Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutu da farin ciki alkawarin dana daukarwa mahaifiyarki cewar bazan taba bari kisha wahala ba a rayuwarki. Bisa wannan daliline gobe zan sa a yi shela har izuwa dukkan sauran kasashe dake wannan nashiya tamu cewar duk wanda yake son ki da auren naki, bisa wadannan matakai guda uku da kika gindaya, amma sharadai biyu na cewar ba zai yi miki kishiya ba, kuma ba zai kara aure ba, koda kin mutu kamar yadda nayi wa mahaifiyarki alkawari, sai bayan an gama gasar zamu bayyana su. " Cikin farin ciki shulaira tace, "Na yarda da hakan ya kai abbana. " Koda wanda zai shiga wannan gasar Nidai na dau damara na dau hanya waye zai take mini baya kodai matsoratane ??? ««« TARWATSA MAZA-2 TYPE C »»» Kashegari da sassafe aka fara shela a cikin birnin sharas ana gayyatar jama'a I zuwa gasar samun auren gimbiya shulaira, sannan aka tashi manzanni a shirin da bakwai suka tafi izuwa sauran kasashen dake nahiyar suna kai wasiku izuwa ga sarakuna na gayyatar su izuwa wannan kasa. Sai da aka kwana talatin ana ta watsa wannan shela, nan da nan kuwa labari ya bazu ko'ina a nashiyar gaba daya har dama sauran kasahen dake wadansu na shiyoyin daban. A cikin nashiyar da kasar sharas take a kwai wata karamar kasa mai suna DUMAR. Sarkin dake mulkin birnin ya kasance a dali mai tausayi da jinkan talakawansa kuma gwarzon jarumi ne na gaske, ana kiransa da suna mushlik. Gaba daya fadawan mushlik azzalumaine, kuma basa son halayen mushlik, babu yadda basuyiba akan su tumbuke shi daga kan mulki ta hanyar amfani da karfin sihiri da makirci, amma abu ya gagara, saboda yafisu karfin sihiri. Komai na duniya allah ya baiwa sarki mushlik, ga arziki kuma ga iyali, amma 'ya'yansa goma sha bakwai ne dukkaninsu matane, namiji guda daya ne ana kiransa da suna yarima zamir. Shekarun yarima zamir basu haura ashirin da biyar ba, kuma ya kasance kyakykyawan saurayi kuma ya gaji mahaifinsa a bangaren kyawawan halayeensa sai dai ko kadan bai kasance jarumi ba tunda yarima zamir yazo duniya ko kiyashi bai taba kashewaba saboda tsananin tausayinsa kuma bai taba ruke takobiba a rayuwarsa a kullum yarima zamir babu abinda yake so sama da zama a cikin yara yana wasa da su suna debe masa kewa ko kadan yarima zamir bai damu da jin dadin duniyaba kuma bai taba ganin wata budurwa ba ya nuna yana sonta komai tsananin kyanta. Dare da rana yarima zamir na tare da kannansa yara maza da mata yana wasa da su. Wannan halaiya ta yarima zamir ba karamin bakin ciki ta jefa sarki mushlik a ciki ba, domin babu yadda baiyi a kan ya sauya yanayin rayuwarsa amma ya kasa. Burin sarki mushlik shi ne yarima zamir ya gajeshi a karagarsa, kuma yayi gagarumin abin bajinta, wanda zai shahara a duniya gaba daya. Dalilin da yasa yake da wannan buri shine yasan cewa duk ranar daya fadi ya mutu, shi kenan mulkinsa da dukiyarsa sun zama na daya daga cikin fadawansa, kuma a dalcin da ake yi wa talakawa an daina. Haka kuma a gaba daya nahiyar ana zunden yarima zamir ana cewa ba a taba yin malalacin yarima ba kamarsa har dariya ake yi masa ana goranta masa ana cewa sarki mushlik yayi a