Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga sama suka ga mutane sun shigo gidan bako sallama sae jefo kaya suke ta koina.
Cikin tashin hankli umma ke kallon kayan ta sa6ule hannunta daga ruwa kana ta kalli bintu tana fad'in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un! bintu me nake shirin gani kmr kayan d'akin ki!?
Bintu dake riqe da bocket zata je shanyi ta kasa cewa komai sae sake bocket d'in tayi tare da gurfanawa gurin kanta qasa ta saki kuka a hnkli marar sauti hawaye masu zafi suka soma gangarowa kan kumatun ta.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 25_*
Kwatsam sae ga Abban bintu ya shigo gidan sae masifa yake tayi da masu jefo kayan wanda sam bae kula da kayan waye ake jefowa ba yana fad'a ne sbd rashin mutuncin su da ya gani,su kuma gabad'aya take suka shiga taitayin su sbd ganin uniform d'in sojawa dake jikinsa suka daina jefo kayan suka ci gaba da sauke komai yanda ya kamata.
A zuciye Abban bintu ya qaraso ciki yana tambayar kayan waye ake watsi dasu haka daga ina suka fito?
Bintu dake gurfane kan guiwoyinta ta tashi ta tafi da gudu d'aki tana kuka.
Duk zuciyar da Abba ya d'ebo take ya sauko ganin yanda hawaye ke fita a idon umma.
Yace"subhanallah umman abdallah yau ke kike yin kuka lafiya me yake faruwa?
Komai umma bata iya ce masa ba ta tafi d'aki da sauri yabi bayanta.
Suma iyayen su sarah da saurin su suka zo a bakin qofa suka la6e domin jin me yake faruwa.
Umma kuwa da shigar ta d'aki a nn falo ta zauna kan doguwar kujera tasa ha6ar zaninta sae share hawaye take wasu na sake zubowa Abba da ya zauna kusa da ita yace"umman Abdallah gabad'aya kun tashi hankalina ki gaya min me yake faruwa kuke ma kuka dake har bintu?
Umma ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace"ni kaina ban san ainihin abinda yake faruwa ba amma na tabbatar rashin jin mgnr bintu ne yasa ta kashe aurenta ta dawo gashi har kayan d'akinta sun korota dashi wacce tun shekaran jiya da tazo gidan nn da uwar akwati nake tambayar ta gaya min me yake faruwa amma yarinyar nn ta 6oye min wae ba komai ashe ja'irar yarinya aurenta ne ta kashe ta dawo.
Abba ya numfasa yace"bari in kira waheed inji me yake faruwa amma na tabbatar tun da har suka mata haka laifin da ta musu yana da girman gaske.
Ya qarashe mgnr ne tare da ciro wayar sa a aljihu ya kira waheed ya jima sosai yana waya da waheed d'in kana ya kashe waya sae jinjina kansa yake yana fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Umma dake kallon sa ta matsu taji me yake faruwa dan abinda taji kawai shine irin haqurin da waheed keta bawa Abba kan komai bae faru a son ransa ba ba yanda zaiyi ne kawae tunda bintu ta riga ta aikata abinda bazai iya kareta ba.
Abba da gabad'aya ransa ya gama 6aci ya miqe cikin rawar jiki ya zaro qaton belt d'insa ya nufi d'akin umma,umma tayi saurin shan gaban sa tace"ka gaya min me yake faruwa tukun"
Abba yace"ki barni in fara dukan ta tukun dmn abinda ta aikata ko kashe ta zan iya yi yau sbd bata da wani amfani a gare mu ta 6ata mana mutunci mu da sunan mu gabad'aya.
Kafin tayi wani yunquri tuni ya fad'a d'akin ta, bintu dake kwance ruf da ciki kan bed tana rusar kuka sae saukar duka ta fara ji ta koina a jikinta,a gigice ta tashi sae ihu take tana ba Abba haquri,haka umma dake biye dashi sae haquri take bashi kan ya saurara ya gaya mata me yake faruwa tukun amma ina kmr qara tunzurasa suke dan baji ba gani yake dukan bintu tamkar Allah ne ya aiko shi.
Su umman sarah dake nn la6e a bakin qofar falo suka tafa hannayen su sae murna suke yau ga rnr da suke jira tazo.
Da saurin su suka bar gurin ganin yanda bintu ta fito aguje Abba na biye da ita har ta fita wajen gidan,
Abba da ya tsaya a qofar gida ya nunata yace"har abadah kar in sake ganin kinzo ko qofar gidan nn ki tafi duk inda zaki je mu bama da buqatar ki kuma ko a hanya kika ganni ban yafe ba idan kika nuna kin sanni.
Wani irin kuka bintu ta fashe dashi ta zube qasa kan guiwoyin ta sae haquri take bashi bai kulata ba ya juya zae koma cikin gida umma tabi shi sae roqon sa take tana bashi haquri, iyayen su sarah kallon su kawae suke murna fal a ransu ko na munafurcin nn dae su sa baki su bada haquri basuyi ba mazajen su ne keda d'an dama kuma duk basa nn ga Abba fir yaqi saurarar umma shifa lallai sae bintu ta bar gidan.

Bintu kuwa tana can waje qofar gida sae kuka take,
kawae sae ga su sarah napep ta ajiye su wa enda dama iyayen su ne suka kirasu kan suyi sauri suzo suga abinda ke faruwa burin su ya cika.
Bintu na ganin su taje da gudu jikin zeenah tana kuka tana fad'a musu Abba ne yace sae ta bar gida.
Sosai suka nuna alamar tausayi a fuskar su har zeenah ta cire gyalen ta da takalmi taba bintu snn kuma ta bata kud'in mota tace taje sokoto gidan anti Hafsa idan komai ya lafa snn.
Ba yanda bintu ta iya ta kar6i kayan sae kuka take ta shiga napep d'inda ta ajiye su yaja suka tafi zuwa tasha kmr yanda su zeenah suka snr dashi.
Wucewar su keda wuya sae ga umma ta fito a babbarkace gabad'aya ta rasa mafita riqe da hijabin bintu da takalmi da kuma en kud'in mota da ta riqo wacce itama niyyar ta ta tura ta sokoto gurin anti Hafsa kafin ta samu ta shawo kan Abba duk da bata ma ji me bintun ta aikata ba.
Dama su zeenah basu riga sun shiga gida ba suka mata bayanin cewa sun tura ta sokoto gurin anti Hafsa idan komai ya lafa snn.
Nan umma ta d'anji sanyi sanyi a ranta ta koma cikin gida gun Abba taji shin me bintun ta aikata da ya yanke mata wnn irin hukunci haka har yana fad'in bae yafe mata ba idan ta ganshi ko a hanya ta nuna ta san shi.

Umma na wucewa su sarah da zeenah suka tafa hannu irin tafawar da sauti baya fita snn suka shiga cikin gidan sae murna suke a ransu babban burin su a rayuwa ya cika wa enda qarin farin cikin su yanzu sun samu mazajen aure har anyi magana rana kawai ta rage a sa.

Bintu abin tausayi kuka take har ta isa garin sokoto wacce da saukar ta mota sae ga Anti Hafsa tazo d'aukar ta acewar su zeenah ne suka snr da ita halin da ake ciki.

Tun a cikin mota anti Hafsa taso tambayar bintu ainihin me yake faruwa sbd su zeenah basuyi mata wani bayani ba amma ganin yanda bintu ke kuka yasa tayi shiru har suka isa gida.

Da shigar su gidan ilham da Abba da daddy suka zo aguje sae murnar ganin bintu suke wacce bata iya kula su ba sbd halin da take ciki sae Anti Hafsa ce taja hannun ta suka tafi d'aki ta zaunar da ita kan bed snn itama ta zauna tasa hannu tana share mata hawaye tana fad'in"bintu gabad'aya hankalina a tashe yake ki daina kukan nn haka ki gaya min me yake faruwa gashi tun kafin ki iso sae kiran umma nake tayi amma wayarta a kashe bana samu su zeenah kuma basu min wani cikakken bayani ba,
ki gaya min ina so inji me ya faru tsakanin ki da waheed da har kika je gida Abba ya koro ki?
Duk da tana gudun irin 6acin randa Anti hafsa zata shiga bata iya 6oye mata komai ba tayi mata bayanin duk abinda ya faru.
Sosai ran Anti Hafsa ya 6aci wacce cikin fad'a tace"amma sae yau na tabbatar ke qatuwar wawuya ce wlh wacce baki san abinda kikeyi ba kan me zaki nemi shawara a gun su zeenah wa enda ko kad'an kinsan iyayen su basa qaunar mu ta yaya kike tunanin suma da gaske suke qaunar ki har da wani gaya musu banzan ra'ayinki kina biyewa shawarwarin su gamu mu en uwanki na jini muna gari d'aya kin kasa tuntu6ar mu ki sanar damu sbd kinsan ba abin qwarai ne kike shiryawa ba koh,
to ae yanzu sae kije suda suka baki shawara har kika shiga matsalar sae su fidda ki a cikin matsalar tunda su masu qaunar ki ne da suka fi mu.
Daga haka anti Hafsa ta fita rae 6ace ta bar mata d'akin.
Bintu ta kwanta sae kuka take ci gaba dayi shikenan ta aikata kuskuren da har abadah baxa ta ta6a iya gyarawa ba wanda kowa yaji sae yayi tir da abinda ta aikata.

Haka ta yini ita kad'ai a d'akin wacce tun lokacin da anti Hafsa ta fita bata sake dawowa d'akin ba sae ilham ta turo ta kawo mata abinci da ruwa amma ko ruwa bata iya sha ba bare taci abinci.

Da dare guraren bayan isha'i bintu na d'akin su ilham wato d'akin yara,tana zaune kan bed ta had'e kai da guiwa wacce gabad'aya jikinta ya gashe sosai yayi zafi sbd zazza6in da ya mata mugun kamu kan kukan da tasha da kuma rashin cin abinci.
Sae ga Anti Hafsa ta shigo d'akin ita da Abdallah yana janye da akwatin bintu a hannun shi wanda sallamar da yayi ne yasa bintu ta d'ago kanta da sauri jiri na d'ibar ta tazo jikin sa cikin kukanta da baya ko fita sosai.
Cike da tausayi Abdallah yaje da ita kan bed suka zauna anti hafsa ta kar6i akwatin hannun sa takae ta inda ta dace snn itama tazo ta zauna dan magana suke son zasuyi da bintu.
Abdallah ne ya fara magana cikin natsastsiyar muryar sa yace"bintu banji dad'in abinda naji ance kin aikata ba ko kad'an,na kuma yi baqinci sosai musamman da nazo na sami umma har kuka take kan abinda taji kin aikata a bakin Abba wacce ba abinda yafi qona mata irin yanda akace wae sun sa kin auri waheed ne dan dukiyar sa, fisabillillah bintu meyasa kika 6atawa iyayen mu suna gashi gabad'aya anguwar mu kowa yaji abinda ya faru wa enda qalilan ne masu taya mu baqin ciki sauran duk ala gwai suke mana kan irin qarya da gaskiyar da iyayen su sarah suka had'a suna ta yad'awa gida gida sae kace wani abun farin ciki,koda yake su agun su abun farin ciki ne kece dae kika kasa fahimtar cewa ba qaunar ki su sarah keyi ba suna nuna miki so ne kawai a fuska wanda yaci ace kin fahimci haka tun lokacinda suka baki shawara kan abinda duk wani masoyin ki na gaske bazai ta6a baki wnn shawarar ba sae dai ya saki a hanya kan kar ki aikata amma sukace kiyi kika kuma yi and still kina ganin wai su masoyanki ne, me yake damunki ne bintu, ina wayonki ya tafi da har kika bar ra'ayin zuciyar ki yayi tasiri akan ki bayan kinsan ba abune mae kyau zaki aikata ba,abun haushi da takaici wae da kanki kike ta kashe 'ya'yanki na halal kina hana su zowa duniya wae ke baki tashi ba Allah ya miki gaggawa knn koh?
Da saurin ta girgiza kanta cikin dasashiyar muryata da tasha kuka tace"kayi haquri yaya Abdallah wlh ba haka bane rashin wayo ne ya d'ebe ni kuma tun a rnr da na aikata wnn kuskure nazo inayin nadama na kuma d'auki alqawarin bazan qara aikata kuskure irin wnn ba amma ban san ya akayi ba da muka je asibiti Dr Khalid yace wae bayan na zubar da cikin farko ina shan magani dan kawae ko na sami ciki ya zube byn ni a sani na wlh bana shan wani magani.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka
Abdallah yace"bintu idan mu mun yarda cewa baki shan wani magani su baza su yarda ba sbd khalid ne ya duba ki,Khalid kuwa aminin waheed ne sosai da sosai da bazai fad'i abinda bashi bane qarin matsalar kuma maganar da mami tajiyo kan kin auri waheed ne dan dukiyar sa har ma akace dalilin hakane yasa kike zubar da ciki kinga kuwa koda sharri ake miki su baza su iya ganewa ba tunda kin riga kin aikata kuskuren farko wanda da ace baki aikata ba da duk hakan bata faru ba kuma koda ace shi waheed yaqi yarda da zancen cewa kin aure sa dan dukiyar sa ne mami zata yarda sbd soyayyar d'anta qwaya d'aya tal ta rufe mata ido dole tayi duk wani abu na ganin ba'a rabata dashi ba dan haka kar kiga laifin abubuwan da ta aikata a gare ki ke kika ja koma mene ne.
Bintu tace"ae ni yaya banga laifin ta ba sbd duniyar nn komai yardar ka da mutum zae iya cutar da kae akan abun duniya amma ina so ta yarda cewa ni yarda ta da ita ta har abadah ce bazan ta6a iya cutar dasu ba duk abinda sukaji sharri ne kawai ake min kuma na tabbatar ba kowa bane sae su zeenah da suka zo rnr su sukayi koma mene ne sbd da muka dawo asibiti yaya waheed bai gayawa mami ainihin abinda ya faru ba haka nasan Dr khalid haka kawai bazae kirata ya gaya mata ba, da haka nake son dan Allah yaya ka taimaka min kaje ka fahimtar dasu ka kuma basu haquri.
Abdallah ya numfasa yasa hannun sa ya share mata hawaye snn yace"naji zan tafi d'in amma sae kinci abinci kinsha magani dmn jikin nn naki yayi zafi da yawa"
Ba musu ta gyad'a masa kae
Anti Hafsa tace"Allah yasa su yarda su saurare ka"
Yace"amin"
Snn ta fita ta kawo ma bintu abinci abdallah da kanshi yake bata abincin har sae da tace ya isheta ya bata magani tasha snn ya fita.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 26_*
Wanka bintu ta nemi zatayi Anti Hafsa ta shiga bathroom ta had'a mata ruwan d'umi a bahon wanka wacce koda ta fito ta sami bintu ta tu6e tana d'aure da towel,bintu ta shiga bathroom
Anti hafsa kuma ta fita d'akin riqe da plate d'inda bintu taci abinci dashi wanda ke d'auke da sauran ragowar abinci akai.

Bata wani jima sosai a bathroom d'in ba ta fito tayi shirin bacci tazo tayi kwance kan bed sae addu'a take a ranta Allah yasa mami ta saurari Abdallah ta kuma yarda da bayanin da zae yi musu.
Ta jima kwance a gurin tana ta fmn addu'a a ranta can kmr daga sama taji sallama kmr ta waheed da saurin ta ta tashi zaune ga mamakin ta kuwa waheed d'in dae ne shida Abdallah suka shigo ae kuwa bata san lokacin da ta miqe tsaye ba bakinta ya kasa rufuwa sae kallon waheed take wae shi d'in dai ne ko kuwa gizo yake mata gashi sae kallonta yake yana murmushi ya kuma ware mata hannayen sa alamar tazo kmr da tsoro ta girgiza kanta dan gani take in taje 6ace mata zai yi.
Yace"kar ki ji tsoro my lady nine ba gizo nake miki ba zo kinji"
Kuka da dariya ne suka su6uce mata lokaci d'aya sbd farin ciki taje da gudu jikinsa ya rungume ta qam a qirjinsa sae fad'in yake"na yafe miki duk abinda kika min fatima dan Allah kar ki koma tafiya ki barni i cnt be with out u.......firgigit ta tashi daga mafarkin da take sae dube dube take dae dai anti Hafsa ta shigo d'akin ta taso da saurinta tazo gun anti Hafsa tana fad'in"anti Hafsa ina yaya waheed ya tafi yanzun nn shida yaya Abdallah, yanzun nn fa na gansu anti har ya rungume ni a jikinsa sae kawae naga ban ganshi ba ko sun tafi su dawo ne Anti?
Anti Hafsa tace"bintu mafar...bintu tayi saurin girgiza kanta tace"dan Allah kar kice min mafarki nake wlh da idona na gansu anti har ma ya rungume ni a jikin sa yana fad'in ya yafe min duk abinda na mishi.
Anti Hafsa ta sauke numfashi tana kallon ta cike da tausayi taja ta suka je kan bed suka zauna tace"naji ba mafarki kikayi ba amma na tabbatar gizo ya miki dmn Abdallah bai ko dawo ba tun lokacinda ya fita.
Qwallah tap a idon ta tace"Anti wlh ba gizo bane shida kansa ma ya fad'a har yace min inzo na kuma je ya rungume ni ba tare da ya 6ace min ba kawae dai ki ce min sun fita su dawo ko anti.
Anti Hafsa tayi shiru tana kallon ta dmn ta fhmci mafarki dae ne bintu tayi,
yanzu idan Abdallah ya dawo basu saurare sa ba ya knn.
Tana kaiwa nn kuwa sae ga Abdallah ya shigo d'auke da sallama a bakin shi,cikin murna bintu tace"kin gani ko anti na gaya miki ba mafarki bane sun fita ne su dawo may be baki san lokacin da suka shigo bane.
Bata jira me anti Hafsa zata ce ba tazo gun Abdallah da ke tsaye a bakin qofa jiki sanyaye ya kasa qarasa shigowa tace"yaya Abdallah ina kuma yaya waheed ba yanzu kuka shigo tare ba?
Abdallah dake kallon ta qwallah ne ke son ciko masa ido yayi saurin had'iye hawayen yace"mafarki kike yi bintu ni ban dawo ba tun lokacin da na fita se yanzun"
Cikin rashin fahimta tace"nifa yaya banyi bacci ba kwanciya kawai nayi ina jiran dawowar ka sae kawae naji sallamar yaya waheed da farko nayi mamaki ko gizo yake min amma da kanshi ya gazgata min cewa shine.
Abdallah ya numfasa yace"bintu kiyi haquri mafarki ne kikayi inaga bacci ya kwashe ki ne baki sani ba"
Bintu dake kallon sa tayi qasa da idonta hawaye suka silalo a hnkli kan kumatun ta,Allah sarki knn d'an kwanciyar da tayi bacci ya kwashe ta a gurin bata sani ba.
Ta share hawayen snn ta d'ago tace"to yaya da kaje ka same su kayi musu bayani sun kuma fahimce ka ko kuwa?
Abdallah dake kallonta ya qara jin tausayin ta a ranshi sbd ba yanda baiyi ba amma mami taqi ta saurare shi.
Bintu dake kallon sa tace"mami bata saurare ka ba ko yaya?
Yace"A'a ban same su bane sun fita"
Tace"Aa yaya kasani koda ka 6oye damuwa a fuskar ka idanuwan ka baza su 6oye ba,ka gaya min koma mene ne zanyi haquri da qaddarar da ta sameni"
Yace"bintu damuwar da ke idona damuwar da kike ciki ce ke damuna dan haka jeki ki kwanta kiyi bacci kinji"
Tace"to gobe da safe zaka sake komawa gurin su?
Ya gyad'a mata kae qwallah nata son ciko masa ido yana had'iyewa.
Bintu kuwa ba musu taje ta kwanta anti Hafsa tasa mata blanket ta rufa mata jikinta ta kuma kashe mata wutar d'akin snn suka fito falo ita da Abdallah.

Bayan sun zauna Anti Hafsa tace"Abdallah na fahimci kmr ba'ayi nasara ba koh?
Yace"hakane anti ba yanda banyi ba taqi ta saurare ni bare ma taji bayanin da nazo mata dashi dmn ganin take kmr duk yaudara ce kawai so muke muyi galaba akan su.
Anti Hafsa tace"har da waheed d'in bae saurare ka ba ko kuwa?
Gidan waheed na fara zuwa dmn nasan shi mutum ne mae sauqin kae da zae fahimce ni lokaci d'aya amma sae ban same shi ba akace yana gidan mami,sae gashi da naje gidan mami bata saurare ni ba har tana cewa idan ban gaggauta fita gidan ba zata kira min police su tafi dani ba yanda na iya dole na fita gidan ba tare da nako ga waheed ba asalima bai ko san abinda ke faruwa ba.
Anti Hafsa tace"ae ko ka ganshi ba yanda za'ayi tunda mami taqi ta saurare ka amma meyasa ka 6oyewa bintu baka snr da ita gaskiyar abinda ke faruwa ba?
Anti Hafsa banso na 6oye mata ba amma tausayin ta yasa na kasa gaya mata dan nasan idan taji bazata iya yin bacci ba sae dai tayi ta kuka.
Anti Hafsa tace"hakane amma mami ta bani mamaki da lokaci d'aya tayi watsi da duk wata yardar da mutuncin da ke tsakanin mu.
Abdallah yace"ki daina mamakin ta anti Hafsa sanin kanki ne mutanen duniyar nn sun lalace qalilan ne masu aminci sae kiga sbd kud'i uwa zata iya saida d'anta,haka d'a zae iya saida uwar sa koma ya kashe ta da hannun sa to meye abin mamaki dan ta yarda da abinda taji wanda abun yazo a sarqaqe ta yanda dole ta yarda.
Anti Hafsa tace"hkne yanzu gobe da safe me zamu cewa bintu?
Zamu gaya mata gaskiya dan abune da bazai 6oyu ba sae dai tayi haquri da qaddarar da ta same ta.
Anti Hafsa tace to shikenan bari in kawo maka abinci kaci.
I cnt eat any more Anti kawae ki bani ruwan Lipton insha,
nn Anti Hafsa ta tashi ta had'o masa ruwan Lipton ta kawo masa.

Washe gari guraren qarfe goma Anti Hafsa ce riqe da hannun bintu suka je kan dining suka zauna dmn yin break fast Anti Hafsa ta d'auki plate ta fara zubawa bintu arish da soyayyen qwai had'i da plantain.
Bintu tace"Anti ya naga mu biyu kawae zamuyi break fast ina su ilham da Abban su?
Anti Hafsa tace"su ilham na kaisu school Abban su kuma kinsan yanzu Abuja yake aiki sae weekend yake dawowa.
Tace"to yaya Abdallah fa?
Yana BQ na kirashi yanzu nn yace zae zo.
Daga haka bintu tayi shiru bata sake cewa komai ba, jim kad'an Abdallah ya shigo sukayi ina kwana snn ya zauna suka fara break fast.
Suna gamawa Abdallah ya tashi zae fita bintu tace"yaya ya zancen mgnr mu ta zuwa gurin mami ko can ne zaka tafi?
Abdallah yayi shiru bae so ace shi zae gaya mata ba yaso ace anti hafsa ce dan shi baya son ganin yanayin da zata shiga ciki idan taji mami bata saurare sa ba amma ya zama dole ya gaya mata da kanshi.
Bintu dake kallon sa tace"yaya kayi haquri na takuraka koh?
Abdallah ya zauna had'e da riqo hannayen ta yace"ko d'aya baki takurani ba bintu amma ina son kiyi haquri da abinda zaki ji daga bakina jiya da nace miki naje ban same su ba na 6oye miki ne sbd bana son ki kwana cikin damuwa amma gaskiyar magana shine da naje mami bata saurare ni ba asalima ganin take kmr wata yaudara ce naje musu da ita amma kar ki damu wani lokaci zan sake komawa koda Allah zae sa idan naje ta saurare ni.
Qwallah ne suka ciko a idon bintu tace"ba komai yaya nagode qwarai da kulawar ka a kaina"
Daga haka ta tashi da sauri ta bar gurin sbd kukan da take ji sosai.

Anti Hafsa ta tashi zata bita Abdallah yace"Kar ki bita anti Hafsa ki barta tayi kukan ko zata ji sauqin abinda ke ranta"
Anti Hafsa tace"wane kuka ne batayi ba Abdallah tayi kuka tayi kuka har da su zazza6i to kan me za'a barta taci gaba dayin kuka bayan kukan bazae mata maganin damuwar da take ciki ba.
Hakane Anti Hafsa amma idan kin lura kukan nn yazo mata ta yanda bazata iya controlling d'insa ba ki barta kawai tayi ni zan tafi gidan Anti nafee sae na dawo"
Anti Hafsa ta masa a dawo lafiya snn ya fita.
Baifi awa d'aya da fita ba sae gashi

Please Login or Register in order to submit comment