Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawaye ya zubo masa sannan yace, "Ya kai dana kayi sani cewa ba komai ne yasa na kasa fita ba face takaicin babu kai a cikin wannan tafiyar da za a yi. Ka tuna cewa kai ne dana wanda ya kamata ya gaje ni, amma saboda rauninka na jarumtaka da rashin kulawarka a kan harkokin mulki ka rasa wannan dama, har ma mutane suna zunden ka a ko'ina, Koda gama rufe bakin sarki mushlik sai suka ji ance tabbas yarima zamir zai shiga wannan gasa, koda jin haka cikin sauri suka waiga bakin kofa bakowane me wannan magana ba face wannan mara lafiyar. Mu hadu a TARWATSA MAZA littafi na uku don jin ci gaban wannan labari daga ni mai debe muku kewa kuma masoyinku dan uwanku ««« TARWATSA MAZA-3 TYPE A »»» Da ranar gasar auren gimbiya sulaira tazo, sai fadar sarki Hasanul mauzur ta cika ta batse da al'umma, kai bama fadarba birnin gaba daya ya cika da baki, wadanna suka zo daga sassa daban-daban na duniya. Sai da yazamana cewa babu inda maza a sauki baki sai dai ka gansu suna kwana akofar gidajen jama'a. Kasuwa, bayan gari,da gefen gari, saboda yawan nasu ya wuce tunani. Tun da duku-dukun safiya, jama'a suka taru a fadar, duk inda mutum ya duba ba abinda zai gani face kawunan bil'adama kai wasu ma saboda babu wajen tsayawa kan ka tangu da ganuwa suka hau suka zazzauna sarki hasanul mauzur da 'yarsa gimbiya shulaira basu fito filin fadarba har saida rana ta take ya zamana cewa mutane sun kosa har sun fara tunanin ko an fasa yin gasar ne koda fitowar sarki da gimbiya sai fadar ta rude da shewa, makada da mawaka suka shiga aikinsu na yiwa sarki kirari bisa jarumtakarsa da aka san shi da ita ta gwarzon shekara, wato jarumin daya ratsa dazuzzuka guda uku. Wadanda ba a taba samun mahalukin da ya shige su ba ya dawo a raye, tsawon shekaru hamsin baya kawo iyanzu. A wannan rana gimbiya shulaira tayi shiga mai tsananin kyau, ta kure adaka, domin ta sanya wata doguwar riga ce mai launin ruwan dorawa matsatstsiya, wacce ta bayyana kyakykyawar surar jikinta, wacce babu wani da na miji lafiyayye daya isa ya ganta bai kamu da tsananin sha'awarta ba. Gashin kanta wanda ya kasance baki sidik mai matukar haske, tamkar madubi yazubo har kasan kwankwasonta, sai sheki da walwali yake, kuma an tufke shi da wani karfen abin ado shi ma mai launin ruwan kwai. Takalmin dake kafarta zuwa dunduniyarta na kwal ne, samansa kuwa da lu'u-lu'u aka yi shi, amma ya kasance dan shafal babu nauyi tamkar da takarda aka yi shi. Cikin tafiyar kasaita gimbiya sulaira da sarki hasanul mauzur suka taka suka hau inda karagar mulki take suka zauna. Shima sarki hasanul mauzur yayi gagarumar shiga mai tsadar gaske, wacce sai sarkin da ya cika gawurtaccen attajiri zai iya yinta. Idan kuwa ya matsa alhalin bai kai matsayin yin ba zai iya talaucewa tamkar al'majiri mai barar abinda zai ci. Zaman sarki hasanul mauzur da gimbiya shulaira ke da wuya sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganin yawan samarin dake cikin tsakiyar fadar wadanda suka zo yin gasar neman auren nata mafi yawansu 'ya'yan attajirai ne da sarakai da kuma gawurtattun jarumai na nashiyar, kowannensu yayi shiga mai kyau da tsada abar burgewa da sha'awa. A wannan