sarar haihuwa. Duk sa'adda sarki mushlik ya tuno da wannan al'amarin sai ya shiga cikin turakarsa ya kulle kansa yayi ta kuka saboda bakin ciki. A ranar da wasikar gayyata ta gasar neman auren gimbiya shulaira ta riski sarki mushlik saihankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ya kamu da tsananin bakin ciki fiye da koyaushe, domin ga bikin zuwa babu zanin daurawa. Abin da yafara fado masa a rai shine yarima zamir ya shiga wannan gasa, domin yayi gagarumar bajintar da ba a taba yin irintaba kuma ya auri gimbiya shulaira wato dai ya jefi tsuntsu biyu da hoge daya. Sarki mushlik ya tuna cewa ko kadan yarima zamir bai iya aikin sihiri ba. Babbar matsalar itace a dokar gasar ba a yarda sarakuna su shiga ba sai dai 'ya'yansu. Bayan sarki mushlik ya gama jin sakon da ke cikin wasikar gasar. Sai ya kasa zaune ko tsaye ya shiga kai-kawo yana ta tunani bisa yadda zai amfani da wannan dama a kan dansa yarima zamir, amma sai ya ga sam- sam babu mafita. Bisa wannan da muwace sarki mushlik yayi shiri ya fita rangadi izuwa bayan gari shi kadai, domin ya sami kadaici kuma ya sami saukin tunani da damuwa. Lokacin da sarki mushlik yayi nisa ga barin gari sai ya yada zango a bakin wata korama ya sha ruwa, dokinsa ma ya sha ya zauna yana kallon ruwan koramar, wanda cibiyace ta wani babban kogi sai ruwa ne ke ta gudu ba tsayawa. Kwazam sai sarki mushlik ya ghango wani allon jirgin ruwa daga can nesa igiyar ruwa na kado shi gaba. Tun daga nesa mushlik ya fashimci cewa akwai mutum a kan allon jirgin a kwance tamkar gawa, domin ko motsi baya yi. Cikin hanzari sarki mushlik ya mike tsaye ya shiga cikin koramar ya tari allon jirgin, don kada ruwa ya tafi dashi. Koda allon yazo zai gifta sai yayi wuf ya ruko shi ya janyoshi izuwa bakin gaba da yake mutumin a kwance yake cikin ruf da ciki, sai ya kama kafadunsa ya dago shi sama sai yaga a she saurayine kyakykyawan gaske. Ga kibiya ta soke shi a cikin gefen kirjinsa kuma bai mutu ba yana numfashi kadan- kadan. Cikin sauri sarki mushlik ya dauki saurayin yaje ya dora shi a kan dokinsa, sannan shima ya hau kan dokin ya zabure shi da gudu izuwa cikin gari. Sarki mushlik na isa gida ya tura aka kira likitansa ya kama aikinsa a kan bakon saurayin, wanda rayuwarsa na tsakanin rai da mutuwa. A wannan lokaci hankalin sarki mushlik ya dugunzuma ainun, tamkar yarima zamir ne a cikin wannan hali. Sai da likitan ya shafe sama da sa'a guda yana aikin a kan bakon saurayin, sannan ya fito daga cikin dakin da aka kwantar da bakon koda fitowar likitan sai sarki mushlik ya tare shi cikin matsananciyar damuwa yace, "me a ke ciki? Shin wannan matashi zai rayu ko mutuwa zai yi? Likitan yayi ajiyar zuciya, sannan yace, "Ya shugabana bakon ka zai rayu amma ba zai iya yin komai ba sai nan da kamar kwana bakwai. Lallai a kula da shi sosai a dunga dura masa abinci ko da ba zai iya ci da kansa ba, kuma akwai magunguna da zan bayar a dunga bashi yana sha kullum sau uku. Idan aka yi fashin ba shi wannan magani ko da na rana daya ne zai iya rasa rayuwarsa, saboda tuni dafin kibiyar ya shiga jikinsa, dole ne ya sha iya a dadin maganin da jinin