Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

««« TARWATSA MAZA-1 TYPE C »»» Koda gama fadin haka, sai nayi bankwana da mahaifiyarki, na juya na fice daga cikin dakinta ban yarda na juyo na kalli fuskartaba, don na tabbatar cewa hawaye take zubarwa , in kwa na ga hawayen zuciyata zata sake karaya na Fasa yin tafiyar. Dama tun a daren jiya boka surub ya hadani da wani hadiminsa aljani barzila wanda zai yi mini rakiya acikin tafiyata domin ya zame min dan jagora, kuma mai debe mini kewa. Koda fitowa kofar fidan sarauta yayinda ake ta Cada wannan ruwan saman mai karfi sai aljani barzila ya baiyana agabana yana mai yi mini sujjada yace, "maza ka hau bayana ya shugabana zan baka kariya daga wannan ruwan sama". Ba tare da gardamar komai ba na hau bayan nasa na zauna. Shi kuwa sai ya bude biyu daga cijin fuka-fukansa shida yai sama dani, yana mai yi mini rumfa da fuka-fukai biyu. Take na jiruwan saman ya daina jikani. Nan fa muka fara keta giza-gizai muna ta tsala gudu a cikin gajimare. Abinka da al'amari na aljan a cikin abin da bai wuce rabin sa'a ba muka iso farkon daji na farko, wato dajin darul shazar inda rikakken goggon biri yake koda aljani barzila ya sauko kasa ya dira bisa turba nima na sauko daga kansa sai yakoma bayana ya rakube jikinsa na kyarma ace kyat ya fita da gudu. Al'amarin daya matukar bani mamaki kenan, na juyo na dubeshi nace meye haka saboda me zaka koma bayana ka ra kube, maimakon ka wuce gaba kayimin jagora har izuwa inda rikakken goggon biri yake?". Yayinda aljani barzila yaji wannan tambaya, sai ya dubeni muryarsa na rawa yace, "ya shugabana ai bala'in dake cikin wannan daji da zamu shiga yafi karfina domin a tarihi ma in banda marigayi mahaifinka, babu mahalukin daya taba ratsawa ta cikinsa ya isa dajin gaba. Ai daga yanzu kaine mai yimana jagora baniba domin ban san komaiba acikin wannan daji". Koda jin haka, saina yi murmushi na gyara makaman jikina gami da zaman gurayena da layu sannan na wuce gaba barzil na biye dani tamkar dan farauta da karensa. Da fara tafiyarmu a cikin dajin, sai na dunga jin gilmawar wasu abubuwa a samanmu,tamkar giftawar walkiya suna dira a can saman karshen wadansu bishiyoyi masu tsawon tsiya. A duk sa'adda muka daga kawunanmu sama bama ganin komai. Al'amarin daya firgita aljani barzila kenan ya kwakumi jikina sai dana daka masa tsawa, sannan ya sakeni. Take na zare takubba biyu a jikina na fara tafiyar sanda ina nazarin kowanne bangarena gabas da yamma kudu da arewa da kuma sama da kasa ina mai jiran ko ta kwana. Ba zato ba tsammani sai naga wani jibgegen biri ya taho kasa daga can kololuwar bishiya zai dira akammu. Cikin tsananin zafin nama na goce ina mai janye aljani barzila daga gurin. Birin ya dira kasa yana mai kawo mana wawan suka da faratan hannayensa koda muka goce hannayensa gaba daya biyun suka nutse a cikin kasa suka yi wani rami zururu. Wato in ba don mungoceba da cikin jikinmu hannayen nasa zasu lume. Kafin birin ya sake yunkurawa tuni na fille masa kai, ya baje a kasa matacce. Kaico ashe na tsokano bala'I ne. Faruwar hakan keda wuya saiga sauran 'yan uwansa su shida suna saukowa kasa jif-jif tamkar giwa ta fado. Kafin muyi wani yunkuri sunyi mana kawanya, babu ta inda zamu iya guduwa. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanina da su, yayinda jikin dan uwansu dana kashe ke malala a kasa tamkar an bude magudanar ruwa. Kawai sai na dafa kafadar aljani barzila yayinda yake ta karkarwa, tamkar an tsomashi a cikin kogin kankara, nace da shi, "Ka tsaya kyam a inda kake kada kayarda ka gusa koda taku daya ne" Lokaci guda sai birirrikan su duka shidan suka tasammana na na ruguntsume da a zababben yaki da su suna masu kawo mana sara da suka ni kuwa ina tarewa ta kowanne bangare ina maida martani. Haka dai muka wanzu muna ta artabu har tsawon sa'a guda batare da na sami nasara ba a kansu, suma kuma basu samu ba, abin da ya tayar mini da hankali. Shine kokadan babu alamar gajiya atare dabirirrikan tamkar wasa jini suke , ni kuwa na tabbatar da cewa idan aka kara samun wata sa'a guda nan gaba zan iya gajiya likis su kaini kasa. Ana cikin haka ne daya daga cikin birirrikan ya sadado ta bayana ya shammaceni ya karta mini farcensa a gadon bayana. Take wajen ya dare jini yai tsartuwa saboda tsananin zafin da naji bansan sa'adda na kwarara uban ihuba, nayi kasa luuuu cikin wani irin matsanancin hali mai kama da suma idanuna na lumshewa koda ganin haka, sai birirrikan suka yi caa a kanmu ni da aljani barzila da nufin su tsinka gabobin jikinmu. Ba zato ba tsammani, sai na yunkura da kugiyata a sannan na fillewa birirrikan kawunansu su duka shidan, take gangar jikinsu ta zube kasa suka zama gawa. A lokacin ne aljani barzila yai a jiyar numfashi yana mai godiya da jinjina a gareni bisa ceton rayuwarmu danayi, kawai sai yaga na sulale kasa ina numfashi da kyar. Cikin rudewa aljani barzila ya bude jakata ya fiddo garin magani ya shafa a raunin gadon bayana, jini ya daina zuba, sannan ya ruga cikin daji ya samo itatuwa yazo ya kunna wuta domin ta rage mini tsananin hunturun sanyi dake kadawa a dajin. Haka dai barzila ya zauna yana jinyata, har izuwa tsawon lokaci, sannan yaje farauto mini wani katon tsuntsu ya zo ya gasashi ya bani naci. Sai da muka kwana uku a wannan wuri ina jinyar raunina, barzila na kula dani, sannan na sami karfin jikina. Koda naji na warware sai na mike tsaye na kama shirye- shirye na ce da aljani barzila, "Mike ka kimtsa yanzu zamu ci gaba da tafiya domin mu isa kogon da uban birirrikan nan yake, kasan shi nake so na kashe na debi kwakwalwar kansa". Cikin kaduwa da mamaki aljani barzila ya dubeni yace, "Haba ya shugabana, raunin jikina fa bai gama warwarewa ba, yanzu kana ganin cewa, zaka iya ci gaba da gumurzu a haka?" "Ko zan iya ko bazan iyaba, dole ne mubar nan muci gaba da tafiya. Karkamanta cewa, yau kwana uku kenan da kashe wadannan birirrika, tabbas yanzu hankalin iyayensu a tashe yake, tunda basu ga sun koma gidaba kaga kenan dole ne su fito nemansu dasuzo su ritsamu a nan gwara ace mune muka je muka riskesu har cikin kogon da suke". Yayinda aljani barzila yaji wannan batu, sai yai ajiyar zuciya, yace, "Hakika maganarka gaskiya ce". Nan take barzila ya matso gareni ya rankwafa na haye bayansa, na zauna ya tashi dani sama muka kara gaba. Kash! Rashin sani yafi dare duhu, ashe ma duk