lokaci sarki Hasanul mauzur na rike da wannan sandar sihiri tasa wadda ya dauko a can kogon dodo gurmazu bayan ya sami nasarar hallaka shi. GiMBiYa shulaira ta dubi sarki hasanul mauzur cikin damuwa tace, "Yakai abbana, ai masu shiga gasar nan sunyi yawan gaske, yaza a yi a tantance wadanda ya kamata suyi wannan gasa?" Koda jin wannan tambaya sai sarki hasanul mauzur yayi 'yar guntuwar dariya yace, "Ai ba a sanin maci tuwo ba, sai miya ta kare. Duk wannan yawan nasu na banza ne, domin da zarar an fara gwajin farko za kiga yadda za'a yi ta zubar dasu har sai sun zama 'yan kadan. Lokacin da sarki hasanul mauzur ke wannan bayani fadar ta rude da hayaniya, amma ana ganin ya mike tsaye sai aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Sarki hasanul mauzur ya dubi bangaren da fadawansa ke zaune da bangaren mutanen gari ya yi gaisuwa, sannan ya fara bayani kamar haka:- "Ya ku jama'ata tare da sauran baki wadanda suka zo daga sassa daban-daban na duniya ina mai yi muku barka da zuwa wannan birni namu mai albarka, wato birnin sharas. Sannan kuma ina mika godiya mara adadi ga dukkan samarin da suka yi kundumbala, domin shiga wannan gasa ta neman auren 'yata GIMBIYA SHULAIRA, saboda gasa ce mai matukar wuya da hadarin gaske, sai mai tsananin rabo ne zai ci wannan gasa, ina so ku sani cewa waka a bakin mai ita tafi zaki, don haka gimbiya ce da kanta za tayi muku bayanin yadda ka'idojin wannan gasa yake, amma kafin a fara komai za'a yi walima ta sa'a daya domin kowa ya taya ni farin ciki bisa zuwan wannan rana." Koda gama fadin haka sai sarki ya zauna a kan karagarsa ta mulki. Zamansa ke da wuya sai ga barori da kuyangi masu yawan gaske suna fitowa da abinci da abin sha iri- iri na alfarma suna rabawa jama'a kafin cikar sa'a daya gaba dayan al'ummar dake wajen sun wadata da ababan ci da na sha ba a sami matsalar wawa ba. Kai komai zurfin cikin mutum na cin abinci a wannan rana dole ne ya kalli abincin ya kawar da kai, domin idan ya matsa sai dai yayi kumallo saboda koshi. Ganin yadda komai ya wadata ne a wajen yasa mutane suka sake tsinkewa da al'amarin sarki hasanul mauzur suka gasgata cewa arzikinsa ya wuce tunanin mai tunani, domin zai Iya ciyar da kasashe uku masu girman kasarsa, tsawon shekara uku ba tare da tattalin arzikinsa yayi rawa ba. Bayan an gama walima, sai gimbiya shulaira ta mike tsaye ta fara bayanin ka'idojin gasar cikin zazzakar muryarta wacce koda mutum ya kwana arba'in yana kuka da bakin ciki da zarar yaji ta zaiji an zare masa dukkan damuwar da tadameshi gimbiya shulaira ta fara bayani kamar haka: "Duk saurayin dake son aurena, dole ne ya biya sadakina na kudi adadin dinare miliyan dubu daya. Sharadi na biyu shine dole ne yayi gumurzu da manyan sadaukai guda dari wadanda babu kamarsu a wannan nahiya tamu ya tarwatsasu. Sharadi na uku shine dole ne ya gwabza yaki da mahaifina wato sarki Hasanul mauzur yakai shi kas. Bayan ya haye wadannan matakai uku zan amince a daura aurena da shi, amma kuma akwai wadansu dokoki guda biyu wadanda dole ne yayi alkawarin kiyaye su bayan aure na. Bazan fadi wadannan dokokiba sai bayan aurena da shi." Bayan gimbiya shulaira ta gama wannan jawabi sai ta koma kan kujerarta ta