Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babban case da kmr wuya su bada beli"
Tayi mgnr ne cikin muryar kuka har hawaye na sauka akan kumatun ta.
Abban ilham ya tafi da ita a hankli zuwa jikinsa yasa tafin hannun sa yana share mata hawaye yana fad'in"kiyi haquri hafsa komai zae zo da sauqi inshaa Allah dmn inspector d'inda case d'in yake hannu sa abokin Abbas ne wanda ko kad'an baiji dad'in da bazai iya bada belin bintu ba amma dai yace musa qarar wa enda muke zargi tukun.
A hnkli ta d'ago daga jikin sa tace"shikenan yanzu ina ka bar yaya Abbas?
Na barshi a mota yana waya amma ina jin kmr ya shigo.
Tace"to muje kuci abinci sae ayi shawarar yanda za'ayi.
Nan Abban ilham ya tashi suka fito suka samu Abbas zaune kan doguwar kujera yana yiwa jabir bayanin yanda abun ya kasance inda jabir yayi shiru cike da damuwa a nn anti Hafsa keyi wa Abbas sannu da zuwa wanda ya kasa cewa komai sae mgnr belin bintu ya mata kan tayi haquri ga yanda abun ya kasance tace"haka Abban ilham ya snr dani yanzu damuwa ta d'aya shine yanda bintu zata yi ta zama a gurin en sanda har se an gama shari'a.
Abbas dake kallonta yayi shiru wanda yanzu wani irin tausayin bintu yake ji a ransa,kana yace"ki kwantar da hanklin ki bana jin shari'ar nn zata jima tunda kunce da kunnen ku kunji irin mugayen furucin da su zeenah sukayi kan se sunga bayan bintu.
Tace"tabbas nida Nafee munji da kunnen mu wanda a lokacin ne ma muka musu tsinannen duka.
Yace"shikenan zan samu qwararren lauya da zai tsaya mana"
Tace"to yaya su umma fa still baza'a gaya musu ba?
Dole zasu sani Hafsa amma ki bari nida kaina zan gaya musu ta yanda hankalin su bazai tashi sosai ba.
"To"
Cewar anti Hafsa wacce ta nemi da su taso suci abinci.

Bayan sun kammala cin abinci ne Nafee tazo gidan tare da mijinta ya jajanta musu kasantuwar abinda ake ciki snn ya koma.

Anti wlh har kuka nayi a yanayin da naje na sami bintu kafin muzo nn,se dai ince Allah ya isa tsakanin mu dasu zeenah,ba kuma zamu ta6a barin su ba wlh,baqin nufin su akan bintu se ya koma kansu wlh shegu en iska wa enda baza su ta6a ganin manzon rahama ba inshaa Allahu.
Anti Hafsa tace" hm bari kawai ni na matsu inga an fara shari'ar nn dmn ina tsoron kar suzo da wani tuggun kuma"
Anti Hafsa addu'a zamu dage da ita ba dare ba rana sam kada musa wasa,da yardar Allah wnn karon baza suyi nasara ba komai tuggun su kuwa.
Anti Hafsa tace"to Allah ya shige mana gaba yasa ayi shari'ar nn cikin sauqi"
Nafee tace"Amin".

*Kebbi*
Dasu zeenah suka ji ansa qarar su sun d'an girgiza amma daga baya abin se ya basu dariya har su za'a sa qara suda yanzu burin su yana gab da cika na kar6e dukiyar handsome daga beauty,da ko nawane zasu iya zubewa na ganin cewa shari'ar ta daqushe bintu ta dawamma a fursun.
A cewar Sarah,zeenah kuwa tace"ke ni Sarah wlh ko kaf duka dukiyar zata qare a kan case d'in nn bani da baqin ciki dmn nafi buqatar inga bintu ta dawamma a fursun kan dukiyar nn,mu zuba muda su shege ka fasa zamu ga tsakanin 6era da giwa wa zae janye wani.
Sarah ta fashe da dariya tace"inafa kin ta6a ganin inda 6era ma yace zai ja da giwa"
D'auke da dariya Zeenah tace"ah to naga zancen suke so zamu ga ko 6era zae cinye gasar ne oho.
*Sokoto*
Abdallah ne yazo gun bintu tare da jabir wacce tana ganin Abdallah ta nemi tayi kuka Abdallah yayi saurin girgiza kansa alamar a'a dan yasan tana fara kukan bazai iya hana fitowar hawaye a idon sa ba,wanda cike da tausayi ya janyo ta jikinsa yana bata magana cikin rarrashi kan tayi haquri na d'an qanqanin lokaci ne wnn inshaa Allah a cikin kwanakin nn da anyi shari'a komai zai dawo kmr ba'ayi ba.
Ta gyad'a masa kai cikin muryar ta mae cike da jin kuka tace"to yaya,yaya waheed fa ance yana asibiti unconscious"
Yace"ki kwantar da hanklin ki inshaa Allah zai sami lafiya Husnah kuwa da ta rasu Allah yaji qanta yasa aljannah firdausi ce makomar ta.
Bintu tace"Amin" tare da sa hannu ta share hawayen da suka zubo mata dmn har ranta taji zafin mutuwar Husna ba kad'an ba.
Abdallah yasa tafin hannun sa ya qara share mata hawayen snn yace"mu zamu koma anjima Barrister usman Ali zai zo ya d'an tattauna dake kinji"

A hnkli ta gyad'a masa kai ba tare da tace komai ba.
Bayan sun tafi da d'an jimawa se ga barrister Usman Ali yazo d'in kmr yanda Abdallah ya gaya mata.
Da kulawa barrister d'in ke kallonta wanda ya kira sunanta a natse ta amsa mishi snn yace"suna na Barrister Usman Ali nine wanda zae kare ki a zaman kotun da za'ayi ina son ki fad'a min haqiqanin gaskiyar cewa shin kece kika tura wa en nn en fashin dmn su kashe waheed da matar sa Husna?
Bintu ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace"wlh bani na tura su ba sharri ake min na rantse"
Shikenan kar ki damu ki kwantar da hanklin ki ki kuma dage da addu'a dmn kinsan shari'a sa6anin hankali ce.
Muryar ta a sanyaye tace"ina kanyi kuma zan ci gaba"
Yace"to shikenan ina son koda anje gaban kotu kar kiji tsoron komai ki fad'i gaskiyar abinda kika sani kinji.
Gyad'a masa kai tayi tare da share hawayen da suka zubo mata sae ga er sanda tazo ta jata suka koma,Barrister Usman Ali da yabi bintu da kallo ya girgiza kansa d'auke da tausayin ta a ranshi.
*Kotu*
Kowa ya Hallara ba wanda bai zo ba hatta su umma dama iyayen su zeenah kama da mami da kuma hajiyar Husna.
Bayan mai gabatar da case d'inda za'ayi shari'a a kansa ya gabatar ya miqa takardun case d'in zuwa ga alqali snn ya zauna.
Alqali ya umarci Barrister's da su gabatar da kansu.
Barrister Usman Ali ya miqe tare da fad'in "ya mai girma mai shar'ia suna na Barrister Usman Ali nine lauyan da zai kare wacce ake tuhuma da laifi.
Kana d'ayan barristern ya miqe"yace ya mai girma mai shari'a suna na Barrister Abubukar Qasim nine lauyan da zae kare wa enda ake qara.
Bayan sun zauna Barrister Abubukar Qasim ya miqe dmn fara shari'a kmr yanda alqali ya buqata.
Yace"ya mai girma mai shari'a ni a gani na dama kutu bata tsaya wahalar da kanta da sauraren wnn qara ba dmn shaidu da dama sun tabbatar da cewa bintu ce ta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi amma tasa qarar wa enda basu ji ba basu gani ba dmn kawai ita ta samu ta ku6utar da kanta.
Muna da hujjoji da zasu tabbatar wa kotu da haka in kotu ta bani dama zan gabatar da hujjojin d'aya bayan d'aya nagode.
Kana ya zauna Barrister Usman Ali ya miqe yace"ya mai girma mai shari'a"ina son tabbatar wa wnn kotu mai adalci cewa bintu baza ta iya aikata laifin da ake tuhumar ta dashi ba dmn a tahiri ko kiyashi bintu bata ta6a kashewa ba bare har ta iya tura en fashi su kashe en Adam ko en Adam d'in ma wae harda mijinta da take mutuqar so sam wnn ba gaskiya bane kuma na tabbatar idan wnn kotu mai adalci taji shaidu da hujjojin mu zata fahimci cewa tabbas ba bintu ce ta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi ba sharri ne kawai.
A nn yayi godiya ya zauna.
Alqali yace"Barrister Abubakra ko da akwai tambayoyin da zakayiwa wacce ake tuhuma?
Eh ya mai shari'a.
Nan bintu ta fito wacce kallo d'aya zakayi mata kasan cewa tayi kuka har hawayen ta sun qafe.
Yace"Bintu kowa yasan cewa kin auri waheed ne dan dukiyar sa shiyasa baki ta6a yarda ma kin haifu dashi ba jira kawai kike lokaci yayi ki kawadda shi ki kwashe dukiyar ki gudu sea gashi kafin ki aiwatar da nufin ki asirin ki ya tonu mahaifiyar sa tasa ya sake ki wanda hakan yasa kika ji baqin ciki da takaicin rashin cikar burinki shine dan kar a zargi kece kika bar se da akayi watanni abun ya lafa kika tura en fashi dmn a kashe shi dashi har matar sa dan kawai ki samu ki kwashe dukiyar dmn ki cimma burinki koh.......objection my lord bai kamata Barrister Abubukar ya riqa yanke hukunci haka kai tsaye ba bayan kaine alqalin bashi ba wnn izgilanci ne dan haka aja hankalin Barrister Abubukar ya gyara.
Alqali yace"Barrister Abubukar ka gyara kalaman ka tambayoyi zaka mata ba yanke hukunci ba.
Yace"A gafarce ni ya mai shari'a snn ya maida duban sa gun bintu wacce gabad'aya kalaman sa sun sa ta soma kuka.


Kuyi haquri da wnn Wlh kwana biyun nn ban zauna ba.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 39_*
Yace"Bintu ko zaki iya gaya mana babbar hujjar ki ko ince dalilin ki da yasa kike zargin su zeenah.
Bintu ta share hawayen fuskar ta wacce cikin muryar kuka tace"eh zancen cewa na auri waheed dan dukiyar sa ba gaskiya bane duk sharrin su ne hujja ta ita ce da bakin su suka gaya min haka ba'a gun wani naji ba"
Kina nufin kice duk cikin da kike samu qarya ne knn ba gaskiya ba?
Aa ina samun ciki amma bani ke zubarwa ba na farkon ne kawai nasan nayi kuskuren zubarwa a bisa qaddara da kuma gurguwar shawarar da suka bani.
Yace"Ma'ana bayan na farkon duk cikin da kike samu knn haka kawai kk ganin yana zubewa ba tare da kin san dalili ba?
A gaskiya da farko bansan dalilin zubewar su ba se bayan munje gun doctor ya fad'i dalilin da yasa ciki baya zama jikina sanadiyar shan wasu pills da basa bari ciki ya zauna wanda nayi mamakin haka matuqa dan bansan na ta6a shan wani magani ba sae gashi daga baya su zeenah da kansu suka gaya min suke samin magani a ruwan sha na idan naje school ko kuma sun sameni a gida.
Hm naji amma ya mai girma mai shari'a ina so wnn kotu mai alfarma tayi duban tsanaki ta fahimci cewa zancen nn na bintu ta fad'a ne kawai dmn taji dad'in bakinta ta kuma yiwa kotu yawo da hnkli sbd ba wani wanda zai maka sharri yazo haka kawai da kanshi ya gaya maka,nagode kana ya zauna.
Alqali yace"Barrister Usman ko kana da tambayoyin da zakayi wa wacce ake tuhuma?
Eh ya mai girma mai shari'a ina da tambayoyin da zan mata.
Bintu"kince su zeenah ne da kansu suka gaya miki sune suka miki duk wani qulle qulle shin ko zaki iya gaya mana ta yanda akayi har suka gaya miki?
A nn bintu ta gaya masa zuwan su zeenah gurinta wato nn gidan anti hafsa da duk yanda akayi har suka kai ga gaya mata.
Yace"to ya kika ji a lokacin da suka gaya miki?
Da farko nayi baqin ciki sosai dmn ban ta6a tunanin zasu iya cutar dani ba a matsayin su na en uwana da muka taso tare,amma kuma bnyi mamakin jin haka daga bakin su ba dmn kafin su gaya min na fahimci sune sukayi qulle qullen sbd a lokacin da muka dawo asibiti nida yaya waheed bai gayawa mami gaskiyar abinda ake ciki ba 6oye mata yayi sae gashi daga baya kwatsam mami taji komai byn ba wanda yasan da mgnr se su zeenah kawai da na gayawa wanda a tunani na en uwana ne masu qaunata dagaske da zasu bani kyakkyawar shawara ashe ba haka bane cike suke da mugun nufi akaina.
Yace"to a lokacin da suka gaya miki sune ke miki qulle qullen ke kad'ai ce ba wani wanda yaji?
Anti Hafsa da Anti nafee duk sunji.
A nn ya nemi alqali da ya bashi dama yana son yiwa su Anti Hafsa tambayoyi.
Bayan sun fito d'aya bayan d'aya kowaccen su ta mishi bayanin tabbas da kunnen su sunji lokacin da su zeenah ke fad'a ma bintu irin sharrin duk da suka qulla mata har ma daga baya suka fad'i mugayen kalamai akan se sunga bayan bintu.
Bayan sun koma sun zauna Barrister Abubukar ya nemi kotu ta bashi dama yana son yiwa wa enda ake zargi tambayoyi.
Alqali yace"kotu ta baka dama"
Bayan su zeenah sun fito d'aya bayan d'aya ya tambaye su shin ko da gaske ne abinda bintu ta fad'a hakane?
Suka ce sam ba gaskiya bane su kam basu ta6a bata muguwar shawara ba asalima cikin farko da zata zubar ba irin yanda basuyi ba kan kar ta zubar amma fafau tace ita bata shiryi kar6ar cikin ba se ta zubar.
Nan ya basu damar su koma su zauna.
Barrister Usman Ali ya nemi yana son zai yiwa mami tambaya.
Alqali ya bashi dama mami ta fito yace"mami shin ko zaki iya gaya mana a bakin wa kikaji cewa bintu ta auri waheed ne dan dukiyar sa?
Mami tace"naji mgnr ne a bakin mai aikina hajjo.
Nan Barrister Usman Ali ya kira Hajjo da izinin alqali.
Bayan mami ta koma hajjo ta fito yace"Hajjo shin ko zaki iya gaya mana ke kuma a bakin wa kika ji mgnr"
Eh nazo zan shiga gida se naji mgnr a bakin wasu en mata da suka zo a kusa da gidan da nake aiki suna kallon gidan suna magana cikin jimamin abunda ya faru.
Yace"to hajjo shin ko zaki iya gane fuskokin wa en nn en matan ko kuwa?
Eh to a gaskiya duk da rnr ne na fara ganin su bazan manta fuskokin su ba dmn na jima ina kallon su ina sauraren abunda suke fad'a.
Yace "knn yanzu idan nace muje ko'a ina ne zaki iya gano min su?
Ae ba se ma anje koina ba suna nn cikin kotun nn wato wa en nn en matan da ake zargi tabbas ba makawa sune ba wasu ba.
A nn ya numfasa d'auke da alamar murmushi a fuskar sa yace"ya mai girma mai shari'a ina son kotu ta sake bani dama in yiwa d'aya daga cikin en matan tambayoyi.
Nan Alqali ya bashi dama hajjo ta koma zeenah ta fito wacce gaban ta se dukan uku uku yake ganin asirin su na neman tonuwa.
Yace"zeenah kunce duk abinda bintu ta fad'a ba gaskiya bane, mgnr hajjo kuma fa ko shima qarya ne bata kangu ba?
Ae kam qarya ne yaxa ace sau d'aya da ganin mutum bata san shi ba bata ta6a ganin shi ba amma tace wai zata iya gane shi da akwai dai wa enda ta gani bamu ba.
Kuna nufin kuce baku kad'ai ne bintu ta gaya ma halinda take ciki ba da akwai wa enda ta gayawa bayan ku?
Oho mu dai ta gaya mana kuma mun riqe mata sirrin bamu san mun gayawa wani ba.
D'an shu'umin murmushi Barrister Usman Ali yayi wanda qyar idon sa akanta yace"idan gaskiya kika fad'a meyasa to gabad'aya kin tsorata se zufa ke karyo miki har muryar ki na rawa alamar duk jikin ki ma rawa yake....objection my lord bai kamata ace Barrister Usman Ali yana mata irin tambayoyin nn ba! kuma ae gaskiya ta fad'a bazai yiyu ace kaga mutun sau d'aya tak kuma da jimawa snn kace in ka ganshi zaka sake gane shi,sam wnn ba gaskiya bane ya mai girma mai shari'a,
kuma ina son wnn kotu mai alfarma ta d'aga wnn shari'ar har izuwa wani lokaci dmn mu samu damar qara yin bincike dmn gano gaskiyar al'amarin.
Alqali yace"shikenan Barrister Usman ko akwai abinda zaka ce?
Eh ya mai shari'a ina son wnn kotu mai alfarma ta taimaka ta bani belin bintu.
Kotu ta baka belin bintu amma da sharad'in en sanda zasu kasance tare da ita har zuwa lokacin da za'a sake wani zama wato nn da bayan mako biyu masu zuwa.
Cikin girmamawa ya d'an russunadda kanshi yace"Nagode ya mai shari'a"

Ana fitowa bintu tazo jikin umma ta rungume ta sosai sae kuka take tana fad'in"Dan Allah umma kuyi haquri ku daina fushi dani ku yafe min wlh yafiyar ku kad'ai zata sa nayi nasara akan komai umma.
Umma da gabad'aya tausayin er tata take ji tace"ba komai bintu na yafe miki kije ki roqi Abbanki shima"
Bintu ta kalli Abban nata dake tsaye yana kallon su tayi tsaye sae kallon sa take cike da fargabar yanda zata je ta same shi ko ya zai kar6e ta.
Abban nata dake kallonta da kanshi ya mata alamar tazo,ba musu taje gareshi ta tafi a hnkli zuwa jikinsa tana bashi haquri.
Komai baice ba sae shafa gadon bayanta da yayi a hnkli alamar ba komai ya wuce sbd yana cikin yanayin da baya son cewa komai dan gabad'aya al'amuran su zeenah sun matuqar d'aure masa kai,dan kwata kwata baisan da sa hannun su ne abubuwan nn keta faruwa ba sae karon nn umma ta gaya masa komai.
Kana ya d'agota daga kan jikinsa tare da sa tafin hannun sa ya share mata hawaye snn yace"ki dage da addu'a kinji mu zamu koma"
Ta gyad'a kanta tare da fad'in"nagode Abba"

Duk abin nn da yake faruwa su zeenah na tsaye suna hango su baqin ciki kmr zae kashe su wa enda suna fitowa beauty ta wuce da sauri ta barsu sbd uzurin gaggawa da ya kamata na zuwa asibiti.
Takaici yasa suka kama hanya dmn barin gurin suna tafe sarah ke fad'in"Nifa zeenah nayi mamakin da kae tsaye alqali ya bada belin bintu bayan laifin da ake tuhumar ta dashi babban laifi ne.
Zeenah tace"Hm! ni bada belin ta sam bai dameni ba Barrister Usman d'in nn ne matsala ta dan na fahimci ya cika qwalailai cewa da saurin gano yanayin da mutum yake ciki.
Sarah tace"ki cire duk wani tsoro da damuwa zeenah, indai Barrister Abubukar Qasim ne ba kad'an ba yasan aikin sa yanda muke son shari'ar nn ta kasance ba makawa haka za'ayi ba tare da an sami matsala ba,yanzu muna fitowa ma ya turo min text a waya yace mu same shi guest house d'inshi da akwai magana.
Zeenah tace"ok da akwai ma wata idea da ta fad'o min akai yanzun nn matso kiji in gaya miki shima in munje sae mu gaya mishi ko idean tawa zata qara taimakawa.
Nan zeenah takai bakinta kunnen Sarah ta gayawa sarah magana,take Sarah ta bata hannu suka tafa had'e da fad'in"wuhuu! ai wlh zeenah wnn idea tayi ta koina ma mun gama lallata shari'ar nn amma muje muji me Barrister zae ce tukun daga can se mu wuce gun beauty.

Bayan su umma sun wuce tare da Abdallah dake driving d'insu.
Abbas yaje ya sami abokin sa inspector yana gode masa kan belin bintu da aka bada.
Yace"ba komai kasan halin kawun nawa (cewa da Alqali)da qyar wlh na samu ya yarda zai bada belin ta dmn ko kad'an baya son wata matsala ta shigo idan yana yin shari'a komai yafi son yayi shi kan gaskiya shiyasa nace ku kwantar da hankalin ku indai har bintu nada gaskiya to ba makawa se gaskiyar ta fita bare barrister Usman yasan aikin sa sosai.
Abbas yace hakane kam nagode sosai mu zamu tafi kaga en sandan da kawun naka ya had'a mu dasu sae jiran mu suke.
Er dariya inspector yayi yace"kuyi haquri fa da tsarin kawun nawa"
Yace"ah haba ba komai ae tamkar escort ne a gare mu dan koda wa en can en iskan yaran nada niyyar wata mugunta wa bintu an toshe musu hanya ba suda yanda zasuyi sae da nace Allah ya tsare kowa da sharrin su yasa a kammala shari'ar nn lafiya.
Inspector yace"Amin"
Nan sukayi sallama inspector ya wuce shima Abbas ya tafi suka wuce gida.

*Asibiti*
Mami ce zaune a gaban waheed kansa da qafar sa ta hagu duk bandage ne wanda kwata kwata bai san inda yake ba ya shiga coma.
Tayi shiru se kallon sa take amma tunanin ta yana kan abubuwan da suka faru kotu kan shaidar da Hajjo ta bayar wacce da fitowar su court ta tambaye Hajjo wae gaskiya ne abinda ta fad'a ko tausayin bintu ne yasa ta fad'i haka?
Hajjo ta rantse mata tace wlh Allah Hajiya kan gaskiya ta sune na gani suna wnn zancen.
Tun daga lokacin mami ta qara shiga tunani har suka zo asibiti ta kasa dainawa.

6angaren bintu kuwa itama zaune take shiru a d'aki ita kad'ai dan en sanda basu wani takurata ba a iya gate sukayi zaman su.
Ga abinci a gabanta ta kasa ci tunanin ta wane hali waheed yake ciki ya farfad'o ko kuwa.
Anti Hafsa ce tazo ta same ta a haka,ta zauna cikin lallami da rarrashi har ta samu taci abincin.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 40&41_*
1 Week later
Har yanzu dai su zeenah basu samu sun kar6e dukiyar handsome daga gun beauty ba sbd sunyi iya nasu wayon sun kasa amma ko yaushe suka zauna sae qara tsara yanda zasu kar6e dukiyar suke kafin a sake wani zama a kotu.
Wannan karon duk tsare tsaren su yana kunnen beauty kasancewar tana la6e a bakin qofa tana jinsu ba tare da sun sani ba wacce sae da ta gama sauraren su kaf snn ta shigo da sakin fuska kmr ba abinda taji.
Haka suma da sakin fuska suka tarbe ta suna mata ya hanya dan isowar ta kenan ta fito daga sokoto.
Bayan ta zauna suke tambayar ta ya mai jiki
tace"to da dama dama za'ace dan har yanzu yana nn kmr wani gawa bai farfad'o ba amma yana samun kulawa sosai dan ko qasar waje albarka likitocin sun san aikin sosai.
Sukace to Allah ya bashi lafiya ya nuna mana kun angwance.
Er dariya tayi tare da fad'in amin.
A ranta kuma mamakin su take yanzun nn ta gama jin mugun nufin su akanta na yanda zasu tura mata mugaye su kar6e dukiyar handsome daga gare ta koma ta kashe ta ne su kashe ta a dai samu dukiyar ta fito amma se gashi a zahiri suna nuna mata tamkar ba wani abu a ransu lallai zata nuna musu ko gaba da gabanta.
Zeenah tace"beauty ya mgnr mu ta zuwa gurin wnn hatsabibin bokan da kika ce kinji labarin aikinsa tamkar yanka wuqa yau zamu tafi qauyen ko sae gobe?
Beauty wacce dama abinda ya kawota knn suje wnn qauyen,
tayi shiru kmr baza tayi magana ba can ta numfasa tare da fad'in"zeenah nayi tunani da mun bar zancen zuwa gurin bokan nn dmn bana jin yanda mutanen nn suke tsaye da kansu boka zai iya convincing Alqali ya yanke hukunci dai dai yanda muke so ba tare da an tsaya wata doguwar shar'ia ba.
Zeenah tace"amma beauty kince fa bokan nn ya shahara gagarumin matsafi ne ba wani aiki da yake masa wahala kawai ya mana convincing kowa mana ta yanda idan an yankewa bintu hukunci ba wanda zai iya musawa bare suce zasu d'aga qarar izuwa wata kotu snn asa kowa ya fita harakarta su manta ta gabad'aya a rayuwar su kmr ma ba a ta6a yinta a duniya

Please Login or Register in order to submit comment