jikinsa ke bukata, wanda zai lalata dafin. " Koda gama fadin haka sai likita yayi sallama ya tafi a kan cewa yana zuwa gida zai turo 'yarsa ta kawo maganin da za a dinga bawa mara lafiyar. Tafiyar likita ke da wuya sai sarki mushlik ya tura aka kirawo 'yarsa mai suna lasmin. Lasmin budurwa ce kyakykyawa ta kwatance kuma kanwar yarima zamir ce wato daki daya suke kuma ita ce bin yarima zamir. A shekara biyu ce tazarar dake tsakaninsu ma'na gimbiya lasmin tana da shekaru a shirin da uku ne. Sarki mushlik yana matukar kaunar gimbiya lasmin kamar yadda yake kaunar yazima zamir, banbancin kawai shine ita mace ce bata da ikon gadon karagar mulki. Sarki mushlik ya yarda da gimbiya lasmin ainun domin koda wani aikin na sirri yake son a yi masa ita yake sawa tayi. Lokacin da gimbiya lasmin taji kiran mahaifin ta sai ta tashi da sauri ta ruga izuwa gareshi inda ta iske shi tsaye a kofar dakin da aka kwantar da mara lafiya. Da zuwanta sai sarki mushlik ya kama hannunta ya ja ta izuwa cikin dakin inda suka iske mara lafiyan kwance bisa gado, kamar gawa, amma yana numfashi kuma idadunsa a rufe suke da zuwansu bakin gadon lasmin tayi arba da fuskar mara lafiyan sai taji nan take ta kamu da kaunarsa, al'amarin daya matukar bata mamaki kenan, domin a rayuwar gimbiya lasmin bata taba yin soyayyaba, kuma ba ta taba ganin saurayin da taji tana soba face wannan mara lafiyar dake kwance. 'Ya'yan sarakai da attajirai da yawa sun nemi auren gimbiya lasmin, amma taki saboda ta kudurce a ranta cewa bazata taba yin aureba face ta ga cikar burin mahaifinta a kan yayanta yarima zamir, sai dai a zuciyarta ta bar wannan buri ko shi kansa sarki ba ta furta masa ba. Lokacin da sarki mushlik yaga gimbiya lasmin taki ta fitar da gwani daga cikin masoyanta sai hankalinsa ya dugun zuma ya kira ta suka kadaita yace, "yake 'yata kiyi sani cewa ina cikin tsananin bakin ciki da damuwa a kan yadda dan'uwanki yarima zamir ya kasance. Kece kadai nake da sauran Buri a kanki, wanda zai share mini hawaye. Hanyar daza ki share mini hawayen shine kiyi aure za ki haifi dan da zai gaji karagata bokayena sun tabbatar mini da cewa yarima zamir ba zai taba gado naba amma ke idan kika yi aure zaki haifi dan da zai gajeni saboda me baza ki gaggauta yin aure ba, domin naga jikana tun gabannin ajalina? Sa'adda sarki mushliik yazo nan a zancensa, sai hawaye ya zubowa gImbiya lasmin ta rungume shi tace, "Ya kai abbana ka tsaya kayi tunani. A halin yanzu shekarunka sun kai saba'in da doriya tsufa ya fara riskarka, yanzu yaushe zan yi aure har na haifi dan da zai girma har ya zama sarki? Tabbas kafin zuwan wannan lokaci a jali ya riske ka. Burinka shine kaga magajinka a kan karagar mulkinka, idan baka mantaba ka taba gayamin cewa idan har yarima zamir yayi gagarumin a bin al'ajabi a duniya zai iya gadon karagarka. Mai zai hana ka cigaba da kokarin ganin faruwar hakan tunda tsafi ya tabbatar da cewa babu wani abu da zai gagara afkuwa a cikin wannan duniya. " Sa'adda gimbiya lasmin tazo nan a zancenta sai jikin sarki mushlik yayi sanyi, ya yi shiru bai ce komai ba daga wannan rana bai kara yi mata maganar aure ba. ««« TARWATSA MAZA-2 TYPE D »»» Bayan sarki mushlik ya nunawa gumbiya lasmin bakonsa mara lafiya dake kwance, sai ya dube ta ya ce, "Yake amintacciyar 'yata daga yau ina son ki cigaba da kula da wannan bakon mara lafiya, har izuwa lokacin da zai samu lafiya muji labarinsa, domin a can bayan gari na tsinto shi a cikin korama bisa allon jirgi an harbe shi da kibiya in ba dan yana da nisan kwana ba da tuni ya hallaka. " Koda jin wannan batu sai gimbiya lasmin ta cika da tsananin mamaki, sannan ta dubi sarki mushlik tace, "Lallai zan kasance mai biyayya ga wannan umarni haka. " Sarki mushlik yayi murmushi, gami da dafa kafadar lasmin yace, "Na san da haka, domin baki taba bani kunya ba. " Koda gama fadin hakan sai sarki mushlik ya juya ya fice daga cikin dakin, fitarsa ke da wuya sai lasmin ta zauna akan gefen gadon ta kurawa. Mara lafiyar idanu a lokacin data ji ta kamu da tsananin tausayinsa. Fitar sarki mushlik ke da wuya, sai ya wuce izuwa lambunsa, domin ya zauna a ciki ya huta. Tun daga nesa ya hango yarima zamir a cikin lambun tare da kannansa suna wasan 'yar buya. Yarima zamir yarufe idanunsa da tsumma yana ta laluben yaran har suna dungurinsa yana faduwa kasa suna ta yimasa dariya. Koda ganin wannan al'amari sai takaici ya kama sarki mushlik har kwalla ta zubo masa. Kawai sai ya fasa karasawa cikin lambun ya juya da baya ya nufi fadarsa. Da isar sarki fadarsa sai ya iske gaba dayan fadawansa a zaune basu watse ba, alhalin tuntuni lokacin tashi daga fadanci yayi. Al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan, ya dube su yace, "ina dalilin zamanku a fada har yanzu?" Koda jin wannan tambaya sai waziri ya mike tsaye yace, "Ya shugabana mun tsaya ne domin muji hukuncin daka yanke bisa wasikar da sarki hasanul mauzur ya aiko. " Da jin haka sai sarki mushlik yayi shiru yana tunani tsawon 'yan dakiku. Daga can sai ya dago kai ya dubi gaba dayan 'yan majalisar yace aje a yi shela duk wanda yake da bukatar shiga wannan gasa ya je yayi shiri na kwana bakwai sai su taru a nan fada ta sannan su dunguma gaba daya su tafi koda gama fadin haka sai sarki mushlik ya juya da nufin ya fita daga cikin fadar, amma sai waziri yayi gyaran murya yace, "Ya shugabana shin babu wanda zai wakilce ka ne a cikin wannan gasa? Ka sani cewa duk mutumin da y sami nasarar lashe wannan gasa sai yayi daukakar da babu wani mahaluki da zai yi kamar ta a wannan zamani. Ina ganin cewa bai kamata a ce kabar wannan dama ta wuce kaba. " Yayin da sarki mushlik yaji wannan batu sai ya juyo ya dubi waziri yayi murmushi, yace, "Zan yi matukar farin ciki idan danka jarumi haslim ya lashe wannan gasa. " Kafin waziri ya bude baki ya kar cewa komai, tuni sarki mushlik ya dufi kofar fita daga ya fice gaba daya. Al'amarin da yasa jikin waziri ya yi sanyi kenan, ya dubi sauran 'yan majalisar suma sai suka sunkui da kawunansu kas ba su ce uffan ba. Jarumi haslim sadauki ne na gaske wanda ake takama da shi a birnin dumur, sarki mushlik ne ka dai aka tabbatar da cewa yafi shi sadaukantaka da karfin sihiri. A duniya babu abin da jarumi haslim ke so sama da gimbiya lasmin, amma duk sa'adda yayi mata maganar SO, babu abin da ke biyo baya face bakar magana ko zagi a tsakaninsu. Har sai da ta kai cewa sarki mushlik ya kira jarumi haslim ya yi masa kashedin karshe a kan cewa ko kallon gimbiya lasmin ya kara yi yayi mat murmushi zai fuskanci hukunci. Bisa dole jarumi haslim ya daina bin hanyar da lasmin kebi, kuma ko wani taro za a yi idan har zata je wajen tofa shi baya zuwa kullum dare darana da wannan bakin ciki yake kwana. Shi kuwa mahaifinsa wato waziri sai ya shiga rarrashinsa yana mai kwantar masa da hankali, kuma ya tabbatar masa da cewa in dai yana raye sai ya aura masa 'yar sarki wacce tafi gimbiya lasmin kyau da matsayi. Lokacin da waziri sharabul yaji bayanin da sarki yayi sai ya cika da tsananin farin ciki, saboda ganin cewa lokaci yayi da zai cikawa dansa alkawarin da ya daukar masa. Ma'ana zai tura jarumi haslim izuwa wannan gasa kuma zai nema masa sa'a a wajen bokaye. A gaba daya birnin dumur babu attajiri kamar waziri sharbul, saboda haka a tunaninsa zai iya siyawa dansa haslim sa'a a wajen bokaye bisa wannan gasa da za a tafi. Bayan fada ta watse waziri sharbul ya isa gida sai ya kirawo dansa jarumi haslim ya sanar da shi duk abinda ya faru tsakaninsu da sarki a fada don haka sai ya umarci jarumi haslim daya yi shirin tafiya ta kwana biyu domin ziyartar manyan bokayen kasar su hudu cikin tsananin farin ciki jarumi haslim yaje yayi shiri cikin gaggawa bayan ya gama kimtsawa, sai waziri sharbul ya kawo dinare mai yawan gaske jaka hudu ya bashi sannan ya kama hanya ya tafi izuwa garurun hudun da manyan bokayen kasar suke. Al' amarin gimbiya lasmin kuwa, bayan sarki mushlik ya fita ya bar ta a dakin mara lafiya ta zauna a gefen gadon ta kura masa ido har tsawon 'yan dakiku sai taji an kwankwasa kofar dakin cikin sauri lasmin ta waigo, koda tayi arba da wanda ke shigowa sai ta juyar da kanta ga barin kallon mai shigowar. Ba wani bane ya shigo face hizra 'yar likitan sarki tana dauke da wata tukunyar kasa cike da rwan magani. Hizra ta tako a hankali ta iso har gaban gimbiya lasmin, sannan ta risina ta kwashi gaisuwa. Cikin jin kai da dagawa lasmin ta amsa gaisuwar batare da ta dubi fuskar hizra ba ita kuwa hizara sai ta tsaya a tsaye cak batace uffanba kuma bata yi komai ba. Cikin fushi lasmin ta dago kai ta dubi Hizara cikin fushi tace, "Ki a jiye abinda aka aiko ki ki kawo ki tafi, me kika tsaya jira?" Koda jin wannan tambaya sai hizara ta sake risinawa cikin biyayya tace , "ya shugabata akwai. Bukatar nayi bayanin yadda za a bai wa mara lafiyar kamar yadda mahaifina yayi mini bayani. " Koda jin haka sai lasmin ta saki fuskarta ta ce, "Maza kiyi bayanin ina sauraronki. " Hizara tace, 'Bayani kadai ba zai gamsar ba sai a aika ce. Da farko dole ne a dafa wannan magani sau uku a rana a ba shi ckin kofi ya shanye, kuma lallai da duminsa za a bashi ya sha. A duk sa'adda aka bashi maganin ya sha sai kuma a mulke kirjinsa da bayansa da ruwan maganin. Yana yin mulka maganin dole ne a dunga danna fatar mara lafiyar ana lailayata sai tayi taushi sosai, domin maganin ya ratsa ta cikin dukkanin kofofin gashin jikiNsa. " Sa'adda gimbiya lasmin taji haka sai ta tari numfashin hizara tace, "Duk da haka ina son ki yi wannan aiki a aikace, domin ban fashimci yaza a yi shi ba" Nan take hizar ta dauko kaskon wuta ta dora tukunyar maganin akai. Dama akwai garwashi a cikin kaskon wanda ake dumama dakin da shi. Sai da tukunyar ta sami tsawon dakiku a kan kaskon, sannan ruwan maganin dake ciki ya tafasa. Nan take, hizara ta dauko kofin zinare ta zuba ruwan maganin a ciki, sannan ta balle maballin rigarsa ta sake debo ruwan maganin cikin kofin da zafinsa ta rinka zubawa a kan kirjin mara lafiyar da kadan- kadan tana mulkawa, tana danna fatarsa. Nan da nan kuwa ruwan maganin ya dinga shigewa ta cikin kofofin gashin jikinsa. Bayan ta gama mulke kirjin sai ta juya mara lafiyar yayi ruf da ciki ta kwaye rigarsa nan ma ta mulke bayan da ruwan maganin bayan ta gama tsaf, sai ta ajiye kofin a kusa da tukunyar maganin, kuma ta rufe tukunyar da murfinta. Sannan ta dubi gimbiya lasmin tace, "Na kammala ya shugabata. Wannan shine yadda za a ringa yiwa wannan mara lafiya, har tsawon kwana bakwai. " Koda jin haka sai lasmin tayi ajiyar zuciya, sannan ta dubi hizara tace, "daga yau na umarce ki da kullum ki zo sau uku a rana kiyi wa wannan mara lafiya abin da kika yi masa yanzu, har tsawon kwana bakwai. " Cikin alamun damuwa hizara tace, "Amma mahaifina ya gaya mini cewa kece zaki kula da mara lafiyan." Lasmin tace, "Wannan gaskiya ne ba karya ya gaya miki ba, amma yanzu nima na umarce ki da wakilci na. A matsayina na 'yar sarki bai kamata na yi wa bako irin wannan aiki ba. Lallai ki kiyaye wannan doka, kada ki kuskura kiyi fushi ko da sau daya ne a rana." Gama fadin hakan keda wuya sai gimbiya lasmin ta mike tsaye ta fice daga cikin turakar kafin ta fice sai da ta juyo ta dubi mara lafiyar ta yi masa wani irin kallo mai dauke da alamar tambaya, wanda yasa ita kanta Hizara ta tsargu kuma tayi zargin cewa ruwa baya tsami banza, amma kuma bata da tabbacin abin da take zargi. ««« TARWATSA MAZA-2 TYPE E »»» Daga wannan rana kullum gimbiya lasmin sai ta shiga dakin bako sau uku, kuma a gaban idanunta hizara ke kula da bakon tana yi masa magani. Sai da aka kwana hudu a cikin wannan hali, amma bakon ko bude idanunsa bai yi ba, bare ya motsa hannunsa ko kafafunsa. Ta hanyar da hizara ke ganewa cewa yana da rai sai ta kara hancinta a dai-dai nasa sannan take jin alamun numfashinsa. A daren kwana na hudu ne da magariba bayan hizara ta gama yi wa mara lafiyar magani sai gimbiya lasmin tariga ta fita daga cikin dakin a ka'ida kullum da magariba kafin hizara ta fice daga dakin sai ta lullube bakon da mayafi iya kirjinsa, amma a wannan rana sai ta manta ba ta lullube shiba. Har ta kai bakin kofa tasa kafarta guda waje sai kawai taji kamar anyi motsi a cikin dakin. Cikin mamaki hizara ta waigo ta dubi mara lafiyan ta ga babu alamar shi ne yayi motsin, yana kwance kamar gawa. Ta karewa dakin kallo tsaf gabas da yamma kudu da arewa bata ga wani abu mai rai ba kawai sai ta sake juyawa da nufin ta fice ta janyo kofar dakin ta rufe. Ba zato ba tsammani sai ta ji mara lafiyan yayi tari. Cikin tsananin farin ciki ta ruga da baya gare shi taje kansa ta tsaya, nan take mara lafiyan ya bude idanunsa suka dubi juna har yayi mata wani irin kallo mai kama da na tsoro, sannan ya dubi kowacce kusurwa ta dakin sai ya rufe idanunsa bai sake motsawa ba, bare ya sake bude idanun nasa. Koda ganin haka sai hizara tayi murmushi, domin ta fahimci cewa lafiya ta fara samuwa. A sannan ne ta lura da cewa ta manta bata lullube shiba. Nan take ta janyo mayafin ta lullube shi iya kirji, kamar yadda ta saba, sannan ta sunbaci goshinsa ta fice daga cikin dakin, zuciyarta cike da mamaki bisa dalilin da yasa take matukar farin ciki bisa ganin mara lafiya ya fara samun sauki. Hizara ta bai kanta amsa a cikin zuciyarta tace hakika na fuskanci cewa na shakuda wannan bako a cikin kwana hudun nan rak da nake jinyarsa. Watakila ko dan ya kasance kyakykyawa ne, domin ko yarima zamir bai fishi kyau ba. Haka dai hizara ta fice daga cikin gidan sarautar tana ta wannan zancen zuci. Daga wannan rana kullum sai mara lafiyan ya bude idanunsa sau daya da magariba yayi arba da mai jinyarsa, wato hizara, kuma wani ikon allah bai taba bude idanunsa ba a gaban gimbiya lasmin, sai bayan ta fita. Haka kuma yakan motsa kafarsa da hannunsa sau dai-dai a kullum sarki mushlik yana shigowa dakin mara lafiyar ya duba shi kuma ya tambayi gimbiya lasmin ko ana samun cigaba sai tace dashi sauki take gani. Raunin dake jikinsa sakamakon kibiyar data soke shi ramin na cikewa. A ranar kwana bakwai ne fadar sarki mushlik ta cika da jarumai na kasar, zaratan samari masu takama da sadaukanta ka. Arziki da tsafi amma a ga ba dayansu babu kamar haslim dan waziri sharbul, domin duk ya fisu sadaukan taka kuma babu mai arzikin mahaifinsa. Wato a wannan rana mutane sun zo daga dukkanin birane kasar don ganin samarin da zasu yi wannan gagarumar tafiya izuwa birnin sharzas don shiga gasar neman auren gimbiya shulaira, don haka duk inda mutum ya duba ba abinda zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masakar tsinke. Ga shidai jama'a sun gama taruwa, amma har tsawon dan lokaci sarki bai fitoba, bare ya gabatar da jawabin taron. Al'amari daya janyo mutane suka kagu da jiran sarki kenan. A she sarki mushlik tsananin ta kaici ne ya hana shi fitowa, saboda ga dama ta samu wacce yake son ya dora yarima zamir a kai, amma babu ikon amfani da damar. Bisa wannan dalili ne sarki mushlik ya zauna a cikin turakarsa yayi tagumi yana zubar da hawayen bakin ciki. Yana cikin wannan hali ne kawai yaji motsin tafiya an shigo cikin turakar tasa. Cikin mamaki sarki mushlik ya dago kai don ganin wanda ke shigowa. Ba wani bane face yarima zamir. Koda ganinsa sai sarki yayi sauri ya goge hawayensa ya mike tsaye ya tare shi ya ruke kafadunsa yace, "Ya kai dana menene ya kawoka har nan cikin turaka ta? A iya sanina baka taba shigowa cikin turakata ba, sai yau." Koda jin wannan tambaya sai yarima zamir yayi ajiyar zuciya yace, "Ya kai abbana nazo ne naji dalilin da yasa kaki fita fada, alhalin jama'a na can suna jiranka?" Yayin da sarki yaji wannan tambaya sai idanunsa suka ciko da kwalla, har

Please Login or Register in order to submit comment