Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TARWATSA MAZA-1 TYPE A ««« A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude, lokacin da ake rayuwa ta zalunci, kafirci da fasikanci, anyi wata babbar daula dake karkashiin wani shahararren sarki mai suna HASANUL MAUZUR. Sarki hasanul mauzur ya kasance gawurtaccen mayaki mai tarwatsa maza afilin daga, wanda atarihin jarumtakarsa bai taba zuwa kasa ba,kuma ba a taba jimasa rauniba komai girman kato kuma komai karfinsa indai yakara da sarki hasanul mauzur sai yayi na dama baya ga wannan sadaukan taka da allah ya bashi, ya kasance mashahurin attajirin da babu kamarsa a duk fadin nashiyar dayake domin shi kansa bai san iyakar. Dukiyar da ya mallakaba. Birnin sharas shine sunan kasar sarki hasanul mauzur kuma a karkashin birnin a kwai manyan birane kimanin guda bakwai amma duk birnin sharas inda fadar sarki hasanul mauzur take ya fi sauran kyau girma da daukaka. Gaba daya mutanen daular suna bautar wani karamin Gunkine mai siffar kyanwa wanda ake wa lakabi da hurzas. Shidai wannan gunki an a jiyeshi ne a cikin wani kasaitaccen gida wanda babu mai shiga cikinsa face mutum biyu kacal. Daga sarki sai bokansa mai suna SURAB IBIN KAIZAR, sai kuma wanda yayi gagarumin abin bajinta ko kuma wanda ya farantawa sarki rai, sai ayi masa izinini ya shiga dakin bautar ta gana da gunki hurzaas. Duk mutumin daya gana da gunki hurzas tofa kakarsa ta yanke saka domin duk irin bukatar da ya yake da ita ta duniya, sai ta biya bisa wannan daliline fa dawan sarki ke ta yimasa shishshigi da neman yarda don kawai a lamince musu ganawa da gunki hurzas. A shekara guda mutum daya kacal akan samu wanda sarki ke lamincewa. Sarki hasanul mauzur na da kyakykyawar 'ya guda daya jal, wata budurwa mai suna SHULAIRA kyawun shulaira yafi gaban kwatance sai abin da idanu ya gani. Ko kadan shulaira bata gado mahaifintaba a wajen jarumta da halaiya domin ita ta kasance mai tausayi son jama'a da taimako, sabanin mahaifinta wanda ko yaushe ba shi da aikin yi face cin zali da kai harin sumame don samo dukiya da bayi ko taimako sarki hasanul mauzur zaiyi sai dai ya yiwa attajiri ko babban basarake amma ba talakan gari ba. A rayuwar duniya babu abin da sarki hasanul mauzur ya tsana sama da talaka. Gimbiya shulaira ta tsani halayen mahaifinta, amma tunda babu yarda zata yi ta hanashi yi, dole ta ke hakuri. Sai dai a duk sa'adda zai yi zalunci in dai tana wajen tana hana shi kuma sai ya hakura dole saboda tsananin son ta da yake don baya son yayi abin da zai sosa mata zuciya tunda mahaifiyar shulaira ta mutu sarki hasanul mauzur bai sake yin aure ba, kuma yayi alkawarin har abada bazai kara yin aureba saboda dama ya dauki wannan alkawari ga mahaifiyar shulaira. Sa'adda ta kwanta cutar ajali, tsawon shekaru uku a wannan lokaci shulaira bata fi sheekara takwas a duniya ba lokacin da imila mahaifiyar shulaira ta tabbatar da cewa cutarta bata tashi bace sai ta dubi sarki hasanul mauzur tace, "ya kai mijina yanzu idan na mutu wacce mace zaka auro ta kaunaci shulaira kamar yadda nake kaunarta?l Koda jin haka sai imila ta fashe da kuka sannan tace, "kayi sani cewa na sha yin mafarki ana nuna mini shulaira a cikin wahala bayan raina bisa haka ne nake tsoron cewa zata sha wahala ne a wajen matar da zaka auro". Koda jin wannan batu sai sarki hasanul mauzur yace, "AIkuwa tunda haka ne, nayi miki alkawarin in dai mutuwa ta daukeki har abada bazan sake sha'awar wata 'ya mace ba bare ma na aureta sai dai na zauna da barori da kuyangina kawai". Sa'adda