Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saurayi mai kwarjini da haiba. " Koda jin haka sai saurayin yayi murmushi, kyawunsa ya karu ainun har gimbiya shulaira taji nan take ya burgeta. Sai yace, Ni sunana yarima ZAMIR, dan sarki mushlik na birnin dumar." Koda jin wannan batu sai sarki hasanul mauzur ya cika da tsananin mamaki, kawai sai ya murtuke fuska yace, "kai yaro karya kake yi ba kai bane yarima zamir, domin ina da labarin cewa yarima zamir rago ne, bai kasance jarumi ba, asalima ko takobi bai taba rikewa ba, bai taba zuwa yaki ba, kuma bai damu da komai ba a duniya face wasa a cikin yara. Ya za a yi yanzu ka zo kace damu kaine yarima zamir?" Saurayin yayi murmushi yace, "Ya kai wannan sarki mai daraja hakika duk abubuwan da ka fada gaskiyane, to amma ka sani cewa rayuwar duniya juyi-juyi ce komai na iya faruwa. Ni yarima zamir na karbi addinin musulunci ba tare da mahaifina ya sani ba, kuma ubangijin musulunci ya sauya mini komai nawa na zama gagarumin jarumi, don haka duk abin da zan yi a yanzu bai kamata ayi mamaki ba." Koda jin wannan batu sai hankalin kowa da ke fadar ya dugunzuma, kuma aka cika da tsananin mamaki, domin wannan shine karo na farko da aka taba samun ma'abocin addinin musulunci ya shigo cikin birnin sharas har ya bayyana kansa, saboda tsananin tsoron sarki Hasanul mauzur da ake yi da kuma sanin tsananin kiyayyarsa akan ko wanne addini, face na bautar gunki hurzas. ««« TARWATSA MAZA-3 TYPE B »»» Tun lokacin da sarki hasanul mauzur yaji yarima zamir yace ya karbi addinin musulinci sai idanunsa suka kada sukayi jawur zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone fuskarsa kuwa kasa saboda tsananin fushi al amarin daya tsorata kawa kenan a wajen amma ban da shi jarumi zamir din. Ita kanta gimbiya sulaira bata san sa adda jikinta ya kama tsuma ba domin bata taba ganin mahaifinta acikin wannan yanayi ba nan fa sarki hasanul mauzur ya kurawa jarumi zamir idanu yana harararsa kawai ya kasa cewa komai da shi. Gashi dai yarima zamir ya riga ya biya sadkin fara wannan gasa babu damar ahana yin gasar. Daga can sai sarki hasanul mauzur ya kauda kai ga barin kallon yarima zamir ya kalli jarumi na biyu yace kai kuma waje? Jarumin ya risina cikin biyayya yace. ” Ni sunana jarumi haslim dan waziri sharbul na birnin dumar. ” Koda jin haka sai sarki hasanul mauzur yayi dan guntun murmushi sannan yace. ” Yakai haslim shin wannan jarumi na farko da gaske shine yarima zamir. Dan sarkinku?“ Hasalim yakalli zamir sannan ya juya ga sarki hasanul mauzur yace. “ Ya shugabana a zahiri dai wannan al ajabi dana ganshi bashi da jarumtaka ko kadan. “ Kodq jin haka sai sarki hasanul mauzurya jinjina kai yace acikin zuciyarsa. “ Dole ne nayi bincike na gano gaskiyar wannan al amari. “ Sarki hasanul mauzur ya dubi jarumi na uku yace. “ Kai kuma waye ? Jarumin na uku ya risina yace. ”Sunana yarima himlar dan sarki huzairu na birnin kushul. ”. Sarki hasanul mauzur yayi murmushi ya dubi jarumi na hudu yace. ” Kai kuma fa ?” Jarumi yace. “ Ni sunana sadauki juhaisu daga kasar taksur. “Nan take sarki hasanul mauzur yakoma kan karagar mulkinsa ya zauna fuskarsa cike da yanayin damuwa. Don haka sai gimbiya sulaira ta dafa hannunsa tace. “ Ya kai abbana ina dalilin damuwarka bisa jin cewa yarima zamir ya kasance ma abocin addinin musulinci ? ” Koda jin wannan tambaya sai sarki hasanul mauzur yayi ajiyar zuciya, sannan yace, "'Yake 'yata kiyi sani cewa na san halin sarki mushlik na birnin dumar fiye da shekara talatin baya, mutum ne mai ra'ayi irin nawa ina nufin ya tsani kowanne addini face wanda yayi imani dashi babu yadda za a yi a ce dan cikinsa ya karbi addinin musulunci ba tare da ya sani ba, idan kuwa har ya sani to da hannunsa zai yanka yarima zamir, duk da cewa yana tsananin sonsa. Lallai sai na gana da gunki hurzas bisa wannan al'amari, domin su ma'abota addinin musulunci suna da karfin sihiri fiye da namu, zai iya amfani da karfin sihiri fiye da namu, zai iya amfani da karfin sihirin ya sami nasarar wannan gasa ya zamo mijinki. " Cikin mamaki gimbiya shulaira ta dubi sarki tace, "ya kai abbana yanzu ashe har karfin sihirinsu ya fi namu kenan?" Sarki hasanul mauzur ya bata rai yace yace, "ya za a yi karfin sihirinsu yafi namu, alhalin addininmu ne gaba da dukkan sauran addinai. Ai ina tabbatar miki da cewa idan har na kai kukana ga ubangiji hurzas sai na gagari duk wadannan jarumai kamar yadda ya bani sa'a na keta dazuzzuka uku na samo abin dana fita nema." Koda jin wannan batu sai hankalin gimbiya lusaira ya dugunzuma ta dubi sarki cikin tsananin damuwa kamar zata yi kuka tace, "To yanzu idan ka gagari dukkan wadannan jarumai menene makomata?" Da jin wannan tambaya sai jikin sarki yayi sanyi, kuma ya kamu da tausayin sulaira don haka sai ya dafa hannunta yayi murmushi mai taushi a gareta yace, "lallai zaki yi aure yake 'yata, kuma zaki auri jarumin da babu kamarsa a wannan zamani, domin nayi imani cewa duk jarumin da ya kai ni kas ya zama cikakken sarkin sadaukai na wannan zamani. " Koda gama fadin haka sai sarki hasanul mauzur ya sake mikewa tsaye ya dubi jaruman gasar gaba dayansu su darin, sannan ya nuna daya daga cikinsu yace, "Za mu fara gasa ta kanka yanzu sai ka farwa 'yan uwanka su duka ka tarwatsasu mu gani. Idan har ka yi nasara shi kenan ka haye mataki na biyu na wannan gasa saura matakin karshe." Shi dai wannan jarumi da sarki ya fara zaba ya kasance garjejen kato, ga tsawo,ga kauri, a gaba dayan dakarun babu mai girmansa. Koda jarumin yaji sarki ya bashi wannan umarni sai ya zare takobi ya kwarara uban ihu ya ruga izuwa kan sauran jaruman guda casa'in da tara, suma sai suka yi kukan kura gaba dayansu suka yi masa kawanya suka rufe shi da sara da suka kamar zasu cinyeshi danye. Ko daya daga cikinsu bai sami damar kaiwa kas ba. Cikin abin da bai wuce dakika uku ba, aka dankara masa sara goma sha daya ajikinsa, duk da cewa yana da matukar zafin naman kare hari da juriya. Nan take jiri ya debe shi ya kifa kasa. Yana faduwa sai jaruman suka ja da baya suka buda hanya dakaru suka rugo da gudu suka dauke garjejen katon suka fita da shi daga filin gasar, domin aje ayi masa magani, kuma a ceto rayuwarsa. Dauke shi keda wuya sai sarki hasanul mauzur ya sake nuna wani jarumin shi ma aka rufar masa. Kafin cikar dakika biyar shi ma ya baje akasa sumamme. haka dai