Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba tofa za'a mata d'aurin rai da rai ta qarasa rayuwar ta can gidan kaso ba ita ba sauran wani farin ciki har abada.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 36_*
Sarah tace"lallai hkn da kikayi yayi dai dai dmn nima burina knn,baqin cikina d'aya yanzu shine rashin auren nn namu da duk wanda ya fito da niyyar auren mu sae ana batun saka date suce sun fasa sbd sun ji labarin mun zubar da mutuncin mu tun a waje,na rasa a ina suke ji bayan duk irin kamilancin da muke nuna musu muna 6oye musu ainihin halin mu dan mu samu muga anyi auren.
Zeenah tace"Matsalar itace binciken da akeyi kafin aure kuma mazan da muke haraka dasu har su d'in basa yarda su aure mu in ma ka musu mgnr aure ya ishi su gaya maka baqar magana daga rnr kuma ka daina ganin su knn.
Sarah tace"shiyasa tun farko zeenah banso mun fara harakan nn ba sbd gudun irin haka gashi muna samun mazajen aure amma da bincike ya nuna halin mu shikenan su fasa sbd duk mutumin kirki ba zae so ya auri irin mu ba kowa fatan sa ya samarwa 'ya'yansa uwa ta gari mai mutunci da bata riga ta zubar da mutuncin ta a waje ba.
Shiru zeenah tayi dmn bata da abinda zata ce ma sarah sbd gaskiya ta fad'a, a yanda suke samun mane man nn yanzu da halin su na kirki ne basu riga sun zubar da mutuncin su a waje ba da yanzu sunyi aure.
Can ta kalli sarah tace"kinga dnt mind ae ko dan kud'in mu za'a aure mu ko kin mata zamuyi wa beauty sakiyar da ba ruwa dukiyar handsome duk ta dawo hannu mu sae abinda muka ga dama muka samma ta.
Sarah tayi dariya tare da bata hannu suka tafa snn tace"Hakane fa na manta har naji d'an sauqi a raina kuma shawara ita ce dukiyar na shigowa hannun mu gidan hayar nn barin sa zamuyi dmn na fahimci yana daga cikin qarin matsalar rashin auren nn namu a matsayin mu na en mata mun kama gidan haya byn kuma da iyayen mu a gari,kinga se mu sayi kantamemen gida tsadadde mu koma can muda iyayen mu.
Zeenah tace"ae kam dama ni yawon dubai ma zan soma yi dan garin nn bai ishen zama ba akin asibitin ma fatali zanyi dashi in shiga harakar sae da gwalagwalai da hajar mata.
Dariya sarah tayi tare da sake bata hannu suka tafa tace"kina wuta ina binki da fetur,ma jame duk inda kikayi can nayi.

*Sokoto*
Anti Hafsa ce ta shigo d'akin su ilham gun bintu wacce ke zaune kan bed ta had'e kai da guiwa sae tunanin mafitar rayuwar ta take.
Sallamar da anti Hafsa tayi ne yasa ta d'ago kanta a hankli tare da amsa mata sallamar.
Jiki sanyaye anti Hafsa ta qarasa kusa da ita ta zauna,fuskarta d'auke da damuwa tace"bintu yaya Abbas ne ya bugo waya wae gobe zae zo yace ki tabbatar kin tanadar masa ainihin takadar da waheed ya baki kafin yazo"
Shine na kira Abban ilham nace ya akayi shida yace mu bar komai a hannun shi amma still yaya Abbas na kan bakar shi,yace wae muyi haquri ya kasa shawo kansa ne,ya kike ganin zamuyi yanzu?
Bintu dake kallonta muryar ta a sanyaye tace"kar ki damu anti ko yazo ba matsala ni na amince zan auri Jabir "
Da mamaki Anti Hafsa tace"kin amince fa kika ce Bintu?
Eh Anti na haqura zan rungumi qaddarar da ta sameni dmn na riga na jawa kaina ba yanda zanyi.
Anti Hafsa dake kallonta tace"No bintu ni bazan so hakan ba kome zai faru sae dai ya faru amma se na snr da umma halin da ake ciki kafin yaya Abbas yazo,shin wae ma tukuna kin manta da auren waheed akanki ne da kike wnn zancen,ko gaskiyar yaya Abbas ne waheed ya sake ki kike 6oyewa?
Ko d'aya Anti bae sake ni ba amma da kaina zan nemi ya sake ni dmn nasan ko na koma bazan sake yin daraja irin ta farko ba, gwanda kawai in barshi da Husnan shi ni kuma in auri jabir.
Jiki sanyaye anti Hafsa ta dafa kafad'ar bintu tare da fad'in"ki daina zancen nn Bintu dmn bana jin waheed zai iya sakin ki tunda har ya kasa sakin ki a lokacin da mamin sa ta umarce shi se basaja da ya mata"
Anti nasan yanda zanyi ya sakeni cikin sauqi shine zan bar mami tasan bai sake ni ba,na tabbatar in taji hakan koshi waye dole ya sakeni koda baya so"
Anti Hafsa tace"kenan kin yarda taci gaba da kallon mu a matsayin mayaudara?
Bintu dake kallonta qwallah cike tap a idonta tace"Aa bayan na auri jabir zata san gaskiyar komai,wnn alqawari ne na d'auka bazan bar taci gaba da kallon mu a matsayin mayaudara ba dole zan dawo da darajar iyayen mu a idonta ko zan samu su daina fushi dani"
Anti Hafsa ta numfasa a hnkli tare da fad'in"amma bintu kina son waheed fa meyasa zakiyiwa kanki haka?
A nn qwallar da suka cika mata ido suka silalo a hankali ta share hawayen tare da fad'in"ba yanda zanyi ne Anti,amma haqiqa rayuwata baza ta6a dad'i ba sae tare dashi dmn ina matuqar sonshi bana jin kuma zan iya daina son shi har abada,amma ya zama dole in haqura dashi.
Tana kaiwa nn ta saki kuka a hnkli, Anti Hafsa da idanun ta suka ciko da qwallah ta jawo bintu zuwa jikinta tare da sa hannu ta share mata hawaye snn tace"yi haquri daina kuka komai mai wucewa ne kinji tashi muje muci abinci jabir yana can yana jiran mu.
Nan taja hannun Bintu suka fito wacce ta kasa cin abincin sae yawo kawai take da spoon tana motsa abincin a hankli cike da tunanin yanda zatayi rayuwa da wani d'a namiji ba waheed ba,abinda ko a mafarki bata ta6a kawo shi ba se gashi yanzu yana shirin faruwa da ita.
Kukane yazo mata ta tashi da sauri ta bar gurin.
Jabir da ya bita da ido ya maida duban sa gun anti Hafsa wacce tayi shiru ta daina cin abinci.
yace"Anti me kuma yake faruwa?
Tace"magana d'aya ce dai da ka sani jabir"
Yace"to Anti da kinje kin rarrashe ta ai ko?
A hankli ta girgiza kanta tace"ka barta kawai jabir ta cancanci tayi kukan ne shiyasa"
Shiru jabir yayi bai sake cewa komai ba har suka kammala cin abinci wanda dashi har Anti Hafsa ba wani abincin kirki ne suka ci ba sunan sunci ne kawai.
Da gamawar su ne jabir ya tashi ya tafi cike da tunani a ransa,Anti Hafsa kuwa fresh milk ta d'ibarwa bintu dan ba kad'an ba tasan tana jin yunwa damuwa ce kawai ta hana ta cin abinci,taje ta sameta a nn d'akin su ilham cikin rarrashi da bata magana ta samu har tasha fresh milk d'in.

Da dare bayan sllr isha sae ga Anti nafee tazo gidan, ilham dasu daddy suka tarbe ta sae oyoyo suke mata.
Hayaniyar su ne yasa Anti Hafsa ta fito wacce tana ganin Anti Nafee fuskarta d'auke da murmushi tace"Au Nafee kece da daren nn ina kika bar su mimi?
Tace"suna can tare da Abban su sunje shopping a fodio mall daga can kuma su harba A.g.g wae duk dan inji haushi ba aje dani ba.
Ta qarashe mgnr ne d'auke da alamar fushi a fuskarta,
a nn Anti Hafsa ta nemi su ilham da su tafi d'aki snn taja hannun nafee suka zauna kan doguwar kujera tana kallonta tace"me ya had'a ku ne dan san haka kawai sadiq bazai fita daga shi se yara bake ba?
Tace"Anti fad'a mukayi shine yake fushi dani yana jiran in bashi haquri ni kuma naqi sae harakar gabana da nake shine yamin haka dan yasan bazan ji dad'i ba.
Anti Hafsa tace"hm lallai kinfi qarfin ki bashi haquri ko,to yanzu da kika zo me kike so in miki?
To Anti ba kya ganin duk ya kwashe su sun fita har isma'il ma da yake shan mamma ya zan zauna ni kad'ai a gida to"
Anti Hafsa tace"naji amma yanzun nn komawa zakiyi kafin ya dawo idan kuma ya dawo ki same shi har d'aki ki bashi haquri,keda ma rashin bada haquri ba halinki bane yaushe kika fara to?
Anti to dan na masa laifi shine zae sameni a gaban su mimi yayi ta min fad'a ni kuma shine a nn gaban su na gaya masa magana mai zafi na tafi na barshi dan inna tsaya na tabbatar komai zai iya faruwa gashi kuma bai kamata ace munayin fad'a a gaban su mimi ba.
Anti Hafsa tace"duk da haka dai ki same shi ki bashi haquri ki kuma nemi yafiyar fitowar da kikayi bada izinin sa ba.
Ta gyad'a kanta snn tace"to anti bari in tashi in koma amma bintu fa ko yau night duty take da?
Aa jeki tana d'aki.
Bayan taje ta dawo Anti Hafsa ta raka ta zata shiga mota tace"ni kuwa Anti kullum damuwar bintu sae qaruwa take dan Allah yaya Abbas yayi haquri mana haka ya barta ta koma d'akin ta ya janye zancen auren nn nata da jabir bana so wlh nafi so ta koma gidan waheed.
A hnkli Anti Hafsa ta numfasa snn tace"ea yanzu ita bintun da kanta tace ta amince zata auri jabir"
Meyasa Anti kuma ta yaya ita da tace da auren waheed a kanta ko qarya take yiwa yaya Abbas ba ainihin takardar da waheed ya bata ta bashi ba kmr yanda shi yaya Abbas yace.
A nn Anti Hafsa dake kallonta tayi mata bayanin duk yanda sukayi da bintu a d'azun.
Nafee tayi shiru can tace"To ke anti kina ganin ba tsoron masifar yaya Abbas ne yasa ta fad'i haka ba kuwa?
Bana jin haka nafee amma dai zan zauna muyi magana da ita gobe da safe kafin su yaya Abbas su zo dan gabad'aya ta kashe min jiki da zancen ta.
Nafee tace"ae ba ke kad'ai ba anti har ni, haka itama ba makawa zancen yana damunta dan duk naga ta qara shiga damuwa Allah dai ya kawo qarshen wnn abun.
Anti Hafsa tace"Amin"
Kana sukayi sallama,Nafee ta shiga mota ta wuce ita kuma ta koma daga ciki.

Qarfe biyun dare Husna na tsakar sllr nafila kwatsam taga qarti zagaye da ita sun shigo d'akin,ta sallame sllr a rud'e tana kallon su d'aya bayan d'aya kafin ta iya cewa komai babban su ya d'aura mata bindiga aka, muryar ta na rawa cikin tsananin tsoro tace"Aa dan Allah ku gaya min duk abinda kuke so zan baku wlh"
Cikin muryar sa kakkausa mai kaurin gaske yace"yarinya rayuwar ki muke so kuma ita zamu kar6a"
Tace"Haba dan Allah me na muku dan Allah kuyi haquri koma mene ne wlh na tuba bazan sake ba na roqe ku,ku tausaya min kodan cikin da ke jikina dan Allah!?
Bai kulata ba sae qara danna mata bindigar yayi aka zae harbe ta ba shiri ta buga wani irin ihu cikin tsananin firgici har waheed dake kwance a d'akin sa yana bacci se da ihun ya tashe sa,nn ya fito da hanzarin sa wanda duk a tunanin sa haifuwa ce tazo mata amma koda yazo d'akin se yaga sa6anin haka a nn hankalin sa yayi mummunan tashi ganin qartin gaske kusan su biyar zagaye da Husna ogan na shirin harbinta aka wanda tsirif ya rage ya sakar mata bullet,ba shiri ya tafi aguje tare da sa qafa ya shure masa hannu harbin ya sami d'aya daga cikinsu ya fad'i kae tsaye a gurin dafe da inda harbin ya saukar masa.
Waheed bae damu ba sae hannun husna ya kama yana son fitar da ita daga d'akin sauran suka yo kansu waheed ya shiga kare Husna dan ya fahimci ita suke son harbi,Husna kuwa se qara la6ewa bayan sa take cikin kuka mai cike da tausayi tana roqon suyi haquri amma ina sae saukar bullet kawai taji a jikinta ogan su ya harbeta, kae tsaye ta saki qara had'e da fad'uwa gurin,a rud'e waheed yayi kanta se jijjigata yake yana kiran sunan ta amma sam ta daina motsi kwata kwata,nn ya tashi cikin kukan kura yayi kan wanda ya harbeta ya had'a sa da bango tare da shaqe masa wuya iya qarfin sa,take idanun sa suka firfito yana neman agaji ya kasa qwatar kansa haka sauran qartin ma duk qarfin su sun kasa qwatar shi nn wani ya sami makami se dukan waheed yake aka ta koina amma waheed yaqi sakin sa ganin da gaske waheed so yake ya kashe musu oga suka d'auki bindiga sae harbinsa suke har sae da waheed ya sake shi suka fad'i tare dashi har ogan ba mai motsi a cikin su.

Firgigit!Bintu ta tashi daga mummunan mafarkin da take hankalin ta a tashe se fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un! take,ta miqe zaune tare da kunna bedside lamp,qarfe biyun dare da mintina ta gani a agogon bangon d'akin,a hankli ta dafe kanta yayinda take jin zuciyar ta kmr zata faso qirjinta ta fito sbd dukan uku uku da take.
Tofi tayi gefen hagunta sau uku snn ta nemi Allah tsari daga shaid'an da abinda ta gani a cikin mafarkin ta sau uku kmr yanda addini ya tanadar.
Sam bata jin zata iya komawa ta kwanta dmn ba kad'an ba mafarkin ya matuqar razana ta,a nn ta tashi ta shiga bathroom ta d'auro arwala tazo sae sllh take tana roqon Allah ya sauqaqa abinda ta gani a cikin mafarkin ta yasa kar ya zamo gaskiya.
Haka ta kasance har asuba bata koma bacci ba.
K'arfe bakwai Anti Hafsa na kitchen ta soma jin ana qwanqwasa qofa ta ajiye abinda take tazo ta bud'e qofa, police ta gani su biyu maza mace d'aya, fuskarta d'auke da mamaki tace"police......
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 37_*
A gidan nn me ya kawo ku to?
D'aya daga cikin su yace"tsohuwar matar waheed wato bintu da aka shaida mana cewa qanwarki ce ita muka zo zamu tafi da ita a bisa mummunan laifin da ta aikata....what! wane laifi ne ta aikata!?
Kallon ta yayi kafin yace komai sae ga bintu tazo muryar ta a sanyaye tana fad'in"Anti lafiya me yake faruwa?
Fuskarta d'auke da rashin fahimta tace"nima bintu bansan me yake faruwa ba wae ke suka zo nema kinyi laifi"
D'auke da mamaki Bintu ta kalle su tace"ni kuma me nayi?
Kallon kin ma raina mu ya mata snn yace"idan munje can kyaji"
kana ya umarci er sandar da take tare dasu kan ta sa mata ankwa su fice.
Anti Hafsa tayi saurin tarewa tana fad'in"Aa dan Allah kuyi haquri kar ku tafi da ita ku gaya mana tukun laifin me akace muku ta aikata"
Nan kai tsaye d'an sandan bai musa mata ba ya mata bayanin laifin da ake tuhumar bintu dashi.
A rud'e anti Hafsa tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!mun shiga uku wlh sharri ake mata ba ita ta aikata ba.
Yayinda Bintu fad'ar yanayin da ta shiga a lokacin abu ne da bazai yiyu ba ta zama kmr wata statue komai nata ya tsaya cak baya motsi sae hawaye dake fita a idonta, shikenan mafarkin ta ya zama gaskiya,gashi kuma anzo ana tuhumar ta wae ita ta aikata,innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahuma ajirni fi musibati wa akhlifni khaira minha.
Ta fad'i hakane a ranta amma a zahiri tana nn still kmr statue wacce tana ji tana gani aka sa mata ankwa suka tafi da ita,Anti Hafsa ta bisu har gate sae kuka take tana roqon suyi haquri kar su tafi da ita wlh sharri ne ba ita ta aikata ba amma ina basu saurare ta ba suka wuce da ita.
Hankali tashe Anti Hafsa ta dawo cikin gida da niyyar taje ta kira Abban ilham a waya ta snr dashi abinda ake ciki sae ga jabir yazo yana tambayar anti lafiya me yake faruwa?
Cikin kuka ta masa bayanin abinda ya faru.
Dafe kansa yayi tare da fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un!kana ya tafi da sauri ya d'auki mashin d'in sa ya fita a cewar zai bisu.
Sosai Anti Hafsa taso su tafi tare amma tuna cewa su ilham na nn basu wuce school ba kuma ba kowa wanda zae kula dasu yasa ta haqura har se ta kai su school snn daga can ta same shi.
Bayan ta same shi a can ba irin magiyar da basuyi wa en sanda ba kan sharri akeyiwa bintu bata aikata laifin da ake tuhumar ta dashi ba,suka nuna sam maganar su ba hujja bace tunda en fashi sun furta da bakin su cewa bintu ce ta tura su dan haka su tafi su basu guri idan har da wanda suke zargin ya mata sharrin suna iya su sashi qara.
Ba yanda suka iya suka baro bintu sae kuka take.
Hakama ma anti Hafsa kuka take har suka zo gida jabir sae rarrashin ta yake yana bata magana wanda shima qarfin haline kawai yake.
Anti Hafsa ta kira Abban ilham ta gaya mishi halinda ake ciki shida yaya Abbas wa enda dukkan su ba qaramin tashin hankali suka shiga da jin zancen ba yayinda yaya Abbas yace da Anti Hafsa kar ta snr da su umma halin da ake ciki tukun ta bari in sun zo zai san abinyi.

6angaren mami kuwa abun ba acewa komai dan bansan ta yanda zan misalta muku tashin hankalin da take ciki ba dmn waheed na can rai ga hannun Allah likitoci bila adadin a kanshi suna bashi taimakon gaggawa.
Husna kuwa koda aka kawo su asibiti abinda ke cikinta kawai aka iya ceto ransa amma ita Allah ya kar6i ranta wacce hajiyar ta tayi kuka sosai da baqin ciki marar misaltuwa yayinda ta qudiri lallai baza a bar bintu ba sae an yanke mata hukunci dai dai da abinda ta aikata.

*Kebbi*
6angaren su zeenah kuwa wa enda musamman jiya a garin sokoto suka kwana sosai sukayi murna da farin ciki amma beauty kam se kuka take sbd halin da taji waheed na ciki wacce su zeenah suka sata a gaba sae rarrashin ta suke kan tayi haquri ta daina kuka.
Tace"haba dan Allah ku barni kawai inyi kuka wlh en fashin nn sun 6ata min rai ashe kwata kwata ma basu san aikin su ba,suda aka ce kar su ta6i lafiyar shi amma shine duk suka hahharbe min shi,shegu en iska naga wanda ze fidda su to.
Zeenah tace"calm down beauty harbin da suka masa duk a qafa ne fa hakan ya nuna da akwai dalili bada niyar kisa suka harbe shi ba.
Hm! zeenah a gaban idona fa asibiti aka wuce dashi duk sunbi sun doddoke shi kanshi se fitar da jini yake taya zaki ce min bada niyyar kisa suka doke sa ba!
Ki fahimce ni beauty ga dukkan alama kokawa ya shiga yi dasu shiyasa suka kai ga ta6a lafiyar sa tunda gashi ogan nasu ya mutu d'ayan kuma yana asibiti.
Duk da haka zeenah wlh duk waheed ya mutu sae na tura har cell an kashe min su da ma wanda ke gadon asibiti dukkan su bazan qyale su ba sae na nuna musu kuskuren su wlh.
Zeenah tace"Aa beauty ki kwantar da hankalin ki da yardar Allah waheed bazai mutu ba kuma ko a birnin sin ne na tabbatar mami zata fitar dashi na ganin cewa ya rayu bai nakasa ba.
Snn ina baki shawara ki janye zancen cewa wae baza ki fidda su ba in kika yi haka sun ga damar su fad'i gaskiyar komai damu harke mu shiga uku, dan haka haquri zakiyi mu cika musu alqawarin da muka musu tunda suma sun cika mana alqawarin mu sa6ani ne kawai da aka samu wanda suma nasan ba haka suka so al'amarin ya kasance ba.
A sanyaye tace"Shikenan naji amma ya zama dole in sake komawa sokoto in ci gaba da zuwa asibiti a matsayin aikina ke kawo ni dmn in riqa sanin halinda waheed yake ciki.
Suka ce shikenan ba matsala.
A nn kai tsaye ta harhad'a kayanta ta shirya ta tafi cikin motar ta sabuwa fil da ta siya a en kwanakin nn.
Bayan ta wuce ne Sarah ke cewa kina ganin dan ta fita harakar su bata fidda su ba za'a iya samun matsala har muma mu shigo ciki kmr yanda naji kince?
Zeenah tace"hm na fad'a ne kawai dmn in nuna mata matsalar ta tamu ce amma mu meye namu a ciki muda rakiyar ta kawae mukayi gurin su sai en shawarwarin da muka basu ta yanda aikin zai yi yanda ake so ba tare da an sami wata matsala ba.
Sarah tace"Gud shiyasa nake sonki yanzu game d'in mu da bintu tazo qarshe we have won,beauty kawai ta rage mana danni na matsu inga dukiyar handsome gabad'aya ta dawo hannun mu.
Zeenah tace"itama kar ki damu nata na zuwa very soon!
A nn sukayi dariya tare da ba juna hannu suka tafa.
*Sokoto*
Su Abbas da Abban ilham suna sauka garin ko gida basu je ba kae tsaye suka wuce police station d'in da aka je da bintu kasancewar Anti Hafsa ta snr dasu.
Koda suka je Abbas yaga ashe d'an sandan da case d'in yake hannu sa abokin sa ne.
Hakan ba qaramin dad'i yayi wa Abbas ba yayinda abokin nasa ko kad'an baiji dad'in da hakan ta faru ga wani nashi da ya sani ba,gashi ba yanda zaiyi ya basu belin bintu kmr yanda suka buqata acewar zasu sa qarar wa enda suke zargi in yaso suci gaba da case d'in can kotu har a biwa bintu haqqinta.
Sosai ya kwantar da kai ta hanyar fahimtar dasu cewa wnn babban case ne da bazai iya bada belin bintu ba amma dai suje su sa qarar wa enda suke zargi tukun.
Duk da basu ji dad'i ba suka ce masa ba komai sun gode amma suna son a fito da bintu su ganta.
Nan yasa aka fito da bintu kmr yanda suka buqata wacce tazo sae kuka take.
Cike da tausayi Abbas ya soma rarrashin ta yana bata magana shida Abban ilham kan ta kwantar da hankalin ta zasu sa su zeenah qara abi mata haqqinta dan sun san ba makawa wnn sharrin su ne.
A nn ta d'an sassauta kukan da take amma da za'a koma da ita sosai ta riqe hannun yaya Abbas cikin kuka bata son komawa wanda cikin rarrashi ya samu da qyar ya sa6ule hannun sa aka koma da ita.
[12/6, 6:29 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*Aminci writers association*





*_page 38_*
Cikin rashin kuzari suka tafi gida,Abban ilham ne ya fara shiga cikin gidan wanda kai tsaye d'akin Anti Hafsa ya nufa d'auke da sallama a bakin shi.
Anti Hafsa dake zaune gefen gado tallabe da goshinta irin na alamar damuwa,ta d'ago kanta a hnkli tare da amsa masa sallama kana ta taso tazo gunshi jiki sanyaye ta mishi sannu da zuwa.
Ya kama hannunta suka je kan bed suka zauna sae kallon sa take dan ta fahimci da akwai damuwa sosai a tattare dashi kafin tace komai yace"kiyi haquri Hafsa da saukar mu garin nn kai tsaye muka wuce police station amma bamu samu yanda muke so ba.
Anti Hafsa dake kallon shi tace"dama nasan irin wnn

Please Login or Register in order to submit comment