Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kad'an ba sunyi nadama da baqin cikin abubuwan da suka faru,dan suna biye musu ne kawai ba tare da sun san ainihin mugun abunda suke shiryawa ba shiyasa sosai suke son ganin sun shirya da d'an uwansu wato baban bintu da kwata kwata sun kasa samun fuska kuma sam ya fita harakar su.

Basu sami Abba a gidan ba baya nn ya koma jos,se umma suka samu wacce ta tarbe su da murna tana musu sannu da zuwa,en jikokinta wato su ilham da 'ya'yan anti Nafee duk suka maqalqale ta suna murnar ganin ta, qwallah ne suka ciko a idon bintu,da yanzu itama da er ta ko yaronta a cikin su.
Waheed ne kad'ai ya lura da yanayin da ta shiga a ciki, yayinda bintu a tunanin ta ba wanda ya lura da ita dan kai tsaye ta had'iye hawayen da suka cika mata qwallah taci gaba da murnar ta kmr a ranta ba komai.
Gabad'ayan su ciki suka wuce suka bar waheed zaune a falo,umma ta fito riqe da makullin d'aki a hannunta wacce bata bashi makullin d'akin ba se zama tayi suka qara gaisawa tana tambayar sa ya qarin lafiyar jiki yace"Alhmdlh jiki yayi sauqi sosai"
Tace"to Allah ya qara baka lafiya ya kuma tsare gaba ya muku katangar qarfe da duk wasu miyagun mutane"
Yace"Amin"
Snn ta bashi makullin d'akin da yake sauka wato d'akin Abbas da yake kira d'akin shi dan haka suke shida Abbas abun waheed nasa ne haka waheed abun sa na Abbas ne,haka amintakar su take abun sha'awa har iyayen su sun biye musu,se dai Abbas bai sake sosai da mami ba kmr yanda waheed ya sake da umma.
Sbd Abbas aikin sojan shi bai barshi ya cika yin ziyara kmr yanda waheed keyi ba.
Kuma ko ganin gida ma se can yake zowa wanda tunda yayi aure ko yazo a gidan sa yake fara sauka shida iyalin sa snn suzo su gaida su umma.

Koda waheed yaje d'akin ya sami d'akin tsaf tsaf se qamshi ke tashi kai tsaye kan sofa yaje ya zauna tare da zaro wayar sa a aljihu.

Umma kuwa tana baiwa waheed makulli,kitchen taje ta shirya masa abincin sa a tray ta kira bintu ta bata tace ta kai mishi.

