bye.
Da sarah har zeenah dariya sukayi had'e da yi mata bye bye har motar su ta fita snn suka kama hanyar komawa hostel zeenah ta qyalqyace da dariya tana kallon sarah snn tace"sarah mae d'an hnkli hnkli"
Sarah tace"uhm barta abin tausayi sae nn gaba zata gane ainihin sarah.

A 6angaren bintu kuwa suna fitowo gate ta snr da driver gidan antin ta Hafsa zai kaita.
Da yake anguwar ba wani nisa,
take suka isa.

Yana kaita ya juya bae jirata ba kmr yanda ta buqata.
Tana shiga harabar gidan ta had'u da twins en qananun yara maza su biyu suna ball.
Suna ganin ta suka zo da gudu.
Anti oyoyo!anti oyoyo!
Cike da murna Bintu ta d'auke su tana fad'in"yeeh Abba da daddy kuna lfy ina maman ku"
D'ayan yace"mama aya ciki aya kayyo"
Bintu ta fashe da dariya tana fad'in"hehehe lallai anti shine tace min kun iya magana narai narai har ma zaku iya saida mutum ashe yamin baki ma kuke.....Aa bazan daukar miki ba kar ki ma 'ya'yana sharri.
Cewar wata kyakkyawar mata da ta fito er sililiya fara tas hanci har baka kmr bafillata duk dae kmr su d'aya da bintu dan kallo d'aya zaka musu kasan en uwan juna ne.
Bintu tace"ba wani sharri anti ai kinsan gaskiya na fad'a ina 'yata ilham?
Hm er ki mae halinki da qyar yau in gaya miki na samu taje islamiya wae tunda taji zaki zo ita bazata ba Abbanta yaja ta suka tafi sae kuka take.
Bintu tace"Allah sarki ilham ae zata dawo ta sameni ina nn sae bayan isha'i"
Uhm iyayen rigima ae saida na gaya mata hk amma taqi yarda,sorry zo mu shiga daga ciki na barki tsaye.
Ae na d'auka ko wani abu ya fito dake anti.
Inafa muryar ki na jiyo kina ma 'ya'yana sharri shine na fito.
Uhm wae anti kina fad'in na musu sharri bayan ga gsky nn a bayyane basu iya magana ba sae yamin baki sun kasa iya magana har yanzu.
Bintu ta qarashe mgnr ne had'e da zama kan kujera dan koda take mgnr sun shigo daga ciki ta sauke yara suka koma abinsu waje suka ci gaba da ball.
Anti Hafsa ta kawo mata lemu da ruwa had'e da abinci ta zauna tana fad'in"Bintu er boko shike nan kin mana wayo kin fara school abinki sae naji kmr nice wlh amma ina karatu ya min fintinkau"
Bintu tace"kan me zaki ce hk Anti hafsa ae ko yanzu bata 6aci ba kina iya kiyi karatun ki meye matsala ko ganin kk yara baxa su barki ba"
Hm Bintu ae in ta yara ne ma da sauqi Abban ilham ne bazai barni ba,ba irin roqon da ban masa ba kan nima ya barni inyi karatu nn wlh ya bushe ido yace ba wani karatu da zanyi,nayi kuka har nagode Allah ke har kukan ma yaja min zazz6i amma mutumin nn yaqi tausaya min.
Bintu tace"cabd'i yanzu anti duk irin qaunar da yaya Yusuf ke maki amma yaqi ya barki bayan yaji labarin Abba yace ya yarda muyi karatu idan sun bar mu.
Hm bari kawai ae yaya Yusuf d'in ne da kishi kinsan fa tunda akayi auren mu baya bari in fita koina sae da niqab.
Bintu tace "to Allah kyauta,Haka itama Anti Nafee da naje gidan ta kwanaki ta gaya min da qyar ne ko yaya sadiq zae barta dan taga ko mgnr karatun ma baya son ta mishi,nace taci gaba da lalla6a shi ko Allah zae sa tayi nasara.
Anti Hafsa tace" to Allah yasa ta dace d'in"
Bintu tace"Amin"
Wacce sae a snn ne ta fara cin abinci byn ta gama suka tsiri wata firar.

Nan bintu ta yini har bayan isha'i snn ta soma shirin komawa gida.
Zaune suke kan bed Anti Hafsa ta bata kayan mata tana mata bayanin yanda zatayi amfani dasu.
Bintu tace"Anti Hafsa da kin barsu"
Anti Hafsa tace"meyasa?
Er dariya bintu tayi snn tace" Hm bari kawai kedai Anti kwanaki da kika bani wasu na gwada hahaha daren rnr na darzu a gun yaya waheed in gaya miki wlh har saida na masa kuka snn ya barni hkn bae hana da safe ya sake nema na ba,hm ni na rasa wane irin mutum ne shi da sam baya gajiya da wnn harakar.
Anti Hafsa tace"ba dole ba ya had'u da er shila"
Hm anti knn ko ba hk ba kinsan fa na cika cin dabino,kwakwa,rake,jiqaqqar aya,mazanqwaila,duk gabad'aya nabi na maida su qwalamata,har shi kanshi yaya waheed na koya masa cinsu da kullum in ya fita sae ya siyo mana, gashi bini bini duk sae nayi mana kunun aya kuma duk dare kafin mu kwanta idan bana sha madarar pick ta ruwa ba bana jin dad'i.
Anti Hafsa dake sauraren ta tayi dariya snn tace"kice ke kika sa waheed ya iya jaraba"
Uhm wlh kuwa anti kullum idan ba ya neme ni ba baya jin dad'i har ma ya saba min da halin shi dan wata ran da kaina sae in neme shi mu kashe juna da soyayya.
Ta qarashe mgnr ne cikin dariya.
Anti Hafsa ta girgiza kae tace"oh bintu ba kunya"
wace kunyar kuma anti mijina ne fa abun qaunata da mukayi auren so bana qiyaya ba.
Murmushi kawai anti Hafsa tayi had'e da girgiza kanta snn tace"nidai gaya min still d'in baza ki tafi da kayan ba ko kuwa?
Bintu ta kar6i kayan ta jawo bedside drawer ta maida tana fad'in"ki barsu kawai anti dan wa en can ma da kk ban suna nn basu ko qare ba"
Nan ta hango wani abu a cikin bedside drawer d'in tasa hannu ta d'auko snn tace"Anti wnn abun fa ya ake amfani dashi gaya min ina so ya ban shawa"
Da sauri anti Hafsa ta kar6e tana fad'in "iya kanki wlh wnn na manyan mata ne ba irinku da ko haifuwa bakuyi ba"
Bintu ta shgwa6e fuska tana kallonta kafin tace komai anti hafsa taja hannun ta tace"tashi muje in rakaki ga drivern ki can yazo sae oda ake tayi.
Bintu ta tashi ta d'auki mayafinta da jakarta tasa takalmi tana fad'in "yau anti korata ma kike"
Na isa ba korar ki nake ba rigima dai naga zaki

Please Login or Register in order to submit comment