aka cigaba da wannan gasa har aka kai mutum goma kas ya zamana saura mutum casa'in kacal a cikin gasar. A sannan ne sarki ya bada umarnin a tashi daga gasar sai gobe da safe a dawo a cigaba. Koda gama fadin haka sai sarki da gimbiya lusaira suka mike suka shiga cikin gidan sarauta, sannan fadar ta watse kowa ya kama gabansa, suma bakin jarumai suka tafi izuwa masaukinsu. Lokacin da yarima zamir ya shiga cikin masaukinsa wato gidan da ya sauka ya shige cikin daki sai ga yarima zamir na gaskiya a tsaye yana kaikawo cikin tsananin damuwa. Da ganinsa sai zamir ya taho gare shi ya ruke kafadunsa cikin fishi yace, "Ya kai sadauki lamras me yasa tun farko baka shaida min cewa kai musulmi bane, har ka juye izuwa kamannina kazo ka shiga wannan gasa? Shin baka tunanin cewa ka yaudari mahaifina kaci amanarsa tunda a rayuwarsa babu abin da ya tsana sama da addininku na musulunci ina son na san yadda aka yi ka iya juyewa izuwa kamannina alhalin naji ance ku musulmai ba kwa yin tsafi?" Sa'adda sadauki lamras yaji wadannan tambayoyi sai yayi murmushi yace, "ya kai wannan dan sarki kayi sani cewa nashiga wannan gasa ne ba don na share hawayen mahaifinka ba ko dan na saka masa, bisa ceton rayuwata da yayi ba sa'adda ya tsince ni a cikin kogi an harbeni da kibiya, sai domin na sami damar da zan tallata addinina a wannan na shiya taku, kuma na sami damar daukar fansa akan sarki hasanul mauzur ina tabbatar maka da cewa ni ba na tsafi, amma ina da wata addu'a ta musamman, wacce duk irin siffar da nake son na zama indai na karantata sai na juye izuwa wannan siffar. Wannan yarda ce ta ubangijina kawai ba sihiri ko tsafi ba. " Sa'adda sadauki lamras yazo nan a zancensa sai jikin yarima zamir yayi sanyi matuka ya sunkui da kansa kas yana tunani. Daga can kuma sai ya dago kai ya dubi sadauki lamras yace, "To wai shin meye amfanin tahowa dani wannan gasar daka yi? Kasani cewa ni a rayuwata ban taba yin soyayyaba, kuma bani da burin yin aure, fatana kawai na gama rayuwat a cikin wasanni tamkar karamin yaro, domin nayi imani cewa idan nasa kaina a cikin son rayuwar duniya dole ne wata rana raina ya baci. Ni kuwa a sanina tun dana zo duniya ban taba yin bakin ciki ba dai-dai da rana daya. Yanzu idan kaci wannan gasa waye zai auri gimbiya lusaira tsakanin ni da kai?" Sadauki lamras yayi dariya yace, "Tabbas kaine zaka aure ta. Tunda da kamanninka nake wannan gasa bada kamanninaba. " Yarima zamir ya bushe da dariya sannan ya ce, "Amma na raina hangen nesanka. Shin ka manta ne cewa kana son kakashe sarki hasanul mauzur ne? Tayaya kake tsammanin gimbiya lusaira zata yarda ta aureni alhalin na kashe mahaifinta a filin gasa?" Lamras yace, "kar ka damu bayan na kashe sarki hasanul mauzur zan juye azuwa ainahin kamannina a gaban lusaira inyaso sai ka fito fili a sannan. Ina tabbatar maka da cewa ita kadai ce zata iya ganinna kuma ta ganka a wannan lokaci, kuma a sannanne zan gaya mata dalilin da yasa na kashe mahaifinta. Ka sani cewa wanzuwar sarki hasanul mauzur a wannan nahiya shine abinda ya hana kafuwar addinina. Daga ranar da sarki hasanul mauzur ya mutu, musulunci zai yadu a ko ina, kai ma kanka sai ka musulinta kuma a sannan