Koda bintu tazo ta same shi zaune kan sofa se waya yake cike da fara'a yana dariya.
Tasan ba kowa ne yake waya dashi ba face yayanta Abbas dan tasan dashi kadai' yake irin 6arkar dariyar nn idan suna waya.
A nn gaban shi ta jawo stool ta d'aura masa trayn abincin snn ta dibar masa abincin a plate, white rice ce da miyar stew wacce taji naman kaji se cucumber salad da ta sa mishi a gefe,snn ta zuba mishi lemu a cup ta miqa mishi dan a lokacin ya gama waya.
Waheed ya kar6i lemun tare da kama d'ayan hannun ta ya zaunar da ita kusa da shi ya kurma lemun ya bata itama dmn tasha,
a hnkli ta girgiza kanta tace"Aa kasha kawai"
Waheed ya ajiye lemun yace"to muci abinci"
Nan ma tace"Aa kaci kawai naka ne wnn ni zanje inci dasu anti Hafsa"
Yace "No muci kawai ae zai ishe mu har ma mu rage"
Bintu bata musa mishi ba ta yarda suka ci abincin.
Bayan sun kammala bintu ta zari tissue tana share bakinta se kallon ta waheed keyi.
D'auke da d'an murmushi bintu tace"yaya lafiya?
A natse ya kama hannayen ta yasa a cikin nashi ya riqe yana kallonta kmr zai ce wani abu se kuma yace"ba komai"
Maqale kafad'a tayi tare da fad'in ban yarda ba da akwai abinda zaka fad'a ka fasa"
Ta qarashe mgnr ne tare da d'an doddoka qafafunta a qasa tana kallon sa cikin shagwa6a,tace"uhm dan Allah yaya ka gaya min mene ne wlh bana son ayi niyyar gaya min abu kuma a fasa"
Waheed dake kallonta a natse ya shafo gefen fuskarta yace"ba wani abu bane my lady dama d'azun ne naga kinsa damuwa a ranki a lokacinda su ilham suka je jikin umma suna murnar ganin ta, tunanin me kike kuma meyasa kika tashi yin kuka a lokacin?
Qwallah ne suka ciko a idon bintu tana batun fashe masa da kuka,da sauri waheed ya girgiza kansa yace"kin gani koh shiyasa kawai naso in fasa mgnr dan nasan zaki iya min kuka,maida kukan idan baso kike muyi fad'a ba"
Ya qarashe mgnr ne yana kallon bintu wacce bata fashe masa da kukan ba amma ta kasa maida hawayen da ke cike a idonta,se hannunta ta d'aura kan cikinta muryar ta a sanyaye tace"yaya ina son in haifu nima inga 'ya'yana"
Waheed dake kallonta yaja ta zuwa jikinsa yana shafa bayanta a natse cikin muryar rarrashi yace"ki kwantar da hankalin ki my lady meye na damuwa duka duka yaushe ne aka miki aiki wata qil ma yanzu haka akwai babyna a jikin ki lokacin bayyanar sa ne kawai baiyi ba.
Bintu ta d'ago hawaye still cike a idonta kmr zasu zubo cikin muryar kuka tace"babu baby a jikina yaya am in on"
waheed yace"yaushe?
Tace"muna isowa cikin gidan nn naji isowar shi"
Yace"kin duba kuwa shine?
A hnkli ta gyad'a masa kai tare da sa hannu ta share hawayen da suka zubo mata.
Waheed da gabad'aya jikin sa yayi sanyi ya sake maida ta kan faffad'an qirjinsa ya kwantar se shafa bayanta yake cike da natsuwa yana bata magana.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 46_*
Har ya samu ta rage damuwar da ke ranta.
A nn ta d'ago daga kan qirjinsa tana tambayar sa yaushe zai koma,yace mata idan anyi sllr zuhur.
Tace"yaya da ka bari da yamma dai dai rana tayi sanyi se ka d'au hanya yafi"
Yace"um um da dai ace Abdallah na nn in samu abokin fira,junaid kuma basa nn bare in tafi gidan shi.
Bintu tace"to amma idan ka koma a can gidan mami zaka riqa kwana koh"
Yace"Aa a gida dai zan riqa kwana har ki dawo"
Cikin damuwa tace"um um dan Allah yaya ka riqa zuwa gurin mami kana kwana a d'akin ka wlh hankali na ze fi kwanciya,banna son ka kwana a wancan gidan kai kad'ai a d'aki ina tsoro"
Waheed dake kallon ta yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta yace"ki kwantar da hankalin ki Inshaa Allah ba abinda zae sake faruwa dani,ko inje d'akin gateman na riqa bacci tare dashi?
Dariya bintu tayi tace"A'a ai duk inda mutum yake Allah yana tare dashi kawai ka riqa baccinka a d'akin ka,as usual zanci gaba da roqon Allah ya tsare min kai.
Waheed da har ransa yaji dad'i yace"nima Allah ya tsare min ke fatima,bari in shiga bathroom inyi arwala in tafi masallaci nasan ba'a nesa da yin sallah.
Ba tare da ya jira me zata ce ba ya tashi ya shiga bathroom ita kuma ta kwashe kwanikan abincin da suka ci ta fito dasu.

Bayan anyi sallah ne waheed yazo yayi sallama da umma dasu anti hafsa acewar zai koma suka masa Allah kiyaye ya tsare hanya yace Amin.
Bintu ta raka shi har mota ya tafi se bye bye take mishi har ya wuce snn ta koma daga ciki.

Kwanan su biyu a garin se ga Abdallah shima yazo ae kuwa gidan se ya qara yiwa bintu dad'i se murna take da dawowar shi,kullum tare suke cin abincin su ita dashi har ma dasu anti hafsa duk tare suke ci su duka hud'u,su ilham da 'ya'yan anti nafee suma a kwano d'aya ake sa musu abinci suci tare dan ba kad'an ba hakan na qara danqon zumunci.
Shiyasa umma sosai take jin dad'in had'in kan 'ya'yan nata,se ka gansu sunyi zaune se fira suke tayi suna kekkewa,dan Abdallah idan yana ga guri gwanin son a zauna ayi ta fira ne ana raha,ae kuwa da lokacin komawar su sokoto yayi suka ji kmr su qara kwanaki akan sati d'ayan da sukayi amma ina sun san ko sun fad'a umma bazata yarda da wnn iya shegen ba,dole rnr lahadi da yamma suka shirya suka koma amma wnn karon a mota d'aya suka koma wato mortar anti Hafsa da Anti nafee ta biyo suka zo tare.
Duk da cewa waheed da kansa yaso yazo ya d'auki bintu tace masa a'a ya barshi kawai motar anti Hafsa da akwai enough space.