zauna wacce ke daf da ta sarki hasanul mauzur. Zamanta ke da wuya sai samarin 'yan gasa suka fara sulalewa daya-bayan daya suna barin tsakiyar fadar sai da ya rage basu fi saura mutum dubu daya ba daga cikin adadin daya haura miliyan daya. Al'amarin daya baiwa kowa tsoro kenan a fadar. Su kansu jaruman dubu idan mutum ya dube su da kyau zai ga alamar karayar zuci a tare dasu face daisaikunsu wadanda zuciyarsu ta kekashe ga barin tsoro. Lokacin da srki hasanul mauzur yaga saura mutum dubu daya jal masu gasar neman auren gimbiya shulaira sai ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi shulaira yace, "Ai dama na gaya miki cewa da sannu zasu ragu. Yanzu zan yi hikimar daza su dada raguwa har su zama su dari daga cikin mutanen darin ne za'a fitar da tauraronki bayan sun biya kudin farko na sadakin aurenki sannan a cigaba da gasar. " Cikin rashin fashimta shulaira ta dubi sarki tace, "Ya kai abbana ban gane manufarka ba?" Sarki hasanul mauzur yayi murmushi yace, "Kada ki damu ki cigaba da zuba idanu da sannu zaki ga komai da idanunki. " Nan take sarki ya mike tsaye ya dubi jaruman dubu yace, "Ina son kowannenku ya zabi abokin gwaminsa a cikinku kuyi kokawa, wanda duk bayansa ya taba kas ya fita daga cikin gasar." Koda gama fadin hakan, sai jaruman suka fara kallon-kallo a tsakaninsu cikin nazari kowannansu kokarinsa shine ya zabi abokin gwamin da ya tabbatar da cewa zai iya samun nasara akansa. Nan take suka kaure da kokawa wanda sai dai kaga an daga kato an maka shi da kasa, sun yi wuf sun dauko shi sun fitar da shi suka zama saura su dari biyar. Haka dai sarki ya cigaba da gasar har ya zamana saura su dari kacal. Wadannan jarumai dari ba karamar jarumta suka nuna ba a wannan rana, don haka sai fadar ta rude da shewar jama'a shi kansa sarki hasanul mauzur sai da yayi musu tafi domin ya san cewa sun yi matukar kokari. Sarki hasanul mauzur ya dubi jaruman dari yace, "Yaku wadannan zaratan jarumai kuyi sani cewa kune wadanda kuka cancanci hawa matakin farko na wannan gasa, saboda haka idan har kuna son kucigaba da wannan gasa dole ne kubiya wannan sadaki na dinare miliyan dubu daya. Ku sani cewa babu wanda za a dawowa da kudinsa ko yaci gasar ko baici ba. Dukkaninku daya bayan daya, mutum daya daga cikinku zai yi yaki da mutum casa'in da tara wanda duk ya sami nasarar tarwatsa ku shine zai hau mataki na karshe, wato ya gwabza yaki dani kaina. Idan har ya kai ni kas to ya samu nasarar lashe gasar, don haka shine zai auri 'yata gimbiya shulaira. Tunda ku dari ne, kullum za a yi gasar ne sau daya wato a kullum daya daga cikinku zai fafata da mutum casa'in da tara. Bisa dokar wannan gasa babu kisa, amma za a iya yi wa mutum rauni komai muninsa kuwa, wanda inda tsautsayi ma raunin ya zamo ajalin mutum. Idan kun amince, kuma zuciyarku bata karaya ba, sai kuzo ku biya sadakin auren 'yata a yanzu. " Koda gama wannan jawabi sai da yawa daga cikin jaruman dari suka yi tsuru-tsuru suna tunani. Wasu dai zuciyarsu tuni ta karaya, domin sun san cewa wannan mataki na biyu ma dake gabansu ba zasu iya haye shiba, domin sadaukin da zai iya tarwatsa wannan cincirindo nasu na zakwakuran sadaukai ba karamin gwarzo bane, sai mai jarumtakar