Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sami damar fita daga cikinsa. Abin da zance da kai kawai shine, ince koka bar wasiyya a gida kafin muyi wannan tafiya?". Yayinda naji wannan tambaya, sai na bushe da dariya, al'amarin daya baiwa dukkanin fursunonin aljanun mamaki kenan, domin gashi su a matsayinsu na aljanu, suna kuka saboda sun shiga bala'In da babu fita, amma ni a matsayina na bil'adama ina dariya. Ti me nake takama dashi? Shin ina zaton zan iya fita ne daga cikin wannan masifa? Amsar da basu sani ba kenan, amma dai ai tunda suna tare dani zasu zuba ido su ga iyakar gudun ruwana. sHIN HASANUL MAUZUR DA ALJANI BARZILA ZASU KUBUTA DAGA HANNUN DODO GURMAZU, HAR HASANUL MAUZUR YA KASHE WANNAN GIWA TA DODO GURMAZU, YA YANKO HARSHENTA? WADANNE SAMARI Ne ZASU SHIGA GASAR NEMAN AUREN GIMBIYA SHULAIRA, KUMA DAGA CIKINSU WAYE ZAI CI GASAR YA ZAMO MIJINTA. Muhadu a TARWATSA MAZA littafina biyu don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. ««« TARWATSA MAZA-2 TYPE A »»» Wa dansu sandunan karafa da ke zube a kasa gudu uku a cikin kejin. Da ganin wadannan karafa a salinsu makamai ne na irin fursunonin dodo gurmazu. Nan take na dau biyu daga cikin karafan na dunga bugasu a kan guda, wato na maishesu gangar kida. Bisa mamaki sai naji dajin gaba daya ya kaure da kidan nawa har karfin kidan ya danne munsharin dodo gurmazu cikin tsananin fushi sauran aljanun nan su dubu biyu suka yunkura suka taso mini kamar zasu cinyeni danye ni kuwa sai nayi wuf na zare takobina nace, "Na rantse da karfin sihirina duk wanda ya iso kaina sai dai uwarsa ta haifi wani. " Da farko sun yi tsammanin cewa kuri nake bazan iya hallaka daya daga ciknsu ba, don haka sai biyu suka afko mini ai kuwa sai nasa takobina na saresu. Take jikinsu ya zagwanye suka zama kwarangwal. Koda ganin abin da yafaru sai sauran gaba daya suka ja da baya a tsorace suka yi cirko-cirko kamar bera ya ga kyanwa suka kama karkarwa. Duk wannan abu dake faruwa aljani barzila na zaune a gefe daya yana din lonmu kawai bai ce uffanba ya zuba ido kawai yaga iyakar gudun ruwana. Daya daga cikin aljanun ya dube ni cikin alamun tsoro da damuwa kamar zai fashe da kuka yace, "Ya kai wannan hatsabibin bil'adama kayi sani cewa wannan kidan daka kama yi ba karamin tashin hankali bane a garemu gaba daya domin zai iya sawa ka farkar da dodo gurmazu daga barci. Idan kuwa ya farka a fusace zai fito ya bude kejin nan ya cinye wasu daga cikinmu a wannan dare ba tare da ya bari ya wayeba. " Koda naji wannan batu sai na bushe da dariya nace, "Amma dai kun cika gaulaye, shashashu. In ban da abinku menene banbancin mutuwar dare da ta safiya? Ai ni yanzu nafi soma dodo gurmazu ya cinyeni da wuri, domin na huta da fargaba. Don haka ba zan fasa yin wannan kida ba, burina shi ne ya tashi yaji na hanashi barcin domin ya kawar dani da wuri. " Koda gama fadin hakan, sai naci gaba da buga wadannan karafuna. Ai kuwa sai dajin ya sake kaurewa da karar karafan tamkar ana aiki a makera Dodo gumurzu na cikin barcinsa sai yaji kunnensa ya dameshi, a sakamakon kidan da nake yi bai san sa'adda ya mike zaune zumbur a fusace. Koda ya gane cewa daga cikin kejin fursunoninsa wannan kida ke tashi sai ya harzuka ya mike tsaye zumbur ya fito daga cikin bukkarsa a matukar fusace ruke da fitilar ice ya nufo inda kejin yake, ni kuwa na cigaba da kidana ban fasa ba, harya iso gaban kejin ya sunkuyo da kansa yayi arba da ni ina ta faman kida tamkar a cikin gidana nake al'amarin daya matukar ba shi mamaki kenan musamman daya ga nayi ido biyu dashi, amma ban fasa yin kidan ba. Nan take gurmazu ya daka mini tsawa wacce tasa na firgita ainun na ji kamar hantar cikina zata fado kasa daga cikin bakina. Su kuwa su aljani barzila sai duk suka koma gefe daya suka cakude suka mammanne da juna suna kyarma. Ni kam a zuci ne na firgita amma a zahiri babu alamar tsoron komai a tare da ni face murmushi a fuskata, sai dai na tsaya cak ga barin kidan na kurawa gurmazu idanu. Gurmazu ya dubeni da kyau sama da kasa, sannan yace, "Ya kai wannan hatsabibin bil'adama kayi sani cewa fiye da shekaru hamsin baya ban taba kama fursunan daya tasheni daga barci ba sai kai lallai ka tsokanowa kanka masifa da bala'I mara misaltuwa idan gari ya waye sai nayi maka mummunan kisan da ban taba yiwa wani ba". Sa'adda dodo gurmazu yazo nan a zancensa sai na kyalkyale da dariya al'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan, kuma ya baiwa sauran aljanun mamaki. Lokaci guda kuma na murtuke fuska nace da shi, "Ai idan ka bari sai da safe zaka dau mataki a kaina baka burge niba yanzu a daren nan nake son ka hallakani idan za ka iya ka sani cewa ko kadan bana shakkar ka kuma ina tabbatar maka da cewa lokacin daka kama ni shammata ta kayi, In ba don hakaba tuni na hallaka ka". Koda jin wannan batu sai dodo gurmazu ya cika da tsananin mamaki ya kura mini idanu sosai ya kasa cewa komai. Daga can sai ya bushe da dariya tamkar ana ruwan kwarankwatsa daga sama ya dubeni yace, "Tabbas barewa bata yin gudu danta yayi rarrafe. Ya kai wannan bil'adama ka yi sani cewa, kai tsatson wani hatsabibin bil'adama ne da na taba kashewa a wasu shekaru da dama da suka wuce, domin na ga kuna kama matuka kai da shi, tamkar an tsaga kara. Bari na nuna ma wani abu." Gama fadin hakan ke da wuya sai dodo gurmazu ya juya ya koma cikin bukkarsa jim kadan sai gashi ya fito ruke da sandar nan ta mulki ta masarautata. Ita dai wannan sanda anyi tane da zallar farin karfe na lu'u'lu'u. Nan da nan hasken sandar ya gauraye dajin gaba daya tamkar safiya ce ta yi badare ba. Sandar ita kadai kyalkyali take da sauya launi, kai dagani kasan sandar sihirice. Daga saman sandar kotace, kasanta kuwa tsinine, tamkar mashi. Dodo gurmazu ya karaso daf da kejin da muke ciki ya tsuguna yana mai nuna mini sandar yace, "ka san wannan?" Koda jin wannan tambaya sai na kyada kai cikin alamun takaici da bakin ciki a lokacin da idanuna suka ciko da kwalla nace, "Kwarai kuwa na san wannan sanda mallakin mahaifina ce, kuma kai ne ka kashe shi kara bashi da wannan sanda ka sani cewa nazo wannan daji ne domin na dauki fansar ran mahaifina kuma na karbi wannan sanda a hannunka na mai da ita masarautarmu. " Koda jin haka sai dodo gurmazu ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda ta haddasa karamar girgizar kasa a dajin gaba daya har sai da ya tsuke bakinsa sannan dajin ya tsaya cak. Gurmazu ya dube ni yace, "Hakika kayi wauta har da kake tunanin daukar fansa a kanmu domin nine karo da dubu ko dubu ta taru sai hakuri hakika ka fusatani irin fusatar da ban taba yi ba a rayuwata amma sai gari ya waye sannan zan nuna maka irin fushina ba ma kai ba hatta wadannan fursunoni 'yan uwanka ka shafa musu kashin kaji. " Gama fadin hakan keda wuya sai gurmazu ya lura da gawar aljanun nan biyu da na kashe a cikin kejin cikin tsananin fushi ya dubemu gaba daya yace wane ne ya bata mini abincina haka daga cikin ku?" Kawai saina yi farat nace nine kuma ina tabbatar maka da cewa yadda na bata maka wannan abinci haka kai ma zan zare maka rushin numfashinka. Idan har ka isa kai jarumine ka fito dani yanzu daga cikin kejin nan mu yi yaki gaba da gaba. " Sa'adda dodo gurmazu yaji wannan batu daga bakinsa. Sai idanunsa suka matso kwallar takaici. Domin tun da ya wanzu a duniya ba a taba yi masa irin wannan rashin kunya ba. Cikin tsananin fushi ya dube ni bakinsa na karkarwa yace, "Kaicon ka yaro hakika kayi babbar sa'a domin dokar tsafina ta hana ni yin komai da daddare. Amma ka kiyayi wayewar gari, domin sai na maisheka misali a kan dukkan sauran bil'adama masu girman kai a duniya. " Koda gama fadin haka sai dodo gurmazu ya juya ya nufi bukkarsa ruke da wannan sandar mulkin ta mahaifina. Koda na ga haka sai na cigaba da kidana har gurmazu ya shiga cikin bukkarsa ban fasa ba. Kai a takaice dai sai da na kwana ina wannan kida, ban runtsaba su kansu su aljani barzila na addabesu. Dalilin da yasa nayi haka kuwa, shine ko ba komai na san cewa na hana dodo gurmazu barci a wannan dare don haka ya kwana da mugun bakin ciki bazan mutu a banza ba, naci ribar hanashi barci. Kashe gari kuwa, da sassafe dodo gurmazu ya zo ya fito daga cikin bukkarsa. Ina kallonsa na ga idanunsa sun yi jajur kai da gani kasan cewa bai samu barci ba, kawai sai na bushe da dariyar mugunta dodo gurmazu ya nufo kejin da muke ciki a fusace yayin dasu aljani barzila suka tsinke da gudawa gaba dayansu, saboda tsananin razana, nikuwA sai na mike tsaye na rike kuguna da hannu biyu cikin takama da jinkai "al'amarin da ya bawa dodo gurmazu mamaki kenan, yace aransa to waishi wannan yaro menene madogararsa ? Ni kuwa zan bashi dama mu fafata yaki domin naga iyakar abin da yake dogaro da shi. Yayin da dodo gurmazu ya iso daf da kejin yaga har a sannan ban ji tsoron komai ba ina tsaye cak ina kallonsa kawai sai yasa hannunsa guda ya bude kejin a lokacin da daya hannun nasa. Ke ruke. Da katon sunguminsa na yaki ya ce dani. "Kai yaro fito naga iya takamarka, ga shi dare ya shude gari ya waye. " Ba tare da fargabar komai ba na fito daga cikin kejin na tsaya a gaban gurmazu tamkar kare ya tsaya a gaban giwa saboda banbancin girma jikinmu. Gurmazu ya dubeni sama da kasa sai ya kyalkyale da dariya, sannan ya turbune fuska ya ce, "Na baka dama idan bazaka iya yakata baka falfala da gudu a cikin wannan daji har izuwa tsawon sa'a guda sannan zan biyo ka na kama ka nayi. Maka irin kisan da nakeso. Idan kuma kana ganin cewa zaka iya yaka ta to mu fara wanne ka zaba?" Koda jin wannan zabi sai na yi shiru ina tunani domin na san cewa wannan fa ita ce dama tata karshe. Abu na farko ni kam na tabbatar da cewa karfin damtsena dana sihirina baza su taba kubutar dani ba a wajen dodo gurmazu domin ya ninka ni sau dari a wannan bangare. Yanzu menene mafita? Kwazam sai wata dabara ta fado mini wacce bani da tabbacin zata yi tasiri, amma da na tuna cewa sai an gwada akan san na kwarai sai. Kawai na duba dodo gurmazu nace, "Na zabi ka bani damar na falfala da gudu in yaso ka kure mini gudun ka kasheni. " Koda jin haka sai dodo gurmazu ya bushe da dariyar mugunta yayi ta kyalkyalawa kamar bazai daina ba, har sai da hawaye ya zubo masa, sannan ya turbune fuska ya maida kofar kejin ya rufe su aljani barzila suka dada firgicewa suka cigaba da tsula gudawa. Gurmazu ya dubeni yace, "Haba yaro yaya zaka yi saurin sallamawa haka. Lallai baka gaji ubanka ba, domin shi ya jarraba yin yaki dani har yasamu nasarar shafe dakika dari uku muna fafatawa. Tabbas na jinjina masa sHi na mijine amma hargobe idan na tuna irin kisan dana yi masa yana bani tausayi. " Koda jin wannan batu sai na ji zuciyata ta harzuko cikin fushi na tambayi gurmazu nace, "Wanne irin kisa kayi masa? Gurmazu yace, "da na soka masa farcen dan yatsana a cikin bakinsa sai da ya fito ta cikin duburarsa a haka ya sankame jikin hannuna ya zama gawa, kuma a hhakan na gasa shi a wuta na rinka gutsurarsa da kadan-kadan ina ci har sai da ya kare tas. " Koda jin wannan batu sai na kwarma uban ihu, kuma na fashe da kukan bakin ciki. Dajin kukana sai dodo gurmazu ya cigaba da kyalkyala dariya, sannan ya zauna dirshan kasa ya runtse idanunsa yace, "Na baka dama yaro ka ruga da gudu kayi ta gudun har tsawon sa'a guda, lallai zaka riskeni a gabanka. " Koda jin haka kuwa sai na falfala da gudu maimakon na nausa cikin daji saina nufi cikin bukkar dodo gurmazu, shikuwa gurmazu bai lura da hakan ba, domin idanunsa a rufe suke yana ta kirga dakikoki, jira yake kawai sa'a guda tacika. Kuyi hakuri bisa tsallaken da kuka gani wannan ya farune sakamakon matsalar fage din ««« TARWATSA MAZA-2 TYPE B »»» Lokacin dana shiga cikin bukkar dodo gurmazu sai nayi arba da kwarangwal na kawunan bil'adama dana aljanu birjik barkatai ba adadi, kuma a jere layi-layi koda na dubi wadannan kawuna sau na fahimci cewa a dadinsu shine adadin mutanen da aljanun da ya cinye a zamansa cikin wannan daji na shjaril maurud nan fa naci gaba da bincike a cikin bukkar ina neman wannan sandar sarauta ta ubana, amma ko alamarta ban gani ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalina kenan. Kwazam sai naga wadannansu hakora na dodo gurmazu guda hudu a ajiye a gefe daya. Ko wanne guda daya ya kasance mai tsawo tsini da kaifin tsiya. Na dubi hakoran da kyau nayi nazarinsa sai na gane cewa duk abin da aka karta ko aka sara sai ya rabe biyu ko ya huje komai karfinsa. Kawai sai na wuce hakoran na cigaba da neman wannan sanda. Kwazam sai naga wata akwatun sihiri wacce aka rufe ta bam da katon kwado mai kauri da girma, wanda inda karti arba'in zasu taru majiya karfi bazasu iya daga shi sama ba. Nan fa na shiga lalube ko zan ga kubar da aka rufe kwadon da ita, amma ko alamarta ban gani ba. Alqkamarin daya dugun zuma hankalina kenan domin a wannan lokaci na tabbatar da cewa baifi saura dakika dari biyu ba dodo gurmazu ya bude idanunsa,ya nemeni a inda nake, nan take nayi amfani da karfin sihirina , domin na bude wannan kwado, amma sai abu ya faskara. Koda na juyo baya na dubi wadannan hakora guda na dodo gurmazu sai dabara ta fadomini. Da gudu na ruga na dauko hakori guda na sari wannan kwado. Take kwadon ya karye ya fadi kasa. Karar sarar kwadon kuwa ta cika dajin gaba daya. Al'amarin da yasa dodo gurmazu ya bude idanunsa kenan ya kallo cikin bukkarsa. Cikin tsananin zafin nama na daga murfin akwatin nayi arba da wannan sandar sarauta. Ai kuwa sai nayi wuf na dauko ta. Kafin na juyo sai naji an yi bal dani nayi sama na fasa sai dana yi sama sosai, sannan na rikito kasa baje wanwar, idanuna na gani dishi-dishi, gaba daya jikina yayi tsami tamkar a cikin turmi aka daka ni. Amma saboda naci ina ruke da wannan sandar sarauta. Kawai sai ganin dodo gurmazu nayi tsaye akaina. Kafin nayi wani yunkuri ya kawo mini suka da farcen hannunsa izuwa cikin bakina. Cikin tsananin zafin nama na goce ya soki kasa yatsan nasa ya nutse gaba daya azuwa cikin kasa. Koda ya zare hannun nasa sai wajen ya zamo rami mai zurfi tamkar an haka rijiya mai tsawon kamu dubu nikaina nayi mamakin yadda aka yi na samu gawurtaccen zafin nama dana gocewa wannan mugun hari nasa. Abinda bansaniba shine, wannan sandar sihiri dake hannuna ita ce ta taimaka mini nanfa muka cigaba da mugun artabu ya zamana cewa dodo gurmazu na kawo mini suka da sunguminsa yayin da na goce ya soki kasa ko ya dake ta sai ya haddasa rami, gami da girgizar kasa. Nan da nan ya tashi hankalin dajin gaba daya ya zamana cewa duk wata halitta mai rai da ke cikinsa ta suma sau ba adadi, domin su aljani barzila kuwa a wannan lokaci suna kan suma na arba'in da hudu. Sai da muka shafe sa'a hudu muna wannan gumurzu, a sannan ne gurmazu ya fara samun nasarar yankar jikina da kaifin faratansa ya zamana cewa yayi mini munanan raunika guda bakwai, sai jini ne ke zuba a jikina har jiri ya fara diba ta, kuma a sannan ne ya fara kokarin kwace wannan sandar sihiri dake hannuna, amma saboda naci sai naki yarda ya kwace sandar. Muna cikin wannan gumurzu ya shammace ni ya kwada mini mari a fuska , saboda karfin marin sai dana yi katantanwa sau uku a sama sannan na fado kasa na baje ko motsin kirki ban yi ba. Cikin tsananin murna dodo gurmazu ya bayyana a gabana ya sunkuyo da fuskarsa, kuma ya tallafo kaina da hannunsa guda ya ajiye sunguminsa a gefe daya. Kawai sai ya daga danyatsansa guda da nufin ya soka mini farcensa ta cikin bakina, don ya yi mini irin kisan dayayi wa mahaifina. Bazato ba tsammani, sai gurmazu yaji na suka masa tsinin wannan sandar sihiri dake hannuna a cikin bakinsa har sai da ta hudo keyarsa. Gurmazu ya kwarara uban ihu wanda ya haddasa kakkaryewar bishiyoyin dajin. Gurmazu ya dunga tsalle yana tumuwa da kasa ya sake haddasa girgizar kasa. A lokacin ne nayi zumbur na mike tsaye na koma gefe daya ina kallon yadda yake ta matagungun. Sai da gumurzu ya shafe rabin sa'a yana birgima a kasa gami da daka tsalle sama yana fadowa sannan ya baje akasa yayin da jini ke ta malala daga cikin kokon kansa, amma saboda taurin rai yaki mutuwa yana ta shure shure a hakan ya juyo da kansa ya dubi inda nake. Sannan ya dude baki yace, "Ya kai magajin ubansa kayi sani cewa ba zan taba mutuwa ba face kazo ka cire wannan tsafin daga cikin bakina idan kuwa ka bar ta har tsawon rabin sa'a nan gaba zan mike tsaye. Tamkar wani abu bai same niba, na hallaka ka. " Koda jin wannan batu sai hankalina ya dugunzuma na nufi inda dodo gurmazu ke kwance da nufin na zare wannan sandar sihiri. Da zuwana daf da shi sai na kai hannu zan zare sandar, amma sai sai na fasa, domin ji nayi zuciyata ta daka mini tsawa tace dani "A kul! Kayi amfani da zancen wannan azzalumin dodo, domin babu mamaki idan ka zare sandar daga cikin bakinsa ya rayu. " Kawai sai naja da baya na dubi dodo gurmazu nayi masa murmushin mugunta nace "Zan jira har rabin sa'ar ta cika sannan na ga yadda zaka iya hallaka ni. " Lokacin da dodo gurmazu yaji wannan batu, sai hawaye ya zubo a idanunsa yace, "Yaro tabbas yau kaga karshena, domin ka karya tasirin sihirina. Inda kayi kuskuren zare wannan sanda daga cikin bakina da tuni duk digon jinina daya zuba akasa ya zamo irina guda tabbas kacika gwarzo abin jinjinawa a wannan zamani. Duk bukatar da kasa a gabanka sai ta biya kasani cewa nan da cikar rabin sa'a zan mutu kuma irin mutuwar da mahaifinka yayi ita zan dandana. Alfarma daya zan roka a wajenka ina son idan na mutu ka kone gawata, kuma koda kasusuwan jikina sun yi saura ka binne su a cikin kasa yadda zasu rube da sauri. " Koda naji wannan batu sai na bushe da dariyar farin ciki nace, "Ya kai wannan azzalumin dodo, wanda ya shafe shekara da shekaru yana kashe mutane da aljanu kayi sani cewa tsakanina da kai har abada babu alfarma, don haka a inda ka mutu din nan a nan zanbar gawarka har ka rube. Ka zama kwarangwal, domin mutane da aljanu su yita ganinka ka zamo abin tunawa. " Gama fadin haka keda wuya sai jiri ya kwasheni na bingire kasa sumamme. Ban farfado ba sai bayan sa'a guda. Ina bude ido naga dodo gurmazu ya zama gawa, bakinsa a wangame har tsuntsaye sun fara tsatstsagar jikinsa. Ni kaina tsuntsayen sun fara kawo mini hari, domin suna zaton na mutu sai da suka ga na yunkura sannan suka tashi fir. Da jan ciki na isa inda gawar dodo gurmazu take na zare wannan sandar sihiri daga cikin bakinsa sannan na sake jan ciki na isa kejin dasu aljani barzila suke ciki. Da kyar da sidin goshi na mike tsaye na sare kofar kejin da sndar ta bude. Cikin tsananin farin ciki su aljani barzila suka fito daga cikin kejin suka kama tsalle da murna tsira da rayuwarsu. A sannan ne na sake faduwa kasa sumamme. Sai da su aljani barzila sukayi jinyata tsawon kwana bakwai a cikin dajin shajaril murud sannan na sami lafiya na dawo cikin hayyacina. A ranar da nasami lafiya ne wadannan aljanu guda dubu biyu fursunonin dodo gurmazu suka yi alkawarin cewa daga yau sun zama bayina kuma duk ranar da nake bukatar su suyi mini wani aiki na nemesu. Bayan aljanun sun tafi sai na bukaci aljani barzila. Daya shiga cikin bukkar dodo gurmazu zai ga wannan giwa da yake kiwo a ciki ya kashe giwar ya yanko harshenta ya kawo mini. Nan take kuwa aljani barzila yaje ya cika wannan umarni a cikin abin da bai wuce dakika dari da ashirinba. Ba tare da bata lokaci ba aljani barzila ya goya ni a bayansa ya bude fuka- fukansa ya tashi sama muka nufi birnin sharas. Tun kafin mu isa gida boka surub ya ga duk irin nasarar dana samu a cikin madubin tsafinsa don haka shine mutum na farko daya tare mu a cikin fada ta. Muna sauka a kasa ya rugo izuwa gare ni ya rungumeni yana mai yi mini barka bisa samun nasara. Ba tare da bata lokaciba, boka surub ya karbi wadannan abubuwa uku dana samo ya zuba su a cikin tukunyar tsafi yayi ta dafa su har tsawon kwana tara. A daren kwana na tarane nayi tsirara na shafe jikina kaf da dafaffen maganin, sannan ya umarceni da tafiya makabarta. Nan take kuwa na tafi makabartar a cikin wannan tsohon dare na nemi kabari wanda ya shekara tamanin bai bajeba, kuma ba a taba haka shiba. Kawai sai na zauna a gaban kabarin na soka hannayena ba. Tsawon kwana ukun babu mahalukin da ya rabi kusa da makabartar walau mutum ko aljan saboda karfin mulkina da karfin sihirina bayan na kammala wannan aiki ne na ji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikina, irin wanda ban taba jin karfi ya shiga jikina, irin wanda bantaba jin kamarsaba a rayuwata domin na gwada karfin nawa ne na kirkiri yakuna bakwai da kasashenda ke makwabtaka da kasata. Duk sai da naci yakokin ko sau daya ba a kaini kasaba kuma ba a yi mini rauni daya ba, Bayan an gama yakokin ne na shirya walimar farin ciki ta musamman, saboda murnar abu uku. A bu na farko shine, na zama gawur taccen jarumin da babu kamarsa a duniya. Abu na biyu na sami nasarar dawo da sandar masarautar kasata, wacce dodo gurmazu ya kwace a wajen mahaifina, wanda a dalilin dawowar sandar arzikin kasata ya bunkasa ainun, a bu na uku shine, na dawo na iske 'yata wadda matata ta mutu ta bari a wannan shine a salin samun jarumtaka ta ta ban al'ajabi, sirrin da babu wanda ya sanda shi face boka surub sai kuma ke da na baki labari a yanzu, sa'adda sarki hasanul mauzur yazo nan a labarinsa sai gimbiya shulaira ta cika da tsananin mamaki kuma ta rungume shi tana mai fashe da kuka tace, "ya kai abbana hakika kasha bakar wahala a rayuwarka kuma ka ruke alkawarin ga mahaifiyata, har abada ba zan taba mancewa da irin wannan gwagwarmaya dakayi ba" Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki hasanul mauzur ya janye jikinsa daga jikin shulaira suka fuskanci juna sannan ya ce, "Ya ke 'yata kiyi sani cewa ni yanzu bani da wani sauran buri a duniya face naga kin auri miji wanda ya fini gwagwarmaya da daukaka a duniya, domin na

Please Login or Register in order to submit comment