Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a karo na biyu ya kyalkyale da
dariyar mugunta wacce tafi ta farko.Cikin
tsananin
razana da dimaucewa sarki da yarima suka rikito
kasa daga kan kafadar dodo lasuruba cikin
yanayin
suma suka iso kan cinyarsa suka baje,koda ganin
haka sai dodo lasuruba ya hura musu iskar cikin
hancinsa suka farfado daga suman da
sukayi,iskar
bakinsa ya hura musu kuwa saida jikinsu ya
zagwanye ya narke saboda zafinta da tururinta
tamkar na dafaffiyar darma ne.Lokacin da sarki
da
yarima suka farfado suka mike tsaye a firgice
bisa
kan cinyar dodo lasuruba sai suka daga
kawunansu sama sukayi arba da fuskar
lasuruba.Nan take suka firgita ainun fiye da
koyaushe saboda ganin yadda fuskar tasa ta
murtuke izuwa tsananin fushi.Dodo Lasuruba ya
dubesu duk su biyun sannan yayi musu guntun
murmushi yace yaku wadannan hatsabiban
bil'adama na baku dama kuma kunyi wasa da
damar taku,don haka yanzu karshen rayuwarku
tazo.Alfarma daya zan iyayi muku a yanzu,idan
kuna ganin cewa zaku iya tsere mini to ku falfala
da gudu ku fice daga cikin dajina.amma nayi
muku
alkawari ko kunfi iska karfin gudu saina kure
muku
gudun na hallaka ku.Koda jin wannan alfarma ta
biyu sai sarki ya dubi dodo Lasuruba ya daka
masa tsawa yace yakai wannan tsohon azzalumi
takadarin matsafi kayi sani cewa ni a rayuwata
ban
taba guduea ba don wuya ko tsoro domin namijin
kwarari baya shakkar mutuwa a filin daga.Ina
tabbatar maka da cewa babu inda zamu dara
daga
nan saidai ka kashemu a nan idan kana
iyawa.Cikin tsananin mamaki dodo lasuruba ya
dubi sarki yace hakika wannan bil'adama ka cika
hatsabibin kanka domin kai ne mahaluki na farko
daya taba yi mini tsawa a rayuwata kuma kaine
wanda ya taba gaya mini bakar magana tunda na
wanzu a doron kasa tsawon shekaru dari bakwai
da sittin da uku.Tun ina rayuwa a can bangon
karshen duniya bangaren yamma har na dawo
nan.Tabbas yau zanyi masa kisan gillah irin
wanda
ban taba yiwa wani mahaluki ba walau mutum ko
aljan.Gama fadin hakan keda wuya sai dodo
Lasuruba ya kawowa sarki cafka da hannunsa
guda cikin shammace,nufinsa idan ya cafke shi
ya
rinka gutsurar sassan jikinsa da kadan kadan
yana
cinyewa harya gama cinye shi gaba daya.Bisa
mamaki sai dodo Lasuruba yaga sarki ya daka
tsalle sama daga inda yake tsaye ya koma can
kan
daya cinyar tasa.Hannun Lasuruba ya kama iska
karfin hucin iskar hannun dodo Lasuruba tayi jifa
da yarima can gefe daya ya maku a jikin wani
dutse take kafarsa ta dama ta karye ya kasa
mikewa tsaye.Bisa dole ya zauna a kasa
dirshana
ya zuba idanu kawai yana kallon mugun artabun
da akeyi tsakanin sarki da lasuruba cikin
tsananin
tsoro domin gaba dayan jikinsa ya kama
tsuma.Dodo Lasuruba ya cigaba da kaiwa sarki
cafka da mangari da dukkan karfinsa da zafin
namansa shima sarki saiya cigaba da gocewa
yana tsalle tsalle a sassan jikin Lasuruba.Duk
sa'adda hannun Lasuruba ya bugi dutse sai kaga
dutsen ya tarwatse komai girmansa da
kwarinsa.Idan kuwa bishiya ce dagargajewa take