ne rayuwarka zata sauya gaba daya ka kawar da dukkan ra'ayinka na rayuwa, har kaso kayi aure. " Koda jin wannan batu sai yarima zamir ya bushe da dariya, sannan yace, "Ai duk wannan jawabin daka yi mini a yanzu jinsa nake kamar ta tsuniya, domin abu ne wanda ba zai yiwuba. Ni na san cewa kai baka isa ka iya kashe sarki hasanul mauzur ba domin a gaba daya wannan nahiya babu mai karfin damtsensa kuma babu mai karfin sihirinsa. Ni yanzu abu biyu nake son na sani a dangane da kai. Abu na farko ina son na san abinda sarki hasanul mauzur yayi maka har kake son ka dauki fansa a kansa. A bu na biyu waye ya harbeka da kibiya har ka fada cikin teku bisa allon jirgin, ruwa ya janyo ka izuwa birninmu?" Koda jin wadannan tambayoyi sai idanun sadauki lamras suka ciko da kwalla, nan da nan hawaye yafara sartu bisa kumatunsa yayi shiru tsawon 'yan dakiku kadan baice komai ba. Daga can sai ya dago kai ya dubi yarima zamir yace, "Yakai wannan dan sarki kayi sani cewa ka tambaye ni labari mai tsawo, amma zan yi kokari na gajarce maka shi cikin kankanin lokaci.............. ««« TARWATSA MAZA-3 TYPE C »»» Nidai asalina na fito ne daga wata kasa da ake kira BAITUL NUR. Mahaifina ya kasance shugaba kuma babban malami na addinin musulunci, kuma jarumin gaske mai tarwatsa maza, wanda ya zamo dodon kafirai dake makwabtaka da mu gaba daya, gaba dayan mutanen birninmu basu fi mutum dubu ashirin ba, amma saboda sun kasance zakwakuran mayaka masu dakakkiyar zuciya gami da imani da addinin musulunci sai ya zamana cewa sun gagari dukkanin kasashen dake kusa dasu. Cikin lumana mahaifina ya dunga aika wasiku izuwa ga sauran kasashen na shiyar yana yi musu tallan addinin musulunci. Duk sarkin daya karbi tayin addini shi kenan, wanda duk yaki kuwa sai a yake shi a kafa daular musulunci da karfin tsiya. Sannu a hankali mahaifina yayi ta samun nasara har ya zamana cewa saura kasa guda daya jal ta rage a nahiyar wadda ba ta karbi musulunci ba, ana kiranta da suna darul husuk. A gaba daya nashiyarmu babu wata kasa mai girma da yawan al'umma tamkar birnin darul husuk, kuma birni ne wanda mutane suka shagala ainun kowa yana yin abin da yaga dama. A kalla akwai addinai iri-iri a kasar sama da guda dari. Sarkin dake mulkin birnin darul husul wani kasaitaccen attajiri ne wanda babu mai tarin dukiyarsa a gaba daya nashiyar, kuma ya kasance babban azzalumi wanda bai san tausayi ba, ko adalci. Duk irin laifin da mutum ya aikata indai zai bashi kudi to kuwa zai yafe masa. A takaice dai babu abin da yake gabansa sama da abin duniya, wato dukiYa. Shi dai wannan sarki ana kirtansa da suna hambaru ibin kamsus. Lokacin da sarki hambaru yaga mahaifina ya ci dukkanin kasashen dake nashiyar saura kasarsa kadai sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yarasa abin da ke masa dadi a duniya, domin da dai ya rasa karagarsa da dumbin dukiyar da ya tara. Da irin jin dadin da yakeyi gwara ya rasa rayuwarsa. Bisa wannan dalili ne ya tara dukkan bokayensa ya umarcesu dasuyi masa bincike bisa hanyar da zai iya bi ya hallaka sarkin birnin baitul nur ya shafe jama'arsa gaba daya. A ranar da ya umarci bokayen nasa dayin wannan aiki ne wasikar mahaifina ta riske shi, domin yi masa tayin addinin musulunci cikin yaudara sarki hambaru ya tarbi manzon da mahaifina ya aiko yasa aka yi masa goma ta arziki kuma yasa aka rubuta amsar wasikar cewa a shirye yake ya karbi addinin musulunci, amma yana neman aba shi alfarmar kwana goma ya aika da wasikar mahaifina ga sauran biranen dake kasarsa. Dama bokayen sun tabbatar masa da cewa a cikin kwana uku rak zasu zo masa da mafita. Kwana uku na cika sarkin bokayen nasa mai suna markuf bin sardus yazo gare shi ya fadi ya kwashi gaisuwa, sannan yace, "ya shugabana mun yi bincike mun gano cewa duk fadin duniyar nan babu wanda zai iya yi maka maganin sharrin wannan sarkin musulmai face wani sarki guda daya wanda ake kira hasanul mauzur wanda ke can wata nashiya dake yammacin taka. Daga nan zuwa can kasarsa wadda ake kira birnin sharas tafiya ce ta wata shida bisa rakumi ko doki ba tare da yada zango, amma ina da wani hadimin aljani wanda zai iya zuwa can din a cikin sa'a shida kacal ana kiransa da suna marzil darkub. Ya shugabana kayi sani cewa sarki hasanul mauzur gawurtaccen attajirine, amma dukiyarka ta linka tashi sau dubu arba'in, lallai zai amince ya yi maka wannan aiki. " Koda jin wannan batu sai sarki hambaru ya cika da tsananin farin ciki ya dubi boka markuf yace, "tabbas ba zan yi kyashin biyan wannan kudi ba, tunda ina son na tsira da mutuncina, kuma ni da kaina zan yi wannan tafiya, saboda haka ina son gobe da sassafe kazo mini da wannan hadimin naka wato aljani marhazil darkub. " Boka markuf yace, "an gama ya shugabana. " Kashe gari kuwa da asuba boka markuf yazo fadar sarki hambaru tare da aljani marhazil darkub dama tuni sarki hambaru ya tanadi jakunkunan kudi da za'a kaiwa sarki hasanul mauzur. Batare da bata lokaci ba aka loda jakunkunan kudin akan marhazu darkub, sannan shi ma hambaru ya hau kansa ya zauna. Nan take marhazil darkib ya bude fukafukansa ya tashi sama suka luluka a cikin gajimare suna falfala matsanancin gudu. Tun da sarki hambaru yazo duniya bai taba ganin wata halitta mai karfin gudu ba, tamkar aljani marhazul darkub. A cikin sa'a shida kacal suka isa birnin sharhas. Abin ka da matsafi ashe tuni shima sarki hasanul mauzur ya san da zuwan sarki hambaru da kuma dalilin zuwan nasa, don haka aljani marhazul darkub na dira a fadar, sai sarki hasanul mauzur ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin tsananin farin ciki tamkar yaga dan'uwansa na jini, wanda suka dade basu ga juna ba, ya tarye shi suka rungume juna, kuma ya ja shi har izuwa kan karagarsa suka zauna. Nan take hasanul mauzur yasa aka kawo abinci da abin sha irin nasu na sarakai suka ci suka sha tare. Bayan sun gama kimtsawa ne sarki hambaru ya bude baki domin yayi bayanin abin dake tafe dashi, sai sarki hasanul mauzur ya tari numfashinsa yace, "Ya kai wannan attajirin sarki ai ba sai kayi mini bayanin komai ba, domin na san duk abinda ke tafe da kai. Kazo ne domin ka biya ni naje na hallaka sarkin musulmi mai mulkin birnin baitul nur, na shafe kasarsa gaba day daga kan doron kasa, kuma ka kawo mini kudi dinare miliyan dubu arba'in ko ba haka bane ?" Cikin tsananin mamaki sarki hambaru yace, "tabbas haka maganarka take. " Sarki hasanul mauzur ya bushe da dariyar mugunta, sannan yace, "Ai wannan aiki naka mai sauki ne, tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai. Yanzu ba da dewa zan bika mu tafi tare domin naje na aiwatat da wannan aiki a gaban idanunka". Koda jin haka sai mamaki da tsoro ya kama sarki hambaru yace, "ta yaya zakaje kayi wannan aiki kaikadai ba tare da sauran dakarunka ba? Kuma ni menene amfanin zuwa dani?" Sarki hasanul mauzur ya sake tuntsirewa dadariya, sannan yace, "Ai ni kadai zan je nayi wannan aiki bana bukatar taimakon kuwa. Dalilin zuwa tare da kai shine kaga zahiri, ka tabbatar da cewa an cika aikinka, ba a ha'ince kaba. Yanzu zan sa a kirga kudin daka kawo mini, domin na tabbatar da cewa sun cika." Sarki hambaru yayi murmushi yace, "Ai babu matsala sai a kirga kudin. " Nan take kuwa hasanul mauzur yasa wadansu bayi suka hau kirga kudin. Su dai wadannan bayi adadinsu ya kai mutum dubu ashirin, amma duk da haka sai da suka bata sa'a bakwai suna kirga kudin, sannan suka kammala aka ga kudin ya cika dai-dai bai ragu ba, kuma bai karu da guda day. A sannan ne sarki hambaru da sarki hasanul mauzur suka dubi junansu suka kyalkyale da dariya. Sarki hambaru yace, "Hakika ka san kudi ya kai hasanul mauzur. " Hasanul mauzur yace, "Kai kuma ka tara su fiye dani ba. "Suka sake bushewa da dariya a tare. Nan dai sarki hasanul mauzur ya shiga ya kintsa yayi damarar yaki ya dauko dukkanin kayan tsafinsa da kayan yakinsa ya fito, sannan yasa aka kai wadaannan kudade miliyan dubu arba'in izuwa cikin baitil malinsa aka rufe. Bayan nan sai suka hau kan aljani marhazul darkub ya tashi da su sama ya nufi birnin baitul nur wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki hambaru da sarki hasanul mauzur a can birnin sharas. A can birnin baitul nur kuwa a wannan lokaci ban fi shekara takwas ba a duniya. A rayuwata babu abinda nake so sama da ganin abubuwan al'ajabi nasha jin labarin aljanu ana gaya mini cewa suna da fukafuki suna tashi sama, amma ban taba ganinsu ba. Mu biyu ne rak a wajen mahaifinmu ni da kanwata malifa wacce tsakanina da ita shekara daya ne jal. Malifa yarin ya ce mai tsananin kyau ga tada farin jini ainun a wajen dukkan jama'ar garinmu kyawun malifa ya wuce kwatancen mai kwatance kuma ni da ita mun shaku ainun dare da rana muna tare babu abin d ke raba mu koda kwanciyar barci kuwa. A daren da masifa zata sauka a birninmu na baitul nur, bayan magariba ne nida 'yar uwata malifa muka tafi can bayan gidan sarautarmu bakin wata tsohuwar rijiya muna wasan buya. Ita dai wannan rijiya ta dade ainun kuma mun ji tarihinta ance rabon da a bude ta anfi shekara hamsin. Wani katon murfi aka dora a kan rijiyar mai tsananin nauyi kuma wata irin kuba ce a jikin murfin mai kama da sakatu guda bakwai. Sakatun basu da wani maruki wanda za a iya ja a zare su bare har a sami damar bude murfin rijiyar. Kawai wata rana da na taba tambayar mahaifinmu tarihin wannan rijiya sai yace dani ai wani hatsabibin aljani ne a ciki wanda ya addabi mutanen birnin. Da kyar kakana ya kama shi ya jefa shi a cikin wannan rijiya ya kulle shi da wannan murfi na musamman. Babu wanda ya isa ya bude wannan rijiya face shi kadai wato shi mahaifin nawa, domin shi kadai ne ya san addu'ar da za a karanta wannan murfin rijiya ya bude, saboda kafin mahaifina ya rasu ya biya masa addu'ar kuma ya gargade shi da kada ya biyawa kowa face dan cikinsa, kuma sai dan nasa ya girma ya mallaki hankalin kansa. Koda naji wannan batu sai na hau rokon mahaifina akan ya koya mini wannan addu'a dayake mahaifina yasan halina zan iya zuwa na bude rijiyar saboda rashin tsorona da son ganin al'ajabina sai yace dani ba zai taba koya mini wannan addu'a ba har sai na balaga. Babu irin nacin da banyi ba, amma sarki yaki yarda ya koya mini wannan addu'a. Bisa wannan daliline na rinka shiga turakarsa a sirrince ina bincike a cikin littattafansa na tarihi ko zan ga wannan addu'a. Sai da. Na shafe wata shidda ina wannan bincike, sannan na gano wani dan mitsitsin littafi a cikin wata tsohuwar akwatu. Ko da na bude littafin sai naga babu komai acikinsa face wata addu'a guda daya kuma addu'ar an rubutata ne da yaren kasar hindu ba yarenmu na larabci ba. Nan take naji a jikina cewa lallai wannan addu'a itace addu'ar bude wannan rijiya. Cikin sauri na boye littafin a cikin rigata na fice daga cikin turakar. Daga wannan rana kullum bani da tunanin da ya fi na koyi yaren hindu, domin na iya karanta wannan addu'a. A gaba daya birninmu na baitul nur wani mutum ne shi kadai ya iya yaren hindu, ana kiransa da suna sariku bin amfaru. Sariku ya kasance tsoho dan kimanin shekaru tamanin da doriya, kuma hadimi ne babba a wajen mahaifinmu, kuma amintaccensa. Babu irin magiyar da ban yi wa sariku ba akan ya koya mini yaren hindu, amma sai yaki. Dana tambaye shi dalili sai yace dani. "Ai duk wadansu abubuwa na sirrin mahaifinka a cikin yaren hindu aka rubuta su, kuma ya gargade ni da kada na koyar daku yaren hindu kai da 'yar uwarka malifa bisa amana, kaga kuwa ba zan yarda naci amanar sarki ba." Koda jin wannan batu sai hankalina ya dugunzuma, domin na san cewa har abada ba zan iya bude wannan rijiya ba. Haka dai na cigaba da boye wannan mitsitsin littafi a wajena kusan ko yaushe dare da rana ina tare da shi, kuma ina boye shi malifa bata taba ganin littafin bare dani. Wata rana sai wani tunani ya fado mini a zuci na ce a raina me zai hana na dunga zuwa gidan tsoho sariku a sirrince ko zan ji irin karatuttukan da yake yi da rubutu a cikin yaren hindu, ko zan dace naji na wannan addu'a dake cikin mitsitsin littafin hannuna koda gama aiyana hakan kuwa saina fara zuwa gidan tsoho sariku ina buya a cikin dakinsa ba tare da ya sani ba. Kullum na kan ganshi ya debo littattafai sama da gudu dubu, amma duk littafin da ya dauko sai naga ya bude shafi daya a cikinsa ya karanta layi daya a cikin rubutun shafin, sannan ya rufe littafin ya dauki wani. ««« TARWATSA MAZA-3 TYPE D »»» Al'amarin daya matukar bani mamaki kenan na rasa dalilin da yasa yake yin haka. Duk sa'adda ya bude kowanne littafi na kan leka naga irin rubutun da yake karantawa, amma ban taba ganin irin wannan rubutu ba da ke cikin mitsitsin littafi dake hannuna. Sai da na kwana arba'in da uku ina shiga dakin sariku ina sauraronsa da

Please Login or Register in order to submit comment