Da isar su garin sokoto bintu suka fara saukewa sbd tafi kusa.
Su anti Hafsa na wucewa bata ko shiga gidan ba sae ga waheed ya fito tarbonta sbd suna isowa bakin gate d'in gidan dai dai kiransa ya shigo dmn yaji shin suna ina,wanda tasowar su ya kirata kusan sau uku,ana hud'un ne tace mishi ai gasu har ma sun iso shine ya fito ya tarbe ta cike da murna ya rungume abar sa qyam kyace wanda yayi wata d'aya rabon shi da ita.
Haka ya shiga da ita gidan manne da ita a jikinsa yayinda gateman ya biyo su da akwati.
Da suka shiga ciki bintu taga komai tsaf tsaf se qamshi ke tashi ko wata mace albarka dan waheed akwai tsafta sosai sam baya son qazanta.
Ga abinci kala kala jere kan dining wanda duk mami ce ta girka mata shi da kanta ta aiko hajjo ta kawo.
Kasancewar a lokacin magrib tayi bintu bata tsaya cin komai ba sae da sukayi sallah snn waheed da kanshi ya d'ibar musu abinci sukaci.
Bayan sun kammala cin abinci har ma sunyi sllr isha sukayi zaune a falo suna fira yayinda waheed ke zaune kan doguwar kujera 3seater bintu kuwa na kwance kan qafafuwan sa tayi pillow dasu se wasa yake da kalabar kanta.
A cikin firar su ne bintu ke cewa"yaya wai yaushe ne hajiyar Husna zata maida maka saif ya dawo hannu mu da zama wlh ina son yaron sbd kunyi kama ba kad'an ba"
A hnkli Waheed ya numfasa yace"saif kam bazai dawo hannun mu ba fatima"
Bintu ta tashi tana kallon sa tace"meyasa?
Yace"yana nn hannun mami ya dawo da zama"
Cikin jin dad'i tace"yes! kaga ma shikenan se kayiwa mami magana nasan zata bamu shi"
A hankli ya girgiza kansa alamar a'a
Bintu tace"meyasa?
Yace"baza ki iya da lalurar sa ba fatima"
Nan take gabad'aya farin cikin bintu ya koma tace"sbd ni ba mahaifyar sa bace zaka gaya min haka"
Da sauri Waheed yace"ba haka bane Fatima"
Qwallah tap a idonta tana kallon sa tace"to idan ba haka bane mene ne,idan ni na haife shi ai bazaka gaya min haka ba wlh"
Tana kaiwa nn ta bar gurin ba tare da ta jira me zae ce ba waheed se kiranta yake amma taqi ta tsaya se kuka ma da yaji ta fashe dashi ta shiga d'akinta.
Jiki sanyaye waheed ya tashi ya bita ya same ta kwance ruf da ciki tana ci gaba da kuka.
Yaje gab da ita ya zauna tare da janyo ta zuwa jikinsa cike da son ya rarrashe ta amma taqi saurarar shi se qwacewa tayi daga jikinsa ta tashi zata bar masa d'akin.
Cikin muryar rarrashi yace"fatima yi haquri kar ki fita zo muyi magana kinji"
Bata fita ba d'in ta tsaya tana ci gaba da kukan ta,waheed ya taso ya jata ya tafi da ita suka zauna kan bed.
A natse cikin muryar rarrashi yace"kiyi haquri fatima ba haka nake nufi ba,ganin nayi gobe goben nn nida ke duk a bakin aiki zamu koma ba qaramar lalura bace dawo da saif hannun mu,snn ba kad'an ba mami tana son yaron ya kasance a gurinta ganin haka yasa hajiyar husna ta maida mata shi da kanta.
Amma kar ki damu kinji duk lokacinda kk off hajjo zata riqa kawo miki shi ya maki yini da dare se a maida shi koh?
A hankli ta gyad'a masa kai waheed yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta kana yaja karan hancinta d'auke da murmushi yace"iyayen rigima ba kya bari ki fahimci mutum se ki d'auki laifi ki d'aura mishi koh"
Murmushi bintu tayi tare da shigewa jikinsa tana fad'in yi haquri kasan mai kaza a aljihu baya jiimirin has se inga kmr dan bai haifu bane"
Waheed da har ransa ya fita damuwa yaga cewa ta haifu yace"hm my lady knn ae kema kin kusa ki haifu da yardar Allah.
Amin Allah ya kar6i bakin ka.
Cewar bintu wacce ta d'ago daga jikinsa tace"yaya ya kamata muje muyi wanka mu samu mu kwanta da wuri kar muyi lettin tashi"
To waheed yace snn ya taya ta cire kayan jikinta ta d'aura towel suka tafi d'akin shi.
Da fitowar su wanka gogan ya kasa haquri ko mai su shafa,se jan bintu yayi zuwa bed ya kwantar tare da zare mata towel d'in jikinta shima ya zare nasa ya jefar suka shiga ba juna haqqin su cike da zallar so.

Washe gari da wuri suka tashi suka shirya bayan sunyi breakfast suka fita waheed ya shiga tashi motar ya wuce gurin nasa aiki,itama bintu ta shiga sabuwar motar ta da waheed ya canza mata,ta wuce gurin nata aiki farin ciki fal a ranta se murna take dan da sassafen nn ne ya mata surprise d'in sabuwar motar.
Wacce kafin su bar gidan se da ta kira umma dasu anti Hafsa ta gaya musu se tayata murna suke,ta kuma ba waheed waya suka mishi Allah ya qara bud'i.

Koda sati ya zagayo bintu ta gama morning tana off hutu take kafin ta fara evening.
Shiyasa rnr waheed kawai ya fita aiki to ten se ga hajjo ta kawo mata saif kmr yanda waheed yayi mata alqawarin duk rnr da take free bata zuwa gurin aiki za'a kawo mata shi ya mata yini da dare se a maida shi.
Sosai bintu taji dad'i dan dagaske har ranta take son saif ji take kmr ma ace ita ce ta haifeshi sbd saif yaro ne mai shiga rai ga jikin sa d'an du6ul du6ul abun sha'awa kuma sam baya da kukan banza se idan yaji yunwa yake yin kuka.
Duk da saif bai yi wani wayo ba amma haka bintu zata tasa shi gaba tayi ta mishi wasa tana cilla shi sama shi kuma yana ta yi mata er dariyar shi da ya fara iyawa.
Idan kuma ta fahimci ya fara jin yunwa yana son yin kuka se ta had'a mishi madarar shi ta bashi yasha har se ya qoshi snn ta goya shi idan da akwai aikin da take son yi.

Har bayan isha saif na nn ba'a maida shi ba,bcos hajjo da ta kawo shi kai tsaye ta koma,kuma dama waheed ne ze maida shi bai dawo ba se 9,wanda koda ya dawo duk a gajiya yake seda yayi wanka yaci abincin snn yayi zancen maida shi.
Nan fa bintu ta marairaice mishi bata son a maida shi tace"yaya dan Allah ka barshi tunda dare yayi kuma gashi na mishi wanka ya samu yin bacci, gobe da safe idan zaka je aiki se ka ajiye mu gidan mami idan ka dawo gurin aiki se ka d'auko ni mu dawo,inshaa Allah mami zata amince ka kirata ka gaya mata kaji yaya.
Waheed dake ta kallon d'an qaramin bakinta dake koro masa bayani,har ransa yaji dad'in soyayyar da take yiwa saif yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta yace"shikenan naji kar ki min kuka ba cewa zanyi a'a ba"
Cike da jin dad'i bintu ta rungume shi tana mishi godiya.
Tana manne a jikinsa ya tafi da ita kan bed suka zauna se kallon saif yake da yake ta sharar bacci abinshi,ya tambayi bintu ko ya mata kuka ta ce mishi a'a,kana ya zaro wayar sa a aljihu ya kira mami ya snr da ita tace ba komai ai da yau da gobe duk d'aya ne,bintu kuma ai mahaifiyar sa ce ta wuce ace kan saif ta nemi alfarma.
Sosai bintu taji dad'i da jin zancen mami ta d'auki saif suka tafi d'akin waheed,kmr yanda waheed ya buqata.

Washe gari da waheed ze je gurin aiki saida ya sauke su a gidan mami snn ya wuce gurin aiki.
Nan ta yini har se guraren six na yamma snn waheed ya dawo daga gurin aiki ya biyo ya d'auke ta suka koma gida.
Bintu ta kwana cikin kewar saif dan kwana d'ayan da yayi a hannunta da kuma yinin da tayi tare dashi a gidan mami yasa ta qara jin qaunar sa a ranta,sai dai bata sa damuwa a ranta ba tuna cewa za'a riqa kawo mata shi duk ranar da bata zuwa aiki.

3months later

Sosai saif ya shaqu da bintu kmr ita ta haife shi sbd kawo mata shi da akeyi duk lokacinda take free bata zuwa gurin aiki,wanda ya shaqu da ita ne sosai sbd irin kulawar da take bashi tana mishi wasa ko kad'an bata son taga cewa yayi kuka,hkn yasa musamman har d'aki ta ware mishi a gidan ta cika d'akin maqil da kayan wasa se abunda babu.
Waheed da mami ba kad'an ba suna matuqar jin dad'in irin kulawar da take bawa saif musamman hajiyar husna wacce ta tabbatar ko husna ce a raye iyakar kulawar da zata bashi knn.
Wayar bintu in ka duba duk fotunan saif ne,wani shi kad'ai,wani ita dashi da kuma wanda sukayi su duka uku tare da waheed,duk koina in ka ganshi bakinsa a washe se dariya yake dmn yaron akwai son fara'a sbd irin wasar da bintu ke mishi dole yaro ko kum kum kum ne ze sake ya fara sabawa da dariya.
Abunda ke damun bintu har yanzu ciki shiru duk wata bata fashin al'ada,ae kuwa duk lokacinda yazo mata ta shiga damuwa knn wani lokacin ma har kuka take se waheed ne zae zauna yayi ta rarrashin ta yana bata magana.
Da karshe ma har asibiti sai da suka je aka dubata ba wata matsala da mahaifar ta take d'auke da ita yanzu lokaci ne kawai bai yi ba.
Bayan wata d'aya da zuwan su asibiti ne,ranar wata assabar da dare waheed na zaune a d'akin shi yana kishingid'e kan bed yana kallon labarai.
Se ga bintu ta turo qofar d'akin a hankali tayi tsaye qwallah tap a idonta tana kallon shi kmr zatayi kuka.
Waheed da ya maida duban sa gareta da kulawa yace tazo.
Ba musa ta qarasa gurin shi ya tashi daga kishingid'en da yake ya kama hannunta ya zaunar da ita kusa dashi hannun sa kan cikinta yana kallonta yace"har yanzu gudawar ce cikin bai daina miki ciwo ba"
Muryar ta can ciki cike da son tayi kuka tace"har yanzu yaya abun ba sauqi se qaruwa yake kmr ma bana shan magani"
Cike da damuwa waheed yace"to Fatima me kikaci ne wai ya 6ata miki ciki haka?
Tace"ni yaya ba wani baqon abunda nasan naci face wnn new chocolate d'in da muka siyo kwanakin nn kuma bana tunanin shine tunda kaima kaci amma bai maka komai ba"
Yace"duk da haka dai fatima ki daina cin sa mu gani kinji"
A shagwa6e tace"yaya bafa shi bane yau two days knn rabona da cin sa amma ciwon cikin se qaruwa yake tayi"
Ta qarashe mgnr ne tare da fashe masa da kuka.
Cikin damuwa waheed ya shiga rarrashinta yace ta tashi suje asibiti, tace mishi um um ya bari taci gaba da shan magunguna tukun idan ciwon cikin bai daina ba snn suje.
Bai musa mata ba sae kwantar da kanta yayi zuwa faffad'an qirjinsa yana shafa gadon bayanta a hankli har tayi bacci.

Washe gari koda suka tashi gabad'aya jikin bintu ya gashe yayi zafi sosai wacce kwata kwata cikin dare ciwon ciki bai bar tayi bacci ba,safiya na wayewa kuma sae amai komai taci kai tsaye take amaryar dashi baya tsayi,shiyasa waheed duk yabi ya damu ga bintu ta sashi a gaba se kuka take mishi yunwa take ji,ya rasa me zai mata tunda ba abinda take ci ya tsaya mata,se mami ya kira ya snr da ita halin da suke ciki,tace mishi gata nn zuwa su tafi asibiti.
Kasancewar bintu jiri take gani bata iya miqewa tsaye da kanshi ya mata wanka ya shirya ta mami na zowa suka tafi asibiti.

Cike da farin ciki suka dawo gidan sbd kyakkywan labarin da suka dawo dashi wato juna biyu ne da bintu na tsawon wata d'aya.
Duk da irin jin jikin da bintu keji kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tsantsar farin ciki, sam ta kasa 6oye murnar ta bare shi waheed uban aiki duk yafi su farin ciki dan babban burin sa shine yaga fatimar shi ta haifar mishi.
Da dawowar su ne mami na cike da murna ta cire mayafinta ta ajiye ta fad'a kitchen dmn girkawa bintu abinda zata samu ta d'an saka a cikinta.
Faten dankalin turawa ne ta mata da aka watsa wake a ciki sai qoda da aka yanyanka gutu gutu yayi kyau har ya gaji se qamshi ke tashi tazo da kanta tayi zaune tana bata har se da tace ya isheta.
[12/6, 6:31 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 47_*
Cikin ikon Allah kuwa se bata amaryar da abincin ba,mami ta 6alla mata magunguna tasha.
Snn ne fa akayi zancen kiran kowa aka sanar dasu,ae kuwa kowa se murna yake yana fatar Allah ya bada rayayye mai albarka.
Kowannen su:
Umma,su anti Hafsa,Abdallah da Abbas duk se da suka kira bintu suna taya ta murna tare da mata kyakkyawar addu'a.
Bayan nn ne mami ta tafi gida.
Tunda mami ta bar gidan bintu ke bacci kan jikin waheed se zuhur snn ta tashi sukayi sallah sukaje kan dining dmn cin abincin da mami ta aiko musu dashi.
Dambun shinkafa ne da yayi matuqar kyau,wanda yaji ganyen zogale sosai da kayan lambu had'a da fried meat da akayi cutting d'insa gutu gutu aka watsa akai se qamshi ke tashi.
Ai kuwa sosai bintu taci danbum dan ba kad'an yayi dad'i da taushi har ya gaji.
Kmr kar su kammala cin abincin ko kan dinning basu sauka ba bintu ta soma jin wani bacci,a d'an shawa6e ta kalli waheed dake share bakin sa da tissue,kafin tace komai ya ajiye aikinda yake,da kulawa ya shafo gefen fuskarta yace"amai?
Tace"um um wai bacci"
Kike ji?
Waheed ya tambaya.
Ta gyad'a masa kai yace ta tashi muje d'akina koh.
Ya fad'i hakane tare da kama hannunta tana manne a jikinsa har suka isa d'akin shi,dashi har ita sukayi baccin su suna rungume da juna har sae la'asar snn suka tashi.

Da dare bayan isha'i guraren qarfe tara waheed ne ya shigo d'akin bintu ya same ta zaune kan bed d'aure da farin towel a jikinta,ta d'auko rigar bacci bata riga tasa ba tana ajiye kan cinyoyin ta tana waya d'auke da alamar jin kunya a fuskarta.
Yana tsaye har ta gama waya snn ya qarasa gurinta ya zauna gab da ita tare da kai hannun sa kan cikinta yana shafawa a hnkli cikin natsuwa yana kallonta yace"da wa ake waya ana jin kunya haka?
Murmushi tayi tare da fad'in"Abba ne fa ya ma ce a gaida ka"
Yace"ina amsawa snn ya d'aura da cewa"ya jikin naki to?
Sai da ta rufe fuskarta da tafukan hannayen ta snn tace"ae murna da farin yasa komai ya tafi yaya,bana jin duk wani ciwo a jikina yanzu"
Waheed dake kallonta d'auke da murmushi ya janye hannayen ta daga kan fuskarta yana kallonta yace"har da ciwon ciki duk ya tafi?
Tace"eh ya tafi"
D'auke da jin dad'i ya shafi fuskarta snn yakai hannun sa kan towel d'in jikinta ya kwance d'aurin

Please Login or Register in order to submit comment