Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dawo shida Anti Nafee,Anti Hafsa taja su suka tafi d'akin su ilham gun bintu kmr yanda Abdallah ya buqata sbd birnin kebbi zae koma.
Zaune suka same ta kan bed ta had'e kae da guiwa sallamar su ne yasa ta d'ago kanta a hankli fuskar ta fayau kmr wata mara lafiya ga idanuwan ta da suka kod'e kan kuka,waya riqe a hannunta ta kira umma yafi a qirga amma taqi d'agawa.
Abdallah ya zauna kusa da ita yana kallonta cikin muryar rarrashi yace"bintu ni zan koma birnin kebbi abu d'aya nake so dake shine ki rage damuwar nn da yawan kukan nn kar kije ki jama kanki wani ciwon abinda ya kamace ki shine ki roqi Allah yafiyar abinda kika aikata ki kuma riqa yin addu'a dmn itace waraka akan komai.
Bintu ta share qwallar da suka zubo mata snn tace"hakane yaya zanyi duk abinda kace amma ni nasan rayuwata ta lalace banida wani sauran amfani a duniyar nn na rasa yaya waheed Abba ya koreni umma tana fushi dani yarda da mutuncin da ke tsakanin mu da mami sun watse duk a sanadin abinda na aikata,nn ta fashe da kuka tace"meyasa kuma bazaku fita harakata ba tunda ni wawuya ce bansan abinda nakeyi ba.
Abdallah ya girgiza kansa kmr zae yi kuka yace"ki daina fad'ar haka bintu kuma ki daina kukan nn ko da gaske so kike muma muyi fushi dake mu fita harakar ki gabad'aya"
Da sauri ta girgiza kanta yace"to daina kuka share hawayen nn bana son ganin su"
Ba musu tasa tafin hannu ta share hawayen fuskarta.
Ya tashi riqe da hannun ta suka fito harabar gidan su dukan su sbd tafiyar knn,driver ma sae jiran sa yake su tafi a motar Anti Nafee da tasa akai shi.
Kafin ya shiga mota ya kalli bintu wacce still yana riqe da hannun ta yace"ki kwantar da hankalin ki qanwata inshaa Allah zan shawo kan umma har da Abba kinji"
Gyad'a masa kae tayi tare da masa godiya snn ya shiga mota tare da saurin share hawayen da suka zubo masa kana driver ya tashi mota suka wuce.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*







*_page 27_*
Snn su kuma suka koma daga ciki inda kae tsaye bintu ta wuce d'akin su ilham, Anti Hafsa da Anti nafee kuwa a nn falo suka zauna.
Anti hafsa ta tashi da niyyar kawo ma Anti nafee ruwa da lemu.
Anti nafee tace"uhm Hafsa zauna kawai ba sae kin kawo min komai ba ni abunda ke damuna kad'ai ya ishe ni wae ace duk shirin nn da su zeenah keyi da bintu tun suna yara zasu iya cutar ta abin ya bani mamaki.
Anti Hafsa tace"hmm kema kina son ki zama irin bintu knn, ae tunda iyayen su basa qaunar mu komai zasu iya yi akan mu"
Haba hafsa fisabilillah ki duba fa tun suna yara tare suka taso komai tare sukeyi cin abinci wanki wanke wanke sharar gida makarantar boko da ta islamiyya duk tare suke zuwa haka idan an aiki wani a cikin su tare suke zuwa snn duk fad'an da bintu take janyowa sune masu shiga mata su kama yaran anguwa su musu dukan tsiya koda kuwa bintu ce mae laifi to ta yaya zanyi tunanin zasu iya cutar da bintu har su bata gurguwar shawara kuma fa tun suna yara suka taso da rashin son abinda iyayen su keyi na rashin kyautawa waenda na d'auka har ransu hakane ba funafurci ba sae dai ko idan iyayen nasu ne suka canza musu ra'ayi daga baya.
Anti Hafsa tace"hm nifa tun suna yara ban yarda dagaske suke son bintu ba duk da basu ta6a nuna mata wani abunda zaisa inga haka ba kawae dai halin iyayen su ne yasa sam ban yarda dasu ba shiyasa na ga wautar bintu da ta biyewa shawarar su na kuma yi mamakin duk ina wayonta ya tafi wacce kan tsananin wayonta ne yasa tun tana er shekara biyu da en watanni aka saka ta school.
Nafee tace"Hafsa ni ban d'auka rashin wayo ne yasa bintu ta aikata haka ba nafi yarda cewa dan tana buqatar zubar da cikin ne ido rufe kuma ko ba haka ba su zeenah sun girme mata wayon su ba d'aya ba snn su kansu haka suka taso da shegen wayo tamkar wasu tom and jerry.
Anti Hafsa tace"To yanzu dae koma mene sun riga sun kaita sun baro sun sakata a matsaloli sun rabata da gidan mijinta su kuma suna batun yin auren su.
Nafee tace"Allah sarki hln saki nawa ne waheed ya mata?
Bata gaya min ba kawae dai tace ya bata takarda.
Anti nafee tace"Allah yasa ba saki uku bane"
Hm nafee ko ba saki uku bane ya za'ayi tunda mami bata ko saurarrar mutane mun fita a ranta gabad'aya ba muda wani sauran mutunci a gurin ta wacce a cikin satin nn ma take shirin kawo ma waheed sabuwar amarya,bintu kuwa ko wani auren tayi ba lalle bane ta iya haifuwa.
Shiru Anti Nafee tayi sae can ta girgiza kanta tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un! haqiqa bintu ta aikata babban kuskure wanda ko kad'an banji dad'in sa ba,ya Allah kasa mufi qarfin zuciyar mu ka kuma kare mu da sharrin maqiya na kusa da na nesa.
Anti Hafsa tace"Amin"
Bari inje inga bintu ina so zanyi magana da ita
Cewar Anti nafee wacce bata jira me anti Hafsa zata ce ba ta tashi ta nufi d'akin da bintu take.
Ta shiga d'akin d'auke da sallama a bakinta ta sami bintu kwance shiru sae yawo take da hannunta a hankali kan bed.
Sae da bintu ta tashi had'e da amsa mata sallama snn Anti nafee taje gab da ita ta zauna ta kama hannunta da kulawa tana kallon ta kafin take cewa"bintu so nake inji saki nawa ne waheed ya miki?
Bintu dake kallon ta ta d'auke idonta tace"kiyi haquri Anti nafee bazan iya gaya miki ba kawae dae ya bani takarda"
Anti nafee tace"ko meyasa ba kya son fad'a?
Kawae dae bana son in fad'a ne.
Anti nafee ta numfasa tace"shike nn bazan matsa miki ba fatana kawai Allah yasa ba saki uku bane dmn burina inga kin koma gidan waheed kuma inshaa Allah zaki koma da yarda Allah komai zae dawo kmr ba'ayi ba.
Anti wnn abu ba abu ne da zae dawo kmr ba'ayi ba na riga na janyowa kaina abinda har mutuwa bazan mantashi ba,Anti ko a mafarki ban ta6a kawo yaya waheed zae yi rayuwa da wata mace bayan ni ba amma gashi a dalilin kuskuren da na aikata zae yi auren sa ya mantani.
Har abada kinsan waheed bazai ta6a iya manta ki ba bintu,dan haka kima daina fad'ar haka.
Anti ko yaya waheed bai manta ni ba zae share dani a rayuwar sa ko dan abinda na masa wanda bae ta6a tsammani ba da har tasa ya furta tsana a gareni.
Bintu addu'a tana maganin komai dan haka kici gaba da yin addu'a kawae da yarda Allah komai zae dawo kmr ba'ayi ba.
Shiru kawae bintu tayi amma ta san ta riga ta cuci rayuwar ta ta janyo ma kanta matsaloli musamman matsalar mahaifar nn da bata san ko nn gaba zata iya haifuwa ba ga waheed auren sa zai yi ya soma hayayyafa abinshi ae dole ya manta ta tunda waheed mutum ne mae matuqar son haifuwa.
Anti nafee da ke kallon ta tace"nasan tunanin ki d'aya shine auren nn da waheed zae yi ,ki tunafa baya son auren nn a tilas zai yi shi.
Anti nasan baya son auren nn amma yaya waheed mutum ne mae son abinda mahaifiyar sa ke so wanda ko kad'an baya son ganin 6acin ranta nasan da sannu soyayyar da yake min zata koma gun wacce zai aura yayinda ta fara haifa masa 'ya'ya soyayya ta zata zamo masa tarihi.
Anti nafee tace"ki daina fad'ar haka bana so a ma daina zancen nn yanzu abinda nake so inji shine tun zuwanki gidan nn su zeenah sun kiraki?
Sun kira ni yafi a qirga amma ban d'aga ba dmn cike nake da mamakin su.
Ae da kin d'aga kiran ko mutuncin en iska kici dmn su san abinda suke shiryawa a 6oye ya bayyana.
Wato anti so nake sae sun zo tukun da akwai abinda na shirya musu.
Au cewa sukayi zasu zo knn?
Eh da suka ga sunyi ta kirana ban d'aga ba sae suka turo min text kan nayi haquri sun san halinda nake ciki bazan iya d'aga waya ba amma kar in damu zasu zo da akwai wata shawarar da suke son zasu bani.
Hm lallai yaran nn so suke suzo su sake guma miki wani knn Allah ya fisu baza su ta6a nasara akan abinda suke so ba en iska.
Shiru kawae bintu tayi bata ce komai ba amma ganin take wace nasara ce kuma basuyi a kanta ba sae dai fatar Allah ya tsare gaba.

Washe gari ne su zeenah suka zo suka sa bintu a d'aki wae su shawara suke bata idan ta amince tazo su koma kebbi can gidan da suka kama haya suci gaba da zama tare zasu smr mata aiki a nn asibitin da suke aiki su riqa zuwa tare tunda Abba dae ya cije kan lallai bazata dawo gida ba.
Bintu dae sae jin su kawai take wato dae sun maida ta wawuya sha ka tafi byn sun saka ta a wnn matsalar so suke su sata a muguwar hanyar da suke ciki in yaso sae ta fand'are tabi duniya.
Tace"hm lallai sae yanzu na qara tabbatar da cewa ba kwa qaunata da gaske,to bari kuji kuda kuka riga kuka bi hanyar lalaci ku zaku ci gaba da lalacewa ni nafi qarfin kuci gaba da sani a matsala wlh Allah bazai barku ba.
Zeenah tace"hm lallai kwanyar ki ta fara ja knn to kema bari kiji har abada munci gaba da saki a matsala knn har sae kin qare rayuwar ki a lalace idan kuma kina ja sae mu gwada muga mu dake waye zae yi nasara.
Bintu tace"uhm ae Allah bazai ta6a bawa azzalumi nasara ba dan haka se kusan irin ramin muguntar da zaku gina dmn kune masu shirin fad'awa tsumbul ba mai fidda ku.
Sarah tace"haba bintu daga shawara shine ke kuma zeenah zaki bar 6acin rae yasa ki biye mata kar fa ki manta bintu mufa en uwanki ne masu qaunar ki da baza mu ta6a iya cutar da ke ba.
Kafin bintu tace komai zeenah tace"sarah lokaci yayi da bintu zata san komu su waye dan haka kima daina wani 6oye mata,bintu kisani tun muna yara mu ba masu qaunar ki bane muna nuna miki qauna a fuskar mu ne kmr yanda iyayen mu suka umar ce mu snn kuma zan gaya miki abinda baki sani ba shine duk cikin da kk samu bayan na farko mune kesa baya zama ta hanyar sa miki magani a ruwan shanki idan kinje hostel gurin mu ko kuma idan munje gidan ki,ke bashi kad'ai ba ma mune muka shirya duk wasu maganganu da komai ta yanda mami in taji kae tsaye zata tsaneki tasa waheed ya sakeki kuma buqatar mu ta biya ko yanzu kasuwa ta watse d'an kola mae rabon ci ya ci.
Bintu ta girgiza kanta cikin jin ciwon abunda suka aikata a gare ta,ta bud'e baki ta fara ci musu mutunci sae abinda ta manta ta zazzage su ta musu tas har iyayen su bata ragawa ba.
Sarah da zeenah ransu yayi matuqar 6aci dan tunda suka zo duniya ba'a ta6a ci musu mutunci irin yanda bintu ta musu d'in nn ba inda cikin zafin nama zeenah ta d'aga hannu zata kaiwa bintu mari bintu ta riqe mata hannu tasa iya qarfinta ta kwad'a mata mari har saida zeenah tayi taga taga zata fad'i,sarah ta kafta wani uban zagi had'e da kukan kura zata ramawa zeenah sae jin saukar marin bintu taji a kuncenta har sae da ta nemi gigicewa kafin suyi wani yunquri dama Anti Hafsa da Anti Nafee a shirye suke suna la6e a bakin qofa suka shigo kowaccen su riqe da makaminta na duka suka taru su duka uku har bintu sae dukan zeenah da sarah suke baji ba gani tamkar Allah ne ya aiko,sae ihu suke suna neman ceto sun kasa qwatar kansu har suka musu zir sae dukan su suke ci gaba dayi ta koina can da qyar da sud'in goshi suka samu suka qwaci kansu suka fita aguje ba tare da sun tsaya d'aukar komai nasu ba sae d'ankwalayyan da suka tsira dasu.

Kuyi haquri da wnn.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 28_*
Kusan kwanaki su zeenah sukayi suna jinyar jikin su yayinda suka qudiri niyyar sae sun rama abinda aka musu fiye da wnn.

6angaren bintu kuwa abinda sukayiwa su zeenah yasa ta d'anji sauqin abinda take ji a ranta amma kullum cikin tunani da nadamar abinda ta aikata take ga kewar waheed da takeji sosai a ranta wanda duk ta tuna aure zaiyi sae ta zubar da qwallah.
Rnr da taji an d'aura auren sa da husna kuwa kuka tayi tmkr wacce akayiwa mutuwa sae anti Hafsa ce ta zauna tayi ta rarrashin ta tana bata magana.

Ranar wata asabar
Anti Hafsa ce zaune ita da mijinta suna fira inda a cikin firar ne yace"ni kuwa Hafsa me zae hana bintu ta ci gaba da zuwa aiki da zaman nn da takeyi kullum cikin damuwa.
Anti Hafsa tace"wlh kuwa kmr ka sani kullum cikin damuwa take musamman da taji waheed yayi auren nn bata da sukuni kwata kwata ko d'aki ma bata cika fitowa ba sae idan na kirata tazo muci abinci snn take fitowa da zarar kuma mun gama sae ta koma.
Mijin anti Hafsa ya numfasa yace"to Allah sauwaqe amma yana da kyau ki bata shawara ta rage damuwar nn a ranta kar ta janyowa kanta wani ciwon.
Anti Hafsa tace"Abban ilham wlh ba yanda bnyi ba kan ta rage damuwar nn a ranta amma ina,inaga sae na had'a ta da Abdallah gobe yace zae shigo daga nn ma sae in gaya masa zancen komawar ta aiki dmn nasan in shi ya mata magana zata koma.
Yace"hakane nama manta ban gaya miki ba gobe jabir zae zo cewa da qanin shi"
Anti Hafsa tace"ae ya kirani ya gaya min sae murna yake anyi posting d'insa a nn zae yi service.
Mijin anti Hafsa yace"hm jabir abinda yake so knn ya kuma samu ae dole yayi murna.
Yana kaiwa nn kawai sukaji sallamar sa ya shigo janye da akwati dukkan su saeda sukayi mamaki mijin Anti Hafsa yace"Aa jabir kaeda kace sae gobe zaka shigo kuma shine yau ka mana bazata"
Jabir yace"kayi haquri yaya wlh ina cikin kewar ganin ku sosai gashi kuma nasan gobe zaka koma abuja shine nace bari inxo yau mu gana musha fira daren yau nawa ne ba na anti ba.
Dariya mijin anti Hafsa yayi itama Anti Hafsa tayi dariya had'e da fad'in bari inje in kawo ma ruwa kasha,kasha hanya.

Bayan ta kawo mishi ruwa da lemu da abinci yaci yasha sukayi zaune sae firar bayan rabuwa suke har yana tambayar bintu Anti Hafsa tace"ae tana ma gidan nn bari in kira ma ita ku gaisa"
Yace"Allah sarki mutuniya ta tana gidan nn knn kira min ita mu gaisa mun jima bamu had'u ba.
Anti Hafsa ta kira mishi bintu wacce suna gama gaisawa ta koma.
Jabir yace"amma dae anti bintu bata da lafiya koh dmn gabad'aya naga yanayin ta ya sauwa kominta a sanyaye kuma bata yi murna irin wacce idan mun had'u muke yi ba.
Nan Anti Hafsa ta gaya masa duk abinda yake faruwa yayi shiru kana ya cire hular kansa cikin jimamin abun yace"bintu tayi babban kuskure Anti wanda ko kad'an banji dad'in sa ba wlh, yanzu ya za'ayi a shawo kan wnn al'amarin.
Yako za'ayi jabir Allah dae ya sauwaqa kawai.
Mijin Anti hafsa yace"amin" had'e da fad'in"tashi muje ka sauke kayanka a BQ"
Jabir da
duk jikin sa yayi sanyi ya miqe janye da akwatin sa suka tafi.

Washe gari guraren 12 na rana Abdallah yazo.
Bintu na d'aki taji shigowar shi ta fito ta same shi zaune kan doguwar kujera ta gaida shi wanda cikin sakin fuska ya amsa mata had'e da kama hannun ta ya zaunar da ita kusa dashi yana kallonta da kulawa yace"bintu ki rage damuwar nn kinji jibi duk yanda kika rame.
Bintu ta kalle sa qwallah tap a idonta kmr zasu zubo tace"ta ya zan iya cire damuwa a raina yaya bayan har yanzu umma da Abba fushi sukeyi dani ba wanda ke d'aukar wayata a cikin su.
Da saurin sa yasa hannu ya share mata hawayen da suka gangaro kan kumatun ta yace"is ok bana son kukan nn kin sani kuma da sannu su umma zasu daina fushi dake kinji"
Gyad'a masa kae tayi tare da qara share hawayen fuskarta
Abdallah yace"da akwai wani abinda kike so?
Tace "um um ba komai"
Anti Hafsa dake jera masa kayan motsa baki tace"ni dae ke son ta koma aiki dan wnn zaman in banda damuwa ba abinda yake qara mata.
Abdallah ya kalli bintu yace"kinji abinda anti Hafsa tace"
Bintu tace"naji zan koma"
Yace"gud sauko muci abinci toh"
Girgiza kanta tayi alamar a'a snn ta tashi ta nufi d'aki sae kallon ta yake har ta shige.
Anti Hafsa tace"shike nn kuma ita da fitowa sae idan na kirata muci abinci ko abincin ma kad'an take ci ta koma.
D'auke da damuwa Abdallah ya girgiza kansa snn yace"jabir fa jiya ya kirani a waya yace min ya shigo koh"
eh amma ya fita kasan yanada frnds sosai a garin nn.
Hakane shifa yaya yusuf ko ya koma Abuja?
Eh tunda sassafe ya koma yama bada saqon wasu hadaddin kaya da ya siyo maka a abuja yace a baka.
Allah sarki shidai baya gajiya nagode sosai Allah ya saka masa da alkairi sae na kirasa in masa godiya.
Tace"Bare gaskiya kayan sunada kyau iri d'aya ya siyo maka kaida jabir dan yaga Hassan da usaini ne ku bakwa son rabuwa idan kun had'u".
Murmushi Abdallah yayi yace" bari ma in kira jabir d'in yazo muga juna dan ganin nake bazan kwana a nn garin ba yau zan koma"
Hm kai ma dae ka fad'a dan kasan jabir kam bazai barka ba kuma nima bazan barka ba sae ka mana ko kwana d'aya ne.
Yace"Anti kisan dis week zan koma school kuma da na koma exam zamu fara,karatu nakeyi ba dare ba rana har bana son in tsallake ko rana d'aya"
Hm kaji iyayen karatu sae kace kanku aka fara.
Abdallah yayi murmushi yace"anti kinsan karatun namu dole sae da haka ba irin wanda zaka sako wasa a ciki bane.
Hkne amma dae kasani nn zaka kwana se gobe da yamma ko zaka koma.
Ba komai anti naji snn ya d'aura da cewa"anti wae ina su ilham ban gansu ba?
Su ilham suna islamiyya duk weekend 8am suke zuwa su dawo 8pm
Yace "gud tsarin ya min inace suna maida hankli kuma suna fahimta?
Tace"wlh sosai kuwa suke maida hankli kuma suna fahimta musamman ilham"
Yace"mashaa Allah,Allah ya taimaka yasa sufi haka "
Amin cewar Anti Hafsa.

Bayan Abdallah ya gama cin abinci ne ya kira jabir yazo suka tafi can BQ sae firar bayan rabuwa suke dan sun jima sosai basu had'u ba.
A nn jabir ke jajanta masa abinda ya faru game da bintu har yana nuna masa rashin jin dad'in faruwar hakan.
Abdallah yace"hm bari kawai jabir abun ba dad'i gaskiya bansan me ya d'ebe ta ba har taji bata ra'ayin haifuwa a lokacin da ta sami ciki wae ita bata tashi ba se ta had'u da su zeenah suka qara kaita suka baro"
Jabir yace"wlh ni tun lokacin da na fara ganin su naji yaran basu min ba kwata kwata ashe mugun haline dasu har wnn zeenah d'in tana wani liqe min wae ita sona take jaka kawai d'an chakwai dani ita kuma jibgegiya ina zan tafi da ita.
Dariya Abdallah yayi had'e da fad'in"kae baka da dama jabir ae zeenah ba wani jiki ne da ita ba kai dai kawai baka sonta"
Jabir yace"wlh Allah ni ta min qatuwa nafi son er chakwai dae dai ni wacce zamu jima muna damawa bata zamar min uwa ba.
Allah ya baka to
Jabir yace"Amin kafin yake cewa ni kuwa Abdallah har saki nawa ne waheed yayiwa bintu da baza a sake zuwa a basu haquri ba ko Allah zae sa wnn karon ta saurare mu dmn nidai bana son ganin bintu cikin damuwar nn nafi son ta koma d'akin mijinta wlh.
Abdallah ya numfasa snn yace"wato jabir bintu taqi ta snr da kowa ko saki nawa ne kuma har ga Allah naso in sake komawa gun mami in bata haquri amma yaya Abbas yace wlh duk yaji na sake zuwa nida shi ne.
Haba shikuwa yaya Abbas kan me zae ce haka.
Hm yaji haushi ne sosai akan abinda yaji bintu ta aikata dmn kasan a dalilin sa ne muka san waheed sbd amintar da ke tsakanin su,kuma kasancewar waheed mutum ne da baya da wani girman kai akai akai in ya sami lokaci yake kawo masa ziyara har ya zamo tamkar d'an gida haka muma muka d'auke sa kmr wani d'an uwan mu har soyayya tazo ta shiga tsakanin sa da bintu wacce tun bata kulashi sbd shirin da basa yi da yaya Abbas har tazo tana kulashi.
To ganin haka ne yasa na kira yaya Abbas na gaya masa abinda ake ciki da niyyar yazo muje gun mami ko ganin sa zae sa ta saurare mu amma yace kar ma in sake masa mgnr bintu ya kuma rantse kan kar in kuskura in koma gidan, inna tafi yaji nida shine,na san halin sa mutum ne mai baqar zuciya wlh komai zae iya faruwa idan naje sbd gabad'aya halin Abba ne dashi ya kuma zo shima ya zama soja like father like son shiyasa dole se na bishi a sannu har in samu ya yarda muje ba tare da mun sami wata matsala nida shi ba.
Jabir ya numfasa yace"hkne kam dmn a d'an sanin da na masa na fahimci mutum ne da kwata kwata baya son raini dole sae an bi yanda yake so ko za'a zauna lafiya.
Ae kam
cewar Abdallah wanda da haka sukayi shiru ba wanda ya sake cewa komai sae tunanin da kowa keyi a cikin ranshi.

Bayan sati biyu da faruwar haka,tuni bintu taci gaba da zuwa gurin aikin ta wacce har yanzu ta kasa cire damuwa a ranta ko zuwa aiki a kan dole take yin shi.
Haka 6angaren waheed yana rayuwa ne kawai dmn farin cikin mahaifiyar sa ba dan yana jin dad'in rayuwar ba,
wanda ba dan yana bin umarnin ta ba da ba wata mace da zaiyi rayuwar aure da ita bayan bintu da har yanzu yana cikin qunci da takaicin abinda ta aikata a gareshi ba wae don ya yarda cewa ta aure sa ne dan dukiyar sa ba sae dan kanme ta aikata haka a gareshi na zubar mae 'ya'ya da tayi da kullum cikin tunani yake ya kasa bawa kansa amsa hakan yasa Amaryar sa Husna sam bata jin dad'in rayuwar auren nasu sbd kwata kwata bata samun wata kulawa a gurin waheed.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 29_*
Sannu sannu lokaci keta tafiya kwanaki da watanni sunja amma

Please Login or Register in order to submit comment