Imila taji haka sai ta cika da farin ciki tace, "Hakika yanzu ne ka nuna mini soyayyarka ta gaskiya, ina yi maka fatan jurewa bisa wannan alkawari da ka dauka". Hasanul mauzur yace, "Tabbas zan kasance mai jaddada wannan alkawarin, har izuwa ranar da nima nawa wa'adin ya cika" Ai kuwa tun daga ranar da Imila ta rasu sarki hasanul mauzur bai kara sha'awar yin aure ba, koda kuwa yaga macen da ta burgenshi, don kada ya karya alkawarin da ma a gaban shulaira ya yiwa imila wannan alkawarin. Lokacin da shulaira ta cika shekara sha takwas a duniya, sai 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai suka yi caa akan neman aurenta. Ita kuwa shulaira sai ta nuna sam bata da ra ayin aure. Al'amarin daya dugunzuma hankalin sarki hasanul mauzur kenan ya kirata yace, "yake 'yata ke kuwa menene dalilin ki na kin yin aure ayanzu, alhalin dukkanin masoyanki babu na banza?" Sa'adda shulaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi, tace, "Ya kai abbana kayi sani a matsayinka na shahararren sarki , mai karfin mulki da karfin arziki, da kuma gagarumar jarumta bai kamata a auri 'yarka cikin sauki ba. Dolene ya zamana cewa wanda zai aureni yayi babbar bajimta, wadda zata zamo abin tarihi a duniya, gaba daYa. Bisa wannan daliline na yankewa kaina sadaki, kuma na shirya mataki da sharadi wanda dole sai anbisu sannan za a sami ikon aurena kosa gimbiya shulaira tazo nan a zancenta, sai sarki hasanul mauzur ya cika da tsananin farin ciki, ya dubeta cikin murmushi, yace, "yake 'yata hakika kin zomini da shawara mai kyau, wadda ta faranta mini raina , saboda haka yanzu saiki yi mini bayanin mataki da sharadin da kika gindaya bisa neman auren naki". Cikin murna shulaira tayi gyaran murya, sannan tace, "mataki na farko shine, duk sauraayin dake son aurena dole ne yabiya sadaki na kudi adadin dinare miliyan dubu daya mataki na biyu ina son a zabo manyan sadaukai guda dari wadanda babu kamarsu a na shiyarnan dole ne manemin aurena ya fafata dasu ya tarwatsasu mataki na uku dolene manemin aurena ya gwabza yaki dakai, ya kaika kasa sharadi kuwa duk wanda ya aureni bazai yi mini kishiyaba, kuma idan na rigashi mutuwa bazai kara aureba har abada". Yayinda shulaira ta zo nan a jawabinta sai idanun sarki suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa ya dubeta yana mai yaken, yace, "yake 'yata hakika kin burgeni matuka bisa wannan mataki da sharadi da kika kirkiro, domin kin nuna min cewa kema kina matukar kaunar mahaifiyarki, kuma kina cikin begenta, dare da rana. Na amince da wannan matakai da sharadi da kika gindaya, amma abin da nake so da ke shine kada a furta sharadin sai sai bayan anci wannan gasa kuma za'a sanar da hakan. Yake 'yata kiyi sani kin kirkiro gasa mai matukar wahala wadda bana zaton za a sami mahalukin da zai iya haye wadannan matakai uku koda mutum ya haye guda biyun, tofa bazai iya haye na ukun ba, dalili kuwa shine a kwai wani sirri mai karfi wanda ban taba gaya miki shiba amma a yanzu zan sanar dake, tunda wannan al'amari ya bijiro". Sarki hasanul mauzur ya kyara zama gami da gyaran murya, sannan ya fara bayani kamar haka..... "Na kasance sadaukin gaske, amma bokana ya tabbatar mini da cewa, akwai sadaukai uku a duniya wadanda su kadai ne zasu iya kaini kas idan muka yi gaba-da -gaba dasu. Lokacin da boka surub ibini kaizar yayi mini wannan jawabi sai hankalina ya dugunzuma na rasa abinda ke min dadi a duniya, don haka sai na dubeshi nace, "ya kai babban boka yanzu me zanyi na kare kimata ya zamana cewa koda na hadu da wadannan sadaukai uku ba zasu iya kaini kasba? Kuma ina son kasarar dani inda wadannan sadaukai suke da kuma suffofinsu domin na kiyaye karona dasu kafin na sami kariya". Koda jin wannan batu sai boka surub yai shiru kuma ya sunkui da kansa kas. Yana mai rintse idanunsa gami da karanta wadansu dalasiman tsafi, daga can sai ya dago kai ya kalleni kawai sai ya bushe dadariya, yace, "ya kai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa, bukatarka zata biya idan har zaka iya jure yin a bubuwan da zamu umarceka dayi. Da farko dole ka samo abubuwa uku domin na hada maka wani magani wanda zaka shafe gaba dayan jikinka da shi, wadannan abubuwa sune, kwakwalwar rikakken Gaggon biri,wanda ya shekara tamanin a duniya sai kuma kitsen zakanya wacce ke dauke da tsohonciki, haihuwa yau ko gobe. Abu na uku shine harshen giwa wacce ta haura shekara hamsin. Za a hada wadannan abubuwa a cikin tukunya a rufe sannan akwanna tara ana dafasu. A daren kwana na taranne zakayi tsirara ka shafe jikinka da waddannan abubuwa uku sannan ka tafi makabartar a cikin tsirara batare da kasa tufafiba idan ka isa makabar tar sai ka nemi kabari wanda ya kai shekara tamanin bai bajeba kuma ba'a taba hake shiba ka zauna agaban kabarin ka soka hannayenka cikin kabarin ba zaka zareba sai bayan kwana uku. Duk bukatarka da zakayi sai dai ka yi ta a wajen, amma babu tashi kuma babu waiwaye. Ya kai wannan sarki idan har ka sami nasarar kammala wannan aiki ba tare daka yi kuskureba to har abada babu wani sadauki da zai iya samun nasarar kaika kasa komai karfinsa kuma kuma harka mutu baza a taba samun galabar yaki a kankaba kuma babu wani kato dazaka yiwa naushi daya batare da ya baje a kasaba kai ko giwa ka nausa sai ta je kas" Yayin da boka surub yazo nan a jawabinsa sai na kawo gwauron numfashi na a jiye, sannan na dubeshi nace "yakai babban boka hakika kazo mini da babban al'amari mai wuyar gaske to amma fani a rayuwata ban taba karaya ba, bisa duk a bin da nasa a gabana. Tunda ga kuruciya kawo izuwa girmana duk abinda na aiyana ina son nayi sai nayi shi, ban taba samun rashin nasaraba saboda haka ni yanzu na amince zan tafi neman wadannan abubuwa uku tai makon da zaka yimini kawai shine, ka fada mini dajin da zanje na samo wadannan abubuwa uku ba tare da na sha wahalar nema ba" Koda jin haka sai boka surub yayi murmushi yace, "A yamma da kasarka akwai wadansu dazuzzuka guda uku wadanda suka yi iyaka da kasar hairuf. Daji na farko ana kiransa da suna Darul-shazar acikinsa ne zaka sadu da rikakken goggon biri, wanda ya shekara tamanin. A duniya shidai wannan biri a halin yanzu babu wani biri mai karfi da girma tamkarsa saboda tsananin karfinsa ma da faratan hannayensa ya kwakule wani katon dutse yayi gidansa a ciki inda ya ke kwana tare da matarsa da kuma 'ya'yan sa guda bakwai. Wannan biri tare da 'ya'yansa sun hana fatake da matafiya ratsawa ta cikin dajin darul-sharzas, domin komai yawan runduna suna iya tarwatsata saboda karfisu da kuma tsagwaron dabararsu ta iya yaki makaminsu shine faratansu idan kuwa suka daka tsalle daga kasa suna iya hawa kan bishiya mai tsawon zira'I dari da hamsin, sannan suna da zafin nama na gaban kwatance, sai dai kawai mutum yaga sun gilma ta gabansa sun bace tamkar kiftawar ido. Ya zama dole ka yi yaki da 'ya'yan wannan goggon biri, ka kashesu suduka bakwan, sannan zaka sami damar kashe ubansu. »»» TARWATSA MAZA-1 TYPE B »»» Kasani cewa karfinka ko karfin sihirinka bazai kwaceka ba, a hannun goggon birin face dabara da hikimar iya yaki da zarar ka