wannan hira da muke yi iyayen birirrikan dana kashe tuni sun iso inda muke suna labe a bayan wata katuwar bishiya suna hangenmu. Barinmu wajen keda wuya sai suka fito daga inda suke boyen suka shiga neman 'ya'yansu. Ai kuwa basu dade ba suna neman suka hango mushen gawarwakin wanda tuni ya gama rubewa, mikiyoyima sun tsatstsagi iya rabonsu. Koda suka ga wannan mushen sai suka takarkare suka rafka kururuwa tsananin karar kururuwar tasu ce ta firgita dukkanin halittar dake cikin dajin. Tsuntsaye suka tashi daga inda suke suka kama shawagi a sama dabbobi suka kama guje-guje, na cikin rami suka firfito, na kan bishiyoyi suka sauko. Aljani barzila dake dauke da ni bai san sa'adda ya dimauce baya rikito damu kasa, jikinsa na tsuma, ya kasa ci gaba da tafiya, yayinda duk gabobin jikinsa suka kama tsuma. A wannan lokaci kuwa mun iso bakin kofar kogon birirrikan. Cikin fishi na sauka daga kan aljani barzila sannan na zare takubbana guda biyu na dubi barzila nace, "Ni zan shiga cikin kogon birinnan na jirashi a ciki, domin nasan cewa cewa yana bayanmu kuma yanzu tuni yaga gawar 'ya'yansa don haka a matukar fusace yake. Idan zaka biyoni, idan kuma zaka nemi wajen buya Ne, ka nema". Koda gama fadin haka saina wuce kai tsaye izuwa cikin wannan kogon dutse, shi kuwa aljani barzila sai ya kama duru-duru yana tunanin abinyi kafin ya ankara tuni na kule a cikin kogon. Bazato ba tsammani sai barzila ya dinga jiyo saukar wasu a bbubuwa masu nauyi akan bishiyoyin baya jif-jif. Cikin razana barzila ya ruga izuwa cikin kogon yana mai kiran sunana, ko waigowa banyi ba na saurareshi har ya riskeni. Sai da muka isa karkashin kogon inda muka ga kasusuwan bil'adama rututu a tsube waje guda, sannan muka tsaya cak. Saboda tsananin tsoro, sai aljani barzila ya shige cikin tarin kasusuwan ya boye kansa, ni kuwa sai na hada wuta sannan na kunna fitilun itatuwa kogon ya gauraye da haske, sannan na zauna ina mi harde kafafu tamkar wanda ke hutawa a cikin gidansa. Jim kadan da faruwar haka sai na ji saukar wannan biri tare da matarsa a kofar kogon tamkar faduwar giwaye, kawai sai suka shigo ciki. Tun daga nesa suka hangoni a zaune, sai suka tsaya cak, suka kura mini ido suna masu mamakina. Inda wadannan birirrka suna magana na tabbata sai sunce wannan wane irin hatsabibin bil,adama ne, mara tsoro. Bayan yakashe mana yayanmu kuma har ya iya shigowa cikin gidanmu ya zauna yana jiranmu? Bayan biran sun gama nazarina, sai mijin ya dakatar da matar tasa yayi mata nunin ta tsaya a baya, kada ta biyoshi kawai sai ya rugo da matsanancin gudu a gareni. Koda ganin haka, sai na mike tsaye zumbur na takubbana biyu na tsaya kyam a tsaye ina jiran karasowarsa. Yayinda yarage saura baifi taku biyar ba ya riskeni, sai ya daka tsalle sama ya wara hannayensa ya saito faratan hannayen nasa biyu da nufin ya sokesu cikin wuyana. Cikin matukar zafin nama na goce kuma na daka tsalle na dira can gefe daya. Ai kuwa gocewar dana yi ce tasa faratan nasa. Suka nutse cikin dutsen kogon, sai ga shi ya ciro katon ya cisge kaina. Nan fa muka fara kallon-kallo nidashi domin kowannan mu ya fuskanci cewa ba karamin gumurzu za a yiba, ita kuwa matar tasa sai ta