kamar an dakata a turmi kuma saita tumbuke har
jijiyoyinta.Saida aka shafe sa'a guda ana wannan
artabu dodo Lasuruba ya kasa taba sarki ko sau
daya.Al'amarin dayai matukar baiwa shi kansa
Lasuruba mamaki kenan domin bai taba haduwa
da wani mahaluki daya gagareshi hallakawa ba a
cikin dakika biyar.Shi kuwa yarima dake zaune
acan gefe daya yana kallon abinda ke faruwa
kamewa yayi kamar gunki saboda tsananin
mamaki ya kasa kifta idanunsa.A iya rayuwar da
yayi zama tare da sarki bai taba sanin cewa sarki
yana da irin azababben zafin nama ba gami da
juriya da jarumtaka haka ba.Lokacin da sarki
yaga
ya fara gajiya da tsalle tsalle gami da goce goce
akan dodo Lasuruba sai hankalinsa ya
dugunzuma
ainun domin yasan cewa idan bai dauki matakin
gaggawa ba karshe lallai dodo Lasuruba zai
hallaka shi sannan ya hallaka yarima.Ko kadan
sarki bai damu da tasa mutuwar ba burinsa
kawai
shine rayuwar yarima ta tsira kuma tafi birnin
kisra
tare da kan dodo Lasuruba domin ya sami damar
auren gimbiya Siyamat.Koda sarki ya ayyana
wannan al'amari a cikin zuciyarsa sai yaji wani
irin
sabon karfi ya shigeshi nan take ya daka wawan
tsalle na ban al'ajabi ya dira akan hannun
Lasuruba.Shi kuwa dodo lasuruba ya dago
hannun
nasa da nufin yayi cilli dashi,damar
da sarki ya samu kenan ya kara yin sama kamar
an harbo shi daga cikin kwari da baka,kai tsaye
ya
shige cikin hancin dodo Lasuruba.Ai kuwa yana
isa
karshen hancin sai ya daddage iya karfinsa ya
naushi hancin.Take hancin ya burma saiga jini na
malalowa waje.Ashe ruhin dodo Lasuruba a cikin
hancinsa yake,nan fa dodo lasuruba ya kama
matagungun daga tsaye ya fado kasa yana
birgima
in badon sarki yayi wuf ya daka tsalle ta cikin
burmammen hancin nasa ba daya kife dashi.Cikin
zafin nama sarki ya suri yarima ya azashi a
kafadarsa ya falfala da matsanancin gudu don ya
fice daga cikin dajin gaba daya.Birgimar da dodo
Lasuruba ya rinka yi a kasa ne ta haddasa
girgizar
kasa.Ruwan jinin daya rinka malala daga cikin
hancinsa kuwa saiya cika dajin gaba daya tamkar
teku ce ta balle har saida ya shanye su sarki
suka
rinka iyo a cikinsa.Har su sarki suka fita wajen
dajin basu daina jiyo ihun dodo lasuruba ba kuma
dajin gaba dayansa bai daina girgiza ba sai bayan
sa'a guda sannan komai ya tsaya cak,a sannan
ne
sarki ya dawo da baya yana goye da yarima a
bayansa suka cigaba da iyo a cikin jinin dodo
lasuruba suka iso har inda gawarsa take.A
sannen
ne sarki ya sauke Yarima a gefe daya sannan ya
zaro wani gatari daga cikin jakarsa ya rinka
saran
wuyan dodo lasurua.Wannan karon sai gashi
gatarin na datsa kasusuwan wuyan dodo
lasuruba
da jijiyoyin amma saboda yawansu da kwarinsu
saida sarki ya shafe sa'a uku yana saransu
sannan
ya sami nasarar gutsure kan.Nan take sarki ya
dawo inda yarima yake ya gyara masa karayar
dake kafarsa sannan ya ciccibi kan dodo
Lasuruba
ya dora akansa kuma ya sake goye Yarima suka
fice daga cikin dajin Shakkaful Zamral cikin
tsananin farin ciki bisa samun wannan
gagarumar
nasara.Kuji Gwarzon Namiji.