kashe birin matarsa zata gudu to a sannanne zaka fafe kansa ka debo kwakwalwarsa ka adanata, sannan ka wuce izuwa daji na gaba wanda ake kira shajaral mausuba. A cikin dajin shajarul mausuba ne zaka riski zakanya mai dauke da tsohon ciki, haihuwa yau ko gobe. Ita dai. Wannan zakanya tana cikin wani kogon dutse ne dake bisa dogon tsauni. Dole ka hanzarta nan da kwana goma shahudu karisketa in ba haka ba kuwa zaka iya tararwa ta haife abin dake cikinta ka ga kenan kitsenta bazai yi aiki ba. Ita dai wannan zakanya tunda cikinta ya tsufa sai ta daina fita ko ina kullum tana cikin wannan kogon dutse mijinta ke gadinta yana kula da lafiyarta, 'ya'yanta kuwa guda uku suke tafiya sunemo mata abin da zataci. Kada ka je kogon dutsen sai da hantsi a sannan ne 'ya'yan nata ke tafiya neman abinci kaga kenan daga ita sai mijinta da zuwa sai ka farwa mijin nata ka kasheshi sannan itama ka far mata. Idan ka kasheta sai ka suri gawarta ka yi ta gudu da ita, har sai ka shiga cikin daji na uku sannan ne ka tsira daga sharrin 'ya'yanta. In kuwa kace zaka tsaya farde cikinta ka debi kitsenta to tabbas 'ya'yan nata zasu iya zuwa su riskeka su hallakaka. Shi kuwa daji na uku shine wanda ake kira shajaril maurud inda zaka riski giwa wacce ta haura shekara hamsin a duniya. Ita dai wannan giwa mallakar wani sihirtaccen dodone mai suna gurmazu. Dodo gurmazu ya kasance matsafi kuMa rikakken dan fashi wanda ke TARWATSA MAZA komai yawansu don haka fiye da shekaru hamsin baya ya kashe hanyar ba a ratsawa. Kai bama mutumba hatta aljanu da dabbobi tsoron shiga dajin sharjaril maurud suke, saboda masifar dodo gurmazu. Idan gurmazu ya kama aljani yakan yi kilishinsa ne, ya cinye domin yana matukar jin dadin dandanonsa a baki, tamkar mutum ya sami kaza. Idan kuwa dabba ya kama daranta yake cinyeta, babu fida ko gashi mutane kuwa koda sunkai dubu dari biyarkuwa sai ya cafkesu, ya zuba su a cikin wani katon keji ya rinka zararsu da dai-dai yana kalaci dasu. Matsafa da mayaka sunsha yin gangami wa 'yanda suka yarda da kansu domin suga bayan gurmazu, amma da zarar sunyi arba dashi tasu ta kare ko mutum daya bazai koma gidaba kai ko duriyarsu baza a sake jiba. Dole kakashe dodo gurmazu kafin ka sami damar kashe wannan giwa da yake kiwo har ka yanko harshenta sannan ka kawo mini abubuwa ukun a hada wannan magani da zaka shafe jikinka dashi". Sa'adda sarki hasanul mauzur yazo nan a zancensa sai gimbiya shulaira ta gyara zama kuma ta tattara hankalin ta a waje daya tana mai kura masa idanu tace, "ina sauraronka ya kai abbana, bani labarin abinda yafaru gareka yayinda ka shiga wadannan dazuzzuka guda uku da yadda aka yi ka sami nasarar dauko wadannan abubuwa uku, hakika ka cika namijin duniya, dolene nayi maka kirari da jarumi uban jarumai, mai TARWATSA MAZA ". Koda jin wannan batu, sai sarki hasanul mauzur ya fashe da dariya sannan yace, ai kowa yazama wane babanzaba duniya bata samuwa daga zaune sai an mike tsaye baki ance yaro bata hankalin dare kayi suna ba?" Hasanul mauzur yai gyaran murya. Sannan yafara bayani kamar haka...... "Yake 'yata kiyi sani cewa, kashe garin ranar da boka surub yai mini bayani nayi shiri na debi makaman yakina gami 'yan guraye da laloyina na tsafi, nayi sallama da mahaifiyarki awannan lokacin tana dauke da tsohon cikin ki saura baifi kwana arba'inba ta haihu. Dama tun a daren jiya nalabarta mata inda zan tafi da kuma abubuwan da zan tafi nema. Har yau har gobe bazan taba mantawa da wannan tafiya ba, domin ina yawan tuna abinda ya faru tsakanina da ita, da