gyara tsayuwarta cikin nishadi da gadara don ta tabbatar da cewa mijinta ne zai sami nasara akaina. Take goggon birin yasake afka mini, muka ruguntsume da sabon azababben yaki yana mai kawo mini sara da suka da faratan hannayensa, ina karewa da takobina ina mayar da martani a duk sa'adda makamaina suka hadu da faratan nasa sai kaji kamar karfe da karfe ne suka haduqn har tartsatsin wuta ne ke tashi, kuma idan na daki jikinsa sai naji kamar dutse na sara ko kwarzanewa ba yayi al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan, na tabbatar da cewa yau fa na gamu da gamona abune mawuyaci na tsira da rayuwata. Sai da muka shafe rabin sa'a cif muna wannan gumurzu dayanmu bai samu nasarar komai a sannan ne kuma naji gajiya ta fara riskata, al'amarin daya kara dugunzuma hankalina kenan domin idan banyi gaggawar daukar mataki ba a koyaushe goggon birin zai iya hallakani kawai sai na daka tsalle naja da baya, kuma nayi wurgi da makamaina ««« TARWATSA MAZA-1 TYPE D »»» Koda ganin haka, sai goggon birin ya tsaya cak yana mai mamaki, kuma ya kura mini ido don yaga abinda da zanyi kawai sai yaga na tsaya cak a waje daya, kuma ban zaro wani makamin ba, koda ganin haka, sai birin ya sake rugowa kaina ya afka mini da dukkan karfinsa, ni kuwa sai na sauya salon fada na shiga tsalle-tsalle da goce-goce ya kasa cafkata, ko sarana, amma a duk sa'adda ya kawo mini hari na goce, duk a binda hannunsa ya buga walau dutse ko bishiya sai sun tarwatse. Nima sai na zamo kamar biri na dunga shawagi a sama tamkar inada fuka-fukai a haka ne na sami wata nasara na gabza masa naushi a tsakiyar kansa ai kuwa sai naga yayi baya taga-taga zai fadi, har layi na dibarsa. Koda ganin haka, sai na cika da farin ciki, na gane cewa a duk gaba daya jikin birin babu inda za a taba ayi masa lahani, face kansa. Nan fa naci gaba da kaiwa kansa hari. Koda birin yaga na gano lagonsa sai ya haukace yaci gaba da kai mini wawan hari yana kokarin hallakani da gaggawa. Nan fa mukakicime da masifaffen gumurzu, har ta kai cewa, ya sami nasarar saran kirjina, kuma ya soka mini farcensa guda akan cinyata. Take farcen ya nutse a cikin cinyata, ya faso bayanta. Ni dai ban san sa'adda na kwala kara ba, sa'adda jini da layi suka kwasheni. Koda birin ya zare farcensa daga cikin cinyata, sai jini yai tsartuwa dama tuni kirjinna ma ya darejini na zuba. Kawai sai na fadi kasa da baya na baje a kas, a lokacin da numfashina ya sarke idanuna suka kafe. Koda birin yaga yasami wannan nasara, sai ya juya ya dubi matarsa yai kururuwa, ita ma sai tayi kururuwar don ta nuna masa farin cikinta. Irin ya juyo ya taho gareni da nufin ya tsitstsinka sassan jikina. Yayinda ya iso kaina ya sunkuya zai cisge mini hannayena, sai kawai yaga nayi zumbur na daka tsalle izuwa samansa kafin ya dago kansa sama ya kalleni, tuni na ta karkare na gabza masa naushi da dukkan karfina a tsakiyar madikar kansa take hannuna ya burma kan ya shige ciki koda na zaro hannuna sai ga gwakwalwarsa a cikin tafin hannuna take birin ya sulale kasa matacce koda matarsa ta ga abin daya faru sai ta juya ta falfala da gudun tsiya, kafin kiftawar ido ta bace daga cikin kogon. A sannanne na sake yanke