Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarki yayi.Nan
yake sarki ya bude baki ya fara karanta wadansu
dalasiman tsafi a fili shi kuma Yarima Farhama
saiya bude baki yana maimaita abinda sarki ya
karanta.Faruwar hakan keda wuya sai wannan
iska
dake yi musu kawanya ta rikide ta zama
wadansu
irin gajerun dodanni yan wadanni wadanda
tsawonsu bai wuce kamu uku ba.Suna da
manyan
kunnuwa fala fala kamar na giwa.Hancinsu
wawakeke ne babu kyan gani.Haka ma
bakunansu,idanuwansu manya manya ne kwala
kwala kuma jajaye tamkar garwashin wuta.Komai
dakewar zuciyar mutum idan yayi arba da
wadannan dodanni sai ya razana musamman
idan
ya dubi murtuka murtukan kafafunsu wadanda
basu da yatsu sai kofato.Gaba daya jikin dodanni
a cike yake da wani irin gashi mai tsini tamkar
kayoyi aka sossoka.Koda sarki yayi arba da
wadannan dodanni sai yayi sauri ya zare
takobinsa
daga cikin kasa ya mike tsaye zumbur yana mai
rike da takobin da hannu biyu,shima yarima
Farhama sai yayi koyi dashi suka jingina da
bayan juna.A wannan lokaci tuni dodannin sunyi
musu
kawanya kuma adadinsu yakai dubu.cikin yanayin
damuwa sarki ya dubi yarima Farhama yace
yakai
dana kayi sani cewa a iya rayuwata ta duniya
ban
taba ganin irin wadannan dodanni ba,kuma ban
taba jin labarin irinsu ba.Saboda haka bani da
yakinin cewa zamu iya kawar dasu idan kuwa har
zamu iya din to tabbas zamu iya shan bakar
wahala kila kuma su hallaka mu.Abinda nake so
dakai shine kada zuciyarka ta karaya domin da
zarar ka sami karayar zuciya shike nan ka baiwa
abokin gaba kofar samu nasara.Lallai mu jajirce
iya karfinmu da kokarinmu a kan wadannan
dodanni domin kubutar da rayuwarmu.Kafin sarki
ya gama rufe bakinsa tuni dodannin gaba
dayansu
sun afka musu.Nanfa wuri ya yamutse aka
ruguntsume da azababben yaki,in badon sarki da
Yarima Farhama sun kasance masu zafin nama
da sadaukantaka ba da tuni dodannin sun hallaka
su
cikin dakiku kadan.Bababban abinda yafi
dugunzuma hankalin su Farhama shine ko kadan
dodanni basa jin SARA DA SUKA domin a
koyaushe ma kare hari suke da hannayensu suna
dade yanyame su sarki,da karfin damtse sarki ke
tarwatsa su suna kutsawa ta cikinsu amma duk
dodan da suka bazar a kasa sai suga ya mike
tsaye zumbur ya cigaba da kai musu hari.Abinda
ya kara daurewa sarki kai shine tsafinsa yaki yayi
tasiri bare yayi amfani dashi wajen hallaka
dodannin.Sa'adda sarki yaga an shafe rabin sa'a
ana wannan gumurzu basu sami nasarar komai
ba
akan dodanni sai hankalinsu ya dugunzuma ainun
domin ya fahimci cewa a duk lokacin da suka gaji
shida yarima sannan ne dodanni zasu sami
galaba
akansu.Koda fahimtar hakan sai hankalin sarki ya
dugunzuma amma dayaga bashi da wata mafita
sai ya dada jajircewa ya ciga da yakin iya
karfinsa.Ana
cikin fafatawar ne daya daga cikin dodannin wani
mai zafin nama da nacin tsiya ya daka tsalle a
sama ta bayan sarki ya karta masa faratan
hannayensa biyu a gadon baya.Saboda kaifin
faratan dodon saida bayan sarki ya dare jini yai
tsartuwa da feshi.Sarki dai bai san sa'adda ya
kwala uban ihu ba yayi taga taga zai fadi amma
saboda taurin rai da karfin zuciya bai fadi ba a
haka ya cigaba da yakin.Koda yarima Farhama
yaga wannan rauni da akayiwa mahaifinsa sai
zuciyarsa ta harzuka ainu shima ya zabura cikin
zafin nana ya daka tsalle sama ya tari wannan
dodo wanda ya yiwa sarki mugun rauni cikin
mugun nufi dodon ya kawowa Farhama suka da
farcen hannunsa a makoshi.Farhama ya sunkuya
dodon ya sari iska.Cikin zafin nama Farhama ya
doki tsakiyar kan dodon da kotar takobinsa.Nan
take sai yaga kan dodon ya lotse har kwakwalwa
tayi fantsama ya fado kasa matacce.Koda sarki
yaga gawar wannan dodo kuma ya fahimci cewar
ruhin dodanni a tsakiyar kansu yake sai ya cika
da
tsananin murna ya kara zage damtse ya cigaba
da
ragargazar dodannin suka rinka bajewa kasa
mattatu.Shima yarima Farhama yayi koyi dashi
cikin kankanin lokaci suka hallakar da kimanin
dodanni dari uku.Koda dodannin suka ga anyi
musu wannan mummunar barna sai suka ja da
baya gaba dayansu a lokaci guda kamar zasu
gudu
amma sai suka dunkule a waje guda kamar an
cura nakiya sannan suka rikide suka zama katon
dodo guda daya wanda tsawonsa yakai zira'i dari
fadin kirjinsa kuwa yakai kamu arba'in.Koda
dodon
ya wangame bakinsa ya kwarara uban ihu saida
dajin gaba daya yayi amsa kuwwa,bishoyoyi suka
kama rangaji suna kakkaryewa,kasa kuwa ta
kama
girgiza kamar zata rufta komai ya fada
cikinta.Koda
ganin wannan al'amari sai hankalin sarki da na
Yarima Farhama ya dugunzuma ainun domin duk
irin tsallen da zasuyi b zasu iya tabo kan dodon
ba saboda tsawonsa yayi yawan gaske bare su
sari
tsakiyar kansa inda ruhinsa yake,haka kuma ba
zasu iya kayar da dodon ba ya fadi kasa tunda
nauyinsa da girmansa yafi gaban wasa.Bayan
dodon ya gama wannan ihu da mugun gurnani
sai
ya fara taka kafafunsa ya nufi inda sarki da
Farhama ke tsaye.Duk taku daya idan yayi sai
dajin gaba daya yayi girgiza kamar zai kife
saboda
karfin takun sawunsa.Sa'adda sarki da Yarima
sukaga wannan dodo ya dora kafafunsa kai tsaye
sai sukaji kamar su yarda takubbansu su ruga da
gudu amma saboda taurin rai da DAKAKKIYAR
ZUCIYA irin ta mazajen kwarai sai suka tsaya
cak
suka cigaba da jiran isowarsa garesu.Yayin da ya
rage saura kamar taku goma a tsakaninsu sai
sukayi kukan kura suka ruga da gudu suka taro
dodon aka ruguntsume da sabon masifaffen
yaki.Sarki da Yarima suka wanzu suna masu
kaiwa dodon sara da suka cikin zafin nama
amma
saboda zafin
naman dodon yafi nasu dole suka rinka ja da
baya
baya.Duk sa'adda takubban nasu ya hadu da jikin
dodon saidai kaji kamar karfe da karfe ne suke
gogayya kuma har tarwatsin wuta ne ke
tashi.Koda
dodon yaga suna bata musu lokaCi sai ya daka
tsalle daya ya dira a gaban yarima.Kafin yarima
yayi wani yunkuri tuni dodon yasa hannu ya
mangareshi a kafada.Yarima yai tsalle can gefe
daya ya fado kasa sumamme,domin tsananin
karfin dukan ma yasa ALLON kafadarsa ya
goce.Yayin da
sarki yaga abinda ya faru ga dansa sai zuciyarsa
ta
kama tafarfasa kamar zata kone saboda
fushi.Kawai saiya takarkare ya kwarara uban ihu
irin wanda ke TARWATSA MAZA a filin
daga,sannan
ya ruga da gudu a karo na biyu ya tari
dodon.Wannan karon saiya daka tsalle ya dira
akan cinyar dodon sannan ya cigaba da tsalle a
sassan jikin dodon tamkar DAN BIRI akan bishiya
yana kokarin ya isa kan kafadarsa.Idan mutum
yaga yadda sarki ke wannan tsalle tsalle cikin
bajinta da jarumta dole ne ya sallama mishi
yasan cewa ya cika GWARZON JARUMI.Lokacin
da dodon
ya fahimci nufin sarki saiya rinka kai masa cafka
da mangari da dukkan hannayensa biyu,shi kuwa
sai ya cigaba da tsalle tsalle kan dodon yana
gocewa harin dodon.Wani lokaci saida kaga sarki
ya dira bayan dodon ko gabansa kai kace
kadangare ne ke hawa bango.Hakika al'amarin
akwai AL'AJABI a cikinsa.Da yake dodon yafi
sarki
zafin nama sai ya zamana cewa a wasu lokutan
dodon na samun damar kartar jikin sarki da kaifin
faratansa.Duk sa'adda dodon ya karci jikin sarki
sai ya zabga uban ihu sakamakon mugun zafin
da yakeji da kuma zogi.Nan da nan ko ina a jikin
sarki ya cika da raunika,jini ya rinka zuba,wannan
rauni na farko dake bayan sarki kuwa yafi dukkan
raunikan girma da rashin kyan gani.Domin shine
ma yasa sarki ya fara galabaita har yaji kamar
numfashinsa na daukewa da dawowa.A wannan
lokaci juwa ta fara daukar sarki.Al'amarin dayai
matukar girgiza hankalinsa kenan domin yasan
cewa idan har wannan dodo ya sami nasarar
hallaka shi shike nan yarima ma bazai rayu
ba,shikenan duk burinsa ya rushe.Koda gama
aiyana haka sai sarki ya kara fusata ainun ya
tabbatar da cewa dole ne yayi yunkuri na karshe
don ceton rayuwar yarima,shi kuwa tasa rayuwar
tuni ya mika wuya domin yana gani cewa abu ne
mayuwaci ya kara sa'a guda nan gaba yana
numfashi sakamakon raunikan dake jikinsa masu
yawa haka.Koda gama ayyana haka sai sarki ya
yunkura iya karfinsa daga kan cinyar dodon ya
daka wawan tsalle sama,bisa tsananin mamaki
sai
yaji ya dira akan kafadar dodon.Yana dira kamar
an tabe sifirin an sakeshi haka ya kara daka wani
tsallen sai gashi a saman kan dodon.Cikin zafin
nama na ban mamaki ya daga takobinsa da
hannu biyu ya caka a tsakiyar kansa.Take
takobin ta
nutsue cikin kan dodon,sai ga jini ya bullutso yai
tsiria sama tamkar IDANIYAR RUWA ta
bude.Kawai
sai dodon ya sulalo kasa a lokacin da sarki ya
dafe
wuyansa.Dodon ya tumu da kasa tamkar giwaye
goma sun fadi ya baje a kasa matacce.Shima
sarki saiya bake akan bayan dodon yana
KAKARIN
MUTUWA.Adaidai wannan lokaci ne yarima
Farhama ya farfado daga dogon suman da
yayi.Koda yayi arba da gawar dodon kuma yaga
mahaifinsa kwance a bayan dodon yana kakarin
mutuwa saiya yunkura domin ya mike tsaye yakai
masa dauki amma saiya kasa sakamakon mugun
zogin da yaji a allon kafadarsa.A sannan ne ya
lura
cewa kashin kafadarsa ya goce har ya kumbura
suntum,Farhama ya kurma ihu cikin tsananin
takaici ya fara kukan bakin cikinKoda yaga cewa
kuka bazai yi masa maganin komai ba sai ya fara
jan jiki da rub da ciki cikin matukar juriya har ya
isa inda dodon yake da kyar da sidin goshi ya
janye mahaifin nasa daga kan dodon sannan ya
bude jakar guzurinsa ya dauko garin magani ya
rinka shafawa a gaba daya jikin sarki.Gama
hakan
keda wuya sai jini ya daina zuba.A sannan ne
sarki ya dan dawo daga cikin hayyacinsa ya rinka
kiran ruwa ruwa..Koda jin haka sai yarima ya
taba
salkar ruwansa yaji babu komai a ciki ya taba ta
sarki dake rataye a wuyansa yaji itama babu
komai
a ciki sai hankalinsa ya DUGUNZUMA ainun.Ba
shiri ya cigaba da jan ciki yayi ta tafiya a haka
har ya riski inda wata korama take ya tsoma
bakinsa
ya fara sha,sannan ya tsoma salkarsa ya cikata
ya
juya da rubda cikin yana jan jiki har ya dawo inda
sarki yake.Da zuwa sai yaga idanun sarki sun
kafe
kuma babu inda yake motsi a jikinsa.Koda ganin
haka sai yarima ya kurma ihu ya sake fashewa
da matsanancin kuka...
Gaskiya Sarki Da Yarima Farhama sun bani
tausayi wallahi.. DAKAKKIYAR ZUCIYA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part B

KODA GANIN HAKA SAI YARIMA YA KURMA IHU
YA
SAKE FASHEWA DA MATSANANCIN KUKA.BA
zato
ba tsammani sai yaga bakin sarki ya motsa
alamar
yana fadin wani abu.Cikin tsananin murna ya
zubawa sarki ruwa a baki ya kwalkwala.Gama
shan
ruwan keda wuya sai sarki yayi ajiyar numfashi
sannan ya dubi Yarima yayi masa dan guntun
murmushi.Cikin tsananin farin ciki yarima ya
dago
sarki ya rungume shi kuma ya sake fashewa da
kukan murna bisa ganin cewa sarki bai mutu
ba.Bayan yarima ya kwantar da sarki sai ya
kama
allon kafadarsa da hannayensa biyu ya shiga
gyarawa domin ya mayar da kashin daya
goce.Kaico komai rashin tausayin mutum idan
yaga yadda yaruma ya rinka kwarara ihu a
lokacin
da yake yiwa kansa wannan gyara na allon
kafada
dole ne ya tausaya masa.Saboda tsananin zogi
da
radadin da yakeji saida ya jike sharkaf da gumi
tamkar an tsomashi a cikin kogi.Yana gama saita
kashin kafadar kuwa ya sulale kasa
sumamme.Duk
wannan abu dake faruwa sarki na kwance daf
dashi
yana kallonsa kawai amma ko motsi bazai iya ba
sai hawaye ne ke sartu a cikin idanunsa.Yarima
Farhama bai farfado ba sai bayan iska mai karfi
ta
kada.A firgice ya farka ya mike zaune ya dubi
sarki
yaga yana nan a inda yake kuma a raye.A
wannan
lokaci ne Farhama yaji raunin jikinsa ya ishe shi
da
zogi cikin hanzari ya dauko garin magani ya
shafawa kansa.Gama hakan keda wuya saiya
mike
tsaye yaje ya kafa musu tanti yayi shimfida a
ciki,sannan yazo ya dauki sarki yakai shi cikin
tantin ya kwantar dashi da rubda ciki,saboda
wannan lafcecen rauni dake bayansa.Saida
Yarima
Ya kwana bakwai yana jinyar sarki da kansa a
cikin
wannan tanti sannan sarki ya sami saukin jikinsa
har ya iya budar bakinsa yayi magana Cikin
sanyin
murya ya dubi Yarima yace yakai dana maza kayi
mana shiri mu cigaba da wannan tafiya domin
saura kwana biyar mu isa dajin shakkaful
zamral.Koda jin haka sai yarima Farhama ya cika
da tsananin mamaki ya dubi sarki a cikin alamun
karayar zuciya yace haba Abbana aini tuni na
hakura da wannan buri nawa na auren gimbiya
Siyamat domin yanzu ne na tabbatar da cewa ba
zamu iya yakar dodo Lasuruba ba har mu sami
damar hallakashi mu yanko kansa.Yanzu fa ka
duba ka gani tun kafin mu hadu da dodo
Lasuruba
mun hadu da wasu dodanni wanda basu da rabin
karfin damtsensa da rabin karfin sihirinsa amma
kiris ya rage su hallakamu.Tsananin sa'a da
nisan
kwana yasa muka tsira da rayuwarmu.Abu na
biyu
ka dubi halin da kake har yanzu fa wannan rauni
na bayanka bai gama warkewa ba kuma ko tafiya
da kafafuwanka ba zaka iya ba.Dajin haka sai
sarki
ya turbune fuska yace nifa ba rokonka nake ba
umarni na baka.Lallai ka tashi ka shirya mana
mu
cigaba da tafiyarmu nan da cikar sa'a guda.A iya
rayuwar yarima Farhama bai taba jin sarki yayi
masa magana da kakkausar murya ba irin haka
kuma cikin bacin rai don haka saiya mike sa
sauri
ya shiga kimtsawa.Kafin cikar sa'a ya gama
dukkan shirye shiryen da ya kamata.Nan da nan
ya kamo dokin sarki yazo dashi inda sarki yake
kwance ta daukeshi ya dora shi akan dokin.Don
gudun kada sarki ya fado daga kan dokin yayin
da
suke tafiya sai daya daddaure shi a jikin dokin da
igiya sannan shima ya hau nasa dokin suka bar
wannan daji suka nausa gaba.Wani abin mamaki
shine duk da cewa sarki baya ruke da linzamin
dokinsa amma kamar shine yake sarrafa
shi,domin
dokin ya jera dana yarima ko tsayawa dokin
yarima
yayi sai shima ya tsaya kuma baya yarda a sami
tazara a tsakaninsu.Haka dai suka cigaba da
tafiya
ba dare ba rana kuma basa yada zango face sun
gaji ko kuma duhu yayi yawa,babu hasken farin
wata har tsawon kana uku.Wani abin mamaki
shine
a tsawon kwana ukun basu sake haduwa da wani
mugun abu ba kuma a sannan ne sarki ya samu
lafiya sosai har ma yana iyayin komai da
kansa,saidai har a sannan raunin gadon bayansa
bai daina zogi da radadi ba,ya zame masa
tamkar
dafin maciji babu alamar zai warke gaba
daya.Bisa
dalilin haka ne sarki yayi bincike a madubin
tsafinsa a sirrance ba tare da yarima ya sani ba
ya
gano cewa wannan rauni dake gadon bayansa
bazai taba warkewa ba har abada kuma shine zai
zama SANADIYAR AJALINSA.Da ganin wannan
al'amari sai hankalin sarki ya dugunzuma ba don
komai ba sai don tsoron kada ajalinsa ya riske
shi
kafin burin yarima ya cika.Sarki yayi shiru yabar
wannan al'amari a cikin zuciyarsa bai sanar da
yarima ba.A daren wannan kwana na uku ne
suka
yada zango a bakin wata korama bayan sun
daure
dawakansu kuma sun kafa tanti sai suka kunna
wuta suka zauna a gaban wutar suna jin dumi
sakamakon sanyin dake kadawa.Tsawon yan
dakiku suna zaune dayansu baice uffan ba.Daga
can sai yarima yaga sarki ya kura masa idanu
kawai,nan da nan kwalla ta ciko a cikin idanun
nasa.Al'amarin dayai matukar girgiza hankalin
Yarima kenan ya dubi sarki cikin matukar
damuwa
yace yakai abbana ina dalilin kura mini idanu da
kayi yanzu kuma har kwalla ta cika maka idanu?
Sa'adda sarki yaji wannan tambaya sai ya girgiza
kai gami da ajiyar zuciya sannan yace yakai dana
kayi sani cewa ba wani abu bane ya sani
kallonka
da zubar wannan kwalla ba face tsananin
tausayinka bisa yadda zaka tsinci rayuwarka a
nan
gaba koda kuwa bayan ka cika burin rayuwarka
ne.Koda jin wannan batu sai yarima ya cika da
tsananin mamaki yace haba ya Abbana saboda
me
zaka ji tausayina alhalin ina cikin daula da farin
ciki a wannan lokaci?Ka tuna cewa fa babu
abinda
zan nema a duniyar nan na rasa tunda muna da
tarin dukiya kuma gamu da karfin mulki.Sannan
gashi na mallaki abar bege na.To mene ne kuma
zai dame ni a rayuwata?Lokacin da sarki yaji
haka
sai
yayi murmushi yace yakai dana kayi sani cewa
kai
yaro ne abinda na hango maka kai ba zaka iya
hango shi ba koda kuwa ka hau kan tsaunin da
yafi dukkan tsaunukan duniya tsawo.Ina
tausayinka
akan abubuwa uku amma yanzu zan iya gaya
maka guda daya,ragowar guda biyun kuwa bazan
fada maka ba saidai ka gansu da idanunka a
lokacin da babu ni.Abu na farko da nake
tausayinka akai shine a halin yanzu kana soyayya
da macen da baka san matsayinka ba a cikin
zuciyarta,kuma sau daya ka taba ganinta a
rayuwarka.Koda ka ci wannan gasa ta neman
aurenta meye tabbacinka cewar zata kaunace ka
kamar yadda kaka kaunarta?Ka sani cewa shi SO
GAMON JINI ne kuma abu ne wanda bashi da
tabbas.Ba a yiwa so dole kuma ba lallai bane
jarumtakar ka ta burge ta ba har taji tana yi
maka
so na gaskiya.Kai kuwa a yanzu kana sonta da
begenta ne saboda tsananin kyawunta kuma
tasan
don haka kake sonta sabanin yadda ni nayi
soyayya da mahaifiyarka,ya zamana cewa mun
so
juna da gaskiya ba don kyau ba ko
matsayi.Lokacin da sarki yazo nan a zancensa
sai
jikin yarima yayi sanyi,nan take yaji yana
nadamar
shiga wannan gasa ta neman auren gimbiya
Siyamat kuma yaji ya tsani komai a
rayuwarsa.Cikin takaici ya dubi sarki a lokacin da
hawaye ya subuto masa yace yakai Abbana me
yasa tun farko baka shaida min wannan al'amari
ba?Na rantse da darajar mahaifiyata idan daka yi
mini wannan bayani tun a farko da bazan shiga
wannan gasa ba.Koda jin haka sai sarki yayi
murmushi yace ai tsananin kaunarka da son
ganin
farin cikinka ne yasa naki nayi maka wannan
bayani tuntuni.Hakika da sannu zaka fahimci
mecece rayuwa a cikin wannan duniya.Nima
sa'adda nake da kuruciya irin taka na aikata
wadannan kura kuran.Yarima ya numfasa yace to
yanzu naji abu daya daga cikin abubuwa uku da
kake tausayina a kansu na kuma gamsu cewa
tabbas ni abin tausayi ne.Ina rokonka da girman
iyayenka da suka gabata da ka gaya mini
ragowar
wadannan abubuwa biyu.Sarki ya bata rai yayi
shiru bai kara cewa komai ba daga can kuma
saiya saki fuskarsa ya dubi yarima Farhama yace
yakai dana kayi sani cewa yanzu muna daf da
shiga cikin dajin shakkaful zamral tabbas nan da
kwana biyu zamu shiga farkon daji.Ka sani cewa
wannan shine karon karshe da zanyi maka
kashedi
kuma wannan ce damarka ta karshe wacce idan
kayi wasa da ita har abada ba zaka daukaka ba a
duniya.Ka sani cewa bani da burin da yayi saura
a
duniya face naga ka lashe wannan gasa ta auren
gimbiya Siyamat in yaso ko a sannan na fadi na
mutu.Babban bakin cikina shine bazanga abinda
zaku haifa ba kaida gimbiya Siyamat.Koda jin
haka
sai yarima ya dubi sarki cikin firgici yace yakai
Abbana waishin wace irin magana kake fada ne
haka?Shin kana zaton zaka rasa rayuwarka ne a
cikin wannan tafiya da mukeyi ko kuwa kana
ganin
cewa ba zaka koma gida a raye ba?Sarki ya kada
kai yace ba zan mutu ba komai gagarin da zamu
shiga kuma zan koma gida a raye.Yarima yace to
yaya akayi kasan cewa ba zakaga lokacin da zan
haihu ba?Dajin wannan tambaya sai sarki yayi
shiru baice komai ba kawai saiya mike tsaye ya
nufi cikin tanti yabar yarima zauna yana mai
binsa
da kallo cikin tsananin mamaki,zuciyarsa cike da
wasi wasi da fargaba.Kashe gari da sassafe sarki
ya tashi Yarima suka kimtsa suka hau
dawakansu
suka cigaba da tafiya suka nausa cikin dawa.Tun
safe da suka fara tafiyar dayansu baice uffan ba
har rana ta fadi a sannan ne suka sake yada
zango
a gaban wani katon dutse sukayi shimfida suka
zauna suka fara cin abinci.Bayan Yarima yayi
loma
uku saiya yi gyaran murya yace yakai Abbana
dazu
kace zakayi min kashedi na karshe amma saika
manta baka shaida mini ko na menene ba.sarki
yace kwarai kuwa na sha'afa dama ba wani abu
bane gace naja maka kunne akan KARAYAR
ZUCIYA.Na fuskanci cewa tun bayan mun fafata
da
wadancan dodanni ka sami karayar zuciya a cikin
wannan tafiya.Ya zama wajibi a gareka ka cire
dukkan tsoro,wasi wasi da fargaba a cikin ranka
kafin muyi arba da DODO LASURUBA.Ka sani
cewa
kwarin gwiwarka shine nawa,idan har zuciyarka
ta
karaya nima bazan sami kwarin gwiwar taimaka
ba.Ina son ka kasance mai DAKAKKIYAR ZUCIYA
a
koyaushe domin sai zuciyar namiji ta dake
sannan
zai iyayin abin al'ajabi wanda ya gagari sauran
maza.Yakai dana inason ka ajiye abin tarihi ya
zamana cewa ka karya alkadarin Dodo Lasuruba
domin labarin jarumtakar ka ya basu a ko ina
cikin
duniya.Koda jin haka sai yarima yaji ya kamu da
tsananin tausayin sarki har kwallah ta zubo masa
yace yakai Abbana ka sani cewa duk abinda zan
zama idan dai babu kai ba zan zama ba.Saboda
haka idan ma nayi wannan gagarumi abin al'ajabi
bazan yi alfahari da jarumtakata ba saidai da
taka,kuma nayi alkawari zansa a sassaka
gunkinka
dana dodo Lasuruba a tsakiyar gidan sarautarmu
nasa a yi bayanin duk abinda ya faru tsakaninmu
dashi a rubuce idan har mun sami nasara domin
yaya da jikokina masu zuwa su riske wannan
babban tarihi.Koda jin wannan batu sai farin ciki
ya
lullube sarki ya rungume Yarima ya kankame shi
a
kirjinsa yana mai zub da hawaye.Daga can saiya
sake shi suka dubi juna yace:-
Maybe tomorrow I will not post.Saboda zanje
wani waje insha Allah.But not really sure.Sai
abinda Allah yayi. DAKAKKIYAR ZUCIYA
Littafi Na Biyu (2).
Part C

DAGA CAN SAIYA SAKE SHI SUKA DUBI JUNA
YACE YA KAI DANA YANZU DA ZARAR MUN
KAMMALA CIN WANNAN ABINCI INA SON MU
CIGABA DA TAFIYARMU SABODA inason mu
shiga
cikin dajin Shakkaful Zamral da rana tsaka ido na
ganin ido.Bana son mu shige shi da
daddare.Dajin
haka sai yarima yace ni kuwa ina ganin cewa ai
zaifi kyau mi shiga cikin daren yadda zamu yi ta
sanda har mu isa inda dodo Lasuruba yake ba
tare
daya sani ba mu shammave shi mi yi masa kwaf
daya.(lol kaima dai Yarima Kazo da wasa.Kamar
Dodo Lasuruba ayi masa kwaf daya.)Koda jin
haka
sai sarki ya bushe da dariya sannan yace yakai
dana na fuskanci cewa ba kasan waye dodo
Lasuruba ba.To ka sani cewa komai sammakon
mahaliko Lasuruba a tafe ya kwana.Komai karfin
damtsen mahaluki jariri ne shi akan
Lasuruba.Komai malamtakar Mahaluki a tsafi
almajirin Lasuruba ne.Ina tabbatar maka da cewa
dodo Lasuruba ya wuce tunanin mai tunani ko
hangen mai hange.Babu wani abu da zaisa mu
sami nasarara a kansa face DAKEWAR
ZUCIYOYINMU da kuma imaninmu bisa yarda da
samun sa'a.Hka dai sarki da Yarima suka cigaba
da hira har suka kammala cin abincin sannan
suka
tashi suka cigaba da tafiya.Sannu sannu su
Yarima suka sake kwana suna tafiya.Lokacin da
gari yayi haske ne suka fara gyangyadi akan
dawakansu saboda bashin baccin da suka
dauka.Yarima Farhma na cikin yin wannan
gyangyadi sai yaji dokinsa yayi turjiya gami da
haniniya.A firgice Farhama ya bude idanunsa
suka
washe sarai,koda yayi arba da dajin da suke ciki
sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi sosai.Tunda
yazo duniya bai taba jin tsoro ba irin na wannan
lokaci ba.Ba komai ne ya tsorata yarima ba face
ganin yanayin dajin da suka shigo.Wani irin daji
ne
wanda ke cike da bishiyoyi,duwatsu,duhuwoyi da
ciyayi irin wanda bil'adama bai taba gani ba
domin
wadannan abubuwa suna da siffofi ne na ban
tsoro.Wasu bishiyoyin saika ha suna yiwa mutum
gizo suna sauya launi.Su kuwa duwatsun wasu
siffofin dodanni gare su wasu manyan macizai da
sauran mugayen dabbobin daji.Ashe duk wannan
abu ba komai bane face karfin sihirin tsafin dodo
Lasuruba.Ba komai ne yasa dokin yarima yayi
turjiya da haniniya ba face ganin yadda kasa ke
fafakewa da kanta tana yin wawakeken rami
wanda
zai fada ciki.Duk wannan kadan ne daga sihirin
dodo Lasuruba.Da yake sarki ne akan gaba yana
jin wannan haniniyar doki na yarima saiya
wartsake.Cikin hanzari ya sauko daga kan
dokinsa
ya zare takobi sannan ya waiga ya dubi Yarima
yace kaima sauko kabi inda duk na sauke
sawuna
kuma ka daure dokinka a nan.Ka sani cewa
rabon
da wani bil'adama ko aljan ya shigo wannan daji
shekara dari kenan.Ko shakka babu dodo
Lasuruba
ya san da shigowarmu cikin wannan daji.Babu
mamaki ma yana kallonmu kawai so yake yaga
iya
gudun ruwanmu.Koda gama fadin haka sai sarki
ya
cigaba da tafiya yana waige waige yana kallon
gabas da yamma,kudu da arewa cikin matukar
nutsuwa,kawai so yake yaga ta inda dodo
Lasuruba
zai kawo musu hari.Hakika masu iya magana
sunyi gaskiya da sukace rashin sani yafi dare
duhu,domin kuwa ashe duk wannan abu da sarki
da yarima keyi dodo Lasuruba ya ganin tun
sa'adda suka shigo dajin don haka saiya kwanta
a
kasa ya saje da kasar dajin gaba daya tamkar
babu
shi a wajen.Takan ruwan cikinsa suke tafiya su
da
dawakansu,wannan kasa data rinka fafewa kuwa
har dokin yarima ya tsorata ashe ba kasa bace
ruwan cikin dodo Lasuruba ne saboda tattakawar
da dawakansu sukayi ne yake motsawa yana
lobawa kasa yana tasowa.Haka dai sarki da
yarima
suka cigaba da tafiya a kasa bisa kafafunsu rike
da
takubba suna waige waige suka baro dawakansu
a
can baya.Koda suka iso daidai kan kirjin dodo
Lasuruba sai ya gwale manyan idanuwansu guda
guda biyu.Cikin razana sarki da yarima suka ja
da
baya domin gani sukayi kamar TAGWAYEN
TAURARI ne suka sauko kasa daga sararin
samaniya saboda tsananin hasken idanu.Duk da
cewa safiya ce saida dajin gaba ya ya sake
haskakewa da azababben haske.Nan take dodo
Lasuruba ya wangame katon bakinsa mai kama
da
kofar gari ya bushe da mahaukaciyar dariya
wadda
ta haddasa gagarumar guguwa.Yawun bakinsa ya
rinka tsiri a sama yana tururi,tururin kuma ya
haifar da zubar ruwan sama tamkar lokacin
damina
ne.Sarki da yarima suka fado daga kan kirjinsa
suka jiyo kamar daga kan dogon tsauni suka
rikito
kasa.Kafin su iso cinyar dodo Lasuruba saida
suka
shafe dakika dubu da dari biyu.A matukar
galabaice suka fado.Da kyar suka yunkura suka
mike tsaye a wannan lokaci dodo Lasuruba ya
sunkuyo kansa ya dubesu sannan ya bude baki
yace yaku wadannan manyan hatsabiban
bil'adama
kuyi sani cewa nayi matukar mamaki bisa yadda
kuka iya shigowa cikin wannan daji alhalin fiye
da
shekaru dari baya manyan jarumai da matsafa
sun
kasa shigowa.Bisa wannan dalili ne naki na
hallaka
ku farat daya.Na sani cewa babu mahalukin da
zai
saida rayuwarsa ya shigo cikin wannan daji face
don ya hallakani ya cire kaina ya tafi dashi.To
yanzu na baku sa'a guda kuyi iya kokarinku ku
datse kaina kuyi tafiyarku,idan kuwa kuka kasa
har
sa'a gudan ta cika zan hallaka ku nayi kalaci
daku.Koda gama fadin haka sai dodo Lasuruba
ya
tsuke bakinsa yai shiru kuma ya daina motsi
tamkar gunki.Koda ganin haka sai sarki ya
kwance
wata doguwar igiya daya nannade a kugunsa
sannan ya bude jakarsa ya fiddo kugiya ya daura
a
jikin igiyar sannan ya wulwula igiyar ya cillata
sama ta sakalo wuyan dodo Lasuruba.Kawai
saiya
maida takobinsa cikin kufe sannan ya kama
igiyar
da hannu biyu ya rinka hawa jikin dodo Lasuruba
domin ya isa kan kafadarsa.Koda ganin haka sai
shima yarima ya maida tasa
takobinsa cikin kufe ya kama igiyar yabi bayan
sarki,saida suka jima suna hawa igiyar har suka
gaji kuma suka jike sharkaf da zufa sannan suka
isa kan kafadar dodo Lasuruba suna ta faman
haki.Dirarsu keda wuya akan kafadar dodo
Lasuruba sai sarki ta sake zare takobinsa sannan
ya karanta wadansu dalasimai na tsafi ya tofa a
jikin takobi.Nan take takobin ta kara kauri da
kaifi
ninkin da sau uku.Cikin hanzari sarki ya karbi
takobin yarima itama ya karanta wadannan
dalasimai na tsafi ya tofa mata ta koma irin
tasa.Gama hakan keda wuya saiya mikawa
yarima
takobinsa yace muyi ta saran wuyan dodo har
sai
mun tsinke nasa kai.Nan take kuwa suka kama
wannan aiki,cikin zafin nama ba sassauci amma
duk sa'adda takubban nasu suka sari wuyan dodo
lasuruba sai suji kamar dutsen wuta suke
sara.Maimakon wuyan ya rinka darewa sai kaifin
takubban nasu ya rinka dakushewa,tarwatsin
wuya
ya rinka tashi yana haifar da tururin hayaki,shi
kuwa hayakin ya cika musu hanci da idanu suka
rinka fita daga hayyacinsu.Amma saboda naci
basu daina saran wuyan dodo Lasuruba ba har
saida takubban nasu suka ratattake kamar an
daddaga danyen ice.Bisa dole suka hakura
sukayi
jifa da ratattakun takubban suka zauna akan
kafadar dodo lasuruba suna ta faman haki da tari
kamar suyi kumallo.A daidai wannan lokaci ne
kan
dodo lasuruba ya motsa kuma ya sake wangame
katon bakinsa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment