Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nn ba.
Beauty dake sauraren ta tasan a yanda taji labarin bokan ba makawa zae iya yin duk yanda zeenah ta tsara.
Amma bazata yarda ayi aikin ba so take ta musu muguntar da har su mutu baza su manta ta ba,ta girgiza kanta tare da fad'in"zeenah ba wai naqi bane ina son ki fahimci cewa mutanen nn su bintu tsaye suke ko yaushe cikin addu'a shiyasa nace miki kawai a bar zancen zuwa gurin boka ko yanda Barrister Abubukar qasim ya tsara yayi ba sae anyi wani abun nn ba ko kuna tantamar kmr bazai iya ba?
Aa we trust him yana da ilimin da zai iya yin komai yanda ya tsara, kawai cece kuncen da akeyi a kotu ne yake d'an bani tsoro dan naga Barrister Usman Ali d'in nn da gaske yake son ganin ya qwatarwa bintu haqqinta.
No kar ki damu ki cire duk wani tsoro a ranki ba abinda zai hana muyi nasara akan shari'ar nn.
Tace"ok to zakiyi kwana nawa a nn kafin ki koma sokoto?
Eh to gaskiya bazan koma ba sae a daren da za'a sake wani zama a kotu sae mu had'u daku a washe gari ko zamu tafi tare da kune gabad'aya?
Zeenah tayi saurin cewa"A'a kije kawai zamu zo daga baya"
Beauty tace"ok to ni zan fita da akwai inda nake son inje"
Zeenah tace"baxa kici abinci ba kafin ki fita?
Aa sae na dawo tukun daga haka ta tashi ta fita ba tare da ta jira me zasu ce ba.
Kmr jira sarah keyi tace"zeenah kinji ta wae sae daren da za'a sake wani zama zata koma ya za'ayi knn muda keson komai ya kammala kafin lokacin?
Zeenah tace"kar ki damu indai har zata koma a rnr ba matsala komai zaiyi yanda muke so kafin washe gari, Barrister kuma ko bayan an gama shari'ar ne se mu cika masa kud'in aikin sa gabad'aya.
Sarah tace"olryt shikenan"
Beauty da ke la6e a bakin qofa bata riga ta wuce ba ta girgiza kanta d'auke da shu'umin murmushi snn tabar gurin wacce da gangan tace har se daren da za'a sake wani zama zata koma sbd tarkon da take shirin had'a musu.

Ranar da beauty zata koma sokoto da wuri ta koma sbd so take ta kammala duk wani tarkon da take shirin had'awa su zeenah ba tare da an sami matsala ba kafin gobe.
6angaren su zeenah kuwa suma sun kitse magana da wa end zasu kwato musu dukiyar handsome gun beauty sun musu misalin gidanta da ta siya a nn sokoto da yanda zasu shiga gidan a sauqaqe duk sun musu bayani dare kawai suke jiran yayi su kai mata farmaki.

Washe gari ne za'a sake wani zaman kowa ya hallara a kotu an kammala duk wani abu da ya kamata ayi kafin a fara shari'a.
Barrister Usman Ali ne ya fara magana acewar yana son kotu ta bashi dama yana son zai yi tambaya wa en fashi.
Alqali yace kotu ta baka dama.
Bayan sun fito barrister Usman Ali ke cewa bincike ya nuna cewa a lokacin da en sanda suka tuhume ku sam baku tsaya wani kwana kwana ko ja'in ja na qin fad'a ba,kai tsaye kuka fad'i cewa bintu ce ta tura ku hakan ya nuna cewa ba makawa sharri ne wato sa akayi ku fad'i cewa ita ta tura ku dan haka kotu na buqatar kuyi mata bayanin gaskiyar wanda ya tura ku ba tare da kun wahaladda shar'ia ba.
Shiru sukayi wa enda basa jin zasu iya yiwa beauty rashin alqawarin da suka d'aukar mata jiya da dare da taje gurinsu cikin 6adda kama izuwa namiji wacce da zuwanta takarda kawai ta miqa musu ta wuce yayinda takardar ke kunshe da tsarin yanda take son su fad'a idan an tambaye su a kotu gaskiyar wanda ya tura su.
