Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murfin rijiyar ba saboda zurfinta. Haka kuma cikin rijiyar dundum yake ko tafin hannun mutum ya daga ba zai gani ba. Tsawon shekaru goma sha uku haka gimbiya malifa ke rayuwa a cikin wannan rijiya kuma bata taba fashin yin sallah ba sau biyar a rana. Duk wannan tsananin duhu dake cikin rijiyar ita bata taba ganinsa ba albarkacin yawan ibadar dake yi a cikin rijiyar. Wani abin mamaki shine ko sau daya gimbiya malifa bata taba yin addu'ar allah ya fitar da ita daga cikin wannan rijiya ba, saboda duk sa'adda ta tuna cewa an kashe iyayenta kuma an rabata da dan uwanta wanda aljani raukaful barwasu ke yawan gaya mata cewa ya kai shi can nahiyar da ake ta yake-yake sai ta dauka cewa tuni lamras ya dade da hallaka, saboda haka sai taga cewar rayuwarta a cikin mutane bata da wani amfani gwara tayi ta ibada a cikin wannan rijiya har izuwa lokacin da aljalinta zai risketa. Gimbiya malifa tayi imani a cikin zuciyarta cewa allah ne ya nufe ta da wannan kaddara ta rashin iyayenta da 'yan uwanta kuma shine ya nufeta da zama a cikin wannan rijiya don haka idan ya kaddara cewa cikin rijiyar ne kabarinta babu makawa a nan zata mutu. Lokacin da aljani raukaful barwasu ya iso kasan rijiyar sai yayi tsafi haske ya baibaye ko'ina a cikin rijiyar, kawai sai ya ga gimbiya malifa a zaune ta fuskanci gabas tana sallah. A duk sa'adda yazo ya risketa tana ibada sai ya zauna a gefe daya har sai ta idar da sallar ta shafa addu'a sannan yake yi mata magana, amma ya kan kura mata idanu saboda ganin tsananin kyawunta wanda yafi gaban kwatance. Idan za a kwatanta kyawun malifa dana sulaira sai dai a ce sulaira jaririya ce akan malifa ko kuma a kira ta mummuna saboda banbancin a baiyane yake. Aljani raukaful barwasu ya sha kamuwa da sha'awar gimbiya malifa, amma da zarar ya yunkura zai afka mata sai yaji kamar wuta mai tsananin zafi na laso jikinsa bisa dole yake hakura ya danne kwadayinsa. Yau ma kamar kullum haka raukaful barwasu ya tsinci kansa a cikin irin wannan yanayi don haka sai ya kurawa malifa idanu har yana dalalar da yawu kamar kura ta ga gawar barewa a lokacin da take fama da tsananin yunwa babu abin da yake baiwa aljani raukaful barwasu mamaki face ganin tun sa'adda ya jefa gimbiya malifa a cikin wannan rijiya duk sa'adda ya kawo mata abinci ya tafi idan ya dawo sai ya iske wannan abinci kamar yadda ya kawo shi ko loma daya bata yiba. Tun malifa na karama har ta balaga ta zama cikakkiyar budurwa haka al'amarin ya kasance. Bisa wannan dalilii ne wata rana ya kasa barin abin a ransa ya dubi malifa yace. "Wai shin ke yaya aka yi kika rayu acikin wannan rijiya ba tare da kin ci kin sha ba? Na fuskanci cewa duk abincin da nake kawo miki baki taba dandana shi ba, sai dai na kawo na iske shi kamar yadda na bar shi, har ma in ya dade yayi funfuna da tsutsa, sai warinsa ya isheki sannan kike haka rami ki binne shi. Tambayata ta biyu itace me yas baki taba jin tsorona ba, duk da cewa duk sa'adda nazo miki saina yi miki hargagi gami da yunkuri kamar zan cutar dake?" Sa'adda malifa taji wadannan tambayoyi sai ta dubi aljani raukaful barwasu cikin murmushi tace, "game da tambayarka ta farko ina so ka sani cewa abinci ba shine ke tallafa wa rayuwar kowanne mahaluki ba. Allah shine mai kashewa da rayawa, don haka koda abinci ko babu abinci ubangijina zai iya rayar dani a cikin kowanne irin hali tunda nayi imani cewar shi ne mai ikon komai da kowa. Kasani cewa tunda ka jehoni cikin wannan rijiya sau daya nayi kuka shima sakamakon tunowa da rashin iyayena da dan uwana ne. Tun daga wannan rana na sallama komai ga allah na lizimci nafiloli, da lazimi da yin sallah akan lokacinta. Ni kam daga sannan ban taba jin yunwa ko kishirwa ba, kullum da ko yaushe nake jina cikin koshiin lafiya ko ciwon kai bai taba riska taba. Ni kaina nasan cewa wannan ba komai bane face ikon allah. Game da amsar tambaya ta biyu kuwa ita ce ni banga dalilin da zai sa naji tsoronka ba tunda na san cewa kai bawan ubangijina ne kamar yadda nake baiwarsa, don haka a ganina babu abin da ya kamata naji tsoronsa face ubangijin musulunci tunda kai ba ka isa kayi min komai ba face da yardarsa." Tunda daga ranar malifa tayi wannan furuci ga raukaful barwasu sai ta yi masa kwarjini ainun bai sake kai mata wani wargiba. Bayan malifa ta shafa addu'a sai ta waigo ta fuskanci aljani raukaful barwasu taga yana yi mata murmushin mugunta. Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan ta dube shi tace. "Ya kai raukaful barwasu kai kuwa akan wane dalili yau kake yi mini murmushin mugunta?" "Ya ke wannan ma'abociyar kyawu kiyi sani cewa tsawon shekaru goma sha uku na zamanki a cikin wannan rijiya kullum karya nake tsandara miki, amma yau zan fada miki gaski kuma ba don komai zan fada miki wannan gaskiya kuma ba don komai zan fada miki wannan gaskiya ba sai domin na haddasa miki gagarumin bakin ciki a cikin zuciyarki." Koda jin haka sai malifa tayi murmushi tace, "yanzu har akwai wani bakin ciki a gareni wanda yafi na rashin iyayena da rashin dan uwana lamras?" Aljani raukaful barwasu ya tuntsire da dariyar mugunta sannan yace, "Ai wannan dan uwa naki wato yarima lamras da nake ta yawon gaya miki cewa ya mutu to fa bai mutu ba, yana nan araye, amma gobe da yamma sarki hasanul mauzur zai kashe shi domin za a yi gasar yaki. Ina mai yi miki tuni da cewa sarki hasanul mauzur shIne wanda ya kashe iyayenku ya baje wannan birni naku, ya kawar da dukkan jama'arku." Lokacin da aljani raukaful barwasu yazo nan a zancensa sai hankalin gimbiya malifa ya dugunzuma ainun ta zancensa sai hankalin gimbiya malifa ya dugunzuma ainun ta ji babu abin da take so sama da ta fita daga cikin wannan rijiya, domin taje ta sadu da dan uwanta yarima lamras kafin ajali ya rabasu. Nan take hawaye ya zubo mata. Koda aljani raukaful barwasu yaga hawaye na zuba a cikin idanun malifa sai ya cika da matukar farin ciki ya dunga kyakyata dariyar mugunta. A daidai wannan lokaci ne gimbiya malifa ta fara rokon allah a cikin zuciyarta tana mai cewa. "Ya allah don isarka da isar mulkinka, don daukakarka da ikonka ka dankwarar da wannan aljani a cikin wannan rijiya ya kasa koda motsa dan yatsansa guda, ni kuma ka fitar dani daga cikin rijiyar nan ka sada ni da dan uwana kafin makiya su hallaka shi." Kafin malifa tagama wannan furuci a cikin zuciyarta sai kawai taga aljani raukaful barwasu ya kife kasa da ruf da ciki yana wani irin haki kamar wanda aka yi wa dukan kawo wuka. Kawai sai yaga malifa ta tashi sama kamar tsuntsuwa zata fice daga cikin rijiya gaba daya. Al'amarin daya matukar firgita shi kenan ya dugunzuma hankalinsa. Kawai sai ya fashe da kuka yana mai kiran malifa da ta taimake shi ta fitar dashi daga cikin wannan hali da ya shiga kada ta fice ta barshi a cikin wannan rijiyar. Koda jin haka sai malifa ta dube shi tayi murmushi tace. "Yakai raukaful barwasu kayi sani cewa ire- iren ku a doron kasa annoba ne, babu inda yafi dacewa da kai sama da cikin wannan rijiya dama nan ne inda yafi dacewa da kai. Dama nan ne inda kakanmu ya ajiyeka amatsayin kurkuku bisa munanan aiyukan daka ke aikatawa yanzu gashi ka dawo makomarka wannan shine sakamakon azzalumi tun a duniya sai kuma ajira lashira ka karbi babban sakamako na karshe." Koda gama fadin haka sai malifa taci gaba da yin sama ta bar raukaful barwasu yana ta rusa kuka. Ai kuwa malifa na gama fita daga cikin rijiyar sai rijiyar ta rufe da kanta. Har malifa ta juya zata tafi sai taga wannan dan karamin littafi mai dauke da addu'ar da ake karantawa rijiyar ta bude. Kawai sai ta dauke littafin ta yayyaga shi gutsin gutsin takardun suka tarwatse a cikin kwatar kuma ruwa ya tafi dasu. A sannan ne malifa ta daga kanta sama ta kalli hasken rana sai tayi murmushi gami da godiya ga allah tace ya ubangijin gaskiya ina mai godiya a gareka daka fito dani daga cikin wannan rijiya a yau domin haka ka nufa a gare ni kuma ina mai dada yin roko a gareka da kakaini inda dan uwana yarima lamras yake koda. A birnin sin ne kafin makiya su cutar da shi ka sadani dashi. Gama fadin hakan ke da wuya sai malifa ta nufi cikin rushashshen birnin nasu tana kalle-kalle. Koda taga yadda birnin nasu yazama a yanzu ta tuno yadda yake ada sai takaici ya turnuke ta ta fara zubar da hawaye a lokacin data rinka ratsewa gawarwakin bil adama da suka zama kwarangwal gasu nan birjik ba kyan gani wasu ma sun fara rugurgujewa. A wannan lokaci ne malifa tayi ta tunowa da abubuwan da suka faru a baya sa'adda suke yara ita da dan uwanta yarima lamras. Ta tuno da duk irin wasannin da suke yi kuma ta tuno da irin tsananin kaunar da iyayensu suka nuna musu. Koda gama tuno wadannan al'amura sai ta zauna a waje daya ta kama kuka. Ba ta gushe ba tana wannan kuka har tsawon sa'a guda kuma gashi garin yayi tsit ba a jin sautin komai face muryarta. Wani abu daya bata mamaki shine gaba daya gineginen garin a rushe suke, masallacin garin ne kawai ba a rushe ba, yana nan garau kamar yadda ta san shi a da malifa na cikin wannan hali na kuka sai kawai taji an bude kofar wannan masallaci. A firgice ta dago kai kawai sai tayi arba da wani kyakywan farin aljani a cikin fararen tufafi ya fito daga cikin masallacin yana jan wata doguwar casbaha. Koda aljanin ya dago kai ya hango malifa zaune a can nesa kadan sai ya cika da tsananin mamaki, don haka yata ho gareta. Batare da fargabar komai ba malifa taci gaba da kallon aljanin tana sauraron isowarsa gare ta. Da zuwansa sai ya budi baki yayi mata sallama. Cikin farin ciki malifa ta amsa masa sallamar. Kawai sai yayi murmushi a gare ta yace. "Yake wannan baiwar allah menene ya kawo ki nan inda babu wani mahaluki da yake rayuwa face ni kadai acikin wancan masallacin kuma har kika zauna anan kina kuka?" Sa'adda malifa taji wannan tambaya sai ta share hawayenta, sannan tayi nuni da hannunta izuwa ga wannan tsohuwar rijiya wadda ta fito daga cikinta tace, "kaga waccan rijiyar, shekara ta goma. Sha uku a cikinta a tsare sai yau allah ya fitar dani daga cikinta." Cikin tsananin mamaki "aljanin ya sake dubanta ya ce, "ya ya aka yi wannan al'amari ya kasance ban san dake a cikin wannan rijiya ba, alhalin yau shekarata tara a cikin wancan masallaci ina ibadar allah kuma hanya ce kawai ta biyo dani tanan da naga yadda aka rushe wannan birni, kuma naga wannan masallaci sai na gane cewa wannan birni ne na ma'abota musulunci kuma duk yadda aka yi kafirai ne suka kawo musu harin sumame suka murkushe su. Domin nayi addu'a ga musulman da aka rasa a cikin wannan birni shi yasa na tare a cikin masallacin na yi ta ibada dare da rana." TARWATSA MAZA 4 >>>D<<< Al'amarin gimbiya lusaira kuwa a lokacin data bi sarki hasanul mauzur da sauri izuwa cikin gidan sarautar sai ta sha gabansa ta tsaida shi ta dube shi cikin tsananin damuwa tace. "Ya kai abbana saboda me zaka zafafa a kan wannan gasa kace ku nemi ran juna kai da wannan bakon jaruni alhalin ba haka ka'idar gasar take ba?" A fusace sarki ya dubi sulaira yace, "Shin bakiji irin kalmar daya furta bane a lokacin da ya sami nasara a kan daya jarumin? Ina sanar dake cewa wannan bakon jarumi makiyin. Mune ma'abocin addinin musulunci kin san kuwa d dai na aurar dake a gare shi gwara na mutu lallai agobe da yamma zanyi masa kisan gilla agaban kowa. Kin sani cewa bana magana biyu saboda haka ki tafi ki bani wuri kada ki kara zuwa mini da wannan furuci. " Koda gama wannan batu sai sarki ya wuce izuwa cikin dakin halwar tsafinsa ya turo kofar ya rufe ya bar gimbiya sulaira a tsaye cikin tsananin tashin hankali. Nan take sulaira ta yanke shawarar tayi badda kama taje har can masaukin wannan bakon jarumi ta roke shi akan ya hakura da wannan gasa yayi tafiyarsa domin idan har ya tari sarki sunansa gawa. Nan take kuwa gimbiya sulaira ta tafi izuwa bangaren da gidanta yake. Da zuwa sai ta kira wata amintacciyar kuyangarta mai suna IKILAIRA ta zayyan mata abin da take son yi. Koda jin hakan sai ikilaira tayi murmushi tace. "Ya shugabata ai wannan abune mai sauki tamkar shan ruwane. Abin da nake so dake shine ki bani 'yan dakiku zan je na binciko masaukin wannan bakon jarumi, sannan nayi shirin yadda zamu fita muje mu riske shi baa tare da kowa ya ankaraba. " Koda jin haka sai murna ta kama gimbiya sulaira ta ce, "Maza kije ki gama wannan shiri kafin magariba tayi."Cikin hanzari kuyanga ikilaira ta fice daga cikin gidan sarautar. Kafin magariba tayi kuwa ikaira ta gama dukkan shirinta don haka sai ta kai wa gimbiya sulaira wadansu tufafi makaskanta na talakawa kuma ta sauya mata kamanni ta hanyar yi mata wata irin kwalliya irin ta mutanen kauye. Komai sanin da mutum yayiwa gimbiya sulaira bai isa ya shaida taba a cikin wannan siffa. Batare da bata lokaciba ikilaira da sulaira suka fice daga cikin gidan sarautar. Duk inda suka zo wucewa aka ganta da bakuwar kuyanga sai a kura musu idanu. Wani wajen ma sai dakaru sun bata musu lokaci da tambayoyi amma cikin sa'a ba a sami wanda ya gano gimbiya sulaira ba, kuma ba a hana su fitaa ba. Yarima zamir da yarima lamras na zaune. Acikin gidan da suka sauka suna cin abinci kuma wannan lokaci yarima zamir ya cire rawanin dake fuskarsa shida lamras kamanninsu yazo iri daya sak kamar tagwaye. Suna cikin cin abinci ne zamir ya dube shi yayi murmushi yace. Wai shin kai meya yasa idan muna tare a nan a kebe baza kayi wannan addu'a ba ka dawo da kamanninka su sauya daga irin nawa?" Koda jin wannan tambaya sai lamras yayi murmushi yace, "Ya kai abokina ka sani cewa kafi ni kyau nesa ba kusa ba, saboda haka a duk sa'adda na dubi fuskata acikin wannan kamanni naka sai naji wani farin ciki a raina duk da cewa nima ina daga cikin kyawawan samari." Koda jin haka sai yarima zamir ya bushe da dariya yace, "Kaga kuwa kai ne ka dace da irin wannan kyau nawa tunda kai zaka iya yin soyayya da 'ya mace. Ni da kokadan ban damu da soyayya ba, menene amfanin kyan a wajena. Ni fa gani nake har abada bazan taba ganin wata 'ya mace ba wadda za ta burgeni har naji na kamu da sonta." Da jin wannan batu sai yarima lamras yayi murmushi yace, "Haka dai kace, amma ai shi so barawo ne kuma baya sallama, a duk sa'adda yaso ya mamaye ba za kasani ba." Kafin yarima zamir ya yunkura zai dauki rawaninsa ya rufe fuskarsa sai yarima lamras yayi masa nuni da kada ya motsa cikin fushi yarima lamras ya dubi 'yan matan biyu yace. "Ku su waye, akan wane dalili zaku shigo mana cikin daki kai tsaye ko kwankwasa kofa baku yi ba?" A lokacin da yarima lamras yayi wa 'yan matan wannan tambaya sai yaga duk sun yi shiru kuma sun zuba masa ido kawai cikin mamaki. Daya daga cikinsu ta dube su tace. "A cikinku waye ya shiga gasar neman aurena a yau? Shin ku 'yan tagwaye ne? Da jin wannan tambaya sai yarima lamras ya dakawa 'yam matan tsawa yace, "Ya baku amsa mana tamba yarmu ba zaku damemu da tamba yarku" Wadda tayi tambayar sai tayi murmushi tace, "Ni sunana gimbiya sulaira 'yar sarki hasanul mauzur wacce ake gasar, neman aurenta a yanzu, wannan kuwa kuyaangata ce sunanta ikilaira. " Koda gama fadin hakan sai sulaira ta kwance mayafin daya daure kanta gashin kanta ya zubo a gadon bayanta har izuwa kan kwankwasonta, sannan tasa wani han kici ta goge duk zanen dake kan fuskarta, sai ga ainashin kyakykyawar fuskarta ta bayyana. Al'amarin da ya matukar girgiza yarima zamir kenan suka cika da tsananin mamaki. Yarima lamras ya dubi lusaira a cikin nutsuwa yace. "Nine wanda ya shiga gasar neman aurenki a yau kuma nine wakiline na wannan abokin nawa yarima zamir, ni kuwa sunana yarima lamras daga marigayin sarkin baitul nur wanda mahaifinki yaje ya kashe shi da taimakon aljani raukaful barwasu ya baje birninmu gaba daya bayan ya kashe gaba dayan jama'ar mu har da mahaifiyata. A wannan lokacine aka raba ni da 'yar uwata ta jini mulaifa. " Nan take yarima lamras ya kwashe labarinsa kaf ya zayyanewa su gimbiya lusaira, daga karshe ya sanar da ita cewa yazo da zummar ya dauki fansa akan mahaifinta lokacin da yarima lamras ya gama wannan labari nasa sai yaga gimbiya lusaira ta kamu da tsananin tausayinsa har kwalla ta ciko idanunta ta dube shi tace,....... @dan gogori ««« TARWATSA MAZA-4 TYPE E TAKUN KARSHE »»» Koda ganin wannan abu da ya faru sai gimbiya sulaira da yarima zamir suka fara kuka su kuwa sauran jama'ar gari sai suka fara sowa suna yIwa sarki kirari da jinjina. Nan take girman kai ya shiga sarki Hasanul mauzyr ya sake rugowa izuwa kan yarima lamsar ya rufe shi da sara da suka da dukkan karfinsa domin ya gididdiba shi gunduwa gunduwa amma sai lamras ya dage iya karfinsa wajen kare kansa, saboda jinin da ke zuba jikin lamras sai jiri ya fara dibarsa, kuzarinsa ya ragu ainun. A sannanne sarki hasanul mauzur ya shammace shi ya caka masa masa adda guda a gefen cikinsa. Take addar ta huda cikin ta bullo ta gadon bayansa, wani irin gudan jini yayi fitar burgu daga cikin bakinsa ya durkushe kasa bisa gwaiwowinsa bai fadi kasa gaba daya ba, saboda juriya irin ta mazan kwarai. Koda gimbiya sulaira taga abin daya faru ga lamras sai ta fashe da matsanancin kuka haka ma yarima zamir. Sarki hasanul mauzur ya tsaya akan lamsar ya dube shi ya kyalkyale da dariyar mugunta, sannan yace. "Kai yaro idan kana da wata wasiya ta karshe ka fade ta yanzu kafin na sare kanka. " Bisa mamaki sai sarki yaji lamrsa ya dago kai da kyar ya dube shi, sannan sai yayi masa murmushi yace, "Maza ka kasheni, domin na isa gidana na gaskiya." Wannan batu ne yasa jikin sarki yayi sanyi baiyi saurin sare kan lamras ba, saboda tsananin mamakin abin da yaji ya furta domin a sannan ne ya gamsu cewa lallai wannan addini na lamras addinin gaskiya ne tun da ga shi yana kan gabar mutuwa amma imaninsa bai raunana ba. Kwatsam sai sarki yaji wata irin iska mai karfi a samansa cikin hanzari ya daga kan nasa sama take yayi arba da wani jibgegen farin aljani dauke da wata zukekiyar budurwa. Koda budurwar ta kyallara ido taga jarumi lamrasa tayi masa kallon tsanaki kuma taga halin da yake ciki sai hawaye ya zubo mata ta kwala masa kira da karfi tace, "Yakai dan uwana na jini lamras maza ka mike kakawar da makiyinmu. Ni ce 'yar uwarka gimbiya malifa tsaye a samanka." Lokacin da lamras yaji wannan batu jiri na dibarsa kuma idanunsa suna lumshewa yana gani dishi dishi, amma sai kawai aka ga ya mike zumbur yasa kafarsa guda ya doki kirjin sarki Hasanul mauzur. Saboda karfin dukan saida sarki Hasanul mauzur yayi sama da baya ya fado kasa a matukar galabaice har yana aman jini. A sannane lamras ya zare wannan adda daga cikin cikinsa ya ruga da gudu izuwa kan sarki hasanul mauzur shima ya caka masa addar a inda ya cakamasa ya zare ta ya sake dagawa sama da nufin ya sare masa kai, kawai sai ya ji sarki Hasanul mauzur yace. "Na bada gaskiya ga ubangijin musulunci." Koda jin haka sai lamras yayi jifa da addar daga hannunsa ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme. Shi ma Sarki Hasanul mauzur sai ya sume. Cikin hanzari gimbiya malifa ta duro daga kan aljani sabi'ul Hasanul ta rungume lamras tana mai fashewa da matsanancin kuka. A sannanne ita ma gimbiya sulaira ta rugo izuwa wajen sarki Hasanul mauzur ta rungume shi tana rusa kuka. Cikin gaggawa aka dauki sarki Hasanul mauzur da yarima lamras aka shigar dasu cikin gidan sarautar domin ayi masu magani. A wannan lokaci ne mutane suka farga da irin tsananin kyawun gimbiya malifa kowa ya kura mata idanu. Wasu basu san sa'adda suka wangame baki ba yawu yayi ta dalala ba. Wasu kuwa suka kam sambatu. Koda malifa da yarima zamir suka hada idanu sai kowannansu yaji zuciyarsa ta buga da karfi, amma da yake hankalinsu akan yarima lamras yake sai suka ruga izuwa cikin gidan sarautar suka bi bayan dakarun da suka dauki su sarki. Sai da likitoci suka bata sa'a shida akan sarki hasanul mauzur da yarima lamras, sannan aka samo kansu suka farfado. Lokacin da sarki Hasanul mauzur ya farfado ya bude idanunsa yaga lamras a kwance kusa dashi, sai yayi masa murmushi yace, "yakai sirikina maza ka shigar dani cikin wannan addini naka. " Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube lamras nan take ya biyawa sarki Hasanul mauzur kalmar SHAHADA ya maimaita. A wannan lokaci gimbiya sulaira da gimbiya malifa da yarima zamir na tsaye a gabansu don haka sai suma suka cika da farin ciki. Take sarki ya dubi lusaira yace, "Yake 'yata maza ke ma ki karbi wannan addini, domin na gamsu cewa tabbas shine addinin gaskiya." Ba tare da wata gardama ba kuwa gimbiya sulaira ta karanta kalmar shahada. Da jin haka sai gaba dayan likitocin da ke cikin turakar da sauran hadimai ma suka biya kalmal shahada. A daren wannan rana babu wanda yayi barci tsakanin sarki Hasanul mauzur, yarima zamir, yarima lamras, gimbiya sulaira da gimbiya malifa, saboda tsananin farin ciki. Kuma a daren ne malifa taba su labarin duk abin da ya faru tsakaninta da aljani Raukaful barwasu a can cikin rijiya har allah ya fito da ita daga cikin rijiyar ta hadu da aljani sabi'ul hasnul ya dauko ta ya kawo ta nan birnin sharas. Koda gama jin wannan labari sai sarki Hasanul mauzur da gimbiya sulaira suka sake yin imani da allah suka tabbatar da cewa babu abin da yafi cancanta da a bauta masa face ubangijin musulunci. Kashe gari kuwa da sassafe sarki Hasanul mauzur ya kafa tutar addinin musulunci da hannunsa a kofar gidan sarautarsa, kuma ya kaddamar da addinin. Bayan nan ne aka daura auren gimbiya SULAIRA dana yarima LAMRAS dana MALIFA da yarima ZAMIR. Tun adaren jiya lamras da malifa suka kasance cikin tsananin farin ciki bisa saduwa, suka yi kukan murna domin basu taba zaton allah zai sake sada su ba. Babu abin da ya baiwa lamras mamaki face yadda malifa ta shaida shi farat daya a lokacin data ganshi har ma ya tambaye ta yadda aka yi ta shaida shi koda jin tamba yar sai ta dube shi tace. "HAba ya kai dan uwana shin ka manta ne nono daya muka tsotsa. Ai jini daya ya wuce wasa dole ne a sami wani abu a jikinka wanda ya zo iri daya da nawa. Na rantse da girman allah idanunka kadai na kalla na shaida ka domin har abada bazan taba mancewa da yanayin idanunka ba, tunda tun ina yarinya in na kura musu ido bana kiftawa." Koda jin haka sai lamras ya bushe da dariyar farin ciki, ya rungume malifa yana mai

Please Login or Register in order to submit comment