jiki na fadi kasa ina numfashi da kyar, kamar raina zai fita. Kawai saina ji motsi a cikin tarin kasusuwan nan na mutane sai ga aljani barzila yai fitar burgu daga ciki. Ni tunima na manta cewa yana cikin kogon koda barzila yaga halin da nake ciki, sai ya rude nan da nan ya gaggauta yi mini magani. Sai da muka kwana shida a cikin kogon dutsen aljani barzila na jinyata, sannan na sami lafiya. Ba tare da bata lokaciba muka yi shiri muka fice daga cikin kogon, dama tuni na tanadi kwakwalwar birin na adanata acikin jakata, gangar jikin birin kuwa mun koneta ta babbake ta zama toka, don kada ta damemu da wari. Kawai sai muka tasamma daji na biyu, wato dajin shajaril mausuba inda zakanya mai dauke da tsohon ciki take, da shigarmu cikin dajin sai na umarci aljani barzila daya nemi bishiyar da babu kamarta a tsawo mu hau kanta mu buya a cikin duhuwar ganyayenta. Batare da gardamar komai ba, aljani barzila yacika wannan umarni. Duhuwar ganyenta. Dama a wannan lokaci farkon safiya ce, muna nan labe akan bishiyar muka hango 'ya'yan zakanyar su uku sun fito farautar abincin dazasu kaiwa mahaifiyarsu har suka zo suka wuce kasan bishiyar da muke kai suna ta shinshine-shinshinensu amma basu ganmu ba. Sai da naga sun yi nisa daga inda muke har sun bace mana da gani sannan na umarci aljani barzila muka bar kan bishiyar muka nufi hanyar da 'ya'yan zakanyar suka fito. Sai da muka yi tafiyar rabin sa'a sannan muka iso bakin kofar kogon da zakanyar take, da saukarmu a kofar kogon sai na sauka daga kan aljani barzila na dubeshi nace, ko zaka shiga kayi mini wannan aiki ne, tunda zakanyar ce kawai da mijinta a ciki?". Cikin firgici aljani barzila ya dubeni yace Haba ya shugabana kasani cewa, wadannan dabbobi fa sihirtattu ne, kai kanka in ba don kana da cikakken shiri ba baka isa ka tunkaresu ba. Da shirin naka ma gashi da kyar kake kai labari, ni a wa zan ce zan taresu alhalin bani da koda rabin shirinka? Ai sama tayiwa yaro nisa, sai kallo". Yayinda naji wannan batu, sai na bushe da dariya nace, "Hakika kayi gaskiya. Ka jirani anan yanzun nan zan fito". Koda gama fadin haka, sai na kunnan kaina cikin kogonn. Da shigata sai naga ashe kogo ne mai tsananin zurfi ko karshensa bana iya hangowa kawai sai na ci gaba da tafiya a cikinsa abu kamar wasa sai da na shafe wata rabin sa'ar ina tafiya sannan na iso karshensa, inda nayi arba da wannan mijin zakanya tsaye a gabana ya kura mini idanu kawai ita kuwa zakanyar na kwance a bayan, ita ma ta tsura mini ido. Tun da nazo duniya ban taba ganin zaki mai girma da kwarjini ba irin wannan. Nan fa muka fara kallon-kallo nida zakin, kowannenmu ya kame kamar babu mai rai a cikinmu don babu wanda ya motsa. Daga can sai na zare takubbana na durfafeshi kai tsaye. Abin daya bani mamaki shine zakin bai motsa ba, sai da yaga saura kiris na riskeshi, sannan ya daka tsalle ya bangajeni da kirjinsa. Duk da cewa na goce da zafin nama sai daya bugi gefen kafadata, inda kuwa mun hada kirji da tuni ya karya mini kasusuwan kirjina. Take nayi tsalle sama da baya na fado kan dutse a matukar galabaice, idanuna na ganin taurarin wahala. Kafin na mike tuni zakin ya dako tsalle zai sake dira a