duk irin kalaman data gaya mini sa'adda muka zo yin sallama. A wannan lokaci ana tsala ruwan sama kamar da bakin kwarya, kuma ana tafka tsawa da walkiya, wadanda suka tsorata gaba dayan mutanen garinnan kowa ya shiga gida yai zamansa, babu batun a fito yin harkoki, amma ni a sannan ne na gama shiri tsaf zanfita. Koda mahaifiyarki taga na tsaya a gabanta da nufin muyi bankwana bisa tafiyar da bani da tabbacin da wowa gida sai ta fashe da matsanancin kuka kuma ta rungumeni al'amarin da ya karya mini zuciya kenan naji kamar na fasa yin wannan tafiya amma da na tuna irin matsayin da zansamu da daukaka idan har nai nasara, sai zuciyata ta kekashe gaba daya cikin raunin zuciya mahaifiyarki ta budi baki a lokacin da take rungume da ni tace, "yakai mijina saboda me zaka tafi kabarni alokacin da nake bukatarka fiye da ko yaushe? Kasani cewa abu ne mawuyaci na haura kwana hansin nan gaba ba tare da na haihuba. Shin baka son kaga magajinka ne, kokuwa so kake magajin naka yazama maraya? Nikam na tsorata ainun da wannan tafiya daza kayi, domin ban taba jin labarin mutumin daya taba keta wadannan dazuzzuka uku ya dawo arayeba. Me zai hana kabari na haihu sannan kayi wannan tafiya?" Koda jin wannan batu sai tausayinta ya kamani har idanuna suka ciko da kwallah, sannan na janye jikina, daga cikin nata muka fuskanci juna yayinda yayinda hawaye ke shatata bisa kan kumatunta. Kawai sai na ruke kafadunta da hannayena biyu, nace kamar yake matata uwar magajina, kiyi sani cewa kamar yadda na kasance jarumi kuma sadauki, haka mahaifina ya kasance, kuma na sami labarin cewa, shima a kokarin nemo wadannan abubuwa uku yabar gida. Har yau, har gobe bai dawo ba, kuma ko duriyarsa ba a ji ba yayin da zai bar gida ya tafi da wata sandar mulki ta wannan birni namu mai albarka na sharas, wacce ya gajeta a hannun mahaifinsa. Masana tarihin sharas sun tabbatar da cewa sandar tafi shekara dari a cikin wannan gidan sarauta tamu kuma a salinta gunki hurzas ne ya samar da ita, don baiwa birnin da sarkin dake mulki cikakkiyar kariya da daukaka. Tunda mahaifina ya tafi da sandar sai arzikin birnin nan ya raunana, kuma kariyar da muka samu ta harin 'yan sumame a gefen kauyuka ta yawaita. Lallai bincike ya tabbatar da cewa, a yanzu haka wannan sandar mulki na nan a cikin gidan dodo gurmazu ni kuwa na dade da shan alwashin sai na dawo da wannan sanda. Kinga kenan riba biyu zan ci a cikin wannan tafiya kuma ina neman daukar fansar ran mahaifina a wajen dodo gurmazu, domin boka surub ya tabbatar mini da cewa mahaifina ya haye sharrin dake cikin dajin darul shajar da shajaril mausuba. A cikin dajin shajaril maurud ne ya hallaka, yayinda yai arba da dodo gurmazu yake matata ina tabbatar miki da cewa sai dai ki yi hakuri domin babu abin da zai hanani yin wannan tafiya, muddin ina raye cikin koshin lafiya, amma dai ki yi sani cewa bani da tabbacin dawowa wata kila wannan shine ganina dake na karshe". Sa'adda nazo nan a zancena sai ta sake fashewa da kuka sai da muka jima a manne da juna sannan na saketa na janye jikina na cire wata sarka mai dauke da hatimin sarautata dake wuyana na dorata bisa tafin hannunta nace, "Ga wannan ki adanata da kyau, duk abinda kika haifa walau mace ko namiji kisanya a wuyansa, dominshi ne alamar cewa zai gajeni idan kuwa nna dawo gida a raye, da hannuna zan cire sarkar a wuyansa domin babu mai daura wannan sarkar a wuyansa face mai mulkin birnin sharas, kin kuwa sani cewa, ba a sarki biyu acikin birni guda.

Please Login or Register in order to submit comment