al'ajabi. Sai da jaruman dari suka jima a tsaye suna shawarwari a cikin zukatansu aka rasa wanda zai fara zuwa ya biya kudin. Daga can sai aka ga wani jarumi wanda ke sanye da fararen kaya kuma yana bisa farin doki ya nufi inda sarki hasanul mauzur ke tsaye da nufin ya biya nasa kudin. Koda ganin haka sai wadansu jaruman guda uku suka bi bayansa suka je suka jeru a gaban sarki hasanul mauzur, a lokaci guda suka rinka kwato jakunkunan dinare daga kan dawakansu suna mikawa dakarun sarki suna kirgawa. Jim kadan da faruwar haka ne ragowar jaruman gasar ma suka nufo inda sarki yake, domin su biya nasu kudin sai sarki yayi nuni dasu tsaya a bayan jaruman hudu na farko, sannan su biya nasu kudaden. Haka kuwa al'amarin ya kasance, wato ragowar jaruman gasar su casa'in da shida suka tsaya a bayan jaruman hudu suna bayar da nasu kudaden ana kirgawa. A wannan lokaci ne sarki hasanul mauzur da gimbiya shulaira suka kurawa jaruman hudu da ke gabansu idanu suna nazarinsu da kyau, domin duk sun kasance kyawawan gaske masu kwarjini da cika ido kallo daya mutum zai musu ya gane cewa 'ya'yan manyan sarakai ne. Sarki hasanul mauzur ya dubi jarumin farko, wanda yake da fararen kaya, kuma mai farin doki yace, "Gabatar da kanka ya kai wannan saurayi mai kwarjini da haiba. " Koda jin haka sai saurayin yayi murmushi, kyawunsa ya karu ainun har gimbiya shulaira taji nan take ya burgeta. Sai yace, Ni sunana yarima ZAMIR, dan sarki mushlik na birnin dumar." Koda jin wannan batu sai sarki hasanul mauzur ya cika da tsananin mamaki, kawai sai ya murtuke fuska yace, "kai yaro karya kake yi ba kai bane yarima zamir, domin ina da labarin cewa yarima zamir rago ne, bai kasance jarumi ba, asalima ko takobi bai taba rikewa ba, bai taba zuwa yaki ba, kuma bai damu da komai ba a duniya face wasa a cikin yara. Ya za a yi yanzu ka zo kace damu kaine yarima zamir?" Saurayin yayi murmushi yace, "Ya kai wannan sarki mai daraja hakika duk abubuwan da ka fada gaskiyane, to amma ka sani cewa rayuwar duniya juyi-juyi ce komai na iya faruwa. Ni yarima zamir na karbi addinin musulunci ba tare da mahaifina ya sani ba, kuma ubangijin musulunci ya sauya mini komai nawa na zama gagarumin jarumi, don haka duk abin da zan yi a yanzu bai kamata ayi mamaki ba." Koda jin wannan batu sai hankalin kowa da ke fadar ya dugunzuma, kuma aka cika da tsananin mamaki, domin wannan shine karo na farko da aka taba samun ma'abocin addinin musulunci ya shigo cikin birnin sharas har ya bayyana kansa, saboda tsananin tsoron sarki Hasanul mauzur da ake yi da kuma sanin tsananin kiyayyarsa akan ko wanne addini, face na bautar gunki hurzas. ««« TARWATSA MAZA-3 TYPE A »»» Da ranar gasar auren gimbiya sulaira tazo, sai fadar sarki Hasanul mauzur ta cika ta batse da al'umma, kai bama fadarba birnin gaba daya ya cika da baki, wadanna suka zo daga sassa daban-daban na duniya. Sai da yazamana cewa babu inda maza a sauki baki sai dai ka gansu suna kwana akofar gidajen jama'a. Kasuwa, bayan gari,da gefen gari, saboda yawan nasu ya wuce tunani. Tun da duku-dukun safiya, jama'a suka taru a fadar, duk inda mutum ya duba ba abinda zai gani face kawunan bil'adama kai wasu ma saboda babu wajen tsayawa kan ka tangu da ganuwa suka hau suka zazzauna sarki hasanul mauzur da 'yarsa gimbiya shulaira basu fito filin fadarba har saida rana ta take ya zamana cewa mutane sun kosa har sun fara tunanin ko an fasa yin gasar ne koda fitowar sarki da gimbiya sai fadar ta rude da shewa, makada da mawaka suka shiga aikinsu na yiwa sarki kirari bisa jarumtakarsa da aka san shi da ita ta gwarzon shekara, wato jarumin daya ratsa dazuzzuka guda uku. Wadanda ba a taba samun mahalukin da ya shige su ba ya dawo a raye, tsawon shekaru hamsin baya kawo iyanzu. A wannan rana gimbiya shulaira tayi shiga mai tsananin kyau, ta kure adaka, domin ta sanya wata doguwar riga ce mai launin ruwan dorawa matsatstsiya, wacce ta bayyana kyakykyawar surar jikinta, wacce babu wani da na miji lafiyayye daya isa ya ganta bai kamu da tsananin sha'awarta ba. Gashin kanta wanda ya kasance baki sidik mai matukar haske, tamkar madubi yazubo har kasan kwankwasonta, sai sheki da walwali yake, kuma an tufke shi da wani karfen abin ado shi ma mai launin ruwan kwai. Takalmin dake kafarta zuwa dunduniyarta na kwal ne, samansa kuwa da lu'u-lu'u aka yi shi, amma ya kasance dan shafal babu nauyi tamkar da takarda aka yi shi. Cikin tafiyar kasaita gimbiya sulaira da sarki hasanul mauzur suka taka suka hau inda karagar mulki take suka zauna. Shima sarki hasanul mauzur yayi gagarumar shiga mai tsadar gaske, wacce sai sarkin da ya cika gawurtaccen attajiri zai iya yinta. Idan kuwa ya matsa alhalin bai kai matsayin yin ba zai iya talaucewa tamkar al'majiri mai barar abinda zai ci. Zaman sarki hasanul mauzur da gimbiya shulaira ke da wuya sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganin yawan samarin dake cikin tsakiyar fadar wadanda suka zo yin gasar neman auren nata mafi yawansu 'ya'yan attajirai ne da sarakai da kuma gawurtattun jarumai na nashiyar, kowannensu yayi shiga mai kyau da tsada abar burgewa da sha'awa. A wannan lokaci sarki Hasanul mauzur na rike da wannan sandar sihiri tasa wadda ya dauko a can kogon dodo gurmazu bayan ya sami nasarar hallaka shi. GiMBiYa shulaira ta dubi sarki hasanul mauzur cikin damuwa tace, "Yakai abbana, ai masu shiga gasar nan sunyi yawan gaske, yaza a yi a tantance wadanda ya kamata suyi wannan gasa?" Koda jin wannan tambaya sai sarki hasanul mauzur yayi 'yar guntuwar dariya yace, "Ai ba a sanin maci tuwo ba, sai miya ta kare. Duk wannan yawan nasu na banza ne, domin da zarar an fara gwajin farko za kiga yadda za'a yi ta zubar dasu har sai sun zama 'yan kadan. Lokacin da sarki hasanul mauzur ke wannan bayani fadar ta rude da hayaniya, amma ana ganin ya mike tsaye sai aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Sarki hasanul mauzur ya dubi bangaren da fadawansa ke zaune da bangaren mutanen gari ya yi gaisuwa, sannan ya fara bayani kamar haka:- "Ya ku jama'ata tare da sauran baki wadanda suka zo daga sassa daban-daban na duniya ina mai yi muku barka da zuwa wannan birni namu mai albarka, wato birnin sharas. Sannan kuma ina mika godiya mara adadi ga dukkan samarin da suka yi kundumbala, domin shiga wannan gasa ta neman auren 'yata GIMBIYA SHULAIRA, saboda gasa ce mai matukar wuya da hadarin gaske, sai mai tsananin rabo ne zai ci wannan gasa, ina so ku sani cewa waka a bakin mai ita tafi zaki, don haka gimbiya ce da kanta za tayi muku bayanin yadda ka'idojin wannan gasa yake, amma kafin a fara komai za'a yi walima ta sa'a daya domin kowa ya taya ni farin ciki bisa zuwan wannan rana." Koda gama fadin haka sai sarki ya zauna a kan karagarsa ta mulki. Zamansa ke da wuya sai ga barori da kuyangi masu yawan gaske suna fitowa da abinci da abin sha iri- iri na alfarma suna rabawa jama'a kafin cikar sa'a daya gaba dayan al'ummar dake wajen sun wadata da ababan ci da na sha ba a sami matsalar wawa ba. Kai komai zurfin cikin mutum na cin abinci a wannan rana dole ne ya kalli abincin ya kawar da kai, domin idan ya matsa sai dai yayi kumallo saboda koshi. Ganin yadda komai ya wadata ne a wajen yasa mutane suka sake tsinkewa da al'amarin sarki hasanul mauzur suka gasgata cewa arzikinsa ya wuce tunanin mai tunani, domin zai Iya ciyar da kasashe uku masu girman kasarsa, tsawon shekara uku ba tare da tattalin arzikinsa yayi rawa ba. Bayan an gama walima, sai gimbiya shulaira ta mike tsaye ta fara bayanin ka'idojin gasar cikin zazzakar muryarta wacce koda mutum ya kwana arba'in yana kuka da bakin ciki da zarar yaji ta zaiji an zare masa dukkan damuwar da tadameshi gimbiya shulaira ta fara bayani kamar haka: "Duk saurayin dake son aurena, dole ne ya biya sadakina na kudi adadin dinare miliyan dubu daya. Sharadi na biyu shine dole ne yayi gumurzu da manyan sadaukai guda dari wadanda babu kamarsu a wannan nahiya tamu ya tarwatsasu. Sharadi na uku shine dole ne ya gwabza yaki da mahaifina wato sarki Hasanul mauzur yakai shi kas. Bayan ya haye wadannan matakai uku zan amince a daura aurena da shi, amma kuma akwai wadansu dokoki guda biyu wadanda dole ne yayi alkawarin kiyaye su bayan aure na. Bazan fadi wadannan dokokiba sai bayan aurena da shi." Bayan gimbiya shulaira ta gama wannan jawabi sai ta koma kan kujerarta ta zauna wacce ke daf da ta sarki hasanul mauzur. Zamanta ke da wuya sai samarin 'yan gasa suka fara sulalewa daya-bayan daya suna barin tsakiyar fadar sai da ya rage basu fi saura mutum dubu daya ba daga cikin adadin daya haura miliyan daya. Al'amarin daya baiwa kowa tsoro kenan a fadar. Su kansu jaruman dubu idan mutum ya dube su da kyau zai ga alamar karayar zuci a tare dasu face daisaikunsu wadanda zuciyarsu ta kekashe ga barin tsoro. Lokacin da srki hasanul mauzur yaga saura mutum dubu daya jal masu gasar neman auren gimbiya shulaira sai ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi shulaira yace, "Ai dama na gaya miki cewa da sannu zasu ragu. Yanzu zan yi hikimar daza su dada raguwa har su zama su dari daga cikin mutanen darin ne za'a fitar da tauraronki bayan sun biya kudin farko na sadakin aurenki sannan a cigaba da gasar. " Cikin rashin fashimta shulaira ta dubi sarki tace, "Ya kai abbana ban gane manufarka ba?" Sarki hasanul mauzur yayi murmushi yace, "Kada ki damu ki cigaba da zuba idanu da sannu zaki ga komai da idanunki. " Nan take sarki ya mike tsaye ya dubi jaruman dubu yace, "Ina son kowannenku ya zabi abokin gwaminsa a cikinku kuyi kokawa, wanda duk bayansa ya taba kas ya fita daga cikin gasar." Koda gama fadin hakan, sai jaruman suka fara kallon-kallo a tsakaninsu cikin nazari kowannansu kokarinsa shine ya zabi abokin gwamin da ya tabbatar da cewa zai iya samun nasara akansa. Nan take suka kaure da kokawa wanda sai dai kaga an daga kato an maka shi da kasa, sun yi wuf sun dauko shi sun fitar da shi suka zama saura su dari biyar. Haka dai sarki ya cigaba da gasar har ya zamana saura su dari kacal. Wadannan jarumai dari ba karamar jarumta suka nuna ba a wannan rana, don haka sai fadar ta rude da shewar jama'a shi kansa sarki hasanul mauzur sai da yayi musu tafi domin ya san cewa sun yi matukar kokari. Sarki hasanul mauzur ya dubi jaruman dari yace, "Yaku wadannan zaratan jarumai kuyi sani cewa kune wadanda kuka cancanci hawa matakin farko na wannan gasa, saboda haka idan har kuna son kucigaba da wannan gasa dole ne kubiya wannan sadaki na dinare miliyan dubu daya. Ku sani cewa babu wanda za a dawowa da kudinsa ko yaci gasar ko baici ba. Dukkaninku daya bayan daya, mutum daya daga cikinku zai yi yaki da mutum casa'in da tara wanda duk ya sami nasarar tarwatsa ku shine zai hau mataki na karshe, wato ya gwabza yaki dani kaina. Idan har ya kai ni kas to ya samu nasarar lashe gasar, don haka shine zai auri 'yata gimbiya shulaira. Tunda ku dari ne, kullum za a yi gasar ne sau daya wato a kullum daya daga cikinku zai fafata da mutum casa'in da tara. Bisa dokar wannan gasa babu kisa, amma za a iya yi wa mutum rauni komai muninsa kuwa, wanda inda tsautsayi ma raunin ya zamo ajalin mutum. Idan kun amince, kuma zuciyarku bata karaya ba, sai kuzo ku biya sadakin auren 'yata a yanzu. " Koda gama wannan jawabi sai da yawa daga cikin jaruman dari suka yi tsuru-tsuru suna tunani. Wasu dai zuciyarsu tuni ta karaya, domin sun san cewa wannan mataki na biyu ma dake gabansu ba zasu iya haye shiba, domin sadaukin da zai iya tarwatsa wannan cincirindo nasu na zakwakuran sadaukai ba karamin gwarzo bane, sai mai jarumtakar al'ajabi. Sai da jaruman dari suka jima a tsaye suna shawarwari a cikin zukatansu aka rasa wanda zai fara zuwa ya biya kudin. Daga can sai aka ga wani jarumi wanda ke sanye da fararen kaya kuma yana bisa farin doki ya nufi inda sarki hasanul mauzur ke tsaye da nufin ya biya nasa kudin. Koda ganin haka sai wadansu jaruman guda uku suka bi bayansa suka je suka jeru a gaban sarki hasanul mauzur, a lokaci guda suka rinka kwato jakunkunan dinare daga kan dawakansu suna mikawa dakarun sarki suna kirgawa. Jim kadan da faruwar haka ne ragowar jaruman gasar ma suka nufo inda sarki yake, domin su biya nasu kudin sai sarki yayi nuni dasu tsaya a bayan jaruman hudu na farko, sannan su biya nasu kudaden. Haka kuwa al'amarin ya kasance, wato ragowar jaruman gasar su casa'in da shida suka tsaya a bayan jaruman hudu suna bayar da nasu kudaden ana kirgawa. A wannan lokaci ne sarki hasanul mauzur da gimbiya shulaira suka kurawa jaruman hudu da ke gabansu idanu suna nazarinsu da kyau, domin duk sun kasance kyawawan gaske masu kwarjini da cika ido kallo daya mutum zai musu ya gane cewa 'ya'yan manyan sarakai ne. Sarki hasanul mauzur ya dubi jarumin farko, wanda yake da fararen kaya, kuma mai farin doki yace, "Gabatar da kanka ya kai wannan

Please Login or Register in order to submit comment