Basu tsaya wahaladda shar'ia ba kmr yanda Barrister Usman Ali ya buqata suka fad'i cewa gaskiyar wa enda suka tura su sune wa enda ake zargi wato su zeenah.
Bansan ta yanda zan gaya muku irin razanar da su zeenah sukayi ba wa enda suka miqe tsaye zumbur cikin tsananin tashin hankali kafin su iya cewa komai,kae tsaye sae ga beauty ta shigo wacce cikin muryar kuka tace"tabbas hakane ya mai girma mai shari'a,ni shaida ce akan abinda suka fad'a sam bintu bata da laifi ko d'aya a kan laifin da ake tuhumar ta dashi kuma duk abunda bintu ta fad'a a gaban kotu su zeenah sun mata gaskiya ne sun qaryata ta ne kawai dmn su cimma burin su na ganin cewa bintu ta qare rayuwar ta a lalace,amma ina son kotu ta bani dama in qara mata gamsasshen bayani.
Alqali ya jinjina kansa tare da fad'in kotu ta baki dama.
Nan beauty taje ta tsaya gaban a kotu(bar).
Wacce sae da ta fad'i ainihin sunan ta snn ta fara bayanin cewa ni qawar su zeenah ce sosai na yarda dasu na basu amana da duk wani sirrina bana iya 6oye musu haka suma wasu abubuwan su duk basa 6oye min har ma abinda suke son aikatawa ga wanda suke hassada suna gaya min,amma kasancewar ko kad'an bana son halin nn nasu na kan zauna na basu magana kan suji tsoron Allah abinda sukeyi su daina ba kyau, amma sam basa jin shawara ta har ya kasance ma sun daina gaya min, ni kuma se na d'auka ko sunji shawara ta ne ashe ba haka bane suna nn hassadar su se qaruwa take kan duk wanda suka ga cewa yafi su da wani abu ko jin dad'in rayuwa se sunyi duk yanda zasuyi suga cewa rayuwar ta lalacewa mutum ya daina jin dad'in ta kwata kwata komai shaquwar su dashi kuwa,mutane sun fi aqirga wa enda suka cutar suka raba su da duk wani farin cikin su,sae dai na bintu nn duk yafi muni dmn sun jima suna son ganin cewa rayuwarta ta ta6ar6are amma burin su ya kasa cika a lokacin da suke so, shine suka qulla mata wnn sharrin na ganin cewa sun gama da ita har abada a manta da wacece ita kwata kwata har iyayen ta ma su manta ta,yayinda ni kuma zan zamo next target d'insu dmn sunga alamun na fara wuce su.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka.
Barrister Abubukar qasim da duk ko'inan sa zufa se karyo masa take yayi qarfin halin cewa"zainab ta yaya akayi kika san komai bayan da kanki yanzun nn kince tuni sun daina gaya miki duk wani tsaren tsaren su hakan na nuna kin shirga qarya ne dmn kiyiwa kotu yawo da hankali koh"
Cikin kuka Beauty ta girgiza kanta tare da fad'in"ko d'aya bana da nufin nayiwa kotu yawo da hankali sae dai na gaya mata gaskiyar abinda yake faruwa.
Alqali yace"ci gaba da bayanin ki, kotu na sauraren ki gaya mana yanda akayi kika san komai"
Tace"naji komai ne a lokacinda nazo zan shiga d'aki yayinda isowa ta knn na fito daga sokoto naje Kebbi.
Ban riga na shiga d'akin ba naji suna magana cikin murna da farin ciki kan irin nasarar da sukayi a rayuwa, suna labarin duk wanda suka cutar da irin nasarar da sukayi akansa har suka zo gun bintu ina jin duk wani bayanin cutar da ita da sukayi da kuma zancen cewa ta auri waheed dan dukiyar sa ne, duk su suka qulla har en fashin da suka kashe Husna duk su suka tura a kashe ta kuma da sanin su suka kira police su kama en fashin dan kawai idan an tuhume su suce bintu ce ta tura su wa enda en fashin sun yarda da haka ne a bisa alqawarin da suka d'aukar musu na cewa zasu fitar dasu kuma ko nawa suke so zasu basu bayan sun fitar dasu.
Basu san ina nn ina sauraren su ba suka ci gaba da bayanin yanda suke son shari'ar nn ta kasance wato zasu je gun wani shaharraren bokan su da ya saba musu aiki ya musu convincing kowa har Alqali dmn ya yankewa bintu hukunci yanda suke so wato d'aurin rai da rai a gidan kaso ba tare da kowa ya iya musawa ba haka kuma kowa ya manta ta gabad'aya tamkar ma ba'a ta6a yin ta a duniyar nn ba,bansan lokacinda kuka ya qwace min ba sbd tausayin bintu da naji,nayi saurin hana fitowar sautin kukan nawa sbd maganata da naji sun d'auko acewar idan sun gama da bintu nice next target d'insu na ganin cewa sun qwace min dukiyar da iyayena suka mutu suka bar min.
Nan kawai na shiga d'akin ba tare da nayi wani tunani ko shawara ba wa enda suna gani na suka san cewa na gama jin komai, amma sam basu damu da hakan ba hankalin su a kwance suke kallona,ban nemi nayi fad'a dasu ko wani abu ba sae ma roqon su da nayi da su tausaya su janye qudurin su a kan bintu ko dan kasancewar ta er uwa a gare su,snn ni kuma ko nawa suke so a dukiya ta su fad'a nayi alqawarin zan basu.
Fafau suka ce ban isa na hana su abinda sukayi niyya ba,ganin haka yasa nace muddin basu janye qudirin su a kan bintu ba tofa lallai zan toni asirin su,suka ce tabbas baza su fasa abinda sukayi niyya ba kuma muddin na toni asirin su sae sun sa an kashe ni,nace sae dai su sa a kashe ni, idan baza su fasa ba nima bazan fasa ba.
Har abun ya zamo mukayi fad'a kaca kaca dasu,na dawowa ta sokoto na kasa zama na kasa tsayi cike da tunanin lallai tunda suka furta zasu sa a kashe ni ba qaramin aikin su bane zasu iya turawo a kashe ni da dare kar washe gari na toni asirin su a kotu nn na yanke shawarar kiran en sanda dmn suzo su bani taimako,hakan kuwa da nayi shi ya taimake ni dmn a cikin dare sae ga qarti kusan su uku sun zo kashe ni ba tare da sun san da akwai en sanda a gidan ba,kafin su min komai en sanda suka zo suka kama su,suka kuma sa su kira su zeenah su gaya musu cewa sun kammala aikin su da suka sasu gobe da safe idan an gama shari'a zasu had'u,shiyasa su zeenah sam basu tashi hankalin su ba suka zo kotu cike da murnar burin su zae gama cika.
A nn ta kawo qarshen zancen ta tare da fad'in idan kotu na son tabbatar da cewa abinda na fad'a gaskiya ne a shirye nake da nasa police su shigo da wa en nn qartin.
Nan kotu ta buqaci ganin su sae gashi kuwa en sanda sun shigo dasu d'aya bayan d'aya tare da inspector Bashir wato abokin Abbas hakan yasa Alqali ya qara tabbatar da zancen beauty gaskiya ne dan yasan inspector bashir mutum ne mai gaskiya babu wani cin hancin da ke tsone masa ido.
Babu wani 6ata lokaci Alqali ya yankewa su zeenah hukuncin d'aurin rai da rai a gidan kaso snn kuma za'a cisu tarar naiar dubi d'ari biyar dmn bintu ta magance matsalar mahaifar ta da suka so hallakawa da gangan.
en fashi kuma hukuncin kisa aka yanke musu ta hanyar rataya haka suma wa en nn qartin ba'a barsu ba aka yanke musu nasu hukunci.
D'auke da murna beauty ke kallon su zeenah wa enda tun lokacinda ta shigo ta fara bayani ita kawai suke kallo hawaye wani na bin wani a idon su, cikin tsananin rud'u da tashin hankali na jin yanda duk tabi ta lauye su ta d'aura duk wani laifi akan su da wanda sukayi da ma wanda basuyi ba.
Suna ji suna gani en sanda suka sa musu ankwa suka tafi dasu iyayen su kmr wasu zautacci suka bi en sandan sae kuka suke suna basu haquri.
En fashi kuwa da za'a wuce dasu kallon beauty sukayi wacce a kafaice ta musu signal kan su kwantar da hankalin su zata fitar dasu kafin a yanke musu hukunci wacce a ranta sam ba haka bane sun mata ganin qarshe knn ba wani fidda su da zatayi idan buqatar en fashi ta taso mata ta nemi wasu dan har yanzu haushin su take ji kan abinda sukayiwa waheed.
6angaren Bintu kuwa farin ciki fal taji a ranta wacce taje cikin kukan farin ciki tana godewa beauty.
cikin sakin fuska beauty ta kama hannyen Bintu tana fad'in ba komai ae yiwa kaine.
A hnkli Bintu ta sa6ule hannayen ta daga riqon da beauty ta mata tana kallon mami da ta qaraso gurin tana kallon ta wacce a hnkli ta ware hannayen ta cikin kuka tana son bintu tazo gareta,hawaye ne suka silalowa bintu a hnkli,ba tare da ta musa ba taje jikin mami wacce ta rungume ta sae haquri take bata kan yarda da abubuwan da taji bayan ta fi kowa sanin irin son da take yiwa waheed,komai bintu bata iya cewa ba sae haquri itama take ba mami kan zubar da cikin farko da tayi bayan tasan waheed ne kad'ai d'anta da take matuqar son ganin jika daga gare shi da shima yake matuqar son haifuwa amma bata dubi hkn ba tabi son zuciya da rud'in su zeenah.
Mami ta d'agota tana share mata hawaye cikin nuna cewa ba komai ae kuskurene na yarinta kana taja hannun ta suka je gun su umma dasu Abba dake tsaye suna kallon su,farin ciki fal a ran kowannen su na yanda shar'iar nn ta kasance.
Cike da nuna rashin jin dad'in abinda mami ta aikata a gare su ta basu haquri suka nuna ae ba komai komai ya wuce asalima su basu ga wani laifinta ba tunda ga yanda abun ya kasance,mami tace duk da haka dai bata kyauta ba suyi haquri suka ce ba komai wlh sun haqura.
Nan suka d'unguma su dukan su gabad'aya zuwa asibiti dmn dubo waheed.

Beauty kuwa gida ta wuce kai tsaye wacce da isar ta motar Barrister Abubukar ta fara cin karo da ita yana tsaye jikin motar tasa yana jiran isowar ta.
D'an shu'umin murmushi ta saki snn ta fito daga cikin mota taje gab dashi tana masa wani kallo kana tace"me kuma ya kawo ka ko kaima so kake in toni asirin ka a yanke ma naka hukunci?
Barrister dake kallonta yace"haba beauty me yayi zafi da zakiyi wa su zeenah haka bayan naga kanku a had'e yake.
Su suka ware ni suna son cutar dani shiyasa na musu haka.
Me suka miki?
Wannan ba damuwar ka bace kuma ina son ka sani kaima ba wai nabar ka bane,dan ina son kamin wani aiki ne yasa ban tona maka asiri ba idan kuma kaqi kamin aikin wlh zan toni asirin ka na fad'i har ma abinda baka yi ba kmr yanda nayiwa su zeenah.
Ba yanda Barrister ya iya yasan zata iya dan ya fahimci ta fishi bala'i.
A sanyaye ya gyad'a kansa tare da fad'in"ina jinki gaya min me kike so in miki.
Waheed nake son kaje ka sato min a asibitin uduth mu bar garin nn dashi cikin daren yau....what! meyasa?
Bana da buqatar ka sani yanzu, kawai dai anjima da dare ka zama cikin shiri zanzo in d'auke ka mu tafi a mota ta.
Yace"no wlh kinsan satar waheed da kmr wuya ko kin manta da sojawan da ke tsare dashi ne"
Ban manta ba Barrister amma banyi tunanin za'a ci gaba da tsare shi ba bayan an gama shari'a.
Duk da haka dai kije da yamma ki duba duk abinda ake ciki sae ki snr da ni.
Tace"ok to"
Kana ya shiga motar sa ya wuce ita kuma ta shiga daga ciki.

Yamma nayi ta shirya taje asibiti mami bata yi mamakin ganin ta ba sbd tasan asibitin take aiki kuma akai akai ta kan zo ta duba waheed wacce sam bata san dalilin hakan ba ta d'auka ko dan tana ma'aikaciya ne take d'an zuwa duba shi, kuma ko kotu a zuwan farko bata lura da ita ba sae wnn karon.
Bata wani jima ba tace zata koma mami ta mata godiya da irin kulawar ta.
Beauty na fita bata zarce koina ba sae inda ta faka motar ta bata shiga motar ba sae jingina jikinta tayi a jikin motar,ta kira Barrister wanda da d'aga wayar yace ya ake ciki sojawan na nn ko kuwa?
Tace"eh still sojawan na nn tsare a bakin qofar d'akin amma kar ka damu zamu iya aiwatar da aikin mu ba tare da an sami matsala ba"
Ta yaya beauty?
zan baka kaya kayi shiri kmr wani doctor ni kuma se nayi shirina a matsayin nurse, kaga hakan zai sa baza su hana mu shiga ba bare ni sun san aiki nake a nn dan haka ka shirya sae dare yayi sosai zan zo har gidan ka in d'auko ka muzo, na tabbatar a lokacin mami tayi bacci amma duk da haka zamu fesa mata wata powder da baccin nata zae qara nauyi ta yanda har mu fita dashi baza ta farka ba yayinda su kuma sojawan zasu d'auka ko zamu canza masa d'aki ne sbd ba haka kawai zamu fita dashi ba akan bed zamu keka shi,hope get it?
Na fahimce ki amma meyasa zakiyi haka bayan kinada hanya mafi sauqi da zaki mallake shi?
Hakane amma wnn hanyar da kaga na d'auko zata fimin dad'i inci kare na ba babbaka.
Kamar ya?
Wato Barrister jiya ne naji wata magana a bakin doctorn da nake samun rahoton lfyr waheed dan yana d'aya daga cikin masu kula dashi,wanda ya gaya min cewa waheed ya sami er matsala a qwaqwalwar sa sakamakon dukan da en fashi suka masa aka wanda ba lallai bane in ya farka ya iya regaining rayuwar sa ta baya shiyasa nake son d'auke shi na tafi dashi can inda nake so,ya farka hannu na kaga bai san kowa ba sae ni ya fara gani,se inyi training life in sa a yanda nake so na aure shi muyi rayuwar mu daga ni sae shi ba wani mai takura mu.
Barrister ya numfasa tare da fad'in to idan qwaqwalwar sa bata sami matsala ba yanda ake tunani ba fa?
Wnn ba matsala bane sae inyi using kwalli na in kuma sa boka yasa ya manta kowa har mahaifiyar tasa.
Amma to meye dalilin ki na taimakawa bintu na d'auka ko kin tausaya mata ne kin haqura da waheed zaki bar mata shine suci gaba da rayuwar su?
Haba dai Barrister kmr baka da fahimta,nifa ba dan tausayin bintu bane yasa na toni asirin su zeenah sae dan ganin cewa nima so suke su hallaka ni dan haka kama fita harakar zancen bintu ko mutuwa zatayi wlh sae na rabata da waheed, kai zan dai rabashi da uwar sa bare ita.
Yace"to shikenan ina sauraren ki anjima se kinxo"
Tace"olryt bye sae nazo d'in,but plz ka zama cikin shiri dan wlh bana son wani 6ata lokaci da mun d'auke shi nake son mu bar garin nn dashi kae tsaye.
Yace"kar ki damu komai zaiyi yanda kike so"
Daga haka suka tsinke wayar ta juya knn zata bud'e ganbun motar ta,se sukayi ido hud'u da mami wacce tun lokacinda beauty ta fara waya tun daga farko har qarshe taji komai amma sae mami ta had'iye duk wani yanayin da ta shiga bata nuna mata taji ba,sae wani tsadadden bracelet na gold ta miqawa beauty tare da fad'in"abun hannun ki ne da ya sa6ule ya fad'i baki sani ba shine na biyo ki na kawo miki"
Beauty wacce da farko har ta tsorata da ganin mami girshi,amma da ta fahimci kmr mami bata ji komai ba, ta sauke ajiyar zuciya a hankali snn ta kar6i abun hannun tare da mata godiya.
Cikin sakin fuska mami tace"ba komai a gaida mutan gida"
D'auke da murmushi Beauty tace"to zasu ji snn ta shiga motar ta ta wuce"
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 42_*
Cabd'i!
cewar mami wacce ta fad'i hakane tare da fitar da nannauyan ajiyan zuciya,ta jinjina kanta had'e da fad'in"lallai wato yarinyar nn dalilin da yasa take yawan zuwa duba waheed knn,shi kuma doctor a tunanin sa duk tausayawa ne yasa har ya gaya mata matsalar da waheed ke d'auke da ita ni bai gaya min ba,
hm! innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Kana ta wuce office d'in likitan qwaqwalwa dan tasan ba makawa a bakin sa ne beauty taji matsalar da waheed ke d'auke da ita a cikin qwaqwalwar sa.
Da shigar ta office d'in cikin girmamawa ya gaida ta tare da nuna mata kujera ta zauna.
Mami ta zauna tana mai kallon sa muryar ta a natse tace"Haba doctor sa'id ashe dama waheed ya sami matsala a qwaqwalwar sa shine baka gaya min ba, sae da na jiyo a shanun talla, meye dalilin ka na qin gaya min a matsayina na mahaifiyar sa da ya zama dole in san da wnn matsalar"
Dr sa'id ya numfasa tare da fad'in"kiyi haquri hjy bana son in gaya miki ne damuwa tazo ta qara miki yawa shiyasa na bar zancen har sae ya farfad'o tukun inga ya yanayin sa zai kasance,amma dan Allah hjy a bakin wa kika ji cewa waheed ya sami matsala a qwaqwalwar sa?.
Mami tace"Har ka manta wacce ka gayama?
Doctor yayi shiru kana yace"Zainab beauty ita kad'ai nasan na gayawa amma bada wata manufa na gaya mata ba wlh sae dan ganin yanda take tausayin waheed ta damu dashi sosai.
Mami tace"shikenan ba komai,amma ina son dan Allah kayi shiru da bakin ka kar ka tuntu6e ta da wnn mgnr"
Yace"inshaa Allah hjy"
Nan mami ta tashi ta fito,ta dawo d'akin da aka kwantar da waheed.
Ta sami sojawan da ke tsare a bakin qofar d'akin ta nemi da su shigo da akwai mgnr da zatayi dasu.
Bayan sun shigo d'akin ta gaya musu duk abinda yake shirin faruwa anjima da dare,dan haka tana son su kula da kyau kuma su zama cikin shiri,zata kira police ta snr dasu suzo dmn so take a kama su red handed.

Beauty wacce gabad'aya ta gama yarda cewa mami bata ji komai ba, dare nayi guraren qarfe 2 taje har gidan barrister ta d'auko shi suka zo asibiti cikin shirin su kmr yanda beauty ta tsara.
Kae tsaye suka nufi d'akin da aka kwantar da waheed kmr wasu masu gaskiya.
Sae dai a zuciyar Barrister sam hankalin sa ba a kwance yake ba,wanda kafin su isa yake cewa beauty"wae beauty kina ganin ba matsala har mu fito da waheed mu wuce dashi a gaban sojawan da ke tsaron shi su kalle mu kawai ba tare da sun ce mana komai ba.
D'an guntun tsaki tayi tare da fad'in "kai ka cika tsoro wlh kaman ba namiji ba,ae nasan yanda zanyi dasu ka kwantar da hankalin ka kawai ka biyo ni muje.
Nan Barrister yayi shiru bai sake cewa komai ba har suka isa,sosai beauty taji dad'in ganin ba sojawa a bakin qofar d'akin,ta kalli barrister tare da fad'in"kaga ma basa nn,dan haka sae ka kwantar da hankalin ka muyi aikin mu yanda ya kamata,amma ka bari in fara shiga tukun inga ko mami tayi bacci,dan matar akwai ibadah,rnr cikin dare nazo a sace dan in ga waheed na same ta sae nafilfili take bayan ta idar kuma tayi zaune a gaban shi sae tofe shi take da addu'o'i.
Barrister yace" shikenan je duba d'in"
Nan beauty ta bud'e qofar d'akin sannu a hnkli

Please Login or Register in order to submit comment