Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta leqa se taga d'akin duk duhu ne ba haske,ta kunna fitilar wayarta ta yada,
a nn ta hango mami kwance kan sofa tana bacci.
Murmushi ta sakarwa Barrister a cewar ya shigo.
Barrister ya shigo yayinda beauty taje gun waheed tayi tsaye sae kallon sa take cike da so d'auke da d'an murmushi a fuskar ta ta kai tafin hannunta a hankli tana shafa gefen fuskar sa,muryar ta a hnkli tace"am sorry my guy zan rabaka da mahaifiyar ka ba dan in quntata maka ba sae dan in nuna maka tsantsar soyayyar da nake maka kaji.
Daga haka ta janye hannun ta daga kan fuskar shi,ta maida dubanta gun barrister ta masa alama da hannu, acewar ya shaqawa mami wnn powder suyi su kama gaban su.
A nn kae tsaye Barrister ya nufi gun mami ya ciro powder a aljihun sa ya bud'e knn zae shaqa mata,kawai haske ya bayyana a d'akin mami dake kwance ta miqe tsaye yayinda police da sojawa suka firfito a bayan curtains duk suka zagaye d'akin.
Hankali tashe barrister da beauty ke kallon su kowannen su yayi arresting nasu da bindiga,
nn take a rud'e suka d'aga hannayen su,beauty ta kalli mami tare da saurin zubewa qasa kan guiwoyin ta tana ba mami haquri.
Mami ta qaraso gurinta tace"gaya min me na miki a rayuwa kike son rabani da d'ana qwaya d'aya tal da nake da shi a duniya?
Beauty muryar ta na rawa tace"Wlh mami ba abinda kika min tsananin qaunar sa ne yasa nake son in tafi dashi,amma wlh Allah na haqura da son shi zan barwa bintu abunta,kar kisa a kamani dan Allah wlh nayi alqawarin zan tafi nesa daku bazan sake waiwayar ku ba har abada.
Mami bata kula ta ba tace da police su kama su su tafi dasu.
A rud'e barrister yace"Aa dan Allah police kar ku tafi dani wlh itace ta tursasa ni banyi niyyar aikatawa ba"
D'aya daga cikin police yace"da yake kai wawa ne mai qwaqwalwar jaki se ka yarda mace ta tursasa ka kayi abinda bakayi niyya ba ko!
Yace"wlh Allah halinta ne na sani zata iya qulla min mummunan sharrin da ban aikata ba, dan ko su zeenah ta qara akan abinda basu aikata ba.
Nan barrister ya tona mata asiri kaf har kashe handosme da tasa akayi bai rage komai ba.
(Sbd komai gaya masa sukayi a lokacin da za'ayi shari'a dan yasan yanda zaiyi ba tare da an sami matsala.)
Cike da alajabi mami ta shiga jinjina kai lallai su zeenah sun had'u da gamon su in taqamar su ba mutun muguwar shawara.
Barrister se roqon ta yake ta yafe mishi kar tasa a tafi dashi,beauty kuwa se kuka take tana fad'in sharri barrister yake mata,mami bata kula su ba,police suka jasu suka tafi dasu kmr yanda ta buqata.

Washe gari da safe bintu na kwance kan darduma wacce tun lokacin ta ida sllr asuba take kwance a gurin bata tashi ba, sei tunanin waheed take tayi wanda tun jiya da suka je duba shi taji gabad'aya ya bata tausayi a yanayin da ta ganshi.
Anti hafsa ce ta shigo d'akin d'auke da sallama a bakin ta,hkn yasa bintu ta tashi zaune tare da amsa mata sallama snn ta mata ina kwana.
Anti Hafsa ta amsa gaisuwar wacce cikin yanayin damuwa da mamaki tace"hm kin san me bintu?
A hnkli bintu ta girgiza kanta tana mai kallon Anti Hafsa wacce tace"yanzu nn yaya Abbas ya kira Abban ilham yake gaya mishi abinda ya faru jiya da dare, wae ashe wnn beauty d'in baqar muguwa ce halin ta d'aya dasu zeenah koma ince tafi su.
Nan Anti Hafsa ta gayawa bintu duk abinda ya faru.
Bintu wacce idanun ta suka ciko tap da qwallah cikin muryar kuka tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku!yanzu idan yaya waheed ya manta waye shi ya zanyi....nan kawai ta fashe da kuka,Anti Hafsa taja ta jikinta sae rarrashin ta take tana bata magana,amma bintu ta kasa daina kukan.
Nan Anti Hafsa ta janye jikinta a hnkli ta tashi taje ta bud'e qofa sbd knocking d'in da taji anayi.
Abban ilham ne ke knocking d'in wanda anti Hafsa na bud'e qofa yace"kin tada su ilham kuwa?
Tace"Aa yanzu dai nake shirin tada su.
Yace"to kiyi ki tada su kar suyi latti.
Anti Hafsa tace"to"
Kana Abban ilham ya juya zai tafi sae kuma ya tsaya yana sauraren sautin kukan bintu dake fitowa a hankli.
Ya kalli Anti hafsa tare da fad'in"me nake ji kmr kukan bintu kaddai kin gaya mata matsalar da waheed yake d'auke da ita ne?
Tace"ya zanyi Abban ilham tunda abu ne da ya zama dole ta sani"
Ransa a d'an mace yace"haba hafsa meyasa, iyakacinki ki gaya mata abinda ya faru bai kamata ace kin gaya mata har matsalar da waheed yake d'auke da ita ba,fisabilillah ba kya jin tausayin ta,duka duka yaushe ne ta fita waccan damuwar da zaki zo ki d'aura mata wata damuwar kuma.
Muryar ta a sanyaye tace"kayi haquri Abban ilham zan rarrashe ta".
Abban ilham dake kallon ta komai bai ce ba ya tafiyar shi.
Anti hafsa ta koma daga ciki jiki sanyaye ta sami bintu taci gaba da rarrashin ta har ta samu bintu ta daina kuka.

Da yamma bayan sallr la'asar sae ga Abbas yazo daga kebbi sbd jiya tare suka koma kebbi shida su umma da Abdallah.

Bayan ya gama gaisawa dasu Abban ilham da Anti hafsa ya nemi ganin bintu,Anti Hafsa taje ta kira mishi ita tazo muryar ta a sanyaye ta mishi sannu da zuwa,ya kama hannunta ya zaunar da ita kusa dashi yana kallon ta da kulawa kana yace"Bintu ance gabad'aya kin shiga damuwa akan matsalar da kika ji waheed na d'auke da ita a qwaqwalwar sa,to ki cire damuwa a ranki kinji inshaa Allah waheed zai sami lafiya bazai manta rayuwar sa ta baya ba da yardar Allah,su umma na kan addu'a haka nima zan taya ki kema ki qara dagewa sosai da addu'a kinji.
A hnkli bintu ta gyad'a kanta.
Abbas dake kallonta yace"dama abinda yasa nazo mami ce taje can kebbi gun Abba da umma ta nemi alfarmar dan Allah idan har ba saki uku waheed ya maki ba tana son a maida auren ki keda waheed a cikin kwanakin nn dmn so take ta fitar da waheed waje dake dmn magance matsalar da kike d'auke da ita.
A nn bayan ta gama bayanin ta su umma suka gaya mata cewa ae ba ma saki a tsananin ku kmr yanda na gaya musu kin min bayani dan haka sae ki shirya a cikin satin nn zaku tafi India inshaa Allah.
Bintu ta kalle sa tace"amma yaya baka ce bazan koma ba kwata kwata?
Abbas yace"Dalilin da yasa knn nazo dmn har umma zata kiraki a waya ta gaya miki buqatar mami nace ta bari kawai inxo in gaya miki dmn dama da akwai bayanin da nake so inzo in miki.
Bayanin shine ni sam ba da gaske nake shirin rabaki da waheed ba,ina hora ki ne sbd ki gane kuskuren ki ta yanda ko maqiyin ki ba kya fatar ya aikata kuskure irin wanda kikayi.
Abban ilham da jabir duk sun san cewa hora ki kawai nake amma sun damu sosai da wnn horon dan ganin suke yayi tsanani musamman jabir wanda da naji zancen yana sonki sosai na lallashe shi na bashi magana kan ya haqura dake yazo ga peeya zan shige masa gaba in yana so(cewa da qanwar mtr shi).
Bintu wacce da gani tausayin jabir take ji tace"to me yace?
Abbas yace"Na nuna masa photon ta tuni ya amince gobe goben nn ma tare zamu tafi dashi Abuja ya ganta suga juna idan ta amince sae ayi magana manya su shigo ciki,bare ma nasan peeya bata da matsala inshaa Allah zata amince ta so shi ko danni da na kawo shi, fatan mu Allah yasa wnn had'i alheri ne a tsakanin su da mu baki d'aya.
Bintu tace"Amin"kafin Abbas ke cewa tashi kije ki gaya wa Hafsa su shirya yanzu muje mu qara dubo waheed.
Nan bintu ta tashi taje ta snr dasu suka shirya gabad'ayan su har jabir suka tafi,da zasu dawo mami ta nemi da su bar mata bintu da dare zata maida ta.
Bayan sun tafi bintu na zaune kan kujera kusa da waheed da still yake kwance kan bed kmr wani gawa, idon ta akan shi sae kallon sa take tayi musamman qafar shi da tasha harbi, da take tsoron kar ita ma qafar azo ace ta sami matsala dan dai ba kad'an ba sun masa rauni a qafar.
Zar taji saukar hawaye a kumatun ta tayi saurin share hawayen kar mami ta gani.
Mami dake kallonta ta girgiza kanta cikin tausayawa,ta matso kujerar ta kusa da bintu ta kama hannayen bintu ta riqe a hnkli snn tace"kiyi haquri bintu ki daina kuka inshaa Allah waheed zai sami lafiya kinji"
A hankli bintu ta gyad'a kanta mami dake kallonta tace"ina kuma roqon Allah ya shiga tsakanin ku da maqiyan ku yasa sun tafi knn har abada baza su fito ba.
Amin cewar bintu wacce tana gama fad'ar haka ne tayi saurin kallon waheed sbd yatsun hannun sa da taga sun motsa.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 43_*
mami kinga yatsun yaya waheed suna motsawa!
Bintu ta fad'a yayinda tayi saurin matsawa gab dashi ta kama yatsun nasa tana kallo.
Mami jikinta na rawa ta matso gab dashi itama tana kallon yanda yatsun nashi ke motsi a hankli.
Suna kallon sa har ya fara bud'e idanun sa sannu a hnkli har ya bud'e su gabad'aya.
Bishi bishi ya gansu kmr wasu katun suna juya mishi dasu har d'akin kmr zasu fad'o mishi aka.
Ba shiri yasa hannuwan sa duka biyu ya dafe kansa da sauri ya kuma rufe idanun sa gam yana jin kansa na masa wani irin masifaffen ciwo tamkar zae tsage ya rabu biyu
Nan mami ta fita da sauri taje ta kira Dr sa'id yazo ya nemi da su bashi guri yana son zae duba shi.
Ba yanda suka iya haka suka fita sae safa da marwa suke a bakin qofar d'akin.
Bayan minti sha biyar dr ya fito ya nemi da su shiga.
Da mami har bintu cikin fargaba suka shiga d'akin,a ransu suna tunanin shin waheed zae tuna su ko kuwa?
Da shigar su Dr ya kalle su snn ya maida duban sa gun waheed dake zaune kan bed bayan sa jingine da pillow yace"to waheed ko zaka iya gaya min su waye wa en nn?
Waheed da tun lokacin da suka shigo idon sa ke kansu,ya kalli dr fuskar sa d'auke da alamun jin jiki muryar sa can ciki ta marasa lafiya yace"wae meye haka ne Dr ka tambayeni sunana da waye ni na gaya ma,kuma shine har mami da fatima sae ka tambaye ni su waye.
Da mami har bintu wani irin dad'i suka ji a ransu,washe da baki mami ta kalli dr da ke d'auke da murmushi a fuskar sa tace"kae Alhmdlh amma naji dad'i wlh ya akayi haka Dr?
Dr sa'id da still fuskar sa ke d'auke da murmushi yace"ikon Allah ne wnn dan nayi mamaki byn na mishi allura ya samu relief na mishi tambayoyi se naji kae tsaye yana bani amsar abinda nake son ji,dan fatana knn inga bai manta rayuwar sa ta baya ba,amma a gaskiya still da akwai er matsala a qwaqwalwar sa, dmn wnn ciwon kan da yazo mishi da farkawar shi shine ke barazanar son mantar dashi rayuwar sa ta baya, amma ba matsala idan aka ci gaba da yi mishi allurar da na mishi d'in nn zae rabu da matsalar inshaa Allah,dan inaga ma koda aka d'auki photon qwaqwalwar sa,qwaqwalwar tasa na cikin wnn yanayin shiyasa naga matsalar,Allah dai ya qara tsare gaba ya kuma bashi lafiya.
Mami tace"Amin"

Nan Dr ya fita wanda kafin ya fita sae da ya rubuta magungunan da waheed zae sha bayan yaci abinci.
Bintu ce ta kar6i takardar ta fita dmn siyo magungunan.
Waheed da yabi Bintu da ido har ta fita,ya kalli mami yace"mami ya na ganki tare da fatima?
Kallon sa mami tayi a natse ta shafo gefen fuskar sa snn tace"zamuyi magana anjima ba yanzun ba kaji"
Yace"To Husna fa sun kashe ta koh?
A hnkli ta numfasa tace"duka duk zamuyi magana anjima,bari na had'a ma tea kasha kafin hajjo ta kawo abinci.
Bata jira me zai ce ba ta tashi taje ta had'o mishi tea ta kawo ta ajiye a nn kan drawer.
Snn ta zubo ruwan gora mara sanyi a cup had'e da er wata tasa dmn ya wanke bakin shi.
Rawa hannun sa ya soma yi bazai iya kar6ar cup d'in ruwan ba sbd gabad'aya jikinsa ya masa nauyi sosai ta yanda gab6an jikin sa baza su iya wani aiki ba.
Hakan yasa mami ta wanke mishi bakin da kanta ta kuma yi zaune tana bashi tea yana sha,a nn sae ga Bintu ta dawo,mami ta kar6i ledar magunguna,bintu taje can kan sofa ta zauna kanta qasa dan sae jin kunyar had'a ido da waheed take,shi kuma shan tea yake yana kallonta jefi jefi.
Bayan ya gama shan tean ne,mami ta bashi magunguna yasha,ya sake tuntun6ar mami amsar tambayar da ya mata d'azun dmn ya qagu yaji dalilin ganinta tare da bintu lafiya lau kmr wani abu bai faru a baya ba.
Haka kuma yana son yaji yanda Husna ta kasance da ma yanda akayi yazo asibiti.
Wannan karon Mami bata musa mishi ba ta nemi bintu da taso tazo kusa dasu.
Bayan Bintu tazo ta zauna kusa dasu ne mami tayiwa waheed bayanin duk abinda ya faru da duk wani sharrin da su zeenah suka qullawa bintu har labarin beauty wacce sai da akayi bincike aka tabbatar da gskyr abinda barrister ya fad'a hkne snn aka yanke mata hukunci d'aurin rai da rai,barrister kuma shekara d'aya a gidan kaso.
Duk haka ta gaya masa komai ba abinda ta rage.
Wani irin yanayi waheed ya shiga na jin tausayin bintu da kuma kashe Husna da akayi.
Idanuwan sa sukayi jajur suka ciko tap da qwallah, yana kallon bintu da hawaye suka shiga silalowa a hnkli kan kumatun ta dan labarin da mami ta bayar se taji komai ya dawo mata sabo.
Mami ta jata jikinta tasa tafin hannun ta tana share mata hawaye.

Bayan sallar isha tuni hajjo tazo ta kawo abinci har ta koma wacce ba kad'an ba tayi murna da farin cikin ganin waheed ya sami lafiya bai kuma manta waye shi ba.
Mami da kanta ta ciyadda waheed abinci har saida yace ya ishe sa.
Bayan ya gama cin abincin ne ya nemi yana son ya watsa ruwa ko jikin sa zae d'an qara sake mishi dan da yaci abinci ya d'an ji sauqin jikin sa ba kmr d'azu ba.
Tare da taimakon mami ya sauko kan gadon ta d'aura shi kan wheelchair ta tura shi zuwa bathroom.
Har zata fita ta barshi sae tayi tunanin kmr wankan zai masa wahala dan ko d'azun da zai yi sllr magrib da isha'i da taimakon ta ne ya samu yayi arwala.
Tace mishi"zaka iya wankan da kanka ko na kira ma bintu tazo ta taimaka maka?
Kansa qasa muryar sa a hnkli yace"eh tazo ta taimaka min"
Nan mami taje ta kira mishi bintu wacce tazo tayi tsaye kawai a bayan shi ba tare da tace dashi komai ba.
Waheed ya juyo da keken gabad'aya yana kallonta kanta qasa se wasa take da en yatsun ta.
A natse yace"Fatima gaya min meyasa kike jin kunyata?
Kallon sa tayi se kuma tayi saurin maida dubanta qasa ta bud'e bakinta a hnkli tace"ina jin nauyin ka ne sbd rashin kyautatawar da na maka kayi haquri dan Allah "
Waheed dake kallon ta cike da so yace"ba komai fatima na yafe miki duk abinda kika min dama wanda baki min ba"
Fuskarta d'auke da d'an murmushi jin dad'i tace mishi ta gode,snn ba 6ata lokaci ta had'a mishi ruwan wanka a bahon wanka.
Tace"na had'a ma ruwan,me kuma kake buqata?
Yace"se kayan jikina zaki tayani cirewa kimin wankan"
A hnkli tazo ta durqusa tana cire mishi kayan jikin nashi har ta cire mishi komai gabad'aya,amma cike take da jin kunya dan se taji kmr yau ne ta fara ganin sa a haka.
Waheed dake kallonta tana durqushe a gaban sa taqi yarda su had'a ido,
yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta snn yace"to tashi ki rage hasken wutar tunda kunyata kike ji yau.
Bintu ta d'anyi murmushi ba tare da tace komai ba ta rage hasken wutar bathroom d'in snn tazo ta taimaka mishi ya shiga bahon wanka.
Nan ta shiga yi mishi wanka cike da kulawa,ba tare da ta bar gun da aka harbe shi a qafa ya sami ruwa ba kmr yanda ake buqata har ta kammala mishi wankan ta d'aura mishi towel suka fito.
Basu sami mami a d'akin ba ta fita, wacce ta basu guri ne sbd ta fahimci ba kad'an ba bintu taji kunya a lokacin da tace taje ta taya waheed wanka, shiyasa ta basu guri har sai ta kammala taimaka mishi ya shirya snn ko zata dawo.
Amma kafin ta fita sae da ta fitar musu da komai da tasan zasu buqata har tufafin sawar shi wato farar riga mai guntun hannu da farin wando 3quarter,wa en da dama an tanade su ne sbd irin wnn rnr koda ya farka.
Haka waheed ya zamowa bintu tamkar wani qaramin yaro komai ita ta mishi, har gashin kansa da sajen fuskar sa duk ita ta taje mishi ta kwantar da sumar tsaf se yayi kyau yana zuba qamshi kmr ba majinyaci ba.
Wacce har qafar sa ma sae da ta sake masa dressing tasa bandage ta rufe masa miki ya fito tsaf tsaf.
Mami kuwa sae da ta tabbatar sun kammala snn ta dawo.
Cikin fara'a tayi wa bintu sannu da qoqari tare da snr da ita cewa ta shirya ta maida ta gida kad dare yazo ya qara yi.
Ba musu bintu ta shirya,mami ta kalli waheed dake zaune kan bed ya jingina bayan sa da pillow tace masa zata je ta dawo,yace mata a dawo lafiya snn suka fita.

Da murna anti Hafsa ta tarbi bintu tana mata congratulation sbd tun asibiti bintu ta kirata ta snr da ita cewa waheed ya farka kuma bai manta rayuwar sa ta baya ba.
Wacce nan take bintu na gama snr da ita ta kira su umma da kowa ta snr dasu har Abdallah dake school,dan ana gama yanke shar'ia ya koma a washe garin rnr.

Washe gari guraren qarfe goma sha d'aya se gasu Abbas dasu umma sun zo,bintu bata yi mamakin zuwan su ba sbd Anti Hafsa ta snr da ita cewa zasu zo duba waheed cos gobe gobe ne tafiyar su india,shine suka ga tunda ya farka ya dace ace sunzo sun ganshi kafin su tafi India d'in.

Tare suka je asibiti gabad'ayan su wato umma da Abba,Anti Hafsa,Abban ilham,jabir,Abbas,Bintu,da kuma Nafee.
Da murna sosai mami ta tarbe su dan bata ko san da zuwan nasu ba se ganin su da tayi, yayinda su kuma fuskar su a sake suka gaisa tare da yiwa waheed sannu da jiki wanda ya amsa cikin girmamawa da mutuntawa.
A nn suka sami hajiyar Husna itama taje duba shi,yana d'auke da d'ansa da husna ta haifa wanda aka saka wa suna saif.
Qwallah ne suka ciko a idon Bintu a lokacin da take kallon saif kamar sa sak da waheed ba inda ya rago shi.
Da kanta ta kar6e shi daga hannun waheed ta ba su umma dasu Anti Hafsa suka ganshi.
Kyakkyawar addu'a suka mishi kan Allah ya raya shi akan sunna Husna kuma Allah yaji qanta yasa ta huta.
Mami da Hajiyar Husna suka ce Amin.
Waheed kuma a lokacin magana suke shida Abbas har yana tambayar sa Abdallah fa yace masa shekaranjiya ya koma school.
Basu kai awa d'aya ba suka ce zasu koma,mami ta raka su tana musu Allah tsare hanya tare da qara yi musu godiyar hidimar da sukayiwa waheed mai yawa,duk da sun san cewa gobe ne tafiyar su india amma basu gaza gurin kawo masa abubuwan da mara lafiya zai buqata ba,wanda mami taji dad'in hkn ba kad'an ba ta kuma yaba da qoqarin su.

Su umma da Abba kai tsaye kebbi suka koma,Abbas,Abban ilham da jabir suka bi jirgin sha biyu zuwa abuja, yayinda Nafee tabi Anti Hafsa zuwa gidan ta,ya kasance Bintu kad'ai suka bari a asibiti tare da waheed dan hajiyar Husna ta ma riga su umma wucewa tare da saif dan a hannun ta yake,mami kuwa bayan sun raka su umma ita da bintu sun dawo ta d'an tafi gida.

Qatuwar darduma bintu ta shinfid'a a nn tsakiya wato tsakanin sofa da bed kmr yanda waheed ya buqata dan so yake ya sauko daga kan bed zaman gadon ya ishe shi.
Bayan bintu ta taimaka mishi ya sauko ya zauna tasa mishi pillow a jikin gina ya jingina bayan shi tare da d'aura mishi wani d'an qaramin pillow ya d'aura qafar sa dake masa ciwo, snn ya buqaci ta d'auko mishi grapes da apples biyu a cikin fridge wacce ta d'auko tazo tayi zaune a gaban shi ta lanqwashe qafafu tana yanyanka apples d'in a plate kmr yanda yace ta mishi.
Yanka apples d'in take ta d'ago taga ya hard'e hannuwan sa a qirji se kallonta yake d'auke da d'an murmushi a fuskar sa,cikin kyakkyawan salo ta d'aga mishi gira had'e da masa wani kallo da kyawawan idanuwanta na alamar kallon fa, kafin yace komai ta d'auki slice d'in apple ta kai bakin shi wai koshi yake so yaci.
Bai bud'e bakin nasa ba sae hannu yasa ya kama apple d'in had'e da lallausan hannunta duk ya kama ya riqe yana kallonta yace"shagwa6ar me naga kina yiwa umma a d'azun harda yi mata kuka me kike so ne?
Sai da ta zare hannun ta a hnkli daga riqon da ya mata snn muryar ta a natse tace"Ban san cewa da wuri zasu tafi ba shine da tace zasu koma nake roqonta karsu tafi yanzu su bari se da yamma,shine tace min a'a komawa zasuyi nace to zan bisu in dawo da yamma,nn ma tace min a'a,shine nayi kuka tace idan ganin gida nake so inje na bari sae mun dawo daga india dai dai jikinka yayi sauqi se naje.
Waheed dake kallonta ya girgiza kansa d'auke murmushi yace"shagwa6a66iya shine kike yima kuka ni nama d'auka ko wani abu kk so ashe rigimar kice kawai ta tashi"
Turo baki kawai tayi tana kallon sa,dan ta san bata da abun cewa ya fita gaskiya,dmn bai kamata ace a yanayin da yake ciki tayi zancen wani zuwa gida ba sae ya sami lafiya tukun,duk da dai tana da buqatar zuwa ganin gida d'in.
Grapes waheed ya d'auka ya tura mata a bakin nata da ta turo se jin yayi ta cije masa yatsa,a take yayi saurin zare yatsan nasa yana yarfi dashi yayinda ya 6ata fuskar sa yana kallon ta kmr wani qaramin yaro,bintu dake masa dariya ta kama hannun sa tana hura masa yatsar had'e da murza masa gurin a hankali.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 44_*
Suna

Please Login or Register in order to submit comment