A Can Birnin Kisra Sarki Da Dansa
Yarima Kuzzaru na zaune a fada jama'a sun cika
makil ana tafiyar da harkokin mulki sai kawai aka
jiyo shewa da hayaniya daga can cikin
gari.Al'amarin daya dugunzuma hankain kowa
kenan a fadar.Nan take sarki ya tashi manzo
yace
dashi ya ruga izuwa cikin garin yaje ya gano
abinda ke faruwa,kuma sannan aka umarci
dakaru
dasu fara shiri ko yaki ne ya barko ba'a sani
ba.Nan da nan kuwa wannan manzo ya cika
umarni sai gashi ya dawo a guje yana haki.Da
shigowar cikin fadar saiya fadi gaban sarki yace
ya
shugabana ai ba wani abu bane ke faruwa ba
face
dawowar yarima Farhama da mahaifinsa daga
dajin
shakkaful Zamral kuma sun sami nasarar kashe
dodo lasuruba har sunzo da kansa.Koda jin
wannan batu sai gaba dayan jama'ar dake fadar
suka mike zumbur suka fice waje da gudu domin
suje suga zahiri da idanunsu.Ya rage saura
sarki,fadawansa,yarima Kuzzaru da boka Zuraita
kadai zaune a fadar.Cikin tsananin tashin hankali
sarki ya dubi boka Zuraita yace yakai
amintaccena
yanzu menene abinyi?Ka sani cewa bazan iya
rabuwa da yar uwata gimbiya Siyamat ba na
bayar
da ita inda bazan sake ganinta ba kuma gashi
ban
isa na karya alkawarin dana dauka ba cewar zan
aurar da ita ga wanda yaje dajin shakkaful
zamral
ya kashe dodo Lasuruba yazo da kansa.Sa'adda
boka Zuraita yaji wannan tambaya sai ya sunkui
da
kansa cikin alamun kunya sannan yace ya
shugabana kayi sani cewa wannan al'amari yafi
gaban tunanina domin har a yanzu ina shakka ne
ace wai yarima Farhama yazo da kan dodo
lasuruba.Mu tsaya muga isowarsu nan fada
tukunna don idanunmu suga zahiri.Ai kuwa kafin
cikar dakika dari uku da hamsin saiga yarima
Farhama tare da mahaifinsa sarkin Kairufa sun
iso
fada bisa dawakansu.Yarima Farhama na dauke
da
kan dodo Lasuraba.Shi kansa wannan kai na
dodo
Lasuruba saiya zamo abin tsoro ga jama'a duk
wanda ya kallashe sau daya sai kaga ya kau da
kai
ga barin kallonsa Don gani yake kamar a
koyaushe
zai iya motsawa ya hallakar dashi.Lokacin daya
rage baifi saura taku goma ba tsakanin su
yarima
Farhama dasu sarkin kisra sai su Farhama suka
ja
linzamin dawakansu suka tsaya sannan mahaifin
yarima Farhama ya sauko daga kan dokinsa ya
dubi sarkin Kisra yace yakai wannan sarki mai
daraja kuma mai adalci na sani cewa kai mai
cika
alkawari ne saboda haka yanzu gashi dana ya
lashe wanann gasa ta auren yar uwarka gimbiya
Siyamat saboda haka saika cika alkawari ka aura
masa ita yanzu ka bamu ita mu tafi da ita izuwa
birninmu na Kairufa.Ka sani cewa wannan kai na
dodo Lasuruba yafi komai daraja a duniya a
yanzu
domin duk wanda ya mallakeshi tamkar ya
mallaki
komai da kowa ne na duniya,to amma mu bama
bukatarsa domin yar uwarka Gimbiya Siyamat
tafishi daraja a wajenmu.Yanzu gani nan gare ka
zan damka maka wannan kai domin ka cika
mana
alkwarin daka daukar mana.Koda gama fadin
haka
sai mahaifin yarima Farhama ya karbi kan dodo
Lasurba daga hannun Farhama ya nufi karagar
sarki da nufin ya damka masa.Saida ya rage
saura
baifi taku uku ba kacal ya isa gareshi sai kawai
akaga wata irin iska mai karfin gaske daga can
kololuwar sama ta sauko kasa ta sure wannan
kai
na dodo Lasuruba daga hannun sarkin kairufa
tayi
masa dashi.Nan take sarkin kairufa yayi nuni da
hannunsa izuwa ga wannan iska domin ya dawo
da kan Lasuruba ga hannunsa ya zamana cewa
shima yana amfani da tasa iskar sihirin amma sai
tasa iskar ta kasa tasiri akan waccan.Yana ji
yana
gani kan dodo lasuruba ya rinka lulukawa can
kololuwar sama har ya kule a cikin
gajimare.Koda
ganin haka sai sarkin Kairufa da yarima Farhama
suka tsandara ihu cikin bakin cikin.Daga can sai
sarkin kairufa ya dubi sarkin kisra yace yakai
wannan sarki mai daraja dajin kai kaga abinda ya
faru yanzu da idanunka,saboda haka inason kaji
tausayinmu kayi mana adalci ka bamu auren yar
uwarka gimbi
Siyamat tunda dai mun cika aiki munzo da kan
Dodo Lasuruba kowa yaga shaida.Koda jin
wannan
batu sai sarkin Kisra yayi murmushin mugunta
sannan yace tabbas kunzo da kan dodo Lasuruba
amma ai baku damka mini shi ba.Ku sani cewa
kan dodo Lasuruba shine fa sadakin yar uwata
Gimbiya Siyamat.Ta yaya kuke tsammin zan
bayar
da auren yar uwata babu sadaki?Ai abin kunya
ne
kuma abin kaskanci a gareni,saboda haka ina mai
shawartarku daku sake bazama neman wannan
kai
na dodo lasuruba ku karbo shi daga hannun
wanda ya raba ku dashi daga nan zuwa kwana
arba'in.Idan kuwa kuka kasa shike nan kun rasa
auren gimbiya.Koda jin wannan batu sai yarima
Farhama ya sauko daga kan dokinsa ya ruga
izuwa
wajen mahaifinsa ya rungumeshi kuma ya fashe
da
kuka yana mai cewa shike nan na rasa
gimbiya,na
rasa gimbiya har abada.Ganin haka ne yasa gaba
dayan jama'ar dake fadar suka kamu da tsananin
tausayin yarima Farhama domin yaga samu kum
yaga rashi.Shi kuwa sarkin kairufa saiya janye
jikinsa daga cikin na yarima Farhama ya dubeshi
cikin murmushi kuma yasa hannu ya share masa
hawaye sannan yace daina kuka yakai dana ka
sani cewa muddin ina numfashi a doron kasa
saika
auri gimbiya Siyamat.Koda gama fadin haka sai
sarkin Kairfufa ya dubi sarkin kisra a fusace yace
yakai wannan sarki ka saurari ranar da zaka rabu
da gimbiya Siyamat,rabuwa ta har abada domin
nasan abinda kake gudu kenan.Ina tabbatar
maka
da cewa shi kansa abin dogaron naka boka
Zuraita
bai isa ya hanani aurawa dana yar uwaraka
gimbiya Siyamat ba.Gama fadin hakan keda
wuya
sai sarkin kairufa ya kama hannun yarima
Farhama
yaja shi izuwa inda dawakansu suke suka hau
suka fice daga cikin fadar.Ai kuwa bayan sati
biyu
da faruwar wannan al'amari ne aka nemi gimbiya
Siyamat sama da kasa aka rasa.Koda boka
Zuraita
yayi bincike saiya gano cewa sarkin Kairufa ne
ya
turo wadansu shararrun barayin aljanu wadanda
babu kamarsu a duniya suka sace gimbiya
Siyamat
suka kaita can birnin kairufa har ma an daura
aurenta da yarima Farhama.Kuma a ranar da aka
daura auren mahaifin yarima Farhama ya rasu
sakamakon wannan rauni dake gadon bayansa.A
wannan rana yarima Farhama ya tsinci kansa a
cikin tsananin bakin ciki da kuma farin ciki.Bayan
an binne mahaifinsa ne yasa wani gwanin
masassaki ya sassaka masa gunkin mahaifinsa
dana dodo lasuruba aka kafa su a tsakiyar gidan
sarautarsa kuma ya bayar da labarin duk irin
fafatawar da sukayi da dodo lasuruba aka rubuta
shi a jikin gini kusa da wadannan gumaka
biyu.Bayan boka Zuraita yaga duk wannan
al'amari
cikin madubin tsafinsa saiya labartawa
sarki.Koda
jin haka sai sarki ya fusata ainun nan take yasa
aka rubuta wasikar yaki ya aikawa da sarki
Farhama shima sarki Farhama saiya aiko da
raddi.Saida aka kwafsa yaki sau shida tsakanin
kasashen biyu amma duk sa'adda akayi yakin
babu bangaren dake samun nasara saidai ayi
KARE
JINI-BIRI JINI har tsawon shekara shida Sarkin
Kisra bai sake ganin yar uwarsa gimbiya Siyamat
ba.Tsananin yawan tunaninta da begenta ne ya
haddasa sarkin kisra ciwon zuciya ya zama
ajalinsa.Tun daga sannan ne gaba mai tsananin
ta
sake kulluwa tsakanin sarki Kuzzaru da Sarki
Farhama.Har kwanan gobe sarki Kuzzaru bashi
da
wani buri wanda yafi ya yaki sarki Farhama ya
kawar dashi domin ya karbo yar uwar mahaifinsa
gimbiya Siyamat.Wannan shine abinda ya faru a
baya kimanin shekaru talatin da suka gabata.
*** *** ***Lokacin Da Sarkin Yaki Huzaika ya isa
gidan boka Zuraita ya sanar dashi sakon sarki sai
boka Zuraita ya kwala ihu idanunsa suka kada
sukayi jawur.Al'amarin daya firgita sarkin yaki
Huzaika kenan.Daga can sai boka Zuraita ya dubi
Huzaika yace ka koma wajen sarki ka sanar
dashi
cewa idan har yana tare da wannan yaro
Shubairu
ban isa nazo kusa dashi ba,idan kuwa nazo saina
hallaka domin yaron yana da TSATSUBA mai karfi
a jikinsa wacce duk wani mai sihirin tsafi idan ya
kusance shi zai hallaka,kuma babu tsafin da zaiyi
tasiri idain dai yana wurin.Haka kuma ka gaya
masa cewa shawarar da yaro Shubairu ya bashi
akan attajiri Ubairu itace mafi alheri a
gareshi,kawai
yayi shirin yaki ya fita ya kawar da Ubairu da
jama'asa.Wannan shine iyakar abinda zan iya
gaya
maka.Koda jin wannan batu sai sarkin yaki
Huzaika ya yiwa boka Zuraita sallama ya tafi
izuwa
gidan sarki Kuzzaru domin ya sanar dashi
bayanin
da boka Zuraita yayi...
SHIN SARKI KUZZARU ZAI FITA YA YAKI UBAIRU
DA JAMA'ARSA?
IDAN AKAYI YAKIN SU WAYE ZASU SAMI
NASARA?
YAUSHE NE SARKI FARHAMA DA SARKI
KUZZARU
ZASU SAKE HADUWA SU KWAFSA YAKI?
SHIN SARKI KUZZARU ZAI CIKA BURINSA NA
KARBO GIMBIYA SIYAMAT DAGA HANNUN
SARKI
FARHAMA?
A WANE HALI GIMBIYA SIYAMAT TAKE YANZU
BAYAN RABUWARTA DA DAN'UWANTA SARKIN
KISRA TSAWON SHEKARU?
WADANNE IRIN ABUBUWAN AL'AJABI YARO
SHUBAIRU ZAIYI NAN GABA A RAYUWARSA?
YAYA KARSHEN GABAR SARKI FARHAMA DA
SARKI
KUZZARU ZATA KASANCE?
Mu Hadu A DAKAKKIYAR ZUCIYA Littafi Na Uku
Domin Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Labari.
Anan Na kawo Karshen Dakakkiyar Zuciya Littafi
Na Biyu.Dama kamar yadda na fada muku Littafi
na daya dana biyu ne kawai suka fito kuma kuka
ce ayishi.To gashi dai mun kammala shi.Saboda
karku yimin korafi.
Dont just read and Pass.
Wai Kusa A ganinku waye ya haddasa Gaba a
tsakanin Wadannan sarakuna guda biyu?
Sarkin Kisra ko Sarkin Kairufa?
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment