Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonsa ba tare daya sani ba. A ranar kwana na arba'in da ukun ne naga sariku ya dauko irin wannan mitsitsin littafi na wajena ya bude sai ga irin wannan addu'a sak dake cikin nawa littafin. Ai kuwa sai na kasa kunne da kyau, domin naji kalmomin daza su fito daga bakin sariku. Nan take naji ya biya wata addu'a gajeriya mai saukin haddacewa. Nan take kuwa na haddace addu'ar. Kashe gari da duku-dukun safiya na tafi bayan gidanmu ni kadai ban yarda naje tare da 'yar uwata malifa ba. Da zuwana gaban wannan tsohuwar rijiya sai na fiddo wannan mitsitsin littafi na bude da nufin na karanta, amma sai na kasa sakamakon tsananin tsoro dana kamu da shi, jikina gaba daya ya kama karkarwa kuma ya dume da zafi. Kawai sai na rufe littafin na juya da nufin na bar wajen. Sai na ji wata kakkausar murya daga cikin rijiyar tace da ni. "Haba yarima lamras saboda me zaka kasa bude wannan rijiya alhalin ka gama shan wahalar kwana da kwanaki wajen nemo mabudinta? Ina tabbatar maka da cewa idan ka bude ni na fito bazan cutar da kai ba, kuma sai na nuna maka abubuwan al'ajabi guda dubu dake cikin duniyar nan wanda babu wani mahaluki daya taba ganinsu" koda naji wannan batu sai na juyo da baya na tsaya agaban rijiyar a lokacin jikina ya cigaba da karkarwa nace, "Ya kai wannan aljani waishin menene sunanka, kuma yaza a yi na gamsu cewa idan na bude kaka fito bazaka cutar dani ba? Kasani cewa ina da labarinka cewa, saboda zaluncinka ne kakana ya kulle ka a cikin wannan rijiya tsawon shekara hamsin. " Koda jin wadannan tambayoyi sai aljanin ya tuntsire da dariya yace, "Yakai yarima lamras ka yi sani cewa ba zan taba cutar da kai ba, saboda idan ka bude ni a yau na fita tamkar ka ceci rayuwata ne gaba daya, dalili kuwa shine nan da wata uku wani gawurtaccen jarumin sarki, kuma matsfi zai zo nan birnin zai kashe mahaifinku ya kashe duk wani mahaluki dake cikin wannan birni. Babu makawa sai wannan abu ya faru, domin kaddara ce wacce ba za a iya canja taba, ammaida ka bude ni na fito daga cikin wannan rijiya nayi maka alkawari zan ceci rayuwarka data 'yar uwarka malifa, don haka ina mai shawartarka daka hanzarta karanta wannan addu'a dake jikin wannan littafi, domin wannan rijiya ta bude na fito tun yanzu na ceci rayuwarka da ta 'yar uwarka. Ina mai sanar da kai cewa sunana Raukaful barwasu. " Sa'dda aljani raukaful barwasu ya zo nan a zancensa sai naji zuciyata ta cigaba da bugawa da karfin, don haka sai na kasa karanta addu'ar don bude rijiyar. Kawai sai na budi baki nace, "Ya kai rauful barwasu kayi sani cewa ina bukatar lokaci domin na yi shawara da zuciyata, kafin na yanke shawarar bude ka, ko barinka." Koda gama fadin haka sai na ruga da gudu na bar bakin rijiyar. Har na yi nisa ina iya juyo kuka da rurin aljani raukaful barwasu cikin tsananin bakin ciki. A wannan dare da muka je bakin tsohuwar rijiyar muna wasan buya ni da 'yar uwata malifa sai kawai muka ga garin gaba daya ya hautsine, mutane sai guje-guje suke da iface-iface, gidaje kuwa sai rushewa suke suna zubewa kasa. Kasa ta kama girgiza tana darewa jama'a na fadawa cikinta tana binnesu. Wata irin gagarumar wuta ta rinka fesowa kasa daga sama tana kona komai da kowa. Kaico bala'I ba a samasa rana. Tun da nazo duniya ban taba ganin masifa ba da tashin hankali irin na wannan rana, kuma ban taba ganin yadda mutane suke mutuwa ba a zahiri sai sannan. Koda muka daga kanmu sama sai muka ga ashe wani narkeken aljani ne ke haddasa wannan masifa, amma. Bisa aljanin wani mutum ne mai kwarji sanye cikin shigar yaki. Nanfa muka firgice ainun nida 'yar uwata malifa muka buya a bayan rijiyar muna makyarkyata muka kasa barin wajen. Muna nan a labe muka ga aljanin ya sauko kasa ya dira shima mutumin sai ya sauko sannanne muka lura cewa mutanen su biyu ne sai kyakyata dariyar mugunta suke. A dai-dai wannan lokaci ne dakarun mahaifinmu suka rugo gare su aka ruguntsume da azababben yaki. Cikin abin da bai wuce rabin sa'a ba, wannan mutum mai kwarjini ya kashe gaba dayan dakarun garin. Ni kam ban taba ganin sadauki mai tsananin karfi da zafin nama ba tamkarsa. Lokacin da ya gama kashe dakarun sai birnin gaba daya yayi tsit tamkar wani abu mai rai bai taba wanzuwa ba a cikinsa. A lokacin ne ni da 'yar uwata malifa muka lura cewa gaba daya mutanen garin sun zama gawa, duk inda ka duba sai dai kaga jini na malala bisa kasa yana gudu tamkar teku ta balle, gawarwaki kuwa har yawo suke a kan ruwan jini. A daidai wannan lokaci ne muka hango gawar mahaifiyarmu ruwan jini ya tafi da ita izuwa wani gangare. Koda hango hakan sai malifa ta yunkura zata mike tsaye ta kurma ihu. Cikin zafin nama na ruko ta na rufe mata baki, kuma na gargade ta cewar kada ta kuskura ta sake yin wani motsi, domin tana yi wadannan mugayen mutane zasu ganmu su hallaka mu. Nan take muka ji wannan mutum mai kwarjini ya fara kwalawa mahaifinmu kira yana cewa, "ina kake ya kai wannan sarki, ka fito fili mana muyi arba. Shin baka ga yadda na ruguje birnin kaba? Shin baka ga yadda na maida jama'arka gawarwaki ba ababan takawa ta, ko kuwa bakaga yadda nayi wa birninku ado da jini ba? Hakika kai mai tsoron mutuwa ne, kuma mai son duniya tunda har ka buya kaki fitowa. Ka sani cewa nine sarki hasanul mauzur dodon dukkanin sarakunan musulmai na duniya. Da sannu sai na karar da dukkanin ire- irenku a duniya, domin na tsane ku, kuma na tsani addininku. Gani tare da sarki hambaru wanda ka aikawa wasikar ta yin addininka a kan idan yaki karba zaka yake shi ka rushe mulkinsa. To yau ga shi kai naka mulkinka ya baje ko a tarihi nan gaba baza tuna da kai ba. " Gama fadin hakan keda wuya sai ga mahaifinmu ya fito daga cikin karkashin kasa yana mai daka tsalle sama tamkar da kugiya aka Janyo shi kuma yana mai kwala kabbara. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin mahaifinmu da sarki hasanul mauzur. Gashi dai kowannansu na ruke da takobi amma an rasa wanda zai fara tunkarar wani saboda shakkar juna. Tabbas shi ma mahaifinmu gwarzon sadauki ne mai matukar kwarjini kuma dama labarin jarumtakarsa ya bazu a ko'ina a duniya a wannan zamani. Mahaifinmu ya dubi yadda birninsa ya ruguje da kuma yadda jama'arsa suka zama gawarwaki sai takaici ya rufe shi idanunsa suka ciko da kwallar bakin ciki, sannan ya dubi sarki hasanul mauzur da sarki hambaru cikin tsananin fushi yace, "Yaku wadannan kafirai kuma azzaluman sarakuna kuyi sani cewa in ba don kun kawo mana harin sumame ba, da baku isa kuyi mana wannan mummunar barna ba. Lokacin dakuka iso ina kwance a turakata ina hutawa kawai sai sai naji gini ya ruguzo mini a ka, kasa kuma ta dare na fada cikinta ta binneni na suma. Lokacin dana farfado ne na Jiyo muryar dayanku yana kuri da cika baki. Tabbas kun yi mini barna da. Koda na kashe ku ba zan huce takaici ba ina son ku sani cewa ko da kun kashe ni yanzu bani da nadama ko sauran takaici, domin zan bi sauran 'yan uwana ne izuwa gidan gaskiya, wato gidan aljanna, gidan da ubangijin musulunci ya tanadarwa bayinsa masu biyayya a gare shi, ku kuwa gidan wuta mai radadi za a jefa ku." Koda mahaifina yazo nan a zancensa sai sarki hasanul mauzur da sarki hambaru suka bushe da dariya, sannan sarki hasanul mauzur yace, "Ai sai mu ga yadda za ka tsira da rayuwarka a yau. " GODIYA mara misaltuwa agareku bisa addu'o'in ku agareni ubangiJi allah yabar zumunci. «««TARWATSA MAZA-3 TYPE E »»» Kafin ya gama rufe bakinsa tuni mahaifina ya daga takobinsa sama ya wurgota izuwa kan sarki hambaru. Kafin hasanul mauzur yayi wani yunkuri na kade takobin tuni ta cake acikin tumbin sarki hambaru nan take yai tsalle sam yana mai kwala ihu sannan ya fado kasa matacce. Koda ganin abin daya faru sai sarki hasanul mauzur ya fusata ainun yayi kukan kura ya ruga izuwa kan mahaifinmu shi ma sai ya tare shi suka kaure da azabebben yaki. Duk wannan abu dake faruwa ni da yar uwata malifa mun labe a bayan wannan tsohuwar rijiya muna kallo. Kuma muna kuka. Sarki hasanul mauzur da mahaifinmu suka cigaba da kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta mai ban al ajabi domin babu alamar cewa dayansu zai gaji sai da suka shafe saa uku cur suna gumurzu dayansu bai sami nasarar komai ba har ya zamana cewa takubbansu sun dakushe ba su da sauran kaifi koda ganin haka sai sarki hasanul mauzur ya fusata ainun yai jifa da takobin hannunsa ya dunkule hannayensa biyu gami da gyara tsayuwa yana mai nuni dasu gwada yar kashi. Da ganin haka sai shi ma mahaIfinmu yayi jifa da tasa takobin ya dunkule hannayensa. Lokaci guda duk su biyun suka ruga ga juna suna haduwa kuwa suka hau naushi da bugun juna hannu da kafa sai da rabin saa ta shafe a haka suna tsaye dayansu baije kasa ba kuma gashi sun hadawa juna jini da majina sai da suka kwamarzu ainun har ta kai cewa sun far layi da tangadi. Tamkar wadanda suka sha giya suka bugu amma saboda naci basu fasa bugun juna ba a hakan. Adaidai wannan lokaci ne muka jiyo muryar aljani raukaful barwasu daga cikin wannan rijiya yace. ” Yakai yarima lamras maza ka fiddo wannan karamin littafi dake jikinka ka karanta wannan addu a dake jikin sa domin wannan rijiya ta bude na fito na ceci rayuwarku data mahaifinku idan kuwa kaki nan da rabin saa sarki hasanulmauzur zai kashe mahaifinku. Sannan kuma yazo ya kashe ku. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama yar uwata malifa tace. ” Au dama ka san yadda za a yi abude wannan rijiya tuntuni. Amma baka gaya mini ba ? Maza ka bude ta domin ka ceci rayuwarmu damuwa na dubi malifa nace. ” Yake yar uwata kiyi sani cewa su kafiran aljanu basu da amana ba lallai bane aljani rauful barwas ya cika alkawari a gare muba. Bayan mun bude shi ya. ” Caraf sai raukaful barwasu ya tari numfashina ay ce. ” Na rantse da darajar shekaru hamsin dana yi acikin wannan rijiya ba zan ci amanar kuba kayi sauri ka bude nina fito tun gabannin lokaci yakure. ” Koda jin haka sai nayi sauri na fiddo wannan mitsitsin littafi daga cikin rigata na bude shi na karanta wannan addu'a dake cikinsa kamar yadda na ji tsoho sariku ya karantata. Faruwar hakan keda wuya sai mukaji karar budewar murfin rijiyar tamkar ana zare manyan sakatu na kofar shigowa birninmu. Murfin na gama budewa muka ji wata irin iska mai karfi tayi fitar burgu daga cikin rijiyar, nan take naga an suri 'yar uwata malifa an jefa ta cikin wannan rijiya mai tsananin zurfi da duhu, malifa ta kwalla ihu a lokacin dana yunkura dominna daka tsalle nabi ta cikin rijiyar. Amma sai naga murfin rijiyar ya dada rufewa. Nan take aka fisge wannan mitsitsin littafi dake hannuna sai ga aljani raukaful barwasu ya bayyana a gabana yana kyalkyala dariyar mugunta cikin tsananin fushi na dube shi nace, "amma kaci amana ta ka cuce ni saboda me zaka jefa 'yar uwata cikin wannan rijiya ka raba ni da ita? Ni kam gwara ka bude rijiyar ka jefa ni ciki na hallaka tare da 'yar uwata. " Koda jin wannan batu sai aljani raukaful barwasu ya kyalkyale da dariyar mugunta yace, "kai yaro ai ni bazan kashe kaba da hannuna tunda kaine ka fito dani daga cikin wannan rijiya, wacce na shekara hamsin a cikinta. Ka sani cewa na jefa 'yar uwarka cikin wannan rijiya ne, domin na dauki fansar abin da kakanku yayi mini. Kakanku ne ya kashe mini iyayena da duk zuri'ata nima kuma nayi alkawari sai na kawar da duk zuri'arku komai dadewa. Yanzu zan taimakawa sarki hasanul mauzur ya kashe mahaifinku kai kuma zan dauke ka daga nan na kaika can wata nahiya wacce dare da rana a cikin yaki suke. A can zaka cigaba da rayuwarka har a kashe ka abanza a wajen yaki. Ita kuwa 'yar uwarka malifa sai ta shekara hamsin a cikin wannan rijiya kamar yadda nima na shekara hamsin ba tare data mutuba, domin nizan dunga ciyar da ita da shayar da ita a ciki, domin tayi zaman kurkuku dana yi sannan na dawo na hallakata. Ka sani cewa babu mahalukin daya isa ya fito da ita daga cikin wannan rijia face yazo da wannan littafi na hannuna ya karanta addu'ar dake cikinsa. Daga yau zan boye wannan littafi a inda babu wanda ya isa yaje ya daukoshi." Koda gama fadin hakan sai aljani raukaful barwasu ya rikide ya zama mashi ya cilla da gudu ya soki mahaifinmu a kirji. Take mahaifinmu ya sulale kasa yana mai karanta kalmar shahada ya rasu koda ganin abin da ya faru sai na kwala ihu na fashe da matsanancin kuka. A sannan ne mashin ya zarr kansa daga cikin kirjin mahaifinmu ya sake rikida ya zama aljani raukaful barwasu ya tsaya a gaban sarki hasanul mauzur yace da shi, "Gaisheka ya kai jarumin jarumai, kayi sani cewa ni da kai duk muna kan tafarki guda na kawar da abokan gabarmu, don haka daga yau zan zamo mai taimaka maka, amma baza ka sake ganina ba sai nan da wadansu shekaru bayan 'yarka gimbiya sulaira ta girma ta zama cikakkiyar budurwa." Koda gama fadin haka, sai aljani raukaful barwasu ya sure ni yayi sama dani. Nan take na bude baki da nufin nayi addu'a amma sai ya shafe ni da fukafukinsa na suma. Sa'adda na farfado na tsinci kaina ne acikin wata alkarya ana ta gwabza yaki. Koda na mike tsaye sai na zabi bangare guda na tayasu yakin. Bisa sa'a kuwa bangaren da nazaba ne suka yi nasara, kuma a garinsu ake yakin haka na cigaba da zama da wadannan mutane har na girma na zama, jarumin gaske mai tarwatsa maza. Duk tsawon shekarun zamana da wadannan mutane da tunanin 'yar uwata malifa atare dani, kullum ina rogon alllah a kan ya bayyana mini inda wannan littafi yake na daukeshi na koma birnin mu na baitul nur inda wannan rijiya take na fito da 'yar uwata. A wannan gari dana yi rayuwa kusan a karshen kowanne wata sai an fita yaki. Bisa wannan daliline. Wata rana muka je yaki a cikin jiragen ruwa a teku aka ragargaza mutanen da jiragen su nima aka harbeni da kibiya na suma akan allon jirgi shi ne makasudin da igiyar ruwa ta janye ni sarki mushlik ya tsince ni a birninsa sa'adda yaje bayan gari ya zauna a gaban korama, har ya ceci rayuwat ni kuma nayi alkawarin share masa hawaye ta hanyar juyewa izuwa kamanninka na shiga wannan gasa ta neman auren gimbiya sulaira. " Sa'adda sadauki lamras yazo nan a labarinsa sai yarima zamir ya cika da tsananin mamaki yayi shiru yana jinjina al'amarin har izuwa lokaci mai tsawo, sannan yace, "Ni kuwa zan ga yarda zaka iya daukar fansa a kan sarki hasanul mauzur, sannan ka sami damar zuwa ka fito da 'yar uwarka daga cikin wannan rijiya." Lamras yace, "Tabbas kuwa zaka gani, domin babu abin da zai gagari ubangijin musulunci. " SHIN SADAUKI LAMRAS ZAI DAUKI FANSA A KAN SARKI HASANUL MAUZUR? WAYE ZAI CI GASAR AUREN GIMBIYA SULAIRA? Muhadu a TARWATSA MAZA LITTAFINA KARSHE 4 DONJIN YADDA ZATA KASANCE ««« TARWATSA MAZA-4 TYPE A »»» Kashe gari da aka dawo fadar sarki hasanul mauzur domin ci gaba da gasar neman auren gimbiya sulaira sai fadar ta sake cika ta batse fiye da ranar farko zaratan samarin gasa guda casa'in suka tsaya a tsakiyar filin, kowannanasu a cikin shirin yaki mai kwarjini da ban tsoro. Sai bayan shudewar rabin sa'a da taruwar jama'a sannan sarki hasanul mauzur da gimbiya sulaira suka fito daga cikin gidan sarauta ana yi musu kade- kade da bushe-bushe irin nasu na masu sarauta. Har sai da suka zauna a kan karagar mulki, sannan aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. A sannan ne sarki hasanul mauzur ya mike tsaye yayi gaisuwa ga jama'arsa da sauran baki wadanda suka halarci wannan gasa. Sarki yace, "Ya ku jama'ar dake cikin wannan fada ina mai sanar daku cewa yanzu ne za a ci gaba da wannan gasa ta neman auren 'yata gimbiya sulaira kuma wadannan ragowar jarumai guda casa'in da suka yi saura lallai a yau ne zamu fitar da zakara acikinsu wanda shine zai fafata yaki dani, idan har ya sami nasarar kaini kas, lallai shine zai zamo mijin 'yata gimbiya sulaira. " Koda gama fadin haka sai sarki ya koma kan karagarsa ya zauna da nufin ya bayar da umarnin ci gaba da gasa. A dai-dai wannan lokaci ne aka ji wata gagarumar iska ta taso daga sama. Nan da nan kowa ya daga kansa sama, ai kuwa sai aka yi arba da wani narkeken aljani mai girman gaske dauke da wani jarumi akansa mai matukar kwarjini wanda ya kasance dogo kuma kakkaura. Kallo daya zaka yi masa kasan cew yacika jarumin gaske. Tun daga nesa sarki hasanul mauzur ya kurawa aljanin idanu, bai damu da jarumin dake kansa ba. Ba komai ne yasa ya kura masa ido ba face yana ganin cewa lallai sun taba. Haduwa, amma sai ya kasa tuno a inda suka hadun da kuma lokacin da suka hadun. Gaba dayan jama'ar dake fadar kuwa sai da suka tsorata ainun da ganin wannan aljani, wasu ma ji suka yi kamar su tashi su tsere da gudu ganin cewa sarki hasanul mauzur na nan ne yasa basu firgice ba sun gudun. Nan take aljanin ya sauko kasa ya dira a kusa da wadannan jaruman gasa casa'in. Mutum daya ne daga cikin jaruman gasar bai firgita da ganin wannan bakon jarumi daya. Ba kowa bane face sadauki lamras wanda ke cikin siffar yarima zamir. Shi kuwa yarima zamir wanda ke zaune a cikin 'yan kallo ya boye fuskarsa a cikin rawani koda yaga wannan bakon jarumi ya zo sai shi ma hankalinsa ya dugunzuma domin yana ganin cewa sadauki lamras ba zai ci wannan gasa ba. Wadda ake yin gasar dominta kuwa wato gimbiy sulaira tana hango wannan bakon jarumi sai ita ma jikinta ya ba ta cewa lallai shine zai zama zakaran wannan gasa. Sarki hasanul mauzur ya taso daga kan karagarsa ya shigo cikin filin gasar ya iso har gaban wannan bakon jarumi ya dubi aljanin daya kawo shi cikin murmushi yace. "Yakai wannan bako ina so ka tunatar dani inda muka taba haduwa. Hakika wannan fuska taka sananniya ce." Koda jin wannan tambaya sai aljanin ya bushe da dariya yace, "hakika na san cewa abu ne mawuyaci ka iya tunawa dani farat daya. Ya kai jarumin sarkin sarakuna ina mai tunatar da kai cewa nine aljani raukaful barwasu wanda ya shekara hamsin a cikin rijiyar sarkin birnin baitul nur nine wanda na taimaka maka sa'ad da kake yaki da sarkin birnin baitul nur na zama mashi na cake shi a kirji ya mutu, sannan na dauke dansa yarima lamras naje na jefar da shi a can wata nashiya daban da ake yaki inda tuni ya hallaka. Wannan jarumi da kaga ni tare dani ba wani bane face sadauki yarima Hizairu dan marigayi sarki hambaru ibn kamsus sarkin da yabaka kwangilar kashe sarkin baitul nur. Shi ma yanzu yazo ne domin ya shiga wannan gasa ta neman auren 'yarka. Ya kai wannan sarki kayi sani cewa dama na gaya maka cewa baza ka sake ganina ba sai a ranar gasar neman auren 'yarka, ga shi kuwa zancena ya tabbata. Kayi sani cewa tun bayan rabuwar mu wato bayan mutuwar abokinka babban attajiri hambaru sai na koma kasarsa na dauke dansa na kaishi can garinmu na aljanu aka yi ta koya masa yaki tun yana da shekara bakwai a duniya har ya girma ya kai saurayi kuma na tsuma shi a cikin tsumin tsafi ba don komai ba sai domin idan ya girma yaci gaba da yakar abokan gabarmu ma'abota addinin musulunci har sai ya shafe su a doron kasa ya zamana cewa babu sauran irinsu. " Sa'adda aljani Raukaful barwasu yazo nan a jawabinsa sai sarki hasanul mauzur ya cika da tsananin farinciki ya bude hannayensa yana mai yi wa sadauki yarima hizairu murmushi. Koda ganin haka sai yarima Hizairu ya sauko daga kan aljani raukaful barwasu ya rungume sarki hasanul mauzur cikin matukar farin ciki kamar wanda ya ga dan uwansa wanda ya dade bai sadu da shiba. Sarki Hasanul mauzur yayi wa yarima Hizairu rada a kunne yace, "Kaine jarumin daya fi dacewa ya zama mijin 'yata tunda kai dan sarki ne wanda ba a taba yin kamarsa ba a karfin arziki da girman kasa. Duk da cewa banga irin jarumtarkaba na san zaka yi abin al'ajabi, domin kuwa biri yayi kama da mutum. Hakika nayi matukar bakin ciki bisa rashin mahaifinka amma ina yi maka fatan nasara a wannan gasa domin ina kaunarka fiye da dukkan sauran wadancan samarin gasa. Yanzu sai kaje ka shiga cikin 'yan gasar kuma kayi kokari ka tarwatsa su su duka ka zamo zakara domin ka kafsa dani ka kaini kasa. Ka sani cewa kokarin ka ne fa zai sa ka kai ga nasara, saboda ba zan daga maka kafaba tunda idan mana daga maka kafar sai jama'a sun gane." Da jin wannan batu sai yarima Hizairu yayi murmushi yace, "Ya kai wannan sarki ina tabbatar maka da cewa lallai zan baka mamaki domin yadda duk kake tsammanina nafi nan. Ina mai sanar da kai cewa daga cikin wadannan jaruman gasa akwai wani dan babban makiyinka wanda yake son sai yaga bayanka a cikin wannan gasa. Na yi iya kokarina a cikin binciken tsafi domin na gano ko waye na kasa, amma na san cewa yanzu ne zamu ga ko wane kuma nine zan kawar dashi. " Koda gama wannan jawabi sai yarima hizairu ya tunkari inda jaruman gasa suke. Koda ya durfafi inda suke sai ya ga suna daddarewa suna ja da baya domin gani suke yarima hizairu babu mai iya hango tsakiyar kansa, idan kuwa yana taka kasa sai kaji kasar na rawa kamar kowa zai rufta cikinta saboda nauyinsa. Hakika siffar yarima Hizairu irin ta mutanen farko ce, bambancinsa dasu kadan ne. Koda yarima hizairu ya iso daidai inda jaruman gasar suke sai ya ga saura mutum daya jal a gabansa wanda ko aamar razana babu a fuskarsa saurayi ne kyakykyawa mai kwarjini da kirar sadaukantaka. Ba wani bane face yarima lamras yayin da sadauki hizairu yazo daf da sadauki lamras ya tsaya sai suka zamo tamkar bera kankani a gaban katuwar kyanwa saboda banbancin girmansu. Nan fa suka kurawa juna ido, Hizairu ya murtuke fuska shikuwa lamras sai ya kama yi masa murmushi. A wannan lokaci tuni sarki hasanul mauzur ya koma kan karagarsa ya zauna. Koda ya hango lamras shi kadai a gaban hizairu sai ya kura masa ido yana kokarin tuno inda ya taba ganin mai irin kamanninsa amma sai ya kasa tunowa. Gimbiya sulaira ta dubi sarki cikin alamun tashin hankali tace. "Ya abbana shin ka sanko su waye wadancan jarumai biyu da suka tsaya daf da junansu ? Naga dazu ka je ka yi magana da ajanin daya kawo dayansu" Koda jin wannan tambaya sai sarki hasanul mauzur yayi murmushi yace, "Na san su, kada ki damu zan yi miki bayaninsu nan gaba. " Gama fadin hakan keda wuya sai sarki hasanul mauzur ya dubi gaba dayan jaruman gasa ya daga musu hannu yana mai yi musu inkiya da su kaure da fada, domin a sami zakara guda daya a cikinsu, wanda zai zama gwani nan

Please Login or Register in order to submit comment