kaina. Koda na sake gocewa faratan hannayensa suka sauka akan dutsen sai dutsen ya ratattake ni kuwa na mirgina can bayansa na sake mikewa tsaye zumbur ganin yadda wannan dutsen ya ratattake ne hankalina ya dugunzuma zuciyata ta karaya da samun abin da nazo nema ««« TARWATSA MAZA-1 TYPE E »«« Nidai a iya yawon da nayi bantaba shiga daji mai kwarjini da ban tsoro ba, tamkar dajin shajaril maurud. Ba komai ne yabawa dajin kwarjiniba, face wasu irin dogayen bishi yoyi gami da tulun ganyaye a sama da suka cika gami gami da duhuwa mai yawan gaske, ga kuma tarin manyan duwatsu masu siffofin ababan tsoro da kuma jibga-jiggan tsaunika. Muggan dabbobin daji kuwa adadinsu ya wuce kima sai dai ka gansu suna ta gilmawa, in ba don a sama muke tafiya ba, da sai mu yita yaki da su sai da muka yi tafiyar sa'a hudu a sama cikin iska a dajin na shajaril maurud, sannan muka jiyo wani irin gagarumin gurnani na dodo gurmazu, koda jin gurnanin wanda ya cika djin gaba daya sai hantar cikina ta kada, duk da jarumtaka da dakakkiyar zuciya irin tawa. Shi kuwa aljani barzila gaba dayan jikinsa ne ya dume da zafi, tamkar an tsomasi a ruwan dumi mai tiriri, ya kama karkarwa bai san sa'adda ya saki fitsarin firgita ba. Duk da cewa a tsorace nake, sai da dariya ta kwace mini, na ce, "Haba namijin duniya, ai ka karya alkadarin jarumtakarka wadda kayi a baya, domin bai kamata ba ace tsoro har yasa ka saki fitsari saboda kawai ka ji gurnanin dodo gurmazu ba". Cikin karfin hali, da rawar murya barzila yace, "Haba ya shugabana, ai bama fitsari ba, ko kashi na saki bai kamata kayi mamaki ba, Katuna fa cewa shi fa dodo gurmazun nan a halin yanzu duk duniya babu wata halitta mai karfin damtsensa da karfin sihirinsa. An ce komai kaurin bishiya, idan ya nausheta da hannu daya, saita ratattake, ta fadi kasa idan kuwa ya kwarara ihu, girgizar kasa ake yi, tsawa da walkiya na amo daga cikin bakinsa. Komai yawan maza a cikin dakika biyar yake tarwatsasu, walau rundunar bil'adama ko ta aljanu". Kawai sai nayi ajiyar zuciya, nace "Lallai kuwa baka yi laifi ba, domin tsoro wajibine, amma fani bana tsoron bala'I dan babu Wanda banganiba, sai dai na firgita da shi. Ai kawai muci gaba da tafiya, ina so ka durfafi inda kake jiyo sautin wannan gurnani". Cikin matukar tsoro aljani barzila yace, "Banki tatakaba ya shugabana, amma dai katuna cewa, "Riga kafi yafi magani. Bai kamata mu tari dodo gurmazu gaba da gaba ba, zai fi kyau mu dunga yin sanda da labiya har mu isa inda yake, ai shi yaki dan zamba ne a duk sa'adda abokin gaba ya fara ankara da abokin gabarsa, to yana iya samun hikimar da zai iya samun nasara akansa da wurwuri". Batare da wata gardama ba, na amince da wannan shawara, saboda haka sai aljani barzila ya sauko kasa ya dira bisa turba, nima na sauko daga kansa muka fara tafiya sanda muna leke-leke, wani lokacin ma har kwanciya muke a kas muna tafiya da ruf da ciki. Kaico! Rashin sani yafi dare duhu, ashe duk wannan tafiyar dudduke da mukeyi dodo gurmazu ya hangomu tun daga can nesa, saboda kwarin idanunsa yana iya hango abin dake tafiyar sa'a shida a bayansa ko gabansa, sannan duk irin abin da ya jingina ajikinsa sai kalar jikinsa ta koma irin launin abin sak komai hasken da ke wajen, ido bazai iya shaidashi ba. A wannan lokaci da muke tafiyar ruf da ciki, dodo gurmazu na can sama bisa wata gabjejiyar bishiya mai tsananin girma da tsawo. Ni kam na tabbatar da cewa, wannan bishiya babu ta biyunta a duniya, domin ko a tarishi ban taba jin labarin bishiya irintaba. Haka dai muka ci gaba da tafiyar ruf da ciki har muka iso gaban wannan narkekiyar bishiya, amma bamu ga komai ba, kuma bamu sake jin gurnanin dodo gurmazu ba. Mun dade a kwance muna kasa kunne ko zamu ji wani motsi, amma ba muji ba. Daga can sai muka mike tsaye na dubi aljani barzila nace, "Abin da zamu yi kawai mu hau can saman wannan bishiya mu tsaya in dai muka yi haka zamu iya hango dodo gurmazu a duk inda yake domin zaton da nake ba a nan kusa yake ba. Yana nesa da mu ne". Koda jin wannan shawara tawa, sai barzila ya cika da murna, yace, "kwarai kuwa kayi tunani mai kyau, haka za a yi" nan take na sake hawa bayan barzila yai sama dani, sai da muka kure tsawon bishiyar sannan muka sauka a kan wani katon reshenta guda. Cikin hanzari aljani barzila ya zaro kwari ya dana akan wannan katuwar baka tashi ya tabe bakan ya shiga kalle-kalle ko zai hango dodo gurmazu ya sakar masa harbi. Ni da Nake bayan barzila sai na daga wani gatari nawa sama na tsaya cak! A waje daya ina kallon gabas da yamma, kudu da arewa, kuma ina leko kasan bishiyar. A binda bamu saniba shine, munyi aikin banza domin kuwa mun kulle kofar gida da barawo a ciki, domin kuwa tsakaninmu da dodo gurmazu bai wuce taku uku ba. Ashe shi ma yana kan bishiyar amma da yake kalar jikinsa ta saje da kalar jikin bishiyar ko kadan bamu ganshi ba. Kwatsam! Ba zato kuma ba tsammani, sai dodo gurmazu ya sauya kalar jikinsa izuwa ainashin tasa ta gaskiya, ya baiyana daf da aljani barzila. Koda barzila yai arba da dodo gurmazu yaga irin kwar jininsa da muninsa sai ya firgita kuma ya dimauce, bai san sa'adda ya saki kwari da bakan dake hannunsaba ya juya da nufin ya bude fuka- fukansa ya tashi sama, amma sai dodo gurmazu ya cabo jelarsa cikin zafin nama, sai ga barzila na reto a sama, tamkar dan biri na wasa. A dai-dai wannan lokaci ne na dako tsalle daga inda nake tsaye na taho a sama zan kirbawa gurmazu sara a tsakiyar kansa, amma sai gurmazu ya mangareni da daya hannun nasa, na rikito kasa, tun asama na fita daga haiyacina, naji kamar anyi mini kanshin mutuwa. Ai kuwa ina fadowa kasa na sume. Nidai ban san abin daya faruba daga sannan sai farkawa nayi na ganni a cikin katon keji tare da aljani barzila, da kuma wadansu aljanu kimanin su dubu biyu, duk suna ta faman rusa kuka shi ma aljani barzila sai ya tayasu kukan. Koda barzila yaga na farfado, sai ya dubeni a fusace, yace, "Kaga irinta ko, ai dama na gayamaka bamu isa mukawar da dodo gurmazu ba, ga shi yanzu ya kamamu. Wadannan aljanu duk fursunoninsa ne, kuma sun gaya mini cewa, sudubu arba'in ne ya kamosu, kullum yana diban biyar yana cinyewa, yanzu saura su dubu biyu kacal, kaga kenan muma mun zama abincin sa. Haka kuma sun tabbatar mini da cewa babu wani makami ko sihiri da zai iya karya wannan keji, har mu

Please Login or Register in order to submit comment