Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kwanta. DAKAKKIYAR ZUCIYA
Littafi Na Daya (1)
Part C.

KAGA SAI KA AURAR DA ITA GA DAN SARKIN
DA
HANKALINKA YA KWANTA.SA'ADDA SARKIN
KISRA
YAJI WANNAN JAWABI NA BOKANSA SAI YA
JINJINA KAI UACE,yakai amintaccen bokana
hakika
a duniya babu abinda nake so sama da wannan
yar uwata tawa Siyamat.Saboda haka kuwa
bazan
iya aurar da ita ga inda bazan sake ganinta
ba.Da
dai nayi asarar Siyamat saidai sarkin Kairufa yayi
asarar dansa Farhama.To yanzu wace irin gasa
ce
wacce babu mai iya lashewa kake ganin zan
shiryawa manema auren Gimbiya Siyamat?
Lokacin
da bokan yaji wannan tambaya sai ya bushe da
dariya sannan yace ya shugabana abinda nake
so
dakai shine kasa a yi shela cewar kana neman
dukkan masoyan gimbiya Siyamat.Bayan sun taru
sai ka shaida musu cewa ba zaka bayar da auren
yar uwarka ba face ga jarumin dayaje dajin
SHAKKAFUL ZAMRAL ya kashe DODO
LASURUBA
ya yanko kansa yazo maka dashi.Koda jin
wannan
batu sai sarkin Kisra ya zazzaro idanu cikin
tsananin mamaki yace haba yakai amintaccen
bokana ai duk wanda yaji wannan gasa yasan
cewa
kawai bana son na aurar da yar uwata ne.Kowa
ya
san cewa fiye da shekaru dari baya babu wani
mahaluki daya ratsa ta cikin dajin Shakkaful
Zamral
ya wuce lafiya ko ya fito a raye.Kai ance ma ko
tsuntsu ma ya gifta ta saman dajin saidai akaga
ya
fado kasa matacce saboda masifar karfin maitar
dodo lasuruba.Masu bincike na duniya sun
tabbatar da cewa babu wata halitta mai karfin
damtse a wannan zamani tamkar dodo
Lasuruba.Kuma babu mai karfin Sihirinsa.Kai naji
ance ma idan mutum ya mallaki kokon kan dodo
Lasuruba zai iya hada wata gagarumar tsatsuba
wacce zai iya mallakar komai da kowa na
duniyar
nan.Ta yaya kake tsammanin cewa akwai wani
mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya shiga
cikin dajin Shakkaful Zamral har yayi arba da
dodo
Lasuruba?Sa'adda sarkin Kisra yazo nan a
zancensa sai bokan nasa ya bushe da dariya
yace
tabbas abinda ka fada gaskiya ne domin kakana
da mahaifina ma duk rayuwarsu ta salwanta ne a
cikin dajin Shakkaful Zamral don kawai suyi arba
da dodo Lasuruba su kashe shi su mallaki
kansa.Matsafa da sadaukai sama da mutum
dubu
arba'in sun hallaka a cikin dajin saboda duk
wanda
ya mallaki kokon kan dodo Lasuruba ya gana
samun sihirin tsatsuba guda dubu daya wanda
babu wanda yake da irinsu a duk fadin duniya.To
amma fa samun kan dodo Lasuruba shine babban
jidali.Koda jin haka sai farin ciki ya lullube sarkin
Misra ya amince da wannan shawara wacce
bokansa ya bashi.Ba tare da bata lokaci ba
sarkin
Kisra tasa akayi shela izuwa sauran kasashen
duniya cewar yana gayyatar dukkanin masoyan
yar
uwarsa gimbiya Siyamat.Nan da nan kuwa birnin
Kisra ya karbi bakuncin manya manyan baki na
yayan sarakai,attajirai da bokaye masu ji da
kansu
a duniya ya zamana cewa birnin gaba daya ya
cika
dasu har an rasa ma inda za'a basu masauki dole
aka rinka kai wadansu izuwa sauran biranen
kasar
da kauyuka.Da ranar taro tazo kuwa saida ya
zamana cewa har akan katangu da rufin gidajen
mutane suka rinka zama don su saurari bayanin
sarkin Kisra.Bayan taro yakai taro sai sarkin
Kisra
ya hau kan wani mumbari mai tsawon gaske a
tsakiyar babban fili na fadarsa sannan yayi
gaisuwa
ga jama'ar gari da manyan baki kuma ya nuna
farin cikinsa bisa amsa gaiyatar da jama'a
sukayi.A wannan lokaci garin gaba daya yayi tsit
tamkar babu wani mahaluki mai numfashi a
cikinsa,ba'a jin sautin komai face muryar sarki
saboda kowa ya nutsu kawai so ake aji yanayin
gasar neman auren gimbiya Siyamat.Sa'adda
sarki
ya gama jawabin gaisuwa da yiwa baki barka da
zuwa sai kuma yayi gyaran murya yace yaku
masoya yar uwata gimbiya Siyamat kuyi sani
cewa
ban taraku anan ba sai domin na sanar daku
gasar
dana shirya ta neman auren gimbiya.Daga cikin
babu wanda zai baiwa auren yar uwata face
wanda
ya shiga dajin Shakkaful Zamral ya kashe dodo
Lasuruba ya yanko kansa ya kawo mini.Koda
jama'a sukaji wannan batu sai wurin gaba daya
ya
rude da hayaniya.Nan take wasu daga cikin
masoya gimbiya Siyamat suka fara kuka domin
sun san cewa har abada ba zasu mallaketa
ba.Nan
fa suka fara sulalewa daya bayan daya suna
barin
filin fadar har ya zamana cewa babu kowa a
gaban
sarki face mutum daya jal ba wani bane wannan
jarumi face Yarima Farhama dan sarkin Birnin
Kairufa.Al'amarin dayai matukar baiwa kowa a
wajen mamaki kenan aka rinka yi masa kallon
mahaukaci.Lokacin da yarima Farhama ya
fuskanci
irin kallon da jama'a sukeyi masa saiya daga
hannunsa sama akayi shiru sannan yace yaku
jama'ar da suka taru a nan kuyi sani cewa a
cikin
masoyan gimbiya Siyamat nine kadai masoyinta
na kwarai tunda na yarda na sallama rayuwata
domin na mallake ta.Na rantse da darajar kaunar
da nake yiwa iyayena saina shiga dajin Shakkaful
Zamral na kashe dodo Lasuruba na kawo kansa a
matsayin sadakin gimbiya muddin ina numfashi a
doron kasa.Da wannan furuci nakeyi muku
bankwana lallai baza'a kara ganina ba sai ranar
dana zo da kan dodo Lasuruba.Koda gama
wannan
jawabi sai yarima Farhama ya juya ya tafi izuwa
inda dokinsa yake da zuwa yai tsalle ya dira
akan
dokin sannan ya zabureshi ya fita da gudu daga
cikin birnin Kisra,dakarun da sukayi masa rakiya
su arba'in suka rufa masa baya a sukwane.A
sannan ne jama'a suka fara watsewa masoyan
gimbiya Siyamat suka tafi izuwa kasashensu
cikin
tsananin bakin ciki suna kuka.Lokacin da Yarima
Farhama ya koma birnin Kairufa ya sanar da
mahaifinsa abinda ya faru a fadar sarkin kisra sai
mahaifin nasa ya kamu da tsananin bakin ciki ya
rungume shi yana kuka yace haba yakai dana
saboda me zakayi wannan wauta alhalin kasan
cewa abu ne wanda bazai taba
yiyuwa na?Koda jin wannan batu sai yarima
Farhama ya janye jikinsa daga cikin na
mahaifinsa
suka dubi juna a lokacin da kowannensu ke zubar
da hawaye yace yakai abbana kayi sani cewa
rayuwata bata da wani amfani muddin ban
mallaki
gimbiya Siyamat ba.Ina tabbatar maka da cewa
idan har ban auri gimbiya Siyamat ba ko shakka
babu zan iya kashe kaina.Dajin wannan batu sai
hankalin sarki ya sake dugunzuma fiye da da ya
sunkui da kansa kasa yayi shiru baice komai ba
daga can saiya dago kai ya dubi Farhama yace
yakai dana kayi sani cewa koda baka sami
nasarar
yanko kan dodo Lasuruba ba bazan bari ka kashe
kanka ba domin ta kowanne hali sai na tabbatar
da
cewa ka mallaki gimbiya Siyamat.Na sani cewa
kai
sadauki ne kuma jarumin gaske amma na ninka
ka
sau uku a komai.Nima rayuwata bata da wani
amfani muddin babu kai a wannan duniya saboda
haka lallai tare dani zakayi wannan tafiya izuwa
dajin shakkaful zamral domin na taimaka
maka.Bani da tabbacin zamu sami nasarar samo
abinda zamu tafi nema amma lallai zanyi maka
babban tanadi akan yadda zaka mallaki gimbiya
Siyamat.Koda ni na rasa rayuwata a cikin dajin
shakkaful zamral kuma zan tabbatar da cewa kai
ka koma gida a raye.Abinda nake so dakai shine
ka saki jikinka ka jirani izuwa kwanaki bakwai
domin na gama yi mana shirin wannan
gagarumar
tafiya.Koda jin wannan jawabi sai sarki ya juya
ya
shiga cikin dakin halwar tsafinsa.Kwanaki bakwai
na cika sarki ya fito daga cikin halwar tsafinsa
nan
take yasa aka shirya musu guzuri aka tanadi
kosassun dawakai guda biyu fari da baki.Cikin
gaggawa sarki da yarima Farhma suka gama
kimtsawa suka fito daga cikin gidan sarautar
suka
iso inda dawakansu suke.Da zuwa sai suka iske
Shadira mahaifiyar yarima Farhama tsaye a
wajen
fuskarta sharkaf da haye.Koda ganinta sai duk
jikinsu yayi sanyi basu san sa'adda su ma suka
fara zubar da hawaye ba suka karasa
gareta.Shadira ta ruga da gudu ta rumgume su a
tare ta fashe da matsanancin kuka.Jim kadai
saita
janye jikinta daga cikin nasu ta fuskance su tace
yaku masoyana inason ku bani amsar tambayar
da
zanyi muku yanzu.Yaya kuke tsammanin macen
data rasa mijinta da danta zaka kasance?Saboda
me zaku tafi ku barni alhalin kunsan cewa inda
zaku tafi baku da yakinin dawowa?Ta Yaya zan
iya
rayuwa a wannan duniya idan babu ku?Sa'adda
Shadira tazo nan a zancenta sai tausayinta ya
sake
turnuke sarki da yarima Farhama suka dada
kankameta a jikinsu.Daga can sai sarki ya janye
jikinsa daga cikin nata ya dubeta yace yake
matata
hakika bamu da amsa ga wadannan tambayoyi
naki amma ya kamata kiyi mana uzuri
musamman
idan kika tuno da yadda na aureki bayan nasha
bakar wahala a gumurzun gasar neman aurenki
har
na kusan rasa rayuwata.Tabbas a wannan lokaci
in
badon ina da DAKAKKIYAR ZUCIYA ba da bazan
iya yin wannan gasa ba saboda tsananin
wahalarta
da masifun dake cikinta.Amma sai gashi tsananin
soyayyarki yasa idanuna suna rufe bana ganin
wannan masifu kawai mallakarki ce a
gabana.Yau
gashi abinda ya faru a gareni a wancan lokaci
yanzu ya faru ga danki.Shin zaki so danki ya
shiga
mugun hali ko ya rasa rayuwarsa gaba daya a
sakamakon rashin masoyiyarsa?Koda jin wannan
tambaya sai Shadira tayi shiru ta kasa cewa
komai
daga can sai ta dubi sarki tace hakika bazan
hana
yarima tafiya neman auren masoyiyarsa ba
amma
ina neman alfarma daya a wajenka yakai
mijina.Lallai inason kuyi wannan tafiya tare dani
domin idan kuka tafi dajin shakkaful zamral kuka
barni a gida fargaba da tunanin halin da kuke ciki
kadai ba zasu barni na zauna lafiya ba kuma
bazan taba samun sukuni ba face naga kun dawo
lafiya cikin koshin hankali.Sarki ya kama kafadun
Shadira yace yake matata kiyi sani cewa a
matsayinki na matar jarumin sarki mai
DAKAKKIYAR ZUCIYA bai kamata ki zamo mai
fargaba ba.Yana da kyau kema zuciyarki ta
kekashe ga barin tsoron komai kuma ki kasance
mai fatan cika buri bisa duk abinda kika sa a
gabanki.Nayi imani cewa ina da sa'a domin a
rayuwata ban taba kokarin mallakar wani abu ya
gagare ni ba saboda haka ina da yakinin cewa
zamu sami nasara a cikin wannan tafiya da
zamuyi
nida yarima.Ki sani cewa duk sa'adda muka tuno
dake sai munfi kara samun kwarin gwiwa da
ZAGE
DAMTSE akan abinda ke gabanmu don tabbatar
da
samun nasararmu domin mu dawo gida a raye
mu
sake ganinki amma idan muka tafi tare dake ko
yaya wani abu ya taba lafiyarki zamu sami
karayar
zuciya ne mu kasa tabuka komai.Koda gama
fadin
haka sai sarki ya sumbaci goshin Shadira sannan
ya kama dokinsa yahau ya sakar masa linzami
yayi gaba.A wannan lokaci ne Shadira ta sake
rungume yarima Farhama ta kankame shi a
kirjinta
tana kuka kamar ba zata iya sakinsa
ba.Al'amarin
daya karya zuciyar Farhama kenan shima ya
cigaba da kukan yaji kamar ya hakura da wannan
tafiya.Da kyar dai ya danne zuciyarsa ya janye
jikinsa daga cikin nata shima ya kama dokinsa ya
hau ya tafi yana waigenta yana zubda hawaye
har
ya riski sarki suka jera sukayi ta tafiya har suka
kule Shadira na tsaye tana kallonsu tana zubar
da
hawaye sannan ta durkusa kasa bisa gwiwoyinta
ta
debi sawun dawakansu ta shinshina a lokacin da
hawaye ke sartu bisa kumatunta.Sarki da Yarima
Farhama suka nausa cikin daji sukayi ta tafiya ba
sassauci su kutsa nan su fita can har rana ta
fadi
magriba ta doso basu hadu da wani mugun abu
ba.Sau daya ne ma sukaga giftawar wata
kuta.Koda kurar tayi musu kyakkyawan kallo
guda
daya sai ta kau dakai tabi wata hanyar daban ta
nausa can cikin dawa.Yayin da sarki yaga
magriba
ta doso kai kuma gashi dawakansu sun fara
gajiya
suna tafiyar sassarfa saiya shawarci yarima dasu
tsaya su yada zango..
Note: wannan littafin ba "Bakin Yamutsi" bane
but an danyi extract dinsa a cikin littafin kamar
yadda akayi extract din "Kasuwar Rayuka" a cikin
Wasikar Jini. DAKAKKIYAR ZUCIYA!!!
Littafi Na Daya (1)
Part D.

SAIYA SHAWARCI YARIMA DASU TSAYA SU
YADA
ZANGO.BA TARE DA GARDAMAR KOMAI BA
KUWA
YARIMA YA KARBI WANNAN SHAWARA SUKA
KARASA KARKASHIN WATA BABBAR BISHIYA
SUKA
SAUKA SUKA DAURE DAWAKANSU SANNAN
SUKA
JE CIKIN WATA Fadama dake kusa da bishiyar
suka debo ruwa suka shayar da dawakansu
sannan kuma suka kafa tanti suka shiga ciki
suka
zauna.Nan dai suka bude jaka suka dauko
abincin
guzuri suka kama ci suna cikin wannan hali
tsawon dakiku dayansu baice kala ba daga can
sai
yarima Farhama ya dubi sarki yace yakai Abbana
tun ina yaro nake jin labarin dajin Shakkaful
Zamral wai shin a ina wannan daji yake ne?kuma
daga nan zuwa can tafiyar kwana nawa ce?
Sa'adda
sarki yaji wannan tambaya sai yayi murmushi
yace
yakai yarima ai daga nan ma inda muke zuwa
dajin shakkaful zamral tafiya ce ta kwana arba'in
da daya.Amma zan yi kokari na gajarce mana
nisan tafiyar da karfin sihirina izuwa kwana
ashirin
da daya.Koda jin haka sai yarima Farhama ya
dubi
sarki cikin mamaki yace to waishin me zai hana
ka
kirawo wani aljani daga cikin hadimanka ya
dauke
mu ya kaimu can a cikin kankanin lokaci tunda
ka
taba gaya mini cewa kana da wani hadimin aljani
wanda yake iya shafe tafiyar kwana arba'in a
cikin
sa'a hudu.Sarki ya sakeyin murmushi a karo na
biyu yace ai a halin yanzu duk duniya babu wani
aljani daya isa yama doshi hanyar data nufi dajin
shakkaful zamral komai karfinsa da karfin
sihirinsa.Ida kuwa yayi gangacin hakan take zai
narke ya babbake saboda karfin sihirin tsaron
dake
dajin.Bisa wannan dalili ne ya zama wajibi a
garemu muyi wannan tafiya akan doki.Ka sani
cewa dajin shakkaful zamral yayi iyaka da birane
biyu wato birnin Askan da birnin Nurhil kuma
tsakaninsa da kowane birni akwai tazara ta
manyan dazuzzuka guda uku uku.Yanzu wannan
hanya da muka biyo zamu bi ta cikin birnin
Askan
ne sannan mu ratsa wadannan dazuzzuka guda
uku mu riski dajin shakkaful zamral.Ina san ran
cewa zamu isa birnin Askan nan da kwana goma
sha biyar inda nake zaton zamu fuskanci matsala
shine a cikin birnin Askan domin na sami labari
cewa basa bari bako ya shiga cikin garinsu kuma
sarkinsu gawurtaccen jarumi ne sadaukin
gaske.A
tarihin rayuwarda ma ba'a taba cinsa da yaki
ba.Saboda haka ya zama dole a gare mu mu
shiga
birnin Askan ta kowane hali koda yaki zai barke a
tsakaninmu dasu domin babu wata hanya da
zamu
iya bi mu isa dajin shakkaful zamral face tanan
sai
kuma ta cikin birni Nurhil.Shi kuwa birnin Nurhil
gaba daya ba awannan nahiya tamu yake ba
yana
can nahiyar birnin Hindu ne idan dai munason mu
shiga ta cikinsa sai munyi tafiyar kwana dari da
hudu kuma masifun dake cikin dazuzzukan
waccan
nahiyar sun ninka wadanda ke wannan nahiya
tamu sai goma.Sa'adda sarki yazo nan a
zancnesa
sai hankalin yarima Farhama ya dugunzuma
ainun
ya tabbatar da cewa aikin dake gabansu ya wuce
gaban misali.Kuma abu ne mayuwaci ma su sami
nasara bisa abinda ya baro su daga gida.Cikin
sanyi jiki yarima Farhama ya dauki battar ruwa
ya
kwankwada sannan ya kishingida domin ya huce
gajiyar tafiya fuskarsa cike da alamun
damuwa.Koda ganin haka sai sarki ya matso
kuwa
dashi ya dafa kafadarsa yace yakai dana inason
ka
sani cewa FADUWAR GABA ASARAR NAMIJI
ce,gwarzon namiji baisan tsoro ba ko fargaba ba
kuma shine mai DAKAKKIYAR ZUCIYA ta
tunkarar
kowane irin bala'i.Abinda nake so dakai shine
kada
ka kuskura ka cire rai ga tsammanin samin rabo
daga cikin zuciyarka.Lallai ko yaushe ka kasance
namiji mai DAKAKKIYAR ZUCIYA da kunar bakin
wake domin har abada matsoraci bashi zama
gwani.Gama fadin hakan keda wuya sai shima
sarki ya sami wuri ya kwanata.Kwanciyarsa keda
wuya saiya fara gyangyadi don haka sai ya dubi
yarima Farhama yace yakai dana zanyi bacci
izuwa
wani dan lokaci saboda haka saika zauna kayi
tsaron lafiyarmu idan na farka sai kai ma ka
kwanta ka matse.Nan take sarki ya cigaba da
bacci abinsa.Shi kuwa yarima Saiya mike tsaye
ya
fito wajen tantin domin ya dan wasa
kafafunsa.Fitowarsa keda wuya saiya hango
wata
tsaleliyar budurwa a can nesa kadan daga inda
yake.Tana sanye da wata farar riga sol mai
shara
shara wacce ke bayyana surar jikinta gaba
daya.Duk da cewa duhu ya fara a wannan lokaci
saida yarima yayi arba da kyakkyawar fuskar
buduwar.Ai kuwa yana yin arba da ita saiya cika
da tsananin mamaki domin ba wata bace face
wacce yake bege DARE DA RANA wato gimbiya
Siyamat.Kawai sai yaga tayi masa murmushi
kuma
ta yafitoshi da hannu tana mai kiransa a lokacin
data juya baya ta nausa cikin daji.Ba tare da
yarima Farhama ya yanke shawara da zuciyarsa
ba
kawai saiya falfala da gudu yabi hanyar da
gimbiya
Siyamat ta bi.Duk da cewa yana falfala gudun
tsiya
amma sai ya kasa riskarta kuma gashi yana
hangota a gabansa tana dada shiga cikin wani
bakin surkuki.Hakika SO makaho ne saboda
tsananin son da yarima Farhama ke yiwa gimbiya
Siyamat ko kadan baiyi mamakin ganinta ba a
cikin wannan daji bare yayi tunanin ko ba itace
ba.Haka ya cigaba da binta da gudu har ta isa
gaban wani katon tsauni wanda aka gina
matattakalar bene a kansa.Siyamat ta cigaba da
hawa kan tsaunin tana taka matattakar shima
gogan naka saiya hau kan matattakalr ya cigaba
da
binta har ya kure matattakalar ya iso kan saman
tsaunin kawai sai yaga wadansu kyawawan
kuyangi
a gaban wani kerarren gida wanda aka gina shi
da
zallan dutsen murjani.Gaba dayan kuyangin na
rike
da kwando kuma kowane kwando a cike yake da
wani jan fure mai kamshi.Koda gimbiya Siyamat
tazo zata gifta ta tsakiyar kuyangin sai suka
rinka
watsa mata wannan fure mai kamshi.Ba tare da
shakkar komai ba shima
Yarima ya ratsa ta tsakiyar kuyangin.Bisa
mamaki
sai yaga shima kuyangin sun kama watsa masa
wannan fure mai kamshi.A wannan lokaci ne
gimbiya Siyamat ta tsaya cak a inda take har
yarima Farhama ya iso daf da ita tana yi masa
wani irin tattausan murmushi mai rikita zuciyar
'da
namiji.Da isowarsa daf da ita sai ta kama
hannunsa taja shi suka kunna kai izuwa cikin
wannan gida.Da shigarsu cikin gidan sai kan
Yarima Farhama ya juya ya zama cikakken dan
kauye ya kama kalle kalee domin tun da yazo
duniya bai taba ganin gida mai kayan kawa ba
kamar wannan.Koda ya kwatanta fadar
mahaifinsa
da wannan gida sai yaga bambancin a bayyane
yake kamar birni da kauye ne.Komai na cikin
gidan
anyi shine da zallan zinare sai sheki da walwali
suke.Hadimai kuwa gasu nan ba adadi sai kai
kawo suke,Siyamat ta cigaba da jan Yarima
Farhama har saida suka ratsa ta cikin kofofi
goma
sha biyu sannan suka iso cikin wata katuwar
fada
wadda ta kawatu ainun fiye da ko'ina a gidan.Da
shigarsu cikin wannan fada sukayi arba da wani
santalelen kyakkyawan saurayi zaune akan
karagar
mulki.Nan take Siyamat ta kufce hannunta daga
cikin na Yarima ta ruga da gudu izuwa ga
wannan
saurayi.Adaidai wannan lokaci ne wata irin iska
mai
karfi ta cika fadar ta banko kofar shigowa da
tagogin fadar duka suka bame.Ba zato ba
tsammani sai yarima Yaga wannan saurayi da
gimbiya Siyamat sun rikide izuwa siffar wadansu
munanan aljanu masu matukar kwarjini da ban
tsoro kuma suka bushe da dariyar mugunta.A
sannan ne Yarima Farhama ya dawo cikin
hayyacinsa ya gane cewa tarko ne wadannan
aljanu suka dana masa ya fada suka ribace shi
da
siffar masoyiyarsa suka janyo shi izuwa cikin
wannan gida.Al'amarin daya matukar dugunzuma
hankalinsa kenan,saboda sanin cewa bashi da
wani karfin sihiri wanda zai iya tunkarar aljanu
yayi
fada dasu.Kawai sai yaji zuciyarsa tana maiyi
masa
tambaya waishin menene dalilin da yasa sarki bai
bani sihirin tsafinsa ba domin na kare kaina bisa
irin wannan rana?Yanzu gashi ya kusa da ni waye
zai kare ni daga sharrin wadannan mugayen
aljanu?Gama ayyana hakan keda wuya sai daya
daga cikin aljanun ya dakawa yarima tsawa yace
yakai wannan dan sarki kayi sani cewa yau
shekara shida kenan muna jiran zuwan wannan
rana da zamu sami damar kamaka domin mu
dauki fansar abinda mahaifinka yayi mana.Lallai
yau sai munyi maka mugun kisan gilla irin wanda
ba'a taba yiwa wani bil'adama ba domin mu
kawar
da bakin cikin zuciyarmu.Ka sani cewa a dalilin
mahaifinka mun rasa dukiyarmu,iyayenmu da duk
danginmu.Sannan mun rasa mulkinmu a kasarmu
saboa kawai mun bata masa wani aiki daya
umarcemu dayi,wanda muka bata shekaru uku
muna wahala akan aikin.Yanzu mu bamuga
tsuntsu ba kuma bamu ga tarko ba don haka
bamu da sauran buri wanda yafi mu cusawa
mahaifinka bakin cikin da har ya mutu bazai
daina
jin radadinsa ba.Ka sani cewa tun kana jariri
muke
kai maka hari domin muga bayanka mu hallaka
ka
saida muka kai maka hari sau saba'in da bakwai
babu nasara.Saboda mahaifinka ya tsareka da
sihirin tsafi kuma daga baya ne muka gano cewa
tsafin ba a cikin jikinka yake ba a cikin harabar
gidan sarautar yake.A kullum bamu da burin da
yafi muga ranar da za'a fito da kai dagta cikin
gidan sarauta ya zamana cewa mahaifinka baya
kusa da kai amma hakan bata samu ba sai
yau.Yanzu take zamu gididdibaka muyi gutsun
gutsun da sassan jikinka,kanka ne kadai ba zamu
daddatsa ba domin mahaifinka ya shaidaka ya
kamu da irin mugun bakin cikin da muma muka
dandana.Gama fadin hakan keda wuya sai
Aljanun
biyu suka bude fukafukansu sukayi sama suka
yiyo
kan Yarima Farhama da nufin su yagalgala shi da
kaifin faratan hannayensu da kafafunsu.Ba tare
da
fargabr komai ba Farhama ya yunkura cikin zafin
nama ya zare takobinsa ya tare su aka fara
azababben yaki.Al'amarin dayai matukar baiwa
Aljanun biyu mamaki kenan domin a zatonsu
cikin
farat daya zasu hallakashi sai gashi sun kasa
koda
lakutar jikinsa,shi kuma yana ta saran jikinsu
amma kamar dutse yake sara.Duk sa'adda
takobin
Farhama ta hadu da jikin aljanun saidai kaji kara
kal.Kamar haduwar karfe da karfe sannan kuma
tartsatsin wuta ya rinka fantsama.Saida aka
shafe
sa'a biyu cif ana wannan gumurzu tsakanin
yarima
Farhama da wadannan aljanu biyu har ya
zamana
cewa Yarima Farhama ya fara gajiya.Babu
abinda
ya batawa aljanun rai face ganin yadda idan
suma
suka sari jikinsa da faratansu sai suji kamar
dutse
suka sara saidai karfin dukan nasu yana kaishi
kas,amma kafin su turmushe shi sai kaga yayi
wuf
ya mike tsaye an cigaba da fafatawa.Koda
aljanun
suka fahimci Farhama ya fara gajiya sai suka
cika
da murna domin sun san cewa da zarar ya
galabaita ainun zasu iya turmushe shi da karfin
tsiya su murde masa wuya ya mutu.
SHIN WADANNAN ALJANU ZASU SAMI NASARAR
HALLAKA YARIMA FARHAMA?
IDAN SARKIN YAKI HUZAIKA YAJE YA ISAR DA
SAKON SARKI KUZZARU GA BOKA ZURAITA
WANE
BAYANI ZAIYI MASA?
ME ZAI FARU TSAKANIN SARKI KUZZARY DA
ATTAJIRI UBAIRU WANDA YAZO DA MUGAYEN
BAKAKEN ALJANU DOMIN A BAJE BIRNIN
KISRA?
SHIN YARIMA FARHAMA DA MAHAIFINSA SUNA
SAMUN NASARAR KASHE DODO LASURUBA HAR
SU YANKO KANSA SU KAWOWA SARKIN KISRA
A
MATSAYIN SADAKIN YAR UWARSA GIMBIYA
SIYAMAT?
Mu Hadu A DAKAKKIYAR ZUCIYA Littafi Na Biyu
Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Labari.

DAKAKKIYAR ZUCIYA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part A.

LOKACIN DA AKA CIGABA DA BAKIN GUMURZU
TSAKANIN YARIMA FARHAMA DA WADANNAN
MUGAYEN ALJANU GUDA BIYU,har izuwa tsawon
dan lokaci sai yarima Farhama ya gaji ainun bai
san sa'adda takobin hannunsa ta subuce masa
ba
ta fadi kasa.Nan take daya daga cikin aljanun ya
shammace shi ya buga masa wawan dundu a
baya
nan take Farhama ya kife a kasa da rub da ciki
yana aman jini a lokacin da yaji kamar an
kakkarya
kasusuwan bayansa saboda karfin dundun da
akayi
masa don haka ko kyakkyawan motsi baiyi ba
tamkar ya zama gawa.Koda ganin wannan
gagarumar nasara sai aljanun suka cika da
tsananin farin ciki.A lokaci guda duk su biyun
suka
yunkura izuwa kan yarima Farhama da nufin su
tsintsinka shi filla filla.Kwatsam ba zato ba
tsammani sai sukaji an sarewa kowannensu
hannu
dai dai.Take hannayen nasu suka gutsure sukayi
tsalle gefe daya a lokacin da jini ya kama feshi
daga cikin dungulmin hannayen nasu suka kurma
uban ihu a lokaci guda.Koda sukayi arba da
wanda
yayi musu wannan muguwar barna sai suka rikide
izuwa guguwa take gaba dayan tagogin fadar
suka
bubbude wannan guguwa ta fice fit ta cikin taga
guda.Wani irin gagarumin ihu na biye da guguwar
suka bace bat gaba daya.Saiga guntulallun
hannayen aljanun biyu nata daka tsalle a gefe
daya
tamkar ruhin aljanun a jikinsu yake.Ba wani bane
ya sare hannayen wadannan aljanu ba face
mahaifin yarima Farhama.A gigice mahaifin nasa
ya ruga izuwa inda yarima Farhama ke kwance
yana amon jini ya sureshi ya aza shi a kafadarsa
sannan ya ruga da gudu ya nufi kofar fita daga
fadar.Yana isa gaban kofar ya sa kafarsa ya
banke
kofar,duk da cewar kofar fadar katuwar gaske ce
kuma mai kaurin tsiya ta bakin karfe saida ta
karye ta fadi kasa rikica.Sarki ya fice ta cikin
kofar a
guke dauke da yarima a kafadarsa.Kafin kiftawar
ido tuni sarki ya gama fice daga cikin gidan gaba
daya har ya iso can inda suka kafa tantinsu.Cikin
hanzari sarki ya shigar da yarima Farhama cikin
tantin ya kwantar dashi sannan ya bude jakar
guzurinsa ya dauko wani garin magani ya jika da
ruwa ya dura masa a baki ya hadiye da
kyar.Faruwar hakan keda wuya sai yarima
Farhama
ya farfado daga dogon suman da yayi.Koda ya
bude idanunsa yayi arba da sarki a gabansa sai
ya kawo gwauron numfashi ya ajiye.A wannan
lokaci
ne sarki ya dubeshi a fusace yace yakai yarima
saboda me kabar harabar wannan inda muka
kafa
tantinmu har ka fada cikin tarkon wadannan
tsofaffun makiya nawa?Koda jin wannan tambaya
sai yarima ya sake yin ajiyar zuciya yayi shiru
baice komai ba har saida ya suri battar ruwa ya
kwankwada sannan ya dubi sarki yace ka
gafarceni
yakai Abbana ka sani cewa tabbas wadannan
makiya naka yaudarata sukayi,dayansu yazo mini
a
cikin siffar masoyiyata gimbiya Siyamat yajani
har izuwa cikin wannan gida nasu dake kan
tsauni.Koda jin haka sai sarki ya gyada kai yace
hakika kana da tsawon kwana a duniya domin in
badan na farka daga baccina ba naga babu kai
nayi binciken inda kake a cikin madubi tsafina da
tuni wadannan abokan gaba nawa sun gama
hallaka ka.Ko dan gaba kada ka sake barin inda
duk muka yada zango ba da umarni na
ba.Sa'arka
daya na baka sihirin tsafina guda daya a cikin
abincin da muka ci dazu ya ratsa dukkan jini
jikinka.In badon hakan ba da tuni aljanun sun
hallaka ka farat daya tun sa'adda kuka fara
wannan
gumurzu.Koda jin haka sai yarima Farhama ya
kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yayi
murmushin murna yace ina godiya a gareka yakai
ABBANA bisa ceton rayuwata da kayi.Dajin haka
sai sarki ya rungume yarima Farhama cikin farin
ciki yace ai aikina ne na tsare lafiyarka da
rayuwarka don ganin ka cika burin rayuwarka.A
cikin wannan tanti sarki da yarima Farhama suka
kwana.washe gari kuwa da sassafe suka mike
sukayi shiri suka cigaba da tafiya bayan sunyi
lakaci.Tsawon rabin sa'a suna tafe dayansu
baice kala ba kuma basu hadu da wani mugun
abu
ba.Daga can sai Yarima Farhama yayi gyaran
murya ya dubi sarki yace yakai Abbana waishin
menene ya haddasa gaba tsakaninka da
wadannan
aljanu guda biyu wadanda sukayi yunkurin hallaka
ni domin su dauki fansar abinda kayi musu?
Sa'adda sarki yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar
zuciya yace yakai dana kayi sani cewa wannan
labari ne mai tsawon gaske ka tambayeni.Domin
daga nan har izuwa karshen wannan tafiya da
zamuyi bazan iya gama labarta maka shi ba.Kayi
hakuri nan gaba idan muna raye zan baka labarin
komai bayan burinka ya gama cika.Gama fadin
hakan keda wuya sai sarki ya tsuke bakinsa yayi
shiru bai kara cewa komai ba suka cigaba da
keta
dazuzzuka.Sannu sannu bata hana zuwa saidai a
dade ba'a je ba.Haka dai su yarima Farhama
suka cigaba da ratsa dazuzzuka iri iri har tsawon
kwana
tara,duk sa'adda suka gaji ko kuma idan dare ya
riske su sai su tsaya su yada zango in yaso da
safe sai su cigaba da tafiya.Tsawon wadannan
kwanaki tara basu sake haduwa da wani mugun
abu ba.Da yammacin kwana na tara ne suka
shigo cikin wani irin mugun daji mai sarkakiua da
duhuwoyi.Hakika dajin yana da matukat kwarjini
da
ban tsoro.Da shigowarsu cikin farkon dajin sai
sarki ya rage saurin tafiyarsa kuma ya zaro
takobinsa daga cikin kufenta yana duban gasab
da yamma kudu da arewa.Koda ganin haka sai
shima
yarima Farhama yayi koyi da abinda sarki
yayi.Nan
take suka fara jin wani irin gurnani ya cika dajin
gaba daya kuma suka rasa ta inda gurnanin yake
fitowa,sannan suka rinka jin hucin wata irin iska
tana gifgiftasu tana kai kawo kuma tana yi musu
KAWANYA.Koda ganin haka sai sarki ya dubi
yarima yace dashi yakai dana ka nutsu duk
abinda
kaga nayi kayi koyi dani.Koda gama
Fadin haka sai sarki ya duro kasa daga kan
dokinsa ya tsuguna bisa guiwoyinsa kuma ya
cake takobinsa a cikin kasa.Cikin hanzari yarima
Farhama yayi duk wannan abu da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment